DAN ASALI COMPLETE BY SHATU

DAN ASALIN COMPLETE BY SHATU

 

*D’AN ASALI….!*🤴🏻

 

 

_*NA*_
*_UMMI A’ISHA_*

 

 

 

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K’AI

_

 

*1*

 

*** Cikin tsawa tareda fushi dattijon ya daka mata wata tsawa mai firgitarwa,

 

“Ke Sadiya ba na hanaki kula wannan yaron marar asali ba? Ba na hanaki kula d’an haram ba, yaron da bashida uba baida asali ba asan mahaifinsa ba? Wuce ki shiga gida ko kuma in b’atar miki anan…”

 

Da gudu matashiyar budurwar wadda aka kira da Sadiya ta juya ta shige cikin gida tana zubar da hawaye,

 

Juyawa dattijon yayi wanda abisa dukkan alamu shine mahaifinta ya kalli saurayin dake tsaye da ita,ya nunashi da yatsa,

 

“Kai kuma ina gargad’inka da kakkausar murya karka kuskura kasake kula ‘yata, ko so kake itama ka lalata min rayuwarta kamar yadda mahaifiyarka ta lalata tata rayuwar? Daga yau sai yau idan ka kuskura kasake shiga harkar Halimatu sai na sa an d’aureka d’auri na har abada…”

 

Fuuuhhhh ya wuce zuwa cikin gida yabar saurayin atsaye cikeda damuwar irin tozarcin da yadade yana yimasa.

 

Afusace mahaifin Sadiya ya shiga cikin gida,zaune ya isketa acikin falon gidan rakub’e jikin mahaifiyarta tana faman gurshek’en kuka,

 

“Halima yanzu akan na kori wancan yaron marar asali shine kikazo kina kuka? Akan yaron da ba asan asalinsaba? Akan dan karuwa? To bari kiji ko zakiyi kukan jini bazan aura miki shiba mutuk’ar ina raye”

 

“Haba alhaji meyasa zakace haka? Yaran nan tunda suna son junansu ya kamata ka tsaya ka zama mai adalci ka aura musu juna ka daina tozarta wannan yaron haka…” Mahaifiyar Sadiya tace cikin sanyin murya,

 

Dakatar da ita yayi,

 

“Ya isa haka hajiya binta, wannan maganar ba taki bace tawace, a matsayina na mahaifin Halima mutuk’ar na aurar da ita ga yaron da bashida asali banyi mata adalci ba dan haka dole ta rabu da wannan yaron wanda yake marar uba kuma d’an haram, taje takawo min wani wanda yake d’an halak kuma D’AN ASALI sai in aura mata shi”

 

Wucewa yayi yafita daga falon ya shige cikin Part dinsa yana cikeda b’acin rai.

 

 

D’ago da Sadiya mahaifiyarta tayi tafara lallashinta,

 

“Halimatu kinji abinda mahaifinki ya fad’a dan haka ki rabu da yaron nan kiyiwa mahaifinki biyayya saboda sanin kanki ne mahaifinki yana sonki kuma yana son farin cikinki”

 

Idanuwan Sadiya suna tsiyayar da hawaye ta kalli ummanta,

 

“Umma wallahi ina son Aliyu, bazan iya rabuwa dashiba, Aliyu bashida laifi ko kad’an…”

 

“Wannan shine abinda mahaifinki yakasa ganewa Halimatu, ya kasa fahimtar gib’in ba daga gareshi yake ba daga iyayensa ne..”

 

Wani kuka Sadiya ta saka ta tashi ta fad’a cikin d’akinta, ta kwanta saman tamfatsetsen gadonta taci gaba da risgar kuka tana tuna farkon had’uwarta da Aliyu.

***

K’arfe 3:30 daidai na yamma agogon dake d’aure a tsintsiyar hannunta yanuna sauke idonta tayi ta mayar da hankalinta izuwa tuk’in da takeyi duk da cewar dakyar take iya yin driving din sakamakon taurin da sitiyarin motar yayi banda wata yar kara da take fitowa daga can injin motar,

Gaf da babbar kasuwa wato (central market) taja burki domin abisa dukkan alamu motar tana bukatar adubata, sauke glass din motar tayi ta tambayi wasu mutane wadanda ke zaune inda zata samu bakanikai domin duba mata lafiyar motarta, sake kunna motar tayi wadda dakyar ma tatashi bayan mutanen sun kammala yimata kwatance,

Ta cikin kasuwar tabi harta samo inda bakanikan suke awani kebantaccen wuri, tura hancin motarta tayi ciki tasamu wuri tayi packing sannan tafito,

Da d’an sauri daya daga cikin bakaniken yanufota yana yimata sannu da zuwa tareda tambayarta abinda yasamu motar tata,

Saida ta dan yatsina fuska sannan cikin sanyayayyiyar murya ta amsa masa,

“Sitiyarin ne yayi tauri gashi tana dan yin wata irin kara…”

“Ok to karaso za aduba miki ita yanzu,sai dai kuma sai kin dan jira saboda wanda zai gyara mikin wani aikin yakeyi…”

“Yawwa nagode”

Tafada gamida komawa jikin motarta ta jingina tana bin bakanikan da kallo daya bayan daya aranta kuma tana jinjina basirarsu gamida hazaka domin suna gyara abinda basune suka keraba,

Tafi minti 20 atsaye ganin shiru yasata nufar wurin wanda akace shine zai duba mata motar duk da bata gane waye aciki ba domin su ukune awurin dukkaninsu suna sanye da blue din kaya riga da wando, biyu suna tsaye yayinda dayan wanda bata hangoshi shikuma yana karkashin motar yana gyara,

Adan fusace takarasa wurin tana siririn tsaki,

“Bayin Allah ya kuka barni atsaye ne inata jiranku…?”

“Kiyi hakuri hajiya bamu karasa wannan din bane amma yanzu zamu gama” d’aya daga cikinsu yabata amsa,

“Bawan Allah da ka taimaka min kazo kaduba min inyaso ko ba ayi gyaran dukanba sai intafi saboda sauri nake”

“Ai bamune masu dubawaba, ga mai dubawa nan” yakarasa zancen yana nuna mata wanda ke karkashin motar da dan yatsanshi,

Matsawa tasake yi domin yiwa na karkashin motar magana,

“Dan Allah nace ko zaka zo ka duba min saboda ina saurine”

Shiru taji yayi mata bai amsa ba nan tasake maimaitawa wai ko baiji bane amma still yasake banza da ita,

“Oga tana magana, wai ko zaka taimaka ka dan duba mata motarta” wani daga cikin na tsayen yayi magana,

“Tabari sai nagama tukunna kuma lokacin salla ma gashi yayi so sai nayi salla”

Haushi ne yazo mata har wuya dan haka cikin takaici tace,

“Malam idan gyaran bazai samuba is better kasanar dani sai inje innemi wani wurin agyara min tunda baku kadaine kuka iya gyaranba bare ku tsaya kuna jawa mutane aji…”

Yanda tafara maganarta harta diga aya bai ko tanka mataba asalima ko hango fuskarshi batayiba balle tagane ayanayin da yake,

Sauran bakaniken dake tsaye awurinne suka soma bata hakuri akan karta tafi ta jira azo agyara mata,

Cikeda bacin rai tajuya takoma wurin motar, tana kokarin budewa tashiga daya daga cikin bakanikan yazo ya dakatar da ita tahanyar bude gaban motar tata yasoma dubawa, ciki tashiga tazauna tana dan hucin takaici tareda kai idonta kan agogon hannunta wanda tuni har karfe hudu da rabi takawo jiki, dan siririn tsaki tasaki,

Kamar wadda akace ta kalla tana daga idonta ta hangoshi yana kokarin fitowa daga karkashin motar da yake, har ta dauke idonta tasake mayarwa domin tana son ganin waye shi sannan dame yakeji wanda har yake yiwa mutane kallon baku isaba……..

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
*HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…*🤴🏻

 

*_NA_*
*_UMMI A’ISHA_*

 

 

*2*

 

***Zuba masa idanu tayi tana kallonshi, wankan tarwada ne dan dogo fuskarshi tana dauke da manyan idanuwa sannan yanada dan gemu kadan madaidaici bamai yawaba, dauke kanta tayi tana jan tsaki,

Can tasake kallon wurin yanzu baya wurin yana can gefe yana yin alwala, wani dan gefe can taga yatafi yashimfida abin salla wanda da alama an tanadi wurinne domin surinka yin salla,

Tana nan zaune cikin motar tacika tayi fam ta hangoshi yana tahowa bayan ya idar da sallar yana tafe yana gyara agogon fatar dake hannunshi,

Motarta yadoso direct yazo ya tsaya kusa da abokin aikinsa yafara duddubawa,cikin muryarshi marar amo taji yana yiwa dayan magana, zuwa wurinta dayan yayi yace tafito zai tada motar, handbag dinta ta dauka takoma waje ta tsaya tana kallonsu,cikin mintunan da basu goma ba taga dayan yafito daga cikin motar ya nufo wurinta,

“Yawwa hajiya an dan gyara yanzu zaki iya tafiya amma gobe sai kin dawo ankarasa domin fita zaiyi yanzu shi ogan namu”

“Ok babu damuwa nawane kudin gyaran?”

Daga murya yayi domin tambayar ogan nasu,

“Oga…. Wai nawa ne kudin gyaran”

Baiko juyoba sai nuni da yayi masa da hannu alamar yabari sai gobe idan ankarasa gyaran,

Hakan da yayine yakara bata haushi domin taga kamar iyayi yayi masa yawa,

“Shikenan nagode, sai goben”

Tana gama fadin haka tanufi motar tata tashiga ta tasheta tafice daga wurin tanata faman mita ita kadai,

“Duk yabi yawani bata min lokaci abanza wanda da tuni najima da zuwa gida nayi abinda zanyi nagama…”

Da haka takarasa gidansu dake can tudun mai rini, da sauri tafito daga cikin motar wadda ko rufeta batayiba ta kutsa ciki da dan gudu gudu domin taga alamar cewar mahaifan nata sun dawo daga tafiyar da sukayi na tsawon sati biyu,

Kamar yadda tazata a main palo ta tarad dasu zaune ga masu yimusu hidima sai faman kaiwa da kawowa suke ashagwabe tatafi jikin ummanta tana murna kamar wata karamar yarinya,

“A ina kika tsayane sadiya…? Tun dazu fa muka dawo” mahaifiyarta tafada tana shafa bayanta,

“Umma natsaya ne anduba min motata saboda wahalar dani sitayarin yakeyi…”

“To kuma inbanda abinki sadiya ai da kin daure kin karaso ahaka inyaso sai akira bakanike har gida ya duba miki…” Mahaifinta yafada wanda tun shigowarta yake kallonta cikeda tsantsar farin ciki,

“Abba ai kafin nakaraso gidanne akwai wahala shiyasa nabari kawai suka dubata acanne ma na bata lokaci amma badan hakaba da tuni nadawo…”

“To ai shikenan Allah yataimaka” inji mahaifinta,

“Yanzu dai duk ba wannanba ya muka dawo muka tarar daku?” Hajiya binta ta bukata tana murmushi,

“Lafiya lau umma sai kadaici na rashinku dake addabata”

“To bagashi har mu dinma mun dawoba, ke mak’o gareki….”

“Ai dole tayi mak’o saboda irin yanda kike gataleta ko sadiya?” Inji mahaifinta,

Dariya dukkaninsu sukayi,tashi sadiya tayi tanufi dakinta tana mai jin farin ciki yana ratsa dukkan sassan dake cikin zuciyarta domin tayi sa’ar samun iyaye nagari masu sonta kuma masu kaunarta wadanda suka zame mata abin alfahari.

Washe gari tun kafin taje makaranta tafara biyawa ta gareji domin akarasa gyara mata motar ta sannan kuma tabiyasu kudinsu,

Lokacin da taje tayi sa’a basuda ayyuka dayawa domin safiyace mota daya kacal tasamu suna faman gyarata amma sauran da suka kwana awurin duk sun kammala,

Kamar jiya yauma parking tayi tafito dama suna ganinta suka taso banda ogansu wanda ke zaune saman benci yana rikeda wani littafi wanda bazata iya tantance ko namenene ba,

“Barka da zuwa ranki yadade, kindawo akarasa miki gyaran ko?” Inji dan larai daya daga cikin bakanikan dake wurin,

“Ehh amma kuma naji birkin kamar shima yayi tauri yau…”

“Ok to bari infadawa oga”

Tana kallonsa yanufi wurin wanda ke zaune akan bencin nan wanda da alama shi ne ogan,

Bataji me suka fada ba tadai ga yataso sun taho tare wurin motar tata amma tun zuwanta wurin har kawo yanzu bai ko kalli wurin datake ba,tsayuwarta tagyara tana kallonsu aranta tana jin cewar wannan ogan mugun dan rainin wayone,

Saida suka danyi dube dubensu dakuma gyare gyarensu sannan taga ogan yashiga motar yatasheta yafita domin ya gwada yaji komai yagyaru ko akwai saura?

Mintunan da basu wuce goma zuwa sha biyarba yakwashe wurin testing din motar sannan yadawo yazo yayi packing awurin da tayi yafito, ko kallonta baiyiba yace da dan larai,

“Kafada mata angyara amma birkin nan nata har yanzu akwai matsala idan zata dawo zuwa yamma to sai akarasa gyarashi gaba daya lokacin ankawo wani abu wanda za asauya domin yanzu bamu dashi…”

Jin abinda yace yasata dan matsawa kusa dasu,

“Ok yanzu school zan shiga amma kamar nawane ake saida abin sai inbaku kudin yanzu?”

Banza yayi mata maimakon yabata amsa ma sai taga yawuce yanufi benci inda yake zaune da farko,

Cikeda takaici ta kalleshi sannan ta mayar da kallonta ga dan larai dake tsaye yarike kugu,

“Waini meyasa ogan nan naku bashida mutuncine? Sai arinka yimasa magana amma yayiwa mutum banza kamar baiji ba…”

“Hajiya wallahi shi haka yake, baya magana da matane sam…”

Tsaki taja bata kai ga yin wata maganarba taga dan larai yanufi wurinsa suna magana mintuna biyu atsakani sai gashi yadawo,

“Hajiya yace 1,500 ne kudin abin wanda kike tambaya…”

Kamar bazata yi magana ba tayi shigewarta cikin mota, handbag dinta tajawo tabude taciro kudin ta mika masa daga nan tatashi motarta tayi gaba…..

 

_*Ummi Shatu*_👌🏻
*HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*DAN ASALI…!*🤴🏻

 

*_NA_*
_*UMMI A’ISHA*_

 

_Yan zauren karatu na Adda Bena nagaisheku gaisuwa marar adadi nasani kudin nawane….._

*3*

 

***Makarantarsu tawuce kai tsaye zuciyarta cunkushe da tunani kala kala wanda mafi yawa na wannan bakaniken ne ,

“Salon wulakancinshi dabanne…” Tafada ahankali tana cije labbanta, chewing gum ta lalubo cikin jakarta tajefa abakinta wanda dayane daga cikin al’adarta kusan koda yaushe cikin taunashi take koda kuwa bata ci abinci ba,

Ahaka tashiga makarantar tayi packing a inda tasaba ajiye motarta akoda yaushe,tana kokarin tattaro kayanta tazuba cikin jakarta domin fitowa taji anbude mata kofar dake side dinta, murmushi kwance akan fuskarta tayi magana tun kafin taga wanda yake tsaye,

“Badai har kazo ba?”

“Gani kuwa tsaye agabanki…” Saurayin dake tsaye sanye cikin kananan kaya wanda kallo daya zakayi masa kagane dan masu dashi ne, yabata amsa,

“To ya akayi haka yau?”

“Kin makare kawai princess” yabata amsa yana mai kokarin karbar handbag din dake hannunta, sakar mishi tayi tamaida kofar motar tarufe bayan tafito, key din tarike tana karkadasu bayan ta ida kulle motar,

“Sabira bata shigo bane?” Ta tambayeshi tana mai kallon fuskarshi, yau daga ke har kawarki amakare kuke ai,

“Ni nakai motata gyarane fa”

“Ohh kuma shine baki kirani narakaki ba?”

Murmushi tayi batare data kalleshi ba tace,

“Nahutar dakai kayi zamanka”

“Nidai ban yarda ba..” Yace da ita cikin tsokana, daga shi har ita dariya suke yi dan haka basu samu zarafin ganin tahowar sabira ba illa jin dariyarta kawai da sukayi agefensu tana tayasu,

Kallon juna dukkaninsu sukayi suka sake fashewa da dariya musamman ma Abdul wanda harda rike ciki,

“Kekuma daga ina?” Halimatu tace da sabira,

“Daga sama…” Tamayar mata da amsa, wata dariyar suka sake kwashewa da ita kafin suka nufi lecture hall, kullum su ukun tare zaka gansu suna al’amuransu, department dinsu daya sannan koda yaushe suna tare kamar wasu yan uku.

Sai karfe 3 suka gama lectures,capteria suka wuce domin dukkaninsu yunwa sukeji musamman ma Halimatu wadda batayi wani breakfast din kirki ba duk da takuratan da umma tayi akan ta zauna ta karya sosai,

“Princess me zakici?” Abdul ya tambayeta cikeda kulawa,

“Komai nasamu ci zanyi friend, akawo min koma meye…” Tafada tana dafe da goshinta,

“Friend kefa?” Yasake tambayar sabira, kawar dakai sabiran tayi tana turo baki,

“Bazanci ba, shine saida kafara tambayar princess dinka sannan zaka tambayeni..”

“So kina jealousy ko?” Halimatu ta fada tana murmushi,

“Ku kuka sani dai…” Sabira ta maida mata da amsa, dariya suka saka Abdul yawuce domin ya iyo musu order din abincin,

Yana tafiya sabira da halimatu suka fara muhawararsu kamar yadda suka saba koda yaushe akan Abdul, ita sabira tana cewa son halimatu yake ita kuma tana musawa acewarta duk wadannan abubuwan ba so bane kawai friendship ne,

Cikin haka yadawo ya iskesu, shiru halimatu tayi amma sabira sai yi take batayi shiruba,

“Idan ta ruba dai zamuji ko kuma in tayi tsami…”

Abdul bai san maganar da sukeyi ba shiyasa bai saka baki ba illa wayarshi da yazaro daga aljihu ya shiga instagram har aka kawo musu abinci,

Kowa da plate dinshi dukkansu jalop rice ce da salad sai drinks,

Anutse halimatu take cin abincin amma kuma cak sai ta tsaya sakamakon tunowa da wannan bakaniken da tayi dan rainin hankali acewarta,

Dakatawa da cin abincin tayi tana ta tunoshi cikin kwakwalwarta batare da tasan dalili ba, haka kawai taji ta samu kanta da son sanin wasu abubuwa game dashi duk da cewar sam bai burgeta ba kuma baiyi mataba saboda kamar yafiya wulakanci,

Zungurarta sabira tayi nan da nan tayi firgigit ta kalleta sannan ta kalli abdul wanda yazuba mata idanuwa yana kallonta fuskarshi dauke da alamun tambaya,

“Princess wai tunanin me kikeyi…?”

Murmushin yake ta dan yi,

“Wallahi ina tunanin yanda zanyi driving motana ne zuwa wurin bakanikai domin ta dan samu matsala”

“Wannan bai kai abinda zai saka ki zurfafa acikin tunaniba malama” sabira tafada tana harararta,

“Kanki akeji, shi ai yasan gaskiya nafada”

Murmushi abdul yayi,

“Yes I trust u princess”

Murmishi ta danyi taci gaba da cin abincinta tana yan tunane tunane gefe daya kuma tana dan sakawa su sabira baki acikin hirarsu da haka suka kammala dukkaninsu suka mike suka fita daga wurin cin abincin bayan Abdul yabiya,

“Ni yanzu nagaji gashi ina son zuwa ball anjima…”

Abdul yafada yana jingine jikin motar halima fuskarshi tayi kalar tausayi,

“Ayya sorry kana zuwa gida kayi wanka da ruwan dumi zakaji ka warware sai kaje ka dan motsa jikinka…” Halima tafada cikin kulawa,

“Good advice princess, nagode bari naje to, kihuta lafiya…”

“Thank you Abdul, bye bye”

Wani murmushin shakiyanci sabira tayi sannan tayi gyaran murya,

“Abun ma yau harda su wariyar launin fata? Uhm”

“To nida ita duk farare ne kece kadai baka kinga kuwa ai kalarki daban….”

Abdul yafada cikin tsokana yana gama fada yawuce yana dariya bai tsayaba,itama halima dariya take saboda jin abinda yace,

Shiga mota sukayi itada sabira suka fita, sai da takai sabira har kofar gidansu sannan tawuce ta tafi izuwa cikin tasha domin komawa wurin bakanikan nan Wanda haka kawai taji aranta bazata iya komawa gidaba har sai taje garejin duk da irin faduwar da gabanta keyi………

 

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
*HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…*🤴🏻

 

*_NA_*
_*UMMI A’ISHA*_

 

*4*

 

***Lokacin da ta isa garejin hangosu tayi suna salla da alama sallar la’asar sukeyi,

Packing tayi daga nesa tana hangosu ogansu yana gaba yana jansu sallar, tabe baki tayi amma kuma takasa dauke idonta daga gareshi,

Akan idonta suka idar da sallar sannan kowa ya mike banda Aliyu wanda yasake gyara zamanshi domin yin addu’a,

Knocking din glass din dataji anayine yadawo da ita daga zancen zucin datake niyyar yi, kallon window din tayi nan taga dan larai tsaye yana murmushi,

“Ah hajiya barka da zuwa, kin dawo ?”

“Ehh nadawo…”

“To bari azo asaka miki dama tun dazu oga yaje dakansa yasiyo…”

Shiru tayi bata sake maganaba,

Tana kallo dan larai yabude gaban motar yafara aikinsa zuwa can kuma sai ga Aliyu yakaraso, tsaye yayi agefen dan larai yana ganin yanda aikin yake tafiya,

Ita kam halima kura masa ido tayi tana faman kallonsa kamar wacce tasamu tv, ahankali ta dauke idonta daga kanshi ganin yana kokarin juyowa,batare da ya kalleta ba yadan sunkuyo yayi magana,

“Fito mugani…”

Bai jira amsarta ba yakoma inda yake dafarko, bude kofar motar tayi ta zagaya barin mai zaman banza tazauna, sam Aliyu bai kula ba yabude motar yashiga bayan dan larai yarufe gaban motar, tashin motar yayi yasoma tukata ahankali,yanda yaki kallonta haka itama ta dauke nata idon tahanashi kallon gefen da yake,

Testing din motar yayi daga wurinsu zuwa wajen titi, kamar babu kowa acikin motar domin tsitt kakeji, har wurin da tayi packing dazu yakoma sannan yafara kokarin fita, cikin sauri ta dakatar dashi,

“Nawane kudin gyaran….?”

Batare da ya kalli gefen da takeba ya amsa mata,

“Kibada abinda yasamu kawai” yakarasa maganar yana niyyar bude kofar motar yafita,

“To jira ka karba mana…” Tafada tana bude handbag dinta nan taciro dubu biyar ta mika mishi,

Karbar kudin yayi batare da yayi magana ba ya dauki dubu uku ya ajiye dubu biyu akan sit yafice,baki ta tabe ganin abinda yayi, komawa sit din driver tayi tarufe daidai lokacin da dan larai ya matso yana yimata asauka lafiya,

Acikin zuciyarta take tunani kala kala wadda takasa sanin dalilin yinshi, ita dai tasan wannan Aliyun ba burgeta yayiba amma kuma tunaninshi sam yaki barin cikin kwakwalwarta acan kasan zuciyarta kuma tana jin wani abu game dashi wanda yafi kamada tausayi,

“To awanne dalili zan rinka jin tausayinsa?” Ta tambayi kanta,

“Koda yake yayi kama da wadanda za aji tausayin nasu” ta sake bawa kanta amsa,

Haka taci gaba da yiwa kanta tambayoyi tana amsawa gameda Aliyu wanda ita kanta bata san dalili ba,

Tsabar zurfi da tayi cikin tunani lokacin da ta shiga gida har takarasa parking space bata ankara ba saida taji wani gummmm alamun taci karo da bango nan hankalinta yadawo jikinta, salatin habu mai gadi ne yasake rudata nan tasan karon da tayi ba karami bane, fitowa tayi tana duba gaban motar wadda tuni danjojinta duk suka farfashe banda lollotsawa da gaban motar yayi,

“Allah yarufa asiri hajiya, Allah yatsare gaba amma garin yaya..?” Inji habu mai gadi,

“Wallahi habu nikaina ban san ya akayi hakan tafaru ba…”

“Kawai dai tsautsayine wanda bahaushe yace baya wuce ranarsa, Allah yatsare gaba”

Bata kai ga amsawa ba taji fitowar abbanta daga ciki ganin abinda yafaru yasashi karasowa yana tambayar dalilin afkuwar hakan,

“Abba wallahi ban san meya dauke min hankali ba har na bugi wannan bangon”

“Dama haka zakice mana bayan watakila wannan latse latsen wayar da kika saba kikeyi, kullum sai nayi miki fadan daukar waya idan kina driving amma bakyaji dayake kin iya taurin kai na tsiya” muryar ummanta tadoki dodon kunnenta wadda take biye da abba domin yimasa rakiya,

“To ya isa dai, koma dai menene tunda mai faruwa tafaru sai ayi hakuri ayi addu’a Allah yakiyaye gaba” Abba yafada yana sake leka gaban motar,

“Allah yarufa asiri, gobe sai akira bakanike yazo yagyara miki ko”

“To abba…” Ta amsa tana ciro handbag dinta daga ciki dasauran takardunta,

“Allah ya kyauta” umma tafada sannan tajuya tanufi ciki, itama Sadiya bin bayanta tayi bayan tayiwa abba adawo lafiya,afalo ta zubarda shirginta da tashigo dasu tazauna kusa da umma wadda keta yimata fadan tadaina taba waya idan tana driving, sun jima da umman a falo sannan ta tashi tashiga dakinta.

Koda tashiga bedroom dinta ma bayan ta kammala abubuwan da suka zame mata na al’adarta wadanda tasaba gudanarwa, tunanin Aliyu ne yaketa kaiwa zuciyarta cafka amma tana kokarin ganin tahana hakan faruwa tahanyar kirkirar abinyi,amma hakan kamar abanza domin bata yin cikakken minti biyu sai tajishi acikin ranta, gabanta ne yafara faduwa sakamakon bakon lamarin dake kokarin ziyartar zuciyarta,

Text book din hannunta ta ajiye agefen gado tasauka daga kan gadon ta fita daga dakin wai dan duk tahana wannan tunanin tasiri,

Bedroom din umma tashiga ta isketa zaune kan stool din mudubi tana gyara fuskarta, nan tayi murmushi domin yanayin ummanta yana burgeta duk lokacin da abba yakusa dawowa to tana kokarin ganin ta gyara jikinta da fuskarta,

Zama tayi agefen gadon Umman tareda dan kishingida ta jingina da pillow,

“Umma kwalliya kike yine haka?”

Harararta umma tayi tace,

“Kedai anyi marar ta ido halimatu, yanzu ni kike cema haka? To da haka kikeso inyita zama babu gyara?”

Dariya Sadiya tayi tace, “umma ni wallahi bahaka nake nufi ba, barima intashi inje in dafawa abbana Lipton”

“Da dai yafi miki” umma ta mayar mata, tashi tayi tafita tashiga kitchen ta dora ruwan zafi, kamar yadda tasaba da kayan kamshi ta dafa Lipton din ta juye a flask ta fita zuwa part din abba, koda tashiga tasamu umma har taje tana zaune suna hira da abba, zama tayi itama suka cigaba da hirar tare har karfe 10 sannan ne tatashi tayi musu sallama tawuce dakinta, wayarta ta jawo bayan tadora laptop dinta akan cinyarta, 2 miss called tagani tana dubawa taga friend, murmushi tayi tai dialing no din bayan ta jingina bayanta da jikin pillow…………..

 

 

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
*HASKE WRITERS ASSO*
_(Home of expert & perfect writers_)

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

 

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

 

*5*

 

***Har wayar tayi ta tsinke bai dauka ba,tana kokarin ajiye wayar kiranshi yashigo murmushin dake kan fuskarta ne yakaru,

“Hello friend…” Tafada muryarta akasa,

“Princess ina kika buya? Nazaci fa ko kin fara baccine”

Murmushi mai sauti tasaki kafin tabashi amsa,

“Ni na isa inyi bacci batare danaji voice dinka ba?”

“To nasani ko yau bakya son jin muryar tawa”

Dariya tayi kafin tace,

“Afuwan naje wurinsu abba ne munyi hira kuma nabar phone din adaki”

“Babu damuwa princess, ki kwanta kiyi bacci kinji, good night and have a nice sweet dream”

“Tnx prince & same to u” tabashi amsa tana murmushi tareda katse wayar, cillata gefe tayi tasoma yin game a system dinta,

Har 11 takai ahaka sai daga bisani sannan tarufe laptop din ta tashi, kayan jikinta tasauya izuwa na bacci bayan ta watsa ruwa,kwanciya tayi taja blanket tarufe rabin jikinta ta lumshe idanuwanta tana son tayi bacci amma sai tunanin Aliyu yafara bijirowa zuciyarta nan baccin yagagari idonta in banda juyi babu abinda takeyi.

12:30 daidai tasamu bacci yayi nasarar dauketa, dan haka dakyar tasamu ta iya tashi da asuba tayi salla wannan dinma saida umma tashigo har sau biyu tana tashinta sannan ta tashi saboda tsananin baccin dake dankare a idonta,

Komawa tayi ta kwanta bayan ta idar da salla, ba ita ta tashiba sai bayan 10,wanka tayi ta shirya tasaka wata pink din gown mai adon stones ajiki sannan ta yi rolling da dan mayafin rigar,

Komai da zata bukata a school ta zuba acikin handbag dinta black mai ratsin pink, turare ta fesa different colours fiyeda guda biyar wadanda mafi yawancinsu oad ne,

A falo ta iske umma tana kallo ga kayan breakfast nan agabanta da alama bata jima da kammala ciba,

“Ai nazaci yau baki da lecture bazaki fitaba shiyasa ban tasheki ba”

“Wallahi umma jiya ban yi bacci dawuriba inata yin game…”

“Aikin dai kenan, ni nazaci ma cemin zakiyi karatu kika zauna yi ashe aikin da bazai amfaneki bane”

Murmushi tayi ta durkusa ta gaidata sannan ta mike ta dauki cup ta tsiyayi ruwan zafi ta hada tea,

Cusa doya da kwan dake gabanta kawai takeyi tana korawa da ruwan tea amma bawai dan tana enjoying breakfast dinba domin gaba daya hankakinta da tunaninta yanaga Aliyu wanda sam bata san daliliba, mutumin dako kalma biyar bata shiga tsakaninsu ba amma daga ganinsa sau biyu kacal duk tabi tadamu dashi,

Mikewa tayi tana daukar handbag dinta, “umma bari inje school amma zan biya gareji inkai motata gyara”

“Ba naji abbanki yace zai turo mai gyara ba?”

“Umma gara dai inkai dakaina agyara agabana”

“Allah ya kiyaye hanya”

“Amin ummata” tafada tana murmushi tareda ficewa,

Tana fita daga gida kiran sabira yafara shigowa wayarta amma bata sami zarafin daukaba saboda tana driving, garejin gyaran motar tawuce kai tsaye domin ayanda take jin zuciyarta tana iya daina cigaba da aiki mutukar bataga wannan tan talikin ba,

Kamar koda yaushe dukkaninsu ma’aikatan suna sanye da uniform suna ta aikinsu banda Aliyu wanda ke zaune akasan rumfar zamansu akan dogon benci yana nazarin wani littafi da yake rike dashi,

Packing tayi tana jin wani sanyi mai kamada kankara yana kwaranya kowanne sako dake cikin zuciyarta, kura masa ido tayi tana kallonsa yana sanye da blue din riga iya gwiwa sai wando jeans kalar ruwan siminti kanshi babu hula,

Wani tunani ne nadaban yafara kai kawo acikin brain dinta wanda tasoma zurfi acikinsa, ahankali taga yadago yana kallon motar tata tsawon mintuna biyu kafin yatashi yanufo wurin motar kasancewar glass din jikin motar tin tact ne,

Kafeshi da idanuwanta tayi har yakaraso yafara knocking din glass din dake saitin mazaunin driver ahankali tasauke glass din karaf suka hada ido for the first time, wata irin bugawa tareda faduwa taji zuciyarta tayi, kamar anjona musu shock haka kowannensu yaji, cikin sauri tajanye kwayar idonta daga nashi, shi dinma kawar da nashi kwayar idon yayi, cikin sanyin murya tace,

“Ina kwana?”

Atakaice ya amsa da,
“Lafiya”

Daga haka bai sake magana ba yajuya yana kwalawa daya daga cikin yaransa kira, kan bencin yakoma yazauna wurinda yake zaune da farko,

“Murtala ga wata mota can ankawo gyara jeka kafara dubawa” yakarasa maganar yana nuna masa motar halimatu da hannunshi,

Tana daga cikin motar tana kallonsa lokacin da yana yiwa murtala magana, faduwa gabanta yaci gaba dayi kamar wadda taga wani abun tsoro,

Dafe goshinta tayi tafito bayan murtala yakaraso wurinta,

“Sannu da zuwa hajiya, nan gabanne inda ya lotse za agyara ko?”

“Ehh nanne amma zai yiyu agyara yanzu kuwa?”

“A’a gaskiya sai dai kidawo zuwa wurin yamma yanzu dai kibar motar anan”

“Ok to babu damuwa”

Juyawa tayi tabude motar tadauko handbag dinta da wayarta tamika masa key din motar sannan tawuce tatafi bayan tadan saci kallon Aliyu Wanda sam hankalinsa baya wurinda take,

Keke napep tashiga zuwa school, lokacin da taje tuni harsu sabira sun fito daga lecture suna zaune itada Abdul,

Da sassarfa takarasa wurinsu tazauna,daga sabira har Abdul kallonta suke suna murmushi bayan alamun tambaya da mamaki dake shimfide akan fuskokinsu,

“Ke dan kin rainawa kanki hankali sai yanzu kike zuwa school?” Inji sabira,

“Bazaku gane bane, yanzu haka daga gareji nake and magana ta gaskiya yau natashi late”

“Ayya sorry princess” Abdul yafada cikeda kulawa yana latsa phone dinshi,

“Tnx friend, amma ya naganku anan?”

“Mun fito daga lecture ko da za atsaya jiranki ne?” Sabira ta amsa mata,

Dariya tayi tarabu da ita suka fara hira da Abdul kafin su sake shiga wata lecture din.

K’arfe 5 tabar school, lokacin da takoma gareji domin daukar motarta tasamu angyara mata motarta tayi kalau kamar babu abinda yasameta jiya abu dayane baiyi mata dadiba shine rashin ganin Aliyu domin kaf wurin idonta ya lalleka amma bai hango mata shiba,

Bayan sun gama dasu murtalan tabasu kudinsu taji takasa hakuri har saida ta yambayesu ina ogansu,

“Oga yatashi tun dazu ai baya kaiwa 5 anan sai dai idan alhamis ce ko kuma juma’a” murtala yabata amsa,

“Nikuwa sai nake ganin kamar ta wurin area dinmu yake, kamar nasanshi”

“Ehh to mai yuyuwa ne domin shidinma ata gangaren masaka yake, gidansu yana nan gaban karamin masallaci”

Dadine ya ziyarci zuciyarta jin bayanin da yayi mata, cikin sauki gashi yasanar da ita inda Aliyu yake,

500 takara masa akan kudin gyaran motar saboda tsabar farin ciki, shiga motarta tayi tawuce tana jin kamar yanzu haka tawuce kai tsaye gidansu Aliyu taje tafada masa idanuwanta basa gajiyawa da kallonshi.

Da tunanin yanda zata cigaba da ganin Aliyu ta isa gida,

Ciki tashiga tana rikeda handbag dinta tana takawa ahankali domin azalzalarta zuciyarta keyi gameda Aliyu ita tarasa gane kan wannan lamari abu kamar abin asiri,

Awurin umma tazauna a balcony din kitchen domin anan ta isketa itada mai yimusu girki suna yanyanka ganyen da za ayi miyar dare dashi,

“Umma kinga yanda aka gyara min motata? Wallahi kamar wani abu bai sameta ba”

“To dai kici gaba da kula dakyau, banda ganganci domin karfe bashida tabbas, Allah yayita karewa” umma ta amsa mata tana shirya alayyahun dake gabanta,

“Amin dai” inji sabuwa mai girkinsu,

“Abba fa yadawo?” Ta tambayi umma,

“Abbanki yau ko zai shigo gidan nan sai da daddare domin wani muhimmin taro sukeyi dan da sassafe ma yafita”

“Ok ashe shiyasa yau ban ganshi ba sam, Allah yadawo dashi lafiya”

Tashi tayi tawuce bedroom dinta, wanka tafara shiga tayi tafito daure da towel, gabanta ne yafadi haka kawai, zama tayi agaban mirror tayi tagumi tana kallon kanta ajikin mudubin saboda yanda taga abubuwa suna neman sauya mata karfi da yaji.

Wasa wasa haka zuciyarta takasance tanata faman addabarta da tunanin Aliyu, gaba daya bacci yana neman kauracewa idanuwanta,

Tunanin mafita tafara yi, daga karshe zuciyarta tabata shawarar kawai tasan duk yanda zatayi ta kulla alaka dashi ko zata samu sassaucin abinda ke damunta acikin zuciyarta, da wannan shawarar ta amince kuma tayi na’am sai lokacin hankalinta yadan kwanta tasamu sukunin runtsawa.

Washe gari bayan ta shirya tafita tambayar kanta tafara shin yadace taje garejin su Aliyu wurinshi haka kawai babu wani dalili?

“Kai idan naje rainani ma zasuyi shida yaransa,to amma gidansu fa? Yakamata nanma a matsayina na mace inje gidansu? Kai gara dai gidan akan garejin” duk wadannan maganganun tana yinsu ne acikin zuciyarta,

Gidansu Aliyun tanufa, nan tahau hanyar da zata sadata da unguwarsu, kasancewar kwatancen da akayi mata jiya yazauna akanta yasata sam batasha wahalar gane gidanba,

Adaidai kofar gidan tayi packing ta zubawa kofar gidan ido domin gidane irin na masu karamin karfi sosai tun daga yanayin ginin gidan wanda ya kasance na kasa ne sai wata yar kofar langa langa dake sakale amatsayin kyauren gidan wadda tasha faci kiris yarage ta balle daga jin katakon da aka makalata ajiki,

Wani iri taji atattare da ita saboda ganin wurin da Aliyu yake rayuwa amma sam bataji yanayin da takeji agame dashi ya sauya ba,sai ko dawasa bata kawowa ranta a irin wannan wurin yake rayuwaba domin sam yanayinsa bai nuna hakanba,

Tafi minti goma awurin taga anturo kyauren da alama fitowa za ayi, ai kuwa shine yafito daga cikin gidan yana sanye da bakar t shirt da wando blue,

Zuba masa ido tayi tana jin faduwar gabanta tana tsananta, tsaye yayi yafito da karamar wayarshi kirar Nokia C1 ya fara latsawa kafin yakara akunnenshi, bata jin abinda yake fada amma tana ganin irin yanda yake yin dan murmushi wanda ya kawata fuskarsa,

Ganin yamaida wayar aljihu yasata saurin bude murfin motar saboda ganin yana shirin wucewa,

“Amm Malam salamu alaikum” tafada bayan tafito daga cikin motar,

Juyowa yayi yatsaya bayan ya amsa sallamar, kawar da kanshi yayi batare da ya kalleta ba saboda jin muryar mace,

Karasawa tayi kusa dashi,

“Sannu ina kwana?”

Kamar bazaiyi magana ba ya amsa da”lafiya”

Dan shirune ya ratsa saboda faduwar da gabanta keyi tama rasa ta ina zata fara,

“Am dama nice wadda nakai gyaran mota wurinku jiya”

“Na’am” ya amsa mata,

“To shine nazo inyi maka godiya saboda gyaran yayi sosai…”

Sai lokacin ya dago ya kalleta suka hada ido, cikin azama tayi kasa da nata idon,

“Babu damuwa” yace da ita yana kallonta,

“Kuma…., kuma idan bazaka damuba…” Shiru tayi takasa karasawa sakamakon bugawar da zuciyarta tayi da karfi,

“Kuma idan bazaka damuba ina son murinka zumunci….”

“Babu damuwa, nagode” Shine abinda yace tareda kokarin juyawa domin tafiya,

“Amm bakajiba….” Juyowa yayi amma bai kalletaba sai dai fuskarshi ta nuna alamun gajiya gamida kosawa,

“Nace ko zan samu phone no dinka?”

Hannu yamika alamun tabashi wayar ta, mika masa tayi tana kallon fuskarshi, saka mata no yayi ya mika mata,

“Sai anjima”

Ya furta ahankali kafin yawuce zuwa cikin gidan, ta dan jima tsaye awurin kafin tashiga cikin motarta ganin abin take kamar acikin mafarki wai yau itace haka ke faruwa da ita kamar wacce aka sihirce,

Tamkar kazar da kwai ya fashewa aciki haka ta tada motarta tabar wurin sai kallon kofar gidansu Aliyu take ko wai zata ganshi yasake fitowa.

School tawuce kai tsaye domin tanada lectures har guda uku ayau amma koda taje har tayi missing guda daya,

“Wai princess what’s wrong with you? 2 days naga some changes atare dake” Abdul ya tambayeta time din data fito daga cikin motarta,

“Wallahi friend babu komai, amma wadannan changes kagani?”

“Naga kamar kina cikin damuwa, akwai abinda yake damunki sannan yanzu kin fara zuwa school late bayan ada bahaka kikeba what’s the problem?”

Girgiza masa kai tayi tana murmushi,

“Makara nakeyi ne a bacci kuma duk its your fault saboda kaine baka tashina”

Murmushi yayi ya karbi handbag din hannunta,

“Shikenan am so sorry insha Allah zan gyara, ayi min afuwa”

“Don’t worry nahakura”

Class suka wuce inda sabira ke zaune tana jiransu.

Kasancewar yau har yamma saida tayi lecture yasa bata koma gida dawuriba sai around 6,agajiye take lis dakyar ta iya yin wanka taci abinci, tana idar da sallar magrib tahau gado takwanta, Aliyu ne yafara yimata gizo acikin kwayar idanuwanta, juyi tayi tajanyo wayarta ta bude, contact dinshi ta tsurawa ido tana jin gabanta yana faduwa,ahankali ta lumshe idonta bayan tayi dialing no dinshi……..

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
*HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*DAN ASALI…!*🤴🏻

*_NA_*
*_UMMI A’ISHA_*

 

*6*

 

***Wani takaicine ya lullube zuciyarta lokaci guda domin sam wayar bata shiga ba asalima wai is the stop computer take fada mata,

Kishingida tayi tarasa gaba daya abinda yake yimata dadi, awannan lokacin da take ciki ji take kamar tayi tsuntsuwa taje ga Aliyu taganshi taga halin da yake ciki,

Dafe goshinta tayi tana tambayar zuciyarta,

“Wannan wacce irin masifa ce? Daga ganin mutum sai hankalina da tunanina gaba daya ya tattara zuwa gareshi ?”

Dan siririn tsaki ta saki bayan ta zame ta kwanta,

Shiru tayi tana jin zuciyarta tana harbawa da karfi da karfi,

Daren wannan ranar batayi wani isasshen bacci ba sai jikin asuba, duk da haka yau tayi kokarin tashi da wuri domin bata son taci gaba da missing lectures dinta,

9 saura tafito cikin shiri tayi breakfast,part din abba taje tagaidashi sannan tayiwa umma sallama tatafi,

Ahankali take tafiya tana bin wakar _selfish_ dake tashi cikin motar wacce ta kunna, wani sanyi ne da farin ciki suke ratsa zuciyarta saboda yau tasawa ranta sai ta ziyarci har cikin gidansu Aliyu,

Koda tashiga school ma su Abdul sunga sai faman fara’a takeyi gashi yau bata makaraba,

6 saura yan mintuna suka fito daga makaranta taje ta sauke sabira agida daga nan tawuce unguwarsu Aliyu,

Tana shiga layinsu tahango Aliyun suna tahowa shida wata budurwa wacce ahaife zatayi kusan sa’arta,

Gabanta ne yayi mummunar faduwa domin abisa dukkan alamu akwai shakuwa mai karfi tsakaninshi da yarinyar saboda irin yanda taga yana ta sakin lallausan murmushi, babu shiri tayi azamar taka burki bayan ta gangara gefen titi,

Kallonsu taci gaba dayi suna tahowa, yarinyar tana sanye da coffee colour din hijab mai hannu wanda yake har kasa sannan ga nikab nan amma ta dageshi, tana rikeda alqur’ani mai girma izu sittin, yayinda shikuma Aliyun yake sanye da shadda milk colour riga da wando,yasanya hula baka akanshi shi dinma rike yake da alqur’ani ahannunshi,

Dai dai kofar gidansu Aliyu suka tsaya shida yarinyar wanda da alama magana sukeyi amma ita bata jiyo abinda suke fada,

Sunfi minti biyar atsaye kafin daga bisani taga yarinyar tasauke nikab din fuskarta daga ita har Aliyun murmushi suke, juyawa yarinyar tayi tawuce shikuma Aliyu yanufi kofar gidansu,

Da sauri halimatu tafito tabishi yana kokarin shiga takira sunanshi, ahankali yajuyo yana gyara rikon alqur’anin dake hannunsa,

“Kayi mamakin ganina da yammancin nan ko?” Tafada wadda gaba daya tarasa abin fada ne shiyasa ta bullo tahaka,

Kawar da kanshi gefe yayi sannan yace,

“Ehh hakane, amma dai ina fata lafiya?”

Dan murmushi tasaki sannan ta amsa,

“Lafiya lau kawai nazone ingaidaka kaida mutanen gida”

Dan jimm yayi kafin yace,

“Babu damuwa bismillah…”

Tura kofar yayi yashiga nan tabishi zuwa cikin gidan wanda yake ginin jar kasa sannan fadin tsakar gidanma bashida wani girma dan karamine ba can ba, dakuna ne guda biyu suna kallon juna sai dan makewayi daga can gefe daya sannan da dan wurin girki wanda aka zagaye da langa langa,

Gani tayi yatsaya akofar dakin dake fuskantarsu yana magana cikin ladabi da girmamawa bayan ya dan rissina,

“Ummi nadawo, amma tareda bakuwa nake tazo gaidaki?

“Muslima ce tazo?” Daga cikin dakin aka tambaya wadda ko ba afada mata ba tasan mahaifiyarshi ce,

“A’a Ummi ba ita bace, watace da na gyarawa mota”

“To bari infito”

Yana tsaye mahaifiyar tashi tafito rikeda tabarma tana yimata sannu da zuwa,

Shimfida mata tabarmar tayi shikuma Aliyu yashige dayan dakin wanda ke fuskantar na mahaifiyarshi,

Cikin ladabi halimatu tagaida ummin tashi aranta tana tunanin may be Aliyu su biyune ke rayuwa acikin gidan daga shi sai mahaifiyarshi domin bataji motsin kowaba gashi gidan ma baiyi kalar wanda jama’a da dama ke rayuwa cikinsa ba, bin gidan take da kallo gashi nan dai ashare yake tass a tsaftace duk da bawani mai kyau bane amma babu alamun kazanta atare dashi.

“Kema makarantarku daya da Aliyu?” Ummi ta tambayeta tana murmushi,

Girgiza kai halimatu tayi kafin tace,

“A’a ba makarantarmu daya ba”

“Allah sarki” Ummi tafada daidai lokacin Aliyu yafito daga cikin dakinshi yadauki buta dake ajiye can gefe guda yanufi kan wani dutsi yazauna yasoma yin alwala saboda magrib tagabato domin wasu masallatan ma har anfara kiran salla,

Ganin haka yasa halimatu tashi tayiwa Ummi sallama tace zata tafi,

Godiya sosai ummin tayi mata kamar halimatun takawo mata wani abu, dan satar kallon Aliyu halimatu tayi nan taga hankalinsa ma sam baya wurinsu yanaga alwalar da yake shirin kammalawa,

Hanyar fita daga gidan tabi yayinda shikuma Aliyu yamike da niyyar zuwa masallaci,

“Bari inje intafi sai wani lokacin…” Tafada bayan ta juya taganshi abayanta,

“To mun gode, kigaida gida” yace da ita kasa kasa,

“Ok” ta amsa masa tareda wucewa,

Ta cikin glass din motarta take hangoshi yana kokarin shiga masallaci, saida taga shigarsa sannan ta murza motarta tabar wurin tana cike da kewar kallon kyakkyawar siffarsa.

WANENE ALIYU?

Aliyu matashin saurayine dan kimanin shekaru 28 zuwa 29,duk inda ake neman cikakke kuma kyakkyawan namiji to Aliyu yakai domin yanada duk wata siffa wacce ake bukata awurin da namiji,kalar fatarsa mai dan haskece ba sosai ba, yanada kyakkyawar fuska mai dauke da manyan idanuwa lumsassu,hancinsa dogo ne madaidaici sai dan madaidaicin bakinsa, atakaice dai yakai duk inda ake neman kyakkyawan saurayi.

Shi kadai ne kwal awurin mahaifiyarsa kuma tun tasowarsa shi kadai yake gani acikin gidansu daga shi sai umminsa, wannan dalilin ne yasa bai shaku da kowa ba sai ita kuma babu wanda yasani bayan ita,

Aliyu yarone mai zuciya sannan mai kokarin neman na kanshi domin tun yana yaro karami dan primary ya iya gyaran mota,kullum idan yataso daga makaranta sai yatafi gareji, dan kudin da yake samowa dashi yake biyan kudin makaranta sannan yasayi littattafa.

Tun lokacin da yafara sanin ciwon kanshi yasamu kansa cikin damuwa sakamakon rashin sanin waye mahaifinsa, kullum da wannan damuwar yake kwana yake tashi,

Acikin yan lokutan da yake samu idan yadawo daga gareji yake tafiya makarantar allo tawani malami mai suna malam lawan liman wanda ya kasance shine limamin wannan unguwar kuma cikin ikon ubingiji a hannun wannan mutumi Aliyu ya samu ilimi mai dunbin yawa wanda har takaishi ga sauke alqur’ani mai girma, ganin haka yasa Malam lawan daukar Aliyu tamkar danshi wanda yahaifa acikinshi shiyasa shi kadai Aliyu yake gani a matsayin uba kuma makusanci.

Komai na Malam lawan Aliyu yasani kuma ya dorashi akai, lokacin da yafara jami’a lokacin Malam lawan yabude islamiyya ta yara da matan aure kuma yadora Aliyu akai a matsayin wanda zai rinka kula da al’amuran makarantar,

Ananne Aliyu yahadu da muslima wacce aka dauketa itama a matsayin Malama, muslima yarinya ce mai kunya da biyayya ga sanin yakamata sannan tanada ilmin addini mai zurfi shiyasa tashiga zuciyar Aliyu sosai.

 

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻

 

*HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI….!*🤴🏻

 

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

*7*

 

***Soyayya ce mai karfi tsakanin Aliyu da muslima domin har Malam lawan yaje gidansu musliman ya nemarwa Aliyu izinin zuwa wurinta kuma mahaifinta ya amince,

Aliyu har yagirma ya mallaki hankalin kansa bai daina fama da damuwar rashin sanin takamaimai waye mahaifinsa ba duk da dabi’un Ummi da halayenta kadai sun isa bashi amsar tambayoyinsa.

***

Tunda halimatu takoma gida take gwada no Aliyu amma abin mamaki bata shiga nan tashiga damuwa sosai, koda yaushe cikin tunaninsa take tana son taje taganshi amma zuciyarta tana hanata.

Aliyu kuwa shi tunima yawani manta da wata wai ita halimatu sabgar da ta dameshi kawai yakeyi,

Misalin karfe 4 saura yabar gareji ya nufi gida, kamar yadda yasani kuma yasaba duk jama’ar dake zagayen unguwarsu basa yi dashi saboda wani dalilinsu nadaban shiyasa shima yake harkarsa shi kadai dan ko aboki bashida shi,

Cikin gidan ya tasamma bayan ya tura kofar wadda saura kiris ta karasa yagewa, a tsakar gida ya iske Ummi kamar yadda ya zata.

Tana kishingide tana sauraron kidan garayar dake faman tashi daga cikin radion dake gefenta sai faman gyada kai take tana bi,

Agabanta ya tsugunna tareda kai hannu yakashe radion fuskarshi kunshe da damuwa,

“Dan Allah Ummi kidaina sauraron ire iren wadannan kide kiden saboda sam basuda amfani, amma Ummi da ace karatu kika kunna ko wani wa’azi kinga da sai ki samu lada….”

Irin kallon da tayi masane yasashi gaggawar sunkuyar da kanshi tareda sake yin kasa da muryarsa bayan ya tausasata,

“Kiyi hakuri Ummi, ki yafe min dan Allah”

“Aliyu meyasa ka rainani ne baka ganina da kima?”

“Bahaka bane ummi, dan Allah kiyi hakuri karki yi fushi dani” yafada atausashe cikin ladabi,

Jijjiga kai tayi bayan tayi kwafa,

“Shikenan,tashi kaje kayi uzurinka”

Mikewa yayi yanufi dakinsa yana cire rigar dake jikinsa, kayan jikinsa yacire yarage daga shi sai gajeren wando da farar singileti, fitowa yayi yadauki bucket yaje yadebi ruwa yashiga ban daki,

Mintuna kadan yafito ya tsugunna yayi alwala har lokacin ummi na nan inda take bata motsaba tana faman taunar goro,

Cikin dakinshi yashiga ya tsane ruwan jikinsa sannan yadauki turaren touch me body spray yafeshe jikinsa sannan ya bude akwatin adana kayansa yaciro wani sky blue din yadi marar kauri yasaka bayan yasauya kananan kayansa naciki,

Perform spray na touch me yadauka yafeshe kayansa dasu sannan ya mayar da komai muhallinsa ya sunkuya yadauki wayarsa wacce ke ajiye kan yar madaidaiciyar katifarsa yasata acikin aljihu, hula yasaka sannan yadauki alqur’aninsa yafito daga cikin dakin yana gyara labulen dakin,

Dan rissinawa yayi agaban ummi,

“Ummi nafito bari inje…”

“To Aliyu Allah yakiyaye hanya yabada sa’a”

Murmushi yayi kafin yace,

“Amin ummina, me zan taho miki dashi?”

“Bana bukatar komai Aliyu, Allah yayi maka albarka”

Murmushi yayi yamike,

“Amin, natafi saboda naji kamar anshiga masallaci…”

“Adawo lafiya”

Da murmushi akan fuskarsa yafita daga cikin gidan, yana fitowa yahango sahibarsa muslima tana tahowa fuskarta rufe da nikab tana sanye da maroon din hijabi wanda yasauka mata har kasa,

Wurinta yadosa kamar yadda itama wurinshi take tahowa,

“Assalamu alaikum ya sayyadi….” Shine abinda tafada lokacin da suka karasa kusa da juna,

“Wa alaikumussalam ya sayyada, ayi min afuwa banyi salla ba,ga alqur’anina kitafi dashi sai nataho, idan kuma zaki shiga wurin ummi to..”

“A’a bazan shigaba, bani dai intafi maka da alqur’anin naka sai kataho”

Mika mata yayi tawuce shikuma yawuce masallaci,

Bayan an idar da salla yafito yanufi makarantar islamiyyar da yake koyarwa,

Hango muslima yayi har lokacin tana tafiya bata karasaba,

Murmushi yayi yadaga kafa har ya cimmata,

“Assalamu alaikum” yace da ita yana daga bayanta,

“Wa alaikumussalam warahmatullah wabrakatuhu, har ka karaso?”

“Ehh mana har nazo na tarar dake ahanya saboda kin tsaya yanga”

Murmushi tayi tajuya ta kalleshi taci gaba da tafiya yana biye da ita,

“Babu wata yanga ya sayyadi, bana sone inrigaka shiga makarantar shiyasa”

“To ai shiyasa nace kishiga wurin ummi kika k’i shiga”

Girgiza kai tayi,

“Ni kunyar zuwa wurin ummi nake wallahi”

“Gashi kuma kin kusa zama sirikarta ya za ayi?”

Murmushi tayi batace komai ba har suka shiga cikin makarantar,

Juyawa tayi domin tabashi alqur’aninshi nan yakafeta da kallo,

“To gimbiya ai sai ataimaka abude min fuskar ingani tunda anan babu mai gane min”

Akunyace tadage nikab din fuskarta dauke da murmushi sai dai idonta akasa takasa kallonshi, alqur’anin ya karba yana bin hannunta da kallo wanda yasha bakar fulawa sannan yatsunta sunsha jan lalle,

“Wannan kunshin yayi kyau dafatan ni aka yiwa dai?”

Juyawa tayi tabar wurin tana dariya, shima dariyar yakeyi yanufi wurin Malam lawan wanda ke can saman baranda yana rikeda dorina da littafin akdari a hannunsa wasu dalibai kanana zaune agabansa.

Abangaren halimatu kuwa yau kimanin kwana biyar da zuwanta gidansu Aliyu, duk yanda takai da son tamance da lamarinsa tacire tunaninsa daga ranta abin yaci tura, bata da wani lokaci nata nakanta saiko na tunanin Aliyu sannan takasa samunshi awaya idan takira sai taji wayar akashe,

Kamar koda yaushe yanzun ma zaune take agaban library itada Abdul wanda suka fito karatu amma sam karatun nata yaki yuyuwa sai faman jan tsaki take,

Matsawa kusa da ita Abdul yayi,

“Princess meke damunki ne? Naga sai tsaki kikeyi kodai nayi laifine?”

Girgiza masa kai tayi tana kallon lecture note din dake hannunta,

“Babu komai kainane ke ciwo…”

“Ayya sorry, kitafi gida kawai kije ki huta da daddare sai kiyi karatun”

“Gaskiya inaga hakan zaifi, bari naje”

Mikewa tayi tana duba agogon hannunta wanda yanuna karfe 6 saura minti shida, binta da kallo Abdul yayi tana sanye da yeluwar atamfa mai digon baki ajiki dinkin doguwar riga tayafa bakin karamin mayafi akanta,

Motarta tabude tashiga taja tana dagawa Abdul hannu, wurin wani mai sayar da fruits ta tsaya bayan tafita daga makarantar nan tasiyi Apple guda hudu manya green da red da kankana kwallo daya,

Gidansu Aliyu ta tasamma zuwa domin tana bukatar ganinshi,

Akofar gidansu tayi packing tadauki ledar fruits din tashiga cikin gidan,

Akan tabarma tatarar da ummi zaune atsakar gida tana gyara abin wuyanta wanda ya tsinke,

Cikin fara’a ummi ta karbeta suka gaisa, zuwa can tace,

“Uhm mama baki ganeni ba ko?”

Dariya ummi tayi irin tasu ta manya kafin tace,

“Ya ban ganeki ba, bakece kikazo rannan kuka shigo tareda Aliyu ba?”

“Hakane kam mama, nice”

“To ai naganeki” ummi tafada tana murmushi,

Mikawa ummi ledar tayi bayan an dan dauki lokaci,

“Mama ga wannan babu yawa dama gaisheki nazo yi”

Cikin fara’a da murna ummi takarbi ledar tabude,

“Lalalahhhh harda wahala haka Sadiya? To nagode madalla, Allah yasaka da alkhairi”

“Babu komai mama, amin”

Halimatu tana son ta tambayi Aliyu amma kuma tana jin kunyar ummi gashi kuma har magrib tayi domin anfara shiga salla awasu masallatan,

“Shima Aliyun yau bai dawo dawuriba daga islamiyya ko a ina ya tsaya?” Ummi tafada bayan ta yunkura zata tashi,

“Allah sarki, Allah yadawo dashi lafiya” inji halimatu,

“Amin, bari inzuba miki ruwan alwala kiyi salla kafin yashigo ko?”

“A’a mama kibarshi ai tafiya ma zanyi idan naje gida sai inyi” halimatu tafada cikeda kunya domin tana fashin salla,

“A’a kijira yadawo mana kuma” ummi tace da ita bayan tadauki buta zata zagaya bayi,

Tana nan zaune akan tabarma ita kuma ummi tana alwala suka jiyo alamun shigowa,

Sallamar Aliyu ce tabugi dodon kunnuwanta kafin daga bisani sansanyar kamshinsa na touch me yakawowa kofofin hancinta sumame tuni tayi suman zaune awurin bayan ta diririce……….

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
[9/22, 6:59 AM] ‪+234 803 929 8487‬: *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*DAN ASALI…!*🤴🏻

*_NA_*
*_UMMI A’ISHA_*

 

*6*

 

***Wani takaicine ya lullube zuciyarta lokaci guda domin sam wayar bata shiga ba asalima wai is the stop computer take fada mata,

Kishingida tayi tarasa gaba daya abinda yake yimata dadi, awannan lokacin da take ciki ji take kamar tayi tsuntsuwa taje ga Aliyu taganshi taga halin da yake ciki,

Dafe goshinta tayi tana tambayar zuciyarta,

“Wannan wacce irin masifa ce? Daga ganin mutum sai hankalina da tunanina gaba daya ya tattara zuwa gareshi ?”

Dan siririn tsaki ta saki bayan ta zame ta kwanta,

Shiru tayi tana jin zuciyarta tana harbawa da karfi da karfi,

Daren wannan ranar batayi wani isasshen bacci ba sai jikin asuba, duk da haka yau tayi kokarin tashi da wuri domin bata son taci gaba da missing lectures dinta,

9 saura tafito cikin shiri tayi breakfast,part din abba taje tagaidashi sannan tayiwa umma sallama tatafi,

Ahankali take tafiya tana bin wakar _selfish_ dake tashi cikin motar wacce ta kunna, wani sanyi ne da farin ciki suke ratsa zuciyarta saboda yau tasawa ranta sai ta ziyarci har cikin gidansu Aliyu,

Koda tashiga school ma su Abdul sunga sai faman fara’a takeyi gashi yau bata makaraba,

6 saura yan mintuna suka fito daga makaranta taje ta sauke sabira agida daga nan tawuce unguwarsu Aliyu,

Tana shiga layinsu tahango Aliyun suna tahowa shida wata budurwa wacce ahaife zatayi kusan sa’arta,

Gabanta ne yayi mummunar faduwa domin abisa dukkan alamu akwai shakuwa mai karfi tsakaninshi da yarinyar saboda irin yanda taga yana ta sakin lallausan murmushi, babu shiri tayi azamar taka burki bayan ta gangara gefen titi,

Kallonsu taci gaba dayi suna tahowa, yarinyar tana sanye da coffee colour din hijab mai hannu wanda yake har kasa sannan ga nikab nan amma ta dageshi, tana rikeda alqur’ani mai girma izu sittin, yayinda shikuma Aliyun yake sanye da shadda milk colour riga da wando,yasanya hula baka akanshi shi dinma rike yake da alqur’ani ahannunshi,

Dai dai kofar gidansu Aliyu suka tsaya shida yarinyar wanda da alama magana sukeyi amma ita bata jiyo abinda suke fada,

Sunfi minti biyar atsaye kafin daga bisani taga yarinyar tasauke nikab din fuskarta daga ita har Aliyun murmushi suke, juyawa yarinyar tayi tawuce shikuma Aliyu yanufi kofar gidansu,

Da sauri halimatu tafito tabishi yana kokarin shiga takira sunanshi, ahankali yajuyo yana gyara rikon alqur’anin dake hannunsa,

“Kayi mamakin ganina da yammancin nan ko?” Tafada wadda gaba daya tarasa abin fada ne shiyasa ta bullo tahaka,

Kawar da kanshi gefe yayi sannan yace,

“Ehh hakane, amma dai ina fata lafiya?”

Dan murmushi tasaki sannan ta amsa,

“Lafiya lau kawai nazone ingaidaka kaida mutanen gida”

Dan jimm yayi kafin yace,

“Babu damuwa bismillah…”

Tura kofar yayi yashiga nan tabishi zuwa cikin gidan wanda yake ginin jar kasa sannan fadin tsakar gidanma bashida wani girma dan karamine ba can ba, dakuna ne guda biyu suna kallon juna sai dan makewayi daga can gefe daya sannan da dan wurin girki wanda aka zagaye da langa langa,

Gani tayi yatsaya akofar dakin dake fuskantarsu yana magana cikin ladabi da girmamawa bayan ya dan rissina,

“Ummi nadawo, amma tareda bakuwa nake tazo gaidaki?

“Muslima ce tazo?” Daga cikin dakin aka tambaya wadda ko ba afada mata ba tasan mahaifiyarshi ce,

“A’a Ummi ba ita bace, watace da na gyarawa mota”

“To bari infito”

Yana tsaye mahaifiyar tashi tafito rikeda tabarma tana yimata sannu da zuwa,

Shimfida mata tabarmar tayi shikuma Aliyu yashige dayan dakin wanda ke fuskantar na mahaifiyarshi,

Cikin ladabi halimatu tagaida ummin tashi aranta tana tunanin may be Aliyu su biyune ke rayuwa acikin gidan daga shi sai mahaifiyarshi domin bataji motsin kowaba gashi gidan ma baiyi kalar wanda jama’a da dama ke rayuwa cikinsa ba, bin gidan take da kallo gashi nan dai ashare yake tass a tsaftace duk da bawani mai kyau bane amma babu alamun kazanta atare dashi.

“Kema makarantarku daya da Aliyu?” Ummi ta tambayeta tana murmushi,

Girgiza kai halimatu tayi kafin tace,

“A’a ba makarantarmu daya ba”

“Allah sarki” Ummi tafada daidai lokacin Aliyu yafito daga cikin dakinshi yadauki buta dake ajiye can gefe guda yanufi kan wani dutsi yazauna yasoma yin alwala saboda magrib tagabato domin wasu masallatan ma har anfara kiran salla,

Ganin haka yasa halimatu tashi tayiwa Ummi sallama tace zata tafi,

Godiya sosai ummin tayi mata kamar halimatun takawo mata wani abu, dan satar kallon Aliyu halimatu tayi nan taga hankalinsa ma sam baya wurinsu yanaga alwalar da yake shirin kammalawa,

Hanyar fita daga gidan tabi yayinda shikuma Aliyu yamike da niyyar zuwa masallaci,

“Bari inje intafi sai wani lokacin…” Tafada bayan ta juya taganshi abayanta,

“To mun gode, kigaida gida” yace da ita kasa kasa,

“Ok” ta amsa masa tareda wucewa,

Ta cikin glass din motarta take hangoshi yana kokarin shiga masallaci, saida taga shigarsa sannan ta murza motarta tabar wurin tana cike da kewar kallon kyakkyawar siffarsa.

WANENE ALIYU?

Aliyu matashin saurayine dan kimanin shekaru 28 zuwa 29,duk inda ake neman cikakke kuma kyakkyawan namiji to Aliyu yakai domin yanada duk wata siffa wacce ake bukata awurin da namiji,kalar fatarsa mai dan haskece ba sosai ba, yanada kyakkyawar fuska mai dauke da manyan idanuwa lumsassu,hancinsa dogo ne madaidaici sai dan madaidaicin bakinsa, atakaice dai yakai duk inda ake neman kyakkyawan saurayi.

Shi kadai ne kwal awurin mahaifiyarsa kuma tun tasowarsa shi kadai yake gani acikin gidansu daga shi sai umminsa, wannan dalilin ne yasa bai shaku da kowa ba sai ita kuma babu wanda yasani bayan ita,

Aliyu yarone mai zuciya sannan mai kokarin neman na kanshi domin tun yana yaro karami dan primary ya iya gyaran mota,kullum idan yataso daga makaranta sai yatafi gareji, dan kudin da yake samowa dashi yake biyan kudin makaranta sannan yasayi littattafa.

Tun lokacin da yafara sanin ciwon kanshi yasamu kansa cikin damuwa sakamakon rashin sanin waye mahaifinsa, kullum da wannan damuwar yake kwana yake tashi,

Acikin yan lokutan da yake samu idan yadawo daga gareji yake tafiya makarantar allo tawani malami mai suna malam lawan liman wanda ya kasance shine limamin wannan unguwar kuma cikin ikon ubingiji a hannun wannan mutumi Aliyu ya samu ilimi mai dunbin yawa wanda har takaishi ga sauke alqur’ani mai girma, ganin haka yasa Malam lawan daukar Aliyu tamkar danshi wanda yahaifa acikinshi shiyasa shi kadai Aliyu yake gani a matsayin uba kuma makusanci.

Komai na Malam lawan Aliyu yasani kuma ya dorashi akai, lokacin da yafara jami’a lokacin Malam lawan yabude islamiyya ta yara da matan aure kuma yadora Aliyu akai a matsayin wanda zai rinka kula da al’amuran makarantar,

Ananne Aliyu yahadu da muslima wacce aka dauketa itama a matsayin Malama, muslima yarinya ce mai kunya da biyayya ga sanin yakamata sannan tanada ilmin addini mai zurfi shiyasa tashiga zuciyar Aliyu sosai.

 

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻

 

*HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI….!*🤴🏻

 

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

*7*

 

***Soyayya ce mai karfi tsakanin Aliyu da muslima domin har Malam lawan yaje gidansu musliman ya nemarwa Aliyu izinin zuwa wurinta kuma mahaifinta ya amince,

Aliyu har yagirma ya mallaki hankalin kansa bai daina fama da damuwar rashin sanin takamaimai waye mahaifinsa ba duk da dabi’un Ummi da halayenta kadai sun isa bashi amsar tambayoyinsa.

***

Tunda halimatu takoma gida take gwada no Aliyu amma abin mamaki bata shiga nan tashiga damuwa sosai, koda yaushe cikin tunaninsa take tana son taje taganshi amma zuciyarta tana hanata.

Aliyu kuwa shi tunima yawani manta da wata wai ita halimatu sabgar da ta dameshi kawai yakeyi,

Misalin karfe 4 saura yabar gareji ya nufi gida, kamar yadda yasani kuma yasaba duk jama’ar dake zagayen unguwarsu basa yi dashi saboda wani dalilinsu nadaban shiyasa shima yake harkarsa shi kadai dan ko aboki bashida shi,

Cikin gidan ya tasamma bayan ya tura kofar wadda saura kiris ta karasa yagewa, a tsakar gida ya iske Ummi kamar yadda ya zata.

Tana kishingide tana sauraron kidan garayar dake faman tashi daga cikin radion dake gefenta sai faman gyada kai take tana bi,

Agabanta ya tsugunna tareda kai hannu yakashe radion fuskarshi kunshe da damuwa,

“Dan Allah Ummi kidaina sauraron ire iren wadannan kide kiden saboda sam basuda amfani, amma Ummi da ace karatu kika kunna ko wani wa’azi kinga da sai ki samu lada….”

Irin kallon da tayi masane yasashi gaggawar sunkuyar da kanshi tareda sake yin kasa da muryarsa bayan ya tausasata,

“Kiyi hakuri Ummi, ki yafe min dan Allah”

“Aliyu meyasa ka rainani ne baka ganina da kima?”

“Bahaka bane ummi, dan Allah kiyi hakuri karki yi fushi dani” yafada atausashe cikin ladabi,

Jijjiga kai tayi bayan tayi kwafa,

“Shikenan,tashi kaje kayi uzurinka”

Mikewa yayi yanufi dakinsa yana cire rigar dake jikinsa, kayan jikinsa yacire yarage daga shi sai gajeren wando da farar singileti, fitowa yayi yadauki bucket yaje yadebi ruwa yashiga ban daki,

Mintuna kadan yafito ya tsugunna yayi alwala har lokacin ummi na nan inda take bata motsaba tana faman taunar goro,

Cikin dakinshi yashiga ya tsane ruwan jikinsa sannan yadauki turaren touch me body spray yafeshe jikinsa sannan ya bude akwatin adana kayansa yaciro wani sky blue din yadi marar kauri yasaka bayan yasauya kananan kayansa naciki,

Perform spray na touch me yadauka yafeshe kayansa dasu sannan ya mayar da komai muhallinsa ya sunkuya yadauki wayarsa wacce ke ajiye kan yar madaidaiciyar katifarsa yasata acikin aljihu, hula yasaka sannan yadauki alqur’aninsa yafito daga cikin dakin yana gyara labulen dakin,

Dan rissinawa yayi agaban ummi,

“Ummi nafito bari inje…”

“To Aliyu Allah yakiyaye hanya yabada sa’a”

Murmushi yayi kafin yace,

“Amin ummina, me zan taho miki dashi?”

“Bana bukatar komai Aliyu, Allah yayi maka albarka”

Murmushi yayi yamike,

“Amin, natafi saboda naji kamar anshiga masallaci…”

“Adawo lafiya”

Da murmushi akan fuskarsa yafita daga cikin gidan, yana fitowa yahango sahibarsa muslima tana tahowa fuskarta rufe da nikab tana sanye da maroon din hijabi wanda yasauka mata har kasa,

Wurinta yadosa kamar yadda itama wurinshi take tahowa,

“Assalamu alaikum ya sayyadi….” Shine abinda tafada lokacin da suka karasa kusa da juna,

“Wa alaikumussalam ya sayyada, ayi min afuwa banyi salla ba,ga alqur’anina kitafi dashi sai nataho, idan kuma zaki shiga wurin ummi to..”

“A’a bazan shigaba, bani dai intafi maka da alqur’anin naka sai kataho”

Mika mata yayi tawuce shikuma yawuce masallaci,

Bayan an idar da salla yafito yanufi makarantar islamiyyar da yake koyarwa,

Hango muslima yayi har lokacin tana tafiya bata karasaba,

Murmushi yayi yadaga kafa har ya cimmata,

“Assalamu alaikum” yace da ita yana daga bayanta,

“Wa alaikumussalam warahmatullah wabrakatuhu, har ka karaso?”

“Ehh mana har nazo na tarar dake ahanya saboda kin tsaya yanga”

Murmushi tayi tajuya ta kalleshi taci gaba da tafiya yana biye da ita,

“Babu wata yanga ya sayyadi, bana sone inrigaka shiga makarantar shiyasa”

“To ai shiyasa nace kishiga wurin ummi kika k’i shiga”

Girgiza kai tayi,

“Ni kunyar zuwa wurin ummi nake wallahi”

“Gashi kuma kin kusa zama sirikarta ya za ayi?”

Murmushi tayi batace komai ba har suka shiga cikin makarantar,

Juyawa tayi domin tabashi alqur’aninshi nan yakafeta da kallo,

“To gimbiya ai sai ataimaka abude min fuskar ingani tunda anan babu mai gane min”

Akunyace tadage nikab din fuskarta dauke da murmushi sai dai idonta akasa takasa kallonshi, alqur’anin ya karba yana bin hannunta da kallo wanda yasha bakar fulawa sannan yatsunta sunsha jan lalle,

“Wannan kunshin yayi kyau dafatan ni aka yiwa dai?”

Juyawa tayi tabar wurin tana dariya, shima dariyar yakeyi yanufi wurin Malam lawan wanda ke can saman baranda yana rikeda dorina da littafin akdari a hannunsa wasu dalibai kanana zaune agabansa.

Abangaren halimatu kuwa yau kimanin kwana biyar da zuwanta gidansu Aliyu, duk yanda takai da son tamance da lamarinsa tacire tunaninsa daga ranta abin yaci tura, bata da wani lokaci nata nakanta saiko na tunanin Aliyu sannan takasa samunshi awaya idan takira sai taji wayar akashe,

Kamar koda yaushe yanzun ma zaune take agaban library itada Abdul wanda suka fito karatu amma sam karatun nata yaki yuyuwa sai faman jan tsaki take,

Matsawa kusa da ita Abdul yayi,

“Princess meke damunki ne? Naga sai tsaki kikeyi kodai nayi laifine?”

Girgiza masa kai tayi tana kallon lecture note din dake hannunta,

“Babu komai kainane ke ciwo…”

“Ayya sorry, kitafi gida kawai kije ki huta da daddare sai kiyi karatun”

“Gaskiya inaga hakan zaifi, bari naje”

Mikewa tayi tana duba agogon hannunta wanda yanuna karfe 6 saura minti shida, binta da kallo Abdul yayi tana sanye da yeluwar atamfa mai digon baki ajiki dinkin doguwar riga tayafa bakin karamin mayafi akanta,

Motarta tabude tashiga taja tana dagawa Abdul hannu, wurin wani mai sayar da fruits ta tsaya bayan tafita daga makarantar nan tasiyi Apple guda hudu manya green da red da kankana kwallo daya,

Gidansu Aliyu ta tasamma zuwa domin tana bukatar ganinshi,

Akofar gidansu tayi packing tadauki ledar fruits din tashiga cikin gidan,

Akan tabarma tatarar da ummi zaune atsakar gida tana gyara abin wuyanta wanda ya tsinke,

Cikin fara’a ummi ta karbeta suka gaisa, zuwa can tace,

“Uhm mama baki ganeni ba ko?”

Dariya ummi tayi irin tasu ta manya kafin tace,

“Ya ban ganeki ba, bakece kikazo rannan kuka shigo tareda Aliyu ba?”

“Hakane kam mama, nice”

“To ai naganeki” ummi tafada tana murmushi,

Mikawa ummi ledar tayi bayan an dan dauki lokaci,

“Mama ga wannan babu yawa dama gaisheki nazo yi”

Cikin fara’a da murna ummi takarbi ledar tabude,

“Lalalahhhh harda wahala haka Sadiya? To nagode madalla, Allah yasaka da alkhairi”

“Babu komai mama, amin”

Halimatu tana son ta tambayi Aliyu amma kuma tana jin kunyar ummi gashi kuma har magrib tayi domin anfara shiga salla awasu masallatan,

“Shima Aliyun yau bai dawo dawuriba daga islamiyya ko a ina ya tsaya?” Ummi tafada bayan ta yunkura zata tashi,

“Allah sarki, Allah yadawo dashi lafiya” inji halimatu,

“Amin, bari inzuba miki ruwan alwala kiyi salla kafin yashigo ko?”

“A’a mama kibarshi ai tafiya ma zanyi idan naje gida sai inyi” halimatu tafada cikeda kunya domin tana fashin salla,

“A’a kijira yadawo mana kuma” ummi tace da ita bayan tadauki buta zata zagaya bayi,

Tana nan zaune akan tabarma ita kuma ummi tana alwala suka jiyo alamun shigowa,

Sallamar Aliyu ce tabugi dodon kunnuwanta kafin daga bisani sansanyar kamshinsa na touch me yakawowa kofofin hancinta sumame tuni tayi suman zaune awurin bayan ta diririce……….

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
[9/22, 6:59 AM] ‪+234 803 929 8487‬: *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*DAN ASALI…!*🤴🏻

 

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

 

*8*

 

***Sunkuyar da kanta tayi cikin gaggawa,

Ciki yakarasa zuciyarsa cikeda mamakin sake ganin Sadiya agidansu akaro na biyu, ita kuwa takasa koda dagowa bare ta iya kallonshi, muryar ummi ta tsinkayo tana cewa,

“Aliyu yau a ina katsaya ne gashi halimatu tazo da tafiya ma zatayi nice nahanata…”

Fuskarshi babu yabo babu fallasa ya amsawa Ummi da,

“Wallahi Ummi Malam ne ya tsayar dani mukayi dan wani aiki”

“Allah sarki to yayi kyau, yana nan lafiya Malam dinko?”

“Lafiya lau yake yana gaisheki”

Duk da yaga halimatu amma haka yayi kokarin saka kansa cikin dakinsa batare da yayi mata magana ba hakan dayayi sai yasa jikinta yin sanyi duk da ta fahimci shi bamai yawan surutu bane dama sannan kamar halayyarsa ce shariya da daga kai,

Jimm kadan yafito daga cikin dakin nan tayi gaggawar gai dashi lokacin har Ummi ta idar da alwalarta,

“Lafiya lau….” Ya amsa daga haka yanufi buta zai dauka yayi alwala nan maganar da ummi keyi ta dakatar dashi,

“Aliyu kaga wadannan kayan da halimatu takawo kayan marmari”

Shiru yayi baiyi magana ba yawuce wurinda zaiyi alwala,

“Dazu kuma da zaka fita namanta ince maka kataho min da goro dama goron nawa saurane kuma har na tauneshi…”

Sai lokacin yayi magana, “idan nagani yanzu zan taho miki dashi”

“Ina za asamu goro yanzu da mangarubar nan Aliyu…”

Alwala yatsugunna yayi bayan ya idar yazo ya ajiye butar yajuya yafita, tashi halimatu tayi tabi bayanshi zuwa waje,

“Amm Aliyu…” Takira sunanshi bayan ta sunkuyar da kanta tana wasa da yan yatsunta,

Tsayawa yayi batare da ya kalleta ba,

“Number din da kabani idan nakiraka bata shiga…”

Batareda ya kalleta ba yace,

“Inajin network ne”

Daga haka yawuce zuwa masallaci, batare data koma cikin gidanba itama tawuce tatafi.

Ganin irin karbar da Aliyu yayi mata abin ba karamin damunta yakeba domin ko baccima ranar dakyar tasamu yinsa dan takaici,

Washe gari sukuku tatashi kamar marar lafiya, tunda tazauna domin yin breakfast umma ke kallonta tana nazartar yanayin datake ciki, dakyar ta iya shan tea rabin cup amma sauran kayan karin takasa koda tabasu,

“Nikam halimatu yau bakida lafiya ne?”

Girgiza kai tayi sannan ta kalli umma,

“Lafiya ta lau umma jikinane dai babu kwari”

“To amma duk da haka da kin daure kin karya ai”

“Umma bakina ne babu taste amma zan siyi moi moi idan nashiga school, saurima nake kar nayi late”

“To Allah yakiyaye yabada sa’a” Umman tafada cikin kulawa, sidebag dinta ta rataya tafita.

Zama tayi acikin mota ta jingina kanta jikin kujera ta tsurawa glass idanu haka kawai yanayin dataga Aliyu yanuna ke mutukar damunta kamar zatayi kuka takeji,

Sau uku sabira tana knocking din glass din side din datake zaune amma bataji ba har saida tayi na hudu ananne tajuyo fuskarta cikeda damuwa tafara sauke glass din.

“Bakida lafiya ne Sadiya?”

“Wallahi lafiya lau nake sabira”

“To meke damunki wanda har yasa kika zurfafa haka acikin tunani?”

“Babu abinda ke damuna”

“Haba baiwar Allah sake tunani dai domin kowa yaganki yau yasan akwai damuwa atattare dake”

Murmushin yake ta kakaro tayi ta dauki sidebag dinta tafito daga cikin motar, kokarin kawar da damuwar dake kan fuskarta tayi inda tasaki ranta suka soma wasa da dariya itada sabira har Abdul yazo ya iskesu,

Karfe 1 na rana tagama lectures dinta suka fito daga lecture hall, kasancewarta ma’abociyar son cin snacks yasata jansu sabira wani dan karamin confectionery dake cikin school din,

Meat pie da spring rolls tayi order sai ko abin jika makoshi, tashi Abdul yayi yaje kawai yakarbo musu a take away yafito domin gida yake son tafiya dad dinshi na nemanshi,

“Nifa kasan guda bibbiyu sunyi min kadan….” Inji halimatu,

“Naki guda hurhudu ne na sabira ne dai guda bibbiyu”

Dariya sukayi dukkansu banda sabira,

“Wallahi Abdul kafadi abinda ke ranka saboda wannan kunbiya kunbiyar babu inda zai kaiku”

Murmushi yayi ita kuma halimatu tayi dariya takarbi ledojin dake hannun Abdul tace,

“Friend jeka katafi kiran da dad yake yi maka kar yagaji da jiranka”

“Nagode princess da wannan izini da aka bani, sai munyi waya ko?”

“Insha Allah” tafada tareda yin gaba, nan sabira tabi bayanta tana mita,

“Ayi dai mugani idan tayi tsami zamuji…”

Dariya halimatu tayi saboda jin abinda sabira tace domin ita abinda ke ranta kuma yake damunta da banbanci da wanda sabira take tunani.

A lungun gidansu sabira tayi packing sabirar tafita tana sake jaddada mata cewar gobe karta manta da sakonta na turaren wanka,

Tana kokarin fitowa daga lungun tahango wani tsoho zaune da tulin goro agabansa da alama na siyarwa ne nan maganar mahaifiyar Aliyu tafado mata wadda tayi jiya akan goro,

Packing tayi tafita zuwa wurin mai siyar da goron, na 1k tasiya farare tatas masu kyau gwanin sha’awa a ido, acikin bakar leda ya zuba mata takarba ta koma mota,

Duk da abinda Aliyu yayi mata jiya hakan bai hanata komawa gidan ba yau,

Ledar goron ta dauka tashiga cikin gidan da sallama abakinta, ji tayi ummi ta amsa wacce ke can cikin dakinta kasancewar rana ce kwall agarin,

“Karaso ciki, lale marhabun”

Cikin dakin tashiga ta zauna akan tarbarmar dake shimfide cikin dakin ita kuma ummin tana zaune gefen katifa,

Fita Ummi tayi domin kawo mata ruwa nan halimatu tafara bin dakin da kallo, babu komai aciki inbanda katifa sai ko wasu akwatunan karfe guda biyu sai wata tsohuwar karamar tv,sai yan tarkacen da ba arasa ba,

Shigowar ummine yasata tsaida idonta awuri daya takarbi kwanon dake hannunta wanda takawo mata ruwan, kafa kai tayi tasha sannan ta ajiye,

“Wannan zafin sai ana shan ruwa…” Inji Ummi tafada bayan ta zauna,

“Ehh danma ruwan da sanyi”

“Ehh ai aranda yake”

Yar hira suka cigaba da tabawa kafin halimatu ta mika mata ledar goron da takawo mata,

“Kai amma Allah yayi albarka, wallahi yau jina nake kamar wata marar lafiya akan banci goron nan ba”

Murmushi halimatu tayi,

“Mama haka goron yake da shiga rai?”

“Sosai ma kuwa ai indai kasaba dashi to duk ranar da baka ciba ji zakayi kamar bakada lafiya wasuma har ciwon kai sukeyi”

Dariya halimatu tayi tana jin dadin hirar domin Ummi tasaki jiki da ita ba kamar Aliyu ba, tashi tayi takoma mota tadauko take away din da suka iyo a school domin taji ummi nacewa indomie Aliyu yadafa musu da safe da soyayyen kwai ita kuwa bata ciba kwan kadai taci gashi bai dawoba har yanzu,

Saka musu snacks din tayi agaba suka fara ci domin ummi ta sakar mata fuska fiyeda zatonta,

Sallamar Aliyu ce takatse mata maganar da takeyi, tunda ya hango takalma hill jikinsa yabashi itace, ai kuwa itance kamar yadda ya zata,

Ransa ne yaji yabaci sakamakon ganin ummi tana cin snacks din data kawo mata, dan daure fuska yayi sannan yakarasa cikin dakin ya ajiyewa ummi ledar dake hannunsa, ko kallon halimatu baiyi ba ya amsa gaisuwarta yafita daga cikin dakin,

Ledar da yashigo da ita ummi tadauka tabude nan taga awara ce da zafinta sai tururi takeyi,

“Aliyu wannan awarar fa?”

“Ummi siyo miki nayi kici kafin abinci yasamu” ya amsa daga can kofar dakinshi wanda yake kokarin shiga,

“To Allah yayi albarka, ya kara budi”

Duk da halimatu najin kunyar Ummi saida taci awarar nan domin ba karamin dadi tayiba gashi tasha albasa da tumatir da kabeji ga yaji agefe, kusan tare suka cinye awarar, shikuwa Aliyu tunda yashiga daki bai fitoba,

Tashi halimatu tayi da niyyar tafiya nan tayiwa ummi sallama, daidai kofar dakin Aliyu ta kalla nan tahangoshi aciki yana zaune gefen katifa daga shi sai farar vest da dogon wando yana yin waya fuskarshi dauke da murmushi wanda ke nuna alamar yana mutukar jin dadin wayar,

Haka kawai gaban halimatu yafara faduwa wanda har taji bazata iya hakuriba sai taje taji koda wa Aliyunta ke yin waya, bata san meya faruba ita dai kawai taganta atsakiyar cikin dakinsa nan kunnuwanta sukaji yana cewa,

“Shikenan duk yanda kikeso haka za ayi sahiba, babu damuwa sai nazo anjima ki tanadar min labari mai dadi…”

Sauke wayar yayi daga kunnenshi ya ajiyeta agefenshi sannan yatashi zaune daga kishingiden da yake ya kalleta bayan ya dage girarshi guda daya fuskarsa da alamun neman karin bayani…….

 

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

*9*

***Da kyar tasamu ta lalubo nutsuwarta bayan tasha gwagwarmaya da zuciyarta,

Har lokacin idanuwanshi suna kanta yana kallonta,

“Am…. Uhmm…dama nazone inyi maka sallama….” Takarshe maganar cikeda shagwabar da ita kanta bata san lokacin da tayiba”

“Shikenan kije ina zuwa…”

Juyawa tayi tafita tana jin gabanta yana faduwa, lokacin da taje gaban motarta tana kokarin budewa tajiyo maganarshi abayanta,

“Meyasa kike zuwa gidanmu??”

Taji ya jefo mata tambaya, kasa juyowa tayi ta tsaya ayanda take tana nazarin irin amsar da ta dace tabashi, jin bata amsaba yasashi sake maimaita mata tambayar nan tasamu ta daidaita nutsuwarta tajuya ta kalleshi,

“Saboda zumunci da kuma….”

“Da kuma me? Zumunci ban hana muyi zumumciba amma gaskiya ba irin wannan ba, nafarko kinga nidai ba saninki nayiba sannan kema bawai wani kwakkwaran sanina kikayiba sannan kuma ko ayanayi na rayuwa yananinmu ba iri daya bane”

Gyara tsayurta tayi saboda jin abinda yake fada har tajira ya diga aya,

“Hakane abinda kafada gaskiyane to amma ai Allah yana shirya al’amuransa yanda yaso koda kuwa mu mutane muna ganin abin bahaka bane ko kuma bai cancanta ba”

Murmushi taga yayi bayan yazira dukkan hannuwanshi acikin aljihun wandonshi,

“Halima kina sona ko?”

Dasauri ta kalleshi sakamakon tambayar dataji ya jefa mata, girgiza kai tayi gabanta yana faduwa,

“A’a me kagani na alamun so? Ko daya ni ba sonka nakeba kawai dai….”

“Naji dadin hakan domin bana bukatar wata soyayya daga wurin wata mace ayanzu haka saboda bana son matsala, ni presently inada wacce nake so kuma itama take sona,sannan dan Allah idan babu damuwa zumuncin ma basai yayi nisa irin haka yanda kika daukeshi ba, ina nufin ki daina zuwa gidanmu domin bana bukatar wani kusanci daga wurin kowa”

Yana kaiwa nan bai jira abinda zatace ba yajuya yakoma cikin gida yabarta tsaye,

Wani bacin raine da damuwa suka kawowa zuciyarta sumame cikin lokaci kankani zuciyarta tayi bakik kirin.

Aliyu nashiga cikin gida dakin Ummi yawuce wadda ke zaune tana karasa cin sauran snacks din da suka rage itada halimatu,

Zama yayi akan tabarma yayi kasa da kansa,

“Aliyu dauki kaima gashi kaci, wannan yarinyar kirkince halimatu tazo dashi…”

Girgiza kai yayi alamun bazai ciba,

“Au, bazaka ciba? Hakama fa jiya kaki cin wannan tufar da kankanar data kawo sai almajirai na sadakarwa da rabin kankanar domin idan nabarta lalacewa zataji tunda nariga da na yanka sauran tufar ne dai gashi can na adana….”

Dagowa yayi ya kalleta,

“Amma ummi meyasa zakiyi gaggawar sakin jiki da ita haka har kifara cin abin hannunta? Nifa wallahi yanzu ko kasheni za ayi ban san wacece ita ba, ban san daga inda takeba kuma ban san manufarta akanmu ba”

“Koma daga ina take to daga gidan mutuncine sannan kuma bata da wata mummunar manufa agaremu sai ta alkhairi,kuma dan tana sonmu ne take zuwa garemu dan haka babu ruwanka da ita, idan kai baka yarda da itaba toni na yarda da ita”

“To shikenan Ummi Allah yahuci zuciyarki”

Daga haka yamike yafita, murhu yaje yahada wuta yadora tukunya yazuba ruwa yarufe yakoma daki, haka yake fitowa lokaci zuwa lokaci yana dubawa har ruwan yatafasa, shinkafa yawanke ya zuba ya koma daki,

Bayan yasauke shinkafar ne yadauko guntuwar miyar jiya dake cikin tukunya ya dumama sannan ya kwashe a flask yakai dakin ummi bayan yadebi yar kadan wacce zaici.

Gareji yasake komawa bayan yayi wanka daga nan bai dawoba sai bayan sallar magrib, dakinsa yashige yayi shirin wanka, wani ash colour din yadi yasaka bayan yayi wankan yasha turaren _touch me_ da _sultan_ yafito yana rikeda hularsa ahannu,

Dakin Ummi ya leka nan yaganta kwance tana yan wake wakenta, girgiza kai yayi yai mata sallama yafita,

Masallaci yafara zuwa yayi sallar isha daga can yazarce gidansu muslima,

Yana zaune a dakalin dake kofar gidan tafito sanye da hijabi dan madaidaici,

Yana ganinta yaji wani farin ciki ya lullubeshi,sallamarta ya amsa cikin kulawa sannan yamike tsaye yana kallonta,

“Masoyiya yakika wuni?”

“Lafiya lau, kaifa?” Tace dashi kanta asunkuye,

“Alhamdulillah sai dai tunaninki kawai da yahana zuciyata sukuni har sai nazo naganki”

Murmushi tayi tarufe fuskarta,

“Banda zolaya dai”

“A’a ba zolaya bace, ina ni ina zolayar gimbiyar mata kuma sarauniya?”

Babanta ne yafito daga cikin gida nan Aliyu yadurkusa har kasa yagaida shi,

“Yawwa Aliyu dama ina son ganinka, idan kakoma gida dan Allah katuro min walin nan naka inason zamu gana dashi” mahaifin muslima yaceda Aliyu bayan sun gama gaisawa,

“To insha Allah” Aliyu ya amsa,

“To shikenan babu laifi” inji mahaifin muslima nan yawuce,

Tashi Aliyu yayi daga durkuson dayake bayan mahaifin muslima yatafi,

“Sahiba kodai ranar aurenmu za asakane shiyasa baba ke neman Malam?”

“Nima ban saniba” tabashi amsa cikin jin kunya,

“Kice dai kawai bakya son fada minne amma nasan kin san komai”

“Allah ni ba abinda nasani”

“To shikenan nayarda, yanzu bari inje intafi saboda naga har 9 tayi, gaskiya naga saurin tafiyar lokacin nan kodan ina tare dakene?”

Rufe idanuwanta tayi dahaka sukayi sallama yatafi dukkansu badan sun so ba.

Halimatu dakyar take driving saboda dacin da zuciyarta keyi mata, ita duk maganganun Aliyu babu wanda yayi mata ciwo kamar cewa da yayi wai yanada wacce yake so itama take sonshi,

Rai abace tashiga gida sa’ar da tayi umma bata nan tana can part din abba tana gyara masa, kulle kanta tayi acikin daki tazauna ta dukufa tafara kuka domin tunda tazo duniya babu wanda yataba yimata irin wannan cin fuskar da Aliyu yayi mata…..

 

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

 

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

*10*

 

***Kuka tayi iya cin karfinta domin saida idanuwanta suka rine sannan kanta yadauki ciwo tamkar jijiyoyin kanta zasu tsinke dole tasa takwanta bayan taja blanket ta lulluba sakamakon zazzabin da yasoma kawo mata cafka,

Mintuna kadan zazzabin ya rufeta gaba daya, haka tayita zama acikin daki har bacci yadauketa,

Daf da magrib bugun da akewa kofarta yasata tashi duk jikinta babu kwari amma zuwa lokacin bata tare da zazzabin sai dan banzan ciwon kai,

Dakyar ta iya saukowa daga saman gadonta tanufi kofar taje ta budeta, kamar yadda tazata Umma tagani Abba yana tsaye abayanta fuskarsa duk lema alamar alwala yayi zai tafi masallaci,

“Halimatu tun yaushe kika dawone?, ko bakida lafiya?” Abba ya tambayeta cikin kulawa,

Kai ta iya dagawa kawai tajuya takoma kan gado ta kwanta, har ciki suka bita kowa nayi mata sannu, kai kurum take dagawa, zuwa can abba yace bari yaje masallaci yadawo inyaso sai asan abinyi,

Daga ita sai umma ne ke zaune Umman nata faman lallabata akan tatashi tasha koda tea ne amma tagagara tashi, sallama suka jiyo daga cikin falo nan umma tatashi tafita domin dubawa, kanwarta khairiyya tagani wadda itace yar autarsu domin kusan sa’ar halimatu ce yanzu haka tana shekarar karshe a makarantar koyon aikin jinya da ungozoma inda take karantar nursing,

Bedroom din halimatu suka shiga nan umma take sanarwa da khairiyya rashin lafiyar halimatu, dubata khairiyya tayi tarubuta magunguna ciki harda allurai guda biyu,

Daya daga cikin ma’aikatan gidan umma tabawa yaje chemist mafi kusa yasiyo magungunan yakawo,

Saida suka lallabata tasha tea sannan tasha maganin, tana kwanciya bayan anyi mata allurar abba yashigo cikin dakin.

Har gaban gadon da take kwance yakarasa yana yimata sannu sannan yakara da cewa,

“Da har nakira likita yanzu, nabarshi yazo ko nace yafasa?”

“Ai kace yabarshi kawai tunda gashi khairiyya ta dubata” umma tabashi amsa,

“To shikenan Allah yabata lafiya bari nakirashi” yakarasa zancen yana kokarin fita daga cikin dakin,

Lumshe idanuwa halimatu tayi wanda har lokacin jinsu take sunyi mata wani irin nauyi, chingum ta dauko acikin bed side drewar dinta tasa abakinta tana tsotsa, aduk sa’ilin da maganar Aliyu tafado mata tana jin kamar tafasa ihu,

Baccine yasake daukarta wanda bata iya tashiba sai misalin karfe 9 nadare,umma tagani akan gadonta itada khairiyya suna zaune suna yar hira irin ta yan uwa ,

Ganin tatashi yasa khairiyya shiga toilet ta hada mata ruwan wanka mai dan dumi, shiga tayi tai wanka sannan tayi brush domin jin bakinta takeyi yana wani daci daci,

Fitowa tayi daure da towel, kayanta ta bincika ta dauko kayan baccinta maroon, riga da wando masu santsi, duk inda tawuce idanuwan umma nakanta tana yimata sannu,

Saida ta dan ware tana saka baki a hirar dasu umman keyi sannan umma tayi musu saida safe tabar dakin,

“Sadiya meke damunki har haka?”

Muryar khairiyya taji tana tambayarta, juyawa tayi tana fuskantarta,

“Ban ganeba, meya faru?”

“Ya ina tambayarki kina tambayata, just answer me…!”

“Umma khairiyya to aini gaba daya ban gane tambayar taki ba” tafada tamkar zatayi kuka,

Karasa saka kayan baccinta khairiyya tayi sannan tazo tahau gadon ta kwanta,

“To bayan dai chronic ulcer dake damunki gaskiya harda damuwa, akwai abinda yake damunki Sadiya koda bazaki fada min ba”

Idanuwanta ne suka fara kokarin tara kwalla,

“Hakane, akwai abinda yake damuna umma khairiyya….”

Kwashe duk abubuwan da suka faru tsakaninta da Aliyu tayi tafada mata tun ranar farko data fara ganinshi,

Cire tagumin datayi tai bayan tagama sauraron labarin da halimatu tabata,

“To ai wannan ba abun tada hankali bane halimatu, addu’a zakiyi, kiyi addu’a Allah yazaba miki mafi alkhairi, idan tsakaninku akwai alkhairi Allah ya tabbatar, sannan ki sakawa zuciyarki cewa komai daga Allah ne kuma rabonki bazai taba kufce mikiba mutukar Allah ya kadarta naki dinne, sannan ki kara da hakuri insha Allah zakiga komai yazo miki da sauki”

Shawarwari sosai khairiyya tabata wadanda sukasa taji nutsuwa tasaukar mata sannan hankalinta yadan kwanta wanda ita kanta bata san lokacin da taji taware ba, hira suka raba dare suna yi basu sukayi bacci ba sai wurin karfe 2 saura,

Koda gari yawaye rass tatashi sai ko dan ciwon kai da taji gefen kanta nayi mata, wanka tayi tashirya cikin wata doguwar riga ta bakin material, tana zaune akan gadonta tana chaten, khairiyya na gefenta kwance itama rikeda waya tana chaten, dukkaninsu basa uhm bare uhm uhm sai dai wani lokacin kaji daya daga cikinsu yayi dariya,

Ruwan Lipton din dake gefenta acikin cup tadauka ta kurba, bata kai ga ajiyewa ba taji sallamar sabira tana kokarin shigowa cikin dakin,

Murmushine ya bayyana akan fuskarta sai kuma tayi mata hararar wasa,

“Me kikazo yi? Bana so ki koma”

Murmushi sabira itama tayi kafin tace,

“To ai ba danke nazoba, dan dubiya nazo”

“Duk da haka dai bana so”

Dariya sukayi su duka, gefenta sabira tazauna tana yimata sannu, tashi khairiyya tayi suka gaisa da sabira tana tambayarta yame jiki,

Sai da suka gama shan hirarsu sannan sabira ke fadawa halimatu cewar tareda Abdul suke,mayafinta tadauka tafita tana mitar shanyashi awajen da sabira tasa sukayi,

Atsaye jikin motarshi ta sameshi yana aikin na latse latsen waya, da murmushi ya dago ya kalleta,

Gaisawa sukayi yayi mata ya jiki suka fara yar hira kafinsu sabira sufito, kayan dubiyar da yakawo mata na dangin fruits yafitar mata dasu, nan sukayi sallama yashiga motar shida sabira suka tafi wacce sai faman yimusu dariya take, daukar kayan sukayi itada khairiyya suka shiga gida.

Aliyu kuwa cikeda farin ciki yabar gidansu muslima zuciyarsa fes kamar anyi masa albishir da aljanna, shi kansa bai san wanne irin so yake yiwa muslima ba amma yasan hakan baya rasa nasaba da kyawawan halayenta da dabi’unta,

Akafa yataka har zuwa gidansu, koda yaje gida tuni har 9:30 tayi dan haka bai samu damar zuwa wurin Malam lawan ba saboda dare ya fara yi,

Cikin gidan yatura yashiga cikin sa’a yana shiga nepa suka kawo wuta, cikeda farin ciki fuskarsa awashe yakarasa dakin Ummi wadda ya tarar harta kwanta, abakin kofar dakin ya tsaya,

“Ummi, nadawo, har kinyi bacci ne?”

“Aliyu kadawo? Shigo”

Jin tabashi izini yasashi daga labulen dakin yashiga, cikeda doki yazauna yafara labarta mata abinda mahaifin muslima yace,

Nisawa ummin tayi sannan tace,

“Aliyu karfa ko maganar yanke ranar aurenku zaiyi, kaga kai har yanzu gashi baka gama shiri ba”

Murmushi yayi ya sunkuyar da kanshi,

“Ai insha Allah bazata gagara ba ummi, Allah zai bada yanda za ayi…”

“To Allah yasa…”

“Amin” ya amsa, yana shirin tashi yafita yaji tace,

“Nikuwa yarinyar nan halimatu da zaka daure sai ka hadasu su biyu da musliman”

Fasa tashi yayi,

“Ai Ummi ni wannan fa ba budurwa ta bace, banida alaka da ita…”

“To Allah ya zabi abinda yafi alkhairi”

“Amin Ummi” ya amsa mata sannan yatashi yafita,

Daren ranar sun jima suna hira awaya shida musliman shi dan haka yayi bacci cikeda kwanciyar hankali…..

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI..!*🤴🏻

 

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

 

*11*

 

***Washe gari Aliyu bai tashi dawuri ba sakamakon jiya bai yi bacci akan lokaci ba,

Misalin karfe 11 nasafe yafito daga shi sai boxer da singileti, dakin ummi ya leka ya durkusa yagaida ta sannan yafito,tsintsiya yadauka kamar yadda yasaba ya share gidan tass sannan yadora ruwan zafi, yan kwanikan da suke ajiye awurin wanke wanke yazauna yawanke sannan yajuye ruwan wankansa yashiga wanka.

Halimatu tayi amfani da shawarwarin da khairiyya tabata kuma alhamdulillah tana ganin alfanu domin taji sassauci azuciyarta, kwananta biyu agida bata zuwa ko ina, yau tatashi da niyyar zuwa school amma tanason tafara biyawa tagaida mahaifiyar Aliyu domin tana jin dadin yanda tadauketa,

Purple colour din atamfa tasaka mai hoton jaka ajiki tayafa purple din gyale bayan tayi daurin show me ur beauty,nan tayiwa jikinta barin turare as usual,

Ruwan tea kadai ta iya sha tayiwa umma sallama tatafi Umman nata fadan rashin cin abincin da batayi, chingum tadauka tasa abakinta tafita,

Ahankali kamar kazar da kwai ya fashewa aciki ta tura kyauren gidan ta shiga, tana shiga Aliyu yana fitowa daga bandaki daga shi sai boxer babu riga ya ratayo singileti dinshi akan kafadarsa hannunsa rikeda bokiti,

Bakinta dauke da sallama amma bata san lokacin da sallamar ta makale akan lebenta ba sakamakon ganinshi da tayi,

Cak ta tsaya takasa cigaba da tafiyar kamar yadda shidinma yaji wata kunya ta saukar masa,ita dinma kunyarce ta lullubeta dan haka tayi azamar sunkuyar da kanta kasa, daure fuska yayi ya ajiye bucket din yashige dakinsa, sai da taga yashiga daki sannan ta wuce zuwa dakin Ummi,

Isketa tayi tana hada kayanta wadanda za a wanke mata tana waresu daban, cikeda fara’a Ummi ta amsheta suka gaisa, sakamakon ganin da tayiwa Aliyu yasa taji duk zaman ya gundureta dan ko hada ido dashi ji take bazata iyaba dan haka tamike batareda tawani jimaba tayiwa Ummi sallama tace makaranta zataje,

Bisa tsautsayi tana fitowa shima yana fitowa sanye da wandon jeans baki da jar t shirt mai dogon hannu,

Sai da ta sunkuyar da kanta sannan tace,

“Ina kwana?”

Kamar bazai amsaba ya kalleta sannan ya amsa da,

“Lafiya”

Daga nan yajuya yakoma ciki, fita tayi tana murmushi duk dai da bataga fuska awurinsa ba har lokacin,makaranta tawuce can ta iske Sabira amma Abdul bai karaso ba,

Shikuwa Aliyu bayan fitar halimatu dakin ummi yashiga nan ta gabatar masa da ruwan shayin dake cikin tea flask sai ko bread, dama dabarar da yakeyi dafa tea din yake da wuri sai yazuba a flask shikenan dasafe koda bai tashi dawuriba sai tadiba tasha da bread,

Yana karyawa ummin take sake tambayarsa gameda maganar muslima wacce yazo da ita ajiya, murmushi yayi sakamakon Ummi ta soso masa inda yake masa kaikayi domin yana masifar son muslima kamar ransa yarinyar tayine tako ina ga kyan hali ga kyan sura sannan ga addini,

Da hirar muslima abakinsa yagama karyawa yatashi ya gyarawa ummi dakin ya kintsa komai yashareshi tsaf sannan ya kunna turaren wuta na tsinke,

Fitowa wurinta yayi inda take zaune akan kujera yar tsugunno tana kokarin saka Kaset acikin radiyonta,

“Ummi bakya bukatar komai?”

“Babu abinda nake bukata Aliyu, Allah yayi maka albarka ya tsareka, sai ka dawo”

Murmushi yayi domin shi dama wannan addu’ar yakeso wacce tasaba yimasa kullum,

“Amin Ummi, bari inje wurin Malam amma ta can zan wuce gareji”

“To sai kadawo”

Fita yayi yatsari abin hawa yahau domin so yake yaje gidan Malam da wuri sai dai abin haushi koda yaje bai samu Malam ba tafiyar gaggawa takamashi yatafi kauye, kokarin kiransa yayi awaya amma sam taki shiga saboda matsalar network, hakura yayi yahau machine yanufi gareji.

Yana zuwa yanemi wuri yazauna akan benci yafito da wayarsa kirar Nokia C1,muslima yakira sai daf da zata tsinke sannan tadaga, cikin ladabi da girmamawa ta gaidashi nan suka fara yar hira cikin so da kaunar juna, sun jima suna hira Aliyu yana tambayarta abubuwan da tayi bayan tatashi da wanda zatayi anjima sannan sukayi sallama sai lokacin ya iya tashi yaje yafara gudanar da aikinsa bayan yagama jin muryarta.

Halimatu kuwa cikin nishadi yau take gudanar da komai nata har suka gama lectures takoma gida, hatta umma saida ta fahimci yau halimatu na cikin farin ciki domin filet ta cika da fried spaghetti din da akayi tadora chips salad akai tazauna wurin umma wadda ke cikin kitchen din tana yiwa abba tuwon accha, tana cin abincin suna hira da umma har tagama dashi sannan tatashi tawuce dakinta, wanka tayi tasa doguwar riga yar kanti tadora hula akanta tafito tanufi side din abba domin taji alamun dawowarsa.

Daren ranar tana son tayi bacci amma Aliyu yana yawan fado mata dan tanata tuno ganinshi da tayi yafito daga wanka, juyi tayi tagyara kwanciyarta daidai lokacin wayarta tasoma ruri hannu tamika ta daukota daga can karshen gadon, ganin Abdul ne yasata yin murmushi nan ta dauka suka fara hira, babu laifi yadanyi nasarar kawar da tunanin da take tareda shi koda suka gama wayarma babu bata lokaci bacci ya dauketa.

Tun daga lokacin bata sake saka Aliyu a idonta ba kuma bata kara zuwa gidansu ba har sai da akayi kwanaki biyar, ranar lahadi ta shiryawa ummin aliyu dashishi tazuba acikin food flask ta dauka tafita ita dai umma tunda tace mata ga inda zataje bata hanata ba idone nata,

Saida ta fara tsayawa awurin wani mai sayarda goro ta siya mata sannan takarasa gidan, da murmushi akan fuskarta tashiga cikin gidan waya makale a kunnenta suna magana da Sabira,

Aliyu tagani zaune kan dutse daga shi sai wando iya gwiwa da blue din t shirt yana wankewa ummi kayanta,sunkuyar da kanta kasa tayi sannan takarasa shiga batare da ta kalleshi ba, shi dinma tun kallon farko da yayi mata bai sake kallon koda wurin da takeba,

Tana kokarin gaidashi taji karar wayarshi dake cikin aljihunshi dan haka tafasa gaisheshi tazo zata wuce,

“Ranki yadade yakike?” Shine abinda taji yace cikin kulawa domin hatta akan fuskarshi hakan ya bayyana, wani abune ya dirar mata a kahon zuci dan haka cikin sauri ta daga kafarta tabar wurin tawuce dakin Ummi……

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

*12*

 

***Da sallamarta takarasa ummi dake cikin daki tana kallo a yar karamar television dinta ta amsa, shiga ciki tayi nan ummin tasoma murmushi tana fadin,

“Yar nan ina kika shigane inata cikiyarki kwana biyu bakya bullowa…”

Dadi halimatu taji dan ko babu komai tasan ummi ta yaba da ita kuma tanuna kulawarta agareta dan haka sai taga bazata iya cewa haka kawai ta dauke kafarta ba,

Zama tayi itama tana murmushin tace,

“Mama wallahi kwana biyune ban danji dadiba shiyasa amma nasamu sauki”

“Allah sarki to Allah yakara lafiya”

“Amin, gashi nakawo miki, abun marmarine”

Mika mata flask din tayi nan ummi takarba tana murmushi, tana budewa taga dashishine yasha kayan lambu sai faman kamshi yake,

“Lallai kuwa abun marmari, sannu Sadiya, nagode wallahi, ni ina son abincin gargajiya amma shi Aliyu sai ya hanani yi bayan kuma ba iyawa shidin yayiba…”

Murmushi halimatu tayi tana mamakin jin wai Aliyu ne ke girki amma gaskiya indai hakane ya cika yaro mai biyayya, bata kai ga sake maganaba taji ummi na kwalla masa kira,

Har cikin dakin yashiga bayan ya amsa kiran,

“Ina kwana?” Tace dashi kanta akasa, kamar bazai amsaba yace,

Lafiya” daga haka ya maida hankalinsa ga maganar da ummi keyi masa,

“Dama kaga dashishi ne halimatu ta kawo shine nace kazo ka diba kaci ko sai kagama wankin?”

Girgiza kai yayi,

“A’a bazan ci ba nakoshi…”

Fada ummi tahaushi dashi,

“Wanne irin ka koshi? Yaufa ni banga ma kasaka komai acikinka ba tunda katashi…”

“Ummi azumi nake…”

“Wanne irin azumi kuma? Yaufa asabar ko kamanta ne, bafa alhamis bace yau kuma ba litinin ba…”

“Ummi kin manta ne yau sha uku ga wata? Azumin tsakiyar wata nakeyi”

“Ohoo natuna, ashe guda ukun nan da kakeyi duk wata ko? To ai sai in ajiye maka idan kasha ruwa sai kaci tunda abin marmarine…”

Baiyi magana ba yajuya yafita yakoma yaci gaba da wankinsa sai dai yana dan jiyo hirar da ummi keyi itada halimatu dahaka har ya gama wankin ya dauraye yaje igiya yashanya duk halimatu na hangoshi, ji take kamar tatashi taje ta tayashi,

Ruwa yadiba a bucket yadauki omo yashiga ban daki yawanke shi fes sannan yafito ya shiga dakinsa, alqur’ani ya dauka yafara tilawa cikin kira’arsa mai dadi,

Tashi halimatu tayi tayiwa ummi sallama tafito domin tafiya gida, jin karatun Aliyu yasata dan dakatawa tana saurarensa ji take kamar ta kwana ahaka taci gaba da sauraronsa,

Karbar flask din da ummi ke Miko mata tayi tawuce tafita duk da ta kalli dakinshi Allah baisa ta hangoshi ba domin yana can lungu kan sallaya akwance baya kan katifarsa,

Koda takoma gida labarin Aliyu da ummi tashiga baiwa umma daga karshe tace,

“Wallahi umma haka kawai nake jin tausayinsu, basuda karfi amma sunada wadatar zuci sannan suna yin rayuwarsu simple sannan yaron nata mai hakurine kuma mai addini dan yau ma wai azumi yake shine anjima zan shirya masa kayan shan ruwa”

Murmushi umma tayi bayan tagama jin abinda halimatun tafada,

“To kodai shine sirikin nawa?”

Dagudu halimatu ta tashi tana rufe fuska tafada dakinta tabar umma da murmushi akan fuskarta.

Misalin karfe 4 bayan ta idar da salla tashiga kitchen, kunu ta dama masa na shinkafa sannan ta soya masa dankali da plantain sos wacce tayita da kwai da kayan lambu, farfesun kayan ciki tayi wanda yasha kayan kamshi sannan tahada masa fruits salad, lokacin da tagama har 6 tayi, dukkan abubuwan data dafa samun mazubi masu kyau tayi tazuba su aciki tasamu babban kwando tasaka tayiwa umma sallama, ita dai umma ido ne nata,

Sunyi sallama kenan shida muslima wadda ke cewa yabita susha ruwa tare amma yace a’a zaizo dai bayan sallar ishah,yana shiga gida yayi alwala zai tafi masallaci sai gata tashigo, dauke kanshi yayi kamar bai gantaba yafara laluba aljihunsa domin yadauko dabino saboda jin ansoma kiran salla,

Bata damu da rashin kulatan da baiyiba tawuce ciki ta kaiwa ummi kayan tace kayan shan ruwansa ne, godiya sosai ummi tayi da nuna farin cikinta,

Lokacin data fito domin tafiya baya wurin da alama yashiga masallaci,

Bayan ya idar da salla yashiga gida, yana kokarin shiga dakinsa yaji ummi na kiransa,

“Cewa nayi baza ka zo kuma kaci abinci ba? Zaka kara shiga daki ka zauna, sarkin zaman daki, zaman daki awurinka kamar mace”

Murmushi yayi yashiga dakin nata, nan yaga kwanuka reras kusan guda biyar banda wani hadadden jug wanda aka zuba kunu aciki, zama yayi yana kallon kayan cikeda mamaki domin shi bai kulaba dasu lokacin da halimatu tazo kasancewar ba kallonta yatsaya yayiba,

“Ummi wannan fa?”

“Nakane halima takawo maka gashi nan…”

Bata rai yayi yaja tea flask dinsu wanda yazuba ruwan zafi aciki zai hada tea,

“Yanaga baka yaba ba? Wai Aliyu meyasa ka tsani yarinyar nan ne dan Allah? Yarinya mai mutumci da nutsuwa”

“Ummi ni ban tsaneta ba kawai nidai bana son shisshigin da take yimana ne acikin rayuwarmu”

“Ba shisshigi bane Aliyu, mutuncine yakawo take mana haka, ka dauki abincin nan kaci”

Girgiza kai yayi sannan cikin muryar ban hakuri yace,

“Kiyi hakuri ummi amma gaskiya ni bazan iya cin wannan abincin ba…”

Zuba masa idanu ummin tayi amma sanin halinshi yasata rabuwa dashi,

Black tea yahada sannan ya zuba Netscape aciki yafara kurba,

“Gaskiya Aliyu ka sauya hali, ace mutum bazai so mai sonsa ba? Duk wanda baiso mai sonsa ba kuwa to da sannu zai so makiyinsa…”

Dan murmushi yayi sannan ya kurbi shayin,

“Ummi wallahi ba haka bane, ni kawai bana son damuwane kin san yaran masu kudin nan matsala garesu musamman ma idan kai din talaka ne bakada komai”

“A’a Aliyu kowa ai da halinsa, ita wannan yarinyar da ace tana daya daga cikin irin wadanda kake fada ai da bazata soma yimana wannan abun arzikin ba”

“To shikenan ummi tunda kince haka, bari in samo awara acan gefen titi indawo”

Tashi yayi yafita,yana fita tsakar gida yaji karar shigowar text ko ba afada masa ba yasan muslima ce, ai kuwa yana dubawa yaga ita dince ta turo masa,

_Mai sanyina barka da shan ruwa, Allah yabada lada, da fatwa kayi mana addu’a lokacin da zaka sha ruwa._

Murmushi yayi wani dadi ya ziyarci zuciyarsa, kiranta yayi nan tashiga, daf da zata tsinke ta dauka,

“Sanyin idaniyata barkanki da shan ruwa….”

“Nagode Abu Hanifaah”

Murmushi yayi domin yana bala’in son sunan, kuma shida ita ne suka tsara kayansu cewar ‘yarsu ta fari sunanta hanifaah,

“Yanzu me kikeyi? Da kika sha ruwa me da me kika ci? Fada min inji”

Da wannan hirar da sukeyi yakarasa wurin da ake soya awarar, yaro yasamu ya aika domin ya siyo masa saboda mai sayar da awarar mace ce shikuma bai fiya son magana da mata ba……

 

 

_Ni Ummi Shatu ina cikiyar marubuciyar auren jami’a, dan Allah idan sakona ya iskeki ina nemanki urgently_

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(HOME OF EXPERT & PERFECT WRITERS)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

 

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

*13*

 

***Yana zaune kan wani kwalabati can nesa da inda ake soya awarar yana rikeda wayarsa a kunne domin har lokacin basuyi sallama da muslima ba yaron da yabaiwa ya siyo masa awarar yadawo rikeda bakar leda wadda aka sako aciki,

Karbar sakon yayi ya laluba aljihunsa ya ciro naira ishirin yabaiwa yaron sannan ya wuce zuwa wani shago ya siyi bread,

Sai da yaje kofar gidansu sannan sukayi sallama da muslima ya kashe wayarsa ya shiga gida,

Ummi na nan tana zaune inda yabarta da tarin kwanukan dake jere wadanda halimatu ta kawo masa abinci,

Anutse ya shiga cikin dakin ya ajiye kayan dake hannunsa yana yiwa ummi sannu nan ta kalleshi tace,

“Ai Kaine da sannu ba niba, kaida aka kawo maka abin arziki amma ka kasa yabawa…”

Murmushi yayi kafin yace,

“Ummi nifa na yabawa ne banyi ba kawai dai cikina ne bana son in cikashi da yawa”

“Sai kayi kuma”

Bai sake cewa komai ba sai ko murmushin da yakeyi,kwano ya dauko ya juye awarar yasaka musu agaba shida ita suka fara ci suna ci yana sanar da ita sakon gaisuwar da muslima tabashi ya fada mata,

Bayan ya kammala cin abincin ne yafita yayi gaggawar yin wanka sannan yashirya yafita, sallar isha’i yafara zuwa yayi a masallaci sannan ya tafi gidansu muslima,

Kamar koda yaushe yauma sunyi hirarsu cikin so da kaunar juna sai karfe 9 saura sannan yabar wurinta yakoma gida,

Washe gari kuwa da wuwwuri yafita gareji kasancewar sunada ayyuka da yawa shiyasa koda halimatu tazo basu haduba ranar sai ummi kadai tasamu, kwanikan da takawowa Aliyu abinci ta karba tatafi dasu gida tasake shiryo masa wani girkin wanda ya hadar da jalop din kuskus da kayan lambu sai kunun shinkafa da farfesun kaji, tana aikin umma na tsokanarta da cewa,

“Wannan sirikin nawa dai da alama ya samu karbuwa kuma ana ji dashi fiyeda tunanin mai tunani”

Murmushi halimatu tayi tace,

“Umma kenan ni bana wani ji dashi”

“Kina ji dashi mana Sadiya, sai ma abbanki yadawo zan bashi labarin ya fara shirin tarbar suruki”

“Kai umma nidai karki fada masa dan Allah” tafada cikeda shagwaba,

Fita daga cikin kitchen din umma tayi tana dariya,

Agurguje tayi wanka ta saka riga da skirt na shadda ta yafa mayafi tafita tsabar sauri ma ashe key din motar umma ta dauka akan kujera ba nataba, ganin idan tace zata sake komawa batawa kanta lokaci zatayi kawai yasata daukar motar Umma tafita,

Dai dai kofar gidansu Aliyu ta tsaya da motar, Aliyu dake zaune a kofar gidan kan wani dan itace ya zubawa motar ido acikin zuciyarsa yana tunanin waye yazo gidansu? Domin girman motar da tsadarta sun kai mutuka gaya duk da yana ganin manyan motoci amma irin wadannan basu cika yawaba agarin,

Kamar cikin mafarki yaga Sadiya tabude kofa tafito sannan tasake zagayawa daya side din ta dauko katon basket din dake dauke da tsadaddun kwanuka aciki,

Sunkuyar da kansa yayi acikin ransa yana tunanin duk inda Sadiya tafito to daga gidan manyan mutane ne domin sutturarta kadai da yanayin jikinta ya isa ya sanar dakai haka ko ba afada maka ba hakanne yasa yaji zuciyarsa takara nesantashi da ita,

“Ina yini haidar?” Muryarta tadawo dashi daga zancen zucin da yakeyi,

“Lafiya” ya amsa mata kamar koda yaushe domin kullum gaisuwarsu bata wuce haka,

Ciki tawuce wurin ummi shikuma yabi bayanta da mamakin karfin hali irin nata domin idan bai mantaba har kashedin zuwa gidansu yayi mata amma tayi watsi da wannan kashedin taci gaba da zuwa yanda ranta keso,

Bata wani jimaba aciki domin iya gaisawa kawai sukayi da ummi ko zama bata yiba ta ajiye mata kayan tafito, yana zaune inda tabarshi tazo tawuceshi batare da ta kara yimasa magana ba shima haka, yana kallonta ta tashi motar tayi gaba, dan takaici ko gidanma bai sake komawa ba yayi tafiyarsa masallaci,

Kamar jiya yauma babu abinda ya dandana daga abincin da ta kawo, ummi ce dai taci kayanta sauran tabawa almajirai.

Har yagama azumin nan kullum sai halimatu takawo masa kayan shan ruwa amma baya ci saboda shi gaba daya hankalinsa baya kanta yana kan musliman shi wanda yaketa Allah Allah Malam yadawo daga kauye domin asaka musu ranar aure amma Malam shiru bai dawoba saida ya shafe sati biyu babu kadan,

Aranar da yadawo aranar Aliyu yaje ya sanar masa sakon mahaifin muslima Malam baiyi kasa agwiwa ba ya tashi ya tafi bayan anfito daga sallar magrib,

Sallama yasa aka yimasa da Malam yahuza mahaifin muslima yan mintuna kadan yafito yana rikeda tabarma ya shimfida musu suka zauna,

Bayan sun gaisa Malam yahuza yace da malam lawan,

“Malam sai kaji kuma kira ko? Wallahi abune yataso babu wani shiri mahaifiyar yarinyar nan ta matsa akan nanda wata 1 zata aurar da ita ga dan yayarta, kasan sha’anin mata sai hakuri kai abinda kake hange daban sukuma wanda suke hangowa daban, duk da na nuna mata shi yaron wajenka bashida aibu amma takasa fahimta tadage akan bazata bashi yarinyar ba saboda wai ba asan mahaifinsa ba”

Cikeda damuwar da fito baro baro akan fuskarsa Malam lawan yace,

“Hakane,amma ni zan yabi Aliyu ako ina, duk da ba asan mahaifinsa ba to amma yarone mai nutsuwa irin nutsuwar da ba duk yara ke samu ba, wani yaronma da yake gaban mahaifinsa wallahi bai kai Aliyu nutsuwa ba kuma koni nayi sha’awar inama inada yara mata da wallahi na aura masa amma ni duk yarana mata nadade da aurar dasu tun yana karami”

“Malam lawan nima nayi sha’awar hada zuri’a dashi kawai dai Allah ne bai kaddara ba dan haka mutaru muyi hakuri kuma mu rungumi kaddara”

“To Allah yasa hakane yafi alkhairi” inji Malam lawan,

Sallama yayi masa ya tashi yatafi zuciyarsa babu dadi domin ya dauki Aliyu kamar dan da ya haifa, yasan kuma muddin yaji wannan bakin labarin to zai shiga wani hali,

Ransa abace yanufi gidansu Aliyu lokacin ana kokarin shiga salla, masallaci ya shiga nan yawuce Aliyu a sahun gaba kamar yadda yasaba,

Bayan an idar yafito yakamo hannun Aliyu suka kebe duk da yarasa ta hanyar da zai fara fada masa, da dabara da wayo ya sanar dashi bayan ya boye wasu abubuwan nan ya shaida masa cewar dan uwanta ne yaganta yake so sukuma iyaye babu halin su hanashi dan kar zumunci ya baci ace sunki gida sun baiwa bare amma maganar gaskiya sun so subashi muslima kawai Allah ne baiyi ba,

Kamar Malam ya daba masa wuka a kahon zuci haka yaji jin wai za ayi auran muslima kuma wai bada shi ba dawani,

Hankalinsa atashe ransa abace dakyar yake iya sauraron nasihar da Malam keyi masa akan muhimmancin hakuri da kuma karbar kaddara, ahaka yagama jin nasihar malam wadda baya iya fahimtarta ko kadan,

Wani jiri ke daukarsa banda rufewar da idanuwansa sukayi badan yasan gidansu farin saniba to da ba lallai ya iya ganeshi ba a wannan lokaci,

Idanuwansa jajur yatura gidan yashiga batare da yayi sallama ba, zama yayi a kofar dakinsa ya zabga uban tagumi zuciyarsa nayi masa suya kamar zata babbake, gaba daya nutsuwarsa da tunaninsa sun gama gushewa sunbar gangar jikinsa banda daci da makogoransa keyi masa,

Yafi minti 30 zaune wurin yarasa abinda keyi masa dadi, ummi ce tafito daga cikin daki zata zagaya ban daki ganinsa yasata fadin,

“A’a Aliyu yaushe ka shigo? Kai da kace bari kaje ka dawo kaci abincinka kuma shine zaka dawo ka zauna anan?”

Shiru yayi bai iya yin magana ba, hango yanayin fuskarsa ummi tayi tacikin kwan lantarkin dake makale atsakar gidan tunda taga haka tasan ba lafiya ba, matsawa kusa dashi tayi nan taganshi kamar zai fashe da kuka dan tsananin damuwa,

“Aliyu….”

Shiru bai amsaba har saida ta maimaita sau uku sannan yabude baki dakyar,

“Na’am…”

“Meya sameka? Ka fada min”

Kamar wanda ke jira tuni hawaye suka fara fitowa daga idanuwansa wanda ya tabbatar da fitarsu ne kadai zai rage masa kaso 70 na cikin darin radadin da ke damun zuciyarsa,

“Kuka kuma Aliyu? Kuka fa, meya hadaka da kuka?”

Hawaye na bin kutamunsa ya amsa mata da,

“Ummi iyayen muslima bazasu bani itaba wani zasu bawa kuma nasan hakan bai rasa nasaba da halin da na tsinci kainaba na rashin sanin takamaimai wanene mahaifina…”

Zama ummi tayi kusa dashi ita kanta abinda taji daga bakinsa baiyi mata dadiba,

“Aliyu kayi hakuri kaji, kayi hakuri ka dauki kaddara, idan sun hanaka muslima ai ga yan mata nan bila adadin….”

“Ummi amma ai komai yawansu babu kamar muslima, nasan na tabkar babbar asarar da bazan samu madadinta ba…”

Ji tayi yafashe da kuka kamar wani karamin yaro, nan tashiga bashi baki tana lallashinsa amma bai iya dainawa ba, sun fi awa biyu awurin dan sai kusan sha biyun dare sannan ta iya shawo kansa wannan dinma saida yaga ranta yana neman baci.

Abincin da yabari azuwan idan yadawo zai ci tashiga ta dauko masa nan yakarba yashiga cikin dakinsa dashi ya ajiye ya kwanta kan katifa zuciyarsa tana yimasa tukiki abincin da baici ba kenan,

Sam kasa bacci yayi a wannan daren daga karshe ya mike ya fito waje yazari buta ya daura alwala ya koma daki,

Washe gari da safe da wani ciwon kai yatashi dan haka ko fitowa tsakar gida baiyi ba, wayarshi ya dauka ya cire sim din ciki ya ajiyeta can gefe, yana nan kwance ya lulluba yajiyo maganar ummi daga kofar dakin…..

 

*_Ummi Shatu_*
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(HOME OF EXPERT & PERFECT WRITERS)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

 

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

*13*

 

***Yana zaune kan wani kwalabati can nesa da inda ake soya awarar yana rikeda wayarsa a kunne domin har lokacin basuyi sallama da muslima ba yaron da yabaiwa ya siyo masa awarar yadawo rikeda bakar leda wadda aka sako aciki,

Karbar sakon yayi ya laluba aljihunsa ya ciro naira ishirin yabaiwa yaron sannan ya wuce zuwa wani shago ya siyi bread,

Sai da yaje kofar gidansu sannan sukayi sallama da muslima ya kashe wayarsa ya shiga gida,

Ummi na nan tana zaune inda yabarta da tarin kwanukan dake jere wadanda halimatu ta kawo masa abinci,

Anutse ya shiga cikin dakin ya ajiye kayan dake hannunsa yana yiwa ummi sannu nan ta kalleshi tace,

“Ai Kaine da sannu ba niba, kaida aka kawo maka abin arziki amma ka kasa yabawa…”

Murmushi yayi kafin yace,

“Ummi nifa na yabawa ne banyi ba kawai dai cikina ne bana son in cikashi da yawa”

“Sai kayi kuma”

Bai sake cewa komai ba sai ko murmushin da yakeyi,kwano ya dauko ya juye awarar yasaka musu agaba shida ita suka fara ci suna ci yana sanar da ita sakon gaisuwar da muslima tabashi ya fada mata,

Bayan ya kammala cin abincin ne yafita yayi gaggawar yin wanka sannan yashirya yafita, sallar isha’i yafara zuwa yayi a masallaci sannan ya tafi gidansu muslima,

Kamar koda yaushe yauma sunyi hirarsu cikin so da kaunar juna sai karfe 9 saura sannan yabar wurinta yakoma gida,

Washe gari kuwa da wuwwuri yafita gareji kasancewar sunada ayyuka da yawa shiyasa koda halimatu tazo basu haduba ranar sai ummi kadai tasamu, kwanikan da takawowa Aliyu abinci ta karba tatafi dasu gida tasake shiryo masa wani girkin wanda ya hadar da jalop din kuskus da kayan lambu sai kunun shinkafa da farfesun kaji, tana aikin umma na tsokanarta da cewa,

“Wannan sirikin nawa dai da alama ya samu karbuwa kuma ana ji dashi fiyeda tunanin mai tunani”

Murmushi halimatu tayi tace,

“Umma kenan ni bana wani ji dashi”

“Kina ji dashi mana Sadiya, sai ma abbanki yadawo zan bashi labarin ya fara shirin tarbar suruki”

“Kai umma nidai karki fada masa dan Allah” tafada cikeda shagwaba,

Fita daga cikin kitchen din umma tayi tana dariya,

Agurguje tayi wanka ta saka riga da skirt na shadda ta yafa mayafi tafita tsabar sauri ma ashe key din motar umma ta dauka akan kujera ba nataba, ganin idan tace zata sake komawa batawa kanta lokaci zatayi kawai yasata daukar motar Umma tafita,

Dai dai kofar gidansu Aliyu ta tsaya da motar, Aliyu dake zaune a kofar gidan kan wani dan itace ya zubawa motar ido acikin zuciyarsa yana tunanin waye yazo gidansu? Domin girman motar da tsadarta sun kai mutuka gaya duk da yana ganin manyan motoci amma irin wadannan basu cika yawaba agarin,

Kamar cikin mafarki yaga Sadiya tabude kofa tafito sannan tasake zagayawa daya side din ta dauko katon basket din dake dauke da tsadaddun kwanuka aciki,

Sunkuyar da kansa yayi acikin ransa yana tunanin duk inda Sadiya tafito to daga gidan manyan mutane ne domin sutturarta kadai da yanayin jikinta ya isa ya sanar dakai haka ko ba afada maka ba hakanne yasa yaji zuciyarsa takara nesantashi da ita,

“Ina yini haidar?” Muryarta tadawo dashi daga zancen zucin da yakeyi,

“Lafiya” ya amsa mata kamar koda yaushe domin kullum gaisuwarsu bata wuce haka,

Ciki tawuce wurin ummi shikuma yabi bayanta da mamakin karfin hali irin nata domin idan bai mantaba har kashedin zuwa gidansu yayi mata amma tayi watsi da wannan kashedin taci gaba da zuwa yanda ranta keso,

Bata wani jimaba aciki domin iya gaisawa kawai sukayi da ummi ko zama bata yiba ta ajiye mata kayan tafito, yana zaune inda tabarshi tazo tawuceshi batare da ta kara yimasa magana ba shima haka, yana kallonta ta tashi motar tayi gaba, dan takaici ko gidanma bai sake komawa ba yayi tafiyarsa masallaci,

Kamar jiya yauma babu abinda ya dandana daga abincin da ta kawo, ummi ce dai taci kayanta sauran tabawa almajirai.

Har yagama azumin nan kullum sai halimatu takawo masa kayan shan ruwa amma baya ci saboda shi gaba daya hankalinsa baya kanta yana kan musliman shi wanda yaketa Allah Allah Malam yadawo daga kauye domin asaka musu ranar aure amma Malam shiru bai dawoba saida ya shafe sati biyu babu kadan,

Aranar da yadawo aranar Aliyu yaje ya sanar masa sakon mahaifin muslima Malam baiyi kasa agwiwa ba ya tashi ya tafi bayan anfito daga sallar magrib,

Sallama yasa aka yimasa da Malam yahuza mahaifin muslima yan mintuna kadan yafito yana rikeda tabarma ya shimfida musu suka zauna,

Bayan sun gaisa Malam yahuza yace da malam lawan,

“Malam sai kaji kuma kira ko? Wallahi abune yataso babu wani shiri mahaifiyar yarinyar nan ta matsa akan nanda wata 1 zata aurar da ita ga dan yayarta, kasan sha’anin mata sai hakuri kai abinda kake hange daban sukuma wanda suke hangowa daban, duk da na nuna mata shi yaron wajenka bashida aibu amma takasa fahimta tadage akan bazata bashi yarinyar ba saboda wai ba asan mahaifinsa ba”

Cikeda damuwar da fito baro baro akan fuskarsa Malam lawan yace,

“Hakane,amma ni zan yabi Aliyu ako ina, duk da ba asan mahaifinsa ba to amma yarone mai nutsuwa irin nutsuwar da ba duk yara ke samu ba, wani yaronma da yake gaban mahaifinsa wallahi bai kai Aliyu nutsuwa ba kuma koni nayi sha’awar inama inada yara mata da wallahi na aura masa amma ni duk yarana mata nadade da aurar dasu tun yana karami”

“Malam lawan nima nayi sha’awar hada zuri’a dashi kawai dai Allah ne bai kaddara ba dan haka mutaru muyi hakuri kuma mu rungumi kaddara”

“To Allah yasa hakane yafi alkhairi” inji Malam lawan,

Sallama yayi masa ya tashi yatafi zuciyarsa babu dadi domin ya dauki Aliyu kamar dan da ya haifa, yasan kuma muddin yaji wannan bakin labarin to zai shiga wani hali,

Ransa abace yanufi gidansu Aliyu lokacin ana kokarin shiga salla, masallaci ya shiga nan yawuce Aliyu a sahun gaba kamar yadda yasaba,

Bayan an idar yafito yakamo hannun Aliyu suka kebe duk da yarasa ta hanyar da zai fara fada masa, da dabara da wayo ya sanar dashi bayan ya boye wasu abubuwan nan ya shaida masa cewar dan uwanta ne yaganta yake so sukuma iyaye babu halin su hanashi dan kar zumunci ya baci ace sunki gida sun baiwa bare amma maganar gaskiya sun so subashi muslima kawai Allah ne baiyi ba,

Kamar Malam ya daba masa wuka a kahon zuci haka yaji jin wai za ayi auran muslima kuma wai bada shi ba dawani,

Hankalinsa atashe ransa abace dakyar yake iya sauraron nasihar da Malam keyi masa akan muhimmancin hakuri da kuma karbar kaddara, ahaka yagama jin nasihar malam wadda baya iya fahimtarta ko kadan,

Wani jiri ke daukarsa banda rufewar da idanuwansa sukayi badan yasan gidansu farin saniba to da ba lallai ya iya ganeshi ba a wannan lokaci,

Idanuwansa jajur yatura gidan yashiga batare da yayi sallama ba, zama yayi a kofar dakinsa ya zabga uban tagumi zuciyarsa nayi masa suya kamar zata babbake, gaba daya nutsuwarsa da tunaninsa sun gama gushewa sunbar gangar jikinsa banda daci da makogoransa keyi masa,

Yafi minti 30 zaune wurin yarasa abinda keyi masa dadi, ummi ce tafito daga cikin daki zata zagaya ban daki ganinsa yasata fadin,

“A’a Aliyu yaushe ka shigo? Kai da kace bari kaje ka dawo kaci abincinka kuma shine zaka dawo ka zauna anan?”

Shiru yayi bai iya yin magana ba, hango yanayin fuskarsa ummi tayi tacikin kwan lantarkin dake makale atsakar gidan tunda taga haka tasan ba lafiya ba, matsawa kusa dashi tayi nan taganshi kamar zai fashe da kuka dan tsananin damuwa,

“Aliyu….”

Shiru bai amsaba har saida ta maimaita sau uku sannan yabude baki dakyar,

“Na’am…”

“Meya sameka? Ka fada min”

Kamar wanda ke jira tuni hawaye suka fara fitowa daga idanuwansa wanda ya tabbatar da fitarsu ne kadai zai rage masa kaso 70 na cikin darin radadin da ke damun zuciyarsa,

“Kuka kuma Aliyu? Kuka fa, meya hadaka da kuka?”

Hawaye na bin kutamunsa ya amsa mata da,

“Ummi iyayen muslima bazasu bani itaba wani zasu bawa kuma nasan hakan bai rasa nasaba da halin da na tsinci kainaba na rashin sanin takamaimai wanene mahaifina…”

Zama ummi tayi kusa dashi ita kanta abinda taji daga bakinsa baiyi mata dadiba,

“Aliyu kayi hakuri kaji, kayi hakuri ka dauki kaddara, idan sun hanaka muslima ai ga yan mata nan bila adadin….”

“Ummi amma ai komai yawansu babu kamar muslima, nasan na tabkar babbar asarar da bazan samu madadinta ba…”

Ji tayi yafashe da kuka kamar wani karamin yaro, nan tashiga bashi baki tana lallashinsa amma bai iya dainawa ba, sun fi awa biyu awurin dan sai kusan sha biyun dare sannan ta iya shawo kansa wannan dinma saida yaga ranta yana neman baci.

Abincin da yabari azuwan idan yadawo zai ci tashiga ta dauko masa nan yakarba yashiga cikin dakinsa dashi ya ajiye ya kwanta kan katifa zuciyarsa tana yimasa tukiki abincin da baici ba kenan,

Sam kasa bacci yayi a wannan daren daga karshe ya mike ya fito waje yazari buta ya daura alwala ya koma daki,

Washe gari da safe da wani ciwon kai yatashi dan haka ko fitowa tsakar gida baiyi ba, wayarshi ya dauka ya cire sim din ciki ya ajiyeta can gefe, yana nan kwance ya lulluba yajiyo maganar ummi daga kofar dakin…..

 

*_Ummi Shatu_*
© *HASKE WRITERS ASSO*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

 

*14*

 

***D’aga labulen dakin ummi tayi ta leka,

“Aliyu kaduba agogo kuwa? Karfe 9 fa yanzu gashi naga ko fitowa bakayi ba”

Sake tukunkunewa yayi kafin ya amsa mata,

“Ummi bana jin dadine, ciwon kai ke damuna”

Jin abinda yace yasa ummi karasawa cikin dakin,

“Haba Aliyu, yanzu ashe bazaka karbi kaddara ba? Shine saida kasawa ranka damuwar da har gangar jikinka ma sai ta san kana cikin damuwa? Haba Aliyu, dan Allah kayi hakuri ka manta da wannan yarinyar”

Idanuwanshi ya bude wadanda suke jajur ya kalleta tareda gyada mata kai amma bai iya yin magana ba,

“Bari naje na kawo maka abin karin kumallo ka karya, ai baza kayita zama da yunwa ba”

Yana jinta amma bai iya tankawa ba har tafice daga dakin taje ta kawo masa flask din ruwa zafi da bread,

“Tashi ka karya tukunna kafin insamo maka maganin”

“Ba yanzuba ummi, sai zuwa anjima yanzu kaina ciwo yake sosai”

“To sannu, Allah ya sawwake”

Samun wuri itama tayi ta zauna acikin dakin sam tarasa sukuni acikin zuciyarta, har karfe 12 tayi Aliyu bai tashi ya karya ba kuma daidai lokacin ne zazzabi ya rufeshi,

Tashi ummi tayi domin taje dakinta ta dauko mayafinta tafita taje ta siyo masa magani,

Tana fitowa daga dakinta taji sallamar halimatu wacce tabiyo ta gidan bayan ta dawo daga school,

“A’a halima, sannu da zuwa”

“Yawwa mama, sannu da gida”

Tsayawa ummi tayi har halimatu ta karaso,

“Nima wai can nake son zuwa insiyowa Aliyu magani kin ganshi can kwance bashida lafiya”

Cikeda damuwa halimatu ta kalli dakin nashi nan ta hangoshi kwance lullube cikin bargo,

“Ayya meke damunsa?”

“Yace kansa ne yake ciwo sannan yanzu kuma yace zazzabi yakeji”

“Allah sarki, Allah yabashi lafiya, bari naje na siyo masa mama ke ba sai kinjeba ki zauna awurinsa”

Bata jira amsar da ummi zata bataba tajuya tafita, khairiyya ta kira awaya ta tambayeta wanne magani yadace ta karbowa Aliyu nan khairiyya ta turo mata sunayensu ta text massage,

Wani chemist taje ta siyo masa maganin sannan ta hado masa da drinks,

Lokacin da ta koma gidan ummi na dakinshi zaune shi kuma yana bacci har lokacin a lullube yake da bargo, zama tayi akusa da ummin tana kallonsa manyan idanuwansa arufe,

Ahankali ta rinka bin dakin nasa da kallo wanda babu tarin shirgi aciki domin daga katifarsa sai akwatin kayansa shikenan sai littattafai fal wadanda ke jejjere can gefe daya,

Jin motsinsa yasata saurin maida hankalinta wurin nan taga ya rirruke kansa da duk hannuwansa guda biyu yana jujjuya kansa alamun ciwon da kan nasa keyi masa yakai intiha wurin azabtar dashi, idanuwanshi arufe yafara maganganu,

“Wayyo kaina, ummi kaina, kaina ummi….”

Kafin tayi wani yunkuri tuni har ummi ta runtuma taje wurinshi tafara kokarin rirrikeshi, azabure itama ta mike taje wurin,

Wani yunkuri yayi cikin sauri Ummi ta rikeshi cikin sauri itama halima ta taya ummi rikeshi nan taji jikinsa da zafi sosai alamun zazzabi,

Salatinshi sukaji daga nan kuma yaci gaba da kiran ummi yana cewa kansa, idon ummi cike fal da kwalla take yimasa sannu,

Sunfi mintuna ishirin suna rike dashi amma abin kamar karuwa yake,addu’a halima tafara tofa masa agoshinsa ummi kuma na faman yimasa sannu ahankali ahankali sukaga alamun ciwon yafara lafa masa domin sunga yayi shiru kuma yadaina jujjuya kan nasa,

Zubawa fuskarsa ido tayi tana kallonsa tana rike da hannunsa daya yayinda kansa ke kan cinyar ummi itama tana rike da dayan hannunshi,

Girgiza kai ummi tayi cikin damuwa tace,

“Shiyasa yaron nan nace kar ya sakawa ransa damuwa domin idan kansa yafara ciwo yana azabtuwa…”

“Mama dama yana yin ciwon kan ne?”

Halimatu ta tambaya cikin jimami,

“Gaskiya tun yana yaro rabonsa da ciwon kan nan nida har ina murna ina tunanin yarabu dashi ashe yana nan” Takarasa maganar tana share kwalla,

“Allah zai bashi lafiya mama, kiyi hakuri”

Shiru dukkaninsu sukayi suna kallon ikon Allah, yajima ahaka kafin yaci gaba da juye juyen halimatu batayi kasa agwiwa ba taci gaba da yimasa addu’a har ciwon yasake lafa masa,

Bacci ne ya daukeshi nan hankalin ummi ya dan kwanta ganin yasamu sauki,

Bai jima da yin baccin ba halimatu tatashi tafita, abinci taje ta siyo musu awani restaurant tadawo har lokacin baccinshi yake akan cinyar ummi, zama tayi agefensa taga ya hada zufa kamar an kwara masa ruwa, tashi tayi taje dakin ummi ta dauko mafici tadawo,

“Mama naga kamar zazzabin ya sauka daga jikinsa ko?” Takarasa maganar tana zama agefensa,

“Ehh da alama kam tunda gashi nan yanata gumi” Ummi ta amsa mata,

Yaye masa bargon tayi tasoma yimasa fifita, har aka kira sallar azahar suna tare dashi sai wurin karfe 2:30 sannan yafarka daga baccin da yake,

Ahankali yasoma bude idanuwansa bayan yayi salati,da halimatu yafara hada ido wacce ke zaune dirshan akusa dashi tana yimasa fifita, ummi yajuya ya kalla ahankali ya yunkura zai tashi ummi tayi saurin taimaka masa,

“Sannu Aliyu….” Inji ummi,

“Ummi kaina ciwo yake yimin kamar ana bubbuga min guduma aciki”

“Sannu, zai daina” Ummi tasake bashi amsa,

“Sannu Haidar… Kadaure kaci abinci kasha magani zakaji sauki…”

“Yawwa miko masa ko zai iya ci” Inji ummi, cikin sauri halimatu ta dauko daya daga cikin take away din da tashigo dashi, tuwon shinkafa ne miyar ogu, bude masa tayi ta mika masa gabanshi,

“Daure kaci Aliyu, ci maza sai kasha magani”

Jin abinda Ummi tace yasashi kallon abincin amma bashida zabin da yawuce yaci din kamar yadda ummi tace domin zazzabar da kansa ke yimasa zazzabar ta isa,

Mika masa cokalin dake kan abincin halimatu tayi nan yakarba yasoma ci kamar yana cin magani, baifi cokali biyar yayiba yature abincin, magungunan da ta siyo masa ta miko masa babu bata lokaci yakarba yasha ya koma ya kwanta ya lumshe jajayen idanuwanshi ahaka bacci ya daukeshi,

Sai lokacin ummi tace suje suyi salla, salla sukayi suka sake dawowa dakin suka zauna ita dai halimatu sai kallonshi take yi yana barci, bashi yatashi ba sai bayan la’asar, tashi yayi ya fita tsakar gida suna faman yimasa sannu, alwala yayi yashigo dakin yana rike da kansa ahaka yayi salla, bayan ya idar ummi tace yadaure yakara cin abincin yaje yayi wanka,

Kamar zaiyi me haka yaja abincin yadan ci bawani mai yawaba,

“Bari inhada maka ruwan kayi wankan ko?” Ummi tafada tana kokarin tashi da flask din ruwan zafin da takawo masa dasafe kuma bai shaba, cikin sauri halima takarbi flask din tana cewa,

“Mama kawo inzuba masa, barshi kizauna”

Dasauri ta fita taje tazuba masa a bucket ta nufi inda taga suna shiga a matsayin toilet, duk da ban dakin bawani mai kyau bane sosai amma awanke yake tsaf babu datti sannan lailaye yakeda siminti,

Fitowa tayi lokacin shima yafito ummi tana bayansa, bashi hanya halima tayi yawuce yanufi bayin,

Suna dakin ummi yafito daga wankan yashiga dakinsa ya kimtsa har lokacin kansa bai lafaba daga azababben ciwon da yake masa kusan acikin karfin hali yake gudanar da komai,

Ganin kamar jikin nasa da sauki yasa halima tayiwa ummi sallama zata tafi gida domin lokacin har magrib tayi, dakin nashi ta leka taganshi kwance idanuwanshi rufe har lokacin yana rikeda kanshi, batayi magana ba tajuya tafice daga gidan idanuwanta sun ciko da kwalla…..

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI..*🤴🏻

 

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

*15*

 

***Zuciyarta cikeda damuwa mai tarin yawa ta shiga cikin gidansu,

Umma na kokarin shiga bedroom dinta taji shigowarta dan haka ta saurara tafasa shiga ta tsaya tana jiran karasowarta,

Fuskarta da alamun gajiya gamida damuwa ta zauna tana kallon umma,

“Yau lectures din naku amma sun yi zafi, wuni guda curr tun safe..”

Saida ta dan nisa sannan ta amsawa umma,

“Umma ai tun 12 da wani abu muka gama lectures, gidansu wannan Aliyun naje kuma sai nasamu bashida lafiya shine na tsaya na taimakawa mahaifiyarsa”

Dawowa tsakiyar falon umma tayi ta zauna tana fuskantarta,

“Allah sarki, Allah yabashi lafiya, amma dai sunje asibiti ko?”

“Ai umma magani kawai na samo masa amma gobe idan baiji sauki ba sai muje in rakasu asibitin”

“Allah yabashi lafiya to, ni danaga baki dawoba ai na dauka kina makarantar”

“Wallahi ina can gidansu, naso in kiraki in fada miki to yanayin ciwon nashi ne sam babu damar ma da za ayi haka”

“Allah ya sawwake yabashi lafiya”

“Amin umma, Abba na yadawo?”

Mikewa umma tayi tana amsa mata da,

“Shima tunda yadawo yayi lunch da rana yasake ficewa shiru kikeji har yanzu”

“To Allah yadawo dashi lafiya”

“Amin” Umman ta amsa tana kokarin shiga bedroom dinta domin yin sallar magrib, tashi itama tayi tashiga nata bedroom din, wanka tafara yi tafito sannan tayi salla, ta dade tana yiwa Aliyu addu’ar samun lafiya sannan tamike tana sanye da hijabin da tayi salla tafita,

Kitchen tashiga ta dafawa Abbanta shayi kamar yadda ta saba sannan itama ta zuba a cup ta nufi falo wurin umma wacce ke zaune taci uban kwalliya ta kunna turaren wuta a falon takamo tashar zee world tana kallo,

“Yanzu ke maimakon ki debo abincin kirki kici shine zaki wani dauko ruwan zafi?”

Zama tayi tana murmushi saboda jin abinda umma tace,

“Umma da bari nayi wai in dan fara dumama cikina tukunna dan wallahi rabona da abinci tun safe”

“Lallai, ana ta jinyar miji ai baza aci abinci ba” Umma tafada tareda maida hankalinta ga kan tv,

Shiru halimatu tayi tana murmushi, da kyar tasamu ta dan tsakuri faten dankalin da umma tayiwa abba taci,

Daren ranar kuwa kasa bacci tayi sai faman juye juye take ta faman yi, Alla Alla take gari yawaye dan taje taga yanda Aliyu ya kwana,

Karfe 8 da yan mintuna tagama dafa tuwon semovita dinta miyar zogale sai farfesun zabbi wanda duk shawarar umma ce,

Ko wanka batayi ba ta dauko babban hijabi ta kwashi kayan tafita,

Lokacin da tashiga gidan ummi tafito daga bayi tana rikeda buta, ganin halimatu yasata fadada fara’arta,

“Halimatu kece kike tafe?”

“Ehh nice mama”

“To sannu da zuwa”

Dakin Aliyu suka shiga wanda ke kwance yana bacci amma kallo daya zakayi masa kasan yana shan wahala mutuka domin har fuskarsa ta fada,

“Mama ya ya me jikin?”

“To da sauki dai za ace Sadiya amma kin ganshi nan jiya sam bamu runtsa ba har jikin asuba, shine sai yanzu yasamu yakeyi…”

Cikeda tausayawa halimatu tace,

“To mama ko asibiti zamuje?”

“A’a Sadiya, dama lokacin da yana tsaka da ciwon kan lokacin da yana yaro Malam lawan ne ya taba samo masa wani magani kuma tunda yasha shikenan bai kara yin ciwon kanba sai wannan, to yanzu yau da sassafe na bugawa Malam din waya na fada masa yanzu tunda safen ya tafi kauyen d’an danshi inda yataba karbo masa maganin zai sake karbo masa”

“To Allah yasa adace”

“Amin, amin Sadiya,ya mutanen gidan naku?”

“Lafiya lau suke”

“Madalla”

“Ga abinci mama”

“Sadiya abincin nan kuwa zai samu shiga? Wallahi jinyar yaron nan ta tayar min da hankali”

“Ai zai samu lafiya insha Allah, kidaure kici abincin dai mama”

Daurewar dai ummi tayi kamar yadda halima tace amma bawai dan tana jin son cin abincin ba nan tajawo kwandon abincin da haliman takawo caraf halima tayi tarike tana cewa,

“A’a mama kawo inzuba miki”

Murmushi ummi tayi ta sakar mata nan tazuba mata tuwon guda biyu tana kokarin saka na ukun ummi tace tabarshi haka, miya tasaka mata ta saka mata farfesu agefe,

Taya ummi hira tarinka yi har tasamu ta danci abincin da dan yawa,

Ganin Aliyu yanata bacci har kusan 12 yasata cewa ummi bari taje gida tadawo domin batayi wanka ba hakama bataci komai ba duk da abincin bawai ya wani dameta bane,

Tana zuwa motarta taga miss called samada guda goma, kamar yadda jikinta yabata Abdul ne sai ko Sabira da itama takirata samada sau biyu,

Sabiran tafara kira tana murmushi,

“Haly ya akayi ne? Ina kika shiga?”

Murmushi tayi bayan ta tadata motar tasoma hawa titi,

“Sabira na danje wani wurine”

“Yau bazaki shigo lectures ba kenan?”

“Gasiya bazan shigo ba saboda inada patient”

“Waye baida lafiya?”

Sabira ta tambaya arude domin duk zatonta umma ce ko abba,

“Rabin jikina ne baida lafiya”

Murmushi sabiran tayi tace,

“To ai shi gashi yashigo school, yanzun nan fa Abdul din yatashi daga nan”

Dariya halimatu tayi,

“Ke nifa ba Abdul nake nufiba, kibari dai yanzu ina driving ne i will call u later…”

Katse wayar tayi tana murmushi ta kira Abdul,

Lokacin da ta koma gida agurguje tayi wanka tasha tea sannan ta danci abinci, wata pink din atamfa tasaka mai zanen tabarma ajiki ta danyi make up kadan, jakarta ta dauka da pink din mayafi tashiga dakin umma, sallama sukayi tafita,

Gabanta har wani faduwa yake domin bata san ayanda zataje ta riski Aliyu ba,

Da faduwar gaba tashiga cikin gidan hango ummi tayi cikin dakinta tana salla dan haka ta leka dakin Aliyu, kamar dama jiranta yake,farkawa yayi daga nannauyan baccin da yake yi dan tsananin azabar ciwon da kanshi ke yimasa, runtse idanuwansa yayi yarike kan yana jan numfashi,

Sai salati yake yana juyi, cikin sauri ta durkusa agabansa tasoma yimasa sannu, kila a tunaninsa umminsa ce nan ya rirriketa da duk iya karfinsa yana cewa,

“Ummi kaina… Kiyi min addu’a ummi, wash kaina ummi”

Rudewa ita tayima takasa yin addu’ar saboda yanda taga yana yi lallai indai hakane dole hankalin ummi yakasa kwanciya kwata kwata,

Hannunta taji yadora akan goshinsa wanda yake da zafi kamar ana tafarfasashi,

“Sannu Haidar…. Yi hakuri zai daina ciwon, zaka samu lafiya”

Sake rirriketa yayi yai wani yunkuri, nan ummi tashigo cikin dakin bayan ta idar da sallar da takeyi, ganin yanayin da Aliyu ke ciki yasake tada mata hankali, daga kai halimatu tayi domin kwantarwa da ummi hankali,

“Mama lokacin da nashigo ma fa bacci yakeyi yanzune yatashi….”

Shiru tayi sakamakon jin ya dauke kansa daga kan pillow ya mayar saman cinyoyinta, zama ummi tayi hankalinta duk atashe tasoma shafa goshinsa,

Ita kam halimatu duk kunya ta dabaibayeta saboda yanda Aliyu yake saman cinyarta duk da tasan da ace lafiya kalau yake hakan bazata taba faruwa ba,

Addu’a suka cigaba dayi masa amma abin sai godiyar ubangiji domin sai la’asar sakaliya sannan yasamu bacci nan ummi ta gyara pillow tace,

“Sadiya dorashi anan kihuta kema”

Cikeda kunya halimatu ta taimaka mata suka kwantar dashi suka dora kansa saman pillow,

Jugum jugum sukayi kowa yakasa magana ita halimatu aranta tunani take da ace Allah bai kawota ba da Ummi ita kadai zata yi ta fama da jidalinshi?

Karfe 6 saura Malam lawan yayi sallama acikin gidan nan ummi tafita tashigo dashi dakin Aliyun,

Kullin magani yafito dashi daga cikin aljihunsa ya mikawa Ummi yana cewa asamu ajikashi yanzu abashi yasha ashafa masa wani agoshinsa,

Halimatu ce takarba tajika a cup din Malam yana tsaye yana kallo, shine ya karba ya tada Aliyu yabashi yasha yakuma shafe masa goshinsa dashi yakoma ya kwanta,

Abinci ummi ta gabatarwa da Malam amma fur yaki ci yace gida zai karasa dan haka yayi musu sallama yatafi ummi tanata yimasa godiya,

Tunda Aliyu yasha maganin shikenan bai sake koda tari ba sai bacci da yaketa yi,har akayi magrib bai tashiba dan haka halimatu tayiwa ummi sallama itama tatafi,

Kamar jiya yauma baccinta ragagge ne domin bata san halinda yake cikiba, sai wurin 3 tasamu bacci, asubar fari kuma umma tashigo ta tasheta,tashi tayi tai salla sannan tashiga kitchen,

Baba Tabawa ta iske mai girkinsu acikin kitchen din nan itama takama nata aikin na shiryawa Aliyu girki, doya ta dafa masa tayi miyar alayyahu da kifi sannan ta dama kunu,

Wanka tashiga tayi tashirya tsaf cikin wani purple din material dinkin duguwar riga, purple din agogo tadaura sannan tafesa turaren smart,classic lady, da kuma oud, gyalenta tadauka shima purple tasa flat din takalmi tafita,

Cikeda jimami umma ke kallonta bayan sun gaisa tace,

“Kodai infadawa abbanki ya taimaka musu ne suje asibiti Sadiya?”

“Ehh to umma amma dai kibari inje indawo naga yadda jikin nasa yake domin jiya ankarbo masa magani awani kauye wanda aka taba karbo masa lokacin da yana yaro”

“To Allah yabashi lafiya”

“Amin umma,bari naje”

“To sai kin dawo, ki gaidasu dan Allah”

“Zasuji umma tah”

Daga haka tafice tabar umman tana murmushi, agurguje tashiga part din Abba tasameshi acikin bedroom dinsa yana sanye da medical glass gabansa fal takardu yanata saka hannu, durkusawa tayi ta gaidashi sannan tafita,

Basket din abincin ta dauka tasa gaban mota sannan tashiga tatafi, tanata tunanin ko ya su Aliyu suka kwana jiya? Ko jiyanma basuyi baccin ba, ko ya jikin yanzu? Da haka tashiga unguwar tana zuwa layin ta hangoshi a kofar gida shida abokan aikinsa su dan larai sunzo dubashi suna tsattsaye,

Murmushi tayi aranta tace,

“Ikon Allah ashe yasamu sauki ma”

Saida ta dan zartasu sannan ta tsaya ta kashe motar tafito tana satar kallonsa, yana sanye da t shirt da jeans ras dashi kamar bashine jiya yake kwance hajaran majaran ba,

Zagayawa tayi ta dauko kwandon abincin tanufi gidan bayan tayi fuska duk da tasan ba lallai ne su dan larai su ganeta ba, ta gefensu ta bi ta shiga cikin gidan bayan ta saci kallon Aliyu cikin rashin sa’a shima yadago ya kalleta suka hada idanu…..

 

_#Anty maijidda,maryam qaumi & miss Xoxo nima ina yinku kamar yadda kuke yin Haly-Al_#_

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI….!*🤴🏻

 

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

 

*16*

 

***Bakinta dauke da sallama tashiga cikin gidan, ummi na zaune a kofar dakinta tana matse lemon tsami acikin cup, jin sallamar halimatu yasata daga kanta ta amsa tana dauke da murmushi,

Itama halimatun fuskarta dauke da fara’a ta karasa ta durkusa ta gaidata tareda jan yar kujerar tsugunnon dake ajiye gefen ummi wadda da alama wurin zaman Aliyu ne kafin yafita,

“Mama ya mai jikin?”

“Jiki ai yayi sauki Sadiya, yanzu dai nafada masa ai sai ya yi hankali ya cireta aranshi tun bai kamu da ciwon zuciya ba…”

“Mama wacece?”

“Wata yarinya ce mana da yabi ya kwallafawa ransa soyayyarta gashi daga karshe dai anhanashi yarinyar anbawa wani shine fa duk dalilinsa na wannan jinyar…”

Dai dai lokacin Aliyu ya shigo,sunkuyar da kai halimatu tayi ahankali ta cewa ummi,

“Allah yasa hakane mafi alkhairi”

“Amin Sadiya, shima dai kuma harda laifinsa domin ya dauki soyayyar duniya ya dorawa wannan yarinya”

Murmushi kawai halimatu tayi batare da tace komai ba tasake yin kasa da kanta,

“Uhm namanta Sadiya ban tambayeki ba ya gajiyarki ta jiya? Allah ya saka miki da alkhairi yabar zumunci”

“Amin mama”

Dago da kanta tayi taga Aliyu tsaye kofar dakinsa yana kokarin hada wayarsa wacce ya wargajeta lokacin da yadawo daga wurin muslima,

“Ina kwana Aliyu?”

Fuskarshi babu yabo babu fallasa ya amsa mata,

“Lafiya lau”

“Yajikin ka?”

“Alhamdulillah”

“Allah yakara sauki”

“Amin”

Daga nan ta maida hankalinta ga ummi wacce ke dab da karasa matsar lemon tsamin da takeyi,

“Yaron nan narasa me yakeji a lemon tsamin nan….”

Jin abinda ummi tace yasashi yin magana,

“Ummi da dadi fa, ki gwada sha kiji”

“A’a kai dai da kasaba kasha abinka”

“Mama kuma haka yake sha babu komai aciki”

“Yana saka sugar wata rana kuma harda kayan kamshi”

Murmushi halimatu tayi batace komai ba,

Zama yayi akan kofar dakinshi da cumb a hannunshi bayan ya gama saita wayar yasoma taje sumar kanshi zuwa gemunsa, yana jin ummi da halimatu suna yar hira jifa jifa,

Tashi ummi tayi ta kai masa lemon tsamin sannan takoma wurin Sadiya,

“Ummi ga abincin fa” Halimatu tafada tana mikawa ummi kwandon da abincin ke ciki,

“Kedai bakya gajiya Sadiya, kiyita dawainiya babu hutu, Allah yasaka da alkhairi yakara arziki, nagode nagode, nagode madalla”

Murmushi kurum halimatu tayi batace komai ba,

“Aliyu inzuba maka abincin yanzu?” Ummi ta tambayeshi daga nan inda take zaune,

“A’a ummi sai dai ko anjima” Ya amsa mata shima daga can wurinda yake zaunen,

Shiru dukkansu sukayi dan haka halimatu ta mike rataye da side bag dinta ta kalli ummi,

“Mama bari naje na tafi…”

“Ah zaki tafi halima, to kigaida gida kinji, kigaida maman taki, nagode madalla”

“Babu komai mama, zataji”

Kasa tayi da kanta ta nufi kofa, lokacin da tazo daidai inda Aliyu ke zaune taji yace,

“Ki gaida gida”

“Gida zaiji”

Daga haka tawuce tafita, makaranta tawuce duk mamakin Aliyu yabi ya rufeta tana ta murmushi aranta tana cewa to shi meyasa ya maidar da shan lemon tsami al’adarsa? Wannan tunanin tarinka yi da haka har ta shiga makarantar.

K’arfe 3 tagama lectures dinta ta koma gida, tunda taci abinci tayi sallar la’asar tahau saman gado ta kwanta domin jikinta ciwo yake sakamakon rashin isasshen hutun da bata samuba kwana biyu alhali ita kuma bata sababa domin babu abinda takeyi daga makaranta sai bacci,

Tunanin Aliyu ne ya bijirowa zuciyarta saboda labarin da ummi tabata na cewar an hanashi budurwar da yake so an bawa wani shiyasa yaketa wannan ciwon, to ko wacece budurwar tashi? Ko kuma yarinyar nan da take yawan ganinsu tare ne? Bata da amsoshin wadannan tambayoyin shiyasa ma ta hakura ta jawo wayarta,

Text massage ta soma rubuta masa duk da cewar da kyar ta tattaro kalmomin da tayi amfani dasu domin sanyaya masa zuciya nan ta tura masa gabanta sai dar dar yake yi ga mamakinta sai taga text din yatafi wanda sam bata tsammaci haka ba duba da irin lokutan da ta shafe tana kokarin kiran layin amma baya shiga.

Fitowarshi kenan daga wanka yazauna agefen katifa ya dauki mai zai shafa, wayarsa dake gefensa yaji tafara kara alamun shigowar text massage baiyi zaton cewar text din wani mai amfani bane domin yasan ba kowane yasan layin ba saboda ya jima baya amfani dashi yanzune dai ya dorashi akan wayar yacire wancan wanda aka sanshi dashi ya ajiye,

Duk atunaninshi mtn ne ko wani shirme dan haka baiko bi ta kan wayar ba ya shiryawarshi yashafa turare ya sa kaya t shirt da boxer yasaka ya dan kishingida saman katifarshi ya dora kansa bisa pillow, wani littafi dake can gefe ya janyo yasoma dubawa,

Yana nan kwance yaji sallamar Malam lawan daga kofar gida ko ba afada masa ba yasan dubashi yazo yi dan haka yayi haramar tashi cikin sauri yafita wurin Malam din wanda ke tsaye bakin kofa ta ciki,

Tsugunnawa yayi yagaida Malam din shikuma yafara tambayarsa ya jikinshi, sun dan jima tare suna tattaunawa daga karshe malam din yatafi baiko shiga ciki sun gaisa da ummi ba,

Cikin dakinsa yakoma bayan ya sanarwa da ummi zuwan Malam lawan, yana zama kan katifa yadauki wayarsa domin duba lokaci nan yaga text din da aka turo masa dazu budewa yayi ga mamakinsa sai yaga ashe ba mtn bane ko wani mai kamada haka number ce ta turo masa nan yasoma karantawa,

_Haidar yajikin naka? Allah yakara baka lafiya,sannan dan Allah kayi kokari ka cire damuwa aranka saboda kaga rashin lafiyarka tana tadawa mama hankali duk da nasan rabuwa da masoyi akwai zafi to amma hakuri zaka bawa zuciyarka sai Allah ya musanya maka da wadda tafita alkhairi._

_ka huta lafiya_

Tunda yagama karanta sakon tunaninshi yabashi cewar Sadiya ce domin yasan ummi ta sanar da ita makasudin rashin lafiyarsa,

Shiru yayi yanata faman bin sakon da ido sai zuwa can ya hakura yakoma yaci gaba da duba littafinshi.

Tunda haka tafaru Sadiya bata samu damar komawa gidan ba saboda makaranta duk da cewar kusan kullum tana tura masa text massage tana tambayarshi ya jiki,

Bayan kwana biyu ta taso daga makaranta ta biya ta gidan, ummi tana dakinta tashiga suka gaisa,

“Halimatu kwana biyu ai da naji shiru nace ko tafiya kikayi ne”

“Wallahi mama ina nan makaranta ce tafara zafi shiyasa bana samun lokaci”

“To Allah yabada sa’a ya taimaka”

“Amin mama, ya me jikin?”

“Jikin nashi ai yayi sauki duk da cewar har yanzu bai fara fitaba dai, yaune ma da yayi niyyar fita to kuma wai yaji jikinsa babu dadi yanzu hakama yana daki”

“Allah yabashi lafiya bari inga”

Tashi tayi ta leka dakin nasa, yana kwance yabawa kofar dakin baya kafafuwansa akan pillow kamar yadda kanshi ma yake kan wani pillown, gefen katifar kuma wani littafi ne a ajiye alamun karantashi yakeyi ya ajiye domin ga alama nan ya ajiyeshi akan shafin da yake karantawar,

Har zata juya sai sunan littafin yaja hankalinta sadaf sadaf ta karasa ta daukoshi,

*RABE RABEN MATA* shine sunan da ke jikin littafin da manyan baki, shafin da yake karantawa ta duba, rabe raben budurci taga anrubuta a heading din nan tafara bi tana karantawa tun daga na daya har zuwa na uku tazo daidai na ukun wanda aka rubuta budurci mai raga raga Aliyu ya juyo, cikin sauri ta ajiye littafin tajuya tafita, mayar da idanuwanshi yayi ya kulle bayan yaga fitarta yasake gyara kwanciyarsa,

Dakin ummi takoma tazauna aranta tana cewa “ashe shima wannan Aliyun A ne tab”

Haka kawai taji kunyarsa ma ta dirar mata domin sai take ganin kamar kawai niked yake kallonta tunda yasan wadannan abubuwan, ji tayi tana kunyar sake hada hanya ma dashi dan haka tafara haramar tafiya,

Tana tattara takardunta zata zuba ajaka ita kuma ummi tafita tattaro mata kwanukan da takawo musu abinci rannan ya daga labulen dakin yashigo yana cewa,

“Ummi me zan dafa ne wallahi yunwa nake j….”

Ganin Sadiya ita kadai acikin dakin yahanashi karasa fadin abinda yasoma fada,

“Ummin tana waje inajin kitchen tashiga” Ta amsa masa idanuwanta na kan jakarta wadda take hada tarkacenta aciki,

“Ok” ya amsa mata tareda juyawa,

“Yajikinka? Dazu ummi ke cewa bakaji dadiba”

Maimakon ya amsa sai ya kama labulen dakin ya tsaya yace mata,

“Meyasa kika daukar min littafi?”

Dagowa tayi ta kalleshi duk da bai jiyoba saida taji kunyarsa dama tasan yaganta kuma tunda yaga ta dauka to yasan ta karanta, shiru tayi masa tana kallon bayansa yanzu yasaka dogon wando sabanin dazu da yake sanye da wando iya gwiwa lokacin da yana bacci……

 

_Afuwan masoya masu bibiyar Dan asali, kwana biyu nashiga wani babban uzurine shiyasa kuka jini shiru amma da yardar Allah yanzu komai ya daidaita, tnx for ur support._

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

 

*_NA_*
*_UMMI A’ISHA_*

 

*17*

 

***Batare da ta bashi amsaba taci gaba da zuba takardunta acikin handbag dinta,

“Bakiji abinda nace bane?”

Dagowa tayi ta sake kallonshi tareda yin fuska duk da cewar tana tsananin jin kunyarshi,

“Wanne littafi kake magana akai?”

Kafin ya bata amsa Ummi tashigo rikeda food flasks din halimatu a hannunta, bata hanya Aliyu yayi tawuce ciki shi kuma yakarasa fita,

“Yawwa ga kwanukan Sadiya,mun gode fa madalla Allah yakara arziki da budi”

“Amin mama”

Tashi tayi ta karbi kwanukan daga hannun ummi tayi mata sallama tafita, bin bayanta ummin tayi domin yi mata rakiya,

Aliyu baya tsakar gidan lokacin da suka fito hakama da ta kalli dakinsa bata iya hangoshi ba dan haka tawuce ummi na biye da ita saida ta rakata har kofar gida sannan sukayi sallama tatafi ita kuma ummi takoma cikin gida,

Hango Aliyu tayi yana kokari hada wuta domin girka abinci,

“A’a da kana ina?” Ummi ta tambaya,

“Ummi ina cikin daki”

“Shine baka fito kunyi sallama da Sadiya ba?”

“Ummi bahaka bane” yafadi yana murmushi,

“Dan dai baka san irin dawainiyar da yarinyar nan tayi dakai bane lokacin da baka da lafiya, da ka sani da kafara mutuntata”

Kallon ummi yayi ya mike tsaye ya rike waist dinshi,

“Ummi to yanzu kuma me nayi? Ba mun gaisa da itaba?”

“Ni ai ba zancen gaisuwa nakeyi ba”

“To kiyi hakuri ummi, na tuba”

Murmushi ummi tayi takoma kofar dakinta ta zauna tana kallonshi ya dora girkin, yana yi suna hira da ummi har ya kammala dafa indommie guda uku yazuba musu a faranti yakai musu domin lokuta da dama tare suke cin abinci da ummi.

Bayan kwana biyu Aliyu ya koma aikinsa domin ya warware sosai, busy ya zama saboda kullum yana hanyar zuwa wurin aiki da hanyar zuwa islamiyya bashida lokacin kansa kamar yadda yake da, halimatu kuwa tun ranar bata sake leka gidan ba sai da aka shafe kwanaki shida,

Ranar alhamis da misalin karfe 6 ta fito daga school taji ya kamata ta leka ta gaida ummi domin kwana biyu basu gaisa ba, gidan ta nufa tana sake sake aranta,

Packing tayi tashiga gidan da sallamarta, Aliyu tagani zaune gaban murhu yana girki gabanshi kuma kayan miya ne yake gyarawa zai jajjaga daga shi sai three quarter da yar t shirt, ita abinma dariya yaso ya bata saboda yanda yayi d’ai d’ai da kwanuka agabanshi,

Batare da ya kalleta ba ya amsa sallamar tata, lokacin da take kokarin shiga dakin ummi ne yabi bayanta da kallo sakamakon kamshin turarenta da yaji ya bugi hancinsa,

Ganinta yayi sanye cikin wani maroon colour din leshi swiss ta yafa dan mayafinta akafada shima maroon, girgiza kanshi yayi ya maida hankalinsa akan girkinshi,

Halimatu dakin ummi ta shiga taganta tana yanka alayyahu nan ta gaidata ta karbi yankan alayyahun,

“Aliyu ne yake azumin nashi na litinin da alhamis shine aka hadani da yankan alayyahu, shi gashi can awaje yana girki”

“Allah sarki, Allah yabada lada” Shine abinda Sadiya ta fada taci gaba da yanka alayyahun, babu bata lokaci ta gama ta dauka tafita yana inda tabarshi azaune yana faman mutsuttsuka idonshi daya wanda ko ba afada mata ba tasan yajine ya shiga,

“Kawo in jajjaga maka”

Baiyi magana ba yatashi daga kan kujerar ya nufi wurin ruwa, sai da ya cika bucket guda sannan yashige bayi,

Zama tayi a inda ya tashi ta jajjage masa kayan miyan nan ummi ta fito,

“Au halima kece mai girkin kuma? Shi din yana ina?”

“Ina jin wanka yashiga”

“Kuma shine zai bar miki, tashi kar kiyi kauri”

Murmushi halimatu tayi,

“Mama babu komai wlhi, barshi in karasa masa ai ma yana kokari, namiji da girki”

Zama ummi tayi nan ta soma bata labarin ai Aliyu tun yana karami shine yake dafa musu abinci kuma duk wani aikin gida wanda mace keyi to shi yanayi babu ruwansa da cewa wai shi namiji ne,

“Lallai matarsa ta huta” Inji halimatu,

“Ai kuwa dai matarsa zata sha girki”

Dariya dukkaninsu sukayi, Aliyu yana jinsu lokacin da yana wanka har yagama yafito hirarsa suke yi,

Dakinsa yawuce baiyi magana ba, ummi ce ta fadawa Sadiya abinda zai dafa wato shinkafa da miyar alayyahu dama kuma tuni ya dora shinkafarsa domin har ta nuna karasa tsantsamewa ne ba tayiba,

Sai da tajira ta tsantsame sannan ta sauke ta dora miyar, ga kayan amfaninsu nan tsaf babu abinda babu harda danyen kifinshi wanda zaiyi miyar dashi, zagewa Sadiya tayi ta rangada musu hadaddiyar miyar jajjage tasa kifi da alayyahun tareda wadatacciyar albasa ai tuni gida ya gauraye da kamshi, shi kanshi Aliyu wanda ke cikin daki yana tilawar hadisan da ya haddace ji yayi kamshin na neman hanashi tilawar domin tamkar acikin dakin tukunyar miyar ke bararraka.

Ji yayi kamar yatashi yaje ya tsaya akan girkin ya shaki kamshin dakyau, shiru yayi ya ajiye littafin yana sauraron hirar dasu ummi keyi itada Sadiya,

Ana daf da za akira salla Sadiya ta sauke miyar nan ummi ta dorawa Aliyu ruwan zafi domin tasan baya iya cin komai idan yakai azumi har sai yasha tea,

Sadiya kam tashi tayi tana kakkabe jikinta domin tafiya gida,

“A’a Sadiya ki zauna kici abincin mana ko ki zuba ki tafi dashi” Ummi tace da ita tana dubanta,

Girgiza kai Sadiya tayi sannan tace,

“Wallahi mama nakoshi, yaushe zan tafi da abinci kuma, wallahi nagode”

Ummi bata kai ga kara yin magana ba Aliyu yafito domin yin alwala, yana jinsu ummi nata cewa ta zuba ta tafi dashi idan bazata ci ananba amma taki tace ta koshi,

Sallama tayiwa ummi tawuce, Aliyu dake alwala yabita da ido, bata jima da fita ba shima yafita domin zuwa masallaci, ganinta yayi tana kokarin bude motar,

“Allah ya kiyaye”

Shine abinda yace yawuceta,

“Yawwa, Amin” ta amsa tareda shigewa cikin mota tana mamakin hali irin nashi.

Ana idar da salla Aliyu yakoma gida tea ya hada ya fara sha kamar yadda al’adarshi take daga nan yazuba abinci ai ji yayi tamkar kunnenshi zai tsinke dan dadi, cakwai yaji abincin komai yaji, maggi yaji haka ma gishiri, tunda ya soma cin abincin baiyi magana ba sai ummi ce ke maganarta ita kadai sai dai wani lokacin yace mata uhm ko um um amma baya magana ita kam ummi bata zaci dadin abincin ne ya hanashi magana ba saboda tasan dabi’arshi ce rashin yin magana musamman idan yana cin abinci,

Sai da yaji ya koshi yayi hamdala sannan ya kalli ummi wadda ta maida hankalinta wurin shimfida zanin gadon da ya wanke mata akan katifarta tashi yayi ya karba duk da tanata hanashi akan yazauna abincin ya tsirga masa amma yaki har sai da ya karba ya shimfida daga nan ya zauna akusa da ita tareda fadin,

“Ummi abincin nan yayi dadi, yarinyar nan ma kamar tafini iya girki”

Dariya ummi tayi kafin ta shafo kanshi,

“To da inbanda abinka taya zaka hada girkin mace da namiji Aliyu?”

Murmushi yayi,

“Allah Ummi nafi wasu matan iya girki musamman yan matan yanzu wasunsu babu abinda suka iya sai chaten da kwalliya”

“To dai banda halimatu domin ita gashi nan tayi kuma har ka yaba”

Murmushi yayi yatashi yafita baice komai ba bayan ya tsiyayi ruwan zafi a cup, dakinshi yashiga ya kwanta domin duk jinshi yake agajiye.

Haka rayuwa taci gaba da kasance musu Sadiya tana dan lekawa gidan jifa jifa dan bata yin kwana uku bataje ba, sannan duk ranar da taje indai ta samu Aliyu yana aiki wanda ya danganci tsakar gida to takan karba tayi, muslima kuwa budurwar Aliyu tuni anyi bikinta dan haka yayi kokarin ganin ya manta da ita,

Yau Sadiya da zazzabi ta tashi tareda ciwon kai shiyasa bata fita ko inaba, duk da tasha magani amma hakan bai hanata wuni akwance ba wasa wasa daren ranar ko bacci bata samu tayi ba dan haka washe gari ta tashi agalabaice domin harda ulcer dinta ta tashi,

Asibiti umma ta kaita ita da Abba nan aka bata gado domin har ta soma fita daga hayyacinta, umma ce ta zauna tare da ita tana kulawa da ita har tsawon kwana biyar.

Ummi kuwa mahaifiyar Aliyu ganin Sadiya tayi kwana da kwanaki bata zo gidanba yasata zargin akwai wani abu, lekawa dakin Aliyu tayi wanda ke kwance yana son ya danyi bacci domin yau ko gareji baije ba kasancewar weekend ne kuma a weekend basu fiya samun aiki da yawa ba,

“Aliyu nace ko zakaje gidansu yarinyar nan Sadiya ka dubo ko lafiya, kaga yau kwananta shida rabonta da gidan nan”

Jijjiga kai yayi batare da yayi magana ba domin shima rabon da yaganta agidan tun ranar da tazo yana kokarin yin wanke wanke ta karba tayi.

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

 

*_NA_*
_*UMMI A’ISHA*_

 

*18*

 

***Gyara kwanciyarshi yayi bayan fitar ummi nan ya dauki wayarshi yana dubawa domin yana tunanin kamar akwai number dinta aciki saboda akwanakin baya ta tutturo masa sako,

Number yafara kira amma kuma akashe wayar take saida yakira fiyeda sau goma amma duk dai maganar iri daya ce ganin yakasa samunta yasa shi mikewa tareda saka wayar acikin aljihu, fita yayi zuwa dakin ummi,

“Ummi nace to ai ni ba sanin gidan nasu nayi ba…”

“Ehh to gaskiya kazo da magana domin nidinma ba sanin nayiba amma dai ta taba kwatanta min unguwar tasu dan haka idan kaje sai dai ka tambaya kace gidan dan kwangila”

“To shikenan ummi bari inje ingani”

“Yawwa dan Allah jeka ka dubo mana, Allah ya kiyaye hanya”

Fitowa yayi daga dakin Ummi ya saka takalmansa yafita, machine yahau tiryan tiryan yana bin kwatancen Ummi har suka je unguwarsu Sadiya, afarkon layin suka tsaya domin tambayar gidan, wani mutum ne yataho akan keke nan Aliyu ya tareshi suka gaisa ya tambayeshi ko yasan gidan Dan kwangila,

“Yaro lafiya kake neman gidan?”

“Lafiya baba amma dai idan kasan gidan ka nuna min”

” Nifa agidan nake aiki, nine mai yimusu bayin flower amma yanzu dai basa nan dukkansu suna asibiti domin yarsu bata da lafiya”

“Baba wanne asibitin kenan?”

“Asibitin nan dai na turawa wanda turawa ne suke duba mutum”

Tunda yafadi haka Aliyu ya gane British hospital yake nufi,

“To Allah ya bata lafiya, nagode”

Machine din yahau yace suje asibitin, nan suka tafi tsawon tafiyar minti 20 suka je, mai machine din ya sallama shikuma ya shiga ciki, kasancewar asibitin na masu ido da kwalli ne kadai yasa bai sha wahala ba wurin nemo dakin da aka kwantar da Sadiya ba,

Tana kwance akan gado duk tayi yaga yaga da ita domin ulcer batayi mata da wasa ba, Khairiyya kuma na zaune kan kujera akusa da gadon wanda ayau tazo ganin zuwanta ne ma yasa umma tafiya gida zataje tadawo,

Saida yayi knocking sannan yabude dakin yashiga da sallamarshi,

Khairiyya ce ta amsa nan ya karasa shiga cikin dakin suka gaisa, Sadiya ya kalla wadda ke kwance jikinta sanye da doguwar riga ta atamfa tayi wani fayau da ita bakinta duk abushe,

“Ya mai jikin?”

“Da sauki” Inji khairiyya,

“Allah yakara sauki, Allah yabata lafiya”

“Amin”

Bude idonta tayi domin sama sama take jin murya kamar ta Aliyu ai kuwa tana budewa taga shi dinne, dan kwalinta ta laluba zata rufe kanta,

“Sannu Sadiya….”

Fuska ta dan saki kafin ta amsa da,

“Yawwa Aliyu” jin ta ambaci Aliyu yasa khairiyya ta sake kallonshi domin tana zaton shine wanda Sadiyan ke bata labari last time,

“Ya jikin naki?”

“Da sauki, ina mama?”

“Tana nan lafiya, bata san bakida lafiya ba ai dan nima sai yanzu da naje unguwarku ina neman gidanku shine aka sanar dani cewa kina nan”

“Allah sarki nagode sosai”

“Babu komai ai, bari yanzu inje inkoma domin in fadawa Ummi, Allah yakara sauki”

“Amin, ka gaisheta nagode”

Sallama yayiwa khairiyya sannan yafita, yana fita khairiyya tacewa Sadiya,

“Shine ko?”

Daga mata kai Sadiya tayi tana murmushi,

“Ai tunda naji kin kira sunanshi jikina yabani cewar shine, gaskiya ya hadu fa amma gashi acikin nutsuwarshi yake yin komai hatta maganarshi ma yana yinta ne ashirye daki daki gaskiya dan gayu ne”

“Umma khairiyya kenan wadannan kadanne kika sani akwai wadanda baki saniba, Aliyu ba irin samarin yanzu bane shi babu ruwansa abinda yasan zai amfane shi kawai yake yi”

“Ai naga alama kuma ni kaina na yaba da nutsuwarshi, sannan abinda na lura dashi kamar yanzu kema kin samo kansa”

Murmushin karfin hali halimatu tayi wani dadi yana ratsata, nan suka cigaba da tattaunawa akan Aliyu wanda har umma tadawo basu gama ba.

Kamar dazu yanzu ma machine yahau zuwa gida, a tsakar gida ya samu ummi tana tattare kayan dake shanye akan igiya wadanda suka bushe, jin sallamar Aliyu yasata dakatawa tana jiran karasowarshi,

“Aliyu Allah dai yasa ka sami gidan”

“Nasamu Ummi amma basa gidan ma suna asibiti domin bata da lafiya”

“Ikon Allah, tun yaushe kenan?”

“Ehh to inaji dai zai kai kwana shida, amma naje har asibitin na ganota zuwa dare sai inkoma idan kuma zamu tafi tare to”

“A’a kai dinma ka isa Aliyu ni basai naje ba tunda kasan inata fama da ciwon kafa”

“To shikenan Ummi Allah ya kara lafiya, nidin sai inje”

“To shikenan kayi mata sannu”

Kayan hannunta ya karba yashiga dakinsa dasu domin ninkewa.

Bayan sallar isha kamar yadda ya fadawa ummi shiryawa yayi domin zuwa asibitin, coffee colour din yadin kufta yasaka yasa hula yayiwa ummi sallama yatafi, sai da ya tsaya ya siyi abin dubiya sannan yawuce asibitin,

Zuwansa yayi daidai da zuwan Abdul wanda shima yazo duba Sadiya domin shi kullum sai yazo fiyeda sau daya sannan ka’ida ne da daddare anan yake hira shida umma idan itama sadiyan taji dama dama tasa baki,

Abdul na shiga dakin shima Aliyu ya shiga, Sadiya na kwance saman gado khairiyya na gefenta umma kuma tana kan sallaya tana salla,

Dukawa saitin fuskarta Abdul yayi yana cewa,

“Sannu princess, ya karfin jikin?”

“Da sauki friend” Tafada ahankali,

Kujera khairiyya ta bawa Aliyu ya zauna shikuma Abdul ya zauna gefen halimatu bayan ta tashi zaune,fuskarta dauke da farin ciki da annashuwa take kallon kowa musamman ma Aliyu wanda bata tsammaci zuwansa ba adai dai wannan lokacin,

“Yajikin naki?” Aliyu ya tambaya fuskarta babu yabo babu fallasa domin haka kawai yaji baiji dadin irin shisshigewar da yaga Abdul nayi mata ba gashi yaje ya wani kunaceta kamar zai hada jikinsa da nata,

“Da sauki Haidar,ya mama?”

“Tana gaisheki” ya fada batare da ya kalli wurin da suke ba,

“Princess ga Tamarin juice din wallahi duk naduba babu kwaya dayan nan nasamo miki” Abdul yace da halimatu yana kokarin bude mata sanyayyen lemon dake hannunshi,

Mika mata yayi kamar zai saka mata abaki nan takarba tasoma sha tana kallon Aliyu wanda ya wani bata rai kamar dole aka yimasa zuwa dubiyar, ganin ummanta ta idar da sallar yasa Aliyu sauka daga kujerar da yake kai ya gaidata daga nan yamike domin tafiya saboda baya jin zai iya cigaba da zama yana kallon wannan Abdul din,

“Harda wahala kuma Aliyu? Allah yasaka da alkhairi to mun gode ka gaida Maman taka” Umma tafada bayan ta dauki ledar fruits din da yakai,ko kallon su halimatu baiyi ba ya nufi kofa domin fita, khairiyya ce tayi azamar cewa,

“Aliyu mun gode ka gaida gida”

“Yawwa” shine amsar da yabata kawai yafita, yana fita yatsaya jikin bangon dakin ya jingina dashi yana jin zuciyarsa na harbawa bayada bacin ran da ya lullubeshi batare da yasan dalili ba…..

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

 

*_NA_*
*_UMMI A’ISHA_*

 

*19*

 

***Yafi mintuna goma jingine ajikin bangon kafin daga bisani ya iya yin jarumtar barin wurin zuciyarsa cikeda bacin rai,

A kasa yasoma tafiya domin yana son ragewa kansa damuwar dake cikin ranshi dan haka ya zabi takawa da kafa,

Wa’azin marigayi sheikh ja’afar Mahmud Adam ya kunna yajefa wayar agaban aljihun rigarshi yana saurare,

Sosai wa’azin yake masa dadi domin malamin yana magana ne akan rayuwar ma’aurata da abubuwan dake kawo tabarbarewar aure a wannan zamanin har ila yau kuma agefe guda malamin wasu points yake bawa mata wadanda zasubi wurin mallakar zuciyoyin mazajensu,

Kasancewar hankalinsa gaba daya yatafi ga wa’azin da yake sauraro yasa sam baiga nisan tafiyar ba lokaci kadan ya karasa unguwar, bai shiga gidaba yasamu wani kwalabati agefen titi yazauna yana mai cigaba da sauraron wa’azin, sai karfe 10 saura minti biyar yatashi daga wurin ya nufi gida, number halimatu yasoma kira cikin sa’a tashiga amma kuma waiting call domin tana yin waya lokacin da Abdul,

Ganin wayar ta nuna masa waiting call yasa yaji gabanshi yafadi domin yasan da saurayi take waya, bai kai ga karasa tunaninshi ba yaji wayar tashi tana kara ganin itace yasashi katse kiran sannan yakirata, muryarta akasa kasa tayi magana,

“Haidar ya kaje gida?”

“Lafiya lau, yajikin naki?”

“Da sauki sosai”

“Allah yakara baki lafiya”

“Amin”

Shiru sukayi daga shi har ita, can dai yayi karfin halin tambayarta,

“Wannan Wanda naganshi a asibiti dazu yayanki ne?”

Sosai tambayar tashi tabata mamaki kuma ta daure mata kai,

“Ko bazaki fada min bane?”

Jin abinda yace yasata saurin dawowa cikin hayyacinta,

“A’a ba yayana bane…”

“Ba yayanki bane?” Yasake tambayarta,

“Ehhh, Dan makarantarmu ne”

Ajiyar zuciya yasauke mai nauyi wadda har saida halimatu ta jiyota,

“Amma shine yaketa wani shisshiga jikinki sai kace muharraminki? Kin san matsayin hakan acikin addini kuwa?”

Murmushi tayi ta kalli umma khairiyya wadda ke zaune gefenta tana jiyo duk maganganun Aliyu daga cikin wayar,

“Bakiji nane?”

“Ina jinka”

“To kuma shine ina tambayarki zakiyi shiru?”

“Ba shiru nayiba”

Saida ya dan ja lokaci sannan yace,

“To ki kiyaye dai domin babu kyau wanda ba muharraminki ba yarinka kusanta dake yana kokarin shiga jikinki kin gane?”

“Ehhh nagane” Tabashi amsa tana toshe bakinta saboda kar dariya ta subuce mata,

“Shikenan Allah yabaki lafiya, sai da safe”

“To nagode, agaida mama”

“Zataji” Daga haka ya katse wayar yashiga gida duk da har lokacin hankalinsa bai wani kwanta ba amma dai yasamu sassauci daga kaso mafi yawa,lokacin da yashiga gidan ya samu ummi tayi bacci shiyasa ma kawai yawuce zuwa dakinsa kayan jikinsa yarage yaje ya watsa ruwa sannan yazo ya kwanta amma kuma sai me?? Tunanin Sadiya ne yafara damun kwakwalwarsa nan surarta da halayenta suka fara shammatar zuciyarsa,

Ajiyar zuciya yaja yagyara kwanciyarsa yana mai tuno labarin da ummi tabashi akan irin kulawar da Sadiya tarinka bashi lokacin da bashida lafiya, yanzu dai yasan zuciyarsa bata da zabin da yawuce na Sadiya domin yaji alamun hakan irin alamun da baiji ba ko a lokacin da yana soyayya da muslima,

Tashi yayi yafara nafiloli yana neman zabin Allah dangane da Sadiya, idan har alkhairi ce agareshi Allah ya daidaita su idan kuma sabanin hakane to Allah ya musanya musu junansu da mafi alkhairi domin yasan Sadiya tana sonsa tunba yanzu ba kuma bata da makusa abangaren halittarta ko halayyarta.

A bangaren Sadiya kuwa suna gama waya da Aliyu ta kalli khairiyya tace,

“Umma khairiyya kinji Aliyu da wani magana kuma,wai tambayata yake meye hadina da Abdul”

Murmushi khairiyya tayi,

“Ina jinku ai, da alama ai Aliyun nan naki kishi gareshi dan naga alamun hakan dazu da yazo ya samu Abdul, idan kin kula da safe yafi faran faran akan dazun nan”

“To shine yanzun harda su yimin wa’azi shi a lallai ustaz”

Dariya sukayi gaba dayansu, sunfi fiyeda 12 suna hirar Aliyu kafin daga bisani suka kwanta.

Washe gari da yamma aka sallami halimatu daga asibiti suka koma gida, duk da Aliyu baida sha’awar sake komawa asibitin domin baya son ganin shisshigin Abdul wannan dalilinne yasa shi tura mata text ya dubata nan ta sanar masa da cewar anjima kadan za a sallamesu,

Tun daga wannan lokacin basu kara haduwa ba duk da tasamu sauki amma sai ta dauke kafarta cak da zuwa gidansu Aliyu wanda dayane daga cikin shawarwarin da khairiyya tabata na cewa ya zama wajibi yanzu tayi nesa da gidansu Aliyu ko dan jawowa kanta daraja da mutunci, duk da basa haduwa Aliyu yakan kirata jifa jifa ya wayince da yimata ya jiki ko kuma ya tura mata text, gashi yana masifar son ganinta amma ganin nata yaki samuwa,

Kasancewar yau alhamis bai dawo gida da wuriba sai karfe 6 saura domin babu islamiyya, sai da yafara yin wanka sannan yashiga dakin ummi,bai jima ba yafito ya koma dakinsa ya kwanta yana jiran lokacin shan ruwa yayi,

Wayarshi ya dauka yasoma kiran halimatu, daf da zata tsinke ta daga,

“Yanmata yakike?”

“Lafiya lau, ya aiki”

“Alhamdulillah aiki babu dadi gashi yasani nagaji sosai”

Murmushi tayi,

“Allah ya taimaka”

“Amin,yaushe zaki zo kigaida ummin taki?”

“Babu rana”

“Saboda me? Kullum fa sai ta tambayeki shine ba zaki zo taganki ba?”

“Ai makaranta ce ta sakoni agaba haidar shiyasa yanzu babu time”

“Shikenan Allah yabada sa’a, ni tunda ina son ganinki nazo school din inganki”

Murmushi tayi har cikin ranta taji dadin abinda yace hakanne ma yasata kasa magana sai faman murmushi dake fita daga kan fuskarta,

“Gobe kina da lecture?”

“Uhmm inada guda daya amma 9-11 ne”

“Babu matsala zan shigo 11 din lokacin da zaki fito”

“To shikenan Allah yakaimu”

“Amin, kihuta lafiya”

“Nagode”

Katse wayar yayi yana tunanin yaushe Sadiya tayiwa zuciyarsa irin wannan shigar wanda shi kansa bai ganeba sai yanzu?.

Kamar yadda yace ranar friday ko gareji baije ba yafara biyawa ta makarantarsu halimatu yana shiga tana fitowa daga lecture, waya yayi mata yace gashi yashigo nan ta kwatanta masa inda take, suna tsaye itada Sabira da Abdul, jin ba lokacin halimatu zata tafiba yasa Sabira tafiya tabarsu,yarage daga ita sai Abdul jingine jikin motarta,

Tun daga nesa Aliyu ya hangosu dan haka yaji bazai iya karasawa ba juyawa yayi batare da yabari taganshi ba ya tinkari gate din fita….

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

_*NA*_

_*UMMI A’ISHA*_

 

*20*

 

***Daf da gate din yaji wayarshi tana kara,cirota yayi daga cikin aljihunsa yaga Sadiya ce ke kiranshi, kamar bazai dauka ba yadai daure ya daga,

“Yaya Haidar ban ganka ba fa…. Gashi inata tsaye arana”

Yanda tayi maganar cikin shagwaba sai yaji bazai iya hakura da ganinta ba dan haka cikin muryarshi kasa kasa yace,

“Yi hakuri gani nan, amma ki shiga inuwa saboda bana son kiyi baki kafin nazo….”

“Babu bakin da zanyi fa…” Tasake fada cikin shagwaba,

“A’a zakiyi mana, kefa fara ce”

Murmushi tayi ta katse wayar,

Ahankali yake takawa har yafara hangota tana tsaye jikin motarta tana daddanna wayarta fuskarta sanye da farin glass na gayu tasha uban dauri kamar wata amarya,

Jikinta kuwa sanye take da atamfa pink colour mai zanen hoton iron ajiki tasa mayafi pink, haka flat shoe dinma dake kafarta shima pink ne, duk da baiga fuskarta ba domin tabashi baya amma sai yaga tayi masa mutukar kyau,

Ta bayanta ya tsaya yayi mata sallama, jin sallamarshi yasata juyowa dauke da murmushi idanuwanta a kasa domin bata jin zata iya hada ido dashi,

“Sannu da zuwa… Mu shiga ciki saboda rana ko?”

“Nagode da wannan karramawar” ya fada shima yana murmushi,ga mamakinta sai taga ya bude mata kofar side din nata, shiga tayi ya mayar kofar ya rufe ya zagaya daya side din yashiga, wani sanyine ya shigeshi sannan wani daddadan kamshi ya biyo baya,

“Ina yini?” Tace dashi kanta akasa hannayenta jikin sitiyarin motar,

“Lafiya lau halima mai tagwayen suna, ya kike?”

Murmushi tayi sannan ta amsa ahankali da,

“Lafiya lau”

Shi kansa ya lura da yanayinta kamar irin tana jin kunyarshi or something like that saboda sam takasa kallonshi,

“Kin jima baki ganni ba amma shine yau bazaki kalleni ba?”

“Na kalleka ai”

Murmushin shima yayi yana duba agogon fatar dake daure ahannunshi wanda ya kasance baki,

Jin kamshin dake tashi daga jikinta yake kamar ana karashi domin duk yabi yagama cika masa kofofin hancinsa,

“Sadiya….” Taji yakira sunanta awata siga domin yafitar da sunan yanda yake a asalce,

“Na’am…!” Ta amsa masa har lokacin idanuwanta na wani wurin,

“Meyasa kike saka turare irin haka? Kin san hukuncin yin hakan acikin addini kuwa?”

Kasa bashi amsa tayi sai dai ta girgiza kanta,

“To babu kyau, annabi ya hana domin turare yana daya daga cikin abubuwan dake saurin tada fitina, shiyasa ba ason tuararen mace yayi karfi da yawa yanda kowa zai iya ji, anfi son tayi amfani da marar karfi ta yadda babu wanda zaiji sai wanda yaje kusa da ita, dan haka kema ki kiyaye domin hukuncin duk matar da ta saka turare idan zata fita to idan ta dawo malamai sunce sai tayi wanka domin kamar tayi zina ne….”

Sai lokacin ta dago ta kalleshi ga mamakinta ba ita yake kalloba amma jin idanuwanta ajikinshi alamun shi take kallo yasashi juyawa shima ya kalleta, saurin kawar da idonta tayi kamar zatayi magana kuma sai ta fasa,

“Me kike son cewa ne?”

Girgiza masa kai tayi alamun babu nan yayi murmushi yana mai cigaba da kallonta yace,

“Nasan abinda kike son cewa, idan nazarina yabani daidai kina so kice tunda ke ba matar aure bace ai wannan hukuncin baya kanki ko? To bahaka bane, a matsayinki na wacce ta mallaki hankalin kanta to duk wani hukunci wanda yahau kan matar aure to yahau kanki keda matar aure daya kuke awurin hukunci”

“Tohm, nagode, Allah yasaka da alkhairi Malam Aliyu, kuma insha Allah zanyi kokari inga na kiyaye”

Murmushi yayi wanda har saida hakoranshi suka bayyana saboda jin ta kirashi da Malam,

“A’a karki kaini inda ban kai ba, ya a matsayina na dalibi amma zaki bani matsayin malami? Karfa ki kaini wurinda bazanyi wuf infito ba…”

Dariya tayi kadan saboda jin abinda shima yafada, kasa dauke idonshi daga fuskarta yayi lokacin da tana yin dariyar domin sosai dariyar ke yimata kyau banda lotsawar da gefen kumatunta daya keyi wanda ke saitinshi, shagala yayi da kallon kyakkyawar fuskarta wacce take fara domin har tafi muslima tsohuwar budurwarshi haske kai gaba dayama babu ta inda za ahada Muslima da halimatu wurin kyawun sura duk da ita Sadiya kyawun nata harda hutu aciki amma duk da haka tafi muslima komai,

Jin alamun har lokacin kallonta yake yasata dan kallonshi kamar yadda ta zata din kuwa itan yake kallo, shiru tayi acikin zuciyarta tana cewa,

“Farkon ganina dakai ko kallona bakayi ba wai kai baka kallon mata amma ji yanzu kallo kamar zaka cinyeni”

“Ya mama?” Ta fada afili saboda son kawar da zaman shirun da suke,

“Tana nan lafiya duk da kinki zuwa gaisheta”

Murmushi tayi ta zare glass din dake idonta tadauki tissue wadda ke ajiye a motar tafara goge fuskarta,

“Zan zo ai in gaidata din amma kafin inzo kafara mika min gaisuwata tukunna”

Sosai yake mamakinta saboda yanayin yangarta da shasshan kamshi duk da ya fahimci kamar nature dinta ne hakan amma shi bai taba fahimta ba sai yau,

“A’a ni babu abinda zan fada sai dai kije da kanki”

“To ai dama zanje, wannan sakon baka shi nayi kafin nazo din”

Make kafadarshi yayi alamun a’a, murmushi hakan da yayi yasata batare da ta shirya ba,

Kallon agogo yayi sannan ya kalleta,

“Kinga saboda tsabar dadin hirar da kike yimin kinsa nakusa makara azuwa masallaci gashi yau ko gareji ban leka ba”

“Kayi hakuri, wanne masallacin kake zuwa?”

“Can na kusa da central market”

“To muje insaukeka”

Bata jira abinda zaice ba tayiwa motar key, har suka fita daga cikin school din babu wanda yayi magana acikinsu.

Saida tafiyar tasu ta fara nisa sannan yajuya ya kalleta chingum take taunawa ahankali yanda sai kayi dagaske zaka fahimci hakan murmushi yayi ya kalli titi,

“Yanzu sai yaushe zamu kara haduwa?”

Rausayar da kanta tayi sannan ta amsa masa,

“Yaushe kake son kara ganina?”

“Koda yaushe ina son iringa ganinki ai, ni ban ki in kwana ina kallonki ba”

Wani jirine taji yafara daukarta saboda bata taba zaton wannan ranar zata zo kwana kusa ba, ranar da Aliyu zai rinka furta mata dadadan kalamai kwatankwacin wadannan ba,

“Banji kince komai ba, ko ke baki son ganina ne? Allah sarki ni Aliyu”

Ya karasa maganar cikin cikar barkwanci, dariya sukayi gaba daya,

“Nifa bance ba…”

“To me kikace?” Yasake tambayarta,

“Nima ai ina son ganinka koda yaushe”

“To shikenan zamu rinka ganin juna koda yaushe din tunda muna son mu rinka ganin juna”

Murmushi tayi ta dan kalleshi sai kuma ta dauke kai taci gaba da taunar chingum dinta ahankali,

“Bani labarin wannan saurayin naki to naji” Yace da ita cikin son bugun cikinta,

“Zan baka amma sai kafara bani labarin budurwarka tukunna”

“Kina son ji?”

“Ehh mana,ko baka da ita ne?” Tabashi amsa gabanta na dar dar,

“Inada ita mana”

“Ohh ai nazaci ko tunda kasha kasa ka hakura”

Murmushi yayi ya kalleta,

“To ai nasake samun wata, har tafi waccar tsada da qualities….”

Sai da gaban Sadiya yafadi saboda jin abinda yace domin ta zaci ko dagaske watan ya samo wadda ba ita ba,

“Fara ce ko baka?” Ta tambaya,

“A’a farace tass tunda kinga ni ai bakine shiyasa gara in nemi fara ko?”

Shiru tayi masa acikin zuciyarta tana nazarin amsar da yabata,

“Ko dai kinfi son innemi bakar irina?”

“Nikuma awa?” Ta bukata cikin takaici,

“Ke a zuciyata mana”

Jin abinda yace yasata yin murmushi wanda ya fidda kyawunta azahiri har Aliyu yakasa daina kallonta,

“Kajika da wata magana, taya nazama zuciyarka?”

Murmushi yayi ganin sun karaso wurin masallacin yasashi cewa,

“Ki bari zan fada miki sai next time yanzu kinga munzo gashi har liman yafara khuduba, sai munyi waya ko?” Ya karashe maganar yana mai rausayar da kanshi,

“Shikenan babu damuwa, adawo lafiya”

“Allah yasa, nagode”

Bude kofa yayi yafita da murmushi akan fuskarshi, itama da murmushin ta rakashi aranta tana jin rashin dadi domin bata so hirar tasu ta kare ba yanzu, jan motarta tayi ta nufi gida tana mai cikeda farin ciki.

Farin cikin da take ciki yau abin ba acewa komai dan har agida ma umma ta fuskanci hakan, tun daga ranar bata bari sun sake haduwa ba sai ja mishi aji takeyi, ahaka har sukayi 2 weeks basu haduba,

Ana daf da yin 3 weeks ne takira shi tace mishi yau birthday dinta, duk da shi bai fiya shiga irin wadannan abubuwan ba amma ya amsa mata domin baya son yayi abinda bazata ji dadiba,

Da misalin karfe 3 yabar gareji yakoma gida yau ko islamiyya bazai je ba domin yana son halattar wurin birthday din Halimatu,

Halimatu kuwa yar gata agida saida umma da abba suka hada mata dan kwarya kwaryar party kowa yabata gift, Abba wata kyakkyawar sarkar daham ya bata mai dan karen kyau yayinda ita kuma umma tabata wani agogo na gold,

Karfe 5 Sabira da Abdul suka zo suka dauketa zasu tafi wurinda zasuyi birthday party din wanda Abdul ya hada mata, fadin irin kyawun da halimatu tayi abin ba a magana, wata lafiyayyar gown tasaka dark blue mai kwalliyar pink ajiki da stones ko ina agaban rigar, fuskarta tasha make up na zamani wanda ya bayyanar da kyawunta afili, kanta kuwa kitsone yafi 40 wanda akayi mata shi da rubber attach, ga farcen roba da aka saka mata banda eye lashes nan Sadiya kamanninta duk suka sauya tafito tamkar wata baturiya,

High hill tasa a kafarta tayafa dan siririn mayafi akanta,

Wani lafiyayyen wurin cin abinci na masu hannu da shuni suka nufa domin acanne Abdul yakama musu sannan yasa akayi decorating din wurin kamar biki za ayi banda wani rusheshen cake da yayi order, ga drinks kala kala, Allah ne kadai yasan adadin kudin da yakashe akan wannan birthday din na halima,

Basu dade da zuwa wurinba Aliyu ya kirata a waya cewar yazo Sabira ta tura ta shigo dashi, tun daga nesa yake kallonta itama tana kallonshi, duk da cewar wurin babu mutane da yawa domin su ukune ma kacal sai ko ma’aikatan wurin amma hakan bai burgeshi ba,

Hannu ya mikawa Abdul suka gaisa yaja kujera ya zauna, daga shi har ita basu yiwa juna magana ba saboda jikinta yabata kamar fushi mutumin nata yake yi, kida aka kunna musu Sabira da Abdul suka fita duk da su dinma ba rawar suke yiba sai aukin daukar selfie,

Matsawa kusa da kujerarshi tayi tayanda zaiji abinda take fada,

“Haidar me ya faru ne?”

Kallonta yayi ya kurawa kanta ido yana kallon kitsonta ta cikin gyalen dake kanta,

“Bakya salla ne?”

Kallonshi tayi cikin rashin fahimta,

“Meya faru?”

“Amsar fa dayace ehh ko a’a…”

“To ai ban gane tambayar taka bane shiyasa”

Murmushi yayi ya kalli side din su Abdul har lokacin suna can wurin cake suna daukar hotuna,

“Ina nufin period kike yi?”

Shiru tayi masa sakamakon jin abinda yace, hannunta taji ya riko kamar a mafarki wani shock taji tamkar anjona mata wayar lantarki, shima din hakan yaji amma yadaure nan ya kurawa farcinan hannunta ido yafi minti biyu yana kallon farcinan sannan ya sakar mata hannun yana kallonta……

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

*_NA_*

_*UMMI A’ISHA*_

 

*21*

 

***Sunkuyar da kanta tayi tana jin faduwar gaba atare da ita,

“Nayi miki magana amma kinyi min shiru ko?” Taji yace da ita yana kallonta domin taji alamun hakan ajikinta,

“Kayi hakuri…”

“To ki amsa min mana, ehh ne fa amsar ko a’a…., kina fashin salla ne yanzu?”

Kai ta girgiza masa alamun a’a,

“Amma shine kika saka wadannan farcinan robar harda karin gashi, to ki fada min ta yadda za ayi ruwa yashiga kasan gashinki da kasan farcenki idan kinzo yin alwala”

Nan dinma shiru tayi masa haka kuma bata dago ta kalleshi ba,sassauta murya yayi,

“Kinga idan duk wadannan guraren ruwa bai shiga ba alwalarki zata zamana da lam’a kuma kin san hukuncin lam’ar?”

Shiru tayi masa duk da bawai sani din tayi ba,

Zuwansu Abdul ne yasashi yin shiru daga maganar da yake yimata, dagowa tayi suna magana da Sabira tana satar kallonshi, kananan kayane a
Jikinshi green din riga mai dogon hannu sai brown din trouser sosai taga yayi mata kyau amma ayau dai kam tana cikeda kunyarsa ita tsoronta ma daya kar yace ya fasa soyayya da ita tunda bata da tarbiyya,

Wannan dalilin ne yasa koda su Abdul suka kirata domin yanka cake taki zuwa saboda bata son tayi laifi awurin Aliyu, shi kuwa gogan sai wani basarwa yake,

Kinkimar cake din akayi aka sa a motar Abdul bayan an yanka daga nan suka kwashi drinks din suka bar saura, dukkaninsu fitowa suka yi nan Aliyu ya kirata gefe, idanuwanta akasa dan haka yasamu damar zuba mata idanuwanshi yana kallonta, yaufa tatafi dashi ba kadanba domin bai taba ganinta cikin kwalliya irin haka ba, shirun da taji yayi yawa ne yasata dagowa nan idonta ya shiga cikin nasa, dakyar ta iya saukar da nata idon, gabanta ya sake matsawa wanda har tana iya jiyo hucin fitar numfashinsa,

“Ga birthday gift dinki…” Yace da ita tareda ciro wani dan karamin ring case pink colour, mika mata yayi takarba fuskarta dauke da farin ciki da kuma jin dadi,

Ahankali ta bude nan taga zoben azurfa mai kyau,kallonshi tayi ta kalli zoben kawai sai ta rufe fuskarta da tafin hannunta tana murmushi,

“Kunyar ta menene? Uhm….?”

“Nagode Aliyu, nagode sosai, wannan ring din yayi kyau sosai”

Murmushi yayi,

“Kina sonshi kenan?”

“Sosai ma….”

“To ina so kiso wanda yabaki shi fiyeda yanda kike son zoben”

Wani murmushin tayi ta juya tasake juyowa tana fuskantarshi,

“Happy birthday to u….”

“Thank u” Ta amsa cikeda kunya, kallonta yayi saboda yanda take jin kunyarshi abin yana bashi mamaki domin sam ta kasa sakewa dashi su rinka magana ta fahimta babu kunya bare rufa rufa,

“Kina komawa gida ki tsefe kitson nan kuma ki cire farcen nan”

“Tohm” Ta amsa mishi,

“Shikenan bari natafi, sai munyi waya ko”

Kai ta daga masa, dakyar tace,

“Nagode,kagaida mama”

“Zata ji”

Daga haka ya wuce ya tafi, tsayawa tayi tana kallonshi har ya bacewa ganinta tadaina hangoshi.

Wani farin ciki ne da shauki ke dawainiya da ita, tana rikeda dan akwatin zoben da yabata tashiga gaban motar Abdul, daga Abdul din har Sabira babu wanda yayi mata maganar Aliyu, sai da suka danyi nisa sannan ta juyo ta dubi Sabira dake zaune saitinta abaya,

“Sabira dan Allah yanko cake babba ki hada da drinks mu kaiwa wancan guy din na dazu…”

Dariya Abdul da Sabira suka yi saboda jin abinda tace,

“Da girman kujerarki our buffday girl….” Inji Sabira nan ta dauki wata yar karamar wuka dake ajiye gefen cake din ta shaftaro katon cake tasa cikin leda,

Har suka zo kofar gidansu Aliyu halimatu ce ke kwatantawa Abdul, lokacin da motar ta tsaya halimatu ta juya ta kalli Sabira tana rokonta akan ta taimaka ta shiga ta kaiwa ummi tace abawa Aliyu, dakyar Sabira ta amince domin ita da cewa tayi sai dai su shiga tare,

Ita kam Sadiya bata son shiga gidan saboda kunyar ummi take ji da kuma shi kanshi Aliyun,

Minti biyar yayi yawa da shigar Sabira sai gata ta fito ta bude motar ta fada suka wuce, halimatu sai tambayarta take yi ko Aliyu na ciki? Amma Sabira tace ita bata ganshi ba mamanshi kadai ta gani, duk da haka dai Sadiya tayi farin ciki domin tasan sakonta zai isa gareshi.

Bayan ta koma gida sun rabu da su Abdul zoben da Aliyu ya bata ta fitar daga ma’adanarsa ta saka a babban dan yatsanta na tsakiya bayan ta nunawa umma, ba kadanba zoben yayi mata kyau domin silver ne sai wani farin stone dake samansa,

Sai da tayi wanka taci abinci ta nutsu sannan ta turawa da Aliyu text din godiya tareda nuna jin dadinta,

Kamar yadda yace mata cikin kwana biyu ta tsefe kitson kanta dama farce kam tun ranar da ta dawo daga wurin birthday dinta ta ciccire shi,

Yau ta kama ranar talata, 10:30 suka fito daga lecture daga ita sai Abdul kasancewar Sabira bata shigo ba,

Suna tsaye suna hira Abdul na gwada mata yanda wani lecturer dinsu keyi idan yana yi musu lecture, ita kuwa Sadiya me zatayi idan ba dariya,

Alamar shigowar text taji cikin wayarta wacce ke rike a hannunta, Aliyu ne dan haka tayi gaggawar budewa,

_Zo gani ina jiranki wurin motarki_

Waigawa tayi nan ta hangoshi tsaye ya juya musu baya, cewa Abdul tayi tana zuwa ta juya ta tafi, kananan kayane ajikinsa da alama gareji zaije,

Har ta karasa wurinsa bai jiyoba, motar ta bude ta kalleshi tace,

“Mu shiga ciki”

Girgiza mata kai yayi fuskarsa ba walwala,

“Sadiya wai menene hadinki da wancan yaron ne?? Tun rannan nake tambayarki amma kin ki fada min alhali duk wasu alamu sun nuna soyayya kuke yi…”

Kanshi ya dafe wanda yaji ya sara ta gefe daya,

“Dan Allah Aliyu kayi hakuri kar kanka yayi ciwo, ni wallahi Abdul ba saurayi na bane kawai friendship ne….” Ta fada arude,

Kallonta Aliyu yayi sai kuma yayi murmushi wanda yasake kona zuciyarshi,

Bude gaban motar kawai yayi ya zauna yayinda itama ta zagaya bangaren mai zaman banza ta zauna tana kallonsa duk hankalinta atashe yake saboda bata son kansa yayi ciwo tunda taga irin wahalar da yake sha,

“Ya angama bikin birthday lafiya?” Yace da ita cikin tsokana,

“Lafiya lau” ta amsa tana murmushi,

“Ke kuma tahaka kika godema Allah da ni’imar da yayi miki ta rai da lafiya da rufin asiri ko Sadiya?”

Shiru tayi tai kasa da kanta a zuciyarta tana fadin,

“Yanzu zai fara”

Dorawa yayi daga inda ya tsaya,

“Al’amarin zamanin nan yana bani tsoro halimatu, bikin birthday yazama kamar wani competition tsakanin yan mata da samari harda masu manyan shekaru ma, wai idan Allah yayi maka ni’ima ba so yake ka gode masa ba? Amma godiyar ai ya kamata kayita ta kyakkyawar hanya amma wasu sai kiga anhada sharholiya an tanadi duk wani nau’i na badala da sunan wai nuna farin ciki da ni’imar ubangiji agaresu, sam wannan bai dace ba kuma kuskure ne”

Shiru ita dai tayi tana jinsa, ita tarasa Aliyu wanne irin mutum ne,

“Kiyi hakuri fa badake nake ba…”

Murmushi tayi bata ce komai,ganin haka yasashi cigaba,

“Wai dan adam da ya kamata duk ranar da ya wayi gari yatashi cikin fargaba da nadama saboda kwananshi karewa yake yana sake kusantar kabari amma shine ko ajikinsa sai yayita yin abinda yake so…”

Sai lokacin tayi magana,

“Nidai idan akaina ne kayi hakuri bazan sake yin birthday party ba”

“Yawwa yanmata nah, walima zamu rinka yi ko?”

Murmushi tayi saboda jin abinda yace, kai ta daga masa alamun ehhh,

“To Allah ya sake rayaki, ya sake rayaki har ki kara shekaru dari nan gaba”

“Woohhh haba dai dari, lokacin ai nazama tsumma”

Dariya ya danyi,

“Kome kika zama ni ina tare dake kuma bazan gujeki ba”

Juyawa yayi ya kalleta,

“Halima ina sonki fa, baki saniba ko? Ina sonki sosai irin son da baki san kalarshi ba”

Tsabar farin cikin da take ciki ji tayi kwalla na neman sauko mata amma tayi ta maza wurin hana hakan faruwa,

“Kefa? Kina so na…?”

Ya tambayeta bayan ya kura mata ido,

Kasa amsa masa tayi saboda yanda ya tsareta da manyan idanuwanshi masu sa kasala,

“Uhm….?” Yace ahankali,

“To kadaina kallo na mana” ta fada a shagwabance,

Dauke idonsa yayi daga kanta,

“Nima ai kasan, ai kasan…..,ina…. Sonka” Tafada cikin sarkewar murya,

Murmushi yayi yana kallon zoben hannunta wanda yabata,

“A’a ni ban saniba sai yanzu da kika fada min…., amma dai nasan son da nake yimiki yafi Wanda kike yimin”

Murmushi tayi,bata kai ga yin magana ba wayarshi tasoma kara, daga aljihun wandonshi ya cirota bayan ya ciro wani dan karamin littafi,

Daga yanda taga yana amsa wayar kadai ya ganar da ita cewar Malam lawan ne, hankalinta ta mayar kan littafin dake ajiye kan cinyarshi, hannu ta mika zata dauka yayi saurin rike littafin, iya karfinta tasa ta fauce littafin,bai kara bi takanta ba yaci gaba da wayarshi yayinda ita kuma duk hankalinta ta tattarashi akan littafin domin littafin bai kai girman karamin hisnul muslim ba amma kuma hadisai ne kananu har guda dari aciki, murmushi tayi acikin ranta tana raya cewa ai idan Aliyu ya zama mijinta ita kam ta more,har yagama wayar bata farga ba domin hankalinta na ga littafin, ganin tafin hannunshi akan littafin yarufe wurinda take dubawar yasata dagowa ta kalleshi,

“Ashe harka gama wayar…”

Murmushi yayi,

“To wannan littafin dai ba irin wancan bane da har kike zumudin gani”

Kunya maganarshi tabata shiyasa dakyar ta iya daurewa tace,

“Nikuma wanne zumudi zanyi akan abinda nariga da nasani”

“Iye, lallai, kenan kin san a rukunin da kike?”

Shiru tayi masa ta dauke kanta ta kalli window,hakan da tayine yasashi yin murmushi.

“Ko?” Yasake tambayarta cikin sigar jan magana,

“Ehhh” Tabashi amsa har lokacin idanuwanta na kallon window,

“To meye na juya min keyar kuma? Uhm?”

Ba tayi magana ba kuma bata jiyo ba saboda har lokacin kunyarce bata saketa ba……

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI….!*🤴🏻

 

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

*22*

 

_Fatan alkhairi ga Momcyn Anas & Khairat up, i like ur comments….!_

 

***Ba tayi magana ba haka kuma bata jiyo ba saboda har lokacin kunyarce bata saketa ba, kallonta yayi yana dan shafa gemunsa,

“Tunda kin gaji da kallona shikenan bari naje na tafi”

Sai lokacin ta juyo da kanta amma bata kalleshi ba,

“Ni ba gajiya nayi da kallonka ba….”

“To menene idan ba hakan ba?”

“Babu komai”

Murmushi yayi,

“To shikenan bari nabarki haka, zanje gareji ana jirana”

“Allah yakiyaye hanya ko inzo in saukeka?”

Girgiza kai yayi yana kallon wayarshi dake hannunshi,

“A’a nagode kiyi zamanki kiyi lectures dinki”

“To shikenan babu matsala”

Atare suka fito daga cikin motar, duk da haka bata barshi ba sai da ta rakashi har bakin gate din fita domin bata son yatafi shi kadai saboda taga tunda suka fito daga motar mutane ke kallonsu especially ma yanmata,

Wata sabuwar sallamar suka sake yi dashi sannan ta koma ciki, Abdul ta samu zaune shida Sabira, Abdul yana yin game awayarshi ita kuma Sabira tana yin waya, zama tayi a kusa dasu,

“Wai yarinyar nan me kike boye mana ne? Kinyi saurayi shine ba zaki fada mana ba?” Ta tsinkayo muryar Sabira da alama tagama wayar,

“Dadi na dake kin iya saka ido…” Inji halimatu,

“Sa ido ko gaskiya, idan tayi tsami dai zamuji”

Shi dai Abdul yana jinsu baice komai ba sai murmushi yake har suka gama,

Akoda yaushe zaka sameta makale da waya suna hira da Aliyu, kuma kusan kullum yana zuwa school ya sameta sai dai bai taba gigin zuwa gidansu ba saboda akwai wani abu da yake hangowa,

Kasancewar yau alhamis har karfe 4 yakai a gareji bai tafi gida ba saboda babu islamiyya, yana kwance akan benci akasan wata bishiyar mangoro Sadiya ta kirashi awaya saboda yau throughout bata jishi ba kwata kwata,

“Yanmata na….” Yafada ahankali,

“Ranka yadade yau ban jikaba kuma ban ganka ba”

Murmushi yayi yana sauraronta har tayi shiru,

“Da sanina ai, sai dare zan kiraki”

“Nidai gaskiya ban yarda ba, kazo inganka”

“Ai ban shirya shan ruwa yanzu ba….”

Dan tunani tayi gameda maganarshi, tabbas yau alhamis to amma me yake nufi? Take kunya ta kamata domin ta ganoshi,

“Kiyi hakuri zan kiraki bayan nasha ruwa, kinji?”

“Naji….” Daga haka ta katse wayar tana dan turo baki saboda jin abinda yace,murmushi yayi ya tashi daga kwancen da yake sakamakon wata mota mai kyawun gaske da yaga an kawo gyara kuma kasancewar akwai aiki da yawa yasa har lokacin babu wanda yaje wurin motar gashi da alama macece ta kawo gyaran,

Tashi yayi ya nufi wurin motar, kamar yadda ya zata kuwa wata yar budurwa ce wacce a haife bazata haura 22 ba tana sanye da bakar doguwar riga tayi rolling kanta da red din veil, bude motar tayi ta fito suka gaisa ta fara yimasa bayanin abinda yafaru cikin turanci duk da cewar ta iya hausa,baiyi magana ba har saida ta gama sannan yace tajira ya duba mata wanda shima da turancin ya fada mata batare da ya kalleta ba, tana tsaye gefenshi yabude gaban motar ya fara dubawa,

Sadiya wacce ta fito daga school kai tsaye garejin su Aliyu ta nufa duk da bawai dama tana zuwa bane amma yau dai tasawa ranta saifa taje ta ganshi, packing motarta tayi agefen motar da Aliyu ke gyarawa wannan budurwar, ganoshi da halimatu tayi shida wata yasanya gabanta faduwa tuni ta bude kofar tafito ta nufesu, har taje kusa dashi bai luraba domin kanshi na kasa yana daure wani noti,

“Sannu da aiki….”

Jin muryarta yasashi dagowa ya kalleta, murmushi ya sakar mata amma ita kuma sai ta daure fuska saboda yarinyar da tagani tana tsaye tare dashi,

“Wa kika tambaya yabaki izinin zuwa nan? Ba nace kiwuce gida ba?”

“Kayi hakuri kawai nazo ganinka ne” Ta amsa masa tana wani shan kamshi, ya fahimceta tsaf shiyasa ya kira daya daga cikin yaranshi yace yaci gaba da duba motar sannan ya kalli halimatu,

“Muje to…”

Batayi magana ba tawuce gaba yana biye da ita abaya tiryan tiryan har wurin motarta, bude mishi tayi ya shiga domin duk hannunshi ya baci da baki, zagayawa tayi itama ta shiga,

Dauke idonta daga kallonsu wannan budurwar tayi sannan ta dubi na lami yaron Aliyu wanda shine ke gyara mata motar ayanzu,

“Waccar din matarshi ce?”

“A’a ba matarsa bace, budurwarsa ce”

Sake kallon wurinsu Aliyu tayi sannan ta dauke kanta,

Sadiya na shiga cikin motar ta dauke kai ko kallon Aliyu ba tayiba ita ala dole fushi take dan taganshi tsaye da mace,

Murmushi yayi ya kalleta,

“Zan shafa miki bakin man nan afuskarki fa”

Batayi magana ba taci gaba da kallon window,

“Idan baza kimin magana ba zan fita inkoma wurin budurwata….” Yace da ita cikin tsokana,

Juyowa tayi ta kalleshi bayan ta kwabe fuska kamar wata karamar yarinya,

“Allah daga yau karka kara kulani tunda abin naka hakane, dama ashe yanmata gareka dayawa shiyasa baka son inzo dan kar insani….”

Dariya taso bashi amma ya danne,

“Ni fa ba hanaki zuwa nayiba yau dinne dai nace karki zo”

“Ehh saboda budurwarka tazo ko?”

“Ohh Sadiya rigima…., to ba saboda haka bane”

“Saboda hakane mana, kar nazo naganku”

“Ni saboda karki zo ki bata min azumina ne yasa nace karki zo amma tunda kinzo shikenan….”

Kifa kanta tayi ajikin sitiyari ta boye fuskarta saboda abinda yafada, dama yasan yanzu zai kashe bakinta shikenan kuma rigima takare,

“Ka fita zan tafi gida”

“Au har kin gama ganin nawa kin fara korata?”

“Ni bahaka bane, kawai dai kafita sai anjima din….”

Murmushi yayi yabude kofar motar zai fita nan idonta yakai kan budurwar da takawo gyaran mota wacce ke tsaye tana jiran Aliyu ganin haka yasa halimatu dakatar dashi…….

 

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

 

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

*23*

 

***Fasa fitar yayi yadawo ya zauna yana kallonta,

“Ya akayi kuma? Ba kin koreni ba kince natafi?”

“Nafasa, kayi zamanka muyi hira saboda ban gaji da kallonta ba….”

Duk da jikinta yabata idanuwansa akanta yake amma haka tayi fuska tana kallon yarinyar dake tsaye ta cikin glass wacce da alama Aliyu take tsaiwar jira,

“Baki gaji da kallona ba?? To shikenan nazauna juyo kiyita kallona”

Murmushi tayi batare da ta kalleshi ba,

“Ehh zan yita kallonka dama…”

“To ina saurarenki”

Shiru tayi tana nazarin wannan yarinyar da ta kawo gyara, ayanda ta kula angama mata gyaran amma tarasa jiran me takeyi wanda ya hanata tafiya, nan taji zuciyarta bata aminta da yarinyar ba sam, kallon Aliyu tayi wanda kansa ke jingine jikin kujera idanuwanshi a lumshe,

“Wai ko azumin ne ke baka wahala?”

Saida ya danyi murmushi sannan ya bude idonsa ya juya ya kalleta,

“Kaji raguwa, an fada miki nima rago ne irinki?”

“A’a Malam daina misali dani, nidinma an fada maka raguwa ce?”

“Raguwa ce mana…”

“Nidai ba raguwa bace”

“To naji, tsakaninki da Allah azumi nawa kikayi?”

Kallonsa tayi nan taga ya dage gira daya yana kallonta alamun son jin abinda zata fada,

“Anki afada din” Ta fada tana dauke kai, murmushi yayi,

“Ni dama nasan baki taba yin azumi talatin ba, sai dai kiyi 21 ko 23 ke har 20 ma kinayi watikil…”

“Ehh naji….”

“To ai kuwa ke raguwa ce tunda hakane”

Kawar da zancen tayi ta hanyar cemishi,

“Malam yau dai katashi a aiki tunda gashi har 5 takusa, muje in kaika gida kafara shirin shan ruwa”

Murmushi yayi mata baice komai ba saboda ya fahimceta, bata so ne tatafi tabarshi da wannan yarinyar shiyasa ta bullo ta haka, bata rai tayi dan kar yace zai musa ma ganin haka yasashi cewa,

“To shikenan bari naje na cire rigar nan na debo kayana inzo mu tafi”

“Muje in rakaka…” Tace dashi bayan ta sake tsare gida,

“To muje”

Batayi magana ba tabude kofar motar tafita, shima fita yayi suka jera, ganin fitowarsu yasa wannan budurwar tahowa wurin Aliyu,

Daure fuska Sadiya tayi ta wani dauke kai kamar taga kashi,

“Am kaga yagama dubawa amma yace wai sai dai inbar motar anan saboda akwai babban gyara da za ayi…”

Murmushi Aliyu yayi mai kamada dariya abinda ya kular da Sadiya kenan domin duk atunaninta wannan budurwar yake yiwa,

“No, kije da motarki kawai inyaso gobe sai ki dawo…”

Tom shikenan, thank you”

“You are welcome”

Daga haka yawuce Sadiya tabi bayanshi, runfar da suke ajiye kayansu yaje ya yacire rigarshi mai kamada lab coat, takalminsa yasa yacire silifas din kafarshi sannan ya dauko littattafansa wadanda yaje dasu, Sadiya ya mikawa wacce ke faman cika tana batsewa kamar zata fashe,

Tana kallonsa ya wuce wurin yaransa, kudi ya ciro daga aljihunsa wanda suka samu yau yabawa kowa hakkinsa sannan ya maida sauran cikin aljihunsa yayi musu sallama ya nufi wurin Sadiya,

Har suka shiga cikin motar bata kalleshi ba sai babbata rai take,

“Wai meya farune? Naga sai fushi kiketa yi”

“Ni babu komai”

“Nifa baki san abinda nake yiwa dariya ba dazu inma akan wannan yarinyar ne, da lokacin da tazo ne taki tayi min hausa to yanzu kuma kila ganinki ne yasata yin hausar”

Duk da bata so yin dariya ba amma sai da ta dara saboda jin abinda yace,

“Kayi kasuwa dai kenan…” Ta fada tana murmushi,

“Awurinki amma ko? Ni ai bana son na burge kowacce mace idan ba ke ba, duk matan duniya ke nafi so, daga ummina sai ke”

Wani farin cikine ya lullube zuciyarta wanda yasa ta kasa magana, driving kawai take yi tana murmushi,

“Ya banji kince komai ba? Kodai baki yarda da abinda nafada bane?”

“Ni na isa? Nayarda mana, nayarda 100%”

“To ai naga ne kamar har yanzu baki huceba” Yace da ita cikin tsokana,

“Da din fushi nayi?”

“Ke dai kawai abar maganar, kinata fushi akan yarinyar da ko kallon fuskarta banyi ba balle nasan yadda take, to kiyi hakuri dai yawuce”

Ita kanta yanzu sai da taji kunya saboda abinda yace, wannan dalilinne yasata yin tsitt sai driving dinta take yi,

Karfe biyar da wurin mintuna 7 suka isa kofar gidan su Aliyu, kallonta yayi yana murmushi ya ciro kudi daga aljihunsa, duk da yasan tafi karfin wannan to amma tunda shi iya karfinsa kenan haka zai bata,

Dubu biyu ya kirgo ya mika mata, martanin murmushin da yake yi ta mayar masa,

“Wannan kudin fa na menene?”

“Baki nayi ko bakya so?”

Murmushi tayi ta karba,

“Bawai bana so bane, dan Allah Aliyu kabar kudinka wallahi inada kudi kullum sai abba ya bani saboda zuba mai a mota da sauran hidindimu”

“Kedai kawai kin raina ne”

“Wallahi ban raina ba, ko kwandala kabani zanyi farin ciki mutukar kyautar daga gareka ne”

Murmushi yayi sannan ya karba,

“Kedai kawai kinyi min wayo”

“Allah ba wayo bane, yanzu dai kaje gida ka huta zan kawo maka kayan buda baki”

“A’a ki hutawarki yau basai kin kawo min ba, wani satin kya kawo min kinji”

Gyada masa kai tayi,

“To shikenan bari naje gida, wallahi ko sallar azahar banyi ba”

Kallonta yayi,

“A school din babu masallaci ne?”

“Da akwai….”

“To meyasa bakiyi ba tun acan?”

“Yanzu idan naje gida ai zanyi, how many minutes nayi nagama”

“Nawane farillan salla ne?” Taji ya tambayeta,

Shiru tayi bata iya magana ba,

“Sunnoni fa?”

Nan dinma shirun tayi masa domin magana ta gaskiya bazata iya jerosu ba, ayanda ya fahimta shima yagane bata saniba amma hakan bazaisa ya sauya soyayyar da yake yi mata ba sannan har gara itama tunda yasan idan yasata zatayi haka kuma yasan ba ita kadai bace,akwai yanmata ire irenta wadanda babu abinda suka sani na daga cikin addini suna da yawa kuma basuda niyyar neman ilmin,

“Sadiya bakya zuwa islamiyya ne?”

Daga masa kai tayi,

“To meyasa?”

“Babu komai” ta sake amsa masa,

“To zaki shiga tamu sai irinka koya miki?”

Kai ta daga alamun ehh,

“To babu damuwa, yanzu kije gida kiyi sallar zamuyi waya”

“Toh”

Dagowa tayi ta kalleshi kamar zatayi magana sai kuma ta fasa, bude kofar motar yayi yafita, ko kadan bata ga alamun canji atare dashi ba, sai da taga shigarsa gida sannan ta tafi.

Washe gari tana class tana lecture yazo, kasancewar ranar friday lecture daya suke yi yasa yajirata har suka fito, yana tsaye jikin motarta yana sanye da farin yadi,

Ta bayanshi tabi da niyyar tsoratashi,

Murmushi yayi ya juya ya kalleta,

“Barka da fitowa”

“Thank u sweetheart” Tafada tana kokarin bude motar, tare suka shiga shi ya zauna a kujerar mai zaman banza ita kuma ta zauna a mazaunin driver,

“Ya kike?” Ya tambayeta yana dan tauna cingum ahankali,

“Lafiya lau, ya gida, ya ummi?”

“Tana gaisheki”

“Ina amsawa”

Bakinta ya kalla yanda itama take taunar cingum,

“Anya ke kuwa akwai ranar da zata fito ta fadi baki tauna cingum ba?”

Murmushi tayi,

“Ai arana ina cin fiyeda biyar infada maka dan ko banci abinci ba dole ne insa cingum abakina”

Murmushi yayi ya kawar da kanshi gefe,

“Hala baki san illarshi ba ko? Allah kirage ci tom idan kuma bahaka ba nidai babu ruwana”

Fuskantarshi tayi ta zuba masa ido,

“Fada min illar tasa naji kaga idan naji kwakkwaran dalili ne sai indaina”

Gemunshi ya shafa yana murmushi batare da ya kalleta ba,

“Ba yanzu zan fada miki ba”

“Why? Ni dai kafada min”

Juyawa yayi ya kalleta,

“Idan kin matsa sai infada mikin amma wallahi zakiji kunya”

Kawar da kanta tayi tana kunkuni,

“Yanzu yaushe zaki fara zuwa makarantar?”

“Duk ranar da kace”

“To kifara zuwa gobe da misalin karfe 4 idan kuma kika makara zakisha bulala”

Murmushi tayi batare da tace komai ba,

Hannunta ya kalla ya kawar dakai,

“Meyasa bakya son yin kunshi ne Sadiya?”

Hannuwanta ta jujjuya tana kallo kafin ta kalleshi,

“Wallahi haka kawai bana so, ni kawai nafi ganewa insa jan farce”

Murmushi yayi ya kalleta,

“Abubuwa guda uku suna rikewa mace darajarta, nafarko yawan yin lalle, na biyu saka kwalli, na uku kiyaye yawo babu takalmi”

“Daraja kamar yaya? Nifa lallen ne kawai bai yimin ba”

“Baki san darajar mace ba?”

Ganin kalar murmushin da yake yi yasata shan jinin jikinta,nan tayi kicin kicin da fuska shi kuwa Aliyu me zaiyi idan ba dariya ba….

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

 

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

 

_Dedicated to Fiddausi Sodangi_

 

*24*

 

***Ganin yanda take babbata rai abin yabashi dariya,

“Ki saki fuskarki ni ba komai zance ba, dama dai kawai zan fada miki abinda baki sani bane amma tunda bakya son sani shikenan….”

Batare da ta kalleshi ba tace,

“To ni na hanaka kafada ne?”

“To ai wannan ciccin maganin da kike yine yake tsoratani, kin san fa ni tsoronki nakeji”

Sai lokacin tayi murmushi ta kalleshi,

“Tsorona fa kace, me nayi da zakaji tsorona?”

Kallonta shi dinma yayi suka hada ido,

“Haka kawai,nifa ko auren ma akayi sai yanda kika yi dani, idan kince ayi sai ayi idan kince kar ayi shikenan sai in hakura…”

“Me…?”

“Wai duk wani abu da ya shafi gida”

Murmushi tayi tana jijjiga kai,

“To in fada miki ko inyi shiru?”

“Fadi mana, ai kai baka kunyar fadin komai”

Dariya yayi,

“Nine marar kunyar halima? Akan ina baki ilmin abinda baki saniba? Kaina fa nake gyarawa, ni ban taba ganinki da kunshi bane alhalin kuma kunshin nan yana da mutukar amfani saboda babu abinda yakaishi maintaining din dumin jikin mace,duk da ban taba,tab’a jikinka ba amma nasan nawa yafi naki dumi….”

“Sai me kuma?” Ta fada cikeda borin kunyar abinda yafada,

“Sai kika cuceni domin zaki hanani nutsuwa yadda ta kamata”

“Ehhh da yake jikinka ne ba”

“Da nawaye? Nawane mana”

“To naji, koma jikina kankara ne saboda tsabar sanyi babu ruwanka”

“Ya babu ruwana? Ai komai naki nawane kinga dole ai in tattalashi”

“Tattalashi dakyau…”

“Yawwa to ki rinka yin kunshi duk sati, kinga budurwata ta da muslima koda yaushe cikin kunshi take saboda tasan ina so”

“To ina ruwana da ita?” Ta fada a kufule saboda jin ya ambaci muslima,

Murmushi yayi ganin ta kawar da kai gefe,

“Hali dubu amma duk na arziki ne guda dayane na tsiwa, to yi hakuri nidai indai nine koma dai yaya kike naji na gani ina so,kuma muslima ni harma namanta kamanninta shikenan?”

Sai lokacin tayi murmushi,

“Bawani har yanzu kana sonta, kai da ka ringa jinya saboda ita gaka baban soyayya”

Murmushi yayi,

“To ai ke baki san ya zanyi ba da ace kece”

“A’a ni karkayi wannan kwatancen dani dan nasan ko jinyar minti daya baza ka yiba”

“Tab kece dai baki saniba, ai da ace ke narasa da tuni zuciyata ta jima da bugawa kila sai dai asa min ta roba”

Daga shi har ita dariya sukayi saboda abinda yace,

“Dama akwai ta roba ne?”

“Ehh mana, idan ma babu za afara daga kaina”

“Hakan ma bazai faru ba, daina fada”

Kallonta yayi,

“Bakya son inmutu kenan…”

“Bana so”

“Saboda me?”

“Saboda na fiso muyi aure mu hayayyafa”

“Hmmmm zaki haihu kam da yawa halima, duk shekara da yardar Allah”

Shiru tayi masa domin idan tayi magana yanzu zai fada mata abinda zai sata kasa hada ido dashi, agogon hannunta ya kalla yana murmushi domin yasan dalilin da ya hanata kara magana,

“Duba min karfe nawa”

“12 dai dai”

“To bari nagudu haka, kullum nazo wurinki sai na makara”

Murmushi tayi sannan ta sunkuyar da kanta,

“Ai ka iya hirane shiyasa,

“Wai dagaske?” Ya fada yana kallonta,

“Dagaske mana…”

“To ai kin fini iyawa ranki ya dade”

Murmushi tayi batare da ta kalleshi ba,

“Shikenan kaje katafi nasan yanzu tana can tana jiranka”

“Wacece?” Ya tambayeta yana kallonta,

“Yarinyar da ta kawo maka gyaran mota jiya”

Sai da ya danyi dariya saboda jin abinda ya fito daga bakinta,

“Wallahi ni harma namanta da ita tun ajiyan ashe ke abin na ranki?”

“Taya ni zan manta bayan ana kokari akwace min abinda nake so”

“To ai babu mai kwace miki ni saboda nakine ke kadai, sai yadda kike so zakiyi dani, ki saki ranki bakida matsala indai akaina ne,bari inje, nabarki lafiya sadiyayye na”

Jin sunan da ya kirata dashi yasata fara dariya, kofar motar yabude yafita domin yasan idan zasu kwana awurin hirarsa da Sadiya ba zata kare ba,ta cikin glass din motar take hangoshi tana murmushi har ya bacewa ganinta.

Ranar asabar da misalin karfe 4:30 tashirya ta tafi makarantar islamiyyar su Aliyu kamar yadda ta alkawarta masa, abakin gate ta tsaya ta kirashi, mintuna biyar tsakani sai gashi ya fito, tun yana nesa take kallonsa, farin yadi ne ajikinsa babu hula ba kadanba yayi kyau,

Gaban motar yabude ya shiga yana rikeda bakar leda,

Kallon juna sukayi na tsawon minti biyu sannan halima tajanye idonta, murmushi yayi,

“Yan mata na kin makara fa”

“Yi hakuri ranka ya dade bazan kara ba”

Murmushi yayi ya mika mata ledar hannunshi nan takarba ta bude, littattafai tagani aciki wadanda suka hadar da hadisi, fiqhu, da kuma tauhid,

“Dama ai kinada alqur’ani ko?”

Daga masa kai tayi alamun ehhh,

“To zamu shiga ciki ko?”

“Toh” shine abinda tace kawai ta zare key din motar suka fito, sanye take da bakar gown tayi rolling da mayafin rigar, gaban wani aji sukaje yace ta jirashi anan, daga Inda take tsaye tana iya hangoshi yana rubutu a allo, sai da yagama sannan ya fito,

A barandar gaban ajujuwan suka zauna,da kananan abubuwa suka fara irinsu tsarki, farillan alwalala da sunnoni sannan ya karanta mata fatiha domin tasan yanda ake karantata daki daki acikin salla, ita kanta saida taji dadin karatun nan domin ya tuna mata abubuwa da dama wadanda ta manta kasancewar tun tana karama rabonta da islamiyya, kuskuren da wasu iyayen keyi kenan sai afi bawa yaro karatun zamani fiyeda na addini alhali wannan ba dabara bace, kowanne da mazauninsa amma na addinin shine akan gaba domin shine zai amfani mutum har a lahira,

Sallama tayi masa ta tafi tana cikeda farin ciki, koda ta koma gida ma bitar abubuwan da ya koya mata tarinka yi da daddare sai wurin 10 sannan ta hakura ta dauki laptop dinta ta kunna wani American film da Abdul ya tura mata, har 12 takai tana kallon sannan ta hakura ta kwanta,

Kullum da yamma take zuwa makarantar bata fashi sai alhamis da jumma’a ne kawai take zama agida kuma alhamdulillah daga lokacin da tafara zuwa makarantar wato sati uku zuwa yanzu ta san abubuwa da yawa,gashi Aliyu baya jin kunyarta duk abinda karatu ya biyo ta kansa shafawa idonshi toka yake yi yafada,shiyasa wani lokacin suna karatun suna fada da haka zasu rabu, wani sa’ilin kuwa sai sunyi fada yafi sau biyar kafin agama karatun,

Yau ma hakance ta kasance, tana sanye da doguwar riga ja kamar yadda ta saba ta nada bakin mayafi,saida ta jirashi yashiga wani aji ya fito sannan yazo ya zauna kusa da ita,

Littafinshi ya bude na fiqhu itama ta bude, satar kallonta yayi saboda zasuyi karatunne akan babin da yake magana akan abubuwan da suke wajabta wanka, saida ya dauki tsawon minti biyar yana nazarin ta inda zai fara, zuwa can dai ya daure yafara bayan yaci magani danma kar tasamu damar kawo wargi acikin lamarin, saida yagama lissafowa sannan ya jefa mata tambayar da ta rikitata domin ji tayi kamar kasa ta tsage ta shiga dan kunya, nan ta daure fuska itama,

“Menene banbanci tsakanin maniyyi da maziyyi da wadiyi?”

Shiru tayi masa kuma taki kallonsa, sau uku yana maimaitawa tayi masa shiru, sai lokacin ya kalleta,

“Malama idan baki saniba kawai gara ki ce baki saniba akan kiyi min shiru”

“Ni ban saniba..” Ta amsa tana turo baki,

“To assignment kije ki samo banbancinsu da siffar kowanne acikinsu”

“A ina zan samo?”

“Oho, aduk inda yadace”

“Nidai dan Allah kayi hakuri kawai ka fada min babu inda zan samo wallahi”

“To ba naga kamar bakya son infada mikin ba? Shiyasa gara ki samo da kanki”

Shiru tayi ta dauki wayarta ta soma browsing, duk da tagani amma bata jin zata iya fada masa saboda kunya,

Shikam bai kara bi ta kanta ba yasoma yi mata bayani dalla dalla akan kowanne daga cikinsu da kuma dalilan dake sanya fitarsu domin wajibi ne kowanne mai hankali yasansu kuma yasan yanda hukuncinsu yake,

Har kalar kowanne acikinsu da yanayin yanda yake fita saida ya zayyano mata, ita kam bata um bare uhm uhm asali ma tallafe kumatunta tayi da tafukan hannunta tana sauraronsa acikin zuciyarta tana fadin,

“Wallahi Aliyun nan bashida kunya, ko kunyata ma bayaji”

“Babu tambaya?” Ta jiyoshi yana tambayarta, shiru tayi masa har saida ya maimaita sannan afusace ta amsa da,

“Babu…”

Kallonta yayi,

“To ai basai kinyi min bala’i ba, tunda babu shikenan”

“Shikenan din” Tafada bayan ta kawar da fuskarta gefe, bai kara magana ba har wata daliba tazo wurin tana sanye cikin uniform yar budurwa da ita amma ahaife bazata kai halima ba,

Durkusawa tayi gaban Aliyu tace,

“Malam kaine damu”

“To Rashida jeki ina zuwa”

Tashi tayi tawuce, kallon halimatu yayi nan yaga tana raka yarinyar da harara, murmushi yayi yana kallonta domin kishinta ita kam dabanne sam bata kaunar taga wata mace tana rabarsa yanzun nan zata cika tayi fam kamar zata fashe, yanzun ma aciken take fam,

“Idan kin gane komai baki da tambaya shikenan bari intafi ajin yan matan can suma in dora musu” yafada cikin son ya tsokaneta,

Shiru tayi masa bata tanka ba ta kalleshi, shima din ita yake kallo ganin taki magana yasashi kwantar da muryarsa kasa kasa cikin sigar rarrashi,

“Halimatu na meya farune? Nayi miki laifi ko? Kiyi hakuri kinji, ni wannan koyarwar ma dan bakya kusa dani ne amma muna yin aure zan daina zuwa, zan zauna agida kawai inyita kallonki”

Sunkuyar da kai tayi tana murmushi, ganin haka yasashi tashi tsaye yana kallonta fuskarsa dauke da murmushi domin lamarin na halima sai yana yimata dabara,da wayo da wayo yatafi yabarta bayan sunyi sallama, littattafan ta kwasa tawuce gida.

Washe gari kam batayi niyyar zuwa makarantar ba saboda ciwon marar dake damunta, ko school ma dakyar taje ta dawo ta kwanta bayan tayi wanka tasha ruwan tea,

Karfe 5 saura Aliyu ya kirata, dauka tayi tanata faman kukkunbura kamar wacce yayiwa wani laifin,ita bata san daliliba duk lokacin da take period sai tarinka jin haushinsa kuma shi kadai koda kuwa baiyi mata laifin komai ba,

“Yau ba zakizo makarantar bane? Idan fa kina fashi karatun naki bazai albarka ba”

Kamar wacce take jira tafara masifa saboda jin abinda yafada, bai kulata ba sai dariya ma da yake yimata, kashe wayar tayi ta tashi tashiga wanka tafito ta shirya, doguwar riga ta atamfa green colour ta saka ta nada babban gyale tafito, a kofar kitchen ta samu umma itada baba tabawa suna aikin abincin dare,

“Sadiya ina kuma zakije keda bakida lafiya? Ko har kinji sauki?” Inji umma,

“Umma islamiyya zan samu in leka tunda na danji karfin jikina”

“Gara kam adan fita ai kwanciyar batada dadi” Inji baba tabawa,

“Hakane kam baba tabawa, shikenan bari inje”

Adawo lafiya sukayi mata tatafi, tun ahanya taga yana sake kiranta nan ta daga tace gata nan ahanya, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya katse wayar,

Ko minti goma batayi ba ahanya ta karasa makarantar, fitowarshi kenan daga aji yana kan baranda yana wanke hannayenshi wadanda suka baci da chalk, kin fitowa tayi ta zauna tana kallonsa daga cikin motar, handkerchief yaciro daga aljihunsa ya goge fuskarsa sannan yakarasa wurinta,kofar ta bude amma bata fitoba dole sai shine ya karasa ya tsaya ta gefenta yana kallonta yana nazarinta, dakyar tafito sukaje wurinda suka saba zama suka zauna,

Da Qur’ani suka fara ya biya mata suratul Qadr,mika mata qur’anin yayi dan ta karanta yaji taki karba, rabuwa da ita yayi ya ajiye ya dauki hadis shima ya dora mata guda daya,

Wannan kam saida itama ta biya da kanta sannan ya dauko fiqhu, babin da yake magana akan alwala da yasoma karantawa,zuba masa ido tayi tana kallonsa aranta tana cewa shi dai Aliyu yasan komai kenan, har yayi yagama batayi ko tari ba ganin sun cinye lokacin yasa shi barin karatun haka yace sai gobe zasu cigaba,

Tare suka jera zuwa wurin motarta, tana kokarin shiga ya dakatar da ita,

“Na baki qur’ani kiyi karatu amma kinki karba alhali kina cikin lalura, yawancin mata kuna yin kuskure, lokacin da kuke al’ada sai kuyi biris da karatun alqur’ani da tasbihi bayan kuma ba acikin tsarki kuke ba, ba dole shaidanu su rinka kusantarku ba?”

Sai lokacin ta jiyo ta kalleshi,

“To ba ance babu kyau taba alqur’ani ba idan anayi?”

“Kinji ai, shiyasa kiyita min masifa kamar nine na dora miki yinsa, ashe bakya karatun alqur’ani lokacin, cikakken alqur’ani izu sittin shine babu kyau adauka idan ana period amma zaki iya daukar wani izifi daga cikinsa kuma zaki iya daukar sauran littattafai domin yin azkar da sauran addu’o’in neman tsari”

Dora kanta tayi kan murfin kofa tana murmushi saboda jin yace wai tanayi masa masifa duk lokacin da take cikin wannan halin,

“Shikenan kije kitafi gida, zamuyi waya”

“To nagode”

Bata yarda ta sake hada ido dashiba ta shige cikin motar tayi waje.

 

_Fatan alkhairi gareku fans masu bibiyar dan asali,kuyi min afuwa kwana biyu kun jini shiru kun san jiki da jini amma alhamdulillah komai yanzu ya daidaita, nagode sosai da kulawarku especially wadanda suka kirani da wadanda suka tura min da text nagode sosai Allah yabar zumunci. Gaisuwa ga Zee Darki tnx for ur support._

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

 

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

 

_DEDICATED TO FIDDAUSI SODANGI_

 

*25*

 

***Lokacin da ta koma gida ba karamin dadin ganinta umma taji ba saboda tasan zata karu mutuka sakamakon zuwa makarantar da take yi,

Zama tayi akusa da umma wacce ke kokarin tashi domin zuwa kitchen karasa girkin da takeyi,

“Umma ba agama tuwon bane? Wallahi yunwa nake ji”

“To ba dole kiji yunwa ba tunda bakya son cin abinci, ankusa saukewa sai kici”

Daga haka umma tatashi tafita ita kuma ta mike akan doguwar kujera tana kallon tv, littafin azkar ta dauka tana dubawa tanayi tana tunanin Aliyu, shi dai tasan kawai kallonta yake yi tun dadewa amma babu abinda bai saniba, juyawa tayi ta gyara kwanciyarta tare da fadin,

“Uhmmm Aliyu manya ahaka dai silent dashi ashe ta ciki na ciki”

Cigaba da kwanciyarta tayi har umma ta shigo mata da tuwon shinkafa miyar taushe, tashi zaune tayi tana yiwa umma sannu, sai da ta ci abincin ta koshi sannan ta lallaba ta koma daki ta kwanta.

Tun daga ranar bata sake fitaba domin ko school sai da tayi kwana biyu bataje ba, tsakaninta da Aliyu sai dai waya domin bata zuwa makarantar,

Yau satinta 1 rabonta da Aliyu, bayan ta fito daga makaranta direct garejinsu ta wuce yana zaune saman benci shi kadai yana daura notina jikin wani karfe tazo, dan neman tsokana horn tafara matsawa taki fita, jin ancika masa kunne da kara yasashi tashi ya nufi wurin, nan ya fahimci Sadiya ce, murmushi yayi ya leka ta window din saitinta bayan ta sauke glass din,

“Wata sabon gani, sai yau kika shirya ganina yanmata?”

Murmushi tayi batare da ta kalleshi ba,

“Yau dinma dai kawai cewa nayi bari in ratso in gaisheka”

“To nagode, ya kin zuwa makaranta? Ko har karatun ya isheki ne?”

“Wane ni, abinda ko quarter banyi ba”

“Atoh nasani ko kinsha karatun har kin koshi”

“Sam bahaka bane”

“To yaya ne?”

Ya tambayeta yana kallonta fuskarsa dauke da murmushi, kafin tayi magana idonshi yakai kan kitsonta wanda ta tufkeshi ya fito ta cikin dan kwali,

“Wai ban hana kitson nan na rubber attach bane?”

Saurin shafa kanta tayi tana kallonsa,

“Bafa shi bane…”

“Kin zaci ban sanshi bane? Allah shine akanki”

“To kitsonne haka sai injishi wani sungul gashi kuma baya kyau”

“Shiyasa kike sawa na attach ko? Sadiya kina son muyi fada?”

Girgiza kai tayi,

“To kidaina cudanya da ire iren kayan nan na zamani masu raunata imanin mutum”

“Insha Allah bazan kara ba”

“To shikenan yawuce, yanzu me kika kawo min?”

Murmushi tayi ta rufe idonta da hannunta daya,

“Ai baka cemin kana son wani abuba da nakawo maka”

“Ai basai na fada ba indai kinyi niyyar bani”

“To zan kawo maka next time”

“To shikenan ina jira, ni yanzu me kike so inbaki?”

“Babu komai,nagode,dama ganinka nazo yi”

Hannunsa yasa acikin aljihun wandonsa ya ciro gidan cingum na orbit ya mika mata,

“Bance kuma kiyita taunarshi ba”

Karba tayi tana murmushi,

“Tun ranar da ka hanani ai nadaina, tsotse zakin kawai nake sai inyar”

“Da dai kin taimaka min”

Murmushi tayi tayiwa motar key,

“Kaje kaci gaba da aikinka sai munyi waya”

“To shikenan nagode”

Matsawa yayi yabata hanya tawuce tana daga masa hannu.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya kullum kara son juna suke da kaunar juna, sun shaku mutuka domin kullum suna tare a makaranta ko a islamiyya, bangaren karatun da yake koya mata kuwa abin sai hamdala domin tana samun cigaba mai tarin yawa kasancewar yanzu har tafara iya hada baki da kanta ta karanta abu wannan dalilin ne yasa akowacce rana take jin sabuwar soyayyar Aliyu tana shiga cikin zuciyarta domin ya kawo mata sauyi cikin rayuwarta kuma yayi mata abinda babu wanda yayi mata tunda ya bata ilmin da zata bautawa mahaliccinta dashi,

Kasancewar yau sunada group discussion da zasu gabatar a makaranta saboda nan da yan kwanaki zasu fara jarrabawar fita, kamar ba zata biya ta islamiyyar ba amma ta daure ta fara biyawa saboda bata san lokacin da zasu dauka suna discussion din ba ta yiyu har atashi daga islamiyyar bata dawoba shiyasa ta zabi ta fara biyawa koma dai yayane su danyi karatun inyaso saita wuce,

Purple din gown ta saka ta danyi kwalliya sama sama sannan tafita bayan ta feshe jikinta da turare,

Agurguje ta biya ta part din abba tayi musu sallama tawuce, lokacin da taje makarantar misalin karfe 4 na yamma dan haka sai lokacin ma daliban ke zuwa, Aliyu ta hango ta mirror yana zuwa shiyasa ta saki murmushi ita kadai,

Budewa yayi ya shiga ya zauna bayan yayi mata sallama amsawa tayi tana kallonsa, jallabiya yasa milk colour da bakin jeans da hula,

“Kayi kyau…” Tace dashi tana murmushi,

“Na hanaki saka turare mai karfi baki yarda ba ko? Shikenan”

“Kayi hakuri bazan karaba fa”

“Kullum ai haka kike cewa”

“Allah daga yau bazan karaba,yanzu dai ka dora min karatun nan da sauri school zan shiga”

“Qur’ani kadai zan biya miki sauran sai ki dorawa kanki da kanki”

Murmushi tayi ta fito da littattafan daga cikin jaka,

“Yi hakuri sweety, kar kamin haka mana”

“Ai ba laifi kikayi ba, gani nayi idan ina dora miki kunya kikeji kuma muyita rikici dake shiyasa nadaina”

“To ai kai dinne ko kunyata bakaji fa”

Kallonta yayi idonshi cikin nata,

“Kunya? Waya fada miki ana kunya a neman ilmi? Nana A’isha Allah yakara mata yarda tace “Allah yajikan matan madina domin basa jin kunya awurin neman ilmi” to sai kece zakiji kunya?”

“To naji duk ba wannan ba nidai yanzu ka biya min intafi”

“Ehh zan biya miki amma badan halinki ba, last karatunmu anan wurin kamar ki dakeni dan kawai na karanta miki babin da yake magana akan Haida”

“To ba nabaka hakuri ba, ko baka hakura ba?”

“Na hakura”

Karatun ya bibbiya mata, duk littattafai hudun da sukeyi sai da ya dora mata sannan sukayi sallama tatafi,

Lokacin da ta fara exams kuwa basu samu damar haduwa ba domin rashin lokaci,sati biyu basuga juna ba har ranar da ta gama sai aranar ne Aliyu ya shirya yimata zuwan bazata domin bai taba zuwa gidansu ba,

Tana bedroom din umma tayi d’ai d’ai tana bacci karar wayarta ya tadata,ganin Aliyu ne ta saki fuskarta,wani tsalle ta dira daga saman gadon jin wai yau yana kofar gidansu,

Powder dake kan mudubin umma ta dauka ta shafa a fuskarta ta dauko hijab din umma acikin drewar ta saka ta fita,

Yana tsaye jingine da jikin gate din gidan sai faman bin unguwar yake da kallo domin yanayinta kadai ya isa sanar dakai suwaye mazauna cikinta, fitowa tayi tana kallonsa, sanye yake da yadin kufta ruwan toka da hula, murmushi suka sakarwa junansu atare domin bai taba ganinta da hijabi ba sai yau,

“Dama kina saka hijabi?” Ya tambayeta cikin tsokana,

“A’a, na ummana ne”

Murmushi yayi mata,

“Yayi miki kyau to ai”

“Nagode, mu shiga ciki”

Basu kai ga shiga ba motar abba ta kunno kai,shida driver Malam Kamilu, nan mai gadi ya wawake gate din motar Abba tawuce ciki,

“Ranka yadade mai yakawo wannan yaron wurin halima?” Malam kamilu yace da abba,

” Malam kamilu wafa? Ko yaron dake tsaye da Sadiya?”

“Shifa Allah yakara maka yawan rai, ai wannan yaron baida asali baida uba wasu ma suna rade radin uwarsa karuwa ce, to kaga kuwa indai hakane gara arabasu da Sadiya karya lalata maka ita”

Jin abinda Malam kamilu yafada yasa Abba hawa, nan ya cika yayi fam domin bai taba ganin Sadiya tsaye da waniba sai Abdul to amma yau ina ta samo wannan kuma?

Yana fitowa daga cikin dingimemiyar motarsa yayiwa mai gadi alama da yazo, da gudu ya garzayo yazo ya durkusa,

“Kira min Sadiya ita da wancan yaron da yazo wurinta”

Da sauri mai gadi ya tafi kiranta dai dai lokacin da ita kuma suka shigo itada Aliyu wanda dakyar ya yarda yashigo domin shi ada kawai su gaisa yajuya shine niyyarsa amma ta dage sai ya shigo ciki,

“Hajiya kizo keda bakonki inji Alhaji” Inji mai gadi, murmushi tayi bata kawo komai aranta ba domin tasan Abba yana girmama duk wani abu wanda take so,haka kuma yana kaunar duk abinda take kauna,

Durkusawa Aliyu yayi yagaida Abba Wanda fuskarsa take a mutukar daure dan dakyar ma ya amsa gaisuwar,

“Kai wanene mahaifinka?”

Shiru Aliyu yayi yasake yin kasa da kansa wanda yasoma sara masa,

“Nace kai dan waye, wanene mahaifinka kuma ina ne asalinku?”

“Abba mahaifina Allah yayi masa rasu…”

Wata tsawa Abba ya daka masa wacce tayi mutukar razanashi ta hanashi karasa abinda yayi niyyar fada,

“Ya isa haka domin na fahimci kai kanka baka san inane asalinkaba kuma baka san waye mahaifinka ba dan haka babu kai babu yata, karka kuskura nasake ganinka tareda yata….” Yakarasa maganar cikin kakkausar murya sannan yajuya ya kalli Sadiya wacce tayi suman tsaye domin bata iya koda motsi saboda jin abinda Abba yayi,

“Wuce ki shiga gida ko na sabar miki awurin nan….”

Tun kafin ya rufe bakinsa tayi hanyar cikin gidan da sauri har tana yin tuntube yayinda shikuma Abba ya nunawa Aliyu hanyar fita da hannunsa alamun yatashi yafice, jikinsa babu kwari idanuwansa jajur yatashi ya kama hanyar fita jiri yana daukarsa…….

 

_Fatan alkhairi gareki Xarah b~b,ur comments is amazing always._

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

 

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

 

 

_DEDICATED TO FIDDAUSI SODANGI_

 

 

*26*

 

***Tana jin wani nannauyan abu yana kai komo acikin kirjinta zuwa tsakiyar kanta, da haka ta samu ta karasa ciki,

Jikin umma ta fada wacce ke tsaye tsakiyar falo da remote a hannunta tana kokarin kamo channel,

Da mamaki umma ta dagota tana kallonta bayan sadiyan ta saki wani kuka mai cin rai,

“Sadiya…, meya faru?” Umma ta tambayeta arude,

Wasu tagwayen hawaye ne suka sauko saman kuncinta atare,

“Umma Abba ya rabani da Aliyu…”

“Me Aliyun yayi?” Umma ta bukata,

“Wai bashida uba, yace daga yau kar ya sake kulani”

Janta umma tayi ta zaunar da ita saman kujera tasoma rarrashinta,

“To kiyi shiru, zanje insamu abban naki inbashi hakuri insha Allah zai yarda da tarayyarku da Aliyu, kiyi hakuri kinji…”

Dakyar ta samu ta tsayar da hawayen ta soma share hawayenta,

Saida umma ta samu nasarar sanyaya mata zuciyarta sannan ta tafi part din Abba wanda yake acike fam da bacin ran abinda halima tayi,

Zama umma tayi bayan ta gabatar masa da abinci, batare da ya ko kalli abincin ba ya kalli umma azafafe,

“Hajiya binta tun yaushe yarinyar can ta soma hulda da wancan maragurbin yaron?”

“Alhaji dan Allah kayi hakuri mubi komai a sannu, dan Allah ka sanyayawa zuciyarka mubi abinnan asannu”

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kalleta yana jijjiga kai,

“Ni kawai na rabata da wannan yaron, karta kuskura in kara ganinta dashi idan ba hakaba zan dauki mummunan mataki akansa”

“Nidai dan Allah Alhaji yanzu mubar maganar nan kaci abinci inyaso sai mu tattauna zuwa anjima…”

Baiyi magana ba yaja flate zai debi abincin amma umma tayi saurin karbewa ta mike domin zuba masa.

Kai kawo kawai Sadiya keyi acikin dakinta sai faman kiran wayar Aliyu takeyi amma akashe, ji take kamar ta dora hannu aka ta runtuma ihu,

Ta kira wayar yafi sau 50 amma duk dai amsar guda dayace wayar akashe take, fadawa saman gado tayi tafara kuka tana shassheka domin bata san yanda Aliyu zai dauki wannan abun da mahaifinta yayi masa ba,

Abangaren Aliyu kuwa komai yayi masa muni domin baki kirin yake kallonsa, hankalinsa idan yayi dubu to duk atashe yake domin ko a mafarki bai taba tsammanin zai fuskanci irin wannan matsalar daga iyayen Sadiya ba,

Gefen kansa inbanda sarawa babu abinda yake yi masa ga wani uban jiri dake daukarsa, acikin wannan yanayin ya karasa gida, ganin Ummi na zaune tsakar gida yasashi daidaita nutsuwarshi yayi sallama, ganin yanayinsa ya fadarwa da ummi gaba nan ta soma tuhumarsa,

“Aliyu yadai? Ya naganka abirkice?”

“Ummi…..,kaina ke ciwo”

Yabata amsa dakyar tareda shiga dakinsa,

Da sauri Ummi tatashi taje dakinta ta binciko masa guntun maganin ciwon kansa wanda Malam lawan ya karbo masa kwanakin baya, acikin cup ta jika masa ta bishi cikin dakin,

“Tashi kasha Aliyu, sannu….”

Babu musu yatashi ya karba yasha, Ummi ta shafe masa goshinsa da ruwan maganin, komawa yayi ya kwanta yana mai lumshe idonsa, kalmar innalillahi wa inna ilaihir raji’un yaketa maimaitawa tun dazu acikin zuciyarsa da haka har yaji sassauci acikin ransa, alqur’aninshi ya mika hannu ya dauko yabude ganin haka yasa Ummi tashi tafita daga cikin dakin, duk da ba gani yakeyi sosai ba amma haka ya fara karanta suratul maryam da daddadar kira’arsa,har magrib tayi yana daki yana karatun aqur’ani, yayi iya iyawarsa don ganin ya hana Ummi fahimtar halin da yake ciki, saida yaji ana kokarin shiga salla sannan yatashi yafito har lokacin idanuwansa kamar barkono suke saboda tsananin jan da sukayi,

Alwala yayi yafita zuwa masallaci, koda aka idar da sallar ma bai fitoba zamansa yayi acikin masallacin yana sauraron tunatarwar da Malam yakeyi kamar yadda yasaba duk bayan sallar magrib zuwa isha,hakan ba karamin tasiri yayi ba wurin rage masa damuwar dake damunsa,

Bai samu damar komawa gida ba sai misalin karfe 9 nadare, dakin ummi ya wuce kai tsaye nan ya isketa tana kallon labaran kasa a yar tsohuwar tv dinta, zama yayi kusa da ita, kwanon abincin ta jawo zuwa gabansa ta ajiye tana kallonsa,

“Gadanga yaufa baka ci abinci ba, ga abincinka nan”

Sanin idan yayi mata musu tana iya gano yana cikin damuwa yasa shi bude abincin wanda shine ya girka da rana, shinkafa ce da taliya jalop tasha kifi da alayyahu, tashi yayi ya wanko hannunsa sannan ya dawo yazauna yafara cin abincin bayan yayi bisimillah, tura abincin kawai yake bawai dan yana yimasa dadiba danma yar hirar da sukeyi da ummi da kuma labaran da yake kallo yana dan taimaka masa hakanne yasa shi cin rabin abincin sannan yarufe ya fita ya wanke hannunsa ya dawo,

Har karfe 11 yana dakin ummi suna hira saida aka rufe gidan tv din sannan yatafi dakinsa, shirin bacci yayi ya kwanta nan bacci yace bai san zance ba, damuwar dazu ce tasake bijirowa cikin zuciyarsa, kamar zaiyi hawaye haka yakeji, gaba daya sai yaji soyayyar ma tafice masa arai, har misalin karfe 1 yakai cikin wannan hali ganin abin ba mai karewa bane yasashi tashi yafita zuwa tsakar gida yayi alwala yadawo daki yafara sallar nafila wanda bashi yayi bacci ba saida yayi sallar asuba.

Yanda Aliyu baiyi bacciba haka Sadiya itama bata runtsaba, wani zubin tayi kuka tayi kuka ta share hawayenta, haka ta raba dare tanayi duk da rarrashin da umma tayi mata amma duk da haka hankalinta ya kasa kwanciya domin bata san halin da Aliyu ke cikiba yanzu.

Washe gari da safe tunda tayi wanka ta shirya take son fita domin taje taga halin da Aliyu ke ciki amma tarasa hanyar fita domin abba yana gida, alla alla ta rinka yi yafita amma bai fita da wuriba sai wurin 12 saura nasafe, ko breakfast batayi ba tana jin fitar Abba itama tafito ta fita bayan ta sanarwa da umma,

Har lokacin da taje gidansu Aliyu wayarshi akashe take bai kunna ba, rasa yadda zatayi tayi domin bata son shiga gidan daga karshe dai haka ta daure tayi ta maza ta shiga,

Tana shiga da Aliyu tafara yin arba yana zaune kan benci yana wanki gefensa kuma cup ne da lemon juice aciki yana dan kurba jifa jifa, jin sallamarta yasashi dagowa ya kalleta yana mai amsa mata sallamar, duk jikinta asabule haka take tafiya amma ganin yanayinsa yasata samun kwarin gwiwar tunkararsa,

Zama tayi kusa dashi,

“Kawo in tayaka…”

Murmushi yayi ya kalleta bayan ya cire hannunsa daga cikin ruwan kumfar da yake yin wankin,

“Kajita sai kace iya wankin tayi”

“Au wai nidin kallon wadda bata iya komai ba kake yimin”

“Gaskiya”

“Shikenan tunda kace haka, ina mama? Bari inshiga in gaidata”

“Duba tana ciki tana aiki”

Tashi tayi ta shiga ciki nan tahango ummi a lungun kitchen tana dama kunun gyada,durkusawa tayi har kasa ta gaida ta, cikeda fara’a akan fuskar Ummi suka gaisa tana tambayar halimatu dalilinta na dauke kafa da zuwar mata, murmushi kawai halimatu tayi batace komai ba, cigaba da zama tayi wurin ummi harta gama dama kununta sannan ta tayata daukoshi zuwa daki,

Sugar ummi tasaka acikin kunun ta zuba musu acikin cup tafita ta kaiwa Aliyu sannan tadawo wurin Sadiya,duk da hirar da Ummi kemata sam ta kasa sakewa suyi hirar kamar yadda suka saba, Aliyu yana jiyosu daga inda yake,

Tana nan zaune har Aliyu ya kammala wankin ya shanya yashiga daki ganin haka yasata yiwa ummi sallama tafita,

Bin bayanta Aliyu yayi zuwa kofar gida anan suka ja tunga suka tsaya, gabanta dukan uku uku yafara domin bata da masaniyar abinda zai fito daga bakinsa a lokacin.

 

_Sakon fatan alkhairi ga masoyana, ina mai kara baku hakuri sakamakon jina shiru da kukayi,ina mutukar godiya gareku musamman wadanda suka kirani suka dubani da wadanda suka tura min da sako, nagode muku all Allah yabar zumunci._

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & parfect writers)_

 

*D’AN ASALI….!*🤴🏻

 

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

_DEDICATED TO FIDDAUSI SODANGI_

 

*27*

 

***Duk da cewa zuciyarsa na ta zugi da radadi amma haka ya daure ya kakaro murmushin dole dan ya kwantar mata da hankali,

“Sadiya meke damunki ne naga duk idanuwanki sun fada?”

Kallonsa tayi sai kuma tayi murmushi,

“Haba Aliyu taya zaka tambayeni abinda ke damuna bayan kasani? Abinda yafaru wallahi Aliyu shine ya tsaya min arai, kayi hakurin abinda Abba na yayi maka….”

Saurin katseta yayi,

“Sadiya karki bani hakuri saboda ni dama banyi fushi dake ba, sai dai bazan boye miki ba ina cikin damuwa da tashin hankali sakamakon abinda yafaru, dole naji babu dadi saboda na taba fuskantar matsala makamanciyar wannan abaya kinga muslima ma haka akamin saida muka shaku da ita sannan aka rabamu, gashi kema za arabamu a lokacin da kika bi duk wani sako da lungu na cikin zuciyata, a lokacin da kika zame min hasken idaniya, a lokacin da kika zama jinin jikina…..”

Cikeda tausayi da tashin hankali take kallonsa sakamakon jin muryarshi na rawa wannan dalilinne yasashi yin shiru, idanuwanshi ta kalla wadanda suka kada suka yi jajur,

“Aliyu kayi hakuri kadauki duk abinda yafaru a matsayin bai faruba, nidai abinda nasani shine har gobe ina sonka kuma ina kaunarka aduk halin da ka tsinci kanka”

“Halima kenan, taya hankalina zai kwanta bayan za arabani dake? Mahaifinki shine zai bani aurenki amma yace bazai aura min keba saboda ni ba *D’AN ASALI* bane, halima ni ina ganin mu hakura da juna kawai domin aurenmu bamai yuyuwa bane, ke yar asali ce nikuma ba dan asali bane, ta hanyar haram aka haifeni….”

“Dan Allah kadaina fadin haka Aliyu” tafada kwalla na sakkowa kan kuncinta, bazai iya jurar ganinta tana kuka ba shiyasa yayi saurin juyawa zai koma gida, gefen rigarshi ta riko da sauri, batare da ya juyo ba yatsaya yana kokarin mayar da kwallarshi,

“Aliyu nifa ko ya kake ina sonka, dan Allah karka rabu dani akan laifin da ba nawa ba”

Saida ya daidaita nutsuwarshi sannan yajuya ya kalleta fuskarshi da murmushi,

“Wayace miki zan rabu dake? Ai komai yawuce bazan rabu dake ba, ki dauka wannan abun da yafaru tamkar bai faruba”

Sai lokacin taji hankalinta ya kwanta ta samu yar nutsuwa,

“Dagaske ka hakura?”

“Allah dagaske nake”

“To dan Allah ka kunna wayarka kaga tun jiya naketa faman kiranka akashe”

“Yanzu ina shiga ciki zan kunna ranki ya dade”

Murmushi tayi ta sunkuyar da kai,

“Shikenan bari natafi”

“To sai munyi waya? Gashi yau fuskarki ko kwalli baki sakaba, wai meyasa bakya son saka kwalli ne?”

Murmushi tayi tajuya zata karasa wurin motarta nan yabi bayanta,

“Aliyu kenan halinka sai kai”

“Wanne irin haline nawan?”

“Zan fada maka ai amma ba yau ba”

“Babu damuwa indai zaki fada min din”

“Nagode to, sai munyi waya”

Tamkar kada ta tafi haka takeji shiyasa dakyar sukayi sallama tawuce yana tsaye yana daga mata hannu, saida ta bace sannan yashiga gida, dakinsa yawuce direct ya zauna yarasa wanne mataki ya kamata ya dauka domin magana ta gaskiya baya jin zai iya rabuwa da halima saboda yana mutukar sonta, sam baya jin zai iya barinta, yafi minti 20 ahaka kafin ya dauki wayarshi ya kunna.

Halima na komawa gida zazzabi ya rufeta kamar dama jiranta yake yi saboda kwanan da tayi tana kuka,

Dakin umma ta shiga ta kwanta ta lulluba ita umma ma bata san ta dawo ba saboda tana can part din abba tana gyara masa, lokacin da ta dawo ta shiga dakinne taga halimatu kwance ta lulluba, zuwa tayi taja bargon ta taba jikinta wanda ya dauki zafi,

“Sadiya baki da lafiya haka? Sannu bari inkawo miki abinci kici kisha magani”

Jijjiga kai kawai tayi batayi magana ba, fita umma tayi zuwa kitchen ta hado mata tea ta dauko bread da farfesun kafar saniya,

Dakyar da sudin goshi ta iya tashi tasha tea din ta koma ta kwanta, da rarrashi umma tasamu ta bata maganin tasha,

Kwanciya ta sake yi haka ta wuni akwance har yamma lokacin da Abba ya dawo,

Tana kwance adakinta a lullube Abba yashiga dakin shida umma, yace tafito suje asibiti tace tasha magani,

Abinci umma ta kawo mata tuwon shinkafa miyar kubewa, agaba suka sata ta tashi taci tasake shan magani ta kwanta, tana kwanciya bacci ya dauketa.

Haka ta rinka zazzabi har tsawon kwana hudu a ranar Abba yasa umma ta rakata asibiti,

Aliyu kuwa duk hankalinsa ya tashi sakamakon rashin jin halima saboda bai san abinda yafaru ba, duk da irin cin mutuncin da abbanta yayi masa hakan bai hanashi niyyar sake tunkarar gidanba domin yana so yaje ya gano halin da take ciki,

Shiryawa yayi yatafi da niyyar ta can zai wuce gareji, yana sauka akan babur yana kokarin bawa mai babur din kudinsa motar su Sadiya tashigo layin, saida suka zo daf dashi sannan Sadiya ta fahimci ashe Aliyu ne, kallon umma tayi tace,

” Umma tsaya kinga Aliyu…”

Tsayawa umma tayi ta sauke glass, ganinsu yasa Aliyu karasawa gaban motar ya durkusa ya gaida umma ta amsa fuskarta asake, bude kofa Sadiya tayi tafita yayinda ita kuma umma taja motarta tawuce cikin gida, tana shiga taga Abba tsaye yana jiran dawowarsu ashe ko fita baiyi ba, ganin umma ita kadai yasashi tambayarta ina Sadiya, nan tace masa wani abokin karatunta ne yazo dubata suna waje, baiyi wata wata ba ya nufi gate umma tana tsayar dashi amma bai tsayaba,

Kallon Aliyu Sadiya tayi bayan ta shagwabe fuska,

“Sai yau zaka zo dubani? Bayan banda lafiya tun ranar da naje gidanku”

“Ayi min afuwa ranki ya dade, kin san ai ban sani bane tunda baki fada minba, sannu ya jikin?”

“Da sauki yanzu ma daga asibiti muke fa kaga har jinina aka dauka aka yi test…”

Ta karasa maganar tana nuna masa inda aka huda ajikin hannunta,

“Ayya sannu, da ina nan bazan bari ahuda miki jiki ba, Allah yabaki lafiya…”

Bata kai ga amsawa ba Abba yafito ganinsu itada Aliyu yasake tunzurashi,

“Sadiya….! Ashe ban hanaki tsayawa da wannan yaron ba?”

Bai barta ta amsa ba yanuna mata hanyar shiga ciki, wani sabon zazzabi ne taji ya dawo mata nan tawuce ta shiga gida kanta a kasa, kallon Aliyu Abba yayi yace,

“Wannan kashedin da zan maka shine na karshe idan ka kuskura kasake zuwa kofar gidan nan sai na daureka”

Daga haka yajuya yashiga gida, Aliyu kasa zuwa garejin yayi sai gida ya koma yana zuwa yafara hada kayansa acikin akwatinsa, Ummi dake tsaye tana kallonsa hankalinta atashe tayi azamar shiga cikin dakin,

“Wai Aliyu lafiyarka kuwa? Meya faru?”

Muryarsa na rawa idanuwansa na zubar da hawaye ya amsa mata yana mai cigaba da zuba kayansa cikin akwatin,

“Ummi garin nan zan bari, nagaji da wannan bakin cikin da nake kunsa, nagaji da goranta min rashin uba da akeyi nagaji da kirana da marar asali da akeyi, duk inda naje neman aure hanani akeyi saboda wai ni ba *DAN ASALI* bane….”

Rufe akwatin yayi ya zuge ya jashi zai fita daga dakin, rikeshi Ummi tayi,

“Kayi hakuri Aliyu, ka dauka taka kaddarar kenan, amma yanzu Aliyu kenan zaka iya tafiya kabarni? Karfa ka manta ni nakasance atare dakai shekara da shekaru tun kana cikin cikina ban taba gudunka ba har ka girma”

“Ummi kiyi hakuri ki yafe min nima ba gudunki nayi ba, so nake inbawa zuciyata hutu, intafi inda zan shimfida sabuwar rayuwa,inda babu wanda ya sanni balle yasan waye asalina ko waye ni, tunda tun farko Ummi na rokeki ki sanar dani mahaifina amma kin gagara yin hakan, tunfa ina dan primary yara suke goranta min ni banida baba….”

Hawayen da yake rikewa ne suka gangaro ta karfi da yaji, sakinsa Ummi tayi,

“Shikenan Aliyu tunda ka zabi tafiya kabarni ni mahaifiyarka kaje Allah ya kiyaye hanya”

Daga haka ta juya tabar dakin tana hawaye, shima hawayen yake yaja akwatinsa,

“Ni Ummi ba tafiya nayi nabarki ba, ko yanzu kika sanar dani mahaifina da ta hanyar da aka sameni zan dauki kaddara inzauna in fasa tafiya…”

Bata ko juyo ta saurareshi ba tashige dakinta yayinda shikuma ya nufi kofa domin fita yana rikeda akwatin kayansa……..

 

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO*
_(Home of expert & Perfect writers)_

 

*D’AN ASALI….!*🤴🏻

*_NA_*
_*UMMI A’ISHA*_

 

_DEDICATED TO FIDDAUSI SODANGI_

 

*28*

 

***Har yakai bakin kofa yaja ya tsaya cak sakamakon wani abu da yatuno wanda ya fado cikin kwakwalwarshi yanzu, tunawa yayi da cewar tabbas idan yatafi yabar Ummi tofa ya gujeta dinne kamar yadda tace bayan kuma ita ta rayu dashi na tsawon lokaci tun bai san kansa ba,

Hawayen da suka taru cikin idonsa ne suka soma kwarara nan zuciyarsa ta karye yaji sam bazai iya yin nesa da ita ba,

Ahankali yaja akwatin yakoma duk jikinsa yayi sanyi, akofar dakinshi ya ajiye akwatin ya nufi dakin ummi, kamar yadda ya zata kuwa hakance ta faru domin samunta yayi zaune tana sharar hawaye,

Zama yayi kusa da ita idanuwansa fall kwalla,

“Ummi dan Allah kiyi hakuri, kidaina zubar da hawayenki akaina, daga yau nayi miki alkawari bazan kara tambayarki wani abu wanda ya shafi asalina ba tunda hakan na fuskanci yana bata miki rai kuma yana sanyaki kuka, kiyi hakuri dan Allah….”

Share hawayenta tayi ta dago ta kalleshi,

“Babu komai, kaje katafi inda kayi niyya…”

“Ummi kiyi hakuri nafasa, babu inda zanje ina nan tare dake koda kuwa duk garin nan zasu hanani auren yayansu, na zabi inci gaba da rayuwa dake ina kyautata miki koda zan mutu ahaka…..”

Murmushin karfin hali tayi ta shafi kansa,

“Insha Allah hakan bazata faruba Aliyu, zaka auri matar da kakeso a lokacin da yadace, yanzu ina kaje neman auren aka hanaka?”

Sunkuyar da kai yayi sannan ya dago dakyar ya kalleta,

“Gidansu wannan yarinyar me zuwa nan gidan”

Kallonsa Ummi tayi cikin rashin fahimta,

“Wacce fa?”

“Halima”

Dariya Ummi tayi ta jawoshi jikinta tana shafa kansa wanda ya dora kan cinyarta,

“Ni dama nasan za arina wai ansaci zanin mahaukaciya, dama nasan kaima kana sonta kawai tsabar jarabar taurin kaine irin naka, wato kenan shiyasa naga ta dauke min kafa ashe anfara surukunta dani…”

Murmushi yayi baice komai ba hakan yabawa ummin damar dorawa daga inda ta tsaya,

“Yarinyar ai tanada nutsuwa Aliyu, kayi hakuri da duk wani abu da yafaru da wanda zai faru gaba indai Sadiya matarka ce to zaka aureta babu makawa kaji? Allah yayi maka albarka”

“Amin ummi, dan Allah ki yafe min”

“Babu komai Aliyu nayafe maka duk laifin da kayi min”

Murmushi yayi yatashi zaune,

“Bari naje na leko garejin nan ummi, duk ranar da banje ba shirme suke zama suyita yi suki yin aiki”

“To ai sai hakuri gadanga, maza tashi kaje Allah ya tsare”

“Amin ummi”

Fita yayi yasa takalminsa yatafi, duk da zuciyarsa na cikin kunci hakan bai hanashi yin wasa da dariya da yaran nasa ba, wuni guda yayi acan sai daf da magrib ya dawo gida bayan ya iyowa ummi tsarabar awara, dafaffiyar gyada da kankana,

Duk da yanata ganin kiran Sadiya amma ya gaza bin kiran, sharewa yayi yaci gaba da al’amuransa domin zuciyarsa akwai rauni acikinta yana bukatar yawarke.

Tun ranar da yabar gidansu Sadiya take kwance bata da lafiya wannan dalilinne yasa taketa kiranshi domin ta sanar dashi amma yaki dauka, ko ba afada mata ba tasan fushi yadauka da ita sakamakon abinda yafaru, daga karshe hakura tayi ta kyaleshi ta daina kiransa,

Shi kuwa Aliyu duk sharetan da yayi kawai karfin haline domin sai yanzu ne yasan yana sonta kuma sai yanzu yagane muhimmancinta agareshi domin ya shaku da ita irin shakuwar da zaiyi wuya ya iya rabuwa da ita lokaci guda, duk da yanata kwadayi da burin jin muryarta amma haka ya daure ya hakura, gashi yau kusan kwananshi takwas rabonshi da ita,

Tunda ya shigo gida yau misalin karfe 9 nadare yayi shirin bacci alqur’aninsa ya dauka yafara tilawa domin azumin ramadan yafara kokarin kawo kai, kwana yayi yana tilawa saida yadawo daga sallar asuba sannan ya kwanta,

Misalin karfe 11 nasafe yafara mafarkin umminsa, wai gata ta kwanta tanata rashin lafiya, tana tsaka da jinyar ta kamo hannunsa tana cewa Aliyu yau dai zan fada maka asalinka, yau zan sanar dakai ta yanda na sameka amma kayi hakuri da duk abinda zakaji, cikin kuka shikuma ya riketa yana cewa babu komai ummi koma tayayane karkiji shayin fada min ki sanar dani, ta bude baki kenan rai yayi halinsa,

Afirgice ya farka duk yajike da gumi, baiko damu da a yanda yakeba yafita yana salati gamida addu’a acikin zuciyarsa wadda akeyi idan anyi mummunan mafarki,

Yana sako kafarshi waje yaga ummi tana zaune a madafa tana toya wainar kwai, wani sanyi yaji acikin zuciyarsa, karasawa yayi wurinta,

“Ummi sannu da aiki, yau da kanki kike yin abincin karyawar”

Juyowa tayi ta kalleshi fuskarta da murmushi,

“To ai naga Kai baka tashi bane shiyasa na hutar dakai, dama niyyata idan na kammala komai sai naje na tasar dakai”

“To ummi, ina kwana” yace da ita bayan ya durkusa,

“Lafiya lau alaramma, gashi nan duk ka hada gumi ai sai kaje ka watsa ruwa, yau garin da zafi”

“Hakane ummi, bari naje”

Daki ya koma ya dauko brush yafito yazo ya cika bucket da ruwa ya nufi bayi yana jin wani farin ciki na shigarsa sakamakon ganin ummi lafiya lau dayayi.

Koda yafito kuma ji yayi zuciyarsa ta karkata ga Sadiya, ko ba komai yana son jin muryarta,

Yana zaune gefen katifarsa bayan ya gama shafa mai ya dauki wayarshi ya soma kiran layinta, tana daf da tsinkewa ta samu zarafin dagawa.

Yanayin da yaji muryarta kadai yasa ya fahimci mawuyacin halin da take ciki,

“Sadiya meya faru ko bakida lafiya ne?”, Yafada hankalinsa atashe,

Wani tari mai ban tausayi yaji tayi sannan ta amsa masa dakyar,

“Aliyu banida lafiya kazo mu gana kafin na mutu…”

Jin abinda tace da yanayin muryarta yasake tayar masa da hankali,

“Sadiya kina asibiti ko gida?”

“Ina gida….”

“To kijira zanzo yanzu, zanzo induba ki”

Daga haka ya katse wayar yatashi ya zira kayansa duk jikinsa sai faman rawa yakeyi karr karr saboda gani yake kamar mutuwar zatayi saboda mafarkin da yayi da ummi sai yadora hakan akan Sadiya kila ita dince,

Agaggauce yagama shirinsa yafita,dakin ummi yashiga ya isketa tana karyawa, kokarin gabatar masa da kayan karyawar tayi ya katseta da cewa,

“Ummi kin manta yau litinin ne? Ina azumi ai”

“Hakane fa, to Allah yabada lada”

“Amin” da haka ya mike yafita, kai tsaye gidansu halima yawuce azuciyarsa yana jin komai zai faru sai dai ya faru, waya ya kirata ta daga a galabaice, mintuna kadan sai gata tafito dakyar, sanye take da jar doguwar riga ta yafo dan siririn farin gyale,

Zama tayi akasa ta jingina da bango saboda bazata iya tsaiwarba duk da ganin Aliyu ya dan kara mata karfi ajikinta,

Durkusawa Aliyu yayi agabanta yana kallonta cike da damuwa,

“Sannu Sadiya, wai meke damunki ne?”

“Ulcer…” Tabashi amsa tana faman yatsina fuska wadda daga gani tana jin jiki,

“Sannu, Allah yabaki lafiya, kina dai shan magani ko?”

“Ina sha”

“Ayya sannu, me kike so inje in kawo miki?”

Bai karasa rufe bakinsa ba sukaji karar horn mai mutukar razanarwa banda wani irin taka burki da akayi kiiiiiiiiiiiiiii, arazane dukkaninsu suka mike tsaye, Abba ne ya fito daga cikin motar sakamakon wasu takardun contract da ya manta wanda aka bashi domin yayi signing shine ya dawo dauka,

Cikin fada ya dakawa Halima tsawa ya korata gida sannan yajuya ga Aliyu yayi masa wankin babban bargo yashige gida afusace ya isketa tana kuka ajikin umma, (mai karatu idan baka mantaba wannan shine abinda yafaru a farkon labarin ashafi na daya dan haka yanzu zamu dora cigaban labarin).

Abba part dinsa yawuce afusace cikin fushi yana shiga ya zaro wayarshi dake cikin aljihunsa, cikin fada yafara magana,

“Dama ai na taba yimaka maganar wani yaro ko? Ka gane shi? To yanzu haka nazo na sake tarar dashi a kofar gidana so dan haka katuro yanzun nan su tafi dashi aje can a ladabtar dashi saboda bana son alakarsu da’yata…., zasu ganshi sanye da wani yadi mai duhu…., ok nagode”

Daga haka yakatse wayar yadauki abinda zai dauka yafita bai ko bi takan halimatu ba wacce ke can daki tana kwance tana kuka,

Ahankali Aliyu ke tafiya kamar mai jin tausayin kasa yasaka dukkanin hannuwansa cikin aljihunsa,

Saida yaje wani junction yatsaya domin samun abin hawa, wata motar jami’an tsaro ce ta kunno kai sai faman jiniya take, agaban Aliyu motar ta tsaya nan yan sanda guda hudu suka fito basuyi wata wata ba suka kamashi suka saka acikin mota,

Al’abine da tsoro suka dabaibayeshi lokaci guda gashi sunki bashi damar yayi magana bare ya tambayi laifin da ya aikata, sukuma sunki sanar dashi, suna zuwa aka turashi cikin cell bayan an kwace komai dake wurinsa daga shi sai dogon wando da farar singileti.

Wuni guda shiru Ummi taga bai dawoba gashi yana azumi amma sai ta zaci ko aikine yayi musu yawa, har aka kira salla babu labarinsa, wasa wasa har dare yayi ananne hankalinta yatashi ta fita zuwa masallaci wurin Malam lawan ta sanar dashi, kwantar mata da hankali yayi yace ta koma gida yasan Aliyu duk inda yake ba wurin barna bane kuma komai dadewa zai dawo sannan shima zaije ya nemoshi, komawa gida tayi amma ba dan hankalinta ya kwanta ba, daren ranar kuwa kasa bacci tayi.

A bangaren halima itama hakan take duk da bata san abinda yafaru ba amma jikinta ya tsananta domin a wannan dare sai a asibiti ta kwana saboda tsananta da jikin nata yayi,

Washe gari Malam lawan babu inda baije ba domin neman Aliyu amma shiru babu labarinsa abokan aikinsa kuwa agareji cewa sukayi sam jiya basuma ga ko keyarsa ba,koda yadawo ya sanar da ummi hankalinta idan yayi dubu to duk atashe yake babu bata lokaci ta soma sharar kwalla, abu kamar wasa saida yayi kwana uku a kulle sannan aka samu labarinsa wannan dinma wani saurayine dan unguwar yaje police station sakamakon karbe masa machine dinsa da akayi yaje kai report shine yaga Aliyu da yadawo yake sanar da Malam lawan, babu bata lokaci Malam lawan yazo yasaka Ummi agaba suka tafi,

Koda sukaje ummi kuka tafashe dashi sakamakon yanda taga Aliyu yazama, kwana uku kacal yafita kamanninsa saboda yunwa da rashin kwanciyar hankali domin rabonsa da abinci tun ranar lahadi,

Abinci Malam lawan yafita ya siyo masa yakawo aka mika masa ummi dai sai kuka take tana tambayarsu laifin da yayi nan suka tabbatar mata da babu abinda zasu iya cewa har sai abinda mahaifin Sadiya yace, wurin Aliyu ta leka tana tambayarsa inane gidansu sadiyan ita zataje da kanta ta roki gafarar mahaifinta sannan yayi hakuri ya rabu da yarinyarsu, daga kai kawai yayi dan haka ummin tajuya wurin Malam lawan ta sanar dashi, daga nan tawuce domin zuwa gidansu halimatu,

Dakyar da tambayoyi mai gadi yabarta ta shiga, babu kowa agidan sai iya mai aikinsu kadai baba tabawa wadda keyi musu girki, bayan sun gaisa da ummi take tambayar masu gidan nan baba tabawa take sanar da ita basa nan Sadiya da umma na asibiti shi kuma Abba yayi tafiya amma ana sa ransa adaren yau, godiya ummi tayi tai mata sallama ta tafi,

Kai tsaye gida tawuce taje ta dafawa Aliyu abinci, ita kanta takasa zaunawa taci abincin nan ta zuba a flask ta dauka ta sake kamowa division din,

Anan ummi ta wuni tunkur saida karfe 9 nadare yayi sannan Aliyu yace taje ta tafi, da hawaye suka rabu takoma gida, washe gari da sassafe kuwa gidansu Sadiya tayiwa sammako amma Abba bai dawoba sai umma tasamu, da fara’a da mutuntawa umman ta karbeta suka gaisa musamman ma da taji cewar mahaifiyar Aliyu ce ai sai tasake girmamata nan suka shiga jajantawa juna umman tace babu komai ta koma gida sai tadawo da yamma domin abban yashigo gari amma bazai karaso gida ba sai yamma, godiya ummi tayi mata tafita azuciyarta tana jin gaskiya Aliyu kam ya zake da yawa da yazo neman aure wannan gida domin yafi karfinsa,

Gida takoma tahada abin karyawa tatafi wurin Aliyu, acan ta wuni karfe uku nayi tabar wurinsa ta nufi gidansu Sadiya, duk da Malam lawan yace tabarshi shi zaije amma taki tace gara taje da kanta,

Umma tafito daga kitchen kenan taga ummi iso tayi mata har part din abba ta kaita, akasa Ummi tazauna ita kuma umma tashiga ciki domin sanar dashi, sun shafe fiyeda mintuna 15 sannan taji fitowarsu, hawayen idonta ta share ta daga ido ta kallesu, shima Abba kallonta yayi na yan sakanni nan mamaki ya bayyana akan fuskarsa karara, itama ummin cikin mamaki ta mike bakinta yana rawa…..

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*

 

*D’AN ASALI….!*🤴🏻

 

*_NA_*
*_UMMI A’ISHA_*

_DEDICATED TO FIDDAUSI SODANGI_

 

*29*

 

***Cikin rawar baki hawaye na bin kuncin ummi ta nuna Abba da yatsa tace,

“Ha…shi..mu…..”

Shi dimma jikinsa rawa yake dan tsananin rudu,

“Lu..ba..ba..tu ke nake gani da gaske?”

“Nice Hashimu…”

Zama Abba yayi kan Sofa sharabb ya daga hannunsa sama yana fadin,

“Alhamdulillah, Allah nagode maka da ka karbi addu’ata ka sadani da lubabatu tun kafin numfashina ya yanke, Allah nagode maka…”

“Alhaji dama ka santa ne? Ai itace babar wannan yaron Aliyu Wanda kasa akaje aka rufe tun shekaran jiya take zarya agidan nan…”

Kwalalo ido waje Abba yayi sannan ya mike zunbur kamar an tsikareshi sakamakon jin abinda umma tace, kallon Ummi yayi cikin gigita yafara tambayarta,

“Dagaske dankine wannan yaron?”

“D’a nane Hashimu shine wanda nabar gida da cikinsa”

Komawa yayi ya zauna cikin sauri yafara laluben aljihunsa domin daukar wayarsa, da sauri yayi danne dannen da zaiyi ya karata a kunnensa yasoma magana,

“Agaggauta kawo min wannan yaron da nasa aka rufe gida, dan Allah bana son adauki lokaci, afito dashi yanzun nan akawo min shi gidana….”

Daga haka ya katse wayar ya rafka uban tagumi fuskarsa kumshe da tarin nadama mai yawa,

Ita kuwa ummi kwalla kawai take sharewa, yayinda umma suka barta cikin duhu domin takasa fuskantar komai sai dai cikin zuciyarta cewa take”shiyasa duk abinda mutum zaiyi ake son ya rinka yi saise saise domin wata rana kar aji kunya, yanzu ina ranar wannan abu da abba yayi?”, dukkaninsu su ukun shiru sukayi babu Wanda yakara magana har tsawon mintuna ishirin daidai lokacin mai gadi ya shigo tareda Aliyu har tsakiyar falon, da sauri Abba yatashi ya rungumeshi yana shafa kanshi,

Abin ba karamin mamaki yabawa Aliyu ba nan zuciyarsa ta shiga yimasa tambayoyi kala kala, dakyar Abba ya iya sakinsa yanufi kujerar zamansa yana rikeda hannunsa,

Shidai Aliyu binsu kawai yake da ido musamman ganin umminshi na share kwalla,

“Lubabatu yanzu wannan shine d’ana? Ashe jinina ne na rinka tozartashi ina wulakanta shi? Allah na tuba, Allah ka yafe min laifin da nayi….”

Kallonsa Aliyu yayi kafin ya maida kallonsa ga ummi alamun neman karin bayani, jijjiga masa kai ummi tayi tace,

“Aliyu ga mahaifinka nan, shine mahaifinka…” Takarasa maganar bayan ta fashe da kuka,

“Ehhh hakane, Aliyu nine mahaifinka, na auri mahaifiyarka tun muna kauyen babban shuri anan cikin garin Zaria, to matsalar da aka samu a wancan lokacin shine bamufi wata biyu da aure ba akaga lubabatu dauke da cikinka wannan dalilinne yasa dangi da sauran mutanen gari suka fara tofa albarkacin bakinsu akan lamarin suna cewa wannan cikin dashi tazo ba nawa bane, nikuma nabi rudin shaidan na amince nayarda da yake a wancan lokacin mace takanyi shekaru uku zuwa biyar agidan miji ba tareda ta haihu ba, nan hudubar shaidan tayi tasiri har na yimata korar kare bayan na saketa saki daya,ban kara jin labarinta ba domin danginta ma da ta koma korarta sukayi sukace ta jawo musu abin kunya dan haka ba zasu zauna da itaba gashi dama marainiya ce bata da uwa bare uba….”

Jin abinda Abba yace Aliyu ya sunkuyar da kansa idanuwansa suna kadawa zuwa ja,

“Lubabatu yanzu tunda kika baro babban shuri anan kika yada zango? Nayita nemanki lungu da sako ban sameki ba?”

Daga kai ummi tayi alamun ehh batare da tayi magana ba,

Mikewa Aliyu yayi daga kusa da Abba yaje wurin ummi ya kamo hannunta yana fadin,

“Ummi tashi mu tafi gida….!

Jin yadda yake didarta yasata tashi batare da ta shirya ba nan yayi hanyar kofa da ita, umma wacce tayi zugum tana kallon ikon Allah ganin abinda Aliyu ke shirin yi yasata saurin tashi,

“Aliyu ina kuma zaku tafi? Bayan ga mahaifinka yau Allah ya hadaka dashi ina kuma zaka tafi?”

Ko juyowa baiyi ba yaja ummi suka fita, tirjewa ummi tayi a balcony ta kalleshi,

“Aliyu me kake shirin aikatawa ne? Hashimu fa shine mahaifinka, ya zakayi masa haka?”

Kawar da kansa gefe yayi yana furzar da wata iska mai zafi,

“Ummi to sai me kuma dan shine mahaifina? Shida ya koreki ya tozartaki ya sakeki yace ba cikinsa bane to danme sai yanzu zaice ni dansa ne? Tunda ya wulakantaki ummi ni babu abinda zai yimin dukda abinda yayi harda jahilci ciki…”

Katseshi ummi tayi cikin fada,

“Kul na kara jin haka daga bakinka Aliyu, mahaifin naka kake fadawa haka?”

Bai kai ga tankawa ba abban suka fito shida umma zuwa wurinsu,

Dafa kafadarsa abba yayi shikuma ya wani dauke kai yana huci,

“D’ana ka yafe min abinda nayi maka, ka daukeshi a matsayin rubutacciyar kaddara…”

“Wannan ba kaddara bace jah….”

Shiru yayi bai karasa ba sakamakon tsawar da ummi ta daka masa,

“Aliyu kar na kara jin kayi magana kana jina ko? Wuce mu tafi gida…”

Cikin sauri umma ta riketa,

“Wanne irin ku tafi gida kuma? Haba Umman Aliyu, dan Allah kuyi hakuri ku shigo ciki a sulhunta dan girman Allah”

Fafur ummi da Aliyu suka ki aminta sai da kyar da sudin goshi sannan umma ta iya shawo kansu, abba kuwa gafara yaketa nema yana nuna nadamarsa afili karara na abunda yafaru, zama sukayi cikin falon abba, cikin fargaba Abban ya kallesu ya soma fadin,

“Ni atawa bukatar shine mu manta baya, mu manta abinda yafaru, kuyi hakuri ku yafe min Ku dawo nan mu zauna tare saboda akwai bangare bangare agidan nan sunfi akirga, dan haka ina mai neman yafiyarku da kuma afuwarku….”

Shiru dukkaninsu sukayi sai da shirun yayi yawa sannan Aliyu ya katseshi ta hanyar cewa,

“Nidai ina ganin maganar dawowarmu nan da zama kawai abarshi dan ba mai yuyuwa bane, gara mu koma can inda muka saba muci gaba da zama inyaso nan din arinka zumunci….”

“Haba Aliyu, kaida gidan mahaifinka amma karinka fadin haka? To menene amfanin gane junan da akayi indai hakane? Ya kamata kumanta baya ku fuskanci gaba dan Allah…” Umma tafada cikin marairaicewa, Ummi dai naji batace komai ba har saida taga Aliyu yaki ya amince gashi hankalin Abba yatashi mutukar tashi wannan dalilinne yasa ta rarrasheshi har ya amince,

Kafin kiftawa da bismilla har angyara part din da zasu zauna wanda ke dauke da komai wanda ake bukata na jin dadin rayuwa, kamar yadda sauran parts din suke shima haka yake, umma ce dakanta ta kaisu ta rakasu ta nuna musu komai yadda yake, bedrooms ukune aciki sai kitchen da store da dining area baya ga babban falo mai dauke da set din kujeru kala biyu,

Tana kammala zagayawa dasu tawuce ta tafi, kallon ummi aliyu yayi,

“Yanzu ummi mun dawo nan da zama mun bar gidanmu?”

“Babu komai Aliyu Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, abban naka yace anjima za akaika ka debo mana duk abun da muke bukata agidan,sannan ina son ka sanar da Malam abinda ke faruwa”

Jijjiga kai yayi ya nemi wurin zama ya zauna yana kallon falon kusurwa zuwa kusurwa.

Jin kiran salla ya tabbatar musu da cewar mangariba tayi, tashi ummi tayi ta shiga daya daga cikin dakunan domin yin alwala shi kuwa Aliyu wanka ma yake son yi ko zai samu yaji dadin jikinsa, kofa yaga anturo nan Abba yashigo dauke da kaya a hannunsa,

“Aliyu ga wannan kayan ko, kayi wanka sai ka sakasu kafin gobe ka shiga kasuwa ka siyo wadanda zasu isheka”

Hannu biyu yasa yakarba yana jin sanyi aransa wai yau shine gashi ga gatansa wato mahaifinsa kuma sai tattalinsa yake,

“Allah yasaka da alkhairi Abba, nagode”

“Babu komai Aliyu, ai dukkan arzikina da abinda na mallaka nakane”

Murmushi Aliyu yayi yana kallon ledar kayan yayinda Abba yajuya yafita, tashi yayi yashiga daya dakin wanda ke ware can gefe guda, bathroom ya shiga yayi wanka son ranshi domin ya barnatar da ruwa samada bokiti biyar kuma cikin sa’a babu abinda babu wanda ake bukata yayin wanka kama tun daga kan sabulan wanka,gel,brushes, sponge, MacLean,da sauransu , saida yayi brush ya gyara jikinsa sosai sannan ya fito saboda yana gudun kada lokacin salla ya kure masa,

Wata farar damfareriyar shadda ya gani nan ya saka sai faman kyalli takeyi, anan cikin dakin yayi salla sakamakon sanin an idar da salla a masallaci yanzu.

Addu’o’i ya gabatar masu tarin yawa bayan ya mika godiyarsa ga Allah daga haka yatashi yafita, fitarsa tayi daidai da shigowar umma wadda ke dauke da kwanukan abinci Abba kuma yana biye da ita,

Zama yayi kusa da ummi, umma ta ajiye musu abincin tana fadin,

“Ga abincin kuci idan kuka gama sai muje mugano jikin Sadiya”

“To shikenan, bari mu gama, Allah dai yabata lafiya” inji ummi, Aliyu kam ko tari baiyi ba sai bin kowa da ido yake yi,

Tare ummi ta zuba musu abincin dashi, Indian jallop rice da salad, duk motsinsa idon Abba nakai yana binsa da ido aransa yana jin cewa tabbas yanzu ne yasamu magaji,

Bayan sun kammala ne suka tattara suka fita gaba daya domin zuwa asibiti wurin Sadiya, driver Abba yakira nan yazo da sauri, ganin Aliyu harda ma mahaifiyarsa yasanya malam kamilu yin wiki wiki da idanuwa, nuna Aliyu da yatsa Abba yayi ya kalli malam kamilu yace,

“Malam kamilu ga yarona…, d’ana ne na cikina, yayan halima ne, daga yau dukkan wasu harkokina zan damka su a hannunsa…”

“Toh toh.. Toh toh abu yayi kyau Alhaji, Allah yasanya albarka”

“Amin yanzu asibiti zamuje ka kaimu”

Da hanzarinsa ya bude musu kofofin mota suka shisshiga suka zauna ya figi motar aransa yana mamakin wannan lamari domin shi da bakinsa ya fadawa Abba cewar Aliyu ba dan halak bane kuma mahaifiyarsa karuwa ce to gashi yanzu ga abinda ya biyo baya shiyasa ya rasa da idon da zai kalli abban,

Lokacin da suka isa asibitin khairiyya suka samu kanwar umma wadda itace ke wurinta, sai faman kaiwa da komowa take sakamakon dan aman jinin da Sadiya keyi duk da likita ya dubata kuma yabata magani,

Hankalin Aliyu ba karamin tashi yayiba lokacin da yayi arba da ita domin duk ta fada, ganin halin da take ciki ya sanya Abba zuwa office din likitan yana neman shawararsa na zai fitar da Sadiya waje, kwantar masa da hankali likitan yayi ta hanyar cewa yanzu ma suna bakin kokarinsu kuma insha Allah zata samu lafiya kuma ko kasar wajenma aka kaita turawa ne zasu dubata kamar yadda anan dinma hakane dan haka su kara hakuri yanzu dai jini suke nema zasu kara mata amma har yanzu ba asamu wanda ya yi daidai da nata ba,

Fita Abba yayi tareda likitan suka koma dakin da Sadiya take ciki nan likita yashiga duddubata shikuma Abba ya sanar dasu umma halin da ake ciki,jin abinda abba yake fada yasa Aliyu matsawa kusa da abban,

“Abba to me amfanin ayita jira bayan anada bukatar kara mata jinin? Agwada nawa kawai idan zaiyi adiba asaka mata…”

“A’a Aliyu baza ataba maka jininka b…”

“Haba Abba, yar uwata fa zan bawa? Dan Allah kar ka hanani”

“To shikenan kuje agwada…”

Bin Dr yayi zuwa lab inda aka gama dukkan gwaje gwajen da ya dace kuma cikin sa’a jinin yazo daidai dan haka babu bata lokaci aka dibi leda daya, gado suka bashi ya dan kwanta ya huta ita kuma Sadiya akaje aka jona mata jinin.

Wurin mintuna talatin yayi akwance kafin yatashi yafita, su umma duk suna zazzaune adakin da halima ke ciki ganinsa yasa Abba cewa suje su koma gida amma sam Aliyu yaki yace suje zai taho daga baya duk da haka su dinma basu tafiba sai wurin 10,har lokacin Sadiya bacci take, alwala yayi yai salla adakin yayinda khairiyya ta fita zuwa reception, jinin na karewa halima ta farka, bude idonta tayi tayi wani dan tari,wani saukine take ji yana samunta kadan kadan,

Mikewa Aliyu yayi yakarasa wurinta, idanuwansu ne suka hadu da na juna nan yayi gaggawar dauke nashi sakamakon tunawa da yayi cewar Sadiya fa kanwarshi ce, murmushi tayi masa ta yunkura ta gyara kwanciyarta ta fuskanceshi tareda kafeshi da idanuwanta….

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

 

_*NA*_
*_UMMI A’ISHA_*

 

_DEDICATED TO FIDDAUSI SODANGI_

 

*31*

 

***Wuri Abba yasamu ya zauna yana fadada murmushin dake kan fuskarshi, shima Aliyu zama yayi akujerar dake fuskantar su Sadiya wadanda ke zaune a k’asa itada khairiyya,

Gyaran murya Abba yayi alamun yana son yayi magana nan kowa yabada hankalinsa gareshi musamman ma Sadiya wacce zuciyarta ke harbawa tana dukan uku uku domin bata son zarginta ya zama gaskiya ga uban tarin tambayoyin dake cikin kwakwalwarta,

“Godiya ahar kullum kuma akoda yaushe ta tabbata ga Allah tsarkakken sarki mai jujjuya al’amura yanda yaso, hakika babu wanda zai iya haka face Allah,

Sadiya bayan kwanciyarki a asibiti wani abun ban al’ajabi yafaru wanda wannan kadanne daga cikin ikon ubangiji,

Duk irin tozarci da cin mutuncin da nake yiwa Aliyu ashe kaina nake wulakantawa domin d’ana ne na cikina ban saniba….”

Jin abinda Abba yafada yasata ware idanuwanta mamaki ya mamaye fuskarta hadi da wani farin ciki marar misaltuwa,

“Woww….! Darling brother..! Tafada ahankali cikeda farin ciki, cigaba Abba yayi da cewa,

“Shiyasa malam bahaushe yace idan zaka gina ramin mugunta kagina karami domin watakila kaine zaka fada, to ni hakance tafaru dani tunda na shiryawa jinina mugunta batare da saninaba sai yanzu na yarda da maganar bahaushe da yace shi d’a na kowane shiyasa babu bukatar kayi masa mugunta, kinga duk wannan kai ruwa ranar da aketa yi wai ashe Aliyu yayanki ne…”

Murmushin farin ciki tasake yi ta sunkuyar da kanta sannan ta dago ta kalli Aliyu Wanda tun shigowarsa falon sai yanzu ya kalleta saboda yana son yaga yanayin da zata shiga amma ga mamakinsa sai yaga ita murna ma takeyi bayan kuma shi zuciyarsa inbanda azalzalarshi da zafin soyayyarta babu abinda takeyi,

Ita kanta sadiyan hakance ke faruwa da ita shine bai saniba amma ko ganin da tayi masa ayanzu bazata iya lissafa adadin kaunarshi da tasake shigarta ba,

Maganar Abba ce ta katse mata tunaninta,

“Aliyu mun gama magana da hajiya binta, idan har umminka ta amince za adaura mana aure da ita cikin mako shidda domin ta koma dakinta,

Haka kuma kaima maganar aurenka da Sadiya za ayishi nanda mako shiddan insha Allah saboda Sadiya yar gidan yayana ce mu’azu marigayi wanda gini ya fado musu shida mahaifiyarta suka rasu sai ita kadaice ta tsira shine na daukota tun tana yar shekara 2 naci gaba da riketa domin tun daga kanka Allah bai kuma bani haihuwa ba, inajin hakan nada nasaba da abinda nayi,

Idan Allah yakaimu akayi aurenku akwai wani part acan baya sai agyara muku shi kuci gaba da zama tare damu domin bama son kuyi nisa, sannan maganar karatunka ka zabi duk kasar da kake so zan kashe ko nawane kakoma karatu idan kadawo sai ka zabi abinda kakeso zan bude maka babban kamfanin da kowa sai ya sanshi a kasar nan….”

Jin abinda abba yace yasanya halima hanzarin tashi tafice cikeda kunya,

Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke yana jin tamkar an tsomashi acikin kankara dan tsabar farin ciki,

“Abba nagode madalla Allah yasaka da alkhairi, amma ni ina ganin ai karatun da nayima ya isheni basai…”

“A’a Aliyu bai isaba zaka kara wani insha Allah, idan akayi bikinku kaida halima gaba daya sai ku tafi can kuje kuyi karatunku idan kun gama sai ku dawo…”

“Hakan yayi Alhaji Allah yakara budi” umma tafada cikin farin ciki, itama ummi farin cikinne ya lullubeta amma batace komai ba wannan dalilinne yasa Abba cewa,

“To ke gimbiya me kikace…?”

Jin haka yasa Aliyu da khairiyya mikewa atare ita tawuce bedroom din Sadiya shikuma yayi waje yana murmushi,

Part dinsu yawuce kai tsaye har lokacin yana murmusawa saboda abinda abba yayi, yana shiga yaganta kwance kan doguwar kujera, zama yayi agefenta yana kallonta,

“Meya kawoki nan?”

Gyalen dake kanta ta dan ja sakamakon rigar da tasaka rubber ce,

“Kawai zuwa nayi inzauna kafin ummi tazo muyi hira…”

“Ban yarda ba…”

“Hmmmm shikenan, wai ashe kai dinma brother nane amma shine kawani tsaya da kanata wahalar dani…”

Murmushi yayi ya kalleta har yanzu arame take sosai,

“To ai gashi yanzu kema kina wahalar dani ba shikenan ba anyi 1-1”

“Ni bana baka wahala…”

“Haka dai kikace, kin dai ji abinda Abba yace ko? Nan da 6 weeks zaki zama matar aure amma ni gaskiya zanso adan kara koda 2 months ne”

Bude idanuwanta tayi ta kalleshi kafin ta tashi zaune tana yimasa wani kallo,

“Saboda kai baka damu dani ba ko?”

Girgiza mata kai yayi yana murmushi,

“Hakane mana…”

“Allah tausayinki nakeji Sadiya…, jibifa yadda kike kamar nayi uff kifadi”

Komawa tayi ta kwanta tana murmushi,

“Gara inbarki kidan murmure ko?”

Can kasan makoshinsa yayi magana yanda bazata jiba,

“Amma akayi auran nan ahaka ai sai in ballaki…”

Bude idonta sosai tayi ta kalleshi,

“Me kace? Allah baka da kunya fa kai dama”

“Nidin sweety….?” Yafada cikin tsokana,

“Kai din mana”

“To Allah yabaki hakuri, shikenan? Nidai zan samu abba abari ki kara girma tukunna”

Shiru tayi batace komai ba kawai tana hango hakan acikin zuciyarta wai itace har aka yanke ranar auranta da Aliyu kamar a mafarki,

Murmushi tasaki ita kadai domin dafarko har taso fidda rai da auransa ashema dan uwanta ne jininsu daya,

Kokarin tashi tayi ta kalleshi, shima kallonta yake ya tallafe kuncinsa,

“Bacci nakeji zanje inkwanta…”

Murmushi yayi ya dauke kansa daga kallonta muryarsa ta danyi sanyi,

“Kedai kawai zaki gudu kije kiyita fadawa kawayenki ansaka ranar bikinki”

“Kajika, Allah kabari bana so, inkayi wasa ma zan fadawa su abba cewa bana sonka…”

Dariya yayi batare da ya kalleta ba,

“Kin shirya biyana jinina dana baki kenan, inyaso sai kije wanda kike so din yabaki wani asaka miki…”

“Au dan ka bani jini shine sai ka goranta min? Shikenan zan biyaka abinka”

“Uhmm dama ai ko baki fada ba dole ki biyani….”

Zira kafafunta tayi kasa tatashi domin tagane inda maganar tashi tasa gaba,

“Saida safe…”

“Wai har mun gama zancen?”

Batare da tajiyo ba ta amsa da,

“Ehhh”

Ganin tafice yasashi tashi yashiga bedroom dinsa,

A hanya sukayi kicibus da ummi tafito daga part din umma,

“Ummi inata sauri inzo muyi hira…”

“To ai sai mukoma muje muyi halima”

Dariya tayi tagirgiza kai,

“A’a ummi kije ki kwanta gobe nazo dawuri…”

“To shikenan saida safe”

Wucewa tayi itama ummi tanufi nasu part din,

A bedroom ta iske khairiyya tayi shirin bacci tana shirya kayanta cikin jaka,

Zama tayi gefenta nan khairiyya tayi murmushi ta kalleta,

“Amarya har angama tadin?”

“Kai umma khairiyya kema tsokanata zakiyi? Shi yagama tashi tsokanar shine kema zakiyi taki?”

“Shima amaryar yace miki?” Ta tambayeta tana murmushi,

“Ehh mana,harda wani sai na biyashi jininshi da ya bayar aka saka min”

Dariya khairiyya tafara yi tana cigaba da shirya kayanta domin gobe take son wucewa school saboda za aturasu practical wani asibiti,

“Shikenan umma khairiyya nagode”

Daga haka ta mike tashiga toilet, wanka tayi tafito daure da towel, khairiyya ta kalla wacce ke kwance tana chaten,

“Wai har kin kwanta da wuri haka?”

“A’a ina jira kizo ne inbaki wani abu ki karanta”

Pant kawai tasaka tazira sleeping gown ta haye gadon ta kwanta,

“Ungo nakune na amare naga anturo…”

Karba tayi ta karanta, kunya ce ta kamata ta mika mata wayar,

“Maza ki zauna kunya idan kunyi auren ya rainaki”

“Ba haka bane umma khairiyya, ni wallahi abinma gani nake kamar a mafarki”

“Zaki auri dan uwanki ba…”

“Ehh mana zan auri darling brother na”

Dariya khairiyya tayi taci gaba da chaten dinta ita kuma ta jawo tata wayar wadda kamar jira ake tana daukowa kira yashigo, Aliyu ne yakira nan ta matsa can karshen gadon ta daga wayar, kasa tayi da murya,

“Darling brother….”

Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan ya amsa,

“Sweet sister…”

Jin yanda muryarshi tayi kasa da wani dadi yasata lumshe ido,

“Bakayi barci ba?”

“Sai naji muryarki, dazu shine kika gudu bamu gama magana ba ko?”

“To ai zamu hadu gobe…”

“Da yaushe?”

“Duk lokacin da kake so”

“Ni koda yaushe ma ina son ganinki ai..”

Sun jima suna hira har 11 sannan sukayi sallama ta kwanta. Shi kuwa Aliyu ba bacci ya kwanta ba nafilfilin da yasaba gabatarwa ya soma yi har tsakiyar dare.

Washe gari misalin karfe 10:30 suka shirya itada khairiyya wacce zata tafi wani purple din swiss lace tasaka riga da skirt, jikinta ta feshe da turare fiyeda kala biyar sannan suka fita tana rikeda dan kwalinta, a falo suka iske umma tana karyawa nan sukayi joining dinta, bayan sun gama ne tafita domin raka khairiyya amma saida suka fara biyawa part din ummi tayi mata sallama tukunna, iya ummin suka gani afalo ita kadai tagama karyawa, cewa ummi tana zuwa tayi tatafi raka khairiyya wacce Malam kamilu ke jiranta zai kaita, khairiyya sai maimaita mata take cewa taci gaba da shan maganinta kar taga ta samu sauki tace zata watsar da haka sukayi sallama ta koma part din ummi tayafa dan kwalinta akanta, tana shiga kamar abin hadin baki Aliyu na fitowa daga cikin daki,

Bata kalleshi ba tawuce wurin ummi ta zauna, shima wurin ummin yaje ya zauna yana gaisheta, suna gama gaisawa tatashi tace bari taje su gaisa da umma,

Saida ummi tafita sannan ta iya kallonshi, wani wa gambari ash colour yasaka sai kamshin turare yake amma shi nata kamshin ne yafi neman rikita masa lissafi wannan dalilinne yasashi kallonta yace,

“Dan Allah tashi daga nan ki koma can…”

Kallonshi tayi ta dan harareshi,

“Kai Darling Brother…”

Tea flask yajawo yabude zai tsiyaya nan ta matso gabashi ta karba,

“Kawo inzuba maka…”

Sakar mata yayi yana kallonta,

“Sadiya wannan turaren naki ai sai ahankali ne…..”

“Kai dai wallahi ai anyi jarababbe” tafada acikin zuciyarta amma afili cewa tayi,

“Me turaren nawa yayi?”

“Tayarwa da mutane hankali mana”

“Kai wallahi….. Allah bana so” tafada cikin shagwaba, kwace flask din yayi da cup din,

“Kiyiwa Allah ki matsa can nesa, kinji…?”

Tashi tayi tanufi kofa zata fita gaba daya,

“A’a nifa ba cewa nayi kitafi ba, matsawa kawai nace kiyi can nesa, kinji sadiyayye na?”

Tsayawa tayi cak batare da ta juyo ba kuma batayi gaba ba,

“Kinji sweet sister, yawwa halima na, dawo ki zauna mana yar autar mata, nifa duk matan duniyar nan muninsu nake gani idan har naga kyakkyawar fuskarki,zo ma kiji wani abu…”

Juyowa tayi tadawo taje can nesa dashi ta zauna tana kallonsa, tea ya hada ya jawo wainar shinkafa da miyar agushi yasoma ci yana kallonta, sunkuyar da kanta kasa tayi tana wasa da yatsun hannunta,

Har ya kammala cin abincin baiyi magana ba,

Saida yagama tass sannan ya tashi ya wanke hannunsa yadawo ya zauna,

“Kiyi hakuri Halimatu na, kin san meyasa nace ki matsa?”

Kallonsa tayi bata amsa ba,

“Za a iya samun matsala ne, amma ke naga kamar ma baki damu ba”

Nan dinma shirun tayi ta sunkuyar da kanta ganin ya kafeta da ido kamar yau yafara ganinta, tashi tayi,

“Bari inje ingaida Abba”

“Nima din ai can zanje wuce muje…”

Sanin idan tawuce gaba kallonta zai tayi yasata ki,

“Kawuce dai”

“To bakece karama ba? Ok ni bari nayi gaban sai kin taho”

Sakashi tayi agaba suka tafi suna hira har part din Abba, yana zaune kan dining yana karyawa, durkusawa sukayi suka gaidashi ya amsa cikin farin ciki daga nan yace su tashi su zauna susa hannu suci abinci,

Badan suna jin yunwa ba sai dan hakan zai ajiye musu wani tarihi na musamman yasa suka saka hannu a farantin wainar abba suka fara ci,

Tare dashi suka fito bayan sun kammala zai wuce office, dan rissinawa Aliyu yayi yace da Abba yana son zaije garejinsu domin yasan suna can suna zuba idon ganinsa kuma idan yatashi da yamma idan yasamu lokaci zaije makarantar islamiyyar da yake koyarwa, fatan alkhairi Abba yayi masa yashiga mota yatafi shida malam kamilu shikuma Aliyu yabi bayan halima,

“Madam za a ara min motar ne inje gareji?”

Juyowa tayi tai masa fari da idanuwanta tajuya tana cewa,

“Anawa?”

Binta kawai yake batare da ya amsaba abin dai da taguda dazun na kar ya kalli bayanta yanzu shidinne yafaru, aransa ji yake yanayin halittarta yayi masa ta ko ina duk da dai bata da cika sosai amma yasan wannan ba matsala bane, har sukaje falon umma bai daina kallonta ba dakyar yayi ta maza, bedroom dinta tawuce domin dauko masa key din tabarshi suna gaisawa da umma,

Fitowa tayi ta key din a hannunta ta mika masa ya karba, ta gefen ido ya kalleta yayi kasa da murya yace,

“Dauko mayafinki ki rakani waje”

Sake komawa daki tayi ta dauko gyalenta ta fesheshi da turaren oud sannan tafito ganinta yasashi tashi yayiwa su umma sallama yafita, nan tabi bayanshi tana kokarin yafa mayafin…..

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI….!*🤴🏻

 

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

_DEDICATED TO FIDDAUSI SODANGI_

 

*32*

 

***Yana gaba tana biye dashi abaya bai jiyo ya kalleta ba har sai da suka fito daga falon umma,

“Lafiyarki kuwa Sadiya?”

“Kamar ya?” Ta tambayeshi tana kallonshi,

“Ni wannan kamshin nakine wallahi nema yake ya rikita min lissafi”

“To wai kai daina shafa turaren zanyi?”

“Ehhh kidaina”

“Tabdijan” tafada tana turo baki bayan ta jingina da jikin bango,

“Kwana biyun nanfa wata sabuwar tsiwa kikeji ko? Shikenan nasan abinda zanyi”

“Idan katafi sai yaushe zaka dawo?”

“Kina son ganina ne?”

Da kai ta amsa masa alamun ehh,

“To zan dawo 6 idan antashi daga islamiyya”

Ido tazaro ta kalleshi,

“Har 6 ai? Kuma abincin fa?”

“Nakoshi ai”

“A’a nidai gaskiya kadawo kaci abinci, idan angama zanyi maka waya….” Ganin abinda takeyi kamar karamar yarinya yasashi juyawa yana dariya yafita bayan yace,

“To zan dawo koma ciki”

Bata komaba taci gaba da tsaiwar tana hangoshi yashiga motarta yafita daga gidan, saida taga fitarshi sannan takoma ciki wurinsu umma, kwanciya tayi akan kujera ta kamo Bollywood tana kallo yayinda su umma kuma keta hirarsu itada ummi,

Kamar a mafarki taji sallamar Sabira kawarta nan ta tashi ta rungumota tana murna, gaisar dasu umma tayi sannan halima tajata bedroom dinta tarufe kofa, akan gado suka baje Sabira tana kallonta,

“Wai yanaga kin rame?”

“Sabira ba doleba nida nayi jinya kamar zan mutu? Ai da sai dai kuji labari dan aman jini na rinka yi”

“Meya sameki to?”

“Ulcer mana, nafa jima kwance a asibiti”

“Tab, Allah yabaki lafiya wallahi ban saniba dan ko Abdul bai fada minba”

“Shima bai saniba ai, ni rabona dashi ma tun kafin inkwanta rashin lafiya”

“Naganku arana, nidai last 2 weeks ya kirani yace zasu tafi umarah shida dad dinshi ta can zasu wuce inane oho dai namanta amma kamar fa yace ya kiraki wayarki akashe…”

“Ke ni ina takaina ina naga time din waya? Wayarma sai awurin umma na sameta”

“Allah sarki shiyasa wlhi duk kin rarrame, Allah yasa kaffara ne”

“Amin Sabira, ina zuwa”

Tashi tayi tafita, drinks da snacks ta kawo mata ta dora mata akan gadon sannan tace,

“Albishirinki….”

“Goro”

“Bikina nanda 6 weeks”

“Dan Allah karki tsokaneni mana, da Abdul din yafada min ai cewar ansa date din bikinku”

“To anfada miki shi zan aura?”

“To wa zaki aura?”

“Aliyu….”

“Wanne Aliyu?”

Kwashe komai Sadiya tayi ta sanarwa da Sabira nanfa aka shiga tsare tsaren yanda biki zai gudana idan lokacin yayi, halima dai damka komai tayi a hannun Sabira kama tun daga kan su anko, sanarwa kawayensu da yan ajinsu da sauransu.

Aliyu koda yaje garejin ba karamin murnar ganinsa yaransa sukayi ba nan suka yanyameshi suna yimasa sannu da zuwa, sanar dasu abin alkhairin da ya sameshi yayi sannan yace akwai wani albishir amma sai nan gaba, kamar yadda yasaba yauma tare dashi akayi aikin, duk wanda yagama aiki aka bashi kudi sai yace abawa Aliyu kamar dai yadda sukeyi, karfe hudu yayi niyyar tashi nan ya tattara kudin duka wanda aka samu ya raba musu domin shi yanzu bashida bukatarsu daga nan yayi musu sallama sai gobe,

Yana shiga mota yaga wayarshi Nokia C1 yama manta da ita nan yaduba yaga Sadiya ta kirashi fiyeda sau 5,yasan yau akwai daru, bai kirata ba saboda gidan zaije,

Gidan yanufa lokacin da yashiga har Abba yadawo yasake fita, part din umminsa yashiga tana zaune ta idar da sallar la’asar ita kuma Sadiya tana kwance tana bacci, abincin ummi tayi masa nuni dashi da dan yatsanta nan ya gyada kai ya shiga bedroom, wanka yayi yafito ya saka wasu kayan yafesa turare sannan yafito, zama yayi yana kokarin zuba abincin saboda ummi tashiga daki, shinkafa da miya da vegetables salad,

Yana ci yana kallon halimatu wacce keta faman bacci ta rufe fuskarta da gyaleta wayarta kuma akan cikinta,

Murmushi yayi aransa yace “halima rigima”

Fitowar ummi ce ta katse masa zancen zucinsa tana yimasa sannu da zuwa, agaggauce yagama cin abincin yafita batare da yatashi halimatu ba saboda ummi na wurin kuma bazata bari ba.

Bai shigo gidanba tunda yafita sai bayan sallar isha, a falon abba duk ya iskesu banda halimatu nan abba ke tambayarsa ko Sadiya tabashi sako yace a’a dawowarshi kenan, abba cemasa yayi to yaje ya nemota ya karba,

Tashi yayi yawuce part din umma domin yasan tana can, lokacin da yashiga falon ganota yayi zaune da sabuwar laptop akan cinyarta, tana sanye da riga da wando pink colour sai siririn mayafi data dora akanta,

Zama yayi akujerar da take kai amma dan nesa da ita,

“Gimbiyata hutawa akeyi ne haka?”

“Ni ai munyi fada dakai darling brother”

“Ayi min afuwa nasan nayi laifi”

Tashi tayi ta matsa wurinsa da laptop din ta ajiye masa bisa cinyarsa sannan tawuce daki, Jim kadan sai gata rikeda katuwar sabuwar waya golden colour kirar galaxy S9,

“Gashi inji Abba, sabuwar waya da sabuwar laptop”

Karba yayi yana cewa,

“Masha Allah, tabarakallah….”

Zama tayi kusa dashi, ganin ya bude laptop din yana murmushi yasata sake matsawa jikinsa kamar zata shiga cikinsa,

“Abba yace kasaka duk wasu documents dinka masu muhimmanci aciki ka ajiye….”

Juyowa yayi ya kalleta baiyi magana ba ya maida kallonsa kan laptop din, hannunta ta kai kan laptop din tasoma dannawa tana kallon screen din laptop din,

“Darling brother kai kam nasan baza kasaka games dayawa ba aciki, nikam sunfi 30 a laptop dina…”

Maimakon yabata amsa sai ya jingina da jikin kujerar domin yaga kusancin nasu yayi yawa,

“Wai Sadiya kinada lafiya kuwa?”

Batare da ta fahimci maganar tashi ba ta amsa masa,

“Lafiyata lau mana, ni yanzu ai nasamu sauki”

“Gaskiya ina tantama…”

Yabata amsa tareda matsawa, zata sake matsowa yayi saurin katseta,

“Dan Allah kiyi zamanki anan, ni idan son samune ma kikoma waccar kujera”

“Kai darling brother…”

Sake matsawa tayi kusa dashi nan ya zuba mata ido yana kallonta,bai sake magana ba suka cigaba da kallon laptop din tare suna duddubawa,

Sai hirar tata laptop din take yimasa tana kai hannunta jikin laptop din, tun yana amsa mata taji yasoma yin shiru,

Ido kawai ya zuba mata yana bin fararen santala santalan hannayenta da kallo,

“Darling brother wai menene…?”

“Shiyasa nace miki bakida lafiya halima, matsa zan tafi…”

“Kai dan Allah baza ka bari ingani ba?”

“Wanne gani kike son yi bayan wannan, sai da safe…”

“Ni Allah a’a, to kabani wayar ingani mana”

“Sai gobe zan baki”

Daga haka ya mike zai fita, rabuwa tayi dashi tashige bedroom dinta bayan ta rufe kofar da karfi alamun tayi fushi, murmushi yayi ya tattara kayanshi yawuce part din ummi, kashe wayarta tayi danma karya kirata tayita buga game dinta har 12 nadare sannan ta hakura ta kwanta.

Shikam Aliyu yanata kiran wayarta amma akashe daga karshe sai hakura yayi ya kwanta, washe gari kasancewar alhamis ne da azumi yatashi, har ya fita bai ga halima ba da ya tambayi umma sai tace bata tashi daga bacci ba, har yaje gareji yana kiran wayarta amma har lokacin akashe,yasan fushi takeyi shiyasa ya tura mata text massage na ban hakuri, lokacin da taga sakon murmushi tayi dama tasan yau yana azumi domin ummi ta sanar da ita,

Har yamma bai dawo gidanba suna can sunata aiki sai daf da shan ruwa yashigo gida, ummi na alwala taji sallamarsa nan tafito bayan ta idar, yana tsaye yana kallon kayan shan ruwan da halima ta hada masa, murmushi yayi yaiwa ummi barka da gida sannan yawuce dakinsa saida yayi wanka yayi alwala sannan yafito cikin kananan kaya, apple guda daya ya dauka yaci yafita salla, shine yaja sallar a masallacin dake kofar gidansu wanda mutane ma ba kasafai suka fiya halatta ba kasancewar unguwa ce ta masu hannu da shuni kusan kowa agidansa yake yi,

Addu’o’insa ya gabatar sannan yakoma gida ahanya yaga abba alamar shima awaje yayi sallar, tare suka karasa gidan inda Abba yawuce part dinsa shikuma Aliyu yawuce nasu,

Da halima yafara yin arba ta dage tana kokarin raba wasu kofina wadanda suka manne wuri daya, pink din material ne ajikinta kanta ko dan kwali babu sai manyan kitson kalabar rubber attach din da Sabira tayi mata jiya da tazo,

Zama yayi akasa yana kallonta,

“Sweety na sannu da kokari”

Kamar bazata amsaba tace,

“Yawwa sannu da shan ruwa….”

“Yawwa…”

Kayan shan ruwan yajanyo yafara budewa, kunun shinkafa ne da dan wake an yanyanka kayan lambu aciki sai fruits salad,

“Kinyi kokari amaryatah, Allah yayi miki albarka”

“Amin ta amsa ciki ciki”

Murmushi yayi yaci gaba da cin abincin, saida ya koshi sannan ya koma saman kujera yana rikeda juice a hannunshi,

“Ba nahana irin kitson nan ba?”

Kallonshi tayi tagyara dan kwalinta,

“To ai bana salla…”

“Allah karya kike yi, to inma hakanne ahaka zakiyi wanka?”

“Zan tsefe kafin lokacin”

Sauya akalar zancen yayi da cewa,

“Ke shine jiya daga fada miki gaskiya zakiyi fushi?”

“Ni ba fushi nayiba”

“Hakane mana, yanzu ma dai wurin abba nake son zuwa infada mishi cewar adan kara lokacin bikin nan”

Gabanta ne ya fadi saboda jin abinda yafada nan ta kalleshi,

“Meyasa?”

“Da alama dai bakiyi lissafin yaushe ne bikinba ko? Azumi saura sati 1 za ayi bikinfa, shiyasa gara kawai abarshi zuwa bayan salla”

“To da yanzun da bayan sallar duk ba daya bane?”

“Gaskiya ba daya bane, haba halima kiyi tunani mana,idan akayi bikinmu azumi saura sati daya ai akwai matsala domin komai na iya faruwa, kinga da azo muna karyawa juna azumi kaffara na hawa kanmu ai gara maganin kar ayi kar asoma, kuskuren da wasunmu ke yawan yi shine sai azumi yazo gab sai ayi aure kuma wai saurayi da budurwa, lokacin fa kowa cikin doki da zumudi yake irin hakane sai kiga suna biyewa zuciya suyita bata azuminsu kuma idan ba isasshen ilmi ne dasu ba sai suyita tafiya ahaka,

Shiyasa iyaye dole sai ankula idan azumi yazo dab da dab arinka bari sai bayan salla dan kar ashiga hakkin su ma’auratan amma yanzu sam ba aduba hakan wasu ma azumi saura kwana 5 sai suyiwa yara aure kuma basa tunanin komai, sai kace dole? Akayi hakurin shekara da shekaru ma bare watanni…”

Shiru tayi ta sunkuyar da kanta tana jijjiga kai alamun gamsuwa da abinda yafada….

 

_Fatan alkhairi ga masoyan dan asali musamman ma dan asali fans group nagode da kaunarku gareni._

 

_*Ummi Shatu*_👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI….!*🤴🏻

 

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

_DEDICATED TO FIDDAUSI SODANGI_

 

*32*

 

***Yana gaba tana biye dashi abaya bai jiyo ya kalleta ba har sai da suka fito daga falon umma,

“Lafiyarki kuwa Sadiya?”

“Kamar ya?” Ta tambayeshi tana kallonshi,

“Ni wannan kamshin nakine wallahi nema yake ya rikita min lissafi”

“To wai kai daina shafa turaren zanyi?”

“Ehhh kidaina”

“Tabdijan” tafada tana turo baki bayan ta jingina da jikin bango,

“Kwana biyun nanfa wata sabuwar tsiwa kikeji ko? Shikenan nasan abinda zanyi”

“Idan katafi sai yaushe zaka dawo?”

“Kina son ganina ne?”

Da kai ta amsa masa alamun ehh,

“To zan dawo 6 idan antashi daga islamiyya”

Ido tazaro ta kalleshi,

“Har 6 ai? Kuma abincin fa?”

“Nakoshi ai”

“A’a nidai gaskiya kadawo kaci abinci, idan angama zanyi maka waya….” Ganin abinda takeyi kamar karamar yarinya yasashi juyawa yana dariya yafita bayan yace,

“To zan dawo koma ciki”

Bata komaba taci gaba da tsaiwar tana hangoshi yashiga motarta yafita daga gidan, saida taga fitarshi sannan takoma ciki wurinsu umma, kwanciya tayi akan kujera ta kamo Bollywood tana kallo yayinda su umma kuma keta hirarsu itada ummi,

Kamar a mafarki taji sallamar Sabira kawarta nan ta tashi ta rungumota tana murna, gaisar dasu umma tayi sannan halima tajata bedroom dinta tarufe kofa, akan gado suka baje Sabira tana kallonta,

“Wai yanaga kin rame?”

“Sabira ba doleba nida nayi jinya kamar zan mutu? Ai da sai dai kuji labari dan aman jini na rinka yi”

“Meya sameki to?”

“Ulcer mana, nafa jima kwance a asibiti”

“Tab, Allah yabaki lafiya wallahi ban saniba dan ko Abdul bai fada minba”

“Shima bai saniba ai, ni rabona dashi ma tun kafin inkwanta rashin lafiya”

“Naganku arana, nidai last 2 weeks ya kirani yace zasu tafi umarah shida dad dinshi ta can zasu wuce inane oho dai namanta amma kamar fa yace ya kiraki wayarki akashe…”

“Ke ni ina takaina ina naga time din waya? Wayarma sai awurin umma na sameta”

“Allah sarki shiyasa wlhi duk kin rarrame, Allah yasa kaffara ne”

“Amin Sabira, ina zuwa”

Tashi tayi tafita, drinks da snacks ta kawo mata ta dora mata akan gadon sannan tace,

“Albishirinki….”

“Goro”

“Bikina nanda 6 weeks”

“Dan Allah karki tsokaneni mana, da Abdul din yafada min ai cewar ansa date din bikinku”

“To anfada miki shi zan aura?”

“To wa zaki aura?”

“Aliyu….”

“Wanne Aliyu?”

Kwashe komai Sadiya tayi ta sanarwa da Sabira nanfa aka shiga tsare tsaren yanda biki zai gudana idan lokacin yayi, halima dai damka komai tayi a hannun Sabira kama tun daga kan su anko, sanarwa kawayensu da yan ajinsu da sauransu.

Aliyu koda yaje garejin ba karamin murnar ganinsa yaransa sukayi ba nan suka yanyameshi suna yimasa sannu da zuwa, sanar dasu abin alkhairin da ya sameshi yayi sannan yace akwai wani albishir amma sai nan gaba, kamar yadda yasaba yauma tare dashi akayi aikin, duk wanda yagama aiki aka bashi kudi sai yace abawa Aliyu kamar dai yadda sukeyi, karfe hudu yayi niyyar tashi nan ya tattara kudin duka wanda aka samu ya raba musu domin shi yanzu bashida bukatarsu daga nan yayi musu sallama sai gobe,

Yana shiga mota yaga wayarshi Nokia C1 yama manta da ita nan yaduba yaga Sadiya ta kirashi fiyeda sau 5,yasan yau akwai daru, bai kirata ba saboda gidan zaije,

Gidan yanufa lokacin da yashiga har Abba yadawo yasake fita, part din umminsa yashiga tana zaune ta idar da sallar la’asar ita kuma Sadiya tana kwance tana bacci, abincin ummi tayi masa nuni dashi da dan yatsanta nan ya gyada kai ya shiga bedroom, wanka yayi yafito ya saka wasu kayan yafesa turare sannan yafito, zama yayi yana kokarin zuba abincin saboda ummi tashiga daki, shinkafa da miya da vegetables salad,

Yana ci yana kallon halimatu wacce keta faman bacci ta rufe fuskarta da gyaleta wayarta kuma akan cikinta,

Murmushi yayi aransa yace “halima rigima”

Fitowar ummi ce ta katse masa zancen zucinsa tana yimasa sannu da zuwa, agaggauce yagama cin abincin yafita batare da yatashi halimatu ba saboda ummi na wurin kuma bazata bari ba.

Bai shigo gidanba tunda yafita sai bayan sallar isha, a falon abba duk ya iskesu banda halimatu nan abba ke tambayarsa ko Sadiya tabashi sako yace a’a dawowarshi kenan, abba cemasa yayi to yaje ya nemota ya karba,

Tashi yayi yawuce part din umma domin yasan tana can, lokacin da yashiga falon ganota yayi zaune da sabuwar laptop akan cinyarta, tana sanye da riga da wando pink colour sai siririn mayafi data dora akanta,

Zama yayi akujerar da take kai amma dan nesa da ita,

“Gimbiyata hutawa akeyi ne haka?”

“Ni ai munyi fada dakai darling brother”

“Ayi min afuwa nasan nayi laifi”

Tashi tayi ta matsa wurinsa da laptop din ta ajiye masa bisa cinyarsa sannan tawuce daki, Jim kadan sai gata rikeda katuwar sabuwar waya golden colour kirar galaxy S9,

“Gashi inji Abba, sabuwar waya da sabuwar laptop”

Karba yayi yana cewa,

“Masha Allah, tabarakallah….”

Zama tayi kusa dashi, ganin ya bude laptop din yana murmushi yasata sake matsawa jikinsa kamar zata shiga cikinsa,

“Abba yace kasaka duk wasu documents dinka masu muhimmanci aciki ka ajiye….”

Juyowa yayi ya kalleta baiyi magana ba ya maida kallonsa kan laptop din, hannunta ta kai kan laptop din tasoma dannawa tana kallon screen din laptop din,

“Darling brother kai kam nasan baza kasaka games dayawa ba aciki, nikam sunfi 30 a laptop dina…”

Maimakon yabata amsa sai ya jingina da jikin kujerar domin yaga kusancin nasu yayi yawa,

“Wai Sadiya kinada lafiya kuwa?”

Batare da ta fahimci maganar tashi ba ta amsa masa,

“Lafiyata lau mana, ni yanzu ai nasamu sauki”

“Gaskiya ina tantama…”

Yabata amsa tareda matsawa, zata sake matsowa yayi saurin katseta,

“Dan Allah kiyi zamanki anan, ni idan son samune ma kikoma waccar kujera”

“Kai darling brother…”

Sake matsawa tayi kusa dashi nan ya zuba mata ido yana kallonta,bai sake magana ba suka cigaba da kallon laptop din tare suna duddubawa,

Sai hirar tata laptop din take yimasa tana kai hannunta jikin laptop din, tun yana amsa mata taji yasoma yin shiru,

Ido kawai ya zuba mata yana bin fararen santala santalan hannayenta da kallo,

“Darling brother wai menene…?”

“Shiyasa nace miki bakida lafiya halima, matsa zan tafi…”

“Kai dan Allah baza ka bari ingani ba?”

“Wanne gani kike son yi bayan wannan, sai da safe…”

“Ni Allah a’a, to kabani wayar ingani mana”

“Sai gobe zan baki”

Daga haka ya mike zai fita, rabuwa tayi dashi tashige bedroom dinta bayan ta rufe kofar da karfi alamun tayi fushi, murmushi yayi ya tattara kayanshi yawuce part din ummi, kashe wayarta tayi danma karya kirata tayita buga game dinta har 12 nadare sannan ta hakura ta kwanta.

Shikam Aliyu yanata kiran wayarta amma akashe daga karshe sai hakura yayi ya kwanta, washe gari kasancewar alhamis ne da azumi yatashi, har ya fita bai ga halima ba da ya tambayi umma sai tace bata tashi daga bacci ba, har yaje gareji yana kiran wayarta amma har lokacin akashe,yasan fushi takeyi shiyasa ya tura mata text massage na ban hakuri, lokacin da taga sakon murmushi tayi dama tasan yau yana azumi domin ummi ta sanar da ita,

Har yamma bai dawo gidanba suna can sunata aiki sai daf da shan ruwa yashigo gida, ummi na alwala taji sallamarsa nan tafito bayan ta idar, yana tsaye yana kallon kayan shan ruwan da halima ta hada masa, murmushi yayi yaiwa ummi barka da gida sannan yawuce dakinsa saida yayi wanka yayi alwala sannan yafito cikin kananan kaya, apple guda daya ya dauka yaci yafita salla, shine yaja sallar a masallacin dake kofar gidansu wanda mutane ma ba kasafai suka fiya halatta ba kasancewar unguwa ce ta masu hannu da shuni kusan kowa agidansa yake yi,

Addu’o’insa ya gabatar sannan yakoma gida ahanya yaga abba alamar shima awaje yayi sallar, tare suka karasa gidan inda Abba yawuce part dinsa shikuma Aliyu yawuce nasu,

Da halima yafara yin arba ta dage tana kokarin raba wasu kofina wadanda suka manne wuri daya, pink din material ne ajikinta kanta ko dan kwali babu sai manyan kitson kalabar rubber attach din da Sabira tayi mata jiya da tazo,

Zama yayi akasa yana kallonta,

“Sweety na sannu da kokari”

Kamar bazata amsaba tace,

“Yawwa sannu da shan ruwa….”

“Yawwa…”

Kayan shan ruwan yajanyo yafara budewa, kunun shinkafa ne da dan wake an yanyanka kayan lambu aciki sai fruits salad,

“Kinyi kokari amaryatah, Allah yayi miki albarka”

“Amin ta amsa ciki ciki”

Murmushi yayi yaci gaba da cin abincin, saida ya koshi sannan ya koma saman kujera yana rikeda juice a hannunshi,

“Ba nahana irin kitson nan ba?”

Kallonshi tayi tagyara dan kwalinta,

“To ai bana salla…”

“Allah karya kike yi, to inma hakanne ahaka zakiyi wanka?”

“Zan tsefe kafin lokacin”

Sauya akalar zancen yayi da cewa,

“Ke shine jiya daga fada miki gaskiya zakiyi fushi?”

“Ni ba fushi nayiba”

“Hakane mana, yanzu ma dai wurin abba nake son zuwa infada mishi cewar adan kara lokacin bikin nan”

Gabanta ne ya fadi saboda jin abinda yafada nan ta kalleshi,

“Meyasa?”

“Da alama dai bakiyi lissafin yaushe ne bikinba ko? Azumi saura sati 1 za ayi bikinfa, shiyasa gara kawai abarshi zuwa bayan salla”

“To da yanzun da bayan sallar duk ba daya bane?”

“Gaskiya ba daya bane, haba halima kiyi tunani mana,idan akayi bikinmu azumi saura sati daya ai akwai matsala domin komai na iya faruwa, kinga da azo muna karyawa juna azumi kaffara na hawa kanmu ai gara maganin kar ayi kar asoma, kuskuren da wasunmu ke yawan yi shine sai azumi yazo gab sai ayi aure kuma wai saurayi da budurwa, lokacin fa kowa cikin doki da zumudi yake irin hakane sai kiga suna biyewa zuciya suyita bata azuminsu kuma idan ba isasshen ilmi ne dasu ba sai suyita tafiya ahaka,

Shiyasa iyaye dole sai ankula idan azumi yazo dab da dab arinka bari sai bayan salla dan kar ashiga hakkin su ma’auratan amma yanzu sam ba aduba hakan wasu ma azumi saura kwana 5 sai suyiwa yara aure kuma basa tunanin komai, sai kace dole? Akayi hakurin shekara da shekaru ma bare watanni…”

Shiru tayi ta sunkuyar da kanta tana jijjiga kai alamun gamsuwa da abinda yafada….

 

_Fatan alkhairi ga masoyan dan asali musamman ma dan asali fans group nagode da kaunarku gareni._

 

_*Ummi Shatu*_👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

 

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

 

_DEDICATED TO FIDDAUSI SODANGI_

 

*33*

 

***Bata sake koda kwakkwaran motsi ba har yagama bayaninshi yatashi wai zai je wurin Abba,

Tana kallonshi yawuce yatafi bayan yayi yayi da ita akan suje tare amma taki,

Kwanciyarta tayi bayan yatafi ta dauki wayarta tana game,

Abba na zaune shida umma suna tattaunawa gameda yanda bikinsu Aliyu zai kasance, gyaran murya umma ta danyi bayan ta kalli abba,

“Yawwa Alhaji dama nikuwa inada wata shawara idan har ka yarda”

Kallonta abba yayi yana gyara zamansa,

“Ina sauraronki uwar gida hajiya binta”

Murmushi umma tayi sannan tace,

“Dama cewa nayi me zai hana yaran nan adan kara lokacin nasu bikin saboda kar mu shiga hakkinsu tunda kaga fa bikin nasu yana gab da watan azumi, ku dai nakun sai abarshi ayanda akace dafarko….”

Murmushi Abba yayi ya ajiye takardun dake hannunsa,

“Wallahi hajiya binta shiyasa akullum kike shiga raina saboda hangen nesanki, wannan shawara taki tayi, kin hango abinda ni ada ban hangoba har saida kika tunasar dani, shikenan nasun zamu barshi zuwa bayan sallar insha Allah saboda gudun samuwar matsala…, amma kina ganin bayan salla da sati daya yayi?”

“Yayi wallahi Alhaji, Allah dai yanuna mana lokacin yasa mugani da idonmu ba agane mana ba”

Kafin Abba yasamu zarafin amsawa Aliyu yashigo da sallama,

Dukkaninsu amsa masa sukayi suna kallonshi kowannensu fuskarshi dauke da murmushi, akasa ya zauna yagaida su nan umma cikin fara’a tace,

“Ansha ruwa lafiya? Yau tunda naga mutuniyar taka tanata aiki na fahimci azumi kake…”

Sunkuyar da kansa kasa yayi yana murmushi,

“Lafiya lau umma…”

Shiru yayi yarasa ta inda yadace yafaro fadar abinda ya kawoshi,

“Yawwa Aliyu kamar dama kasan ina nemanka kuwa saboda yanzun nan nida ummanku muka gama wata muhimmiyar magana dangane da bikinku, mun dage bikinku zuwa nanda bayan salla da sati daya saboda wani dalili, ina fatan hakan yayi maka?”

Aliyu ji yayi kamar yayi me dan farin ciki, kamar abba yasan zuciyarsa shiyasa yayanke wannan hukuncin,

“Ehh Abba hakan yayi, babu wata matsala”

“Yawwa to Allah yayi muku albarka, sai ka fadawa ita kanwar taka”

“Amin Abba, atashi lafiya”

Daga haka yafita zai je masallaci domin lokacin sallar isha yakawo jiki.

Yana fitowa ya hangota tana fitowa daga part din ummi rike da cups din da ta wara dazu, da hannu ya kirata kamar bazata zo ba sai dai ta taho tana kunkuni ahankali,

“Shi wannan Darling brother din wallahi….”

“Abba yace infada miki andage biki sai bayan salla da sati daya kamar yadda kika bukata…”

Jin abinda yace yasata zaro ido tana kallonsa,

“Nice nace adage da zaka fadi haka?”

“Nidai babu ruwana abinda Abba yace infada miki kenan…”

Bai jira abinda zata ce ba yajuya yatafi yana dariya domin baya so lokacin salla yashiga suna tare.

Zamansu yaci gaba da tafiya cikin aminci da kaunar juna domin dukkaninsu sun aminta da irin kaunar da sukewa junansu, hatta dasu iyayen nasu sun san dagaske suke son juna bada wasa ba,domin koda yaushe suna tare suna hira indai Aliyu yana gida, soyayya suke mai tsabta wacce ke cike da koyarwar addinin islama wadda babu hudubar shaidan balle rudin zamani aciki,

Bangaren karatun da yake koya mata kuwa har yanzu bai fasaba kullum da daddare yanzu suke karatun a sashen ummi, duk wani abu wanda yasan ya shafi ibadarta yana kokarin ganin ya wayar mata da kai, akoda yaushe zaka iskesu suna hira ko a part din umma ne ko na ummi ko kuma a compound din gidan,

Duk ranar litinin da alhamis kuwa zaka samu Sadiya a kitchen tana kiciniyar hada masa abun shan ruwa wanda zaiyi mutukar yabawa da ita, shiyasa yanzu suka shaku fiyeda da suka zama tamkar abu guda daya saboda tsantsar shakuwa da kulawa da juna, har wani duhu halima ke ganin gidan yayi mata idan Aliyunta baya nan saboda kullum yakanje gareji sannan da yamma ya wuce islamiyya, wani lokacin kuma yana raka abba office ko wata unguwar wacce keda muhimmanci.

Kasancewar komai ya daidaita yasa Abba sanar dasu gaba daya cewar acikin satin nan su shirya zasuje kauyen babban shuri sukai ziyara domin Aliyu yaga danginsa suma su ganshi haka itama ummi,

Ranar laraba da sassafe suka shirya bayan sunyi kintse kintsensu sunyi breakfast misalin karfe 7:30 suka tafi a katuwar jeep din Abba,

Karfe 11 daidai suka isa kauyen wanda yanzu ya dan soma zama birni sakamakon cigaban da abba ke kaiwa sannan gwamnati itama tana taimaka musu,

Family house dinsu Abba suka fara zuwa wanda acanne suka zauna shida ummi lokacin da akayi musu auren saurayi da budurwa, har dakin da suka zauna da ummi saida Abba ya nunawa Aliyu wanda yanzu dakin an mayar dashi wani babban falo domin saukar baki,

Yan uwa sunyi murna kuma sunyi farin ciki da ganin Aliyu da mahaifiyarsa nan abba yayi rabon kudi yara da manya kamar yadda ya saba daga nan kuma suka wuce danginsu ummi wadanda da yawa daga cikinsu duk sun tsufa suna cikin wahalar rayuwa danma Abba yana tallafa musu,

Bayan yan koke koke da akayi da gaishe gaishe gamida neman gafarar juna akan amanta baya afuskanci gaba daga nan Abba suma yayi musu sha tara ta arziki, anan suka ci abinci sukayi sallar azahar da la’asar, basu bar kauyen babban shuri ba sai bayan sallar magrib shiyasa basu sukaje gida ba sai goman dare harda yan mintuna,

Tunda suka koma halimatu daurewa kawai take saboda ciwon marar dake addabarta, azaune tayi salla tasha tea ta kwanta, da safe kuwa bata fito ba tana tukunkune cikin bargo tana murkususu har umma ta shiga domin lokacin karfe 11 saura,samunta umma tayi tanata kuka tana juye juye,

Fita umma tayi domin tasa akawo mata magani sukayi kicibus da Aliyu wanda ke kokarin shigowa cikin falon, durkusawa yayi ya gaidata ta amsa da fara’arta nan take fada masa dama fita zatayi ta samu ta aiki wani domin ya siyowa halima magani tana daki kwance bata da lafiya,

Cewa umma yayi zaije ya siyo mata amma bari yafara zuwa ya dubata tukunna, bedroom dinta yanufa akaro na farko ita kuma umma ta nemi wuri ta zauna cikin falon.

Saida yayi knocking sannan yatura kofar yashiga, can tsakiyar gado ya hangeta tana tukunkune cikin bargo, gaban gadon ya karasa ya zuba mata ido yana kallonta,ahankali yayi magana,

“Sweet sister…, meke damunki?”

Fito da kanta tayi wanda ke cikin barko ta kalleshi tana yamutsa fuska,hawaye nabin kuncinta,

“Marata….”

Sunkuyawa yayi ya tsugunna gaban gadon,

“Ayya sorry, Allah yabaki lafiya kinji, yazo ko har yanzu?”

Runtse idonta tayi bata amsa masa ba,

“Yi hakuri ki fada min kinji, fada min karki ji kunya magani zan hado miki kuma sai kin fada min zan san wanda yadace inkawo miki…”

Dakyar ta bude baki tayi magana,

“Yazo dazu…”

“To sorry, zakiji sauki very soon kinji? Yi hakuri ina zuwa”

Tashi yayi yafita, key din motar umma ya karba yafice daga gidan gaba daya,

Baifi mintina talatin ba ya dawo, ruwa mai zafi sosai ya zubo a cup yashiga dakin har lokacin bata daina kukanba,

Zama yayi agefen gadon ya dauki tea spoon ya dibi garin hulba cokali biyu sannan ya zuba zuma bayan ya disa ruwan zamzam aciki sai ruwan kal shima tea spoon biyu, gaurayawa yashiga yi har na tsawon dan wani lokaci, kallonta yayi cikin sanyayyiyar murya yace,

“Sister tashi kisha maganin kinji….”

Dayake tana cikin zafin ciwo bata damu a yanda takeba ta tashi zaune bayan taja bargo ta rufe kirjinta domin rigar baccine ajikinta pink colour marar nauyi,hawayen fuskarta tasa bayan hannu ta goge,

Mika mata cup din yayi tana karba ta toshe hanci,

“Yi hakuri kinji, daure kisha magani ne sadidan insha Allah zaki samu lafiya…”

Kin sha tayi yayi yayi da ita amma taki daga karshe ma ajiye maganin tayi kan bedside drewar tajuya zata kwanta, fushi taga yayi nan yatashi zai fita juyowa tayi ta kalleshi ya dauke kai zai sauka daga kan gadon babu zato yaji tayi saurin riko hannunshi,

Komawa yayi ya zauna yana kallonta,

“To idan bakya son natafi kitashi kisha”

Tashi ta yunkura tayi har lokacin tana rikeda da hannunshi, da dabara ya zare hannunshi daga nata ya karbi cup din yakai saitin bakinta,

“Rufe idonki to kigani, karbi karki saki sai kin shanye kinji Sadiya na, yawwa leema tah…”

Yanda yace tayi ta rufe idonta dukda bata son wannan warin na hulba amma haka ta daure gudun kada yayi fushi, kwanciya takoma tayi bayan ta sakar masa cup din sai faman yamutsa fuska take yi, murmushi yayi ya kalleta,

“Sannu halimatu na, da ace wani na iya daukewa wani ciwo to da babu abinda zai hanani dauke miki har na tsawon shekaru bila adadin…, amma ki fada masa bayan salla zanyi maganinsa zan baki baby tayadda bazai kara zuwaba bare har ya wahalar min dake har na tsawon watanni tara….”

Juya masa baya tayi tana murmushi domin har ciwon yafara lafa mata,

“Sannu…, yanzu yaya kikeji? Da ciwon sosai kamar da?”

Kai ta girgiza masa alamun a’a bai kara magana ba harsu ummi suka shigo itada umma babu shiri yatashi ya fita, kamar yafasa zuwa gareji tunda halimatunsa babu lafiya amma sai kawai yaga gara yatafi inyaso saiya dawo da wuri ashe tsautsayine ke kiransa,

Ita kuwa halimatu tafiyarsa habu dadewa taji ciwon ya lafa mata gaba daya dan haka tatashi taje tayi wanka da ruwan dumi kamar yadda taga ya bata umarni ta sakon text massage din da yaturo mata, shiryawa tayi cikin fitted gown ta atamfa kalar ruwan shanshan bale, kwalliya tayi tasha turare kamar ba itace ke kwance dazu babu lafiya ba, saida ta danci abinci sabanin da wanda indai tafara ciwon marar nan ko abinci gagararta yake, wayarta ta dauka bayan ta kammala ta soma kiran noorul qalbi kamar yadda tayi saving amma kuma har wayar tayi ta katse ba adauka ba….

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

 

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

 

_DEDICATED TO FIDDAUSI SODANGI_

 

*34*

 

***Bata sake kiranshi ba domin azatonta ko aikine yasha kansa shiyasa bai samu damar daga wayar ba,

Part din ummi taje ta sameta suka soma hira daga karshe bacci ya kwasheta anan saman kujera,

Karfe 3:30 Aliyu yadawo shida dan larai wanda yakawoshi a motar halima, karbar key din yayi yashiga ciki,

Ummi na zaune ta idar da sallar la’asar yashiga da sallama ya zauna akan kujera yana kallon Sadiya wacce ke kwance tana bacci, zuba mata mayalwatan idanuwanshi yayi yana kallonta yanda taci uban kwalliya kamar ba itace dazu ke kuka ba bata da lafiya,

Juyowa ummi tayi ganinshi yasata zabura tana rafka salati,

“La’ilaha ilallahu, me zan gani ni lubabatu? Aliyu meya sameka?”

Saida ya gyara zamansa sannan yayi murmushi,

“Ummi wallahi ina gyara wata motane to na shiga kasanta sai abinda aka tokareta dashi ya goce shine tafado min, gashi ma har na karye a hannu….”

“Ikon Allah, tsautsayi baya wuce rana, Allah ya rufa asiri ya kiyaye gaba…”

“Amin, ummi ai tazo da sauki ma da abin ya tsaya iya haka”

Tashi ummi tayi ta karaso kusa dashi takama hannunshi mai karayar tana dubawa,

“Sannu, gashi nan ai naga har andoraka…”

“Ehhh andora ni, dan larai ne yakaini wurin wani mai gyara…”

“To Allah ya rufa asiri”

“Amin ummi, ko salla ma fa banyi ba, bari inyi wanka sai inyi salla”

“To, to shikenan muje”

Bin bayansa ummi tayi har cikin dakinsa tashiga bathroom ta zuba masa ruwan wanka sannan tafito, ita ta taimaka masa ya cire kayan jikinsa ya rage daga shi sai gajeren wando sannan tafita shikuma ya shiga wanka,

Bayan ta koma falo ne ta iske halima ta tashi tana mika, zama ummi tayi tana sanarda ita tsautsayin da Aliyu ya gamu dashi,

Hankalinta ne yatashi nan taji kamar tayi kuka domin idonta har yayi ja,

Suna nan zaune ya leko batare da yafito gaba daya ba yana yiwa ummi magana akan tazo ta tayashi zaisa kayanshi, juyawa halima tayi tai maza ta dauke kanta domin daga shi sai gajeren wando, tashi ummi tayi tabishi zuwa dakin ita kuma halima ta zauna tana jiran fitowarsu, iya ummi ce kadai tafito domin shi ya zauna aciki zaiyi sallar la’asar,

Saida ya kwashe fiyeda mintuna 15 sannan yafito lokacin har Sadiya ta kosa da zaman jiranshi zama yayi akusa da ita yayinda ummi ta tashi ta fice,

“Kai Darling brother gaskiya ka jima, wai me ka zauna yine har haka?”

“Sallah nayi ko dan ke bakya yi shine zaki hanani nima?”

“Ni bance ba, sannu, ummi tace kaji ciwo mugani”

Mika mata hannun yayi sai lokacin taga gyaran karayar dake hannunshi, kwalla ce ta ciko idonta,

“Sannu Darling brother…, dama karyewa kayi shine ummi tace min kawai kaji ciwo? Sannu”

Murmushi yayi ya kalleta,

“Ke babu wani zafifa yanzu, ni kinga yunwa ma nakeji zo kibani abinci”

Dining taje wurinda abincin yake ta zubo masa, dambun kuskus ne da vegetables sos sai coconut juice,

Kasancewar a hannunshi na dama ya karye yasashi daukar spoon din da hannun hagu, karbewa tayi tana kallonshi,

“Sauko kasa inbaka…”

Baiyi musu ba ya sauko ya zauna ta soma bashi abaki yana ci itama tana ci,

“Amma dai bazaka sake komawa garejin nanba ko?”

“Saboda me? Zan koma mana”

“Nidai Allah a’a, jibifa ciwon da kaji kuma shine zaka kara komawa” tafada cikeda shagwaba,

“To ai ko naji ciwo hakan bazai hanani sake komawa ba…”

“Nidai Allah bazaka komaba, ko zaka koma sai ka warke…”

“To shikenan gimbiya, yanda kikace ai haka za ayi”

Juice din ta tsiyaya ta saka masa abaki nan ya kurba ya lumshe ido,

“Kinsha wannan juice din kuwa?”

Girgiza masa kai tayi,

“To kisha dayawa dan zaiyi miki amfani”

“Wai ka mantane banda lafiya? Yaushe kuma zan sha zaki”

“Wannan ai babu matsala sai maslaha”

“Bana sone fa, bazan sha ba”

“Allah zai kara miki ni’imar jikinki….”

Harararsa tayi taci gaba da cin abincinta, kallonta yayi kafin ya dauke kanshi,

“Ke wai sai inyita fada miki abubuwan da zasu gyara miki jikinki amma sai kiyi biris dashi, nace ki ringa kunshi kinki, nace ki rinka saka kwalli kin ki, yanzu nace kisha wannan shima kin ki, magana ta gaskiya fa ni kikewa mugunta…”

Zumburo baki tayi ta debi abincin ta mika masa saitin bakinshi,

“Ke badan ma yar gata bace kin taba ganin a inda miji ke yiwa matarsa haka? Bafa kowa ne ke gyara matarsa ba sai ke yar baiwa….”

Jin abinda yace yasata yin murmushi batace komai ba har suka kammala cin abincin, sama ta koma kan kujera ta mike hakan yayi daidai da shigowar su umma itada abba sai ummi domin ummi ta sanar dasu abinda ya samu Aliyu har karayar da yayi, Abba kamar zaiyi me nan yashiga jajantawa daga karshe yace ko asibitin kashi zasuje aduba shi? Cewa Aliyu yayi a’a wannan gyaran ma da akayi masa ya isa kuma insha Allah zai samu lafiya,

Fita Abba da umma sukayi ita kuma ummi ta zauna suna hira dasu Aliyu, basu suka tashiba saida aka kira sallar magrib, ummi ce ta soma shiga dakinta domin yin alwala, tashi Aliyu yayi yana kallon halimatu,

“Kinga ummi ta manta bata yimin alwalar ba ta shige daki, ko zamuje kiyi min?”

“Toh, muje”

Murmushi yayi yace,

“Tabdijam ashe yau zan jima banyi sallar ba…”

“Saboda me?” Ta tambaya cikin mamaki,

“Saboda alwalar bazata zauna ba mutukar da tattausan hannunki akayi mai kamada auduga”

Murmushi tayi ta mike tafice bayan ta boye fuskarta, jiran ummi yayi harta fito sannan sukaje ta taimaka masa yayi alwalar yafita masallacin kofar gida wanda yanzu kusan duk yan layin nan suke zuwa suyi.

Sati uku ya dauka yana jinyar hannunshi kafin ya warke ras, sai lokacin yafara fita gareji da islamiyya, kasancewar bikin Abba da ummi yanata karatowa domin har anfara gyaran part din da zata zauna nan abba yace Aliyu ya tattare kayansa yakoma part din da zasu zauna shida halima wanda ke can gefe daya ta baya, halima ya kira domin ta tayashi, tana tayashi tana yimasa gwalo,

“Allah sarki yayana, ashe ankoreka daga daki, shikenan zaka koma can kai daya…”

Murmushi yayi ya kalleta,

“Allah sarki yarinya kwana nawane zamu zama mu biyu”

“Kaida wa kenan?”

“Nida matata mana”

Shiru tayi sakamakon wasu littattafai da ta ciro daga drewar,nafarko tafara dubawa, fa’idoji gameda jinin al’ada sai dayan magungunan cutukan da suka shafi mata a musulunci,

” Kinzo kina yimin bincike kina karanta min sirrina ko?”

“Darling brother kenan, wai kai meye hadinka da irin wadannan littattafan kaida ba maceba?”

“Saboda zan auri macen ai”

Tattara masa kayansa tayi tana duddubawa, wani taji kunya ma idan taga title din,da haka ta gama ta kinkima ta kai masa can part din ta shirya masa acikin dakin da zai zauna,

Saida ta gyara masa komai ta share dakin ta goge tasaka turaren wuta da air freshener sannan ta rufe ta fita domin shi har yajima a garejinsu.

Gyara aka yiwa ummi sosai a part dinta sannan Abba yabawa umma makudan kudi suka fita tare aka siyo mata kaya akwati biyar domin dagaske abba ke nufin mayar da ita amaryar gata, aranar da daddare kuma aka kawowa Aliyu sabuwar mota ta zamani yar yayi mai tsadar gaske,

Halima ya dauka suka fita d’ani zuwa cikin gari, kowa yaga motar sai yasake kallonta dan haduwarta.

Basu dawo gida ba sai dare bayan sun ziyarci wurare daban daban,

Azumi saura sati daya aka daura auren Abba da ummi akan sadaki naira dubu goma da kujerar hajji,

Duk da ba wani biki za agabatar ba amma ummi tayi dan jan kunshinta wanda tayi sunkube kafa da hannu ta kwana dashi sannan da rana ta caba ado cikin wani swiss lace coffee colour mai stones ajiki,

Ita kuwa halima kunshin da Aliyu keta yimata naci tasha alwashin yi awannan bikin na ummi da Abba,dayake khairiyya tazo tare suka tafi gidan kunshin akayi musu baki da ja sannan suka biya ta saloon, tun safe suka fita amma basu suka dawoba sai yamma bayan Aliyu yasha zaman jiranta har yagaji fita yayi saboda Abba ya aikeshi banki zai ciro masa kudi,

Su halima na dawowa wanka sukayi ta caba uban ado kamar itace amaryar tasa wata hadaddiyar shadda dark purple tasha dauri, dayake Abba ya shirya walima ya gayyato abokansa nan compound din gidan akayi decoration aka jera fararen kujeru domin abba har Malam lawan ya gayyato gun walimar a matsayin mai gabatar da wa’azi awurin walimar dama kuma shine ya daura auren,karfe biyar jama’a suka fara halarta makota da abokan arziki sai danginsu wadanda suka zo daga babban shiru maza biyar mata uku,

Agurguje Aliyu yakai sakon Abba dakin Abban yafita zuwa part dinsa domin har ankunna karatun alqur’ani yana tashi cikin kira’ar sheikh Ahmad sulaiman kano a manyan lasifikun da aka saka,wanka yayi yasa farar shaddarsa gezna kar dinkin half jamfa da hula yafito yana kamshi, lokacin da yazo wurin har mutane sun zazzauna bangaren mata daban suma maza suna daya bangaren,

Kujerar da aka ware musu shida Malam lawan yaje ya zauna akusa dashi domin shine zai jawa Malam din baki,

Saida Abba ya zauna shida tawagarsa sannan aka bude taro da addu’a daga nan aka fara gudanar da wa’azin,

Su halimatu iyayen biki ana can cikin gida itada khairiyya suna kaiwa da kawowa wurin ganin anyiwa baki kyakkyawar tarba, abincin da za aci suketa shiryawa suna badawa ana fita dashi,

Wani siririn gyale ta dauka purple kalar shaddar jikinta suka fita wurin walimar itada khairiyya suka fara bin mutane suna raba musu ruwa da juice masu tsananin sanyi,ita khairiyya na bawa mata itada wasu daga cikin yan aikin gidan yayinda halima ke rabawa maza itada masu bayin flower,

Wani saurayine wanda ya rako dad dinshi ya kafeta da ido baya ko kiftawa, Aliyu sai faman wuwwulla ido yake yana son hangota amma bai samu zarafin hakanba sai zuwa can ya ganota tana rabawa jama’a ruwa da lemo mayafinta akafada taci wani uban dauri, ba kadanba tayi kyau yau dinnan tamkar itace amaryar domin ga lalle tasha sannan ga kwalliya harda su kwalli,

Dai dai lokacin da taje gaban wannan saurayin ta mika masa Aliyu yasake maida hankalinsa wurin, rausayar da kai yaga saurayin yayi yana yimata magana……

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI….!*🤴🏻

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

_DEDICATED TO FIDDAUSI SODANGI_

 

*35*

 

***Bai iya dauke idonshi daga Kansu ba har halima tawuce layin da saurayin yake zuwa nagaba, wani abune mai masifar daci da nauyi yakaiwa zuciyarsa da makogwaronsa ziyara sakamakon ganin har lokacin idanuwan wannan saurayin na kan halimatu,

Alla alla yarinka yi ayi atashi daga walimar amma ba atashiba sai misalin karfe 6 da yan mintuna wato dab da magrib,

Halimatu na kokarin shiga ciki itada khairiyya taji ana yimata magana abayanta, juyawa tayi nan taga wannan saurayin na dazu yana yimata murmushi,

“Dan Allah yanmata minti biyu….”

Saida tayi damm saboda jin abinda yace sannan ta tsaya ita kuma khairiyya ta shige ciki,

“Wallahi ban taba kallon mace mai kyawunki ba…., ni sunana walid dan gidan Alhaji Abbas ne abokin dad dinki….”

“Nagode walid amma kayi hakuri domin inada miji wanda har ansanya mana date din biki”

“To tunda ba ayi bikinba ai inaga har yanzu inada sauran dama…”

Wani kallo tayi masa bata kai ga kara yin magana ba tahango Aliyu yana tahowa shida su umma, duk sai taji babu dadi saboda ganin yanda yanayin Aliyu ya sauya lokaci guda da ya hangota tsaye da wani,

“To dan Allah nidai kayi hakuri katafi, sai anjima” Tafada aduburburce,

“To kibani number dinki…”

“Banida waya….”

Tana kokarin juyawa yayi saurin riko mayafinta, atsorace ta fisge tana kallonsa,

“Menene haka? Nace maka banda waya”

Ciro tashi wayar yayi daga aljihu ya mika mata,

“To ga tawa nabaki kirinka amfani dashi”

Su umma ne suka zo suka giftasu suka wuce Aliyu ko kallonsu baiyiba yashige,

“Ni bazan karbi wayarka ba dan Allah kayi hakuri”

“To shikenan sunanki fa”

“Halima”

Daga haka tawuce tayi shigewarta ciki tanaji yana fadin,

“To shikenan zan dawo idan kin nutsu”

Tana shiga sukayi kicibus da Aliyu ahanya shikuma zai fito tsayawa sukayi dukkaninsu suna kallon juna, irin kallon da taga yana yimata yasata sunkuyar da kanta kasa taja mayafinta tana rufe jikinta, matsowa kusa da ita yayi dab,

“Kin kyauta, ki kalli dan gyalen da kika saka maza sunata kallonki….”

“Kayi hakuri bazan sake ba”

Da yatsanshi ya nuna mata kirjinta,

“Kalli kirjinki a bayyane kowa yana gani, kin kyauta kenan”

“Kai Darling brother me ake gani nida banda wani….”

“Ke kikasan haka amma shaidan yana kawata musu surarki”

Daga haka yawuce yabarta tsaye awurin duk da ta juya tana kiranshi bai ko juyo ba yayi tafiyarsa,

Tun daga wannan lokacin bata kara ganinshi ba sai washe gari da yamma sun fito itada khairiyya zasu fita shikuma ya shigo dawowarshi kenan daga gareji,

Ta cikin glass din motar ya zuba mata ido yana kallonta, sosai tayi masa kyau cikin fitted gown dinta ta atamfa dar blue mai hoton takalmi ajiki,

Yana kashe motar yaga tana tahowa wurinshi tana zuwa tabude gaban motar tashiga ta zauna tana dan taunar cingum ahankali,

Kallonta yayi yakawar da kanshi shikenan bai kara kallon side din da takeba, ita kam kallonshi kawai take domin kananan kayane ajikinshi sumar kanshi da gemunshi duk an gyarasu sunyi kyau da alama aski yaje yayi ayau,

“Darling brother, har yanzu baka huce bane?”

“Ni anfada miki dama nayi fushi ne? Badai kin samu saurayi ba mai sonki? Kije ki aureshi ni nabar masa”

Jin abinda yace yasa taji haushi ya turniketa bata tanka masa ba ta bude kofar motar tayi fitarta taje wurin khairiyya wacce ke tsaye jikin motarta tana jiranta, gidansu Sabira sukaje kamar yadda suka alkawarta mata cewar zasu je.

Yanda taga Aliyu ya koma miskilinshi irin nada can tun lokacin da ta sanshi itama saita kama kanta babu ruwanta dashi, kwana biyu kenan yau suna yar tsama gaisuwa kawai ke hadasu,

Dayake khairiyya tatafi yanzu saura ita kadai ya rage, tana falon umma kwance tana kallo awayarta mai gadi ya leko yace ana sallama da ita,

Batayi wani dogon maganaba ta dauki farin karamin gyalenta ta yafa akanta tafita,kamar yadda ta zata walid ne, yana zaune kan lilon dake runfar shakatawa, inda yake ta karasa itama ta zauna kallonta yake tana sanye cikin doguwar riga na material,

Duk da bata so zuwansa ba amma taji dadin hakan domin Aliyu yana gida tasan zai fito yagansu, ai kuwa ba ajimaba sai gashi ya fito daga part din ummi zai tafi nasa, ganin halima tana zance da wani abun ya tsaya masa arai sam bai san wanne irin kishi yake dashi ba akanta,

Part dinsa yawuce kasancewar alhamis ne kuma yana azumi, tunda yashiga daki ya kwanta bai fitoba har akayi magrib gashi shine yake jan salla a masallacin kofar gida amma shiru shiru, ita kanta ummi sai zuba ido take taga yazo yasha ruwa amma shiru,

Saida lokacin sallar isha yayi sannan Abba yashiga part din Aliyun, kwance yaganshi da wando three quarter babu riga ajikinshi ya dafe kansa,

Nan abba ke tambayarsa ko lafiya yace kansa ke ciwo,fita abba yayi zuwa part din ummi nan ta dauki magani da abincin shan ruwansa tanufi wurinshi shikuma abba yashiga part din umma,

Fitowar halima kenan daga dakinta taji abba na fadawa umma rashin lafiyar Aliyu, kawai ficewa tayi ta yi hanyar part din nasa,

Lokacin da taje ummi na kansa yana zaune yana shan kunu, ko kallonta baiyi ba saima kara daure fuska da yayi kamar yadda yake yimata ada, kamar tajuya saboda ganin babu riga ajikinshi amma tadaure tashiga tana yiwa ummi ya mai jikin,

Kara ummi tayi mata tafita daga dakin tabarsu iya shida ita, kallonta yayi tayi saurin sunkuyar da kanta,

“Tashi ki fita daga dakin nan…..” Yafadi bayan yaja riga zai rufe jikinshi,

“Dan Allah kayi hakuri yaya Aliyu, bazan karaba Allah”

Harararta yayi,

“Ki kalli jikinki amma dazu ahaka kikaje wurin saurayi ko?”

Sake sunkuyar da kanta kasa tayi shikuma hakan yabashi damar kallonta,

“Kayi hakuri bazan kara ba”

“Naji”

Duk da yace mata ya hakura amma bai sakar mata fuska ba har tsawon kwana biyu sai ana igobe azumi sannan tasamu kansa har sukayi hira sosai cikin wasa da dariya,

Kowannensu cikin farin ciki ya kwana washe gari aka tashi da azumi banda halima domin ita ulcer dinta tayi tsananin da bazata iya azumi ba sai dai ta ciyar,

Karfe 10 tatashi tayi wanka ta shiga kitchen zata dafa indomie saboda wata yunwa takeji,

Tana zuba indomie din Aliyu yashigo dama tunda yaji kamshi a kitchen yasan itace,

“Gandiya,sahur za ayi?”

Murmushi tayi ta rufe tukunyar ta juyo tana kallonsa yayi kyau cikin manyan kaya harda hula,

“Ina zakaje da sassafen nan?”

“Malam ne ya kirani wai inje yau zamu bude wa’azin mata wanda mukeyi duk shekara”

Zumburo baki tayi,

“Nidai Allah idan kaje mata kallonka zasuyita yi kilama har da yan mata aciki”

Murmushi yayi ya jingina da jikin bango,

“Karma wannan ya dameki, nida nakeda kyakkyawa kamarki wacce macece zata burgeni awaje? Kinfi kowacce mace kyau a idona”

Murmushin jin dadi tayi tace,

“To Allah ya dawo dakai lafiya”

“Amin, umma tatashi?”

“Inajin bata tashiba dan banji motsinta ba”

“Duk gidan ke kadaici kika tashi kenan,dan ummima bata tashi ba”

Daga haka yajuya yatafi, tun da aka fara azumi ya zama busy basa samun lokacin hira da halima domin da safe suna tafiya wa’azin mata da yamma kuma suyi na maza yana dawowa kuma lokacin shan ruwa yayi gashi shike jan yan unguwar salla har sallar tarawih, duk da haka kayan shan ruwansa daban halima ke shirya masa sai bayan yadawo daga sallar tarawinne suke samun lokacin hira.

Akwana atashi har azumi ya dauko gangara domin saura guda goma ayi salla nan shirin bikinsu yatashi,makudan kudi abba yabashi domin ya hada mata lefe,

Shida itane ke zuwa suna zabo kayan da yayi musu, dakansu suka hada komai da komai,akwatina 24 kamar na amare 4 ba daya ba,dauke kanshi yayi lokacin da yaga tana dauko braziers, bayan tagama zaba ya karba domin kaiwa wurin biya,aranshi yana cewa dama kin dauko wadanda sukafi wadannan domin babu jimawa zasuyi miki kadan.

Ana igobe salla duk takai kayan dinki,dawowarta kenan ta tarar da khairiyya tazo, zama tayi afalo ita kuma khairiyyan na salla, dakin ummi ta leka itama sallar take dan haka tadawo falo ta zauna, tana zama Aliyu na shigowa,

“Ina umma?”

“Salla take yi”

Zama yayi akusa da ita,

“Kowa yana salla banda ke”

“To ni nayi tawa ai”

“A ina? Bayan yanzun nan naga shigowarki fa”

Murmushi tayi ta kalleshi,

“To nidai ya isa haka…”

Murmushin shima yayi nan khairiyya ta taso tana tsokanarshi tana fadin,

“Kaga ango, ango kasha kamshi”

Tashi yayi yafita bayan sun gaisa da khairiyyan,

Daki khairiyya taja halima ta ciro mata katuwar jakar da takawo mata kananan kaya na kece reni ganin kayan yasa halima duk kunya ta kamata saboda ganima take kamar bazata iya saka wadannan kayan agaban Aliyu ba,saida suka gama adana kayan suka boye sannan suka fita wurinsu umma wadanda ke can sunata soye soye da dafe dafe na abincin gobe.

Washe gari takama ranar salla, da wuri suka tashi sukayi wanka sukayi shirin masallaci, hijabin umma duk suka aro suka fita, Abba shima har yafito yana jiran Aliyu yazo su tafi, suna tsaye yafito cikin danyen boyel dark blue da hula yana rikeda dadduma,

Gaba dayansu a motar Abba suka tafi masallacin, Aliyu sai kallon halima yake ta cikin mirrior domin shine yake driving din itama sai satar kallonshi take saboda kyawun da yayi da zarar sun hada ido saisu sakarwa juna murmushi.

Bayan an idar da salla suna dawowa gida suka iske har bakuwar umma tazo daga borno wacce aka daukota musamman domin gyarawa Sadiya jikinta,

Aranar ya gana tafara aikinta na gyaran jikin halima, gida kuwa tuni anfara gyare gyare domin zuwan bikin, biki yarage saura kwana biyar Abba yace suje su zabo funitures, tareda umma da Sadiya da Aliyun da khairiyya suka tafi wani kamfanin da ake sayarda kayan daki,Aliyu sai satar kallonta yake dayake tana kusa dashi saboda gaba daya fatarta ta sauya sai wani sheki take tana daukar ido tayi luwai luwai,

Wani tamfatsetsen gado Sadiya ta zaba mai mutukar kyau kudinsa ya doshi miliyan daya zuwa da rabi.

Su umma ne suka zabi sauran gadajen guda biyu kasancewar dakunan guda ukune,

Kiran Aliyu halima tayi domin yaga gadon nan yazo yana gani, gadon ba karamin haduwa yayi ba gashi kusan gaban gadon madubine ta ko ina,

Murmushi Aliyu yayi yajata suka koma gefe suka bar wurinsu umma, kallonta yayi na wasu yan mintuna kafin yayi magana,

“Halima wannan gadon menene fa’idarshi?”

“Yaya Haidar ai yanada kyau sosai, ko kai bai burgeka bane?”

“Ya burgeni mana amma kin lura da abinda na lura dashi? Duk jikinsa fa mudubine?”

“To kuma Darling brother menene?”

“To yanzu idan zanyi jima’i dake da rana Sadiya haka zamu rinka kallon junanmu ta jikin mudubin?”

Kunya maganarshi tabata shiyasa tayi saurin juya masa baya,

“To sai acanja wani tunda baiyi ba”

“Yawwa masoyiyata, asauya kinji, wancan baiyi ba sam”

“Toh..”

Bata bari tajiyo sun kara hada ido dashiba tawuce takoma wurinsu umma, sabon zabe suka sake itada khairiyya ta zabi royal bed dan gasken sannan suka gangara wurin kujeru, duk kayan nata light purple ne, bayan anbiya anyi komai ne suka shiga mota suka tafi domin za akawo musu kayan har gida, ko ahanya ma halima kin yarda su hada ido da Aliyu tayi domin wata matsananciyar kunyarshi takeji sai dai kuma tunda bikinnan yagabato take jin wata irin faduwar gaba wacce bata San dalilinta ba……

 

_Gaisuwa mai tarin yawa ga members na d’an asali fans group,& kundin haske group members._

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

 

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

_DEDICATED TO FIDDAUSI SODANGI_

 

*36*

 

***Dafe kirjinta tayi da hannunta domin ya tsananta faduwa fiyeda dazu,

Lokacin da suka je gida Aliyu tsayar da ita yayi, zama tayi acikin motar batare da ta kalleshi ba,

“Darling brother baka fa bani invitation cards dinnan ba har yanzu”

“Zan baki ai badai anbugo ba, saurin me kikeyi ne?”

“A’a ni ba sauri nakeba bana sone mutane suga ba akai musu da wuri ba…”

Kula da yanayinta yayi ya fahimci halin da take ciki, fuskantarta yayi sosai yana kallonta,

“Wai meke damunki ne? Naga kamar bakida lafiya”

Sai lokacin ta kalleshi,

“Wallahi gabana ne yake faduwa sosai kuma kamar na yau ma yafi na kullum Allah dai yasa ba wani abune zai faru daniba”

Murmushi yayi yabude wani dan akwati dake gefenshi ya ciro invitation cards,

“Babu abinda zai faru dake Malama…”

“Allah yaya Aliyu dan bakaji yanda nake ba, taba kirjina fa kaji zuciyata kamar zata fito dan bugu”

“Babu komai dama kusan kowacce amarya haka takeji ai lokacin bikinta amma matsalar bakwa addu’a ne halima, ko dan azkar dinnan na tashi daga bacci da na kwanciya bacci duk mantawa kuke dasu kuyita harkokinku, yanzu ke yaushe rabonki da kiyi azkar din kwanciya bacci da natashi daga bacci?”

“Ni wallahi dama ban haddace shi da ka ba….”

“To ko da littafin basai ki dage ki rinka karantawa ba, kirinka yawaita addu’a babu abinda zai sameki, yanzu ungo invitation cards din, karbi”

Karba tayi ta dauki guda daya ta karanta take fuskarta ta canja ta kalleshi,

“Darling brother menene haka?”

“Mefa?” Ya bukata,

“Amma dai ai nace maka events guda biyar zanyi ko? Nace maka akwai kamu (sa lalle), sannan nace maka zamuyi fulfulde day, zamuyi picnic evening, sannan zamuyi mothers night sai dinner party…, amma banga ko guda daya ananba, kamu da walima da yini kadai nagani”

“Yanzu halima duk wadannan abubuwan da kika zayyano a wannan bikin za ayi? Haba halima nifa wallahi bama na zuwa party balle wani dinner…”

Akufule tajuya ta kalleshi hawaye har sun soma diga daga idanuwanta,

“Amma ai lokacin da nafada maka ka amince bakace min a’a ba ko? Kuma dan kai baka zuwa ni ina ruwana, ai tun wuri sai kafada min baza kaje dinner din bikinmu ba inyaso ni sai inyi ladies night ni kadai da kawayena…., kai komai sai ka hana ko kace zaka yiwa mutum wa’azi, yanzu dazu gado na zaba kace wani kaza da kaza nayarda nabi abinda kake so kai meyasa baza ka rinka bin abinda nake so ba? Ga invitation cards dinka nan bana so kaje kayi abinda zakayi dasu, kamun ma da walimar basai anyiba kawai adaura aure akaini basai kowa yazo bikin ba….”

Jefa masa invitation cards din tayi zata fice daga cikin motar, karo nafarko da yayi yunkurin tabata ya riko hannunta domin yayi mata bayani amma taki ta fincike tana kuka ta nufi cikin gida, dama abinda yake gudu kenan shiyasa tun farko yaki bugo invitation cards din dawuri domin magana ta gaskiya duk wadannan events din da takeso ayi shi bashida ra’ayin ko guda daya aciki shi ra’ayinsa kawai adaura aure suyi walima aci asha shine kawai burinsa, tattara katinan yayi shima yafito yashiga cikin gidan,

Halima da kuka ta shiga gida, umma da ummi na falo suna shirya wasu frames acikin babban kwali, khairiyya na gefe tana hada wa halima maganin da ya gana take bata kullum wanda ake hadawa da kindurmo, ganinta sukayi tashigo da kuka bata yiwa kowa magana ba tawuce bedroom dinta umma na kiranta amma bata amsaba,

Khairiyya ce tabi bayanta ta sameta kwance kan gado tana kuka, zama tayi gefenta,

“Sadiya meya faru?”

Tashi tayi hawaye face face fuskarta ta kalli khairiyya,

“Umma khairiyya kiji wulakancin da Aliyu yayi mana fa wai baza ayi dinner ba baza ayi komai ba sai iya walima kadai bayan har ankon dinner din muka raba…”

“Kema dama kin san ba lallai yabarki ba tunda kinfi kowa sanin mijinki ustaz ne, sai kiyi hakuri kawai”

“Wallahi bazan hakura ba, shi komai sai ya hanani, wallahi bazai yuyu ba, yanzu kamar ni ace bikina ba ayi ko ladies night ba gashi babu dinner…”

Dai dai nan ummi da umma suka shigo cikin dakin,

“Wai meyake faruwa ne?” Umma ta tambaya,

“Umma ba Aliyu bane, waifa cewa yayi wai babu abinda ya za ayi na shagalin biki sai iya walima kawai da wuni, ni wallahi bazan yarda ba…”

“To kuma shine me? Dole ne dinner din ko kuwa idan ba ayi picnic din ko ladies night ba fasa auren za ayi?” Umma tafada cikin fada,

“A’a karfa kiga laifinta ita kadai shima yanada laifi kuma zaizo ya sameni…” Ummi tafada, tana rufe baki saiga Aliyun yashigo hannunsa rikeda invitation cards,

“Umma…., Ummi… Am dama”

Ummi bata barshi ya rufe bakinsa ba ta katse shi,

“Kai Aliyu me kayiwa yarinyar nan take kuka? Kai kuma haka zakayi naka yayin? Wannan nuna iko har ina? To baka isaba yarinya zatayi dukkan abubuwan da ta shirya itada kawayenta inyaso kai kar kaje, ince shikenan?”

Kallon ummi yayi ya sunkuyar da kanshi kasa,

“Ummi kiyi hakuri ni wallahi ba hanata nayiba kawai dai banida ra’ayin wadannan bidi’o’inne a bikina…”

“Jeka abinka Aliyu, Allah yayi maka albarka, kuma tunda baka so to ina mai tabbatar maka da baza ayi wadannan events dinba kuma har Alhaji sai nafadawa wannan maganar…” Umma nagama fadin haka ta karbi invitation cards din hannunshi ta mikawa khairiyya tana fadin,

“Gashi nan idan kun gadama ku raba idan kuma baku gadama ba kubarshi karku gayyaci kowa kuma hakan bazai sa mufasa daura muku auranba idan ranar tazo” Daga haka tafice tabar dakin, harara ummi ta zabga masa yayi saurin yin kasa da kanshi, dagota Ummi tayi ta fara rarrashinta,

“Yi shiru yata kinji, share hawayenki babu wanda zai hanaki yin shagalin bikinki kinji”

Daga kai tayi ta share hawayenta nan ummin tafice, gaban gadon yakarasa ya zauna ganin haka yasa khairiyya tashi itama tafita da invitation cards a hannunta.

Ko kallonshi kin yarda tayi tai saima bata rai da tayi ta cuno baki tana hararar gefe,

“Haba halima na, menene abin yin kuka anan? Dan Allah ki fahimceni kinji….”

Sauka tayi daga kan gadon tawuce toilet tabarshi zaune anan, murmushi yayi yatashi ya fita,

Da bacin rai ta wuni har yamma, tana jin abba yadawo taje takai karar Aliyu ta fada masa abinda yafaru amma ga mamakinta koda abban yakira Aliyu harda su umma sai duk suka goyi bayansa ummi ce kadai ta goyi da bayanta nan abba ya kashe magana yace party da dinner da wani picnic baza ayisu ba tunda ango baya so dan haka suje su raba katinsu haka,

Wasu sababbin hawaye takeyi ta tashi tabar falon Abba ko kallon Aliyu bata yiba, tashi shima yayi yabi bayanta yana kiranta tayi banza dashi tawuce, daf da zata shiga part din ummi yasha gabanta, kamar jira take ta fashe da kuka,

Kallonta yasoma yi yana jin kukan nata har cikin ranshi zuciyarshi na amsawa,

“Zo muje falon ummi inyi miki bayani, dan Allah ki saurareni one love, zo muje kiji”

Gegareshi tayi tawuce zuwa ciki, tana shiga falon ummi ta fada saman doguwar kujera ta soma kuka harda majina, zama yayi gefenta yayi shiru yana sauraron kukan nata, saida ta tsagaita sannan yafara magana ahankali,

“Halima na dan Allah kiyi hakuri ki fahimceni, nifa gadon nan da nahanaki siya wallahi illar hakan nahango, kin dai san madubi daya daga cikin wurin zaman shaidanu ne ko? To meye fa’idar muzo muna rayuwar auratayya kusa da shaidanu? Kila ma su shafemu ko su shafi yaron da zamu samu, Amma kiyi hakuri tunda bakiji dadin hakan ba,

Sannan duk wadancan events din da kikayi niyyar yi babu fa guda daya wanda za ace Allah yace annabi yace, shin kina sone auren namu yazama marar albarka? Yawaita bidi’o’i a harkar aure wallahi sune suke kwashe albarkar auren domin angayyato shaidan da tawagarsa sun bada muhimmiyar gudun mawa,anyi bushasha,anyi kade kade da raye raye da sauranabubuwa marassa kyau shiyasa sai kiga ko anyi auran ankasa samun farin ciki da zaman lafiya,dan Allah kibar maganar su dinner party dinnan….kuma kiyi hakuri…. Sannan ki yafe min kukan da nasaki”

Juya masa baya tayi har tana bugeshi,bata tanka masa ba sai sharar kwallarta take har khairiyya ta shigo cikin falon domin taje su tafi rabon invitation din,

“Umma khairiyya kawai kuje ku raba, ki duba dakina mukullin motata yana nan sai ki biyawa Sabira kutafi tare ita tasan wadanda yadace ku kaiwa”

“To shikenan ga abinki” nan ta mika mata cup din dake dauke da tukudi aciki,kawar da kai Sadiya tayi,

“Bazan sha ba”

“Khairiyya kawo nan, zata sha”

Bashi tayi tajuya tafita nan ya zubawa tukudin ido yana son yayi magana amma yana tsoro domin dama abirkice take to inaga ya sake tsokanota,

Sauko da kafafunta kasa tayi tawuce dakin ummi taje ta kwanta domin kanta ciwo yake yi mata……

 

_D’an Asali fans daga yau bazaku kara ganin sabon post ba har sai kunyi comments adadin da bazai lissafu ba._

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI….!*🤴🏻

 

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

 

_DEDICATED TO FIDDAUSI SODANGI_

 

*39~40*

 

***Shine agaba tana biye dashi abaya sai faman rusar kuka takeyi kamar zata karar da hawayenta,

Dai dai lungun da zai sadasu da part dinsu ya tsaya yana jiranta, nan ta karaso tana lullube da mayafinta,hannunta mai masifar taushi ya kama hakan yasata kara sautin kukan da takeyi, shi kansa karfin haline kawai amma ji yake tamkar shima yayi kukan,

Bude kofar falon yayi suka shiga ciki sannan ya mayar da kofar ya rufe harda murza key, cikin bedroom dinta wanda ya kawatu da kayan alatu ya nufa da ita,inbanda kamshi babu abinda falon da dakin nata keyi,

Agefen gado ya zaunar da ita shima ya zauna,

Tagumi ya rafka yana sauraron kukanta dake fita ahankali, sunfi minti ishirin ahaka kafin ya nisa ya cire tagumin nashi ya kalleta,

“Wai wannan kukan jin dadi kikeyi ne ko me?”

Bata amsa masa ba taci gaba da kukanta,

“Uhmmm? Nace kukan jin dadi kikeyi ko? Mata nawane suka tafi wata kasar ma kawai ata sanadiyyar aure? Sai ke da agida ma kike shine zaki zauna kina kuka? Tashi to kije kiyi alwala kizo muyi salla”

Saida ta danyi kuka ta goge fuskarta sannan ta amsa masa,

“Ni inada alwala ta ban jima da yin salla ba”

“Kinada alwala? Tsawon awa nawa yanzu? Haba halima mata fa basa rike alwala,ki daure kidai sake wata inyaso ma idan kinada waccan din bata karyeba shikenan kin samu Karin haske saboda alwala akan alwala haske ne akan haske inji annabi”

Tashi tayi tana kuka tashiga bathroom, da kallo yabita har ta shige, mintuna kadan ta fito lokacin har ya shimfida musu abin salla,

“To tsaya abayana zamuyi salla raka’a biyu”

Kamar yadda yace haka tayi ta tsaya daga bayanshi yajasu salla raka’a biyu,

Bayan sun idar ne ya juya ya kalleta, har lokacin hawaye basu bar zuba daga idonta ba, hannunshi ya dora akanta yayi addu’o’i sannan ya shafa,

“Halima kibar kukan nan inkawo miki abinci kici nasan kina tareda yunwa”

Girgiza kai tayi alamun bazata ciba,

“Kaza ce fa sai madara, bazaki ci ba?”

Daga kai tayi, bai kara magana ba yatashi yafita, gefen gadon ta tashi takoma ta zauna taci gaba da kukanta,

Bai wani jimaba yashigo dauke da glass cup da madara aciki sai flate mai dauke da gasasshiyar kaza mai romo,

Zama yayi akusa da ita yajawo dan karamin glass table din dake gefen gadon ya dora kayan akai,

Kafadarta ya riko yajata zuwa jikinsa yasoma bubbuga bayanta ahankali alamar rarrashi,

“Kukan ya isa haka one love…., sorry, daina kuka, ya isa haka….maza karbi abinci kici,khairiyya tafada min rabonki da abincin kirki tun ranar da aka fara bikin nan…, kinga kuma kinada ulcer idan yunwa tayi miki yawa tashi zatayi…,sorry… Yi shiru…., kiyi hakuri kinji”

Dakyar ta iya yin shiru, yana rungume da ita ajikinsa ya dauko naman yabata yasa mata abaki, daurewa tayi ta karba ta taune nan yaci gaba da bata tana kwance a kirjinshi, kanta ta kawar zuwa cikin tsakiyar kirjinshi alamun ya isheta haka, cup din dake dauke da madara ya dauka yabata tasha rabi amma bai amince ba saida yasake saka mata ta shanye gaba daya,

Sakinta yayi ya tashi ya kwashe kayan zuwa kitchen yadawo, abun mamaki abun dariya sai yasake zuwa ya isketa tana kuka, kayanshi ya shiga cirewa yana murmushi,

“Lallai yarinyar nan dadin kukan kike ji…”

Daga haka yawuce bathroom, wanka yayi ya fito daga shi sai gajeren wando yazo yahaye gado ya kwanta yana kallon agogo, karfe 12 daidai agogon ya nuna,tarin pillows din dake kan gadon yafara turewa wadanda suka doshi guda 12 koma fiyeda haka,

“Ki tashi kije kiyi wanka kizo ki kwanta, wai ko bakya jin barcine?”

Shiru tayi masa taci gaba da shasshekar kukanta,

“Bakiji abinda nace bane?”

“Ni nayi wanka dazu”

“To matso ki kwanta”

Can karshen gadon ta lallaba ta kwanta, matsawa kusa da ita yayi ya yaye mayafin da ta tukunkune dashi, ya dagota,

“Bari inrage miki kayan nan yanda zakiji dadin barcin, kina ji ana zafi amma ke kina kokarin laftawa jikinki kaya…”

Jin ya kamo rigarta yasata tsananta kukanta tana kokarin kwacewa, wutar dakin ya kashe duhu ya mamaye dakin,

“To tsaya incire miki kinga ai yanzu babu hasken bazan ganki ba…”

Dakyar ta aminta ya cire rigar amma zani fur taki yarda, kyaleta yayi ya kwantar da ita awurinda ta kwanta da farko,

“To shikenan kwanta kiyi baccin but don’t forget to pray….”

“Uhumm” Tace tana gyada kai kamar kadangaruwa,

Daga haka ta kwanta yayinda shi kuma ya matsa can gaba shima ya kwanta bayan ya tura mata pillow guda daya,

Tana jinshi yayi addu’a ya shafa, bata iya bacci ba saida ta tabbatar da cewar bacci ya daukeshi. Cikin dare ya farka daidai lokacin da ya saba gudanar da sallar nafilarshi amma yau kam baya jin zai iya tashi domin yana bukatar baccin kasancewar agajiye yake, split yatashi ya rage ya kashe fanka sannan ya koma kan gadon, phone dinshi ya dauka ya haskata ta hasken kan screen din wayar, a tukunkune yaganta alamar tana jin sanyi, murmushi yayi saboda abinda taketa boye mishi dazu yanzu gashi nan afili, duvet yaja ya lulluba mata sannan ya kwanta kusa da ita yadora kanshi saman pillown da kanta ke kai,babu jimawa bacci yasake gaba dashi bashi ya farka ba sai 5:56 a.m,

Tashi yayi zaune ya kalli halima wacce ke lullube tanata bacci, sauka yayi zuwa toilet yayi alwala sannan yafito ta gefen kanta ya tsaya yadan sunkuya ya soma tashinta, bude ido tayi ta kalleshi take ta tuna da a inda fa take, yamutsa fuska tayi kamar me shirin yin kuka.

“To sarkin kuka atashi ayi salla…”

Yunkuri tayi zata tashi sai kuma tafasa saboda tunawar da tayi babu riga ajikinta”

Turo baki tayi tana harararshi,

“Ina kasa min rigata?”

“Oho….,ko kin bani ajiyane?” Yabata amsa bayan ya bude closet dinsu, jallabiya ya dauko milk colour ya zira ya juya ya kalleta, har lokacin bata da niyyar tashi tana nan akwance lullube,

“Wai ko ba zakiyi sallar bane inyi tawa ni daya?”

Abin salla ya shimfida yatada sallarshi saboda ganin lokaci nata kurewa, saida taga yayi sujjada sannan tayi maza ta tashi ta dauki rigar wacce ke can karshen gado ta fada toilet, brush tayi dafarko kafin tayi alwala sannan tawanke fuskarta da sabulu kafin ta fito daga cikin bathroom din, kwance ta hangoshi saman gado ya kunna wayarshi yana sauraron karatun alqur’ani suratul yunus cikin kira’ar sheikh Abdurrahman sudais,

Closet tabude ta ciro wani zurmemen hijab Wanda tasan aikin Aliyu ne, sallar itama tayi bayan ta idar ta tashi tana nade abin sallar, satar kallonshi tayi taga idanuwanshi alumshe kamar mai yin bacci, hijabin ta cire ta mayar wurinda ta daukoshi sannan ta lallaba ahankali kamar marar gaskiya ta hau kan gadon ta kwanta domin baccin bawai dama isarta yayiba domin acikin dar dar tayishi.

Yana jinta duk abunda take domin ba barci yake yiba amma ya kyaleta, babu jimawa bacci yayi gaba da ita, shima sama sama yakejin karatun da yake saurara bacci yayi nasarar daukeshi wanda bashi ya samu ya tashi ba sai 10 nasafe daidai, wayarshi ya dauka ya jona a charge sannan ya shiga wanka, tun yana cikin bathroom yake jin ana knocking din kofar falonsu wannan dalilinne yasashi yin gaggawar fitowa, window ya leka nan ya hango baba tabawa ce mai aikin umma, jallabiyar da ya cire yazira ya fita ya bude mata bata yarda ta shigoba suka gaisa ta bashi warmers din dake hannunta guda uku tajuya ta koma, mayar da kofar yayi ya rufe ya kai kayan kan dining ya ajiye, bedroom ya koma yacire rigar jikinshi yaje gaban mirror, ta mirror din yake hangota tana yin firfita da hannunta guda daya alamun zafi takeji,gaban gadon yaje ya sunkuya yana kallonta ta dan soma hada zuffa, karamin towel din dake hannunshi yasa yagoge mata goshinta zuwa wuyanta sannan ya matsa, fanka ya kunna yakaro mata karfin air condition din dake cikin dakin duk a lokaci daya.

Cigaba yayi da shirinsa bayan yagama shafa mai ya dauki cumb yana gyara sumarshi zuwa gemunsa,

Saida yagama shafe jikinsa da turare sannan ya nufi wurin kayansu, duk abinda yake yi halima na kallonshi domin tun lokacin da baba tabawa ta soma bugun kofarsu ta farka,

Wani purple din material na maza taga ya ciro marar nauyi dashi mai tsananin kyau kuma shara shara, farar vest yasaka aciki sannan ya saka kayan wanda tsayin rigar iya cinyarshi ne haka tsayin hannun ma iya gwiwar hannunshi ne,

Gaban mirror yasake komawa yafesa turaren lailatul abyad da black oud,

Inda halima ke kwance ya nufa domin so yake ya tasheta tayi wanka taci abinci, kamar me baccin gaske haka tayi zama yayi agefenta yakai hannu saman fuskarta juyawa tayi tabashi baya, dan kwalin kanta ya gyara mata yakai hannunshi kan kunnenta yana magana ahankali,

“One love wannan earrings din ai sai su cimiki kunne…mantawa nayi jiya da daddare ban cire miki ba saboda duk kin rudani da kukanki…..”

Ahankali ya cire dan kunnen kasancewar mai barima ne, juyota yayi ahankali ya cire mata dayan yana kallon kyakkyawan hannunta wanda yasha kunshi gwanin ban sha’awa,fuskarta ya kalla yana shafar kunshin hannun nata,

Tashi yayi yafita daga bedroom din, sauran bedrooms din guda biyun duk yabi ya lalleka sannan ya rufesu ya shiga kitchen,

Electric cattle ya ciro daga kwalinta ya dauraye sannan ya jona ruwan zafi, yana tsaye ruwan yatafasa ya ciro tea flask babba shima ya dauraye shi sannan ya juye ruwan zafin aciki yafita yakai kan dining,

Kitchen ya sake komawa ya dauko musu flate guda biyu da spoons sai cups duk ya dauraye ya ajiye agefe, flate din da sukayi amfani dashi da cup jiya da daddare ya wanke ya ajiyesu a wurin da aka tanadar musu,

Flate da spoons din da yawanke da farko ya dauka yafita zuwa kan dining,kayan tea wadanda ya hado musu jiya ya cicciro ya kawo kan table din,warmers din da baba tabawa takawo ya soma dubawa dan ganin abinda ke ciki, nafarko wainar shinkafa da sinasir ne aciki, dayan kuma miyar agushi ne aciki sai na karshen farfesun kafar saniya,

Tea ya hada sannan ya zuba farfesun kadan a flate ya dauki bread yayi bisimilla yasoma ci,

Tashi yayi bayan ya kammala yakoma bedroom din ya dauko wayarshi da laptop yadawo falon domin har lokacin halima bata tashi ba wani baccin ta koma,

Sai 11 tatashi hamma tayi tai mika tatashi zaune, Aliyu ta hango yana kokarin ciro charger din laptop dinshi daga cikin jakar adana laptop wacce ke cikin drewar din mudubinta,

Gunta yanufa bayan ya dauki charger din,

“Ba mika zakiyi kiyi shiru ba madam, addu’a zakiyi sai ki wuni cikin farin ciki, kice Alhamdulillahil lazi ahyana ba’ada ma amatana wa ilaihin nushur….”

Maimaita mata yayi tana fada, wucewa yayi yafita daga cikin bedroom din bayan tagama maimaita addu’ar, murmushi tayi tabishi da kallo saboda sosai taga yayi kyau ya fito a angonshi sak, gaban kofar toilet taje taja towel dake rataye a kofar bathroom din tashiga wanka, sai da ta kara yin brush bayan tayi wankan sannan tafito,

Kwalliya ta zauna tayi sannan ta gyara gashinta wanda ba wani mai yawa bane asalima dakyar yake yin packing, ribbon tajera wurin guda hudu sannan ta tashi, turarenta da yagana tabata ta ciro ta shafe jikinta take dakin ya kaure da kamshi, wani leshi ta ciro wanda akayi mata dinki fitted riga da skirt kalar ruwan kwai, sarka da dan kunne ta saka bayan ta saka kayan sannan ta saka bangles duk golden,

Jikinta tabi da turaren smart lady sannan ta fesa bakhur,

Kan bed din da suka kwana taje ta gyarashi tsaf ta maida pillows din ta jeresu ta dauko flat shoe kalar kayanta ta saka ta fita,

Kishingide ta ganoshi afalo yasa laptop agabanshi yana bin karatun dake tashi ahankali daga cikinta,

Jin fitowarta yasashi daga kai ya kalleta, murmushi ne ya subuce masa saboda ganin irin kwalliyar da tasha ga dinkin jikinta yayi mata cacas sai kace ba itace ta kusan kwana tana kuka ba.

“Ina kwana?….” Tace dashi tana wucewa zuwa dining table,

“Haba one love har yanzu fushinne ba ahuce ba?”

Tea ta hada ta debi farfesun ta zauna taci, wurinshi ta dawo bayan ta gama ta zauna akan kujerar dake makwabtaka da tashi,lumshe idanuwanshi yayi sakamakon daddadan kamshinta da ya kawowa hancinsa sumame,

“Sadiyayye na wai har yanzu fushinne? Ke kuwa ki huce mana, haba aminiyata….”

“Ai darling brother wallahi kaima kasan abinda kayi baka kyauta ba, ko ladies night fa kin barina inyi kayi, ni wallahi ka kwafsa min”

“To ai nabaki hakuri ai, idan kin haihu zamuyi dinner din, ke duk haihuwa ma sai munyi, shikenan?”

Murmushi tayi batare da tayi magana ba, lekawa tayi kan screen din laptop din domin ganin abinda yakeyi nan ta hango bulugul maram yake saukewa na marigayi sheikh ja’afar, tv tace ya hada mata zatayi kallo nan yatashi ya hada mata ya kunna, tashar zee world ta kamo ta mike tana kallo shikuma yana yan bincike bincikensa a internet na littattafan addini wanda yayi masa sai ya sauke da haka har 12:50 tayi, kashe laptop din yayi ya mike tsaye,

“Leematu na zanje salla azahar tayi”

“To,saika dawo,Allah ya kiyaye hanya”

Bedroom yawuce ya dauro alwala ya fito yana cemata itama tatashi tayi salla kafin ya dawo, kofar yabude yafita, bai jima da fitaba itama tatashi tayi salla, wata kwalliyar ta sake tsantasarawa sannan ta koma falo ta zauna…..

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI….!*🤴🏻

 

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

 

_DEDICATED TO FIDDAUSI SODANGI_

 

*39~40*

 

***Shine agaba tana biye dashi abaya sai faman rusar kuka takeyi kamar zata karar da hawayenta,

Dai dai lungun da zai sadasu da part dinsu ya tsaya yana jiranta, nan ta karaso tana lullube da mayafinta,hannunta mai masifar taushi ya kama hakan yasata kara sautin kukan da takeyi, shi kansa karfin haline kawai amma ji yake tamkar shima yayi kukan,

Bude kofar falon yayi suka shiga ciki sannan ya mayar da kofar ya rufe harda murza key, cikin bedroom dinta wanda ya kawatu da kayan alatu ya nufa da ita,inbanda kamshi babu abinda falon da dakin nata keyi,

Agefen gado ya zaunar da ita shima ya zauna,

Tagumi ya rafka yana sauraron kukanta dake fita ahankali, sunfi minti ishirin ahaka kafin ya nisa ya cire tagumin nashi ya kalleta,

“Wai wannan kukan jin dadi kikeyi ne ko me?”

Bata amsa masa ba taci gaba da kukanta,

“Uhmmm? Nace kukan jin dadi kikeyi ko? Mata nawane suka tafi wata kasar ma kawai ata sanadiyyar aure? Sai ke da agida ma kike shine zaki zauna kina kuka? Tashi to kije kiyi alwala kizo muyi salla”

Saida ta danyi kuka ta goge fuskarta sannan ta amsa masa,

“Ni inada alwala ta ban jima da yin salla ba”

“Kinada alwala? Tsawon awa nawa yanzu? Haba halima mata fa basa rike alwala,ki daure kidai sake wata inyaso ma idan kinada waccan din bata karyeba shikenan kin samu Karin haske saboda alwala akan alwala haske ne akan haske inji annabi”

Tashi tayi tana kuka tashiga bathroom, da kallo yabita har ta shige, mintuna kadan ta fito lokacin har ya shimfida musu abin salla,

“To tsaya abayana zamuyi salla raka’a biyu”

Kamar yadda yace haka tayi ta tsaya daga bayanshi yajasu salla raka’a biyu,

Bayan sun idar ne ya juya ya kalleta, har lokacin hawaye basu bar zuba daga idonta ba, hannunshi ya dora akanta yayi addu’o’i sannan ya shafa,

“Halima kibar kukan nan inkawo miki abinci kici nasan kina tareda yunwa”

Girgiza kai tayi alamun bazata ciba,

“Kaza ce fa sai madara, bazaki ci ba?”

Daga kai tayi, bai kara magana ba yatashi yafita, gefen gadon ta tashi takoma ta zauna taci gaba da kukanta,

Bai wani jimaba yashigo dauke da glass cup da madara aciki sai flate mai dauke da gasasshiyar kaza mai romo,

Zama yayi akusa da ita yajawo dan karamin glass table din dake gefen gadon ya dora kayan akai,

Kafadarta ya riko yajata zuwa jikinsa yasoma bubbuga bayanta ahankali alamar rarrashi,

“Kukan ya isa haka one love…., sorry, daina kuka, ya isa haka….maza karbi abinci kici,khairiyya tafada min rabonki da abincin kirki tun ranar da aka fara bikin nan…, kinga kuma kinada ulcer idan yunwa tayi miki yawa tashi zatayi…,sorry… Yi shiru…., kiyi hakuri kinji”

Dakyar ta iya yin shiru, yana rungume da ita ajikinsa ya dauko naman yabata yasa mata abaki, daurewa tayi ta karba ta taune nan yaci gaba da bata tana kwance a kirjinshi, kanta ta kawar zuwa cikin tsakiyar kirjinshi alamun ya isheta haka, cup din dake dauke da madara ya dauka yabata tasha rabi amma bai amince ba saida yasake saka mata ta shanye gaba daya,

Sakinta yayi ya tashi ya kwashe kayan zuwa kitchen yadawo, abun mamaki abun dariya sai yasake zuwa ya isketa tana kuka, kayanshi ya shiga cirewa yana murmushi,

“Lallai yarinyar nan dadin kukan kike ji…”

Daga haka yawuce bathroom, wanka yayi ya fito daga shi sai gajeren wando yazo yahaye gado ya kwanta yana kallon agogo, karfe 12 daidai agogon ya nuna,tarin pillows din dake kan gadon yafara turewa wadanda suka doshi guda 12 koma fiyeda haka,

“Ki tashi kije kiyi wanka kizo ki kwanta, wai ko bakya jin barcine?”

Shiru tayi masa taci gaba da shasshekar kukanta,

“Bakiji abinda nace bane?”

“Ni nayi wanka dazu”

“To matso ki kwanta”

Can karshen gadon ta lallaba ta kwanta, matsawa kusa da ita yayi ya yaye mayafin da ta tukunkune dashi, ya dagota,

“Bari inrage miki kayan nan yanda zakiji dadin barcin, kina ji ana zafi amma ke kina kokarin laftawa jikinki kaya…”

Jin ya kamo rigarta yasata tsananta kukanta tana kokarin kwacewa, wutar dakin ya kashe duhu ya mamaye dakin,

“To tsaya incire miki kinga ai yanzu babu hasken bazan ganki ba…”

Dakyar ta aminta ya cire rigar amma zani fur taki yarda, kyaleta yayi ya kwantar da ita awurinda ta kwanta da farko,

“To shikenan kwanta kiyi baccin but don’t forget to pray….”

“Uhumm” Tace tana gyada kai kamar kadangaruwa,

Daga haka ta kwanta yayinda shi kuma ya matsa can gaba shima ya kwanta bayan ya tura mata pillow guda daya,

Tana jinshi yayi addu’a ya shafa, bata iya bacci ba saida ta tabbatar da cewar bacci ya daukeshi. Cikin dare ya farka daidai lokacin da ya saba gudanar da sallar nafilarshi amma yau kam baya jin zai iya tashi domin yana bukatar baccin kasancewar agajiye yake, split yatashi ya rage ya kashe fanka sannan ya koma kan gadon, phone dinshi ya dauka ya haskata ta hasken kan screen din wayar, a tukunkune yaganta alamar tana jin sanyi, murmushi yayi saboda abinda taketa boye mishi dazu yanzu gashi nan afili, duvet yaja ya lulluba mata sannan ya kwanta kusa da ita yadora kanshi saman pillown da kanta ke kai,babu jimawa bacci yasake gaba dashi bashi ya farka ba sai 5:56 a.m,

Tashi yayi zaune ya kalli halima wacce ke lullube tanata bacci, sauka yayi zuwa toilet yayi alwala sannan yafito ta gefen kanta ya tsaya yadan sunkuya ya soma tashinta, bude ido tayi ta kalleshi take ta tuna da a inda fa take, yamutsa fuska tayi kamar me shirin yin kuka.

“To sarkin kuka atashi ayi salla…”

Yunkuri tayi zata tashi sai kuma tafasa saboda tunawar da tayi babu riga ajikinta”

Turo baki tayi tana harararshi,

“Ina kasa min rigata?”

“Oho….,ko kin bani ajiyane?” Yabata amsa bayan ya bude closet dinsu, jallabiya ya dauko milk colour ya zira ya juya ya kalleta, har lokacin bata da niyyar tashi tana nan akwance lullube,

“Wai ko ba zakiyi sallar bane inyi tawa ni daya?”

Abin salla ya shimfida yatada sallarshi saboda ganin lokaci nata kurewa, saida taga yayi sujjada sannan tayi maza ta tashi ta dauki rigar wacce ke can karshen gado ta fada toilet, brush tayi dafarko kafin tayi alwala sannan tawanke fuskarta da sabulu kafin ta fito daga cikin bathroom din, kwance ta hangoshi saman gado ya kunna wayarshi yana sauraron karatun alqur’ani suratul yunus cikin kira’ar sheikh Abdurrahman sudais,

Closet tabude ta ciro wani zurmemen hijab Wanda tasan aikin Aliyu ne, sallar itama tayi bayan ta idar ta tashi tana nade abin sallar, satar kallonshi tayi taga idanuwanshi alumshe kamar mai yin bacci, hijabin ta cire ta mayar wurinda ta daukoshi sannan ta lallaba ahankali kamar marar gaskiya ta hau kan gadon ta kwanta domin baccin bawai dama isarta yayiba domin acikin dar dar tayishi.

Yana jinta duk abunda take domin ba barci yake yiba amma ya kyaleta, babu jimawa bacci yayi gaba da ita, shima sama sama yakejin karatun da yake saurara bacci yayi nasarar daukeshi wanda bashi ya samu ya tashi ba sai 10 nasafe daidai, wayarshi ya dauka ya jona a charge sannan ya shiga wanka, tun yana cikin bathroom yake jin ana knocking din kofar falonsu wannan dalilinne yasashi yin gaggawar fitowa, window ya leka nan ya hango baba tabawa ce mai aikin umma, jallabiyar da ya cire yazira ya fita ya bude mata bata yarda ta shigoba suka gaisa ta bashi warmers din dake hannunta guda uku tajuya ta koma, mayar da kofar yayi ya rufe ya kai kayan kan dining ya ajiye, bedroom ya koma yacire rigar jikinshi yaje gaban mirror, ta mirror din yake hangota tana yin firfita da hannunta guda daya alamun zafi takeji,gaban gadon yaje ya sunkuya yana kallonta ta dan soma hada zuffa, karamin towel din dake hannunshi yasa yagoge mata goshinta zuwa wuyanta sannan ya matsa, fanka ya kunna yakaro mata karfin air condition din dake cikin dakin duk a lokaci daya.

Cigaba yayi da shirinsa bayan yagama shafa mai ya dauki cumb yana gyara sumarshi zuwa gemunsa,

Saida yagama shafe jikinsa da turare sannan ya nufi wurin kayansu, duk abinda yake yi halima na kallonshi domin tun lokacin da baba tabawa ta soma bugun kofarsu ta farka,

Wani purple din material na maza taga ya ciro marar nauyi dashi mai tsananin kyau kuma shara shara, farar vest yasaka aciki sannan ya saka kayan wanda tsayin rigar iya cinyarshi ne haka tsayin hannun ma iya gwiwar hannunshi ne,

Gaban mirror yasake komawa yafesa turaren lailatul abyad da black oud,

Inda halima ke kwance ya nufa domin so yake ya tasheta tayi wanka taci abinci, kamar me baccin gaske haka tayi zama yayi agefenta yakai hannu saman fuskarta juyawa tayi tabashi baya, dan kwalin kanta ya gyara mata yakai hannunshi kan kunnenta yana magana ahankali,

“One love wannan earrings din ai sai su cimiki kunne…mantawa nayi jiya da daddare ban cire miki ba saboda duk kin rudani da kukanki…..”

Ahankali ya cire dan kunnen kasancewar mai barima ne, juyota yayi ahankali ya cire mata dayan yana kallon kyakkyawan hannunta wanda yasha kunshi gwanin ban sha’awa,fuskarta ya kalla yana shafar kunshin hannun nata,

Tashi yayi yafita daga bedroom din, sauran bedrooms din guda biyun duk yabi ya lalleka sannan ya rufesu ya shiga kitchen,

Electric cattle ya ciro daga kwalinta ya dauraye sannan ya jona ruwan zafi, yana tsaye ruwan yatafasa ya ciro tea flask babba shima ya dauraye shi sannan ya juye ruwan zafin aciki yafita yakai kan dining,

Kitchen ya sake komawa ya dauko musu flate guda biyu da spoons sai cups duk ya dauraye ya ajiye agefe, flate din da sukayi amfani dashi da cup jiya da daddare ya wanke ya ajiyesu a wurin da aka tanadar musu,

Flate da spoons din da yawanke da farko ya dauka yafita zuwa kan dining,kayan tea wadanda ya hado musu jiya ya cicciro ya kawo kan table din,warmers din da baba tabawa takawo ya soma dubawa dan ganin abinda ke ciki, nafarko wainar shinkafa da sinasir ne aciki, dayan kuma miyar agushi ne aciki sai na karshen farfesun kafar saniya,

Tea ya hada sannan ya zuba farfesun kadan a flate ya dauki bread yayi bisimilla yasoma ci,

Tashi yayi bayan ya kammala yakoma bedroom din ya dauko wayarshi da laptop yadawo falon domin har lokacin halima bata tashi ba wani baccin ta koma,

Sai 11 tatashi hamma tayi tai mika tatashi zaune, Aliyu ta hango yana kokarin ciro charger din laptop dinshi daga cikin jakar adana laptop wacce ke cikin drewar din mudubinta,

Gunta yanufa bayan ya dauki charger din,

“Ba mika zakiyi kiyi shiru ba madam, addu’a zakiyi sai ki wuni cikin farin ciki, kice Alhamdulillahil lazi ahyana ba’ada ma amatana wa ilaihin nushur….”

Maimaita mata yayi tana fada, wucewa yayi yafita daga cikin bedroom din bayan tagama maimaita addu’ar, murmushi tayi tabishi da kallo saboda sosai taga yayi kyau ya fito a angonshi sak, gaban kofar toilet taje taja towel dake rataye a kofar bathroom din tashiga wanka, sai da ta kara yin brush bayan tayi wankan sannan tafito,

Kwalliya ta zauna tayi sannan ta gyara gashinta wanda ba wani mai yawa bane asalima dakyar yake yin packing, ribbon tajera wurin guda hudu sannan ta tashi, turarenta da yagana tabata ta ciro ta shafe jikinta take dakin ya kaure da kamshi, wani leshi ta ciro wanda akayi mata dinki fitted riga da skirt kalar ruwan kwai, sarka da dan kunne ta saka bayan ta saka kayan sannan ta saka bangles duk golden,

Jikinta tabi da turaren smart lady sannan ta fesa bakhur,

Kan bed din da suka kwana taje ta gyarashi tsaf ta maida pillows din ta jeresu ta dauko flat shoe kalar kayanta ta saka ta fita,

Kishingide ta ganoshi afalo yasa laptop agabanshi yana bin karatun dake tashi ahankali daga cikinta,

Jin fitowarta yasashi daga kai ya kalleta, murmushi ne ya subuce masa saboda ganin irin kwalliyar da tasha ga dinkin jikinta yayi mata cacas sai kace ba itace ta kusan kwana tana kuka ba.

“Ina kwana?….” Tace dashi tana wucewa zuwa dining table,

“Haba one love har yanzu fushinne ba ahuce ba?”

Tea ta hada ta debi farfesun ta zauna taci, wurinshi ta dawo bayan ta gama ta zauna akan kujerar dake makwabtaka da tashi,lumshe idanuwanshi yayi sakamakon daddadan kamshinta da ya kawowa hancinsa sumame,

“Sadiyayye na wai har yanzu fushinne? Ke kuwa ki huce mana, haba aminiyata….”

“Ai darling brother wallahi kaima kasan abinda kayi baka kyauta ba, ko ladies night fa kin barina inyi kayi, ni wallahi ka kwafsa min”

“To ai nabaki hakuri ai, idan kin haihu zamuyi dinner din, ke duk haihuwa ma sai munyi, shikenan?”

Murmushi tayi batare da tayi magana ba, lekawa tayi kan screen din laptop din domin ganin abinda yakeyi nan ta hango bulugul maram yake saukewa na marigayi sheikh ja’afar, tv tace ya hada mata zatayi kallo nan yatashi ya hada mata ya kunna, tashar zee world ta kamo ta mike tana kallo shikuma yana yan bincike bincikensa a internet na littattafan addini wanda yayi masa sai ya sauke da haka har 12:50 tayi, kashe laptop din yayi ya mike tsaye,

“Leematu na zanje salla azahar tayi”

“To,saika dawo,Allah ya kiyaye hanya”

Bedroom yawuce ya dauro alwala ya fito yana cemata itama tatashi tayi salla kafin ya dawo, kofar yabude yafita, bai jima da fitaba itama tatashi tayi salla, wata kwalliyar ta sake tsantasarawa sannan ta koma falo ta zauna…..

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

 

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

 

_DEDICATED TO FIDDAUSI SODANGI_

 

*41*

 

***Tana kwance kan doguwar sitter taji shigowarsa, kujerar da take kai yaje ya zauna agefenta yana kallon film din da take kallo a tashar mbc bollywood,

“Kinyi sallar kuwa?”

“Nayi mana….”

Hannunshi ya mika mata na dama ya kamo nata,

“To assalamu alaikum…, ai sai mu gaisa ko?”

Murmushi tayi, tana jin yanda yake murza hannun nashi acikin nata,

“Kaga Abba lokacin da ka fita salla?”

Yana rikeda hannunta acikin nashi ya kalleta yana jin dariya na taso masa,

“Wai ke daga kawoki jiya shine har zaki soma tambayarsu Abba?”

Fuska ta narke ta turo baki,

“Waya kawoni? Ni ai ba kawoni akayi ba zuwa kayi ka daukoni”

Sai lokacin dariyar da yake dannewa ta samu zarafin fitowa,

“Nidai Aliyu laifuka na da yawa awurin rabin raina….”

Sake turo baki tayi tana kunkuni,

“Ai wallahi kayi min abubuwa da yawa…, kaga gashina ko packing bayayi shiyasa nace zanyi kitso amma ka hanani…”

Matsawa yayi kusa da kanta ya cire dan kwalinta da hannu daya, daya hannun kuma yana rike da hannunta,

“Ba naga kinada gashi ba, mugani…”

Kanta ya dora akan cinyarshi yacire ribbons din dake daure da gashin nata,

“Ni banida gashi, gashi ina masifar son gashin nan wallahi amma yaki zuwa wurina…”

Dariya yayi yana shafa kumatunta wadanda suke luhu luhu,

“To ai yanzun ma babu laifi halimatu na, kin san ai kowanne mutum tara yake bai cika goma ba, kuma ai akwai mata dayawa wadanda kika fisu wasu abubuwan….”

“Me nafi su? Ni babu abinda nafi sauran mata”

“Gashi kuwa…, kin fi wasu fari kinfi wasu hanci kinfi wasu idanuwa…, gashin ma ki kwantar da hankalinki akwai abinda zan baki yafito very soon….”

Ai halimatu na jin haka bata san lokacin da ta rungumeshi ba tana murna,

“Yawwa my darling brother, dan Allah kabani yanzu ma…”

Dariya yake yana karawa saboda ganin yanda duk ta rude akan maganar gashi,lallai mata na kaunar gashi,

“Ba yanzu zan bakiba, me kike ci na baka na zuba? Zan baki ai Sadiya na..”

“To nagode darling brother…”

“Haba sweet sister ai basai kinyi godiya ba kin wuce haka…”

Sakin hannunta yayi ya wuce bedroom dinsu mintuna kadan yafito rikeda wani babban littafi yazo ya zauna bayan ya dauko laptop dinshi,

“Wai darling brother wanne ne naka bedroom din?”

Kallonta yayi,

“Gashi nan naki, ai bedroom guda daya zamuyi shearing…”

“To amma ai cewa akayi naka daya nawa daya na baki daya…”

“A’a nidai daya ya ishemu nida ke shiyasa ma zakiga kayana ban kaisu ko inaba duk suna bedroom dinki sai dai idan bazaki hada daki daniba sai inbar miki abinki”

Dan kwalinta ta daura takoma ta kwanta batare da tace masa komai ba, shi dinma abinda yasha masa kai yasoma yi domin wani nazari yakeyi da bincike akan littafin risalah.

Ita kam halima kallonta takeyi domin harta canja channel zuwa African magic tana kallon wani Nigerian film,

Knocking suka ji anfara daga waje nan Aliyu yatashi yaje yabude duk da dai abude ma kofar take,

Khairiyya yagani rikeda matsakaitan warmers tana tsaye, da murmushi akan fuskarshi yayi mata sannu da zuwa yabata hanya tawuce, tashi halimatu tayi tana murnar ganin khairiyya,

Nan ta tareta ta karbi warmers din takai kan dining table lokacin khairiyya suna gaisawa da Aliyu yana yimata godiya da ban gajiya,

Kamo hannun khairiyya Sadiya tayi suka koma daya falon suka bar Aliyu a babban,

“Umma khairiyya dama ashe kece shine harda wani tsayawa yin knocking?”

Dariya khairiyya tayi ta bugi kafadar Sadiya,

“To waya fada miki ana shigarwa amare gida kai tsaye? Yanzun ma dai kawai karfin hali nayi nashigo….”

“Au da niyyarku babu mai zuwa kenan? Ni ko sauran yan biki ma fa banga kowa yazo ba”

“Au…, to ai yanzu gidan nan babu kowa duk sun tafifa kowa idan akace yazo sai yace ai yariga da yaga daki dan haka basai yadawo ba…..”

“Shikenan ai tunda hakane…”

Dariya khairiyya tayi,

“Ke munata surutu bakije kin bawa bawan Allah abinci ba…”

Tashi halima tayi tana murmushi tafita daga falon,

Yana nan ayanda tatafi tabarshi sai dai yanzu kuma kallon tv yake yana kallon labarai,zama ta danyi akusa dashi tana kallonshi, shi dinma kallonta yake yi,

“In kawo maka abincin ne?” Ta tambayeshi muryarta ahankali,kumatunta ya shafo da hannunshi,

“A’a,na koshi sai dai zuwa anjima…., wancan abincin ma da aka kawo da safe zan fita dashi tunda yayi mana yawa…”

“To shikenan, bari nakoma wurinta”

Kai ya daga mata tatashi takoma wurin khairiyya,

“Umma khairiyya in zubo miki abincin?”

“A’a nagode, guntuwar kazar jiya ta amarci dai zanci…”

Tashi tayi tana murmushi tashiga kitchen cikin wata takarda mai kyalkyali taga rabin kazar gefe kuma cabbage ne da su tumatur nan ta daukota ta zuba acikin flate bayan ta dauraye ta kai mata, babban falo ta koma ta bude fridge, shake ta ganshi da milk kala kala amma babu juice ko daya aciki tasan aikin Aliyu ne, ziza milk ta dauko mata sai battle water takoma wurinta,

Dariya khairiya tayi tana kallon ta,

“Sannu, amma ya naganki rass?”

“Kai umma khairiyya wai da ayaya kike son ganina?”

“Ai nazaci zanzo in sameki ranga ranga…”

“To wallahi babu abinda akayi, baccinmu muka sha danni banma tashi ba sai 11”

“Lallai an daga miki kafa”

“Dama ni nasan halin kayana”

“To Allah huta gajiya…”

Halima bata kai ga amsawa ba tajiyo karar wayarta afalo da gudunta ta dira daga kujera ta fita amma kafin taje har wayar ta yanke duk da Aliyu yataho kawo mata, karba tayi ta juya tana duba wanda ya kira, kamar a mafarki taga number Abdul,

Bata bi kiranba ta ajiye wayar suka cigaba da hirarsu da khairiyya har wurin 3 lokacin tajiyo muryar Aliyu yana kiranta,

Tsaye taganshi yana babballe links din hannun rigarshi da alama wanka yayi domin yanzu ba kayan dazu bane ajikinsa,milk colour din yadine yanzu ajikinsa sai kamshin turare yake,matsawa daf da ita yayi yasoma yi mata magana cikin rada rada,

“Nifa fita zanyi tunda naga antynki tazo gara imbaku wuri kuji dadin hirarku, babu wani abu?”

“Babu komai sai ka dawo, Allah ya kiyaye hanya” Tafada tana murmushi,hannunta ya kama sannan ya amsa da,

“Amin sweetheart…”

Warmers din safe da baba tabawa ta kawo ya dauka ya fita dasu, har balcony ta rakashi sannan tajuya ta koma ciki.

Samun khairiyya tayi ta fito da wata bakar leda mai dauke da magungunan ta aciki wanda ta baraso agida bata taho dasu ba,

“Ga magungunanki inji yagana… Duk da madara ake sha”

Yamutsa fuska halima tayi,

“Ni wallahi duk wadannan magungunan sun isheni gasu da shegen daci…”

“Haka dai zaki daure kiyita sha har subi jikinki”

“Toh”

Kallonta khairiyya tayi ta danyi dariya,

“Meyasa kika saka wadannan kayan bayan kinada dinkuna na garari, ai da sai kisaka daya daga cikin masu heart style dinnan”

Dariya halima tayi itama,

“Ba yanzu ba umma khairiyya, yanzu lallabashi nake tukunna”

“Shikenan ai idan kin kwana biyu kya saka”

Har magrib suna tare da khairiyya bayan sunyi salla halima tashiga wanka tafito, wata sabuwar kwalliya tayi ta saka wasu riga da skirt na atamfa bayan ta feshe jikinta da turarukanta masu dadin kamshi,

Daf da sallar isha khairiyya tatafi, rufe kofar falon tayi ta zauna tana kallo kafin tatashi tayi salla tana idarwa aka dauke wuta,

Tsoro ne ya kamata ta zauna awurin tana jiran taji antada Gen amma shiru ga uban duhu gashi wayarta na daya falon, tashi tayi ta laluba ta bude kofar falon ta fita kan baranda nan kuma sauro yace muje zuwa babu shiri ta koma ciki, tana shiga ko minti uku ba ayiba Aliyu ya dawo,

Takure ya ganta kasan rug abin har yaso bashi dariya, kafin ya zauna aka kunna gen nan haske ya mamaye falon,

“Sadiyayye na yaya?”

Zumburo baki tayi tatashi tana cire hijabin da tayi salla dashi,cikin shagwaba tace,

“Ba kaine ba katafi kayi zamanka ba”

“Yi hakuri one and only, ai naga ne kinada abokiyar hira amma ayafe min, wurin malam naje acan najima saboda nasameshi yana wani muhimmin abu…”

“To sannu da zuwa”

Zama tayi akusa dashi nan ya zuba mata idanuwanshi yana kallonta musamman ma wuyanta wanda yake jajur dan tsabar fari ga wasu guraye kamar sarka saboda yar kibar da tayi,hannayenta ya kamo ya rike cikin nashi,

“Inkawo abinci?”

“Kawo mana tare muci saboda kema nasan baki ciba”

Tashi tayi tana murmushi tanufi dining, white rice ne sai stew wanda taji naman kaza nan ta zubo musu sannan taje fridge ta ciro musu hollandia babban kwali guda daya ta hado da ruwa ta kawo inda yake zaune,

“Sannu da kokari one love”

Murmushi tayi takoma kitchen ta dauko cups guda biyu ta dawo, a kasa suka zauna suka fara cin abincin, ganin halimatu kawai cakular abincin take yasashi ture kayan dake gefenshi ya jawota kusa dashi kafin ta ankara sai jinta tayi cikin kirjinsa ya zagaye kafadarta da hannunshi guda daya,

“To bude bakin…” Yafada bayan ya debo abincin a spoon, budewa tayi ya saka mata sannan shima ya debo yaci, haka yarinka bata abincin yana cewa,

“Kinada ulcer amma baki son cin abinci, naga alama sai ina dura miki sannan zaki rinka ci…”

Murmushi take hannayenta duka na bisa cinyarshi,

“Yanzu duk abincin da nake ci darling brother baka gani? Kaga fa yanda nayi kiba kayan nan ma duk sunyi min kadan sun matseni saboda lokacin da aka gwada ni ban kai haka ba”

“Kedai kawai aure dama kike so shiyasa ana saka mana rana kika fara hada teba kika barni da rama…”

Dariya tayi tana kallon kyakkyawar fuskarshi,

“Kaima Allah baka rame ba”

Hancinta yaja sannan ya saka mata nama abaki bayan ya lashi lips dinta da nashi,

“Zaki sakani inyi ai ko?”

“Woohhh haba ranka yadade, idan ka kara kiba kuma ai muni zakayi”

Dariya yayi ya tsiyaya musu hollandia a cup yabata tasha sannan shima yasha,

“Bawani kedai kawai kice bakya son nayi kiba saboda kar na kara nauyi”

“A’a nidai kawai ka zauna ahaka Allah kafi kyau yanzu”

“To ai ya danganta da irin kulawar da zaki bani”

“Nidai zan kula dakai sosai amma bazan bari kayi kiba ba”

“To nagode, ai nakine ke kadai nidin, duk yanda kikeso haka zakiyi dani…”

Murmushi tayi ta rufe fuskarta, suna cin abincin suna hira yana yi yana lashe mata baki da nashi shiyasa basu san lokacin da suka cinye ba, itace ta tashi ta tattare kayan takai kitchen ta ajiye sannan ta dawo, saman kujera ta hau ta zauna kusa dashi suna kallon Africa tv 3,

Har 10 taga bashida niyyar tashi domin wani wa’azi yake kallo nan tatashi tabarshi tawuce bedroom tayi shirin bacci bayan tayi wanka, sleeping gown ta saka mai rubi biyu sannan ta saka hula ta kwanta duk da ta manto wayarta a falo amma haka ta kyale tayi kwanciyarta.

Kasa bacci tayi tanata zulumi har Aliyu ya shigo, lamo tayi tai lukus kamar mai bacci tana ganinshi ya shiga wanka ya fito, da iya boxers kawai yazo ya kwanta bayan ya kashe hasken, jikinta har wani kar kar yakeyi ganin ya matso kusa da ita amma ga mamakinta sai taga yayi kwanciyarshi ko tabata baiyi ba kawai dai ya dora kanshi asaman pillown da ta dora kanta, tana ji yayi addu’a ya shafa ajikinsa sannan itama yafara shafa mata kasancewar duhu ne, agarin shafe mata jiki da addu’a tsautsayi yasa hannunshi shafo wani lallausan abu mai mutukar laushi,wani shock ne ya jashi babu shiri ya janye hannunshi addu’ar da bai karasa shafa mata ba kenan yayi kwanciyarshi, itama lokacin da taji hannunshi awurin sai da numfashinta yaso daukewa dan tsananin fargaba da tsoro, idonta asoye batayi bacci ba saida taji Aliyu yayi, tsorone kuma ya shigeta jin yayi barci ya barta sai ita kadai, kasancewar ya juya mata baya saboda abarin shi nadama ya kwanta yasata matsawa bayanshi sosai ta kwanta ajikinshi kanta saman wuyanshi ahaka tasamu tayi baccin.

K’arfe uku saura yan mintuna ya bude idonshi, jin irin matsarshi da halima tayi abin yabashi dariya domin kamar wacce ke tsoron wani abun karya zo ya dauketa haka ta manne mishi ajiki ta kankameshi ta baya,

Ahankali da dabara yasamu ya janye jikinsa duk da sai sake rukunkumeshi take, lullubeta yayi sannan yatashi yawuce bathroom ya dauro alwala yafito, doguwar riga jallabiya yasaka ya shimfida abin salla,

Bayan ya idar ne yagama addu’o’inshi ya tashi ya koma kan gadon ya kwanta lokacin karfe 4 da mintuna 50,yana kwanciya yaji halima ta sake manna jikinta da nashi kamar wacce ke jiranshi dama,janta jikinshi yayi ya gyara mata kwanciyar.

Asubar fari ya tashi yayi alwala domin lokacin salla yayi, saida ya fito daga bathroom sannan ya tasheta amma furr taki tashi, ruwan hannunshi ya shafa mata a kumatu nan ta tashi tana mummuttsuka ido saida yaga ta shiga bathroom yin alwala sannan yayi raka’atanul fajr yafita masallaci,

Lokacin da ta fito bata ganshi ba tasan masallaci yatafi domin ga muryarshi nan ma tanaji a loudspeaker dake masallacin kofar gida, sallarta tayi ta koma kan gado ta kwanta.

Tana nan kwance taji shigowarshi saurin lumshe idanuwanta tayi,wayarshi ya dauko yazo gefen gadon ya zauna yana jin hannunshi na faman yi masa kaikayi domin abinda suka tabo jiya abisa kuskure suke burin sake tabawa yanzu.

_Dubun gaisuwa da fatan alkhairi to Dan asali fans,wallahi kunyi yawan da bazsn iya rubuto sunayenku bane, but remember u are always in my mind, thought and my heart,indeed am so proud of u, am really enjoying ur wonderful and thoughtful comments keep on following,like seriously am deeply grateful._

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

 

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

 

_DEDICATED TO FIDDAUSI SODANGI_

 

*42*

 

***Gyara zamanshi yayi ya juya ya kalleta nan yaganta kamar bacci take hakan yasashi dan dofana agefen gadon ya kwanta,

Wayarshi ce ta soma vibrating yadauka ganin malam lawan ne yasashi tashi zaune, bayan sun gaisa ne malam din ke sanar dashi cewar yazo da misalin karfe goma na safe akwai wurin da zai rakashi,

Komawa yayi ya kwanta bayan ya gama wayar yana jin kamar ya matsa jikin halima ya kwanta,

Itama halima jira take taga ya kwanta taje kusa dashi domin daga daren jiya kadai ta fasa gardin hakan,

Ganin ya lumshe idanuwanshi kamar mai yin bacci yasata matsawa ta shiga jikinsa, rungumeta yayi yana jin wata nutsuwa tana saukar masa, ahaka bacci ya daukesu,karfe 8 shidai ya tashi, agurguje yayi wanka ya fito, yana tsaka da shiryawa yaji knocking daga kofar falo, riga ya zira yaje ya bude, warmers guda biyu kadai yagani an ajiye awurin amma babu kowa, murmushi yayi ya dauka ya shigar ciki yana kissima kara da alkunya irinta mutanen da domin yasan baba tabawa ce ta kawo,

Saida ya jona ruwan zafi a electric sannan yakoma dakin yaci gaba da shiryawa,

Sabuwar shadda kar ya ciro yasaka milk colour domin shima a bikin nan nasu wurin kaya kala arba’in Abba yabashi ya dinka, hula ya ciro yana gyara karin dake jikinta yana kallon kanshi a mirror, saida ya fesa turaruka kaloli daban daban sannan ya nufi falo bayan ya gyarawa halima kwanciyarta,

Tea ya hada yahau table, chips da kwai yaga ankawo musu sai farfesun kayan ciki,

Har yagama ya koma falon ya zauna yana duba tafsirin wata surah acikin laptop din halima bata fito ba, sai 9:30 tafito tasha kwalliya cikin blue colour din material fitted gown,

“Saura kadan infita da baki tashi ba…”

Zama tazo tayi tana kallonsa,

“Ina kwana?”

Saida ya kalli agogon fatar dake hannunshi sannan ya amsa bayan ya mika mata hannunshi na dama domin suyi musabaha, akunyance ta mika masa nata ya kama,

“Lafiya lau sweetheart,yakika tashi?”

Murmushi tayi kafin ta amsa bayan ya saki hannun nata,

“Lafiya lau, kayi kyau, ina zakaje?”

Idonshi na kan laptop din ya amsa mata,

“Dazu da asubah Malam ya kirani awaya yace inshirya zan rakashi wurin wata walima da karfe 10 wai wasu mata ne sukayi saukar alqur’ani shine zamuje wurin walimar…”

“Mata….? Allah yasanya alkhairi”

Tashi tayi tana turo baki saboda ji take kamar ta hanashi zuwa dan kar a kalle mata shi, tea ta hado ta zubo chips din a flate ta dawo falon shi dai sai murmushi yake yana binta da kallo,

“One love baki son inje ne wurin walimar?”

“To bayan idan kaje wurin nasan kallonka mata zasu yi tayi”

“A’a sweet sister babu macen da zata kalleni fa saboda duk matan aure ne”

“To ai kafi mijinsu kyau”

Dariya abin yabashi nan ya mike yana kokarin saka hularshi bayan ya kashe system dinshi,

“Idan kin gama ki saka min laptop dinnan a charge kinji…”

Mikewa tayi itama tana kallonshi,

“Allah kayi kyau tsaya muyi pics”

“Kai halimatu na rigima ce dake dole dai sai kin makarar dani…”

Da gudu gudu taje ta dauko wayar ta dawo, bashi tayi,

“Yi mana selfie kaga kafini tsawo…”

Karba yayi ya jawota jikinsa ya rungumeta babu shiri ta rufe fuskarta da hannunta,

“Kai darling brother bafa haka ba”

“To ai haka mata da miji suke yi idan zasu dauki hoto da ace keba matata bace iya kanwata ce shine sai ki tsaya agefe na”

Kunyace duk ta kamata saboda harda su zagaye cikinta da hannunshi da rike kugunta daga karshe ya dauki wani yana sumbatarta a wuya,

Wayar ya mika mata yana daukar key din mota da wayarshi yana cemata,

“Ki ajiye idan nadawo zan gani, sai nadawo”

“To ka tsaya mana in gyara maka hular taka baka saka daidai bafa”

Sunkuyawa yayi ta cire hular ta kara saka masa shikuma yana zira wayarshi a aljihun rigarsa,

“Idan nayi kyau da yawa dai wata tagani ta yaba babu ruwa na..”

“Duk ma wacce tagani ta yaba tayi abanza tunda kwalelenta ba samu zatayi ba,jirani 1 minute”

Kafin yayi magana ta ruga da gudu zuwa bedroom dinta, yana kokarin saka bakin takalmin da ya fito dashi sai gata rike da wani sau ciki kalar birni milk colour,ajiye masa tayi agabanshi hannunta rikeda turarenshi na black oud, ita ta saka masa takalmin sannan ta mike tana fesa masa turare ajikinshi,

“Allah ya tsare min kai kuma ya dawo min dakai lafiya yayana, kuma mijina”

Hannunta ya rike guda daya yajata jikinshi ya riko waist dinta ta baya,

“Nagode one love, ki kular min da kanki kafin indawo kinji…,and ban yarda ki zauna da yunwa ba, karki jirani kici abincinki idan nadawo sai mukara ci tare kinji”

Kai ta daga masa tana sussunne kai akirjinsa saboda jin kirjinta bisa nashi,dago kanta yayi yana dariya ba shiri ta lumshe idanuwanta hakan yabashi dama da kwarin gwiwar dora tausasan labbansa kan nata, makarar dai da yaketa gudun yi saida yayita batare da ya fargaba.

Tare suka fita ta rakashi har balcony dinsu anan yace ta tsaya ta koma, tana tsaye tana waving dinshi har saida taga kulewarshi domin part dinsu a lungu yake sune ma na karshe, ji tayi kamar karta koma ciki domin tasan ita kadai zataje tayi zaman kadaici, dole babu yanda ta iya haka ta juya ta koma ciki tana zuwa ta dauki wayarta tasoma bin pics din da sukayi tana gani daya bayan daya, dukka sunyi kyau kuma sun dauku rangadadau, whatsapp dinta ta shiga tasaka pics din a status amma wasu kasa dorasu tayi saboda kunya bata saurari comments din friends dinta ba ta tashi ta soma dan gyara gidan duk da bawani datti yayi ba amma dai tanada bukatar tsaftace shi, bayan tagama komai ne tana bin lungu da sako tana fesa air freshener taji maganar khairiyya,

“Amarya inshigo?”

Da murnarta ta nufi kofar,

“Shigo umma khairiyya ni kadaici fa”

“Atoh ai da alama, wani status nagani yau wanda yataso ni dole nace bari inzo inyi comment”

Dariya halima tayi taja hannun khairiyya bayan ta bude kofar,

“Umma khairi kenan”

“Atoh ai naga yau kun rabarbashi soyayya kun rakarkashe kun bawa kauna hakkinta,da alama anwuce wurin”

“Ni wallahi umma khairiyya bana so, nafada miki fa babu komai”

“Lallai Aliyu dan albarka ne, ni gobe ma zan wuce tunda naga komai lafiya lafiya”

Dariya halima tayi suka zauna saman kujera ta kunna musu tv tana mitar wai daga umma har abba da ummi babu wanda yazo ganinta har baba tabawa mutuniyarta ko ta lekota su gaisa,

Suna nan itada khairiyya suna shan hira saiga sabira itama tazo nan abun yayiwa halima dadi nan suka fara hira da shewa, da rana bayan sun idar da salla baba tabawa ta kawo musu abinci nanne itama tashigo saboda sanin cewar Aliyu baya nan, babban flate halima ta dauko ta zuba musu abincin chicken fried rice da vegetables and egg salad,sannan ta dauko musu hollandia masu sanyi guda biyu,

Wuni cur sukayi banda baba tabawa wacce bata wani jimaba tatafi tace aiki zataje tayi, lokacin sallar la’asar tashiga wanka bayan tayi salla, da turaren wankan da yagana ta bata yau tayi wanka ta fito ta shirya, wata green din atamfa riga da skirt ta saka ta ci dauri, su Sabira naganinta ta fito suka hau shewa nan suma sukace sai sunyi hotuna da amarya dan asan sunzo,

“Yawwa Abdul dinki fa yace daya san hakane bazai dawo Nigeria yanzu ba tunda wai kikayi aure”

Dariya halima tayi,

“Ki rufa min asiri, ai naga jiya ya kirani”

“To ashe dai shi sonki yake kece dai batashi kikeba time din”

“Ai kuwa dai anrigashi sai yayi hakuri” Inji khairiyya, basu sake dadewa ba sosai suka tafi ta rakosu takoma ciki babu jimawa Aliyu ya dawo, sannu da zuwa tayi masa amma yaki amsawa har saida ya rungumota zuwa jikinsa sannan ya amsa yana yi mata magana ahankali asaitin kunnenta,

“Sadiyayye na yagida,ya zaman kadaici, nabarki ke kadai ko?

Girgiza masa kai tayi, sakinta yayi yana murmushi ya zauna saman kujera,wucewa tayi itama tana murmushin,

Kitchen taje ta kawo masa ruwa mai sanyi da hollandia ta ajiye masa sannan taje ta hado masa abinci ta kawo,

“Zo muci to mana..”

“Ni ai naci wannan nakane”

“Ban yarda ba, na fahimci dai kina jin dadin durar da nake yi miki ko”

Hannunta ya kama suka sauka kasa yayi mata yanda yasaba wato ya sanyata ajikinshi ya soma cin abincin itama yana bata, shiru kakeji domin shi dabi’arshi ce wannan idan yana cin abinci bai cika magana ba har sai ya gama, sosai Aliyu ya cika mata cikinta sannan ya bata madara tasha,janta jikinshi yayi bayan sun kammala cin abincin, lokacinne yafara janta da hira yana tambayarta wadanda suka zo da baya nan, sosai ta fara sakin jiki dashi suna hira kafin yace ta hada masa ruwa zaiyi wanka, tashi tayi taje ta hada masa bayan salt din da ta zuba harda turarenta na wanka ta saka masa sannan ta fito acikin bedroom din ta sameshi yana kokarin rage kayan jikinshi nan taja masa kofar ta fita ta koma falo ta tattara kayan da suka ci abinci takai kitchen sannan ta dawo falon ta zauna tana kallon tashar mbc bollywood.

 

*_Yan uwa ina yimana nasiha da muji tsoron Allah, a hakikanin gaskiya yanada kyau mu rinka tunawa da fadin annabi Muhammad S. A. W cewa abubuwa guda uku haramunne ga musulmi akan dan uwansa musulmi, nafarko jininsa, dukiyarsa da mutuncinsa, awani hadisin ma annabi Muhammad cewa yayi musulmi dan uwan musulmi ne kada ya zalunceshi, kada yaci mutuncinsa, kada ya tozartashi, kada ya karyatashi sannan kada ya wulakantashi, a matsayinmu na musulmai masu koyi da annabi ya kamata mu rinka sara muna duban bakin gatari, idan kana ganin wani yayi maka ba daidai ba to idan Katashi ramawa kada kawuce ka’idar abinda yayi maka domin Allah ma acikin littafinsa mai tsarki cewa yayi idan anyi muku abu to ku rama kwatankwacin abinda akayi muku amma da zakuyi hakuri shine yafi alkhairi domin Allah yana tareda masu hakuri, idan hakane to babu bukatar mu zauna muna cin mutuncin junanmu, muna aibata junan mu ko kuma muna wulakanta juna saboda muna ganin ai social media ce duk abinda mukayi babu abinda zai faru to mudaina wannan tunanin domin idanuwanmu da bakunanmu da hannayenmu da dukkan gabbanmu masu bada shaidane agaremu ranar alkiyama, duk wanda ka batawa ko ka wulakanta wallahi Allah sai ya tsaidaku yayi muku hisabi mutukar mutumin bai yafe makaba domin annabi cewa yayi zagin musulmi fasikancine yin fada dashi kuma kafircine, kuma abubuwa dayawa a matsayinmu na yan adam bai kamata mu rinka shigarsu ba mutukar idan bawai dole takama sai mun tofa albarkacin bakinmu ba domin yana daga kyawun musuluncin mutum yabar abinda babu ruwansa idan kuma takama dole saika tofa albarkacin bakinka to kafadi alkhairi ko kayi shiru inji annabi saboda wannan maganar da annabi yafada sahabbai daina magana sukayi sai sahabi yayi kwana uku baice uffan ba saboda yana tsoron kar yafadi maganar da bazata zama alkhairi ba to sai mune zamu dage mu takarkare muyita fadin abinda muka gadama? Dan Allah mu zama masu tausasa lafuzanmu domin kyakkyawar magana sadakace, cin mutunci da tozarci wallahi babu inda zasu kaimu sai ko tashar dana sani domin annabi yace duk wanda yaci mutuncin dan uwansa musulmi to Allah zaici mutuncin fuskarsa da wuta ranar alkiyama, sannan annabi yace ya ishi mutum musulmi sharri ya wulakanta dan uwansa musulmi sharrin yakai sharri mutum yaci mutuncin dan uwansa musulmi ko yafada masa bakar magana wacce zata bakanta masa zuciya ta sakashi acikin damuwa tofa idan bai yafeba wlhi Allah sai yayi masa sakayya, sannan ku kuma masu murna kuna dariya idan hatsaniya tafaru kuna cewa anayi kuna jin dadi to kuyi gaggawar tuba domin babu kyau a matsayinka na musulmi kaga wane da wane suna jin haushin juna ko suna tozarta juna amma ka koma gefe kana dariya saboda bada kai akeyi ba mutuna shifa sulhu alkhairi ne haka Allah madaukakin sarki yace sannan sulhunta musulmai dayane daga cikin ayyukan alkhairi wanda annabi ya lissafa mudaina zama kanwa uwar gami ko yan ba ruwana domin kwatankwacin irin wannan dabi’ar wasu al’umma sukayi abaya Allah ya halakar dasu basa umarni da kyakkyawa sannan basa hani da mummuna wa’iyazubillah,idan munga ba daidai ba murinka gyarawa da harshenmu ko da hannunmu ko mu kyamaci abin azuciyarmu wanda shine mafi raunin imani kamar yadda annabi yafada, ubangiji Allah yaci gaba da tsare mana mutuncinmu ya hada kawunanmu mu musulmai, ya ankarar damu gaskiya yabamu ikon binta ya nisantamu da shaidan da tawagarsa, wannan dai yar tunatarwa ce garemu domin dukkaninmu mun sani shaidanne kawai ke walagigi da tunaninmu, ina yimana sallama irinta addinin musulunci yar uwarku a musulunci Ummi A’isha._*

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI….!*🤴🏻

_*NA*_

_*UMMI A’ISHA*_

 

_DEDICATED TO FIDDAUSI SODANGI_

*D’an Asali fans ban san ta inda zan fara yimuku bayani ba, narasa bakin magana amma ina mai baku hakuri, gaisuwa mai yawa agareku akuma duk inda kuke, naga sakonninku da kiranku araina saida nace ashe haka leemah-Ali keda masoya?*

 

*43*

 

***Tana nan zaune yafito falon sanye da jallabiya brown colour hannunsa rikeda bakar leda,

Zama yayi akusa da ita nan asirtaccen kamshinsa ya doketa,

“Ka fito?”

“Ehhh, wannan menene? Acikin drewar dinki nagani”

Sai lokacin ta lura da bakar ledar dake hannunshi, magungunanta ne wanda khairiyya ta kawo mata su jiya,

“Magani ne…”

“Maganin me?” Ya tambayeta yana kallonta,

“Magani kawai”

Murmushi taga yayi,

“Maganin mata ko?”

Dauke kanta tayi ta mayar saitin tv,

“Kin san dame aka hada ko dai kawai sha kike batare da kin san abubuwan da akayi amfani dasu wurin hadawa ba? Nidai dan Allah indai dan ni zaki rinka sha na hutar dake basai kinsha ba kiyi zamanki ayanda Allah ya halicceki wallahi zan cigaba da sonki ahaka….”

“To nikam wai yin kaina ne? Nima fa ba son sha nakeba dan anyi min dole ne, abu duk daci….”

Daukosu yasoma yi daya bayan daya yana dubawa,

“To da aka baki basai ki zubar ba? Mata wallahi kuna bani mamaki kudai bakuda ilimin abu amma sai ku kamashi ku rikeshi gam gam, kowacce mace da kike gani akwai irin ni’imar da Allah yayi mata, wata tana da isasshen ruwa ajikinta amma bata da dandano to wannan batada bukatar abubuwan karin ni’ima sai dai abinda zai bata dandano, wata kuma tana da ni’imar da dandanon amma ba amatse take ba dan haka ita abinda zai matseta zata nema, to amma matsalar ku bakwa tsayawa ku fuskanci a inda matsalarku take ku gyara sai ku hautsina abubuwan duka ku cakuda daga karshe sai komai ya dakushe ku rasa ni’imar ku rasa dandanon amma da ace kuna bin komai bisa ka’ida ita budurwa ma bata da bukatar wadannan tarkace tarkacen naku sai fruits, fruits kadai zai saukarwa mace dukkan ni’imar da take bukata…”

Tagumi ita dai tayi tana jinsa wato shidai Aliyu komai da ya shafi mata yasani kenan, hab’a ta rike aranta tana godewa Allah da yasa ta mallakeshi a matsayin miji,,

“One love bakice komai”

“To me kake so ince?”

“To shikenan tunda babu abinda zakice yanzu kitashi muje in koya miki yanda zaki hada abubuwanki da kanki wadanda zasu saukar miki da ni’ima cikin kankanin lokaci ke kisha nima insha kowa yasamu…”

Kunya ce ta kamata ta rufe fuskarta da hannunta yayinda shikuma ya mike harda cire jallabiyar jikinshi,

“Zo muje ki gani”, hannunta yakamo zuwa kitchen, blander yaciro daga cikin kwali sannan ya nufi fridge, kankana ya dauko rabi ya ciro apple guda biyu manya sannan ya dauko ayaba guda biyu,

Sai da ya dauraye blander din sannan yasata ta yayyanka kankanar yana tayata, ayabar ya bare itama ya saka aciki tareda apple din nan ya hadesu yabata yace ta markade, milk ta ruwa ya juye aciki bayan tagama blanding din, ya gauraya yana kallonta,

“Bamu da zuma amma zan siyo mana sai ki rinka saka mana aciki kirinka sha nima haka…,ki samo abu yanzu ki juye inyaso sai ki saka fridge ni masallaci zanje gashi can ana kira”

“Toh, adawo lafiya”

Daga haka yafice daga kitchen din ita kuma tayi yanda yace, saida ta dan zuba a cup tasha danma cikinta acike yake sannan tasaka sauran acikin fridge.

Bai dawo gidan ba sai da yayi sallar isha sannan yadawo, kallo suka kafa sunayi har 11 sannan sukaje suka kwanta, yauma kamar jiya manne masa tayi ajiki har gari yawaye,

Washe gari da safe khairiyya tazo tayi mata sallama zata tafi lokacin suna yin mopping din falo itada Aliyu, kayan kwalliya sosai ta hadawa khairiyya ta bata sukayi sallama tatafi Sadiya harda kukanta dakyar Aliyu ya rarrasheta.

Yau kam agida ya wuni babu inda yaje sai dai idan lokacin salla yayi yafita masallaci idan yayi yadawo, da yamma bayan yafita masallaci kafin yadawo halima tasake wanka tayi sabuwar kwalliya tasaka shadda dark purple doguwar riga tasha dauri sai kamshi take zubawa, zama Aliyu yayi akusa da ita bayan yashigo,

“One love kinyi kyau…, wai yaushe zamu zama miji da mata ne kullum sai kwalele kwalele kike yimin…”

“Kai darling brother wanne miji da mata kuma? Yanzu ba miji da matane ba mu?” Tafada tana wasa da yatsunta fuskarta dauke da murmushi,

“Ehh yanzu ma mu miji da matane amma ai har yau bamuyi abinda miji da mata keyi ba”

Rufe fuskarta tayi cikeda kunya,

“Nidai zamanmu haka yafi”

“Saboda me yafi?” Ya tambayeta bayan ya tallafe kumatunsa da hannuwanshi yana kallonta,

“Nidai dan Allah kayi hakuri basai munyi abinda miji da matar keyi ba”

Dariya ce ta fito masa batare da ya shirya ba,

“To saboda me mu zamu zauna ahaka?”

“To banaji ance da wahala ba kuma da zafi”

Dariyarshi ya danne,

“Waya fada miki? Ni ai zanyi playing dake sosai so ba zakiji wani zafiba”

Rufe fuskarta tayi hakan yabashi damar jawota saman cinyarshi, hannunshi yakai kirjinta yana yi
mata rada,

Jin abinda yace yasata tashi ta gudu ta koma daya falon, dariya yayi yana bin bayanta da kallo, tun daga lokacin kuma aka fara jin kunyarsa amma dayake shidinne zuwa isha tasake dawowa inda yake sai dai duk lokacin da yayi yunkurin taba kirjinta sai ta k’i.

Washe gari da rana suna zaune kuwa cemata yayi gobe zai fara fita gareji kuma yanada wani acikin ranshi wanda yake so yafara gudanarwa dan haka tunda agidan babu abinda yakeyi daga gobe zai soma fita,

Kallonshi tayi tai narai narai da ido,

“Haba darling brother yanzu idan ka fita sai ni kadai fa”

“Ehh mana ai gara infita tunda zamana agidan baida amfani babu abinda kike bani nima bana baki komai”

“Dan Allah nidai kayi hakuri”

Murmushi yayi yana kallon tv,

“To shikenan nahakura amma fa ban hakura da fita gobe ba”.

Dayake yanzu ta saba da bacci ajikinsa shiyasa ko taje ta kwanta ita kadai bata iya bacci har sai yazo, yauma hakance ta faru domin tun 9 ta shiga bedroom ta kwanta tabarshi afalo amma sai taji takasa baccin bayan kuma kafin ta shigo baccine a idonta sosai, remote ta dauka ta kunna tv tana kallo ahaka har yashigo, kashe tv din tayi tana jiranshi yahawo gadon amma bai hawo ba duk da cewar yagama shirin bacci,

“Darling brother kazo muyi baccin mana…”

“Kiyi baccinki ni karatu zan danyi”

Kafada ta makale,

“Wallahi nakasa, dan Allah kazo sai kayi anan din kaga fa ni nafi son kwanciya ajikinka, jikinka yafi katifar nan dadin bacci”

Murmushi yayi ya ajiye littafin dake hannunsa,

“To amma fa sai dai muyi trade by batter, kiban gishiri inbaki manda”

“Mefa?”

Kan gadon ya hau sannan ya rage hasken dakin,

“Ki barni in taba nan nima sai inbarki kiyi bacci ajikina, saima kin zabi a inda zakiyi idan abayana zaki kwanta ko a kirjina”

Ganin ya nuna kirjinta da kuma jin abinda yace yasata jin matsananciyar kunya ta rufeta, fuskarta ta cusa cikin pillow, tana son tace a’a kuma tana son yin bacci ajikinshi,

“Kin amince ko baki amince ba?”

Kai ta daga masa alamun ehh,

“Kin amince?” Kai ta kara daga masa, murmushi yayi ya jawota jikinsa wanda jikinta yafara yar rawa domin idan da abinda ta tsana to bai wuce ataba mata kirjinta ba shikanshi ya fuskanci haka,hannunshi dake kaikayi yabawa abinda yake yiwa,

Jin jikinta yana rawa sosai yasashi hakura yace, “to shikenan kwanta kiyi baccin saida safe”

“To kajuya mana” tafada cikeda kunya, juya mata bayanshi yayi nan ta makalkaleshi ta kwanta ajikinshi tana mai lumshe ido.

Kamar yadda yafada washe gari ya fara fita gareji amma yakan dawo da rana yaci abinci,

Kullum yanzu take hada musu lemon da ya koya mata shida ita, har yau kuma su umma ke aiko musu da abinci gashi har ankwana 6 da bikinsu, daga umma har Ummi da Abba bata ga kowa a part dinta ba sai dai awaya amma shi Aliyu kullum safe da yamma yana shiga ya gaishesu.

Halima kam ba karamin sakin jiki tayi da Aliyu ba yanzu saboda ganin har yau baiyi yunkurin yimata wani abuba sosai abin yabata mamaki shiyasa ta saki jiki sosai dashi bata da wurin zama da wurin bacci sai jikinshi idan zai fita kuwa har wani special kiss da hugging akeyi masa shikuwa duk ya shanye yakai zuciyarshi nesa akanta shiyasa arashin wayonta ta zaci haka zasu cigaba da tafiya,

Yau bayan sun gama breakfast yana kokarin fita ta tambayeshi anjima zataje ta gaida su umma bai hanata ba yace taje, nan ta rakashi yatafi sai faman zuba kamshi yake na turaren da ta fesheshi dashi, saida ta gama ayyukanta kaf ta gyara ko ina kama tun daga kan dakin baccinsu zuwa kitchen dasu falo, wanka ta sake yi sannan ta fita,

Part din Ummi ta fara zuwa ai kuwa ummi kamar bazata ajiyeta akasa ba tajima anan sannan suka rankaya zuwa part din umma,

Umma farin ciki baki har kunne tafara yimata sannu da zuwa, dukda ada tayi fushi dan su umman basu taba shigar mata ba amma bata san lokacin da ta wareba ta shiga harkokinta, sai yamma da Aliyu ya dawo sannan suka koma tare, tun daga ranar kullum sai ta shiga part din Ummi da umma can take wuni,

Yauma kamar kullum tana sashen umma suna aiki da baba tabawa, dambun shinkafa sukeyi bayan an dora tace bari taje ta dawo zata yiwa Aliyu girki dan ba lallai yaci dambun ba,

Part dinsu ta koma ta dora masa kus kus da miyar kayan lambu sannan ta hada musu lemon kankana, bayan tagama ta shiga wanka, har yau kunshin bikinta na nan rangadadau a hannunta domin matar da tayi mata idan tayiwa amare wata guda yakeyi ita kuwa yau kwananta takwas agidan Aliyu,

Wata fitted gown ta atamfa tasaka maroon colour daga kirji anyi heart style dan haka kirjinta a bude yake muraran tana kokarin daura dan kwali Aliyu ya shigo,

Sannu da zuwa tayi masa sai kallonta yake musamman ma inda style din heart din yake, abincin ta gabatar masa yace ba yanzu ba yanzu bacci zaiyi dama kuma ta lura tunda yashigo yake faman lumlumshe idanuwa, duk girman idanuwa irin nashi yau kam sun zama kanana, tana kokarin fita yace tazo ta tayashi kasancewar tagama sakin jiki dashi yasa batayi tunanin komai ba ta amsa gayyatarshi, hannunta ya riko ya kwantar da ita ajikinshi, lumshe idanuwanta tayi tana murmushi domin idan da sabo ta saba kwanciya jikinshi wata rana ma har da yan wasanni sukeyi, yanzun ma da haka yasoma,janta da wasa yafara yi tana biye masa suna faman dariya da haka har lamari yayi nisa, koda wasa bata yi yunkurin yi masa gardama ba lokacin da ta fahimci abinda yake shirin aikatawa sai dai duk hankalinta yatashi zuciyarta sai bugawa take da karfi.

Ko kadan Aliyu baiyi gareji ba kuma baiyi tabargazar da samarin yanzu keyi ba, yanda yake komai nashi cikin nutsuwa yanzun ma hakance ta kasance, ita kuwa sai faman tsittsilla ido take kamar sabuwar munafuka, ahankali taji yana yimata magana,

“Duk abinda kikaji nafada ki maimaita kinji”

Kai ta daga masa nan yasoma karanta addu’ar da annabi ya koyar wurin kebantuwa da iyali, kamar yadda yace mata haka tayi yana fada tana binsa har ya gama fada,

Ahankali yabi da ita kamar ruwan sanyi, duk da ya sameta acikin sa’idan mata wadanda ko cikin mata dubu ba afi asamu daya ba amma hakan baisa ya cutar da itaba,

Mintuna sun shude haka awanni suma duk sun wuce amma har lokacin Aliyu bai iya cimma burinsa ba domin da alama kwanakin da yabarta ta shana batare da komai ba yau saiya fanshe kayansa.

Bayan sallar la’asar ya samu komai ya wakana, bayan komai ya lafane ya tashi zaune, Sadiya ya kalla wacce idonta ke jajur fuskarta kuma babu walwala,

Baiyi mata magana ba saboda ganin lokacin salla yadade da wucewa, tashi yayi ya fada toilet nan ta yunkura ta tashi tana kallon wurin da abun yafaru bai wani baci ba hakanne yasake tunzurata ta fashe da kuka, tana tsaka da kukan ya fito daga bathroom din,

Hannu ya mika mata ya kamo nata bayan ya mika mata towel, tana kuka ta tashi ta karbi towel din ta daura,

“Muje kiyi wanka na zuba miki ruwan zafi…”

Da kafarta ta taka tawuce cikin toilet din tana cigaba da sharar hawayenta, acikin toilet dinma saida tasha kuka sannan tayi wankan tafito bayan ta shiga ruwan zafin da ya hada mata,

Lokacin da ta fito ta ganshi yana janye bedsheet din duk da bawani baci yayiba saiko dan abinda ba arasa ba, doguwar riga tasa ta zira hijabi ta tada salla,

Tana idarwa ta sake fashewa da kuka, inda take yazo ya zauna yana kallonta fuskarshi cikeda damuwa,

“Dan Allah halima ki fada min abinda yafaru…!”

Kukanta taci gaba da yi batare da ta bashi amsaba, zama yayi ya zuba mata ido yana kallonta.

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

 

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

_DEDICATED TO FIDDAUSI SODANGI_

 

*44*

 

***Ganin bata da niyyar magana ya sashi mika hannu ya tayar da ita tsaye, hijabin jikinta da tayi salla ya cire sannan yasoma kokarin cire doguwar rigar jikinta,

Towel ya dauko mata ta daura yakama hannunta har zuwa tsakiyar gadonsu,har lokacin bata bar hawaye ba,

“Nace ki fada min abinda yasaki kuka kin ki, ko zafi kikeji?”

Girgiza masa kai tayi alamun’a’a,

“To menene abin kukan?”

Saida ta boye fuskarta ajikinshi yanda bazai iya ganin idonta ba sannan tafara fada masa cikin kuka,

“Toh…toh… To ni banji naji wannan mahaukacin ciwon da ake fada ba…,sannan kuma….”

Murmushi yayi yasake riketa yana shafa bayanta,

“Sannan kuma me? Karki damu ki fada min duk abinda ke zuciyarki nikuma zanyi miki bayani dalla dalla yanda zaki fahimta”

“Sannan banga wannan blood din dayawa ba kamar yadda ake fada, kuma ance ana kasa tafiya sam ba a iya takawa nikuma gashi ina iya zuwa ko ina da kafata shiyasa nace kodai ni din ba budurwa bace…!”

Dariya taji yafara yi mata hakan yasata dagowa tana kallonshi, mamaki abin yabata domin ganin yanda yake dariya har hakoranshi suna bayyana awaje,

Mayar da kanta tayi jikinshi takara sautin kukanta,

Pillow yajawo ya kwanta halima na jikinshi, juyo da fuskarta yayi yasa harshe yana lasar hawayen nata, jin harshensa har saman idonta yasata fara rage kukan nata,

Kalar rarrashin da yake matane yasata dole yin shiru sai ajiyar zuciya datake saukewa,

“One love kin bani dariya fa sosai, ni wallahi da naga kinata wannan kukan na zaci ciwon da nake gudun ji miki shi naji miki…., yanzu ke dama akan wannan kike kuka?”

Daga kanta tayi tana jan ajiyar zuciya,

“To ki kwantar da hankalinki indai akan wannan ne bakida bukatar yin kuka, wallahi a cikakkiyar budurwa na sameki lafiyayya mai tarin ni’ima, ke lafiyayyar macece sannan kuma kinga ai nabiki ahankali saboda tausayinki da nakeji shiyasa kika ga ke baki fuskanci duk wadannan wahalhalun ba, ina sonki da yawane kuma ina tsananin tausayinki bana son ki wahala…., amma har ga Allah kin kaini wata duniya yau…,kin samu 9 credit, ke idan ma akwai 100 credit to kin samu!”

Jin abinda yace yasata cusa fuskarta a gefen wuyanshi tana murmushi,

“To kefa? Baki fada min komai ba…”

Bakinta na jikin wuyanshi ta amsa masa,

“Radadi da zugi amma ba can sosai ba…sannan duk gabobina ciwo suke yimin…”

Kanta wanda ke jike da ruwa ya shafo,

“Ayya duk dai dabarata saida nayi hurting dinki, to sannu, am sorry…”

Kai ta daga masa tana kanannade ajikinshi, yanata zuba mata santi amma ita bata san abinda yake yi ba domin sama sama take jinsa dalilin baccin dake fusgarta,

“Onle love baccin yamma? Kiyi hakuri kar kiyi bacci yanzu kibari sai zuwa anjima”

Jin yana kokarin tadata yasata fara kuka, jijjigata yasoma yi yana hura mata iska a kunnenta babu jimawa bacci ya dauketa, kwantar da ita yayi yasauka daga kan gadon ya fita, fridge ya fita domin dauko ruwa, har zai koma bedroom yafasa yaje ya bude kofar falo ya leka nan yaga food flask medium ajiye akofar falon, daukowa yayi ya bude, dambu yagani na shinkafa da zogale yasha uban mai da yaji agefe, baba sabuwa ce ta kawo tun dawowarsa babu jimawa ta dade tana knocking amma ba abude ba shine ta ajiye musu anan ta tafi.

Kan dining yakai ya ajiye sannan yakoma bedroom din, zama yayi yasha ruwan yana mai kallon halima wacce ke bacci,

Wanka ya shiga yayi ya fito ya shirya yasa yadi fari yafesa turaren black oud, gun halima dake kwance ya nufa ahankali ya dagota zuwa cinyarshi, lebenshi ya dora kan nata yasoma tsotsa ahankali, bude ido tayi ta kalleshi,jikinta wani ciwo ciwo yake yi mata gaba daya,

“Tashi kici abinci kiyi wanka kinga magrib ta kusa….”

Lumshe idonta tayi sannan ta budesu akan fuskarshi, towel din dake daure ajikinta ta gyara nan ya taimaka mata ta tatashi,

“Abincin zaki fara ci sai kiyi wankan ko?” Jijjiga masa kai tayi,

“A’a bari infara wankan”

Riketa yayi ta sauko daga kan gadon suka shiga bathroom din tare, ruwan zafi yatara mata a bathtub,

Taimaka mata yayi sosai ta gasa jikinta fiyeda dazu sannan ta silla wanka suka fito, tun daga cikin bathroom din tafara jin saukin ciwon da jikinta keyi mata, zama tayi zata shirya agaban mirror shikuma yafita zubo musu abincin,

Kwalliya ta tsantara tasha turare,tana kokarin tashi ya shigo rikeda faranti babba mai dauke da abinci akai, murmushi ya aika mata dashi itama ta maida masa da martani,

Kaya ta ciro tasa,marron colour din swiss lace riga da skirt wadanda sukayi mutukar kamata domin rigarma haka kawai tasata bata saka komai aciki ba,

Wurinshi taje ta zauna tana ta zuba kamshi bayan ta gama shiryawar,

“Ga dambunki da aka kawo miki…”

“Yaushe aka kawo?”

“Ai nima kawai ganinshi nayi abakin kofar falo amma ban san lokacin da aka kawo ba..”

Spoon ta dauka ta soma ci bayan ta gaurayeshi,

“Kinada ulcer amma kina cin yaji ko?”

“To ai yajin bashida zafi”

“Duk da haka dai, anjima zaki iya fita muje unguwa ko har yanzu jikin naki yana miki ciwo?”

Girgiza masa kai tayi,

“A’a yadaina, dama kuwa ina son kilishi kaga sai mu taho dashi ta can…” Ta amsa masa saboda tana son fitar domin wannan ne karo nafarko da zata fita,

Murmushi yayi,

“To ko har mun samu karuwa ne?”

Harararshi tayi tana murmushi,

“Saboda Kaine wa?”

“Dan baiwa mana”

Daga shi har ita dariya sukayi lokaci guda, cikin raha da barkwanci tareda tsokanar juna suka kammala cin abincin,

Jin anfara kiran salla a masallaci yasashi tashi tsaye yana kallonta,

“Bari inyi alwala inje masallaci….”

“Toh..” Ta amsa masa,

Bathroom yashiga ya dauro alwala yafito bai tarar da ita acikin dakin ba, yana fita falo ya jiyo motsinta a kitchen, lekawa yayi ya ganta tana tattara kayan da sukayi amfani dashi tana tarawa a wurin wanke wanke,

“Kibar wannan wanke wanken kizo kiyi salla…”

Ajiye kayan tayi tajuyo tana murmushi, waist dinta ya rike suka fita,

“Idan zaki kama ruwa kirinka amfani da ruwan zafi kinji zakiji dadin jikinki….”

Kai ta daga masa,sakinta yayi yafita ita kuma tawuce ciki, afalo ta fito tayi sallar bayan ta idar tana zaune akan abin sallar yashigo, sannu da zuwa tayi masa ya amsa ya zauna kusa da ita.

Kwanciya tayi ta dora kanta saman cinyarshi, gashin kanta yake bi ahankali yana shafawa yana yi mata hira har lokacin sallar isha’i yayi, masallaci yatashi yatafi ita kuma tayi sallarta anan,

Tana kwance akan kujera bayan ta idar da sallar yashigo, zama yayi agefenta,

“Ki tashi ki shirya muje unguwar, ko ba zaki iya zuwa ba?”

“Zan iya mana….” Tafada tana turo baki,

“To shikenan tashi”

Tashi tayi tawuce daki yayinda shi kuma ya maida hankalinsa kan film din da take kallo atashar zee world,

Ta kwashe mintuna samada guda 15 sannan ta fito tasha kwalliya ta yafo dan madaidaicin gyale sai zuba kamshi take tana rikeda high hill dinta a hannu,

Kallonta yake yi har ta karaso kusa dashi,

“Darling brother muje…”

“Ina? Ahakan zamuje sweetheart? Da wannan gyalen?”

Turo baki tayi ta bata fuska,

“Me gyalen nawa yayi?”

“Haba sadiyayye na in banda rikici irin naki inake ina fita da irin wannan mayafin? Ni wallahi bazan iya fita dake ahaka ba, inafa tsananin kishinki….”

“To waye zai ganni?”

“Kinga nidai ko babu mai ganinki kiyi hakuri kisa hijab muje”

Makale kafada tayi tana turo masa baki, karasawa wurinta yayi yajata zuwa jikinsa yana kokarin hada bakinshi da nata,

“Kiyi hakuri kisa hijabin kinji sweety, kinga gidan malam zamuje bai kamata kije da mayafi ba”

Bazata iya yimasa musu ba dole ta je ta dauko hijabin tafito sai zuba kamshi mai dadi take,

Tana gaba yana biye da ita suka fita ya rufe kofar falon nasu sannan suka wuce, part din umma suka shiga domin suyi mata sallama amma bata nan haka itama ummi domin dukkansu suna part din abba,acan suka tarar dasu sunata hirarsu gwanin ban sha’awa, akasa halima ta zauna suka gaidasu, umma ta kalleta tace,

“Dazu kuma tunda kika tafi shiru shiru sai tabawa nabawa abincin tabiki dashi itama taje tarinka sallama shiru tace sai ajiye miki tayi kila kuna can ciki bakuji ba….”

Murmushi halima tayi ta kalli Aliyu suka hada ido sannan ta sunkuyar da kanta,

“Ehhhh bacci nayi lokacin amma da yaya Aliyu yafito yagani yadauko…..,angode”

Murmushi kowannensu yayi ciki kuwa harda Abba, dan muskutawa Aliyu yayi yace,

“Bari muje dama wai unguwa zata rakani…”

Adawo lafiya suka yi musu suka tashi suka fita su Ummi suka rakasu da Allah yayi musu albarka,

Gaban motar ya bude mata tashiga ya mayar ya rufe sannan ya zagaya mazauninshi ya zauna, jingina tayi da jikinshi ta rike dantsen hannunshi wanda ke gefenta,

Ahankali ya tada motar suka fita daga gidan, wani nishadi ke dawainiya dashi a wannan lokacin,

“Me ya kamata mu kai musu tsaraba?”

Daga kanta tayi ta kalli fuskarshi tayi murmushi tana shafo gemunsa,

“Mu kai musu duk abinda yasamu”

Murmushi yayi ya rage gudun da yakeyi,

“Ke wai ina ruwanki da gemuna ne…..”

Saida tayi dariya sannan ta bashi amsa,

“Ai nawane kaga kuwa dole inyi yanda nakeso, garama da ka tuna min idan mun koma zan gyarashi in saitashi sannan in tajeshi sai in shafa masa mai…”

Dariya abin yabashi nan yasoma yi harda su kwarewa,

“Lallai gemun nan dan gatane kamar ma anfi sonshi akaina…”

“Kai…. Haba Darling brother wama zai hada ai kai nafi sonka fiyeda komai”

Murmushi yayi ya dan dora kanshi jikin nata wanda ke jingine da kafadarsa,

“To nagode, ni dama ai kin dade da sanin matsayinki agareni ko?”

“Ni ban saniba, ka fada min inji”

“Kin sani mana…”

“A’a ni ban saniba kawai dai nasan baka sona nice kadai ke sonka kai akwai wadda kake so”

“Lalalalahhh…., dama akwai wadda nake so bayan ke? Ke kadai ce fa ke mulkar zuciyar nan tawa duk fadinta, daga ke babu wata”

Murmushi tayi ta sake kankame hannunshi cikeda annashuwa, awani provision store ya tsaya yafita ya siyowa su malam tsaraba, sabulan wanka da na wanki sai man shafawa da omo manya guda uku,

Lokacin da ya shiga motar tana jingine jikin kujera tana game awayarshi, har suka je gidan Malam lawan abinda take yi kenan sai dai wani lokacin suna yin hira dashi, koda suka je gidan sunyi sa’a sun iske malam na nan domin yana kofar gida zaune da wasu magidanta su biyar suna yin karatun muwadda malik, tare suka fito ya rakata cikin gidan sannan yafito yaje wurin Malam lawan wanda ya dukufa yana karatu.

Saida yajira Malam din ya kammala sannan suka gaisa ya sanar dashi cewa tareda halima suke, cikin gidan suka shiga nan suka tarar matan gidan sun yiwa halima kyakkyawar tarba domin ga ruwa nan da tuwon biski miyar taushe ankawo mata kasancewar matan gidan guda biyune kuma masu kirki duk bakon da yazo gidan basa nuna banbanci dan wurin daya kazo ko wani abu makamancin haka,

Gaishe da Malam tayi sannan takoma ta zauna su baba Marka sunata tura mata tuwon akan taci nan taja tafara ci Aliyu sai cemata yake ta saki jikinta fa nan shi gidansu ne,

Hira sosai sukayi agidan basu suka tafi ba sai karfe 9 nadare nan su baba marka suka hada mata su tsintsiya, kuka da dakakkiyar kubewa suka bata, saida suka fita sannan Aliyu yabawa sulaiman jikan malam kayan da suka kawo musu daga nan suka yiwa malam sallama suka tafi.

Wurin da ake gasa nama yabi dasu ya siyo mata kilishin da take so cikin takarda sannan ya sai balangu yazo suka tafi,lokacin da suka koma gida basu shiga part din kowa ba suka wuce nasu saboda dare yayi, afalo suka yada zango yabude musu balangu da kilishin da sukazo dashi bayan yadauko musu fresh milk zama yayi yarinka bata abaki, sosai halima taci kilishin tayi nak sannan tatashi bayan tasha madara, bedroom tawuce tabarshi awurin,wanka tayi da ruwan dumi tayi shirin bacci ta kwanta, shi kam saida ya hada kayan wanke wankenta yawanke a wannan daren ya kife a kwando sannan yanufi dakin bayan ya kashe komai na falon,

Kwance yaganta da wayarshi a hannunta tana karatu, wanka yashiga bayan ya tsokaneta da “madam ni kike jira inzo ayi aikin lada ko?”wannan ne yasa kafin ya fito ta ajiye masa wayarshi tayi baccin karya.

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
[12/20, 9:20 AM] Saude Ahmad: © *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

 

_*NA*_
*_UMMI A’ISHA_*

 

_DEDICATED TO FIDDAUSI SODANGI_

 

*45*

 

***Murmushi ya saki lokacin da ya hangota tayi baccin karyar, gaban mirror yaje ya shirya bayan ya tsane jikinsa, kamar koda yaushe jikinsa yabi da dadadan turare masu mutukar kamshi, kayan bacci ya ciro yasaka akaron farko riga armless da wando iya gwiwa masu santsi,

Kan gadon ya hau yana leka fuskarta, murmushi yayi yajata jikinsa suka kwanta,

“Ki bude idonki sweetheart babu abinda zanyi miki kawai dai playing zamu danyi kafin muyi bacci…”

Jin abinda yace yasata sake nutsar da fuskarta cikin kirjinsa tana murmushi,

“Nifa bacci nakeyi…”

Dariya yayi yana shafa kumatunta,

“Dama idan ana bacci ana magana?”

Kai ta daga masa alamun ehhh, murmushi yayi yasake kanannadeta ajikinsa,

“Shikenan tunda bakya so, yi baccinki, amma Kafin nan….”

Nutsuwa tayi tana son jin abinda zaice,

“I love u sweet sister, kiyi bacci dani acikin ranki kuma ki sakawa zuciyarki cewa Aliyu zaici gaba da kaunarki tareda sonki har karshen rayuwarsa, sannan zuciyarsa bazata gusheba cikin sonki har ranar da zaiyi bankwana da duniya……., Halima i soo much luv u, u are the apple of my eyes….!”

Lumshe idanuwanta tayi tana sauraron tausasan kalamansa masu dadin gaske, har cikin bargonta da jijiyoyin jikinta kalmomin suke shiga suna bin kowanne lungu da sako na lakar dake aiki ajikinta suna kasheta,

Dagota taji yayi ya azata samanshi gaba daya daidai tayadda zai iya sumbatar bakinta, lumshe fararen idanuwanta tayi tana jin bakinshi cikin nata, kamar yadda yafada mata hakance ta faru iya wasannin kadai sukayi wanda dolenta itama ta sake tana maida masa martanin wasannin da yake mata.

Wayarshi dake ajiye gefe ya dauko ya duba time nan yaga karfe 1 harda mintuna 9,kasa yayi da muryarsa sosai tayadda koda ace akwai mutum acikin dakin to bazai taba iya jiyo abinda zai fada ba sai iya ita kadaice zataji,

“Zaki iya yin wanka yanzu?”

Girgiza masa kai tayi cikeda shagwaba tace,

“Ni bacci nakeji gaskiya, gobe nayi”

Kanta yasoma shafawa,

“Yi hakuri abar kaunata, daure kiyi yanzu kinga kin huta goben ko?,kuma kinga ba aso mutum ya kwana da janaba atareda shi gara ko alwala ne yayi, yawwa my luv dan kokarta muje…”

Turo baki tayi cikin shagwaba kamar zata saka kuka, tashi yayi ya sauka ya dauko mata towel, bathroom yashiga batare da yajirata ba, kafin ta shigo har ya hada musu ruwan wanka mai dumi,

Atare sukayi wankan suka koma daki, rigar baccinta ta mayar jikinta ta kwanta tana jiransa domin bacci takeji sosai, yana kwanciya tabi jikinsa ta kwanta kamar yadda tasaba,addu’a yayi musu ya shafa sannan ya lumshe idanuwansa yana rada mata kalaman so har bacci ya dauketa.

Da asuba kasa tashi tayi saboda bacci har yaje masallaci yadawo bata tashi ba, zama yayi gefenta yana jan yatsun kafarta zuwa na hannunta, har lokacin sake lumshe ido take tana bacci, kumatunta ya shafa ya dan ciji lips dinta na kasa ba shiri ta bude idanuwanta, dan dole ta tashi taje ta dauro alwala tazo tayi salla Aliyu na zaune gefen gadon yana karatu,

Komawa tayi ta kwanta bayan ta kammala addu’o’inta, ajiye alqur’anin yayi yakwanta bayan yahada jikinsa da nata.

Bacci sukayi mai cikeda nutsuwa gamida nishadi har 11 saura sai lokacin Aliyu ya farka, kai tsaye kitchen ya shiga, tsayawa yayi ya rike kugunshi yana tunanin abinda yadace ya dafa wanda bazai dauki lokaci ba, bashida zabi dan haka ruwan zafi kadai ya tafasa yajuye ya dora indomie, saida yayi grating din albasa da attaruhu yazuba aciki, kwai ya soya musu sannan ya hada kan kayan yakai kan dining.

Bedroom yakoma har lokacin yar shagwabar tashi bata tashi ba tana lullube tana bacci, bai tashetaba illa bathroom da ya shige, babu bata lokaci yayi wanka yafito nan ya tsaya ya shirya yasaka kaya, falo yawuce yaje ya hada tea yasoma karyawa yana yi yana kallon tv inda ya kamo tashar African news,

Yana nan zaune shi kadai duk zaman ya isheshi sakamakon rashinta akusa dashi, agogo ya kalla nan yaga 12 tayi, mikewa yayi ya shiga daki, tashinta kenan tana zaune tana mutsuttsuka ido, zama yayi akusa da ita tamkar zai shige jikinta,

“Halimatu na sai yanzu aka tashi….? Kin dai yi addu,a ko?”

Kai ta daga masa tana faman lumlumshe ido,

“To barka da tashi, adaure aje ayi wanka azo akarya ko….”

Janye bargon tayi ya kama hannunta ya sauko da ita daga saman gadon, har kofar bathroom ya rakata taja towel ta shige sai lokacin yajuyo yadawo tsakiyar dakin, kan gadon ya gyara musu ya jera pillows kamar yadda suke sannan ya kintsa dakin tsaf, turaren wuta na tsinke ya kunna kafin yafita ya koma falo.

Koda tafito daga wankan tsaf ta samu dakin murmushi tayi ta zauna ta fesa kwalliya, bayan tayi wanka da madarar turare kala kalane ta dauko kayan da zata saka, wata jar riga mai budadden gaba taciro marar hannu sai wasu jeloli guda biyu da ake zargesu ta wuya sannan tsayin rigar duka duka bai kai koda kugunta ba, bakin wando tasaka wanda ya lafe ajikinta gaba daya marar nauyi sannan ta saka bakar hula mai gashi,

Falo ta nufa sakamakon yunwar da takeji, Aliyu yana kwance saman three sitter yana kallo, jin motsinta a dining area yaja hankalinsa, ahankali ya daga kai ya kalleta tuni ya nemi sumewa awurin sakamakon tafiya da tunaninsa gaba daya da shigarta tayi dashi kasancewar dukkanin kirar da Allah yabata yau ta gama bayyana ta cikin tufafin da ta saka, kasa komawa ya kwanta yayi sai zaune yatashi ya kura mata ido, ita kuwa breakfast dinta take kwasa cikin sauri tamkar itada wani suke ci dan tsananin yunwar dake damunta, ba kadanba indomie da kwan suka yi mata dadi domin komai yaji daidai misali shiyasa ita bata da matsala ta fannin girki domin Aliyu ya iya kusan dukkan girke girke sabanin wasu mazan da ko ruwan zafi wahala yake basu wurin dafawa.

Sai da ta gama ta koshi sannan ta nufi wurinsa, zaune ta ganshi ya tallafe kuncinsa da tafukan hannayensa yana kallonta ko kiftawa bayayi, shi dinma kananan kayane ajikinsa wanda mafi yawan lokuta yafi sakasu idan yana gida, farin wando three quarter sai riga t shirt maroon colour, sosai yafito mata adan saurayi wanda kuruciya ta samu muhallin zama awurinsa,

Agabanshi ta durkusa ta dafa gwiwowinsa tana kallon fuskarshi, kurawa juna ido sukayi har tsawon wani lokaci kafin ta janye nata idon tana murmushi,

“Darling brother ina kwana?”

Saida ta sake maimaitawa sannan yayi firgigit, dagota yayi gaba daya ya sakata cikin jikinsa acikin wuyanta yayiwa kanshi masauki yana shakar kamshin jikinta, cikin rada rada yake amsa mata,

“Kin tashi lafiya my love? Ina fata dai baccin ya isheki Sarauniyar mata, ko zaki sake wani yanzu in tayaki?”

Lumshe idonta tayi ta kwantar da kanta kan kafadarshi bayan ta daga masa kai alamun ehh,

Zamewa yayi ya kwanta kan kujerar yana rike da ita,asamanshi ya kwantar da ita yana shafa gadon bayanta wanda ke bayyane,

“Sadiyayye nah….!” Yakirata cikin rada,

“Uhmmm…!”

“Yi baccin to my love…., ina mutukar sonki leemah nah”

Murmushi tayi takai bakinta kan wuyanshi bayan ta saka hannunta cikin rigarshi tana shafa cikinshi zuwa kirjinsa,

Kamar yadda yake mata magana ahankali rada rada ita dinma haka take yimasa maganar,

“Yaya Aliyu nima ina sonka sosai, kaine mahadin rayuwata bazan taba iya jure rashinka ba……”

Lumshe idanuwanshi yayi jin abinda tace, hannunta datake wasa dashi a kirjinshi ya rike,

“Daina yimin tafiyar tsutsa….”

“Kaima fa haka kake yimin”

Murmushi yayi shima yafara kwaikwayon abinda take yimishi, ganin suna kokarin fadowa kasa yasashi ciccibota suka dawo saman rug gaba daya.

K’arfe daya daidai yafita masallaci bayan sunyi wanka, ita dinma salla tayi bayan ta idar ta shiga kitchen, lokacin da yadawo yajita cikin kitchen binta yayi, tare sukayi girkin suna aiki suna zuba soyayya har suka kammala girka shinkafa da miya sai vegetables salad.

Tare suka ci abincin cikeda kulawa suna ciyar da junansu, lemon kankana suka kora dashi sannan ta tattare kayan takai kitchen, hada komai da tayi amfani dashi tayi zata dauraye taji motsinsa abayanta, rungumeta yayi ta baya ya tayata suka wanke kayan sannan suka fita, shiryawa yayi zai fita domin jiya lokacin da ya dawo yabar wata mota da yasoma gyarawa yace kar ataba sai yadawo zai karasa da kansa kuma sai bai komaba, ita ma shiryawa tayi suka fita tare,tana kokarin kulle kofa taji ya rungumeta yana sinsinar jikinta, karasa rufe kofar tayi ta juyo tana kallonsa har lokacin yana rikeda ita ajikinsa.

Kallon juna sukayi suka saki murmushi atare, kissing din goshinta yayi sannan suka nufi part din ummi, kokarin kwace jikinta ta shiga yi daga nashi domin tana mutukar jin kunyar ummi, murmushi yayi yasaketa daidai lokacin da zasu shiga balcony din ummin,

Tare suka shiga, kishingide suka isketa saman center carpet tana kallo ga carbi a hannunta tana ja,ba kadan ba Aliyu yaga ummin nashi ta canja domin taci ado sosai wannan dalilinne yasa kuruciya samun wurin zama awurinta,

Zama yayi agefen ummi cikeda shagwaba, kallonsa halima tayi bayan ta zauna can nesa dashi, cikeda kulawa ummi ta tashi zaune tana yimusu barka da zuwa musamman ma halima wacce ummin ke jin kaunarta har cikin ranta,

Ganin ba tashi ummin keyiba ya mike tsaye bayan sun gaisa, cikin shagwaba ya kalli ummi,

“Shikenan ummi bari inje intafi tunda na fuskanci yanzu andaina yayina….”

“Allah ya kiyaye hanya, andaina yayinka kam yanzu yayin ‘yata nake”

Kallon halima yayi fuskarshi kunshe da murmushi,

“Sai na dawo sweety…” Yace da ita bayan ya kashe mata idonshi guda daya, sunkuyar da kanta tayi cikeda kunyar ummi,

“Adawo lafiya” shine abinda ta iya ceda shi kadai, wucewa yayi yafita ummi nayi masa addu’ar dawowa lafiya tareda nasara da samun alkhairai afitar tashi.

 

_Fatan alkhairi gareku aduk inda kuke, Feedhom, Mrs salees,Khairat D/dawaki, hussaina Dan larabawa, Anty baraka,Mamie hamma da duk wanda ban ambata ba._

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
[12/21, 2:55 PM] 0mmr Farouk: © *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI….!*🤴🏻

 

_*NA*_
*_UMMI A’ISHA_*

_DEDICATED TO FIDDAUSI SODANGI_

 

*46*

 

***Duk da tana jin kunyar ummi saida ummin tayita janta da hira wanda ita kuma dakyar take iya maida mata da amsa domin har yanzu ta kasa sakewa da ummin saboda kasancewarta mahaifiyar mjinta wannan dalilinne yasa take yi mata kallon suruka akoda yaushe duk da cewar ita ummin kusan kullum tana fada mata cewa ita a matsayin ‘ya take kallonta ba wai suruka ba,

Tajima sosai a sashen ummi kafin ta tafi sashen umma, can kam bararrajewa tayi ta cire mayafinta ta ajiye suka sha hirarsu da umma, saida aka kira sallar magrib sannan tayiwa umma sallama ta koma part dinsu tana dauke da tuwon semo miyar ganye wanda akayi na dare,

Bude falon tayi ta shiga, saida takai abincin saman dining sannan tawuce bedroom, agurguje tayi wanka tafito ta mulke jikinta da oil na mukhalatul taibah sannan ta saka doguwar riga marar nauyi baka mai santsi, abin salla ta shimfida tayi salla tana idarwa ta cire hijabin ta fita falo hakan yayi daidai da shigowar Aliyu,tsayawa tayi tana kallonsa takalminsa yacire ya karaso gareta, hancinta yaja kafin ya kamo hannayenta yana kallonta fuskarshi dauke da murmushi,

“Sannu da zuwa Yallabai…” Tace dashi itama tana murmushin,

“Yawwa sadiyayye nah…, yakike? Kinyi missing dina kuwa?”

Saida ta dan dara sannan ta kalleshi takai hannu kan gemunshi tafara ja sannu sannu,

“Nayi missing dinka mana,shine katafi kabarni inata missing dinka….” Tafada cikeda shagwaba,

Janta yayi zuwa kan kujera yazauna tareda dorata saman cinyarshi,

“Yi hakuri my love…., aikinne ya dauki dogon lokaci shiyasa amma bada niyya na jima ba…!”

Goshinta yake kissing zuwa wuyanta yana shakar kamshin dake fita daga jikinta,

“Muje inbaka abinci kaci…. Tuwo ne wanda umma tayi”

“To godiya nake, muje”

Mikewa yayi yana rikeda hannunta nan ta noke kafada alamun a’a cikeda shagwaba tace,

“Nidai ka goyani”

Murmushi yayi ya duka yana cewa,

“Zaki bani punishment kenan lovely wife….”

Batayi magana ba ta dale bayanshi tana murmushi, rungumeshi tayi sosai tabaya, maimakon yayi dining area din sai kawai yafara zagaye falon da ita abayanshi daga karshe ya lelleka sauran bedrooms dinsu yana cewa,

“Ya kamata yau mu sauya dakin kwana ko?”

Kwantar da kanta tayi tana murmushi,

“Nidai ba yau ba…”

“To shikenan duk yanda kike so haka za ayi ranki yadade…”

Ya dade da ita abayanshi daga karshe ya kaisu dining table, tuwon da tazo dashi suka ci cikin so da kauna suka ciyar da junansu.

Sallar isha yafita bayan yadawo yace suje su gaida Abba, ba karamin murna tayi ba nan suka rankaya suka tafi can sukayi hira domin sun iske su umma acan, basu baro part din abba ba sai 10 nadare.

A daddafe tayi wanka bayan dawowarsu daga sashen Abba sakamakon ciwon da mararta ke danyi mata sama sama,

Karfin hali kawai takeyi wurin biyewa Aliyu lokacin da ya kwanta kusa da ita yana yimata yan wasanni, da kanshi ya fuskanci kamar akwai abinda ke damunta nan yafara tambayarta cikeda kulawa,

“My love kamar bakya jin dadi ko? Fada min meke damunki…”

Saida ta kwantar da kanta saman kirjinshi sannan ta bashi amsa da cewa mararta ke ciwo, kwantar da ita yayi kan pillow ya sauka daga kan gadon, kasancewar bashida magungunan da zai hada mata na musulunci yasashi samo mata ruwan zafi mai dan dumi sosai amma ba can ba, kan gadon ya koma,fara tas din sleeping gown din dake jikinta ya cire yabarta daga ita sai farin pant, ruwan dumin ya soma jika karamin towel dashi yana gasa mata mararta zuwa waist dinta da bayanta,

Lumshe ido halima tayi domin tana jin ciwon yana dan raguwa da kadan kadan, wani sauki taji yana saukar mata babu tsammani, sosai gashin ke yi mata dadi saboda tamkar a aji aka saka Aliyu aka koya masa yanda ake gashin domin bin kowacce gaba ta jikinta yake yi yana gasa mata sannu sannu cikin nutsuwa sannan cikeda kulawa.

Tana can duniyar tunani bata ankaraba taji gashin ya koma kirjinta kamar yasan ciwon nata har da nan, kasa daidaita nutsuwarshi yayi sakamakon abinda idanuwanshi ke gane masa, ahaka yagama gasa mata jikin nata duk jikinsa amace, komawa yayi ya kwanta ya rungumeta.

Washe gari garau tatashi wanda hakan ba karamin mamaki yabata ba domin bata taba yin period cikin sauki ba sai wannan, wanka tayi ta shirya tahaye gado ta kwanta domin lokacin 6 da yan mintuna.

Bata wani jima da kwanciya ba Aliyu ya shiga dakin domin tun lokacin da yadawo daga masallaci a falo yayi birki, ganinta yayi sanye cikin riga da wando dukkaninsu kalar ruwan hoda duk da bata yiwa fuskarta wani dogon kwalliya ba amma tayi mutukar kyau gashi inbanda kamshi babu abinda ke fita daga gareta, zama yayi agefenta ya kai hannu ya dafa kafadarta yana kallonta,

“Good morning darling brother…”

Murmushi yayi jin abinda tafada, maimakon ya amsa sai ya mika mata hannunshi kamar yadda yasaba dan suyi musabaha,

Kama hannunshi tayi ta matse cikin nata tana kallon kyakkyawar fuskarshi,

“Yayana baka amsa gaisuwa ta ba”

Tace dashi tana shafar hannunshi, murmushi yayi ya tallafe kumatunshi da hannunshi guda daya yana kallonta,

“Ba kin amsawa nayi ba, ya jikinki? Shine baki jirani nazo nakara gasaki ba kika shirya”

Saida ta rufe fuskarta sannan tace,

“Nifa nawarware darling brother….”

Hannunshi yakai saman mararta yashiga shafawa,

“Dagaske….?,kwana nawa zakiyi kinayi?….”

Har lokacin idanuwanta arufe suke jin tambayar da yayi mata yasata bude idonta ta kalleshi,

“Kai darling brother….. Kwana biyar ne fa babu yawa….”

“Awurinki ba, nidai awurina dayawa gaskiya, nida nake son da inji kince gobe ko jibi zaki gama…”

“Saboda me?”

“Saboda ina son mu raya sunnah…”

Murmushi tayi ta sake rufe idonta, gefenta yabi ya kwanta yana yimata dariya, ita dai daga karshe baccine ya kwasheta ba ita ta tashiba sai 11 saura, tana ta saurin taje ta hada breakfast ta hangoshi acikin kitchen din yana soya chips da kwai,

Jin motsinta yasashi juyawa ya kalleta, kallonshi tayi daga shi sai gajeren wando blue,

Abayanshi ta tsaya ta rungumeshi,

“Sannu da aiki…”

“Wai har kin tashi daga baccin?”

“Haba darling brother har ne ma? Nabarka da yunwa ina naga ta bacci…”

Murmushi yayi ya kwashe chips din sannan ya kashe gas din,

“Muje kiyi breakfast ni wanka zanyi…”

Hannunta ya kama yana rikeda tea flask ita kuma tana rikeda food flask din da ya zuba chips aciki,

Afalo yabarta shikuma ya shiga wanka, motsin karar kofar kitchen tabaya da ta jiyo yasata tashi ta leka, ganin kofar abude abin yabata mamaki domin ita lokacin da ta shiga wurin Aliyu da yana aiki sam hankalinta bai kai wurin ba,

Lekawa ta danyi bayan part din nasu nan ta hangi abin mamaki domin kayanta ne jere akan igiya Aliyu yawanke mata kama tun daga inner wears da kayan baccinta wadanda tayi amfani dasu har zuwa yan kayan da tasaka domin tun zuwanta gidan batayi wanki ba sai na panties.

Gefe daya kuma shima nasa gajerun wandunan ne da fararen vest, maida kofar tayi ta rufe sannan ta nufi ciki, yana kokarin zama kan daya daga cikin kujerun dake zagaye a dining area tashiga, tun daga nesa take kallonsa tana shakar kamshin dadin dake tashi daga jikinsa domin duk turarukanshi masu mutukar karfine, hannu ya mika mata ya zaunar da ita saman cinyarshi,fuskarshi take kallo wacce akoda yaushe kyawunta take gani yana karuwa ga gemunshi wanda keta faman sheki, dark blue din yadin kufta yasaka wanda aka yiwa aiki da bakin zare sannan andora farar kwala irin dinkin samarin zamani,

“Darling brother ashe aiki kayi sosai…., shine harda su yimin wanki? Breakfast dinma da ka hada ai ya isa basai ka wahalar da kanka ba wurin wanke min kayaba,kuma kaga ga washing machine ma ai da kawai sai awanke dashi….”

“Haba sweetheart, dan nayi miki wanki menene? Karfa ki manta kece sirrina sannan kina da babban matsayi agareni….,ni bana bukatar yin wanki da wani washing machine gara kawai nawanke miki da kaina….”

“To abawa mai wankin abba mana”

“Kai kai….. Lallai sadiyayye na, abawa mai wanki fa kikace”

“Ehh mana ai yafi dai akan azo a iskeka kana yimin wanki”

Dan madaidaicin bakinta da take turo masa yakaiwa cafka,

“Baki san ina kishinki dayawa ba ko? Tayaya zan iya bawa wani kayanki ya wanke? Ai gara nawanke da kaina komai yawansu da inbawa wani, nidai nahada nawa kayan nabashi zai wanke….”

Kallonsa tayi tana shafar gemunshi,

“Meye abin kishi acikin wanke kaya?”

“Bana son kowa ya gane min wadannan kuma kinga har wani dan gida ake yimusu…” Ya karashe maganar yana pointing din kirjinta tareda kai hannunshi wurin, makale wuyanshi tayi bayan ta cusa fuskarta cikin kirjinshi,

“Nagane wayonki dai, kawai kedai kina son jin kamshin jikina shine zaki wani fake da jin kunya amma nasan babu wata kunya da kike ji, keda kike alla alla na taba….”

Jin abinda yace yasata dagowa da sauri tana kallonshi shi dinma ita yake kallo nan idanuwansu suka hadu hakan yasata kwabe fuska ta soma yimasa shagwaba kamar zatayi kuka,

“Nidai Allah yaya Aliyu bana so, yaushe kaga ina so…?”

“Au infada suji?”

Jin abinda yace yasata saurin rungumeshi ta boye fuskarta akirjinshi tana dukanshi,

“Allah kaga bana so…”

“Allah nasan kina so…”

Tea ya hada a cup yanayi yana tsokanarta nan yaci gaba da bata tea din da sauran kayan soye soyen sai faman tsokanarta yake tun tana cewa ba haka ba har ta dawo tace ehh tana so din, cikin barkwanci da armashi suka gama breakfast din lokacin 12 saura mintuna 20,goyonta yayi ta rakashi balcony anan ya direta suka tsaya yin sallama,sai da sukayi sallama ta musamman sannan yatafi yana mai shafar kumatunta,

“Kije ki kwanta kiyi bacci gimbiya…., karki tashi saina dawo tunda kinga ai kina fashin salla balle ace zaki tashi lokacin salla…”

Murmushi tayi itama tayi digirgire ta shafi nashi kumatun,

“To adawo lafiya, ban yarda wadannan sexy and beautiful eyes din su kalli kowacce maceba……”

“Insha Allah zan runtse idanuwana bazan kalli kowacce maceba har sai nadawo gareki sannan zan budesu…., dama kuma ke kadai suke iya kalla”

Janyoshi tayi ya rankwafo saitinta nan ta bashi wani sanyayyen kiss a kumatunsa da lips dinsa, dakyar suka rabu ya tafi yana waiwayenta, ita dinma tsaye tayi ta jingina da karfen dake zagaye da balcony din ta harde hannuwanta akirjinta tana kallonshi, dukkansu ba karamin kyau sukayi a idon junansu ba……..

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI….*🤴🏻

 

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

_DEDICATED TO FIDDAUSI SODANGI_

 

*47*

 

***Dan murmushi tayi ta juya ta koma ciki, kamar yadda yafada bacci ta kwanta tayi mai isarta dan yau ko wurinsu umma bata samu lekawa ba,

K’arar wayarta ne ya tadata tana tsaka da bacci, ganin Aliyu ne yasata komawa ta kwanta bayan ta kara wayar a kunnenta,idanuwanta ta lumshe lokacin da taji yana yimata sallama,

“Sarauniyar mata ayi min afuwa na tasheki kina tsaka da yin bacci ko? Tuba nake…..” Taji yafada bayan ta amsa masa sallamar,

“Darling….., ya aiki?”

Murmushi taji yayi sannan ya amsa mata,

“Lafiya lau amma ba sosai ba tunda kinyi nesa dani”

“Nima inata missing dinka ai, kabarni ni daya agida…”

“Sorry my love ai nakusa dawowa, bayan tafiyata me da me kikayi?”

“Bacci…..” Ta amsa masa ashagwabance,

“Meyasa ba kici abinci ba? Bana son kina zama da yunwa fa”

“Ni bana jin yunwa, na koshi…”

“To shikenan ki kwanta kici gaba da bacci tunda bakya…..”

Shiru yayi bai karasa ba sakamakon tunawa da yayi ba shi kadai bane awurin akwai yaransa dake ta faman kaiwa da kawowa kuma suna ji.

“To nagode, sai ka dawo, i love u…”

“I love you too….”

Kashe wayar yayi bayan ya amsa mata, yana kokarin saka wayar acikin aljihunsa nagaba yaji Dan larai na fadin,

“Oga ko har anfara neman ta biyune?”

Murmushi Aliyu yayi yai masa shiru yaci gaba da aikinsa.

Ita kuwa halima bayan sun gama waya da Aliyu baccinta tasake komawa wanda yakaita har karfe 2 saura, kitchen ta shiga bayan tayi wanka ta shirya cikin Pakistan kalar ruwan kasa,

Sassaukan abinci tayi domin bata jin karfin jikinta, ta kammala kenan ko fitowa daga kitchen din batayi ba taji shigowar Aliyu, cikin kitchen din yabita lokacin tana kwashe abincin acikin food flask,

“Sannu da kokari, shine baki bari idan nadawo nayi girkin ba kika wahalar da kanki?”

“A’a Darling brother ai zan iya,menene amfanin zamana agidan indai bazan girka maka abincin da zaka ci ba”

“To ai hakkina ne inciyar dake leematu nah…”

“Duk da haka dai…”

“To shikenan Allah yayi miki albarka”

“Amin” ta amsa tana murmushi saboda jin ya saka mata albarka,

Shi ya tayata daukar abincin da filet da spoons din da zasuyi amfani dashi, wanka yafara yi sannan yafito falo inda take zaune tana jiransa, zama yayi akusa da ita ya karata da jikinshi suka shiga ciyar da juna domin ya fahimci kamar bata ra’ayin cin abincin, suna ci yana yaba kwalliyarta da haka suka gama,

Tare suka fita ta shiga sashen su umma shikuma ya tafi masallaci ta can kuma ya wuce islamiyya.

K’arfe 8 yadawo gida, a part din umma ya sameta domin yanzu kunyar ummi take ji idan taje bata sakewa da ita sosai, rankayawa sukayi suka tafi part dinsu, indomie da kwai ta dafa musu ta zubo ta kawo falo domin anan tabarshi abin mamaki sai ta iskeshi yana goge kayanta wadanda ya wanke mata da safe, katse gugar yayi ya zauna suka soma cin abincin,har 10 yakai yana gugar kayanta ita kuma tana gefenshi tana tayashi hira idan tace yakawo ta tayashi kuma yaki yarda da haka har yagama suka shiga bedroom

Kayan jikinshi ya soma kokarin cirewa nan ya saka hannunshi a aljihun rigarsa, kwalbar turaren almiski ya ciro guda biyu ya mika mata,

“Ungo sakonki mantawa nayi tunda nashigo ban bakiba….”

Karba tayi tana dubawa, turaren nada mutukar kamshi gashi da kauri sosai kuma fari ne kal kamar koko,

“Ajikina zan rinka shafawa?”

Murmushi yayi ya karasa cire kayan jikinshi sannan ya kalleta yana rikeda kugunshi,

“Idan kin gama period zakiyi amfani dashi…..”

Murmushi tayi tabude mirror drewar dinta ta zuba su ciki tana fadin,

“Darling Aliyu kenan…..”

Ta rigashi shiga wanka domin shi yatsaya bincike cikin laptop dinshi wanda bata san ko namenene ba, saida ta fito sannan yashiga yana tsokanarta,

“Maimakon ki jirani muyi tare shine zakije kiyi ke daya? Sunnah ce fa mai karfi garama ki sani….”

“Gara dai kowa yayi nashi daban, ban so kaga kazanta….”

“Kece ke ganin haka, ni ina kaunarki da bukatarki cikin kowanne hali….”

“To kashiga kafito sai mu karasa hirar…” Tayi hanzarin katse zancen,

Shiga yayi ganin haka yasata saurin kimtsa jikinta turaren da ya kawo mata ta disa ajikin pant dinta kafin tasaka pad sannan ta disa a hannunta ta shafe cinyoyinta dashi zuwa mararta,

Sosai ta dauki kamshi sakamakon kalolin turarukan da tayi amfani dasu masu dadin gaske banda humra yan gasken,

Rigar bacci ta dauko ta saka skye blue sannan ta saka bakar hula mai gashi,

Tana kwance tana latsa wayarta yafito nan shima ya shirya yaje kusa da ita ya kwanta dama jiransa take babu bata lokaci ta shige masa jiki, kamshin da yaji daga gareta ne ya rikitashi duk da yau yayi niyyar kyaleta tayi bacci amma kamshinta yasashi gazawa dole saida suka yiwa juna yan wasu abubuwa.

Ta rigashi yin bacci dan haka yasata tsakiyar kirjinshi ya kwantar da ita yana shafa kanta har shima baccin ya daukeshi, amma karfe uku yatashi yayi nafila kamar yadda yasaba.

Haka yayita riritata tamkar wata jaririya har ta gama period dinta, ita kawai kallon Aliyu take domin ya shallake tunaninta saboda ana igobe zata gama period baba tabawa ya bawa sako ta tahowa da halima da ganyen magarya cikin yaluwar leda,yace ta tafasa idan tayi wankan tsarki ta rinka kama ruwa dashi, makale kafada halima tayi tana kwance ajikinshi a falo saman kujera, kallonta yayi yana lasar lips dinsa,

“Haba sadiyayye nah, sunnah nefa amfani da magarya da almiski bayan gama jinin al’ada saboda matan manzon Allah ma haka sukeyi….”

“Tab, nida har yanzu ban gama tashi daga amarya ba waya aikeni sake matse…..”

“Ke raguwa ce gaskiya…., keda bakima wani sha wahala ba, amare na kukan wahala ke amma naki kukan na jin dadi ne wai wani nan bakiji zafi ba kuma bakiga jini ba….”

Dariya tayi ta sake rungumeshi,

“Kaga bana so….”

“To nidai ki cire tsoron komai aranki kiyi abinda nasaki, haba leematu nah…, ke banda abinki ma akaron farko banyi garaje ba sai yanzu da nasoma sanin gari….”

Tashi tayi daga jikinsa daga shi har ita dariya suke,

“Darling brother baka da kunya Allah, katafi kawai sai ka dawo na sallameka…..”

“Au yau korata ma ake?”

“Uhm…, katafi sai anjima”

“Shikenan Allah yakaimu dare,ki nemi abokin kwana dan yau raba daki zamuyi….”

Jin abinda yace yasata yin dariya tashige bedroom tana cewa ehh tayarda,

Kasa hakuri yatafi yayi yabita bedroom din domin wata mini skirt ce iya cinya ajikinta orange colour sai body hug ita kuma baka, ko dan sunkuyawa tayi yakan hango pink din pant din dake jikinta shiyasa lokacin da yadawo gidan yaganta lokacin tana sunkuye gaban tv set tana saka sucket zata kunna kallo rufe fuskarshi yayi da tafukan hannunshi yana fadin,

“Subhanallahi….. One love me zan gani haka?”

Juyawa tayi ta kalleshi tana dariyar ganin abinda yayi wato rufe fuska,

“Halak dinka…” Tabashi amsa, jin abinda tace yasashi bude fuskarshi yana dariya,

“Ashe hakane fa, mantawa nayi, sweet sister kin dai dage sai kin mayar dani dan duniya karfi da yaji, kullum sai kin sani ganin abinda yafi karfin idanuwa na…, ohh ni Ali, da dai kam ban san komai ba, ban taba ganin komai ba amma yanzu sadiyayye ta sani nasan komai….”

Saman cinyarshi tazo ta zauna tana cewa,

“Wallahi dama can kasani kawai dai aikatawa ne baka taba yiba har saida kajira Abba ya aura maka ni, naga nasan irin littattafan da kake karantawa,wai dan Allah lokacin azuminka baya karyewa?”

Dariya yayi ya gyara mata zamanta akan cinyarshi yana sinsinar wuyanta,

“Yana karyewa mana idan naganki amma bawai dan na karanta wadannan abubuwan ba…”

Hannunshi ta soma turewa tana dariya saboda jin yasoma yimata tafiyar tsutsa a wuyanta,

“Kar kamin sharri malam ni ban taba karya maka azuminka ba…”

“Ai yafi akirga yarinya, shiyasa tun farko na hanaki zuwa gidanmu saboda farkon ganina dake saida kika tashi azumina daga aiki, kuma daren ranar har mafarkinki nayi saida kika yimin sanadin wanka da ruwan sanyi da asuba….”

Dariya halima tayi masa sosai harda su kwalla.

Binta cikin bedroom din yayi tana gaban wardrobe yakarasa kusa da ita, saida ya dan rage zafin da ta hada masa sannan yayi mata sallama yafita.

Washe gari tafara salla bayan tayi duk yanda ya umarceta na yin amfani da miski da ganyen magarya domin sunnah ne, da zai fita yatafi da ita ya sauketa gidansu Sabira domin tayi mata kitso,

Tunda Sabira taganta take santinta saboda hasken da ta kara yi tamkar wacce aka sauyawa fata sai faman sheki take nan Sabira tasoma tsokanarta tana cewa ciki gareta, shiru halima tayi mata tana dariya domin bata manta hudubar da Aliyu yayi mata na banda barbadar da sirrinsu domin ranar tisata yayi agaba da rokonta akan ta kiyaye masa sirrinsa,

K’arfe uku yazo ya dauketa suka tafi, ta anam restaurant ya biya dasu domin yin lunch saboda yace yau halimanshi ta huta babu girki yau dashi kawai yake son taji, ita Aliyu mamaki yake bata gashi dai ustaz amma abubuwa dayawa baya kyanatarsu mutukar ba addini ne ya hanaba, ta tabbata maza dayawa baza suyi haka,

Dashi da ita kowa order din abinda zaici yayi, shi tuwon shinkafa miyar ganye ita kuma sakwara, kallonshi halima tayi lokacin da suka fara cin abincin,

“Darling brother babu ruwanka da kunyar mutane…”

“To ai ba ni kadai nazo ba da mutuncina nazo tunda ina tare da matata ko?”

Murmushi tayi, “mufa saurayi da budurwa ne”

Daga mata kai yayi tareda dage girarshi guda daya yana kallonta,

“Kin rage mana matsayi kenan, nida nake son angoncewa muna komawa gida idan kikace haka ai sai ummi tazo zaman jinyata…”

Dariya tayi itama,

“Kajishi….kai dinma ashe ragon ne”

“Lalalahhhhhh nidin? To bari muje gida zan nuna miki jarumtata kuwa, ai Ali ko afilin yaki yakan nuna shi gwarzone”

“Kenan yau mu dinma yakin zamuyi?”

Dariya yayi ya kalleta,

“Da alama dan yau sai inda karfina yakare”

“Ko?” Ta bukata,

“Zakiga tabbaci idan mun koma, kin san ni banida juriyar barin dare yayi, wancanma da rana tsaka akayi dan rashin kunya kuma kika bude ido kina kallona ko?”

Dariya tayi tasa hannu daya ta kare idanuwanta,

“Kai yaya Ali… Nifa ban kalleka ba”

Manyan fararen idanuwanshi ya zuba mata,

“Sai dai kar akuma, naganki fa”

Dariya tayi batace komai ba har lokacin kuma bata bude idonta ba,

“Yanzu dai ai kingane dalilina na hanaki siyan mirror bed ko? Ni dan every time ne, koda yaushe zan iya bukatarki ba sai dare ba….”

Jin tayi shiru kuma taki bude fuskarta yasashi sake matsawa kusa da ita,

“Ban son gulma kawai ki bude idonki sadiyayye, anjiman ma ki zuba min idon ki kalleni son ranki halak dinki ne…., yi sauri ki gama ki tashi mutafi gida”

Bude idonta tayi amma taki kallonshi nan taci gaba da cin sakwararta wanda shi tuni yagama nashi, wata budurwa dake can yamma dasu tun shigowarsu taji sun burgeta domin duk atunaninta saurayi da budurwa ne saboda yanda taga suna ririta juna da kulawa da juna, tana kallonsu sai hirarsu sukeyi kasa kasa domin ko akusa dasu kake bafa zakaji me suke cewa ba wannan dabi’ar Aliyu ce mutukar zaiyi magana da halima to sai ya rage murya koda kuwa su biyune awajen musamman ma idan da daddare ne lokacin kam gaba daya maganarsu rada rada take komawa wanda har halima ta koya itama, da wuya kaji tana yimasa magana muryarta asama, ganin suna kokarin tashi su fita yasa wannan budurwar azamar mikewa daga mazauninta cikin zuciyarta tana kudurta cewa saita raba wadannan masoyan biyu sakamakon wani boyayyen al’amari dake cikin zuciyarta.

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

 

_DEDICATED TO FIDDAUSI SODANGI_

 

*48*

 

***Jerawa sukayi suka fita daga cikin restaurant din wanda ya amsa sunansa domin ba kowa ke ziyartar wurinba sai manyan yara sannan masu da akwai.

Saida ya bude mata gaban motar ta shiga kamar yadda yasaba sannan ya zagaya side din driver shima yashiga,har motarsu tabar wurin wannan matashiyar budurwar na biye dasu atata motar,

Kallonshi halima tayi hannunta daya cikin nashi,

“Darling brother ya naji hannunka da dumi?,ko baka jin dadine?”

Saida yayi murmushi sannan ya daga mata kai bayan yacire hularshi ya ajiye agefenshi,

“Kawai tsananin bukatarki ne fa….”

Murmushi tayi tana harararshi awasance,

“Au hararata ma kikeyi akan nafadi gaskiyar abinda ke damuna?…. ”

“Nidai ka kyaleni bacci nakeji”

“Bakida matsala madam…”

Murmushi tayi ta kwantar da kujerarta, har suka kusa zuwa gida babu wanda yakara magana acikinsu, sai dai yakan dan tsokanota ta hanyar tabota lokaci lokaci batace masa komai sai dai tayi murmushi, saida yatsaya ya sai musu fruits da tsire sannan suka karasa gida,

Tun afalo ya zame dan kwalinta yana son ganin kitson da sabira tayi mata, 2 step ne mai zigzag sosai kitson ya zanu kuma yayi kyau, shafa kitson yafara yi yana yaba kyan da yayi, fruits din da suka shigo dashi kawai suka sha yace suje suyi wanka,duk kunyarshi da takeji kin barinta yayi yace sai sunyi wankan tare yakare maganar da cewa,

“Bana son gulma nasan kin dade kina son muyi wanka tare shine yanzu zaki wani bijire, muje….”

Sakata yayi agaba tana turturjewa ita adole kunya amma bai hakura ba saida yakaita har ciki,

Tun acikin bathroom din al’amura suka soma tafiya dama abinda yake muradi kenan daga karshe daukota yayi suka dawo cikin daki, fadin irin soyayyar da ya nuna mata bata bakine, ita kanta halima sosai yau taji takara kaunar mijin nata domin ya shayar da ita zumar soyayya.

Kwanciya lamo tayi ajikinsa tana sake kankameshi kamar zata koma cikinsa, murmushi ya sakar mata bayan sun hada ido, cikin sauri ta kawar da fuskarta wai kunya,

Kanta ya shafa ya kamo jelar kitsonta yana wasa da ita,

“Kitson nan naki yayi kyau my love….,sai dai yanzun nan…. Zai sha ruwa…” Ya karashe maganar yana yimata dariya,

“Ai wallahi kaine….”

Dago kanta yayi yana kallonta,

“Nine wa? Kema fa dama a matse kike one love, Allah dama kema alla alla kike nace miki kule kice cass…..”

Jin abinda yace yasata murmushi tana boye fuskarta,

“To yanzu dai katashi lokacin salla yawuce…”

Sai lokacin ya maida hankalinshi ga agogo, karfe 5 harda mintuna 56 agogon yanuna babu shiri yatashi tareda daukarta sai cikin bathroom.

Agaggauce suka fito yajasu salla sukayi,bayan sun idar ya mike ya soma shirin fita, ita kam kishingida tayi tana kallonsa hannunta rikeda casbaha tana ja,

“Yawwa nikam wai yaushe zaki fara zuwa makarantar islamiyya ne?”

Kallonshi tayi ta makale kafada alamun a’a,

“Meyasa ba zakije ba?”

“Ni inada malami na agida”

Abinda tafada ne yasa shi yin dariya,

“To shikenan tunda kince haka, insha Allah zan tsaida lokaci inci gaba da koya miki….”

Daga kanta tayi taci gaba da kallonshi har ya kammala shirinsa, tare suka fito ta rakashi sannan ta koma falo bayan tafiyarshi.

Zama tayi bayan ta yanko fruits akan faranti, fork tasa tafara sha tana kallon tashar zee cinema da haka har lokacin sallar magrib yayi. Saida akayi sallar isha sannan Aliyu yadawo bayan yabiya ta sashen su Abba, hannunsa rikeda food flask yashigo wanda dagani ummace ta bashi yakawo mata ko ummi, agefenta ya zauna jikinsa cikin nata, karbar flask din tayi ta bude nan taga farfesun kifi manya manya, filet tatashi ta dauko musu ta juye musu, abaki yarinka bata cikeda kulawa har suka cinye,kwanciya tayi bisa cinyarshi tana yimasa shagwaba shikuwa ya biyeta yana riritata gamida lallabata. Kasancewar yau agajiye take ta rigashi kwanciya dan lokacin da yazo dakin har ta jima da yin bacci, addu,a yayi musu bayan ya kwanta agefenta nan yayi mata matashi da kirjinsa ya rungumeta,

K’arfe 3 saura yan mintuna ya tashi saida ya iyo alwala sannan yazo yafara tashinta ahankali, ganin taki tashi yasashi shafa kumatunta da hannunshi wanda ke dauke da laimar ruwa babu shiri ta bude idonta sakamakon sanyin da ya ratsata, dakyar ya lallabata ta tashi tana hada hanya sakamakon baccin dake idonta, bathroom tashiga kafin tafito ya shimfida musu abin salla yafito mata da hijabi da zanin da zata daura,

Sosai suka raya wannan dare da sallolin nafila domin har aka kira assalatu suna tsaye suna gabatar da ibada, saida sukayi sallar asubah sannan suka kwanta nan kuma taji mutumin nata yasoma nuna alamun abinda yake bukata, turo baki tayi tana cewa ita bacci takeji nan yashiga lallabata yana cewa bashifa da lafiya idan har bata aminceba Allah zazzabi zaiyi, da haka ya lallabata yasamu abinda yake so wannan dalilinne yasata wuni akwance tana bacci domin ko sanin lokacin da yatashi batayiba, har ya gyara musu gidan ya hada musu breakfast yayi wanka yashirya duk bata saniba, bai tasheta ba ya karya ya fita lokacin karfe 11:20 nasafe.

Ba ita ta tashiba sai 12 da wasu mintuna, bayan tayi wanka ta shirya cikin wata body hug ja da bakin short nicker iya gwiwa falo tafita ta zauna bayan ta debo abinci zata karya, wayarta ta dauka tana dubawa duk miss called din Aliyu ne samada guda biyar sai sako guda daya wanda yace,

_Sweetheart har yanzu baki tashiba,kiyi hakuri yau nafita batare da munyi sallama ba, ki kular min da kanki sannan idan nadawo zan sanar dake adadin farin cikin da kika sani yau da asubah, ina mutukar kaunarki & I soo much luv u…!_

Murmushi tayi ta tura masa reply yana gani ya kirata nan suka kwashe lokaci mai tsawo suna hira tamkar wasu saurayi da budurwa, kai kanka alokacin idan ba sani kayiba zaka zaci saurayi da budurwa ne ba miji da mata ba.

Suna zamansu lafiya gwanin ban sha’awa domin sunada fahimtar juna sannan uwa uba so da kaunar da suke yiwa juna, lokaci kankani halima ta goge ta ilmantu da ilmin zaman aure wanda take koya wurin malaminta Aliyu, yanzu kam har taso finshi zakewa da dokantuwa acikin rayuwarsu da suke gudanarwa, kullum cikin gayu da tsaftace jikinta take domin burgeshi, yana so yaci gaba da azuminsa na litinin da alhamis kamar yadda yasaba tun yana yaro amma ta hanashi,duk lokacin da yafadi haka dariya halima keyi masa,

Yauma kamar koda yaushe tana kwance tana bacci sama sama saman sofa shikuma yana zaune gefenta yana shirin fita, hannunshi yakai wuyanta yana shafawa dakyar ta bude idanuwanta ta kalleshi,

“Wai har kayi wanka zaka fita?”

“Ehh mana, ke ba kin zauna kinata bacci ba”

Murmushi tayi ta lumshe idonta,

“Malam kabarni inyi bacci kawai, ba kaine ka hanani baccin ba…”

Murmushi yayi ya kama hannunta,

“To shikenan kinga anyi 1-1 kin hanani azumi nikuma na hanaki bacci…”

“Ni nayarda kayi azumin yau da gobe harma da jibi duk kayi amma nima kabarni inyi bacci”

“A’a ban yarda ba, ai ko kallona kikayi muna hada idanu zai raunana ko ya karye”

Murmushi tayi tajuya taci gaba da baccinta yayinda shikuma yatashi ya bude closet yaciro farar shadda yasaka ajikinsa yasa hula,saida yayi kissing dinta sannan yafita falo, nan ya zauna ya karya sannan yafita ita kuwa tana kwance tana hutawarta.

***

Bincike sosai matashiyar budurwar ke gudanarwa dangane da Aliyu da duk wani abu wanda ya shafeshi domin yayi mutukar tafiya da tunaninta tun ganin farko da tayi masa,

Sai dai tayi tsananin mamaki lokacin da taji cewa wai yanada aure ita duk azatonta baida mata domin baiyi kamada magidanta ba, har ila yau ta shiga rudu lokacin da taji cewa sana’arshi kaninkanci ba awani ministry ko private organization yake aiki ba.

Zubawa kawartata ido tayi cikeda damuwa domin tagama kwallafa ranta akan Aliyu, sonshi take kamar zatayi hauka,

“Zarah yanzu yakike ganin zanyi? Kinga dai wallahi dagaske nake sonshi…”

Murmushi wacce aka kira da zarah tayi ta kalli kawartata mai zubin yan baraki kuma mai kamada yan duniya,

“Tinah wannan guy din kin san dai ba dan iska bane so bazaki taba samun shiga ba awurinsa….”

“Zarah waye yafada miki wannan harkar nake son yi dashi? Ni wallahi aure nake so muyi dashi”

Dariya zarah tayi saida tayi mai isarta sannan ta kalli teenah,

“Gaskiya bakida hankali…, yanzu har tunani kike wannan nutsattsen yaron zai aureki? Me zaici dake? Karfa ki manta shi ustaz ne marar son hayaniya da sabon Allah…”

“To shine me? Shine dan yana ustaz sai akace miki bazai so mata ba?”

“Koda ace zai so mata to zai so nutsattsu ne irinshi ba irinki ba…”

Mikewa tsaye teenah tayi tana huci sakamakon abinda zarah tafada,

“Zarah zan baki mamaki, ni teenah ina mai alkawarta miki cewa zan samu soyayyar Aliyu har kuma muyi aure”

“Ina neman tabbacin hakan…” Zarah tafada tana karkada kafa,

Batare da tasake magana ba ta sabi handbag dinta tayi gaba tana jin kwarin gwiwar cika burinta…..

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI….!*🤴🏻

 

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

_Gaisuwa da fatan alkhairi gareku masoyan leemah -Alee, wannan shafin tukwicine agareku._

*49*

 

***Tun daga wannan rana teenah ta saka damarar shiga cikin rayuwar Aliyu da matarsa halima, duk wasu motsi nasa ta sansu da wuraren da yake zuwa kama daga garejinsu zuwa makarantar islamiyyarsu domin wadannan wuraren guda biyu su kadaine wurin yawonsu idan ba nan ba to agida zaka sameshi.

Halima kuwa akoda yaushe burinta bai wuce ta faranta ran mijinta ba domin shima baida wani buri wanda ya wuce ya faranta mata, kullum akuma koda yaushe cikin yi mata hidima yake sannan gashi da iya tattalinta domin yanda yake tattalinta tamkar wata jaririya, wani lokacin hatta abincin da zasu ci shi yake dafa musu haka kowanne dare sai ya tasheta sunyi sallar nafila mutukar tana salla,wani lokacin ko bata sallar ma sai ya tadata tayi tilawar karatun alqur’ani. Yanzu kam tagama karantar mijinta tsaf sannan kuma tasan wanne kalar miji tasamu, kullum yana ware lokaci ya koyar da ita karatun addini kamar yadda yace sannu sannu kuma tafara daukar komai akanta,

K’arfe 1 saura kwata ta tashi daga bacci saida tayi wanka ta matse cikin English wears pink din riga armless da bakin three quarter sannan tashiga kitchen,dan wake tayi musu ta yanyanka vegetables da dafaffen kwai,saida ta kammala aikace aikacenta sannan gogan nata yadawo, hannunsa rikeda takardu,

Tsalle ta daka ta daleshi kamar yadda ta saba nan ya riketa har cikin bedroom tana makale dashi,

“Darling brother sannu da zuwa….”

Saida ya sumbaci bakinta sannan ya amsa fuskarshi dauke da nurmushi,

“My love, kinyi kyau sosai….”

“Nagode darling brother…., yanzu muje kayi wanka sai muzo mu ci abinci”

Tashi yayi kamar yadda tace, tare suka shiga bathroom din ta taimaka masa sannan suka fito, gajeren wando ne kadai ajikinsa suka wuce falo nan ta gabatar musu da abinci, shi dai yakasa daina kallonta domin ji yake kamar yau yasoma ganinta,

Iska yaji ta hura masa a idonshi da bakinta ahankali ya lumshe idonshi sannan ya budesu akanta,

“Kina rikitani dayawa sweetheart…, kinga ko abincin ma jinsa nake kamar bazan iya cinshi ba…”

Murmushi tayi ta shafi sajenshi,

“Gaggawar me kakeyi Darling…, ka daure kaci abincin nan, kasan dai bazan hanaka farin cikinka ba, ashirye nake da infaranta maka ranka”

Duk da yaji dadin maganarta amma hakan bai hanashi sakin baki yana kallonta ba domin sosai take bashi mamaki kwana biyun nan saboda irin yanda take fitowa fili ta nuna masa kauna sabanin da datake jin kunyarsa sosai, ada ko mu’amular aure sukayi bata iya hada ido dashi amma ayanzu ko yagama uzurinsa indai ita bata kammala ba sai ta fada masa duk ma ba wannan ba abinda yafi bashi mamaki shine kwana biyu da suka wuce da tsakar rana ta kirashi wai yazo bata da lafiya kasancewar ranar da wuri yafita aiki dan ko ma tashi daga bacci batayi ba amma koda yazo acikin bargo ya isketa daga ita sai wata yar guntuwar riga, yana zama kusa da ita ta kamoshi tana yi masa rada,

“Nayi missing dinka ne Darling….., sannan kuma kaga ai kwana biyu bamu ga junaba….”

Murmushi yayi saboda yagane abinda take nufi shiyasa babu bata lokaci yabada hadin kai yadda ya kamata.

“Wai Darling brother lafiyarka kuwa? Naga ka sakani agaba kanata kallona, tunanin me kakeyi?”

Sai lokacin hankalinsa yadawo jikinsa ya kalleta sannan ya maida hankalinsa ga abincin da ta zuba musu,

“Kawai tunanin rashin kunyarki nake yi baby…. Yanzu kiri kiri kike fada min kowacce irin magana, sannan babu kunya har gayyatata kike….”

Saurin toshe masa baki tayi bayan ta boye fuskarta jikinshi,

“Darling brother gaskiya bana so…”

Dariya yayi mata baice komai ba saiko kallonta da yakeyi wanda ke dauke da ma’anoni daban daban, abincin yasoma ci itama yana bata yana tsokanarta cewar yanzu ta koyi fitsara, saida cikinsu ya dauka dam sannan yajata zuwa bedroom acan suka baje kolin soyayyar da suke yiwa junansu kamar yadda suka saba,sai karfe 5 saura sannan yabar gidan bayan sunyi wanka sunyi salla, makarantar malam lawan yatafi akan hanyarsa ta zuwa makarantar ya hangi wasu motoci guda biyu alamun accident akayi gefe daya kuma mutane sun dan taru ga wata budurwa nan sai zuba tijara suke itada wani sunata fada,

Packing yayi agefen titi yafito ya isa wurin, ganin abinda ke faruwa yasashi tsoma baki ya sasanta ta hanyar cewa budurwar shi ya dauki nauyin gyara motar gobe ta kai masa gareji nan ya kwatanta mata garejin nasu daga haka case din ya mutu saurayin da sukayi karon tare yanufi motarsa yana cewa,

“Inama baki samu wanda zai gyara ba inyaso inga uban da zai gyara miki wannan akwalar motar taki….”

Ko tanka masa batayi ba ta shiga motarta tayi gaba abinta, shima Aliyu motarsa yanufa yashiga yawuce aransa yana jin cewa yayi abinda yadace domin sasanta tsakanin mutum biyu aikin alkhairi ne,

Saida teenah taga wucewar aliyu sannan tatsaya nan zarah tazo tashiga cikin motar suka wuce, kallon teenah zarah tayi,

“Gaskiya sai yanzu na tabbar da cewar tabbas zaki iya abinda kika fada kuma da alama zakiyi nasara domin naga gayen yanada saukin kai…”

Wata shu’umar dariya teenah tayi sannan tace,

“Wato da kin dauka da wasa nakeyi? Zan baki mamaki ai domin zanyi iya iyawata na ganin na dauke hankalinsa sannan zan hadashi da malamai su kame min shi tass sai yanda nayi dashi..”

Wata uwar shewa zarah tayi tabata hannu suka tafa. Aliyu kuwa zuciyarsa daya yayi rabiyar fadan nan batare da yasan abin nasu shirine ba kawai sunyi hakane domin su samu damar da teenah zatayi magana dashi, bayan yatashi daga islamiyya bai koma gidaba awurin malam yazauna har sukayi sallar isha sannan yatafi gida,

Irin kyakkyawar tarbar da halimanshi tayi masa abin ya kayatar dashi, saida suka kammala kallo suka kwanta sannan yake bata labarin nemar musu admission din da abba keyi a kasar Cyprus da China dan haka duk wacce suka samu can zasu tafi,wannan albishir ba karamin dadi yayiwa halima ba wannan dalilinne yasata bawa Aliyu tukwici mai tsoka wanda sakamakon hakan yasashi hanasu runtsawa dama kuma sun saba kwana suna ibada ta hanyar nafilfili to yau dinma hakance ta kasance basuyi bacci ba saida sukayi sallar asuba.

Washe gari agaba yasata sukaje wurin abba tare suka kara yimasa godiya, nan suka shiga part din Ummi da umma, sun tarar umma bata jin dadi tana kwance saboda mura dake damunta sai zazzabi,

Tunda suka fito halima ke son yiwa Aliyu gulma shiyasa suna rufe kofar falon umma ta rikoshi tana yimasa rada,

“Darling dina meka fuskanta da wannan rashin lafiyar ta umma?…”

“Ban fahimci komai ba, mekika gani ke?”

“Tabdijam…., gaskiya ka kara himma, tsoffi ma gashi suna neman zarceka a kwazo…”

Murmushi yayi sai lokacin ya fahimceta sarai, murmushi yayi aranshi yana cewa kenan nufinta ni ban dageba?,

Hannunta yakama suka nufi part dinsu saida suka shiga falo sannan yajata jikinsa,

“Wai kina nufin umma ciki gareta…?”

“Ehhh kai ba ka tsaya wasa ba”

Dariya yayi yai saman babbar kujera da ita,

“To tsaya inyi nasafe tunda dama yau da asubah baccinki kikayi”

“Da yamma fa?” Ta tambayeshi idonta cikin nashi,shima nashi idon cikin nata yabata amsa yana murmushi,

“Za akara wani, twice a day yanzu zamu rinka yi ko muma Allah zai tsaga da rabonmu mu samu baby… Ko? Idan kin yarda ma harda dare duk sai ayi”

Girgiza kai tayi,

“Nasafe da yamma yafi….”

“Ki karasa mana, fadi abinda zaki fada…..”

Rufe fuskarta tayi alamun kunya, murmushi yayi ya matseta ajikinsa sosai, take sakonninsa suka soma shigarta yadda ya kamata.

Ranar baije gareji ba sai karfe 1 domin duk ya cinye lokacinsa awurin halima suna manne da juna kamar wasu tif da taya. Lokacin da ya karasa garejin yasamu teenah tana jiransa domin tun karfe 11 tazo amma bata sameshi ba nan ta nemi wuri ta zauna tana jiransa,tana hangoshi lokacin da yayi packing ta glass din motarta, fitowa yayi daga motarshi yana sanye cikin sky blue din yadin kufta kansa da hula kai idanba ka saniba baka taba cewa Aliyu nada mata sannan gayunshi da kwalliyarsa bazai sa ka fahimci shi bakanike bane sam sai idan gani kayi da idonka, idon teenah tsaf akansa lokacin da yafito daga cikin motar yana rikeda waya a kunnensa suna hira da halima kamar ba yanzu suka rabuba dariya yake danyi sakamakon jin abinda tafada,

“Darling brother kasan wani abu…? Allah tunda nagama cin abincin nan nake jin tashin zuciya da jiri na daukana kai daga karshe ma sai da nayi amai sannan naji dadi, duk na amayar da abinda naci…” Tafada cikin narkakkiyar murya ta shagwaba, hakan da tafada ne yasashi yin dariya,

“To ko har na harbe ki ne?” Yafada cikin rada,

“Nima tunanin da nakeyi kenan…, amma har za agane haka da wuri?”

“Kedai kibari sai na dawo zan bincikaki sosai, amma yanzu yaya kike ji?”

“Babu komai sai ko dan ciwon kai”

“To me kike sha’awar ci inkawo miki?”

“Dabino… Mai laushin nan irin na saudiyya”

“An gama sweety…” Yafada cikin sigar so,

Yakai mintuna uku yana wayar kafin yayi sallama da ita kamar zasu lashe juna dan so, wayar ya mayar cikin aljihu, yana kokarin barin wajen daya daga cikin yaransa yazo yana yimasa sannu da zuwa sannan yake sanar masa da teenah wacce ke jiransa, saida yayi dagaske sannan yatuna ta, motarta ya nufa tana hangoshi ta zaro wani shu’umin kwalli na mallaka wanda tazo dashi musamman domin shi, kuma malaminta ya sanar da ita muddin suka hada ido da Aliyu sannan yazama mutum nafarko wanda ya kalli idanuwanta da zarar tasaka kwallin tofa sai yanda tayi dashi duk umarnin da ta bashi dole yabi, tana gama saka kwallin ta ji yana kwankwasa mata glass ahankali tabude kofar ta ziro kafarta ta fito……

 

*_Ummi A’isha_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

*DAN ASALI….!*🤴🏻

 

_*NA*_
*_UMMI A’ISHA_*

 

_Ina mutukar ji daku domin ku din na dabanne kamar yadda comments dinku yake na musamman, Anty maijidda musa, Aminiya Maryam Qaumi,yar dakina Miss Xoxo & Mamie Hamma kawata, fatana Allah yabar zumunci._

 

*50*

 

***Ganin tana kokarin fitowa yasa Aliyu dauke kansa daga kallonta kunsan mutumin naku dama bai fiya son kallon kowacce mace ba asalima shi maganar ma da mata ba sonta yakeyi ba saboda tsabar ustazanci,

Duk yadda teenah taso su hada ido abin ya faskara domin ya dauke kanshi yakaishi wani waje daban harta gama bayaninta na cewa itace wacce sukayi alkawari dashi jiya, bai tanka ba yayi gaba abinshi tana nan tsaye yaje wurin yaransa suka gama tattaunawa sannan suka dawo wurin motarta shida daya daga cikin yaran nashi, abin ba karamin bawa teenah tsoro yayi ba domin sam Aliyu yaki kallonta duk kuwa da irin kisisinar da take tayi gamida shagwaba tareda narkar da murya, saida aka kusa gama gyaran sannan yayiwa yaransa sallama yatafi yana jaddada musu karsu karbi kudin gyaran teenah domin kyauta yayi mata, abin yayi mutukar kular da ita domin sai take ganin kamar ba wancan Aliyun da tagani a restaurant bane wanda yaketa raha da barkwanci tareda murmushi da wata ba, wannan sam ya banbanta da wancan domin wannan miskili ne ma’abocin girman kai kuma mai jiji da kai gamida dagawa wanda ko kallo mutane basu isheshi ba.

Nan take teenah ta kuduri niyyar sauya dabara domin ta rantse sai taga karshen wannan girman kan na Aliyu kuma saita kure ajinsa.

Shi kuwa Aliyu zuciyarshi daya ba wai da niyyar wulakanci ko girman kai yayiwa teenah abinda yayi mata ba, shi dabi’arshi ce haka sam baya son mu’amala da mata idan bawai zama dole yayi ba shiyasa abaya halima tasha wahala kafin ya karbi soyayyarta yafara sonta, kai tsaye kasuwa yawuce yaje ya tarkatowa halima dabino harda irin na cikin kwali dinnan wanda ake kawowa daga saudiyya daga nan gida yawuce duk da lokacin anata kiraye kirayen sallar la’asar.

Da sallamarsa ya shiga cikin falon, kwance ya ganta kan rug tana lullube da hijabinta,

Matsawa yayi kusa da ita ya zauna yana taba fuskarta da bayan hannunshi,

“Sorry my Dear…., ya jikin? Babynmu na wahalar dake ko?”

Sai da tayi dariya sakamakon ganin yanda ya langabar da kai, ledar dabinon ya dauka ya ajiye mata agabanta,

“To tashi ga dabinon kici…”

Tashi zaune tayi tana yamutsa fuska yaciro mata ta zabi wanda take son ci yabata, tunda taci wannan dabinon taji dadin jikinta sosai nan yaci gaba da lallabata da riritata saboda daga shi har ita sun dauka cikinne yasamu shiyasa yaketa tsokanarta da,

“Kinata yiwa umma tsiya ai gashi nan kema kin kamu…, Bari ma intashi inje infadawa ummi kin samu ciki daga can sai inwuce in fadawa umma daga nan sai Abba…”

Saurin rikoshi tayi ta kankameshi,

“Dan Allah Darling Brother ka rufa min asiri, kabarshi idan yafito sa gani…”

Dariya yayi yana shafa sumarshi, harararshi tayi,

“Dole mana kayi dariya tunda kasan ba ajikinka za aganshi ba”

Kallonta yayi yasake dariyar tareda zuba mata idanuwanshi,

“Amma dai kowa yasan ai ni nayi shi ko? Kinga ko ba aganshi ajikina ba an san nine na sakashi acan din kuma an san hanyar da nabi wurin ajiyeshi”

“Nidai to wallahi ban yarda ka fada ba”

“To naji, nifa dama wasa nake yimiki, tayaya zan iya fadawa su ummi wannan maganar? Ke inada kunya fa”

Dariya tayi ta kalleshi,

“Ahakan?”

“Ehh mana kema wani lokacin ai inajin kunyarki”

Baya ta juya masa ta dauke kai tana fadin,

“Banga alama ba,da kanaji da baka gayyaceni da ranar Allah tsaka ba”

“Au hakama zakice,ke baki san sirrin yi awannan lokacin ba ko? Tab gaskiya kinada saura yarinyar nan”

Rabuwa tayi dashi ta saka dabinonta agaba tanata ci, gaba daya yanzu riritata yakeyi samada irin wacce yake yi mata ada ita kuwa inbanda shagwaba babu abinda take zuba masa, shikuwa yayita biyeta suna shiriricewa, kwana biyu ta dauka tana fama da rashin dandano abakinta da dan ciwon kai sannan ta warware.

Yau tunda yadawo daga sallar asubah ya tattara kayanta masu datti ya nufi baya yasoma wankewa, har 8 bai gama ba,

Halima ce ta biyoshi tana sanye da rigar bacci mai santsi pink colour ko cireta batayi ba,zama tayi akusa dashi tana yamutsa fuska ga kuma murmushi gefe daya kwance saman fuskar tata,

“Sannu da aiki Darling yaya Ali”

Murmushi yayi ya kalleta,

“Kin tashi lafiya Maman baby?”

Jin abinda yace yasata fara dariya, ganin irin dariyar da takeyi yasashi dakatawa daga wankin da yakeyi ya zuba mata ido,

“Kasan me? Ba dazu da katasheni da asubah kaga najima cikin toilet ba har ka fita masallaci ban fito ba….?”

Kai ya gyada mata bayan ya daga girarshi daya yana kallonta,

“Umhummm sai meya faru?”

“To wallahi infada maka lokacin period dina yazo….”

Tun kafin ta rufe bakinta ya shiga watsa mata ruwan dake gabanshi,

“Da alama ma ke farin ciki kike yi ko?…. Kika rinka wahalar dani ashe duk babu wani ciki”

Kare ruwan tashiga yi tana dariya, daga karshe tazo ta rike hannayenshi, duka hannuwansu ke cikin ruwan kumfar dake cikin bucket din da yake wankin, hannunta yake ta laluba da nashi acikin ruwan kumfar suna faman dariya, sun jima ahaka kafin ya saki hannuwanta yana kallonta,

“Kinga kina neman ki shagaltar dani inkasa karasa wankin nan, tashi ki tafi daki ki kwanta maza….”

Makale kafada tayi,

“Zan tayaka ne fa”

“Nagode kitafi kawai nace”

Saida taga dagaske zai jikata jagab da ruwan kumfa sannan ta gudu bayan ta sumbaci kumatunshi daya, da murmushi yabita yaci gaba da abinda yakeyi shi dai aduniya yana mutukar kaunar halima bashida wani buri wanda ya wuce ya mayar da ita sarauniyar matan duniya gaba daya shiyasa babu abinda bazai iya yimata ba mutukar abin zai sata cikin farin ciki.

Kafin yagama wankin har tayi wanka taci kwalliya ta shiga kitchen ba wani abu mai wahala ta hada musu ba ,ruwan zafi ne kawai sai kunu da ta dama musu sai wainar kwai data soya,

Tana kokarin fitowa daga kitchen din taganshi shima ya gama yashigo daga shi sai three quarter, kayan hannunta ya karba ya tayata fitar dasu sai zuba kamshi take, bakinta ya kalla tanata faman taunar cingom domin a yan kwanakin nan tunda tasoma fama da rashin dandano abakinta ta sarkafi cingum koda yaushe shine abakinta, kallonta yayi bayan ya dire kayan hannunsa akan table,

“Ohh sweety ban san ranar da zan rabaki da cin abinnan ba”

Dariya tayi taci gaba da abinda takeyi hakan yabashi damar rungumeta ta baya tareda kai bakinsa saitin kunnenta,

“Buda mata yakeyi fa shiyasa kikaga tun kafin muyi aure ina hanaki cinsa dayawa, ban son kibude…..”

Rufe fuskarta tayi tana dariya,

“Kai yaya Ali…. Ta yaya zakace cingum yana buda mace”

“Au baki yarda ba? Allah cinsa dayawa yana sawa jijiyar da ta tafi zuwa wurin ta saki….”

Jin abinda yace yasa ta jijjiga kanta,

“Insha Allah zan rage to….”

“Atohh nidai ina ruwana, karma ki rage nikam ina jin kin sauya wata zanje in auro sabuwa fil….”

Tunda taji yafadi haka ta sauya fuska tafara neman tureshi daga jikinta, sosai ta bashi mamaki saboda fitittikewar da tayi tana yimasa rigima kamar yaune zai iyo auren, dakyar yasamu ya rarrasheta, aranar ya sake tabbatar da irin zafin kishinta akansa, wani irin kishi gareta musamman akan Aliyu,

Saida yasha rarrashi sannan ta sauko har ta rakashi bathroom tayi masa wanka, ita da kanta ta shirya shi ta saka masa wani material na maza kalar ruwan zuma,saida ta fesheshi da turare sannan suka fita falo sai faman nanuka take ajikinsa tana shakar kamshinsa, zaunarta yayi saman cinyarshi yana murmushi,

“Yau da kwadayi kika tashi gashi kuma kina off…”

Sake rukunkumeshi tayi tana murmushin itama,

“Kabari kawai Darling…., but u should try ur best”

Dariya yayi ya hada musu tea sannan ya zuba musu kunun suka fara karyawa,

Saida suka bawa junansu madarar soyayya sannan suka fita tare, a part din umma yabarta wanda itama umman ta dan samu ta warware domin murar ta saketa, daga can ficewa yayi yatafi gareji.

Teenah ganin bata samu kan Aliyu ba yasata sake bin wata hanyar nan malaminta yafara yimata aiki na musamman akan Aliyu domin babban burinta shine ta raba tsakaninsu da halima ita kuma yasota kamar hauka sannan yakasance mai yimata biyayya akan dukkan abinda ta sakashi, acikin kowanne dare Aliyu baya shagala yayita bacci yafi maida hankalinsa wurin ibada shida halima dan ko bata salla sai ya tasheta shiyasa itama yanzu har ta saba da tsayuwar daren wannan dalilinne yasa asirin teenah baiyi tasiri sosai akansu ba duk da kwana biyu sun fara fuskantar yar matsala wacce basu san takamaimai ko daga ina takeba. Sannan teenah tafara kaiwa Aliyu ziyara zuwa garejinsu sai dai bata samun fuska awurinshi shiyasa abun yataru yayi mata yawa.

Cikin wannan yanayi Ummi da Abba suka tafi sauke farali wato aikin hajji aka bar iya umma domin ita dama taje basau daya ba, tunda ummi taje kasa mai tsarki Aliyu take yiwa addu’a shida halima domin ya fada mata damuwarsa, cikin hukuncin ubangiji suka dawo normal kamar yadda suke abaya kai harma zaman yaso yafi nada armashi,

Kusan kullum sai sunyi waya dasu ummin, gulmar umma kuwa kullum sai sunyi ita dashi akan zarginsu na wai Umman nada ciki, wani lokacin yakan ja hancinta yace wai saura su.

Ana saura kwana biyu salla Sabira tazo suka tafi gyaran gashi da gidan kunshi saboda layi basu samu dawowa ba sai bayan sallar magrib, sosai kuwa aka yarfo mata kunshi irin wanda gogan nata ke ra’ayi shiyasa kafin yashigo tayi wanka ta sha gayu cikin wani purple din material mai santsi da stones ajiki,bata daura dan kwali ba illah daure gashin nata kawai da tayi da purple din ribbom.

Tana kitchen tana soya plantain domin shi take sha’awar ci sai gashi yashigo, tunda sukayi arba ya rikice ya nemi susucewa domin tayi masifar yimasa kyau.

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*DAN ASALI….!*🤴🏻

 

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

_SAFNANCY kina ina? This page is yours my friend…!_

 

*51*

 

***Agefenta ya tsaya ya jingina da bango yana kallonta domin sosai kayan dake jikinta suka mata masifar kyau bayan bayyanar da surarta da sukayi afili, gani yayi gaba daya ta sauya mishi ta canja,

“Baby kinyi masifar kyau yau…”

Cikeda yauki ta juyo ta kada masa idanu,

“Nagode my D, barka da dawowa”

Matsawa yayi kusa da ita ya kama hannuwanta gaba daya ya rike cikin nasa yana yaba kunshin da akayi mata, ganin yanda yadage yaketa kissing din hannayen nata yasata dan tureshi baya,

“Yaya Ali plantain dina zai kone….”

Cikata yayi yana dariya,

“Gaskiya gobe bazan zauna agidan nan ba”

Tana kokarin tsame plantain din ta amsa masa da,

“Meyasa?”

“To ina son inyi azumin arfa amma nasan mutukar muna tare sunan azumin karyayye…”

Dariya tayi ta kashe gas sannan ta dauki plantain din ta kama hannunshi suka fice tana cewa,

“Lallai ashe gobe ni kadai zaka bari agidan”

Afalo suka zauna suna cin plantain din, zuba mata ido yayi sakamakon yanda yaga tana cin plantain din hannu baka hannu kwarya,cikeda tsokana yace,

“My one and only kodai mun samu babyn ne?”

Dariya tayi ta nunashi da yatsa,

“Kaganka ko…., tun yaushe nake fada maka”

Kwantar da kanshi yayi jikinta yana murmushi,

“Zamu gani ai tunda yau saura 13 days time din period dinki yayi…, idan ma yaudarata kike i shall know”

Dariya taci gaba dayi masa tana kallonshi, kwanciya yayi akan cinyarta ya dora kansa tafara shafa sumar kanshi.

Washe gari kamar yadda ya fada mata da sassafe yabar gidan, ita dinma da rana tayi sai suka fita supermarket itada Sabira nan suka bata lokaci sosai domin duk abubuwan da zatayi amfani dasu na yin abincin salla saida ta sissiyo shiyasa bata dawo gidan da wuri ba, koda ta dawo atsaitsaye ta shiga part din umma tafito, tana zuwa nasu sashen kuma wanka kawai tayi ta shiga kitchen domin hadawa Aliyu kayan shan ruwa tanayi tana tunaninsa domin yau sau daya sukayi waya dashi throughout alhalin kuma bahaka suka saba ba domin arana sukanyi waya fiyeda sau biyar.

Saida ta kammala yimasa kayan shan ruwan sannan tasamu nutsuwa, zuzzubawa umma duk abubuwan da ta dafa tayi da baba tabawa takawo mata kosai wanda Umman tayi sai tabata tatafi dashi,

Wanka ta sake fesawa sannan ta feshe ko ina da air freshener bayan ta kunna dan turaren wuta wanda kamshinsa ke tashi ahankali, saida ta tanadarwa da Aliyu ruwan wanka sannan tafito tana ta kamshin turaren Arabian perfumes, wando three quarter ne ajikinta pink colour da rigarsa itama pink mai siririn hannu marar kauri, gashinta ta daure sannan ta yanko wani gaba,

Sai da akayi sallar magrib sannan yashigo, ganinta yasashi jin duk kishin ruwan da yakeji ya kore, take ya rungumeta yayi sama da ita yana juyi atsakiyar falon dakyar ta samu ya sauketa tanata shagwabar daga zuwanshi ko ruwa baisha ba zai dauketa yana bawa kansa wahala,

Wanka yafara yi yayi brush sannan yazo ya zauna zaman cin abinci, tea yafara sha sannan yaci Irish potatoes plan din da ta hada masa wanda yaji dafaffen kwai da sauran kayan lambu wanda idanma ba sani kayiba baka taba cewa ka taba saninsu.

Saida ya koshi yadda ya kamata sannan yakoma gareta yana lullumshe mata idanuwanshi nan ta tarbeshi cikin farin ciki da kauna wannan shine daya daga cikin abubuwan dake kara dasa masa kaunarta acikin zuciyarshi domin halimanshi daban ce acikin mata sannan sam baya taba kosawa da ita kamar yadda itama bata kosawa dashi.

Bayan yadawo daga sallar ishah shine ya tayata ta yanyanka vegetables din da zatayi amfani dasu gobe wurin dafa fried rice dinta shiyasa basu sukayi bacci ba sai 1 domin harda su soye soyen kaji da sauransu sukayi,

Washe gari kuwa wato ranar salla tunda tayi sallar asubah bata koma bacci ba kitchen ta shiga, chicken pepe tayi sannan ta dora fried rice with liver and vegetables sos babu bata lokaci gidan ya kaure da kamshi shiyasa Aliyu da yashigo direct kitchen din yabita domin tun daga compound din gidan yake jiyo kamshi, tare suka karasa girkin ta soya shinkafarta tayi kyau shar da ita,

Kafin ta kammala tuni har Aliyu yayi wanka yashirya domin lokacin tafiya masallaci yayi shiyasa ita agurguje tayi wanka ta fito domin tagama dukkan ayyukanta cow slow ne kadai bata hadaba tabarshi sai ta dawo,

Wata tsadaddiyar atamfa dark purple tasaka dinkin riga da skirt powder kadai ta shafa sai kwalli data saka a idonta daga nan ta dauki hijab da abin salla tafita, a balcony ta iskeshi yana daura agogon hannunshi nan ta karba ta daura masa ya rufe kofar falo suka tafi, sosai taga farar shaddar da yasaka yau ta karbeshi.

Bayan sun dawo daga masallaci part din umma suka shiga sukayi mata barka da salla duk da sun isketa a kitchen ita da masu aikinta sunata dafe dafe da soye soyen su waina, funkaso, sinasir da sauransu.

Saida halima ta dibar wa Aliyu abubuwan da Umman ta daddafa sannan suka wuce part dinsu, suna zuwa ta gabatar masa da abincin da tayi da wanda umma tayi sannan ta kwashi duk abubuwan da ta dafa taje ta kaiwa umma da wanda za amikawa makota, daga can wurin Aliyu ta koma,saida suka gama cin abincin sannan ya kalleta kallo irin na kauna,

“Madam happy sallah…. Allah ya maimaita mana”

“Amin sweet Darling….”

“To ina barka da salla dina?” Yafada yana janta jikinsa,

“To sakeni indauko maka…”

Saida yayi kissing din kumatunta sannan ya saketa ta mike, kayan da suka ci abinci ta kwashe sannan tawuce bedroom dinsu, ta kai akalla mintuna shida kafin tafito, har ta zauna bai kalleta ba kasancewar hankalinsa na kan tv inda yake kallon news,

“Darling brother gashi amma fa babu yawa…”

Sai lokacin ya juya ya kalleta, agogo ne na silver mai bala’in kyau kirar kamfanin Gucci, sai turare oud mai kyau irin wanda yake shafawa sai ko greeting cards guda biyu masu dauke da kalaman soyayya da kuma taya murnar barka da salla,

Sosai abin ya burgeshi har takaishi ga rungumeta da sumbatarta babu adadi,

“Thank u sweetheart…., tunda hakane kema bari inkawo miki naki….”

Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta tana jin farin ciki yana ratsata har cikin ranta ashe dai maza na jin dadi idan matansu sukayi surprising dinsu ta hanyar yi musu kyauta komai kankantarta bawai sai babba ta dunbin kudi ba kuma dama haka ma’aurata ya kamata su kasance atsakaninsu su dan rinka bawa juna kyaututtuka musamman lokaci irin wannan na bukukuwan salla ko lokacin zagayowar ranar haihuwa da dai sauransu bawai sai saurayi da budurwa ne kadai zasu rinka yiwa juna kyauta ba,

Tana tsaka da tunanin lamarin taji zamanshi akusa da ita,

“Rufe idonki….”

Murmushi tayi tabi umarninsa ta hanyar rufe idanuwan nata nan taji ya cire sarkar wuyanta da dan kunne ya saka mata wasu harda abin hannu da zube,

“To ga barka da sallarki nan Allah ya maimaita mana”

Rungumeshi tayi tun kafin taga kalar sarkar, godiya tayi masa sosai sannan ta mike da azamarta tawuce bedroom,

Sarkace golden colour mai masifar kyau wacce akayi ta da heart design duk da ba ta gold bace amma tayi mata kyau domin sai walwali take yi wanda kai ka rantse cewar sarkar daham ce, ganin yanda sarkar ta haskata abin ya burgeta, komawa falo tayi wurinsa nan ta sameshi yana waya dasu ummi suna yiwa juna barka da salla, ajikinsa ta zauna yabata wayar itama ta gaisa dasu tayi musu barka da salla,rike hannunshi tayi wanda yaketa wasa da sarkar tata, bayan sunyi sallama ne ya mike tsaye da ita yace zai fita zaije ya yanka shanun layyar abba da ragon su na layya suma daga can kuma zaije wurin malam lawan yayi masa barka da salla, abincin da tayi ta zuzzuba masa a flask manya domin yakaiwa su Malam,

Saida ta rakashi sannan ta koma ciki, bayan fitarsa babu jimawa itama tafita ta kulle sashenta tawuce na umma, acan Sabira kawarta ta isketa babu dadewa itama khairiyya tazo nan suka tisata gaba da tsokanar fari da kyawun da tayi, duk abubuwan da tayi na abincin salla saida ta zubo musu nan aka fara shigo da kayan cikin shanun da aka yanka da raguna, diba tayi ta ajiye agefe domin tana son tayiwa Aliyu farfesu dashi, khairiyya sai tsiya take yi mata saboda yanda taga suna yi awaya itada Aliyu tamkar zasu hadiye juna,

Suna falon umma zaune suna ta shan cafta ita kuma Umman na can wurin masu aiki tana basu umarnin yanda zasu sarrafa naman kafin tawuce takoma ciki saboda kamshin man dake neman hawar mata kai, bedroom dinta tawuce ta kwanta ai kuwa halima aka samu nayi domin kasa hakuri tayi saida ta fadawa Aliyu ta hanyar tura masa da sakon text massage.

Har isha tana part din umma itada khairiyya bayan Sabira ta tafi, ba ita tabar sashen umma ba saida Aliyu yadawo suka tafi tare bayan ta daukar masa farfesun da tayi masa da soyayyen hanji sai wata shagwaba take yimasa tana fadin,

“Darling yaufa tun safe rabona dakai…, ni dai Allah kar ka sake yimin irin wannan”

Shiru yayi bai rarrasheta ba saboda khairiyya dake wurin domin shi akwai kunya sam baida wannan rawar kan saida suka shiga part dinsu sannan ya fara rarrashinta yana cemata, “In banda abinki baby ai sai iya nida ke sannan zan lallabaki amma ba akan idon mutane ba….”.

Washe gari yawo ya kwashesu itada khairiyya sune park daban daban harda na yara agaban khairiyya sai rikeshi take tana cemasa suma idan sun haihu nan zasu rinka kawo yaransu wasa,sai dai yayi murmushi kawai baya magana saboda yana jin dan nauyin khairiyyan, sai yamma suka baro wuraren shakatawar da bude ido yakaisu gidan malam suka yimusu barka da salla, sabbin kudi ya samata ajakarta yan dari bibbiyu domin ta bawa yara barka da salla ai kuwa haka tayita rabonsu kowanne yaro sai ta danka masa harma da manyan, daga can gidansu Sabira suka je canma haka ta bawa kannen Sabira da yaran makotansu daga nan suka koma gida,kai tsaye part din umma taje ta debo masa dambun nama da tuwon shinkafar da akayi ta kai masa,haka suka rinka shagalinsu har bikin salla yakar.

Ana saura yan kwanaki su Ummi sudawo admission dinsu na kasar Cyprus yafito shi zai karanci mechanic Engineering yayinda ita kuma zata karanci international relation,ba karamin murna halima tayi ba shi kansa Aliyu shima cikin farin cikin yake domin yajima yana burin yayi masters amma abun bai yuyuba ashe yana gaba.

Cike da farin ciki yaje gareji bayan yaje wurin malam ya sanar masa, zuwansa yayi daidai da zuwan teenah wacce yau ta dauri aniyar fada masa sirrin dake cikin zuciyarta game dashi saboda tabi duk hanyar da zata bi amma samunsa ya gagareta……

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert, & perfect writers)_

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

*52*

***Sosai yabata lokacin sa domin su tattauna sai dai har tayi bayaninta tagama bai kalleta ba har saida ta furta cewar tana sonshi lokacinne ya bude idanuwansa sosai ya kalleta, sam baiji ta kwanta masa arai ba domin duba daya zaka yi mata ka gane tsantsar barikancin dake tattare da ita gamida rashin tarbiya,

Amfani yayi da kaifin tunaninsa wurin tausasa harshensa yabata hakuri bayan ya sanar da ita cewa yanada mata kuma bawai ya jima da auren bane sannan ko kadan baida ra’ayin kara aure nan kusa, duk da cewa bata ji dadin abinda ya fito daga bakinsa ba sannan batayi farin ciki ba amma tayi kokari wurin bayyanar masa da rashin damuwarta sai dai fa ita kadai tabarwa zuciyarta abinda zata aiwatar domin bata jin cewar zata iya hakura dashi, sallama sukayi tatafi shikuma ya kama aikinsa gadan gadan.

Bayan salla da yan satittika su ummi suka dawo, dukkansu sukaje suka taro su harda umma bayan sun shirya musu tarba ta musamman,fadin irin farin ciki da murnar da iyalan ke ciki abun sai wanda yagani, ranar har 11 dare halima da Aliyu na sashen ummi kamar can zasu kwana saida taga 12 ta kusa sannan ta koresu tace bacci zatayi saboda gajiya,

Tun daga ranar can suke tarewa su sakata agaba ita kuwa halima duk abinda ta dafa saita kaiwa ummin, ranar da aka kunce tsaraba kuwa ta halima tafi ta kowa yawa domin ummi komai tagani irin mai ban sha’awar nan na yanmata sai ta siyowa halima, su warwaro ne,sarka, dogayen riguna, mayafai da sauransu, Aliyu har fushi yafara saboda tsarabar halima tafi tashi yawa amma acikin ransa dadi yakeji Ummi na tayashi son abinda yake tsananin so.

Lokaci nata tafiya al’amura na rayuwa na sauyawa, su Aliyu shirye shiryen tafiya karatu kasar Cyprus ya kankama wanda idan suka tafi sai sunyi shekaru kusan biyu basu zo ba, sunje sun yiwa yan uwa da abokan arziki sallama domin har kauyensu na babban shuri sukaje sannan sunje gidajensu malam lawan,Sabira da sauran abokan arziki duk sunyi musu ban kwana.

Suna kwance kan gado tana manne dashi kamar yadda tasaba ana gobe zasu tafi, shafa kanta yayi sannan cikin tsokana yace,

“Ni wannan watan baki samu cikin bane? Naga duk wata kike yin ciki amma kuma sai innemishi inrasa, ko sai munje Cyprus zakiyi acan?”

Dariya tayi ta rufe ido,

“Kasan Allah Darling brother bafa laifina bane…”

“To ai nima ba wani abu naceba kawai tambaya nayi…”

“Uhm….uhm….ban yarda ba”

“Kinga nidai bacci nakeji saida safe….” Yafada yana lumshe idanuwanshi, kin barinshi yayi baccin tayi ta shiga neman magana tun yana kyaleta har ya soma kulata yana tanka mata.

Washe gari ranar laraba da misalin karfe 6 na yamma jirginsu ya daga zuwa kasar Cyprus bayan sun samu rakiyar su Abba.

Awani babban hotel suka sauka acikin babban birnin kasar nan suka kwana washe gari Aliyu yafita dan samar musu wurin zama kuma dama abba ya hadashi da wani mutum mai suna Alh Bukar wanda shine ambassador na can kasar wannan dalilinne yasa basu wani sha wahala ba wurin samun inda zasu zauna ba,

Acikin rukunin wasu kananun gidaje dake makwabtaka da makarantarsu anan suka kama gida, gidan upstair ne su suna sama wata mata da mijinta akasa, dan madaidaicin falo ne aciki sai bedroom da bathroom sai kitchen da store,

Ba kadan ba rayuwar kasar tayi musu dadi domin basuda damuwar komai illa ta karatunsu wanda shi kuma asaukake ake koyar dasu,tun zuwan halima nafarko makarantar ta samu kawaye yan Nigeria guda biyu, shi kam Aliyu kasancewar ba mai yawan magana bane tsakaninsa da kowa gaisuwa ce kawai,

Abangaren kulawar da yake bawa halima kuwa tun agida Nigeria kusan kulawar yanzu tafi ta da domin yanzu bashida lokacin kowa sai nata da na karatunsa domin yasan tahowa wata kasa da ita da yayi wata babbar amana ce ya dauko wannan dalilinne yasa yake kaffa kaffa da ita ko kuda bai son ya taba masa ita, basu fi wata biyar da zuwa ba halima tafara kewar gida Nigeria duk da cewa kullum ka’ida ce sai sunyi waya dasu umma wani sa’ilin ma har video call suke yi awayar Abba. Lokacin da umma ta haihu kuwa kuka tasa Aliyu agaba tanayi ita fa dole gida zata koma,

Lallabata da rarrashinta Aliyu yashiga yi cikin kankanin lokaci ta watsar da tunanin gidan ta saki jikinta suka cigaba da rayuwarsu mai dadi cikin wannan kasa, sai dai fa kullum suna makale da yan gida awaya kullum suna jin labarin abinda ke tafiya agida,ranar suna aka sakawa babyn umar faruk, duk wash abubuwa wadanda aka gudanar saida aka tura musu ta waya suka gani, hatta kawarta Sabira da anty khairiyya kusan kullum sai sunyi waya kuma sai sunyi chat.

Zamansu a wannan kasa ba karamin gogewa da wayewa ya kara musu ba tareda sanin inda duniya ta sa gaba idan kaga Aliyu sai ka kara kallonsa shiyasa uwar rigimar tasa take kishi haka kawai wani lokacin zata hanashi fita domin hatta fararen fata burgesu yake haka kawai zasu zo su rinka mika masa hannu wai su gaisa amma abun burgewa bai taba gaisawa da kowacce mace ba imma bakar fata ko farar fata sannan aduk lokacin da yaga wani abun da ya burgeshi yakan dawo gida ne ya umarci matarsa da tayi masa irin abinda yagani, ita kanta Sadiya tasan tayi dacen miji domin da wanine duk da yana da mata tofa da dama ta samu ta sheke aya amma sam Aliyu shi ba haka yakeba sau da yawa yakan cemata aduk kasar da mutum ya tsinci kansa to ya dauka cewa shi jakada ne na addininsa da kuma gidansu dan haka duk abinda ya aikata to kamar yana nuna tarbiyar gidansu da addininsu ne.

Akwana atashi sai da su halima suka shekara biyu cif akasar Cyprus sannan suka nufo gida niki niki da kayan tsaraba,

Misalin karfe 5 na yammacin ranar talata suka sauka, Abbane yaje taraso sai ko driver, gani sukayi abba ya canja musu kamar yadda suma suka canja masa sosai, nan suka rankaya sai gida sun samu gidan shima ya sauya ansake gyareshi yasha sabon fenti kal kal dashi, yan sannu da zuwa kuwa harda khairiyya da Sabira duk suna gidan sannan ga faruk shima yayi wayo sosai sai surutu yake yi nan aka shiga rungume juna dan farin ciki,

Basu suka sami zarafin shiga part dinsu ba sai 11 na dare, komai na furnitures din da suka bari ansauya anzuba sabbi pink & silver, kan gado kawai ta fada tana hamma, Aliyu dake tsaye yana kokarin cire kayan jikinsa domin yin wanka ya kalleta,

“Ke ba zakiyi wankan bane?”

Lumshe ido tayi,

“Darling brother bacci wallahi….”

Murmushi yayi,

“To shikenan yi baccin maza….”

Wanka ya shiga koda ya fito har tayi bacci, rigar bacci ya saka mata bayan ya shirya nan yayi musu addu’a ya shafa musu.

Washe gari kuwa yan sannu da zuwa kamar me harda su Malam lawan da iyalansa da yan gidansu Sabira banda yan garejinsu Aliyu, tun safe suke baki har dare saida 9 tayi sannan kafa ta dauke. Kusan kullum yanzu hakane sai baki sun zo musu da haka har sukayi sati guda da dawowa akullum kuwa halima na makale da faruk bacci ke rabasu,

Neman shawarar halima Aliyu yayi gameda kudinsa kimanin miliyan 6 da Abba yabashi wai kudin filinsa ne wanda ya mallaka da dadewa shine gwamnati ta siye zata yi hanya ta wurin,

Hannunsa halima ta kama ta rike cikin nata tana kallonsa,

“Darling kai da ara’ayinka me kake ganin zakayi dashi?”

“Kingane ne one love nida inada niyyar siyan fili sai ingina islamiyya ko masallaci sannan ina son yin rijiya mutune su rinka amfani da ita…”

Kada kai tayi tana murmushi,

“Kayi tunani mai kyau sweetheart…, idan hakane mai zai hana kaje ka gyara makarantar islamiyyarku ta Malam sai ka yi mata sabbin tsare tsare tunda kaga tanada girma inyaso anan din zaka samu wurin da zaka gina masallaci kuma zaka samu wurin yin rijiyoyi…..”

Ido ya zuba mata yana kallonta har saida ta tsargu da ko shawarar tata bata samu karbuwa ba, hannunta taji ya matse cikin nasa tareda kaiwa labbanta kiss,

“Shiyasa kullum nake godewa Allah da yabani mace tagari…, hakika mutane na kuskure da suke kin shawartar matansu suke ganin kamar tunanin mata baya zuwa ko ina, my one & only naji shawararki kuma zanyi amfani da ita, barima dai ki gani…”

Mikewa yayi domin fita, zaije yaga ta inda ya kamata ya fara, saida ta rakashi sannan ta koma ciki.

Cikin kankanin lokaci aka fara aikin kamar yadda Aliyu ya tsara sai dai duk da taimakawar da Abba keyi ginin tafiyar wahainiya yake yi domin andeboshi da fadi, daga karshe ma tsohon gidansu ya sayar batare da sanin abba ba yasake narka kudin wurin ginin wanda ahalin yanzu ansamu nasarar dora bene na biyu,

Watansu daya da dawowa aka saka ranar khairiyya zata auri wani kwararren likita wanda yakasance lecturer dinsu lokacin da tana school of nursing, murnar da halima tayi ba yar kadan bace saboda suna nan za ayi bikin dayake ba wani watanni mai yawa aka sakaba.

Tuntubar Aliyu Abba yayi kan irin aikin da yake ganin zaiyi amma Aliyu yace sai yayi shawara, halima yasamu da maganar saboda baya ra’ayin yin aikin gwamnati yafi so ya tsaya da kafarsa nan tabashi shawara da to ya sanarwa Abba ya gina masa kamfani wanda zai rinka kawo kayayyakin gyaran mota kowanne iri daga kasar waje sannan agefe kuma atanadi wurin gyaran motoci mai kyau wanda shi da yaransa zasu zauna hakan zai bashi damar taimaka musu tunda albashi zai rinka biyansu, sosai yaji dadin shawararta kuma yayi na’am da ita nan da nan yaje ya sanarwa da Abba, murmushi Abba yayi yace to shikenan tunda haka suka yanke shida kanwar tashi domin yasan da ita yayi shawara.

Ya rage saura sati uku su tafi suka shiga hidimar bikin khairiyya, zirga zirga halima ta shiga yi daga gidansu zuwa inda ake gudanar da bikin domin so take ta ramawa khairiyya wahalar da tayi mata ta bikinta ranar kamu tun sassafe tabar gida domin ranar akayi musu kunshi da gyaran gashi harda dilke ta biya itama akayi mata, sam ranar basuyi waya da Aliyu ba domin wayar ma tana cikin motarta ta mutu babu charge, saida aka ci kamu aka watse misalin 8 nadare sannan suka rankaya gidan da amare suke zama, yunwace tsagwaronta acikinta saboda basu wani ci abinci ba ita kanta amaryar maltina da madara kadai tasha wunin ranar, zama tayi aka kawo musu abinci shinkafa da miya har ta saka hannu ta tsame hannuta ta kalli khairiyya,

“Umma khairiyya nabar mijina agida yau wuni guda ban sakashi a idona ba banji muryarsa ba, bazan iya cin abincin nan ba bari kawai inje gida…”

Shewa kawayen khairiyya suka sa ciki kuwa harda Sabira, mikewa halima tayi tana saba mayafinta akafada tana fadin

“Ba zaku gane bane….”

Duk yadda khairiyya tayi mata nacin ta zauna taci abincin nan ki tayi sai a flask aka zuba mata, ko umma bata nemaba bare ummi ita ta mijinta take, Sabira ma tana son tazauna taci abinci amma fur halima taki tace inbata tasoba sai dai ta nemi mai ajiyeta gida ita tafiya zatayi, dolenta ta tashi suka tafi, wani uban gudu take shararawa wanda ya tsorata Sabira lokaci kankani ta ajiye Sabira ta nufi agida tana yiwa sabiran dariya,

Komai nata ahannu ta rirriko kama tun daga kan high hill din da ta saka da gyalenta, handbag dinta sai food flask din abincin da ta taho dashi, gidan didim yake da duhu dan ba atada Generator ba, kofar falonsu abude tajita hakan yabata damar turawa ta shiga nan dinma duhunne kamar babu mutum aciki, muryar Aliyu ta jiyo a dayan falon yana fadin,

“Waye…?”

“Darling nice, nadawo…” Ta amsa masa tana zube kayanta saman kujera, kuma sai taji gaba daya tausayinshi ya kamata,

“Sannu da zuwa, anje ansha biki amma manta dani ko…”

“Ni na isa inmanta da rabin raina…, kayi hakuri, amma meyasa ka zauna aduhu haka?”

Tana tafiya zuwa wurinshi take amsa masa,

“To ai dama kece fitilar dake haske gidan tunda kin dawo nasan yanzun nan gidan zai gauraye da haske….”

Acikin duhun ta laluboshi yana kwance kan doguwar kujera ta zauna saman kafafuwanshi hannunshi ta lalubo bata kai ga yin magana ba haske ya gauraye falon, tashi zaune yayi ya zuba mata ido bayan ya kama yan yatsunta……

_Manya manyan masoyan Haly ~Aly ga taku gaisuwar ta musamman, Ummu hilal, Hussaina Dan larabawa, Ramlat Muhd, Anty Baraka, Hussaenert,Indon Birni,Khadija mai kano, da duk wanda ban ambata ba….!_

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…!*🤴🏻

 

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

_Pherty Xarah where are u? Here is ur page yanmatan…..!_

*53*

 

***Nata idanuwan ta zuba cikin nashi itama,

“Ya Ali yana jin jikinka haka? Baka da lafiya ne….?” Tafada arude, murmushi yayi kafin ya rike hannunta wanda take taba jikinsa dashi,

“Wani dan zazzabi nake ji but da sauki….” Yafada yana kwantar da kanshi akafadarta,

“To kasha magani ne?”

Jijjiga mata kai yayi alamun a’a,

“Bari to kaci abincin sai kasha maganin…”

Tashi tayi tafita, abincin da ta zo dashi ta kawo musu sannan taje ta dauko paracetamol da table water ta dawo duk jikinta babu kwari, tare suka ci abincin suka gama yasha sannan taje ta hada musu ruwan wanka mai dumi, shirya shi tayi cikin kayan bacci lemon green colour,basuyi wata doguwar hira ba domin dukkansu agajiye suke.

Washe gari babu inda halima taje duk da cewar ranar ne mothers day sannan kuma angwaye sun dan shirya musu wata yar liyafa, kusan agida ta wuni saboda Aliyu yatashi da zazzabi da dan ciwo ciwon kai, suna zaune afalo yana kwance akan cinyarta yana wasa da hannayenta wadanda suka sha kunshi yajuya ya kalleta,

“Ki tashi ki shirya kije wurin bikin naku mana….”

Kansa ta soma shafawa bayan ta kalleshi,

“Haba Darling brother…., dan dai nice uwar rashin hankali baka da lafiya sai inkama hanya intafi biki?”

Murmushi yayi yatashi zaune yana kallonta,

“To ai naji sauki, zazzabin fa yasauka and kuma nima fita nake son yi fa…., zanje wurin malam”

Sai lokacin taji hankalinta ya kwanta da fitar nan ta tashi tayi maza maza ta shirya ta hade cikin wani tsadadden leshinta coffee colour har ta fito yana falo yana jiranta saboda tare zasu fita zata saukeshi gidan malam ita kuma saita wuce,

“Zo nan one and only…” Yace da ita yana kamo hannunta, saman cinyarshi ya zaunar da ita,

“Jiya ban hanaki saka turare ba idan zaki fita? Ko so kike inki bari aje bikin ne?”

Kafada ta makale cikin shagwaba tace,

“Kayi hakuri bazan sake ba please….”

Saida ya dan bata tukwicin yaba kwalliyarta da yayi sannan suka fita, part din Abba suka fara zuwa suka gaisa sannan suka bar gidan, akofar gidan malam lawan ta saukeshi sannan tawuce bayan tasha ruwan kisses ba adadi.

Ranar da wuri tadawo gida saboda miji babu lafiya agidan bikin ma motsi kadan ta kirashi taji yajikinsa hatta su khairiyyan ta ishesu da jimamin mijinta ba lafiya abu kadan zatace ana jimawa zata tafi mijinta baida lafiya dakyar dai da sudin goshi takai magriba ana yin salla kuwa takoma gida dan can ma tabar Sabira yau, ita kam komawa gida tayi taje taci gaba da zaman jinya, ohh Aliyu yaga tattali da kulawa awurin mutuniyar tasa badan babu dadi jinya ba shikam da sai yayi fatan Allah ya maimaita masa saboda irin kula dashin da takeyi duk bayan minti daya sai ance masa,

“Sannu Darling brother…, me kake so?”

Cinyarta kuwa itace ta zame masa pillow, duk da zazzabin nasa yajima da sauka amma bata daina tattalinsa ba, washe gari garau yatashi abinsa yayi wanka yafita gareji bayan ya karya, rakashi balcony tayi tana fada masa da daddare fa tare zasuje dinner, murmushi kawai yayi yatafi baice komai ba domin shi bai cika ra’ayin wadannan abubuwan ba, duk da haka saida tasashi ya shirya suka tafi wata dark maroon din shadda yasaka ita kuma ta saka net din da suka dinka a matsayin anko wato pink da blue din head.

Basu suka dawo gidaba sai 11 saura nadare. Tsabar ta gaji ba kadanba sai shine ya rage mata kayan jikinta sannan suka kwanta,

Ahaka aka karasa bikin aka kai amarya gidanta dake alkalai quarters, ana kammala biki suka soma shirye shiryen tafiya domin zasu fara biyawa kasa mai tsarki inda zasu sauke farali sannan sai suwuce kasar Cyprus.

Tunda yarage saura sati 1 su tafi suka fara zuwa sallama wurin yan uwa da abokan arziki domin har kauyensu sukaje, ana saura kwana uku su tafi kuwa gidan amarya khairiyya taje ta wuni sai magrib yaje ya daukota,

Kamar tafiyarsu tafarko wannan karon ma jirgin karfe 6 suka bi sai kasa mai tsarki, ibada sosai suka gudanar a wannan kasa bayan sun gama aikin hajji kuma suka bude babin soyayya kullum sai sun fita yawo sunje sunga wurare addu’ar kowannensu acikin ranshi shine Allah yabasu baby mai albarka tunda har yanzu sunji shiru.

Daga kasar saudiyya kasar Cyprus suka wuce inda sukaje suka cigaba da gudanar da rayuwarsu cikin kulawa da juna, gefe daya kuma agida Nigeria ana cigaba da ginin da Aliyu yabari wato ginin islamiyya da masallaci wanda yanzu haka ginin har yakusa kammaluwa.

Sun shiga wata na 10 da tafiya akayi bikin Sabira inda ta auri wani babban dan jarida, halima harda kuka wai anyi biki bata nan danma khairiyya na ta turo mata videos din duk event din da akayi, ganin yanda Sabira ta hade itada angonta ranar dinner abin yaburgeta,tana kallo tana, unzunbura baki Aliyu dake kwance kusa da ita yayi matashi da kafafuwanta yana karatu ya daga kai ya kalleta,

“Dear ya akayi…?”

Sake zunburo baki tayi kafin ta mika masa wayar yagani,

“Nima fa kaga irin yanda naso muyi amma kaki, ai wallahi ko….”

“Ai wallahi me? Kibari idan kika haihu zamuyi”

Harara ta dalla masa,

“Bayan ko cikin ma banida shi, kana ganin umma khairiyya har cikinta ya tsufa ta kusa haihuwa ta barmu….”

Hawaye yagani sharr suna sauka daga idonta hakan ya tayar masa da hankali mutuka ba shiri yatashi zaune yajata jikinsa kamar wacce take jira nan ta fashe masa da kuka sosai domin harga Allah rashin haihuwar nan da batayi da wuriba abun yafara damunta domin yanzu shekarunsu uku da aure,

Rungumeta yayi ajikinsa tsam tsam yana rarrashinta,

“Haba halima ni banga abin kuka ananba…, haihuwa fa ta Allah ce kuma zai bamu, da yawa Allah yakan hanamu abu a lokacin da muka so domin yasan abin ba alkhairi bane agaremu, sannan yakan bamu kyautarsa a lokacin da bamu tsammata ba saboda yasan a lokacinne abin zai zama alkhairi agaremu, dan haka ki share hawayenki karki kara yin kuka akan wannan maganar, wallahi daga ni har ke lafiyarmu lau kuma zamu haihu da yardar Allah…., kin sanfa ‘yaya da dukiya fitina ne haka Allah yace, kawai kedai kiyi mana addu’a Allah yabamu masu albarka.”

Sosai maganganunshi suka sanyaya mata zuciyarta, gaskiya tayi sa’ar miji domin Aliyu ya iya rarrashinta duk abinda ke damunta yasan hanyar da zaibi wurin mantar da ita damuwarta yabata farin ciki, yanzun ma hakance ta faru saida ya rarrasheta sosai sannan yafara tsokanarta ganin ta saki fuska har tana dariya,

“May be ma ayanzu mu samu da zaki yarda….”

Murmushi tayi ta rufe fuskarta sannan ta tashi zata gudu nan yabita suka soma tsere daga falo zuwa bedroom har yasamu nasarar kamata daga karshe. Dan ya mantar da ita damuwarta yau har yawo suka fita wurare daban daban na shakatawa babu laifi ta saki jikinta sosai kusanma ta manta da maganar, sunsha hotuna ba kadanba awuraren da suka ziyarta sai dare sannan suka koma gida.

Tun daga ranar bata kara daga hankalinta kan maganar ba domin Aliyu yabi duk wata hanya wacce yakamata yabi dan hanata wannan damuwar,cikin hukuncin ubangiji sai waya sukaji anyi musu wai umma ta sake haihuwar baby boy, halima kamar zatayi tsuntsuwa ta dawo gida takeji har ranar suna kullum cikin vedio call suke dasu Abba suna jin labarin babyn har ranar suna ta zagayo yaro yaci suna Abubakar sadiq nanfa su halima aka samu abunyi domin kullum sai an turo musu hotunan sadiq da na Faruk,ahaka ahaka dai suka yita tafiya har lokacin gama karatunsu yazo,cikin karshen wannan shekara suka kammala karatunsu suka dawo gida cikeda dunbin nasarori masu yawa domin Aliyu saida yakarbi award guda biyar banda gwarzon shekara da ya zama.

Nan gida Nigeria kuwa shirye shiryen tarbarsu iyayensu keta faman yi saboda dokin dawowarsu Abba saida yasake shirya musu part dinsu sosai aka gyarashi ta hanyar sake fenti da furnitures,

Ranar juma’a da daddare suka sauka da misalin 12 na dare duk da cewa basu iso da wuriba amma gidan babu wanda yayi bacci kowa yana zaman jiransu dan hatta su faruk ma idonsu biyu, nan su abba sukaje suka daukosu, koda suka karaso gida babin hira suke kokarin budewa da iyayen nasu amma Abba ya hana yace suje su kwanta su huta sai gobe ayi hirar,

Halima kamar tayi me dan dadi duk da taji dadin kasar Cyprus amma harga Allah kasarta ta haihuwa ta fiye mata shiyasa yau take jinta cikin walwala kasancewar ta dawo gaba daya. Shi kansa Aliyun shima hakan take domin ya fahimci duk wanda yabar gida to gida ya barshi, bacci suka kwanta sukayi mai cikeda nutsuwa cikin kwanciyar hankali.

 

_*Ummi Shatu*_👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI….*!🤴🏻

 

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

_Ahar kullum ina alfahari daku domin ku din na musamman ne agareni, Hauwa Jidda Aliyu & Khaleesat Haydar,na baku wannan shafin kyauta domin jin dadinku._

 

*54*

 

***Washe gari basu tashi da wuriba domin suna tare da gajiya,

Sai misalin karfe 11 sannan suka farka sakamakon bugon kofar da sukaji wanda abisa dukkan alamu su sadiq ne domin ga muryoyinsu nan suna zuba surutu,

“Ki tashi ga kannanki can sunzo dubaki….”

Zumbura baki tayi tana muttsuka idonta,

“Kannanmu dai ai harda kai”

“Ni ai basu fi yarana ba, dan wallahi da na samu haihuwa da wuri babu abinda zai hana in haifi kamarsu”

Dundu tayi masa abaya sannan ta mike tafita taje ta bude musu kofar, ashe tare da baba tabawa suke breakfast suka kawo musu nan suka gaisa baba tabawa tajuya bayan ta bata abincin sukuma su Faruk suka biyota ciki,

Kallo ta kunna musu ta kamo musu channen din cartoon sannan ta wuce bedroom, tarar da Aliyu tayi yana wanka,dakin ta dan kintsa kafin ya fito sannan itama ta shiga.

Sai wurin karfe 2 sannan suka shiga wurinsu umma can kuma suka tare har dare,

Washe gari Abba ya hada musu walima ta musamman inda yan uwa da abokan arziki suka zo tayasu murna ciki kuwa harda khairiyya da Sabira, kowaccensu dauke da yaronta, ita khairiyya yaronta Affan ita kuma Sabira sunan danta Aiman,

Gajiya lis yauma suka yi shiyasa saida suka yi sati guda suna hutawa inbanda bacci babu abinda suke yi, saida suka nutsu sannan suka fiddo tsaraba nan kuma sukayi ta rabo kowa da nashi su faruk kuwa uban kayan wasa halima ta jibgo musu, banda kayan sawa masu tsada.

Dawowarsu da sati biyu akayi walimar bude islamiyyar Aliyu wadda yagina ashe tuni abba yayi duk abinda ya kamata shiyasa ginin ya kammalu batare da sanin Aliyu ba, sosai makarantar ta kayatu domin idan baka saniba zaka dauka makarantar kudi ce irin mai tsadar nan domin anyita fiyeda hasashen mai hasashe saboda hatta harabar makarantar ma interlock ne babu kasa, bene hawa uku mai dauke da wadatattun ajujuwa banda staff room da office din malam lawan daban haka shima Aliyu ga office dinshi nan daban sannan ga babban masallaci aciki wanda za arinka kamsussalawati harda sallar juma’a, ga bandakuna guda goma na mata da na maza sannan ga famfunan ruwa reras wanda ko mutanen unguwa na iya zuwa su diba,sosai makarantar tayi kyau kuma ta tsaru daga waje anrubuta *ABUL ASLAM ISLAMIC FOUNDATION*,wannan shine sunan da Aliyu ya zabawa makarantar ahalin yanzu domin yanada burin sakawa yaronsa wanda yake saka ran halimatu zata haifa masa sunan,

Ba Aliyu kadai ba hatta halima abin ya burgeta da iyayensu, anyi biki sosai sannan taro ya watse inda aka fara karatu gadan gadan.

Tun dawowarsu babu inda Aliyu ke zuwa kullum yana gida tare da halima idanma ta matsa akan ya fita sai yace shifa amarci yake yi, kullum suna tare idan kaga yafita to yammace tayi zaije islamiyya domin har gobe yana koyarwa a makarantar.

Saida sukayi watanni uku sannan Abba yakirashi yayi masa albishir na kamfanin da zai bude masa acikin birnin abuja sannan kuma can zasu koma shida halima sai dai su rinka zuwar musu dan hutu da dafarko halima abin baiyi mata dadiba amma jin Aliyu yace tazauna shi sai yatafi shi kadai yasata hakura suka shiga shirye shiryen tafiya, gaba daya gidan suka tafi ranar domin yin launching din bude kamfanin,

A unguwar maitama gidan da zasu zauna yake wanda mallakin Abba ne gidan kuma sosai gidan ya hadu wanda ke dauke da part uku,

Ba karamin burge halima unguwar tayi ba domin area din da suke unguwace tsararriya wacce bata da hayaniya sannan babu yawan jama’a awurin.

Washe gari akayi launching din bude kamfanin wato *Abul Aslam motors* domin kamfanin motoci ne Abba ya bude masa sannan gefe daya ga kayan gyaran mota nan sababbi fil sai dan garejin gyaran mota agefe, sosai kamfanin yayi kyau sannan ya burge kowa, satinsu umma daya agidan suka tafi suka barsu, washe gari shima yafara fita office wanda tuni su dan larai sunzo sun fara gudanar da aikinsu babu kama hannun yaro. Ranar wuni sukayi suna waya da mutuniyarsa halima domin bata saba yafita yabarta ba irin haka domin kullum suna tare,

Kafin yadawo ta shirya masa lafiyayyar white rice da kidney sos sannan ga lemon ayaba mai mutukar sanyi wanda yasha zallar madara,ita kanta tayi zallar kyau cikin jar rigar da ta saka da bakin jeans, yau da yake yan shagwabar na kusa shagwaba tayita yimasa akan wai ya wuni da yunwa ita kar ya sake yi mata haka shi dai babu bakin magana afuwa kawai ya shiga nema wannan dalilinne yasa yasoma zuwa cin abinci da rana tunda bawai nisa sosai company din nashi yayi da gida ba.

Satinsu uku agarin abuja ranar juma’a suka tafi Zaria weekend, duk da Monday zasu koma amma hakan bai hanata ziyartar su khairiyya ba wacce ta sameta tanata fama da laulayi dariya halima tayi tafara tsokanarta,

“Umma khairiyya kunika agidan likita?….”

“Ke waya fada miki cikine? Keda mijinki yafi nawa naci ma bakiyi kunika ba sai ni”

Dariya halima tayi ta nemi wurin zama tana kallonta,

“Wlhi mijina baida wani naci nima, barina yake in shana…”

“Zakiga shanawa duk ranar da kika ganki a labour room hajiya…”

Dariya sukayi gaba dayansu,anan gidan khairiyya ta wuni itada su Faruk da sadiq sai la’asar sannan suka koma gida.

Haka suke ziyartar Zaria duk bayan sati biyu sai sunzo weekend tun Abba na fada yana cewa su rinka zamansu har ya hakura domin abin har ya zame musu kamar doka indai basu zo wannan week dinba to wani week din zaka gansu,

Kamar koda yaushe wannan week dinma tunda yadawo daga sallar juma’a suka taho domin dama tagama shirinta shi kadai take jira, acikin sababbin motocin da aka shigo masa dasu ne ya dauko daya kirar Mercedes new series 2018,dark ash shine colour dinta shi kuwa gogan farar shadda kal yasaka dinkin tazarce,yana driving suna yar hira da madam din tashi duk da ya kula sai wani ciccije lebe take,

“Ko abokin fadan nawa ne ke shirin zuwa?” Yafada cikin tsokana,juya kanta tayi sannan ta amsa masa,

“Haka nake tunani but nazaci date din baiyi ba ai…”

Dariya yayi yaci gaba da driving dinshi,

“To ai date din naki ne zai canja,shiyasa time din da kika cemin kirjinki duk nayi miki ciwo nace miki ba wani abu bane, yau zaki ganshi ko gobe so sai ki tanadi tsumman kunzugunki akusa….” Ya karashe maganar cikin tsokana yana dariya,

Duka takai mishi akafada tana fadin,

“Da rigarka zanyi kunzugun ai”

Wata dariyar ya kuma yi harda dukan sitiyari,

“Ai nasan tunda kike baki taba kunzugu ba amma yau dai zaki fara, ki dauki dan kwalinki daya ki yaga…”

“Idan nacire sai inbar maka ka wanke ko”

Dariya yayi ya kalleta,

“Kin san Allah idan har zaki saka tsumman nikuma nayi alkawarin zan wanke”

“Ehh tonidai babu wani tsumma da zan saka ehe,kawai ni in zaka siya min pad ka siya min”

“Zan siya miki maida wukar, yi dan murmushi mana gimbiya…”

Saida ya sakata dariya sannan yabarta ta soma dan gyangyadi. Kasancewar basu isa da wuri ba yasa bai fita ko ina ba ranar sai washe gari da yamma,

Milk colour din boyel yasaka yafita zuwa islamiyya, lokacin da ya shiga yayi packing yafito zai wuce zuwa office din malam lawan saida gabansa yayi wata mummunar faduwa domin wata ya hango sak mai kamada muslima a wani aji tana koyarwa, bai sake kallon wurinba yawuce,daf da office din malam din sukayi kicibus wanda shima yafito da niyyar zuwa wani wuri nan suka tsaya kan barandar suna gaisawa yana tambayar malam yanda al’amura suke gudana,

Suna tsaye da Malam awurin ya hangota tafito duk da baya son kallonta amma saida ya kalleta domin yana son ya tabbatar ko ita dince ko kuwa?, tabbas wannan muslima ce to amma meya dawo da ita makarantar nan itada ba agarin takeba? Wannan tambayar itace keta faman kai kawo a kwakwalwarsa wanda yakasa hakuri har saida ya tambayi Malam cewar me yadawo da muslima? Nan Malam ya amsa masa da,

“Ai kasan mijin nata ne ya rasu wanda har ta kammala takaba sannan shikuma mahaifin nata na kwance agida bashida lafiya ko fita baya yi to shine rannan taje har gidana ta sameni tace idan da hali in taimaka mata zata dawo taci gaba da koyarwa domin su dan samu damar rage wasu matsalolin shine nace to ta dawo dama ai munada bukatar malamai mata….”

Jijjiga kai Aliyu yayi yana kallon Malam baice komai ba, sallama sukayi da Malam domin fita zaiyi shikuma yaci gaba da zagayawa yana duddubawa musamman ma yanda malaman ke koyar da dalibai, ana daf da za atashi ya nufi motarsa dan tafiya,yana kokarin bude motar yaji zazzakar muryarta wacce bazai taba mancewa da itaba tana yi masa sallama,

“Assalamu alaikum ya sayyadi…”

Har cikin ransa yaji sunan domin wannan sunan shine wanda take kiransa dashi shekarun baya da suka wuce lokacin da suke tsaka da zuba soyayya, amsa mata yayi ya juya ya kalleta, ba kadan ba ta rame banda baki da tayi sannan uwa uba alamun rashin maraya da ya dabaibayeta domin kallo daya zaka yi mata ka fahimci a karkara ta rayu tsawon lokaci,

“Muslima….” Yafada bayan ya amsa mata sallamar,

“Na’am ya sayyadi ya iyali, ya kuma kwana biyu”

“Lafiya lau, ya hakuri kuma? Ashe mijinki ne ya rasu?”

“Ehh wallahi, hakuri mun goda Allah”

“To Allah ya jikansa ya gafarta masa”

“Amin amin, Allah ya bada lada”

Daga haka sukayi sallama yashiga motarsa ya wuce tana tsaye tana kallonsa gani tayi ya kara kyau da gogewa yazama cikakken namiji dan gayu na kece raini irin wanda kowacce mace zata yi burin kasantuwarshi a matsayin mallakinta.

Bayan yafito daga sallar magrib gidansu muslima yawuce wanda yana nan kamar yadda yake abaya babu abinda yakaru saiko lalacewa da gidan yakara yi,

Yaro yasamu ya tura yayi masa sallama da ita yana tsaye jikin motarsa dukkan hannuwanshi cikin aljihunsa tafito sanye da jan hijabi tana rikeda wani karamin yaro dan kimanin shekara shida wanda abisa dukkan alamu danta ne,

Sosai tayi murna da ganin Aliyu wanda hakan yakasa boyuwa akan fuskarta, sallama tayi masa ya amsa yana kamo hannun yaron nata,

“Ya sunanka? Uhm dan saurayi?”

Shiru yaron yayi sai itace ta amsa masa,

“Sunanshi sadauki”

Murmushi Aliyu yayi,

“Wannan ai ba suna bane, kodai bakya fada ne saboda kina kunyar dan fari?”

Murmushin itama tayi nan yasake tambayar yaron sunanshi,

“Ya sunanka abokina, zan baka sweet fa ko bazaka sha alawa ba?”

“Zan sha…” Yaron ya amsa,

“To ya sunanka?”

“Aliyu haydar”

“Sunanka Aliyu? Ashe ma takwara nane”

Mikewa tsaye yayi daga sunkuyon da yayi yana kallon yaron, motarshi ya bude ya ciro chocolate guda hudu irin wanda halima ke ajiyewa, hannu yasa a aljihunsa ya ciro dubu biyar ya damkawa yaron nan yawuce gida da gudu yana murna, juyawa ga muslima yayi yana kallonta yayinda ita kuma ta sunkuyar da kanta kasa……

 

 

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI….*🤴🏻

 

_*NA*_

_*UMMI A’ISHA*_

 

*55*

 

_Kina raina ahar kullum kanwata abar alfaharina, ASMY B ALIYU shafin yau nakine ke kadai, gaba dai gaba dai Antyn laila khaleepha..!_

***Sun kai kimanin minti biyar ahaka babu wanda yayi magana acikinsu kowanne yana sakar zuci,

Aliyu ne ya katse shirun nasu ta hanyar yin yar gyaran murya sannan yakira sunanta cikin tausassiyar muryarsa,

“Muslima…..”

Sai lokacin ta dago ta kalleshi tareda amsawa,

“Ammmm……….nace wanne irin ciwo ke damun baba ne?”

“Wallahi irin wannan shanyewar rabin jikince……”

“To amma kun kaishi asibiti?”

Girgiza kai tayi alamun a’a,

“To saboda me? Bakya ganin yin hakan kamar sakaci ne ga lafiyarsa?”

“Ba sakaci bane wallahi, kasan sha’ani ne na kudi…..”

“Hakane kuma, to yanzu ina so zan dubashi idan har hakan zata yuyu”

“Babu damuwa…., ina zuwa to”

Juyawa tayi tashiga gida ya rakata da idanuwanshi masu yalwa, babu jimawa ta fito tace yashigo, tana gaba yana binta abaya har cikin gidan, wani daki suka shiga wanda Baban nata ke ciki yana kwance akan tabarma gefe kuma Babar su muslima ce zaune fuskarta dauke da alhini kamar zata fashe da kuka ga kuma tarin nadama da borin kunyar abinda tayiwa Aliyu abaya,

Cike da tausayawa Aliyu ya gaishesu yayi musu jaje tareda ta’aziyar mutuwar mijin muslima daga nan yatashi yafita, bin bayanshi muslima tayi zuwa kofar gidan, tsayawa yayi yana kallonta batare da yace komai ba zuwa can ya nisa yabude motarsa yashiga kafafuwansa awaje tsawon minti biyu sannan yafito,

“Muslima ga wannan kudin gobe dan Allah ku kai baba asibiti….., Allah yabashi lafiya”

Karbar kudin tayi jikinta asanyaye saboda ganin yawansu ita kanta bazata iya kiyasta adadinsu ba,

“Mun gode madalla ya sayyadi, Allah yasaka da alkhairi yakara budi, Allah ya albarkaceka kaida iyalinka….”

Katseta yayi ta hanyar cewa,

“Banfa baki kudin nan dan kiyita yimin godiya ba tunda ba ke nayiwa ba, baba nayiwa…..”

“To shikenan Baba yagode sosai….”

“To ni zan tafi, sai wani lokacin kuma”

“To mun gode agaida gida….”

Har yajuya ta dakatar dashi, karasawa wurinshi tayi nan daddadan kamshinsa na turaren oud ya ziyarceta,

“Am….am ya sayyadi…. Dama cewa zanyi ya yara kuma?…. Nasan yanzu kila sun kai biyar…. Ko?”

Murmushi yayi yabude kofar motarshi sannan ya kalleta,

“Matana biyu yayana goma….”

Saida gabanta ya fadi wanda har ya karanci hakan akan fuskarta,

“Ahhhhhh….. Wai dagaske?”

“Ehh mana”

“To Allah ya rayasu, agaishesu”

“Amin, zasu ji”

Daga haka yashiga mota yayi mata key yatafi muslima na tsaye tana kallonsa tana daga masa hannu.

Kamar halima jira take yabar wurin muslima domin ko layin bai bariba yaji tana kiransa, daukar wayar yayi yana murmushi,

“Darling brother kana inane?”

“Meya faru?”

“To ai najika shiru ne, ina ka tsaya?”

“Na danje wani wuri ne? Kina nemana ne?”

“Sosai kuwa, dan Allah ka taho min da kilishi”

Murmushi yayi ya rage murya,

“Bakon namu yazo ne?”

“Tun yaushe, ai kana fita”

“Tom gani nan zuwa, i love you”

Saida ta amsa masa kafin ta katse wayar,

Sakon da tayi masa ya biya ya siya sannan yawuce gida, akwance ya sameta afalo tana kallo, hularshi ya cire yaje kamar zai zauna a kan cikinta babu shiri ta runtse idanuwanta ta saki yar kara,

“Yaya Ali ka zauna akaina ai mutuwa zanyi yau….”

Zama yayi agefenta yana dariya,

“A’a one love wallahi banda sharri, keda kika fini nauyi ma ban mutuba duk zaman da kikeyi akaina sai kece zaki mutu dan yau daya na zauna akan ruwan cikinki?”

“Nidai rufa min asiri Darling brother…., ina kilishin?”

Nuna mata yayi da yatsanshi yana jingina ajikinta,

“Kai ai ba sai na sanmaka ba ko?”

“To idan baki baniba me zaki bani?”

“Me kake so?”

“Ai bazan samuba, amma kinfi kowa sanin abinda nake so ai….”

“Kai wai baka gajiya ne?”

“Waya fada miki ana gajiya da aikin lada…”

Zura kafafunta tayi zata sauka, kallonshi tayi sannan tace,

“Nikam kodai kaima harijin ne?” Daga haka ta gudu duk da cewar bata jin karfin jikinta, murmushin shima yayi,

“Dama kin daina gudu dan ba yanzu zan baki amsa ba sai ranar da wannan abun yadaina zuwa….”

Tana dariya ta dawo dauke da plate da fork ta zauna kasa jikin kafarshi,

“Yawwa ka tuna min ma white musk dina fa yakare….”

“Baki fada min da wuriba ai da na taho miki da shi sai dai gobe kuma….”

“Sai kuma…..” Shiru tayi bata karasa ba,

“Sai kuma me? Ana so za a zautar dani ko? Kibarni haka ma basai kina bani wahala ba dan Allah”

Kafarshi ta buge tana harararshi,

“Nifa magarya zance shine ka wani fassarani…”

Saukowa kasa yayi kusa da ita ya dauki balangu yakai bakinsa domin shi kilishin ba sosai ya dameshi ba, ido ya tsura mata bayan ya dage gira,

“Na zaci wannan abun ai na rannan kike magana wanda na siyo miki shine da zance bakiga wahalar da kika baniba ranar….”

Harararsa tayi tana dariya,

“Nabaka wahala kodai ka bani? Ai wallahi gara first night sau dubu da wannan ranar….”

Ajiye fork din yayi dan dariya, gyara zamansa yayi yana kallonta,

“Ke wallahi nima fa na wahala fada miki ne kawai banyi ba,amma harda hawayena”

Me halima zatayi inba dariya ba, harda kwanciya dan dariya, shima dariyar yake yi daga zaune yana kallonta,

“Ranar ai naga masifa baby wallahi kamar an watsa mana gam”

Dariya halima tasake kwantawa tanayi tana kallonsa,

“Danma dai kaine ka kawo abun da hannunka, wai a ina ka samo?”

“Bazan fada ba, bayan dariya kike yimin”

Tashi tayi tana kunshe dariyarta taci gaba da cin kilinshinta, dariya taji shima yafara yimata yana kallonta,

“Kin san me na tuna? Ke kuma ranar harda rarrafe”

Gimtse fuska tayi,

“Kaga Allah bana so…”

Balangunsa yaci gaba da ci yana dariya kasa kasa,

“Wallahi Darling brother kabari tom….”

Dagowa yayi ya kalleta sannan ya sunkuyar da kansa yana cigaba da dariya,

“Dama dariyar babu dadine amma ni kika rinka yimin?”

Shiru tayi batace komai ba saiko hararar da take aika masa, ajiye fork din hannunsa yayi yana duba agogonshi,

“Ni kinga ma lokacin salla yayi kina nema kisani in makara….”

“Nima wanka zanje inyi domin ina jin kamar nayi staining ma”

Kallonta yayi yana cewa,

“Tashi mugani…..”

Mikewa tayi tana juyo masa bayanta ai kuwa gaba daya yellow din rigar dake jikinta ta baci harda short din trouser din da ta saka,

“Wai wai….. Kin sha wani abun zaki da bana nan ko?”

“Ni babu abinda nasha fa”

“Babu wani nan”

Kayan da sukayi amfani dasu ta sunkuya zata kwashe nan ya hanata,

“Kije kawai barshi zan dauke…”

Wucewa ciki tayi shi kuma ya kwashe kayan zuwa kitchen, saida ya dauko duster da omo ya goge wurin da ta zauna domin wurin ya dan baci sannan yashiga ciki domin yin alwala, tana cikin bathroom din yashiga ta tube duk kayan da ta saka ta tukunkune su abisa dukkan alamu yarsu zatayi domin yasan halinta da tsantsami musamman ma jinin menses,

Kwashe kayan yayi har pant din da ta cire ya jefa cikin bucket ya zuba ruwa aciki yabarsu, ita kam cikin bathtub ta shige tasoma wankanta,

Kau da kanshi yayi lokacin da yafara alwala,

“Ki daina kallona karki karya min alwala…”

Dariya tayi ta watsa masa ruwan kumfa bai rama ba yabude kofa yafita yana cemata,

“Bari naje salla kinga ma na kusa makara…”.

Kafin yadawo tayi shirinta tsaf cikin maroon din night gown mai masifar kyau da daukar hankali duk da ba wata kwalliya sosai tayi ba domin dan light makeup kadai tayi,

Tana kan kujera afalo tana game a laptop dinshi sai gashi ya shigo, saida yasa key ya kulle kofar sannan ya karaso ciki, akusa da ita ya zauna yana kallon game din da takeyi na super Mario,

Wayar shi ya zaro a aljihu bayan tayi masa sannu da zuwa,

Kowa da abinda yakeyi sunayi suna dan taba hira har hankalinsu ya karkata ga wani Nigerian film da aka saka atashar African magic wanda wasu yanmata keta masifa da fada akan wani saurayi,

Hakura da game din halima tayi suka raja’a wurin kallon,

“Gaskiya yaya Ali wallahi bakwa kyautawa kuyita hada mata fada…”

Dariya yayi ya kamo yan yatsunta cikin nashi,

“Menene abin fada anan?”

Kanshi gaba daya ta koma ta zauna tana jan gemunsa,

“Au kai baka gani ba? Tab”

Sinsina wuyanta ya shiga yi yana jan hancinta,

“To ke duk ranar da na kara aure kenan ya za ayi?”

Dagowa tayi ta kalleshi take idanuwanta suka kada sukayi ja,

“Darling brother kishiya fa,ai ni duk ranar da ka kara aure to mutuwa zanyi ranar……..”

Baiyi mamaki sosaiba jin abinda tafada domin kishinta yawuce gaban haka,

“Kai…, to shikenan ya isa, mubar maganar ma kawai”

Kwantar da kanta tayi akan kirjinsa tana jin zuciyarta na yi mata wani irin zafi, lura da yayi cewar yanayinta ya sauya yasashi fara neman fada nan kuwa suka fara da haka har ta saki jiki ta dawo normal. Koda lokacin baccinsu yayi bai kwanta ba saida yawanke kayanta na dazu wadanda ya jika, bayan yagama wankewa ne yayi wanka yazo ya kwanta abayanta yayi matashi da gadon bayanta wanda take kwance tana game da wayarshi.

Har suk koma abuja bai sake ganin muslima ba itama musliman haka, saida sukayi sati biyu sannan suka zo weekend amma wannan karon tun ranar alhamis suka shigo Zaria,washe gari bayan sallar juma’a yaje gidansu muslima, yauma yaro ya tura yayi masa sallama da ita, kamar dama shi take jira sai gata ta fito cikin kwalliya nan suka gaisa ya tambayi jikin baba tace masa ai jiki yayi sauki dan har an sallamo shi daga asibiti ma,

Saida ta shiga gidan tafito sannan tace yakarasa domin yana son zai duba jikin baban, asoron gidan suka tsaya sai kallonshi take kasa kasa farin tissue ne ajikinsa da farar hula mai ratsin baki, hatta takalminsa fari ne half cover, banda kamshinsa da ya mamaye harabar wurin, wayarshi taga ya zaro a aljihu sai kuma taga yayi musrmushi domin halima ce ta turo masa da massage din happy friday daga karshe kuma tace idan yadawo gida zata bashi goron barka da juma’a tarufe text din da kalmar i love u, saida ya maida mata da reply sannan ya mayar da wayar aljihu, muslima ce ta mika masa wayarta kirar tecno mai madannai tana murmushi,

“Yawwa kafin inmanta saka min number dinka, rannan wallahi saida ka tafi sannan natuna gashi bayan katafi inata son inji muryarka….”

Karbar wayar yayi wacce duk ta koke tagama shan wahalar duniya dan hatta madannan ma sun goggoge ba aganesu, saida yajuya wayar a hannunsa sannan yasoma laluben nambobin yana sakawa kalmarta ta karshe tanata juyawa acikin kwakwalwarsa,”gashi bayan ka tafi inata so inji muryarka….”

Da haka suka shiga gidan, ayanda yaga jikin mahaifin nata tabbas kam yasamu sauki akan yanda ya ganshi wancan lokacin, ita dai mahaifiyar muslima kunya bata barta ta hada ido da Aliyu ba, kama hannun haydar yayi dan muslima ya dorashi akan cinyarshi aranshi yana jin da tunifa yaron nan nashi ne shida muslima kila ma harda kannenshi amma Allah bai nufa ba, muryar Baban muslima ce ta katse masa tunaninsa,

“Wato Aliyu gara da Allah ya kawoka domin kazo akan gaba,kazo a lokacin da nake nemanka, nagode sosai da alkhairin da kayi mana,

Sannan Aliyu ina mai farin cikin sanar dakai cewa yanzu ashirye nake tsaf dan ganin na daura maka aure da muslima domin abaya ma nayi burin hakan Allah ne bai kulla ba, amma ayanzu ko yau kake ra’ayi za adaura muku aure da ita, nabaka ita halak malak ko na mutu ban yarda muslima ta auri wani miji ba sai kai….”.

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…*🤴🏻

 

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

*56*

 

_Dan asali fans kuna ina? Gaskiya ban san haka kuke da mutukar yawa ba,yau ga naku babin kyauta domin jin dadinku hakika comments dinku na kayatar dani…._

 

***K’asa da kai Aliyu yayi jin abinda mahaifin muslima yafada, bai iya yin magana ba sakamakon bugun da zuciyasa keyi, tabbas idan yace baya son muslima yayiwa zuciyarsa karya to amma baya buri ko fatan saka halimanshi cikin damuwa ko bakin ciki sannan baya son tayi masa kallon butulu saboda tabashi dukkan wani farin ciki kuma har gobe bata daina ba,yasan dakyar idan zata fahimci matsananciyar kaunar da yake yi mata,

“Aliyu ni aganina idan har babu matsala to bama sai mun ja abin da nisaba tunda bawai aurene na saurayi da budurwa ba, sannan iya sadaki kadai na yarje maka ka bayar……”

Sunkuyar da kai Aliyu yayi yana jin faduwar gabanshi tana karuwa,

“Shikenan Baba nagode madalla, amma zan dai je inyi shawara da magabata na tukunna aji me zasu ce”

“Ehh to ai hakanma yayi kuma babu aibu, yayi dai dai hakan, Allah yayi albarka, dan Allah sai ka gaishesu idan kaje…”

“Zasu ji, nagode….”

Daga haka ya mike yana rike da hannun haidar sukayi waje, suna tsaye yanata yimasa tambayoyi muslima ta fito, daga dan nesa dasu ta tsaya tana kallonsu yanda Aliyu ya takarkare yana hira da haidar din abin yabata dariya, mikewa tsaye yayi daga durkuson da yayi yana kallonta,

“Me kike yiwa dariya?”

“Babu komai ya sayyadi, kawai dai…”

“Kawai dai me? Yanzu dai ni zanje inwuce gida madam na jirana”

“Allah sarki to ka gaidasu…” Tafada tana gyara hijabinta,

“Zasuji…”

Maida kallonshi yayi ga haidar,

“Aliyu inbaka barka da juma’a?”

Yauma dubu biyar ya bawa haidar kamar zuwanshi na rannan, daga nan yabude motarshi yafara firfito da kayan da ya kawo musu na abinci wanda sai yara yasa suka kinkima suka shigar musu dashi ciki, bai jira komai ba yafada motarsa yatafi, lokacin da yaje gida a kitchen ya samu halima ta kammala girki tana hada musu coconut & milk shake,

Ganinta yayi tayi masifar yi masa kyau domin body hug ce ajikinta yellow sai bakar mini skirt kanta ba dan kwali, lallabawa yayi ya rufe mata idanuwanta da hannunshi, dariya yaji tayi ta dora hannunta saman nashi,

“Darling brother kenan…wai ka zaci zan tsorata?”

Bude mata idanuwan nata yayi shima yana dariya,

“Ban hana zama babu dan kwali ba? Uhm..??”

Rike hannunshi tayi wanda yake shafa cikinta dashi,

“Sorry bazan kara ba, yanzun ma yana falo acan na mantoshi”

“Ai bakya son dan kwali ban san meyasa ba”

“Kaifa nayiwa kwalliya, ka kalla mana ka gani” Ta karashe maganar cikin shagwaba,

“To ai idan bana nan sai arinka rufe min kayana ana suturceshi idan ina nan kuma sai abar min abude ingani ko?”

Murmushi tayi ta kalleshi daidai lokacin da take juye coconut and milk shake din acikin glass jug,

“Kajishi wai kayanshi….”

“Ehh mana ko ba nawa bane? Gaba dayanki fa mallakina ne sai yanda naso zanyi da abuna”

Dariya maganarshi tabata, abincin ta harhada akan babban farantin ta mika masa,

“Tohh carry this…., mu tafi yunwa nakeji gashi na gaji dayawa”

Karba yayi tana biye dashi rikeda jug da cups suka fita,

“Kince yunwa kikeji to wacce aciki? Kin san kala biyuce, yunwar abinci ko kuma yunwata….?”

Ya karasa tambayar yana tsareta da ido,

“Nidai gaskiya kabari, agajiye nake fa kaga yadda tuwon nan ya wahalar dani wurin tukashi? Yau da inada karamin ciki da kila sai ya zube…”

Arazane ya kalleta harda zazzaro manyan idanuwanshi,

“Cewa zakiyi yau da kin tafka min babbar asarar da ban taba yinta ba…., to gaskiya karki kara tuka tuwo agidan nan ma daga yau, ki rinka bari idan nadawo sai muyi tare…., zubewar ciki? Tab…. ai ranar…. Kedai Allah ya rufa asiri kawai”

Dariya tayi ta kwanta akan cinyarsa, dakatawa yayi da zuba abincin da yafara ya shafa gashinta,

“Duk ka wani rude sai kace dagaske cikin ya zube”

“Ai bama na son inji kina maganar zubewar nan sadiyayye, nidai ki rufa min asiri ki daina aikin wahala ni gara ki rinka sakani koma menene sai inyi miki”

“To wai ansamu cikin ne da kaketa wannan labarin da kafa dokokin?”

Rada yayi mata a kunnenta,

“Za asamu ai yarinya, sai kin gama shan…….. tukunna……”

Rufe fuskarta tayi da hannu daya,

“Dan Allah kabari…., ni bana so”

“Au bakya so? To shikenan daga yau nadaina tunda bakya so”

Tashi zaune tayi tasa hannu acikin abincin da yagama zuba musu tuwon shinkafa miyar agushi wacce taji naman ganda da kayan ciki,

Kallonta ya tsaya yi yanda take cin abincin da sauri sauri, dauko babbar lauma yayi ya saka mata abaki,

“Bari in tayaki in kara miki ko?…..”

Kai ta daga yaci gaba da bata itama tana bawa kanta har saida ta koshi lokacinne yafara ciyar da kanshi,

“Naga Kinsha ruwa saura…,saura wannan” Ya gama maganar yana nuna mata milk shake da idanuwanshi,

“Kai na koshi kuma…”

“To yar bakin ciki hanani shanawa”

Dariya tayi sannan ta tsiyaya tasha cikin cup ta kwanta tana kallonshi, karar shigowar text yaji awayarshi dake ajiye gefe daya, daukar wayar tayi ta mika masa kamar yace ta bude ta karanto sai kuma ya karba, duk da baida number din amma ya fahimci sakon daga wacece saboda dunbin godiyar da yaga tayi masa tareda addu’ar samun budi,goge sakon yayi gaba dayanshi bayan ya gama karantawa, karbar wayar tashi halima tayi tana kallon picx dinsu,

Zare ido tayi sakamakon ganin wani hotonta wanda ta tura masa tun farkon komawarsu abuja lokacin yana office ta tura mishi daga ita sai bra da pant,

“Kai yaya Ali ai baka goge wannan hoton ba….”

Karbar wayar yayi ya kalli hoton,

“Akan me zan goge bayan ina enjoying kallonshi…. Karki goge min kayana Allah”

“To idan wani yagani fa?”

“Babu wanda zai gani, wa yake taba min wayata idan bake ba sai dai ko idan kece wanin….”

Karba tayi taci gaba da gani wani tayi dariya wani kuma kunya ta kamata ma domin mafi yawa daga ita sai bra ko half vest ashe idan ta tura masa baya gogewa adana kayansa yake,

“Gaskiya Darling brother duk ranar da wani ya karbi wayar nan shikenan nikam…”

“Wai waye ya fada miki wani zai kallar min waya ne? Wayar nanfa sirrina ne aciki akan me zanyi sakaci da ita?”

Batace komai ba taci gaba da abunda take har yagama cin abincin ya jawo pillow akan kujera ya kwanta kusa da ita,

“Zo muyi baccin kalula”

Nokewa ta soma yi,

“A’a nidai yi kai kadai ni banaji”

Ta karfi yasata ajikinsa yana dariya,

“Sabon salo wato yau ni nake gayyata ana kin amsa min ko? Kema da wasa kike ai wallahi tunda kika bani abinci na koshi harda madara kema kin san dole ta motsa min…..”

Kokawa suka fara tana zillewa daga karshe nan suka bar komai ya goyeta suka koma bedroom can suka karasa wasan. Bacci sukayi sosai har la’asar basu tashi ba sai 5 saura sannan ta bude idonta, ganin yanda Aliyu ya rufu akanta kamar yana gudun kar adauke masa ita kafin yatashi daga bacci abin yabata dariya, kokarin dagashi daga kanta take dan ta tashi amma abin ya gagara,

“Ya Ali to tashi….”

Tafada tana shafa sumar kanshi,

“Au har kokarin naki yakare? Ai najirane inga ta yadda za ayi adauke ni atashi”

“Ohh dama kana jina? To ai zan iya tunda baka da wani nauyi, Allah ji nake kamar babu mutum ajikina”

“To ko in sakar miki duka nauyin nawa kiji?”

“A’a dan Allah bari, Allah zaka saka cikin ma ya zube idan yashiga, ka tashi nidai sannan Allah gemun nan naka kasan yanda zakayi dashi dan…..”

Dariya yayi yatashi yana kallonta wuf ta ja blanket ta rufu lokacin da yatashi,

“Sabon salo…. Wanne dare ne wanda jemage bai gani ba kuma?”

“Malam wai yau ba zakayi salla bane?”

“An yimin uzuri ai tunda ganawa nayi da iyalina…., yawwa me gemun nawa yayi ne?”

Harararshi tayi taja mini skirt dinta ta sakata ta sama ta tashi duk da bata gama rufe mata jiki ba,

“Idan ka gama neman maganar kana iya zuwa kayi wanka…”

Daga haka tawuce bathroom nan yasauka yabita shima,

Sam bai kara fita ba ranar saida dare yayi ne ma suka shiga wurinsu umma hira, wurin 11 saura suka dawo part dinsu nan yasake ganin massage din muslima wato goodnight text massage bai barshi awayar ba ya gogeshi kamar na dazu domin yasan duk ranar da yar rigimar tasa ta gani mai rabasu sai Allah.

Washe gari kuwa da yamma lokacin da yaje makaranta yana office wayar muslima ta katse masa aikin da yakeyi na tsara albashin malamai, bayan sun gaisa ne tace zatazo tayi gaisuwa nan yace yana office daga haka ya katse wayar yaci gaba da aikinsa,

Tana sanye da nikab da dogon hijabi ta shiga office din tunda ya dago ya kalleta sau daya bai kara kallonta ba ahaka suka gaisa tana zaune kan kujerar dake gaban teburinsa sai dan satar kallonshi take shadda ce ajikinsa ruwan toka da hula sai agogon azurfa daure a hannunsa, shi dai gashi ba fari bane amma kalarshi ta dace dashi ko ba afada mata ba tasan jikinshi inbanda laushi da santsi babu abinda zaiyi, maganarshi ce ta katse mata tunaninta,

“Ya jikin baba?…”

“Da sauki yana cewa ai akara yimaka godiya yagode sosai Allah ya saka da alkhairi”

Murmushi yayi har lokacin idonshi akasa yana kallon paper din da yake rubuce rubuce akai,

“Kai haba, ai babu komai, Allah dai yabashi lafiya….”

“Amin…”

Cigaba da satar kallonshi tayi har yagama ya dago nan suka hada ido, saurin sauke nikab dinta tayi tana murmushi, shima murmushin yayi baice komai ba ya kawar da kanshi. Ta jima a office dinshi sai dai duk dagowar da zaiyi sai sun hada ido domin ita yanzu Aliyu bala’in burgeta yake fiyeda yanda yake burgeta abaya, sai daf da lokacin tashi sannan ta bar office dinsa ta tafi, tun daga wannan rana al’amura suka dan fara sauyawa tsakaninsa da muslima shi kawai tausayinta yakeji saboda irin yanayin da ta tsinci kanta aciki, koda suka koma abuja bai fiya kiranta ba musamman ma idan yana gida ita kuwa koda yaushe cikin tura masa da text massage take da zarar ya karanta yake gogewa domin baya son halima ta gani ta shiga damuwa domin bata da shamaki da wayarshi.

Yau kasancewar ya tashi da mura bai fita da wuriba sai wurin 12 wannan dinma zai samo maganine sannan yana son yakira muslima domin sai kiranshi take tayi yana gida daga karshe sai kashe wayar yayi,

Bai wani jima ba yadawo lokacin har halima tagama yi masa farfesun kayan ciki, sosai take kula dashi yau atishawa goma sannu goma. Bayan sunyi sallar la’asar yana kwance ya tasa kai da cinyarta suna kallo wayarshi ta soma vibrating,katse kiran yayi saboda ganin muslima ce ita kam halima bata ma kula ba dan sam hankalinta baya wurin. Washe gari ya fita aiki domin yaji dan dama dama, yana tsaka da hada tayar wata sabuwar mota da su dan larai suka kasa yaji kiran halima da murmushi ya daga domin yasan ganin har yanzu bai koma yaci abinci bane yasata kira ai kuwa hakanne domin yana dauka ta fara shagwaba bai fargaba duk ya bata farar sabuwar shaddar dake jikinshi wurin biye mata, sallama sukayi yana kissing dinta ta cikin wayar, narke murya tayi sosai tace,

“Nidai Allah darling brother afili nake so ba awaya ba….”

“To bani 15 minutes zanzo kinji…”

“Tom ina jiranka,i love you”

Saka wayar yayi cikin aljihunsa yana murmushi agurguje yayi yagama aikin ya nufi gida, tana zaune tana zaman jiransa ganinshi da yanda kayansa suka baci da baki abin yabata dariya musamman ma da taji wai itace sila, dakyar ya yarda yaci abincin domin tunda yashigo yaganta ya dage wurin touching din abunda yafi so rike hannunshi tayi tana harararshi,langabar da kai yayi yai kalar tausayi hakan da yayi yasata yin dariya,

“Yau rowa ake yimin ko?”

“Ba rowa bane kaci abincin tukunna darling brother…”

Gyada kai yayi ta shiga bashi abaki shima yana bata.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya wanda ahalin yanzu Aliyu yana jin kaunar muslima acikin zuciyarshi amma ko kusa yasan bata kama koda kafar halima ba acikin ranshi, sosai yasake nunka kulawar da yake bawa halima akan na da wannan dalilinne yasa sam bata fahimci yana zawarcin muslima ba, kasancewar baya son yayi abinda zaizo agaba yana dana sani yasashi dukufa da addu’a tareda barwa Allah zabi akan lamarinsu da muslima, sosai yaji auren ya kwanta masa arai sabanin da dayake jin dar dar sai dai fa har yanzu gabansa bai bar faduwa ba idan ya tuno da halima domin yasan za asha daga da ita.

Malam lawan yafara samu da maganar nan yasa albarka kuma yayi fatan alkhairi daga nan kuma yasamu Abba shima ya fada masa shima abban bai bada matsala ba Ummi ce dai ta dan so tayi tangarda domin aganinta duk wanda ya ki ka da safe da daddare kuma yazo yace yana sonka to karya yake yi domin abinda iyayen muslima suka yi masa yayi mutukar yi mata ciwo,

Duk yanda yaso yashawo kan ummi kin amincewa tayi daga karshe ma da fada ta rufeshi kamar zata cinyeshi abinda bata taba yi masa ba domin tun yana yaro shi mai biyayya ne agareta bata taba hanashi abu sau biyu da zarar ta haneshi akaron farko yake nisantar abun,

Dagowa yayi ya kalli ummin bayan tayi shiru daga fadan data rufeshi dashi,

“Wallahi tallahi Ummi bawai zanyi auren nan da wata manufa bane sannan bawai zanyi shi dan in batawa halima ba, Ummi ko halima yau wani take aure baniba ni mai tsaya mata ne wurin ganin na hana a zalunceta balle ni da kaina….,wallahi ummi babu macen da zan yiwa irin son da nakewa halima, kuma ni sam aurena bashida alaka da maganar wai bamu haihu ba saboda nasan haihuwa ta Allah ce, nidai kawai ina tausayin muslima ne kuma ina burin taimaka mata….”

“Kaga Aliyu katashi kabar dakin nan domin ba aminta zanyi da maganganunka ba”

Bai kara cewa komai ba yatashi yafita, gaba daya ummi kin amincewa tayi da maganar har saida malam lawan yazo har gida yayi mata maganganu na fahimta da nutsuwa sannan ta sauko saboda darajarsa amma da cewa tayi yanda abaya suka hanashi auren yarsu to yanzu itama ta hana danta auren tasu yar suje subawa dan asali ba shege ba.

Su halima na abuja Malam lawan da Abba sukaje gidansu muslima nan babanta yace sadaki kawai Aliyu zai bada sai adaura aure nanda mako uku, hankalin Aliyu yanzu tashi yayi sosai saboda jin abinda su Abba suka yanke domin shi har yau bai bari halima ta fahimci wani abuba shi babban tashin hankalinsa ma yanzu ta yanda zai fuskanceta ya fada mata cewar zaiyi mata kishiya wannan damuwar kusan yanzu itace take hanashi bacci,yanke shawarar tunkarar Abba yayi akan yataimaka masa ya fadawa halima zai kara aure domin shi bazai taba iya furta mata wannan maganar ba, abba ya amince yace karshen Sati su shirya suzo gida inyaso sai su hadu da iyayensu mata su fada mata cikin lumana da kwanciyar hankali……

 

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI…*🤴🏻

 

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

*56*

 

_Dan asali fans kuna ina? Gaskiya ban san haka kuke da mutukar yawa ba,yau ga naku babin kyauta domin jin dadinku hakika comments dinku na kayatar dani…._

 

***K’asa da kai Aliyu yayi jin abinda mahaifin muslima yafada, bai iya yin magana ba sakamakon bugun da zuciyasa keyi, tabbas idan yace baya son muslima yayiwa zuciyarsa karya to amma baya buri ko fatan saka halimanshi cikin damuwa ko bakin ciki sannan baya son tayi masa kallon butulu saboda tabashi dukkan wani farin ciki kuma har gobe bata daina ba,yasan dakyar idan zata fahimci matsananciyar kaunar da yake yi mata,

“Aliyu ni aganina idan har babu matsala to bama sai mun ja abin da nisaba tunda bawai aurene na saurayi da budurwa ba, sannan iya sadaki kadai na yarje maka ka bayar……”

Sunkuyar da kai Aliyu yayi yana jin faduwar gabanshi tana karuwa,

“Shikenan Baba nagode madalla, amma zan dai je inyi shawara da magabata na tukunna aji me zasu ce”

“Ehh to ai hakanma yayi kuma babu aibu, yayi dai dai hakan, Allah yayi albarka, dan Allah sai ka gaishesu idan kaje…”

“Zasu ji, nagode….”

Daga haka ya mike yana rike da hannun haidar sukayi waje, suna tsaye yanata yimasa tambayoyi muslima ta fito, daga dan nesa dasu ta tsaya tana kallonsu yanda Aliyu ya takarkare yana hira da haidar din abin yabata dariya, mikewa tsaye yayi daga durkuson da yayi yana kallonta,

“Me kike yiwa dariya?”

“Babu komai ya sayyadi, kawai dai…”

“Kawai dai me? Yanzu dai ni zanje inwuce gida madam na jirana”

“Allah sarki to ka gaidasu…” Tafada tana gyara hijabinta,

“Zasuji…”

Maida kallonshi yayi ga haidar,

“Aliyu inbaka barka da juma’a?”

Yauma dubu biyar ya bawa haidar kamar zuwanshi na rannan, daga nan yabude motarshi yafara firfito da kayan da ya kawo musu na abinci wanda sai yara yasa suka kinkima suka shigar musu dashi ciki, bai jira komai ba yafada motarsa yatafi, lokacin da yaje gida a kitchen ya samu halima ta kammala girki tana hada musu coconut & milk shake,

Ganinta yayi tayi masifar yi masa kyau domin body hug ce ajikinta yellow sai bakar mini skirt kanta ba dan kwali, lallabawa yayi ya rufe mata idanuwanta da hannunshi, dariya yaji tayi ta dora hannunta saman nashi,

“Darling brother kenan…wai ka zaci zan tsorata?”

Bude mata idanuwan nata yayi shima yana dariya,

“Ban hana zama babu dan kwali ba? Uhm..??”

Rike hannunshi tayi wanda yake shafa cikinta dashi,

“Sorry bazan kara ba, yanzun ma yana falo acan na mantoshi”

“Ai bakya son dan kwali ban san meyasa ba”

“Kaifa nayiwa kwalliya, ka kalla mana ka gani” Ta karashe maganar cikin shagwaba,

“To ai idan bana nan sai arinka rufe min kayana ana suturceshi idan ina nan kuma sai abar min abude ingani ko?”

Murmushi tayi ta kalleshi daidai lokacin da take juye coconut and milk shake din acikin glass jug,

“Kajishi wai kayanshi….”

“Ehh mana ko ba nawa bane? Gaba dayanki fa mallakina ne sai yanda naso zanyi da abuna”

Dariya maganarshi tabata, abincin ta harhada akan babban farantin ta mika masa,

“Tohh carry this…., mu tafi yunwa nakeji gashi na gaji dayawa”

Karba yayi tana biye dashi rikeda jug da cups suka fita,

“Kince yunwa kikeji to wacce aciki? Kin san kala biyuce, yunwar abinci ko kuma yunwata….?”

Ya karasa tambayar yana tsareta da ido,

“Nidai gaskiya kabari, agajiye nake fa kaga yadda tuwon nan ya wahalar dani wurin tukashi? Yau da inada karamin ciki da kila sai ya zube…”

Arazane ya kalleta harda zazzaro manyan idanuwanshi,

“Cewa zakiyi yau da kin tafka min babbar asarar da ban taba yinta ba…., to gaskiya karki kara tuka tuwo agidan nan ma daga yau, ki rinka bari idan nadawo sai muyi tare…., zubewar ciki? Tab…. ai ranar…. Kedai Allah ya rufa asiri kawai”

Dariya tayi ta kwanta akan cinyarsa, dakatawa yayi da zuba abincin da yafara ya shafa gashinta,

“Duk ka wani rude sai kace dagaske cikin ya zube”

“Ai bama na son inji kina maganar zubewar nan sadiyayye, nidai ki rufa min asiri ki daina aikin wahala ni gara ki rinka sakani koma menene sai inyi miki”

“To wai ansamu cikin ne da kaketa wannan labarin da kafa dokokin?”

Rada yayi mata a kunnenta,

“Za asamu ai yarinya, sai kin gama shan…….. tukunna……”

Rufe fuskarta tayi da hannu daya,

“Dan Allah kabari…., ni bana so”

“Au bakya so? To shikenan daga yau nadaina tunda bakya so”

Tashi zaune tayi tasa hannu acikin abincin da yagama zuba musu tuwon shinkafa miyar agushi wacce taji naman ganda da kayan ciki,

Kallonta ya tsaya yi yanda take cin abincin da sauri sauri, dauko babbar lauma yayi ya saka mata abaki,

“Bari in tayaki in kara miki ko?…..”

Kai ta daga yaci gaba da bata itama tana bawa kanta har saida ta koshi lokacinne yafara ciyar da kanshi,

“Naga Kinsha ruwa saura…,saura wannan” Ya gama maganar yana nuna mata milk shake da idanuwanshi,

“Kai na koshi kuma…”

“To yar bakin ciki hanani shanawa”

Dariya tayi sannan ta tsiyaya tasha cikin cup ta kwanta tana kallonshi, karar shigowar text yaji awayarshi dake ajiye gefe daya, daukar wayar tayi ta mika masa kamar yace ta bude ta karanto sai kuma ya karba, duk da baida number din amma ya fahimci sakon daga wacece saboda dunbin godiyar da yaga tayi masa tareda addu’ar samun budi,goge sakon yayi gaba dayanshi bayan ya gama karantawa, karbar wayar tashi halima tayi tana kallon picx dinsu,

Zare ido tayi sakamakon ganin wani hotonta wanda ta tura masa tun farkon komawarsu abuja lokacin yana office ta tura mishi daga ita sai bra da pant,

“Kai yaya Ali ai baka goge wannan hoton ba….”

Karbar wayar yayi ya kalli hoton,

“Akan me zan goge bayan ina enjoying kallonshi…. Karki goge min kayana Allah”

“To idan wani yagani fa?”

“Babu wanda zai gani, wa yake taba min wayata idan bake ba sai dai ko idan kece wanin….”

Karba tayi taci gaba da gani wani tayi dariya wani kuma kunya ta kamata ma domin mafi yawa daga ita sai bra ko half vest ashe idan ta tura masa baya gogewa adana kayansa yake,

“Gaskiya Darling brother duk ranar da wani ya karbi wayar nan shikenan nikam…”

“Wai waye ya fada miki wani zai kallar min waya ne? Wayar nanfa sirrina ne aciki akan me zanyi sakaci da ita?”

Batace komai ba taci gaba da abunda take har yagama cin abincin ya jawo pillow akan kujera ya kwanta kusa da ita,

“Zo muyi baccin kalula”

Nokewa ta soma yi,

“A’a nidai yi kai kadai ni banaji”

Ta karfi yasata ajikinsa yana dariya,

“Sabon salo wato yau ni nake gayyata ana kin amsa min ko? Kema da wasa kike ai wallahi tunda kika bani abinci na koshi harda madara kema kin san dole ta motsa min…..”

Kokawa suka fara tana zillewa daga karshe nan suka bar komai ya goyeta suka koma bedroom can suka karasa wasan. Bacci sukayi sosai har la’asar basu tashi ba sai 5 saura sannan ta bude idonta, ganin yanda Aliyu ya rufu akanta kamar yana gudun kar adauke masa ita kafin yatashi daga bacci abin yabata dariya, kokarin dagashi daga kanta take dan ta tashi amma abin ya gagara,

“Ya Ali to tashi….”

Tafada tana shafa sumar kanshi,

“Au har kokarin naki yakare? Ai najirane inga ta yadda za ayi adauke ni atashi”

“Ohh dama kana jina? To ai zan iya tunda baka da wani nauyi, Allah ji nake kamar babu mutum ajikina”

“To ko in sakar miki duka nauyin nawa kiji?”

“A’a dan Allah bari, Allah zaka saka cikin ma ya zube idan yashiga, ka tashi nidai sannan Allah gemun nan naka kasan yanda zakayi dashi dan…..”

Dariya yayi yatashi yana kallonta wuf ta ja blanket ta rufu lokacin da yatashi,

“Sabon salo…. Wanne dare ne wanda jemage bai gani ba kuma?”

“Malam wai yau ba zakayi salla bane?”

“An yimin uzuri ai tunda ganawa nayi da iyalina…., yawwa me gemun nawa yayi ne?”

Harararshi tayi taja mini skirt dinta ta sakata ta sama ta tashi duk da bata gama rufe mata jiki ba,

“Idan ka gama neman maganar kana iya zuwa kayi wanka…”

Daga haka tawuce bathroom nan yasauka yabita shima,

Sam bai kara fita ba ranar saida dare yayi ne ma suka shiga wurinsu umma hira, wurin 11 saura suka dawo part dinsu nan yasake ganin massage din muslima wato goodnight text massage bai barshi awayar ba ya gogeshi kamar na dazu domin yasan duk ranar da yar rigimar tasa ta gani mai rabasu sai Allah.

Washe gari kuwa da yamma lokacin da yaje makaranta yana office wayar muslima ta katse masa aikin da yakeyi na tsara albashin malamai, bayan sun gaisa ne tace zatazo tayi gaisuwa nan yace yana office daga haka ya katse wayar yaci gaba da aikinsa,

Tana sanye da nikab da dogon hijabi ta shiga office din tunda ya dago ya kalleta sau daya bai kara kallonta ba ahaka suka gaisa tana zaune kan kujerar dake gaban teburinsa sai dan satar kallonshi take shadda ce ajikinsa ruwan toka da hula sai agogon azurfa daure a hannunsa, shi dai gashi ba fari bane amma kalarshi ta dace dashi ko ba afada mata ba tasan jikinshi inbanda laushi da santsi babu abinda zaiyi, maganarshi ce ta katse mata tunaninta,

“Ya jikin baba?…”

“Da sauki yana cewa ai akara yimaka godiya yagode sosai Allah ya saka da alkhairi”

Murmushi yayi har lokacin idonshi akasa yana kallon paper din da yake rubuce rubuce akai,

“Kai haba, ai babu komai, Allah dai yabashi lafiya….”

“Amin…”

Cigaba da satar kallonshi tayi har yagama ya dago nan suka hada ido, saurin sauke nikab dinta tayi tana murmushi, shima murmushin yayi baice komai ba ya kawar da kanshi. Ta jima a office dinshi sai dai duk dagowar da zaiyi sai sun hada ido domin ita yanzu Aliyu bala’in burgeta yake fiyeda yanda yake burgeta abaya, sai daf da lokacin tashi sannan ta bar office dinsa ta tafi, tun daga wannan rana al’amura suka dan fara sauyawa tsakaninsa da muslima shi kawai tausayinta yakeji saboda irin yanayin da ta tsinci kanta aciki, koda suka koma abuja bai fiya kiranta ba musamman ma idan yana gida ita kuwa koda yaushe cikin tura masa da text massage take da zarar ya karanta yake gogewa domin baya son halima ta gani ta shiga damuwa domin bata da shamaki da wayarshi.

Yau kasancewar ya tashi da mura bai fita da wuriba sai wurin 12 wannan dinma zai samo maganine sannan yana son yakira muslima domin sai kiranshi take tayi yana gida daga karshe sai kashe wayar yayi,

Bai wani jima ba yadawo lokacin har halima tagama yi masa farfesun kayan ciki, sosai take kula dashi yau atishawa goma sannu goma. Bayan sunyi sallar la’asar yana kwance ya tasa kai da cinyarta suna kallo wayarshi ta soma vibrating,katse kiran yayi saboda ganin muslima ce ita kam halima bata ma kula ba dan sam hankalinta baya wurin. Washe gari ya fita aiki domin yaji dan dama dama, yana tsaka da hada tayar wata sabuwar mota da su dan larai suka kasa yaji kiran halima da murmushi ya daga domin yasan ganin har yanzu bai koma yaci abinci bane yasata kira ai kuwa hakanne domin yana dauka ta fara shagwaba bai fargaba duk ya bata farar sabuwar shaddar dake jikinshi wurin biye mata, sallama sukayi yana kissing dinta ta cikin wayar, narke murya tayi sosai tace,

“Nidai Allah darling brother afili nake so ba awaya ba….”

“To bani 15 minutes zanzo kinji…”

“Tom ina jiranka,i love you”

Saka wayar yayi cikin aljihunsa yana murmushi agurguje yayi yagama aikin ya nufi gida, tana zaune tana zaman jiransa ganinshi da yanda kayansa suka baci da baki abin yabata dariya musamman ma da taji wai itace sila, dakyar ya yarda yaci abincin domin tunda yashigo yaganta ya dage wurin touching din abunda yafi so rike hannunshi tayi tana harararshi,langabar da kai yayi yai kalar tausayi hakan da yayi yasata yin dariya,

“Yau rowa ake yimin ko?”

“Ba rowa bane kaci abincin tukunna darling brother…”

Gyada kai yayi ta shiga bashi abaki shima yana bata.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya wanda ahalin yanzu Aliyu yana jin kaunar muslima acikin zuciyarshi amma ko kusa yasan bata kama koda kafar halima ba acikin ranshi, sosai yasake nunka kulawar da yake bawa halima akan na da wannan dalilinne yasa sam bata fahimci yana zawarcin muslima ba, kasancewar baya son yayi abinda zaizo agaba yana dana sani yasashi dukufa da addu’a tareda barwa Allah zabi akan lamarinsu da muslima, sosai yaji auren ya kwanta masa arai sabanin da dayake jin dar dar sai dai fa har yanzu gabansa bai bar faduwa ba idan ya tuno da halima domin yasan za asha daga da ita.

Malam lawan yafara samu da maganar nan yasa albarka kuma yayi fatan alkhairi daga nan kuma yasamu Abba shima ya fada masa shima abban bai bada matsala ba Ummi ce dai ta dan so tayi tangarda domin aganinta duk wanda ya ki ka da safe da daddare kuma yazo yace yana sonka to karya yake yi domin abinda iyayen muslima suka yi masa yayi mutukar yi mata ciwo,

Duk yanda yaso yashawo kan ummi kin amincewa tayi daga karshe ma da fada ta rufeshi kamar zata cinyeshi abinda bata taba yi masa ba domin tun yana yaro shi mai biyayya ne agareta bata taba hanashi abu sau biyu da zarar ta haneshi akaron farko yake nisantar abun,

Dagowa yayi ya kalli ummin bayan tayi shiru daga fadan data rufeshi dashi,

“Wallahi tallahi Ummi bawai zanyi auren nan da wata manufa bane sannan bawai zanyi shi dan in batawa halima ba, Ummi ko halima yau wani take aure baniba ni mai tsaya mata ne wurin ganin na hana a zalunceta balle ni da kaina….,wallahi ummi babu macen da zan yiwa irin son da nakewa halima, kuma ni sam aurena bashida alaka da maganar wai bamu haihu ba saboda nasan haihuwa ta Allah ce, nidai kawai ina tausayin muslima ne kuma ina burin taimaka mata….”

“Kaga Aliyu katashi kabar dakin nan domin ba aminta zanyi da maganganunka ba”

Bai kara cewa komai ba yatashi yafita, gaba daya ummi kin amincewa tayi da maganar har saida malam lawan yazo har gida yayi mata maganganu na fahimta da nutsuwa sannan ta sauko saboda darajarsa amma da cewa tayi yanda abaya suka hanashi auren yarsu to yanzu itama ta hana danta auren tasu yar suje subawa dan asali ba shege ba.

Su halima na abuja Malam lawan da Abba sukaje gidansu muslima nan babanta yace sadaki kawai Aliyu zai bada sai adaura aure nanda mako uku, hankalin Aliyu yanzu tashi yayi sosai saboda jin abinda su Abba suka yanke domin shi har yau bai bari halima ta fahimci wani abuba shi babban tashin hankalinsa ma yanzu ta yanda zai fuskanceta ya fada mata cewar zaiyi mata kishiya wannan damuwar kusan yanzu itace take hanashi bacci,yanke shawarar tunkarar Abba yayi akan yataimaka masa ya fadawa halima zai kara aure domin shi bazai taba iya furta mata wannan maganar ba, abba ya amince yace karshen Sati su shirya suzo gida inyaso sai su hadu da iyayensu mata su fada mata cikin lumana da kwanciyar hankali……

 

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI….*!🤴🏻

 

_*NA*_

_*UMMI A’ISHA*_

 

*57*

 

***Ranar da suka sauka Zaria da daddare halima ta amsa kiran Abba wanda ke zaune falonsa shida su umma ita kadai taje domin tabar Aliyu a part dinsu,cikeda tausayi ummi tabita da kallo lokacin da tashiga cikin falon,

Zama tayi kusa da umma a kasa taja sadiq wanda keta rashin ji shida Faruk ta dorashi saman cinyarta tana yimasa wasa,

Saida Abba yayi amfani da kalaman ban hakuri da kwantar da hankali sannan ya fayyace mata abinda ke faruwa, wani dummm taji sakamakon jin zuciyarta kamar ta daina aiki tun daga nan ta daina gane komai, harsu abba sukayi maganganunsu suka gama bata san me suke cewa ba ita dai kawai tayi shiru kanta a kasa, saida ummi tazo ta dagata domin kasa motsawa daga wurin tayi, har kofar part dinsu suka rakata suna bata baki sannan suka barta kowa yawuce part dinsa,

A balcony ta zauna ta rafka uban tagumi gama daya ta rasa gane meke damunta domin jinta take kamar kowacce jijiya ta jikinta ta saki banda tsayawa cak din da take jin kamar zuciyarta tayi,tafi awa biyu azaune awurin batare da tasan me take tunani ba.

Shiru shiru Aliyu yaga bata dawo ba ganin har 11 na neman yi yasashi tashi yabita turus yayi saboda ganinta zaune bakin baranda ta rafka tagumi ko sauron dake kaiwa da kawowa bataji,

Karasawa wurinta yayi ya nemi ya dagota nan ta zame jikinta ta shiga ciki, afalo ta zauna shima ya biyota,

Zama yayi agefenta yayi kasa da murya cikin tausasawa ya soma magana,

“Halimatu na dan Allah dan annabi karki sawa ranki damuwa…., ki fahimceni kuma ki yarda dani wallahi ke kadai nake so…, halima ban taba son wani abu a duniyar nan kamar keba, kowanne bugu da zuciyata keyi to sonki na nan makale acikinta…, bai kamata ki daga hankalinki ba akan maganar auren nanba domin babu macen da zata kai koda rabin inda kike acikin zuciyata…. Wallahi kinada matsayi mai girma agareni…, karfa ki manta halima ke yar uwata ce sannan kuma matata uwar yayana wacce nake mutukar kauna…., Dan Allah karki bari shaidan yayi miki huduba halima…., karki tada hankalinki akan auren nan, bazawara ce fa wacce ta haihu…., ko budurwa zan auro bana tunanin zata samu rabin soyayyar da nake yi miki bare bazawara kuma bazawarar ma wacce ta haihu….!”

Shiru tayi masa har yayi maganarsa ya gama bata tanka ba nan yadora daga inda ya tsaya nan dinma tayi biris dashi zuwa can ta kalleshi da jajayen idanuwanta wadanda suka kada,

“Yanzu ya Aliyu ni zaka yiwa kishiya ko? Saboda kaga ni ban haihu ba shiyasa zaka auro wata ta haifa maka yara, shiyasa zaka auro bazawara wacce ta taba haihuwa domin kasan ita zata haihu maka ko..?”

Hankalinsa idan yayi dubu to saida yatashi saboda jin abinda tafada, ita kanta bata taba ganinsa cikin irin wannan yanayin ba sai yau,

“Halima ki yarda da abunda zan fada miki wallahi tallahi aurena baida alaka da maganar haihuwa, wallahi halima ni mai iya zama dake ne ahaka har karshen rayuwata koda kuwa bazaki haifa min yara ba….”

“Babu komai naji ni ban haihu ba, ita amaryar taka idan tazo ta haifa maka taron arfa….”

Daga haka ta tashi tabar wurin ta shige bedroom, tana shiga tafada kan gado ta soma rusar kuka, binta yayi yafara rarrashinta amma sam bata saurareshi ba duk yanda yaso ya fahimtar da ita taki fahimta asalima ko saurararsa batayi ba, haka yayita lallabata amma sai sake botsarewa take tana kuka, yau kam kusan kwanan zaune sukai domin har asuba bata bar kukanba. Lokacin da yadawo daga salla bai isketa a dakin ba tana can daya bedroom din ta rufe kanta nan yayi yayi da ita ta bude taki, har azahar bata fito ba gaba daya tagama tayar masa da hankali, saida yaje ya kira umma tazo tayi magana sannan ta bude ta fito, zaunarta umma tayi ta rufeta da fada,

“To wannan abun da kika tsura shine zai hana ayi auren ko yaya? Akanki aka fara kishiya da zaki musgunawa rayuwarki da ta wani? To wallahi kar na ji kar na gani, idan yasake zuwa yace kinyi wani abu sai ranki ya baci….”

Daga haka umma ta fice tabarta shikuma yana daga daya falon yana jinsu, kayan tea ya hado mata ya kawo da tea flask domin ta hada ta sha, mikewa tayi tai ball da tea flask din nan take ya fashe ruwan zafin ciki ya tsiyaye, ko kallonsa batayi ba ta wuce daki, rike kai Aliyu yayi yana jin hankalinsa yana sake dugunzuma.

Wasa wasa tun daga ranar bata kara cemasa koda uffan ba tsakaninta dashi kawai ido amma idan zai kwana yana mata magana bazata amsa ba, ga uban kuka da ta mayar halayyarta yanzu koda yaushe cikin yinshi take ga kin cin abinci kullum sai ya kira umma ko ummi sannan zata yarda taci. Ita kam yanzu gaba daya gidan haushinsu takeji kamar tayi me dan bakin ciki domin gani take kamar dukkansu sun daina kaunarta musamman ma su umma domin mara masa bayan da sukayi basu hanashi ba,

Har ana saura kwana biyu daurin aure bata saurareshi ba bare yasa ran zata sauko, shi yar ramar ma da tayi ita tafi komai damunsa, ranar daurin aure kuwa tun safe yake zaune yana rarrashinta amma bata tanka masa ba tadai ci kukanta ta koshi musamman ma da taga ya shirya ya tafi wurin daurin auren,

Lokacin da yadawo daga daurin auren ita kadai yasake tararwa domin bata fadawa kowa ba tana zaune tagama kuka idanuwan nan jajur, zama yayi kusa da ita,

“Dan Allah halima kiyi hakuri….., ki yimin adu’ar zama adali a tsakaninku…. Gobe idan Allah yakaimu zamu tafi Abuja…”

Wani kallon da ta wurga masa ne yasashi kama bakinsa yayi shiru haka suka cigaba da zama har dare yayi daga nan Abba yashigo bayan yadawo daga sallar isha, wannan shine karo nafarko da Abba yazo sashensu, zama yayi yai musu nasiha sosai sannan yayiwa Sadiya albishir din ya mallaka mata sabuwar mota da jarin miliyan biyar domin tafara kasuwanci dan dogaro da kai, godiya sukayi masa ya tashi ya tafi daga nan suka cigaba da zaman kurame domin ko yayi mata magana bata amsa masa.

Washe gari duk yanda yarinka lallaminta akan ta shirya su tafi abuja banza tayi dashi daga karshe sai ummi yaje ya sanarwa koda ummin tazo tayi mata magana kuka tasa tace ita ba zataje ba nan ummi tace to ya barta anan tunda bata son zuwa shi yaje ya tafi ba dan yasoba haka yatafi yabarta bayan yaje ya dauki muslima,

Tunda yatafi kuma tasoma rashin lafiya daga karshe saida aka bata gado a asibiti, kullum idan yakira wayarta akashe da haka har akayi sati aranar ya bar muslima acan yataho Zaria, koda yazo lokacin kwana biyu da sallamarta daga asibiti, tana zaune afalo itada su Faruk baba tabawa na kitchen tana yi mata girki, ko kallonshi bata yiba ta dauke kanta duk da taga irin kyawun da yayi nan kishi ya turnuke zuciyarta tana ganin aikin gama dai yagama Aliyu ya kwana da wata wacce ba ita ba, zama yayi yana yimata sannu amma bata kalli ko inda yakeba. Tashi yayi yashiga daki nan tayi kwafa ta maida idonta kan tv, lokacin da ya fito lokacin baba tabawa ta gama aikinta zata tafi dama itace kullum take zuwa tana yimata yan aikace aikace,tareda su Faruk suka fita gaba daya har shi bayan ya jona wayarshi a charge, yana fita ta tashi ta shiga bedroom dinta gaba daya kayanshi ta kwaso takai su can daya bedroom din ta dauki key ta rufe dakinta ta koma ta zauna saman rug, bayan yayi sallar la’asar ya shigo gidan bedroom dinta ya nufa yajishi arufe juyawa yayi zuwa wurinta,

“One love ya naji dakin a kulle…..?”

“Ehh ni na kulle saboda nawane, ga kayanka can…..”

Murmushi yayi yana kallonta,

“Saboda me?”

“Saboda bazan kara hada makwanci dakai ba…..”

“Allah ya huci zuciyarki amma adai yimin afuwa”

Ko kallonsa bata kara yiba taci gaba da cin abincinta, daya bedroom din yawuce zaiyi wanka, karar wayarshi ce taketa damunta domin wurin sau uku kenan ana kira, jawo wayar tayi nan ta fahimci muslima ce domin ga sunanta nan jiki, wurgi tayi da wayar nan ta tarwatse kan tiles hakan yayi daidai da fitowar Aliyu, baice komai ba ya sunkuya ya tattara wayar ya koma ciki.

Kwananshi biyu amma babu wani abu mai dadi da yafaru domin bata yimasa magana sannan babu abinda takeyi agidan sai shine keyi, ko girki batayi idan kuma shi yayi bazata ciba sai dai ta tura su faruk su karbo mata awurin umma idan dare yayi kuma tarufe dakinta da mukulli, har yakoma Abuja bata kulashi. Kwananshi hudu a abujan yasake dawowa Zaria, ranar da yadawo, tana falo itada su Faruk suna game domin ranar babu islamiyya, daga ita sai pink din vest da short trouser iya gwiwa, wannan karon ma ko arzikin kallo bai samuba bare sannu da zuwa, bayan ya huta kitchen ya shiga yayi girki,yana kokarin fita bayan ya dora girkin ita kuma tana kokarin shiga, hannu yakai kan kirjinta azuciye ta doke hannunsa tana hararsa, wucewa yayi yana murmushi ita kuma tana harararsa,

Lokacin da yagama abincin tare ya zubo musu yazo inda take sake fakar idonta yayi yakaiwa kirjinta sumame hannunta tasa ta doke hannun nashi,

“Karka kara taba min kirji….” Tafada afusace,

“Haba halima nida halal dina….”

“Dole sai nawa zaka taba? Ita muslimar bata da nonon ne? Kaje ka taba nata….”

“Ko tana dashi ni ba nata nake so ba naki nake so….”

Rabuwa tayi dashi daga karshe ma tatashi tabar falon ta shige bedroom dinta ta kulle, bai sake ganinta ba sai dare nan dinma kitchen tafita taje daga haka shikenan sai washe gari, yana zaune afalo yana jira ta bude kofarta domin hado kayan wankinta, karfe 9 daidai tafito da rigar bacci tana ta faman hamma kitchen tawuce yabita da kallon sha’awa, bedroom dinta yashiga gaba daya ya tattaro kayanta masu datti wadanda tasaka yafita, ta kitchen din yabi yabude kofar baya ya bita, da harara ta rakashi cikin sa’a ya juyo ya gani,

“Wannan shine tukwicin da za abani kenan ko?”

Idan kofar dake wurin ta amsa masa to itama ta amsa haka ya karaci jan maganarshi yatafi batare da ta kulashi ba.

Har yayi weekend dinsa yagama babu wani canji a zamansu, ranar da zai tafi kuwa kishinne ya motsa nan ta rikice tafara yi masa masifar wallahi bazai tafi ba sai ya saketa, kallonta ya tsaya yi yanda ta tare bakin kofar da zai wuce,

“Halima kin kuwa san abinda kike fada?….babu kyau fa mace ta bude baki ta nemi miji ya saketa… Zunubi take daukarwa kanta….”

“Koma menene nidai ka sakeni, kaje ka zauna da wacce kakeso tun farkon rayuwarka, dadinta nima kuma inada mai sona, Abdul ko rannan da muka hadu dashi a hospital shine Dr din da ya dubani kuma har gobe yace yana sona dan haka ka sakeni kaci gaba da zama da matarka nima inje in auri Abdul mai sona…..”

Bata kai ga rufe bakinta ba taji ya warwara mata mari abinda bai taba faruwa ba a tsakaninsu,

“Anki a sakeki din, kina iya tafiya kije ki aureshi ahaka…. And this is the last warning wallahi idan kika kara kira min sunan wannan yaron sai ranki yayi mummunan baci….”

Daga haka ya figi jakarshi yayi waje yana huci kamar wani zaki yabarta durkushe wurin tana kuka,haka suka yi rabuwar bacin rai kowa zuciyarsa babu dadi musamman ma shi wanda yake bakin cikin marin da yayi mata akaron farko na rayuwarsu.

Tunda yatafi saida yayi kwana biyu sannan ya kirata, tana ganin wayar amma taki dauka, text massage kuwa sunfi goma duk na ban hakuri akan marin da yayi mata amma taki kulashi, har yayi sati daya da tafiya kullum sai ya kirata amma bata dauka haka text ko ya turo mata sai tayi biris dashi, wannan weekend din bata san meya hanashi zuwa ba domin har yakare shiru baizo ba. Ranar monday da safe misalin karfe 11 umma khairiyya tazo saida tafara zuwa sashen umma sannan suka tafi sashen halima itada su Faruk, zama tayi tana kallon halima cikeda mamaki,

“Ke baki koma abujan ba ashe? Ni kin san tunda muka koma maidugurin nan da Baban affan wallahi shikenan nadaina samunku….”

Kwalla ce ta cikowa halima ido,

“Umma khairiyya ni nabar yaya Aliyu har abada, nabar mata shi taje ta dafashi ta cinye amma nidai bazan kara rayuwar aure dashi ba….”

Salati khairiyya ta rafka sannan cikeda takaici ta kalli halima,

“Sadiya amma kin bani kunya wallahi…., akan kawai yayi aure shine zaki kaurace masa kibarwa wata mijinki? Gaskiya kina nema ki tafka babban kuskure, Aliyu fa yana sonki wannan auren ki daukeshi a matsayin wata kaddara, ki rungumi mijinki ki manta da maganar kishiya ta hakane kawai zaki dawo da martabar sonki acikin zuciyarsa amma wallahi wannan ba mafita bace,wannan abun da mata mukeyi muna ganin kamar hakanne zaisa mazajenmu su fifita mu ko Sufi sonmu fiyeda amaryar wallahi shine kesawa mu fita aransu, yanzu da yazo kinyi banza da shi kinata fushi wai ke kishi to karfa ki manta yanzu ku biyune, ada idan kina yi masa abu yana binki yana baki hakuri tofa yanzu zai iya shareki shima domin yanada wacce zata huce masa takaici, yawancin mata suke jawowa kansu matsala ayayin da miji ya kara aure yagama kwanakin amarya ya dawo dakinki maimakon ki tareshi da farin ciki da soyayya da kauna ki nuna kinyi missing dinsa a’a sai wai ki hau fushi tun yana shan kanki yana baki hakuri har shima yagaji yai watsi dake domin yanzu bake kadai bace yanada wacce idan yaje ransa abace zata tarairayeshi ta tattalashi sannan ta kula dashi to yawanci kuskuren da mata keyi kenan wallahi daga karshe sai kiga mijin ya daina ji dake yadaina gudun bacin ranki idan kina fushi bai damuba bare ya lallabaki sai dai kiyi ki gaji dan kanki ki sauko ita kuma amarya duk lokacin da ta fuskanci kin bata masa saita jashi ajiki ta lallabashi daga karshe sai kiji mata taje tana cewa amarya tazo ta rabata da mijinta suna zamansu lafiya yana sonta amma yanzu amarya ta kwaceshi tasa yadaina sonta, to wallahi duk wannan shine ke jawo hakan ba komai ba amma da lokacin da ya dawo miki kin karbeshi hannu bibbiyu kin danne zuciyarki kin faranta masa to wallahi darajarki da kimarki saita karu a idonsa sannan kecefa sirrinsa kin san mijinki fiyeda uwar da ta haifeshi to menene abin damuwa? Duk matar da zata sanshi bayanki fa zata bi, wata matar wallahi harta mutu bazata san abinda ke kika saniba game dashi tunda kece matarsa ta farko, kiduba kigani ko acikin iyaye da kakannu akwai wanda zakiga yanada mata uku ko hudu amma ba ataba jin kansa da uwar gidansa ba kuma kowacce mace agidan tana girmamata da gudun fushinta sannan itace star to duk ba komai bane ke kawo haka ba face iya rike miji,ko ku nawane awurin miji mutukar zakiyi respecting kanki wallahi dolensa shima yai respecting dinki shida matansa….”

Sosai khairiyya tabata shawarwarin da suka kamata kuma suka dace da ita, har dare suna tare sai bayan sallar isha baban affan yazo ya dauketa suka tafi, tabbas ta dauki shawarar da khairiyya ta bata kuma ta daura aniyar aiki da ita, acikin daren ta fara bawa kanta agajin gaggawa ta hanyar hada kayan da zasu saukar mata da ni’ima cikin gaggawa, washe gari da safe ta tafi gidan ya kurah kanwar ya ganah wacce ta gyarata lokacin aurenta, gyaran jiki tayi mata sosai sannan ta hada mata duk abubuwan da suka dace, kullum safe da yamma take zuwa gyaran jikin har na tsawon kwana hudu, akwana na biyar dinne akayi mata jan lalle da kitso kanana, washe gari da safe ta shiga tayiwa su umma sallama wai Abuja zata tafi, da driver Abba ya hadata acikin sabuwar motarta suka tafi.

Misalin karfe 2 na rana suka isa Abuja karbar tukin tayi takai driver tasha yahau mota ita kuma tawuce gida, wata iska take ji tana shigarta domin fa tazo da shirin buga rashin mutunci domin sai ta nunawa muslima kuskurenta na aurar mata miji da tayi,

A tsakiyar gidan tayi parking ta fito muslima dake zaune a falonta duk tunaninta Aliyu ne mikewa tayi ta leka ta window nan gabanta ya fadi sakamakon hango wata balarabiyar mata da tayi duk da bata hango fuskarta sannan bata taba ganinta ba, jakar kayanta ta ja ta nufi part dinta, akan idon muslima ta bude kofar tashiga ta turo kofa,

Tana shiga mamaki ya cikata domin komai nata ansauya shi ansaka sabo kalar fentin da akayi mata sannan ga kyawawan akwatina nan set biyar sabbi fil na fadar kishiya, wanka ta shiga batare da ta zauna ba, Aliyu da shima dawowarsa kenan yana shigowa yaga motarta wacce Abba yabata anan yagane tazo, gabanshi nata dar dar yawuce part dinta ko part din muslima bai leka ba, shigarsa bedroom dinta yayi daidai da fitowarta daure da towel, fuskarta babu yabo babu fallasa tazauna bakin gado,

“Sannu da zuwa….” Tafada adakile kamar wacce aka tilasta,

Wani dadi yaji hakan yabashi kwarin gwiwar karasawa kusa da ita ya zauna jikinsa cikin nata,

“Yawwa one love…, kinsha hanya sannu da zuwa, waye ya kawo ki?”

“Driver…” Tafada atakaice domin har lokacin fa kishin na nan akasan ranta yana sokarta,

“Sannunki da hanya to…. Me zakici inje in samo miki?”

Kawar da kanta tayi kafin ta amsa masa,

“Shinkafa kowacce iri, duk wacce ka samo”

Da rawar jiki yatashi yafita, shiryawa tayi cikin doguwar riga ja tayi kwalliya tafita falo, bata wani jima da zama ba sai gashi yadawo dauke da ledojin take away mai tambarin Rahusa restaurant, ajiye mata yayi agabanta nan ta sauko ta bude, banda jalop rice din da ya siyo mata mai dauke da rabin kaza harda snacks, yana zaune taci ta koshi nan ya dauki sauran yaci duk da ba wata hira sukeyi ba amma yakasa tafiya saida yaji ana kiran sallar la’asar sannan yafita sai lokacin ya tuna da muslima na cikin gidan amma da harga Allah ya manta da ita, part dinta yashiga ya dubata agurguje yafita.

Bayan sallar magrib yadawo gidan bayan yabiya ya siyo mata abincin da zata ci da daddare, part din muslima yashiga yace tazo suje su gaisa da halima bata musaba tasa hijabinta ta bishi,

Tana kwance afalo daga ita sai bakin wando tied iya cinya da pink din riga mai karamin hannu wacce ko cibiyarta bata kaiba banda budadden kirji da rigar keda shi domin kana iya hango halittar kirjinta kaf, gama aikinta kenan na goggoge dakunanta da falo shine ta kwanta tana hutawa,

Jin sallamarsu yasa ta daga ido ta kallesu ganinsu yasata mikewa tawuce bedroom taje tayi kwanciyarta, ganin shiru shiru bata fito ba yasa Aliyu tashi yabita……

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI….!*🤴🏻

 

_*NA*_

_*UMMI A’ISHA*_

 

_Afuwan masoya kuyi hakuri da jina shiru da kuka yi hakan yafaru ne sakamakon rashin da akayi min da fatan zaku karbi uzurina._

 

*59*

 

***Hawaye ne ke kwaranya daga idonta suna sauka saman kuncinta, ahankali ya dago da kanta ganin abinda ke faruwa ya bashi mamaki mutuka, da sannu sannu ya shiga share mata hawayen yana kallonta,

“Wai dagaske kike yi…….?”

Kai ta daga masa,

“Wallahi dagaske Darling brother nayi mafarki na haihu har yara guda biyu sannan ka yimin kishiya da tsohuwar budurwarka……”

Jin abinda tace yasashi bude baki alamun mamaki,

“Wai wai…..cewa zakiyi mafarkin naki mai yawa ne….”

“Nidai wallahi banso ka tashe ni ba saboda dadin mafarkin….. Amma fa lokacin da kayi min kishiyar ko…..”

“Badai mutuwa kikayi ba domin jiya jiyan nan kika gama fada min cewar duk ranar da nayi miki kishiya mutuwa zakiyi”

“A’a ni ban mutuba kawai dai inata kuka sannan bana yi maka magana amma fa kullum cikin kuka nake….kuma mutane ma duk haushinka suke ji wai kayi min kishiya”

Hannunta ya hade ya matse cikin nashi,

“Ai mafarkin kuka alkhairi ne…. Amma kuma mafarkin kishiya da kika yi ta yuyu Allah yana son fahimtar dake wani abune dangane da zafin kishin da kike dashi….lallai ke yar gatace tunda har tayaki kishin mutane keyi”

Kallonshi tayi idonta cikin nashi,

“Yaya Ali wallahi nadaina….ai acikin mafarkin ma zaman lafiya mukayi da ita…. Nadaina kishi daga yau, idan kana son kara aure kawai ka karo may be ma amaryar ta haifa maka yaya”

Tausayinta yaji saboda jin abinda tafada ya tabbatar zuciyarta na cikin wani hali shiyasa yayi azamar fara rarrashinta,

“To ni kara auren me zanyi bayan gashi kinyi mana mafarki mun haihu, very soon mafarkinki zai zama gaskiya da yardar Allah……,kuma da kike maganar inkawo wata ke kuma inyi yaya dake? Kefa harija ce 24 hours kike yi a online…..”

Jin abinda yace tayi tsalle ta fada kanshi babu bata lokaci suka fara tumurmusa juna, duk ta yamutsa masa boyel din dake jikinsa,

“Wai nikam bakya jin yunwa ne? Gashi bakiyi wanka ba kuma kina al’ada”

Turo baki tayi tana kwance akansa,

“To ba kaine ba….”

“To ai najanye kalamai na nace nine harajin bake ba…”

Dagashi tayi tana kallonsa,

“Ina zakaje naga kayi kyau haka?”

“Ba kince kinyi mafarki na auro muslima ba? To dama jiya na hadu da ita a makaranta wai babanta bashida lafiya shine zamuje asibiti mu dubashi nida Malam….”

“Allah yabashi lafiya, saika sake wasu kayan nidai nashiga wanka”

Daga haka ta fada cikin bathroom, duk da haka bai tafiba sai da ya jirata tafito, tana daure da pink din towel iya cinya, kawai tunanin mafarkin da tayine keta kai komo a kwakwalwarta, yana zaune gefen gado yana kokarin daura agogo taje ta dare cinyarshi,yamutsa fuska yayi cikeda tsokana ya kalleta,

“Ke nikuma da zan tafi zance ya kike kokarin bata min kayana?”

Kiss ta manna masa a kumatu ta tashi ta nufi gaban dressing mirror,

“To ya Ali Allah ya kiyaye hanya agaidata….. Ni ai ba hanaka zanyi ba”

Murmushi yayi ya mike tsaye suna kallon juna ta cikin mirror din,

“Nidai da wasa nake kar sai natafi ki hada kai da gwiwa kiyita kuka”

Dariya tayi tana kallonshi tana shafe hannayenta da mai,

“Da kenan wallahi….”

“Kamar gaske” yafada bayan ya gyara tsayuwarshi yana kallonta,

“Kwarai kuwa” tabashi amsa tana kokarin sauke towel din, kasa dauke idonshi yayi daga kanta bare har ta kaishi ga tafiya, matsawa yayi ya tsaya abayanta ya karbe lotion din,

“Kawo kiga inshafa miki….”

“Ka shafa min mai ko dai kayi barna?”

Daga shi har ita dariya sukayi,

“Ashe kema kin sani”

Dakyar ta samu ta shirya cikin blue din leshi saboda yunwa take masifar ji, potatoes and egg plan taga yayi musu sai kidney sos nan ta ciko plate taje ta zauna kan cinyarshi, duk da yana bata hakan bai sata kin bawa kanta ba, babu bata lokaci ta cinye har da neman kari, sauran taje ta kwaso ta dawo shi dai kallonta yake yana mamakin irin wannan cin da take kamar ba acikinta take durawa ba,

Saida yajirata ta gama sannan ya mike da ita ajikinsa,

“Bari naji ko kin kara nauyi yau?”

Wuyanshi ta sakale da hannuwanta,

“Babu nauyin da na kara Darling brother…..”

“To ai yau dinne naga kin ci abinci da yawa ko dan baba ke haramar zuwa?”

Murmushi tayi ta kwantar da kanta bisa kirjinshi,

“Da hakan zata kasance wallahi zan fika farin ciki”

“Har kin gaji da amarcin kenan?”

“Kajika, wanne amarci kuma? Nidai na dade da gama wani amarci”

“To shikenan insha Allah kina daf da kamuwa….”

“Bansa rai ba….”

Jin abinda tafada kuma sai yasa yaji duk tausayinta ya dirar masa,

“Haba halima itafa haihuwa da kike gani itama lokaci gareta kamar yadda mutuwa keda nata lokacin…. Ki sawa ranki zamu haihu nan bada jimawa ba”

Murmushi tayi ta shafi gemunsa,

“To Allah yabamu masu albarka..”

“Amin sannan kuma masu yawa kamar 20 haka”

Ido ta zaro, “awanne cikin?”

“Wannan cikin mana”

Hannunta ta dora kan nashi wanda yake shafa cikinta dashi,

“Taya zamu haifi yara har 20 bayan mun dade muna…..” Rada tayi mishi akunne, jin abinda tace yasa shi yin dariya,

“To ai da akwai saura da yawa…”

A balcony ya sauketa domin tare zasu fita zata leka su umma,

“Allah ya kiyaye hanya idan za adawo ataho min da abun dadi”

Kiss din da ta bashi a kumatu ya mayar mata da martani bisa lebenta,

“To shikenan sai nadawo, i love you”

“I luv you too sweet Darling”

Sakin hannunta yayi yawuce ita kuma ta nufi part din umma, tun daga balcony din umman take jiyo hayaniyarsu faruk suna yin tv game kamar karamar yarinya haka taje ta karbi na sadiq suka cigaba da yi itada Faruk nan ta shantake har 2 da rabi saida taga karfe uku na neman yi sannan ta tafi sashensu dauke da dan waken da umma tayi. Wanka tafara yi ta shirya sannan ta zuba rabin dan waken taci tabarwa Aliyu rabin, kitchen ta shiga ta dora abinci faten doya da danyen kifi, bata kai ga gamawa ba Aliyu ya dawo, ko zancen muslima bata yi masa ba taci gaba da harkokinta, tare suka karasa abincin tanata yimasa shagwaba daga karshe saida ya goyata sannan tabarshi ya tafi masallaci.

Kamar yadda suka saba ranar Monday suka koma Abuja Aliyu yaci gaba da zuwa aikinshi, kullum halima saita bishi office ta kai mishi abincin rana domin idan aiki yayi musu yawa baya zuwa yaci abinci shiyasa take kai masa har can dayawa daga cikin abokan aikin nashi wadanda basu santa ba zatonsu budurwarshi ce domin kullum idan tazo sai sunyi hira a office ko aiki ta tarar yana yi na duba mota sai taje yanayi suna hira sannan bayan yaci abincin sai ya rakata har motarta sannan asake sabuwar hira sai kuma ayi sallama tatafi cikeda kaunar juna tamkar baza arabu ba. Yauma kamar kullum bayan ta gama dafa masa tuwon amala da miyar shuwaka ta zuba a basket, jikinta ta nade da laffaya sannan ta fita, lokacin da ta karasa companyn nasu yana gareji shida sauran yaransa suna aikin wata sabuwar mota wacce suke daura mata notina da tayoyi, abayan Aliyu ta tsaya bayan ta dafashi,

“Barka da aiki Yallabai….”

Murmushi yayi batare da ya juyo ba,

“Ranki yadade da tsakar ranar nan kike tafe? Ai da kin hutawarki kawai ni kince inzo”

“To ai nasan ko nace kazo ba zuwa zakayi ba….”

Jin zata fara yi masa shagwabar tata yasashi barin aikin yace yaransa suci gaba, yana gaba tana binshi abaya zuwa office dinshi, daidai kofar office din ya tsaya ya karata da jikinsa harda shafar kumatunta da hannunshi mai dattin baki, ahaka suka shiga office din yana rikeda ita domin harga Allah yamanta da yarinyar dake zaune aciki wadda itace wacce ake hadawa wannan sabuwar motar,yarinyar na zaune saman kujera acikin jerin kujerun baki dake gefe daya cikin office din nashi, gaida halima yarinyar tayi fuska asake halima ta amsa abinda yabawa Aliyu mamaki domin yasan da adane da tuni tahau fushi, janta bathroom yayi domin ta wanke masa hannunshi tana wanke masa kamar ance ta kalli mirror nan taga bakin da ya goga mata ruwa ta watsa mata afuska tana cewa,

“Shine ka shafa min baki afuska ko?”

“Powder fa nashafa miki…”

Daga shi har ita dariya suke, saida ta sakashi agaba taga yaci abincin sannan ta tafi.

Haka rayuwar taci gaba da juyawa tana wucewa, cikin yan kwanakin nan dai halima bata rabo da bacci ga shegen cin abinci kamar gara shiyasa babu bata lokaci ta hau ta sake zama yar lukuta ga uban farin da tayi jajur duk Aliyu na kula da ita saboda ko abinci zata ci sai tasa shi ya nemo mata tsire taci dashi, acikin satin suka tafi weekend Zaria tunda sukaje halima taki cin komai sai awara shi Aliyu abinma dariya yake bashi domin ko ba soyayyiya ba cin kayarta takeyi ahaka, yanzun ma da yake shiryawa tana falo tana cin awarar da miyar kwai, kayanshi yasa ya nufi wurinta kanshi babu hula, akusa da ita ya zauna yana kallonta domin lokacin da ya shiga wanka yaga tsinken gwajin ciki har guda hudu acikin dustbin din dake cikin bathroom din alamun tayi gwaji,

“Kin koshi kuwa…?”

“Nakusa dai, dan Allah idan ka fita ka taho min da wata amma mai dumi sosai”

Murmushi yayi ya zubawa kirjinta ido kamar zai cinyeta,

“Baby are you pregnant….?”

Kallonshi tayi taja dan kwali ta rufe kirjinta domin daga ita sai bra da dogon wando,

“Me ka gani wai?”

Murmushi ya sake yi,

“Naga abubuwa da yawa”

“Kamar wanne da wanne?”

“Kinfi da kyau yanzu, sannan yanzu kina satisfying dina fiyeda da and kuma kinga kin kara cika ta nan da nan……and when last kikayi period dinki ne? Kamar fa tun last 2 months har yau baki kara yiba”

Kurawa juna ido sukayi na yan mintuna, kawai ji yayi ta rungumeshi kamar abin hadin baki dukkaninsu kwalla suke fitarwa tana ji hawayenshi na sauka akan fuskarta, sun jima ahaka babu mai rarrashim wani zuwa can yayi ta maza ya dago kanta,hannunshi yasa yana share mata hawaye bayan ya share nasa,

“To ke menene abin kuka keda abin farin ciki ya samemu?”

Kallonshi tayi da jajayen idanuwanta,

“Kaima fa kukan kakeyi ya Ali…..”

Jijjiga mata kai yayi, “Ni ba kuka nake yi ba….., addu’a nake yi mana Allah ya bamu yara masu albarka da tsoron Allah”

Dauke idonta tayi daga kanshi tana matse kwalla, ganin taki dainawa yasashi jan hancinta yana murmushi,

“Nan da yan watanni zaki fara haka…….”

Yanda ya rike kugu yaturo ciki gaba shine yabata dariya har takai masa duka akafada tana murmushi, hannunta ya rike yakai nasa saman cikinta yasoma shafawa,

“Allah mai iko…. Wai yanzu da ajiyata anan…., Allah ya baki lafiya Sadiya nah”

Kanta ta dora kan kafadarshi ta rungumeshi, fitar da baiyi ba kenan suka shantake sai aikin shafar cikinta yake kamar wanda yake neman wani abu, can dai ya daure ya dagota,

“Taso muje mu fadawa su umma….”

Hijabinta ta dauka tana zumbura baki bayan ta zira doguwar riga,

“Nidai gaskiya kunya nake ji….”

“Daga baya kenan”

Da haka suka fita suka nufi sashen ummi, tana zaune itada dasu Faruk, zama suma sukayi bayan sun gaisa kowannensu sai kuma yayi shiru,duk zumudin da yake na yazo ya sanarwa Ummi sai ya kasa shiru yayi yanata fara’a amma yau yarasa hujjarshi ta jin nauyin ummi domin ada baya boye mata komai amma yau gashi yarasa ta inda zai bullowa maganar cikin da halima ke dauke dashi, haka suka karaci zamansu suka tashi dan zuwa wurin umma yanata son ya fadawa ummi amma yakasa haka suka fito kowa bakinsa gum basu fada ba, rikeshi halima tayi tana dariya,

“Ya Ali dama kana da kunya? Wlhi sai yau na yarda”

Dariyar shima yayi ya kalleta,

“Nafiki kunya fa…. Tom dan dai babu kyau ne bari inyi shiru”

“A’a wallahi……,kama fada dai”

“Ai kin bani hakuri kince kar infada”

Dariya sukayi atare, gurin umman ma basu iya fada ba daga karshe ma tafiya yayi yabarta yawuce masallaci sai bayan ya dawo suka fita siyan awarar, cikin flask ya siyo mata mai zafin gaske shiyasa tun acikin mota tafara ci tana yiwa Sabira waya akan ta yi mata kafi tsire mai kifi, shi dai jinta yake yana tukinshi. Daren ranar baiyi bacci ba sallah ya kwana yana yi yana mika godiyarsa ga ubangiji washe gari kuma yatashi da azumi sannan lokacin da yafita saida yayi sadaka sosai, daurewa tayi ta hada masa kayan shan ruwa duk da bata jin karfin jikinta. Tunda yafara azumin bai tsayaba kullum sai yayi, yauma da azumin ya tashi gashi yagama mayar da halima yar gata, baya barinta tayi aikin komai sai shine yakeyi hatta abinci shine yake dafa mata ita sai dai taci ta kwanta, daga wanka ta fito ta iskeshi yana shirya mata kayanta cikin wardrobe, zama tayi gefen gado tana goge kunnenta da gefen towel din jikinta,

“Darling brother cewa nayi ya maganar kaini gidan lallen…?”

“Ki shirya idan kika ci abinci sai muje amma ina so mu fara zuwa asibiti adubaki”

Murmushi tayi tana tsane jikinta,

“Nifa lafiyata kalau, badai yau ma azumin kakeyi ba?”

“Azumi nakeyi mana..”

“Kai dan Allah, wai har guda nawa zakayi azumin ne? Tunfa muna Zaria kafara”

“Yi hakuri daga yau nagama bazan karaba shikenan?”

Kai ta daga masa, kusan atare suka shirya yabata abinci taci suka fita, wani private hospital ya kaita aka dubata tareda yi mata test, cikinta watanni uku babu kadan, daga shi har ita bakinsu yaki rufuwa, har yakaita gidan kunshin basu bar maganar cikinba.

Wannan satin basu je Zaria ba domin baya son ta wahala da zaman mota, kasancewar yau weekend suna zaune falo tana kwance ajikinsa suna kallo wayarshi ta soma amo, dauka yayi ya kara a kunnensa,ahankali ya sauke idonshi akan fuskar halima gabanshi na faman faduwa……

 

*_Ummi Shatu_*👌🏻
© *HASKE WRITERS ASSO.*
_(Home of expert & perfect writers)_

 

*D’AN ASALI….!*🤴🏻

 

_*NA*_

*_UMMI A’ISHA_*

 

*60*

 

***Domin bazai taba iya mance mamallakiyar muryar ba,shiru yayi ya gagara amsawa har saida ta maimaita maganar sau biyu,

“Lafiya naga ban ganka ba wannan satin?…. ”

“Lafiya lau inada dan uzurine shiyasa…”

Ya amsa mata idonshi akan halima bai kara magana ba yakatse wayar yana shafar gashin halima wanda yasha gyara,

“Sorry my heart….. Wai… Wai… Muslima ce take tambayar ko lafiya bata ganni ba”

Murmushi halima tayi tana wasa da zoben azurfar dake hannunshi,

“Shine baka fada mata gaskiya ba? Ai da sai kace babynka kake bawa kulawa baka son wani abu ya sameshi…”

“Banda lokacin yin wannan dogon bayanin ranki ya dade…”

“First love din naka kake fadawa haka? Lallai ya Ali…. Muslima ce fa wadda karinka jinya akanta kamar zaka mutu….” Ta karashe maganar tana yimasa dariya, pillow ya dauko daga saman kujera yasoma kai mata duka, rirrikeshi tayi tana dariya,

“Dan Allah bari… Daga fadin gaskiya?”

“Ni ban san zancen ba….”

“Gaskiya baici ace ka manta da first love dinka haka ba……”

Tureta yayi ya kwanta,bayan ya toshe kunnuwanshi da hannayenshi,

“Ni bacci zanyi kyaleni….”

Sake kankameshi tayi tana yi masa magana a kunne da karfi,

“Haba na muslima bude kunnenka kaji mana….”

Janyota yayi yana fadin,

“To zo ki fada min din inji… Dama ankwana biyu ana yimin rowa gara yau in fanshe bashina….”

Dariya tayi tana tureshi,

“Ni dai gaskiya a’a…”

“Ai baki isaba yarinya…”

Har yamma suna gida sai karfe 5 suka fita domin zaman duk sai suke jinsa wani iri domin basu saba weekend anan ba sunfi yi a Zaria.

Haka suka cigaba zama a Abuja basu je weekend ba har saida suka yi watanni biyu lokacin ne suka shirya suka tafi,cikin halima har yafara fitowa kadan, gaba daya kunyar su umma take ji saboda zasu ganta da ciki,

Tun ahanya muslima ke yimasa waya taji ko sun taho yanata kin amsawa daga karshe dai ya dauka, shi yarasa ma tayanda akayi ta samu number dinshi. Lokacin da suka karasa gida kallo daya baba tabawa tayiwa halima ta fahimci tana dauke da juna biyu amma daga Ummi har umma basu ganeba domin halima sai faman barbaza mayafinta takeyi tana turashi gaba,

Suna part din umma dukkansu suna cin dan wake baba tabawa ta shigo dauke da jug wanda aka hada juice aciki, tsiyaya halima tayi tana kallon baba tabawa,

“Baba tabawa ya babu sanyi sosai? Dan Allah asaka mana kankara aciki yakara sanyi…”

“Haba uwar dakina ai yanzu kuma sai ki dan rage shan sanyi da cin zaki ko dan saboda abinda ke cikinki….”

Sunkuyar da kai halima tayi tana cewa,

“Baba tabawa nifa banida komai…”

Dariya Aliyu keyi kasa kasa kansa asunkuye yana zaune kusa da ummi,

“Haba yar nan ai duk wanda yaganki yasan kina dauke da ciki, dan Allah ki rage shan ruwan sanyin nan dai….” Inji baba tabawa, shiru halima tayi tana jin umma da baba tabawan nata mita akan shan sanyin da takeyi ummi ce dai batayi magana ba ana kara kasancewar Aliyu dan fari.

Dakyar ta iya tashi dan komawa sashensu cikeda kunya bayan sun gama cin abincin, tana shiga falo Aliyu na shigowa shima zama yayi saman kujera yana kallonta,

“Duk boye boyen mutum dai sai da aka gane…”

“To agane din mana,ai dai ansan ba aruwa nasha ba”

Dariya ce ta subuce masa batare da ya shirya ba,

“To zo ki fada min ame kika sha?”

“A lemo…”

Dariya yasake yi yakoma ya kwanta jikin kujerar,

“Lallai kinji dadi”

“Yanzu nidai wanka zanyi zo muje ka tayani”

“Ai ko baki roka ba sweety, dole muje inyiwa baby na wanka”

Tare sukaje har cikin bathroom din tayi wankan tafito yana biye da ita, kayan da zata saka ya fito mata dasu tana gaban madubi tana shiryawa, da taimakonshi ta shirya tsaf sai badada kamshi take. Tunda su umma suka fahimci tana da ciki shikenan suka hanata aikin komai dama kuma bayi takeba Aliyu ke yimata, kullum sai baba tabawa tazo ta tambayeta abinda zata ci sannan adafa akai mata,gata da kulawa kam tana ganinshi awurin kowa na gidan musamman ma uban gayya Aliyu, Abba kuwa lokacin da yaji albishir din da umma tayi masa na cikin dake jikin halima har sashensu ya shiga yayi mata sannu da addu’ar rabuwa da cikin lafiya. Aranar da suka zo yaje wurin muslima domin jin ba’asin kiran da taketa yimasa nan take shaida masa batun aurensu da mal salahu daya daga cikin malaman makarantarsa, fatan alkhairi yayi da alkawarin yimata gado saboda satin sama za adaura Auren.

Kwanansu uku suka koma da dafarko ummi tace yabarta anan shi yakoma shi kadai amma sai ta fahimci itama haliman tafi son tabi mijinta wannan dalilinne yasa bata matsa ba tabarsu yasake komawa da ita, suna hanya yana tuki tana makale a barin jikinsa kanta bisa kafadarshi,

“Ummi bata san yanda kike da son jikiba yanzu shiyasa har take cewa intafi inbarki”

“Kajika…. Ba Kaine ka koya min ba, Allah awurinka na koya”

“To naji, amma da ace na tafi nabarki ya za ayi?”

“Da zan biyo ka daga baya dan wallahi nasan bazan rinka iya bacci ba…”

“Baza mu iya bacci ba zakice dan bake kadai ba harda ni”

“To ai har gara kai ya Ali”

“Babu wani gara malama, ni wallahi da ahanani kwana tare dake gara an hanani abinci domin zan iya jure yunwa amma bazan taba iya jure rashinki ba….”

Murmushi tayi ta daga kai ta kalleshi sannan ta sake mayar da kanta kafadarshi,

“Su Darling brother ba sauki”

“Babu kam indai akanki ne”

Dariya tayi tana muskutawa domin gyara zamanta. Haka suka rinka ririta juna suna bawa juna kulawa Aliyu ko ya fita aiki baya mintuna talatin batare da ya jirata yaji lafiyarta ba, yau kuwa da ya kirata yaji bata dauka ba hankalinshi kasa kwanciya yayi dan haka baiyi wata wata ba ya nufo gida yana zuwa ya sameta afalo tana baccin nata da ta saba ko pillow babu akasan carpert wayarma bata kusa da ita tana can bedroom dinta lokacin da yashiga dauko mata pillow yaganta, saka mata pillow din yayi ya gyara mata kwanciyar sannan ya koma aikinsa sai lokacin yaji ya samu nutsuwa.

Cikin halima ahalin yanzu ya fito sosai domin ya fara girma dan watanshi shida, daga khairiyya har Sabira basu san cewar tana da cikinba sai a wannan zuwan da tayi shine taje musu dariya Sabira ta rinka yi tana cemata ai kuwa cikin yayi mata kyau sosai lallai Aliyu ya iya ajiya, rabuwa da ita halima tayi tana dariya domin daga sabiran har khairiyyan tsohon ciki garesu haihuwa ko yau ko gobe.

Tun daga wannan lokacin da suka koma abuja Aliyu bai kara bari sun dawo Zaria ba har saida khairiyya ta haihu wannan dinma dakyar ya yarda ana igobe suna suka tafi domin halima tayi nauyi sosai yanzu, da ita aka sha shagalin sunan yar khairiyya wadda aka saka mata Ni’ima, hanjin da aka soya kuwa sakashi agaba halima tayi tana ci saida tayi nak Sabira sai tsokanarta take tana cewa taci bashi tunda itama tana kan hanya, har dare tana gidan suna sai bayan sallar isha yazo ya dauketa, kallonshi tayi ganin yasha ado yanata kamshi,

“Daga ina kake ne?”

“Daga gida mana, ko kin aikeni wani wurinne?”

“A’a ni na isa…”

“Har kinfi ranki ya dade”

“To ai naganka ne kayi gayu kasha kyau”

“Ke nayiwa ai madam…”

“To nagode, kayi kyau sosai”

“Nifa ba godiya nake so ba, tukwici zaki bani…”

“Na me?” Ta tambaya tana zaro ido,

“Kar idon ya fito…, da zaki kyauta idan muka je gida….. ”

“Gaskiya Darling brother…. Wallahi wahalar dani zaka yi kawai, shekaran jiyama fa haka ka bani wahala..”

” Allah gata nake miki…”

Jin abinda yace yasata yin shiru bata kara magana ba, awurin mai balangu ya tsaya ya siya musu,labarin naman da taci agidan suna ta shiga bashi yana dariya yana cewa gaskiyar sabirane bashi taci kam da haka suka karasa gida. Saida aka gama hidimar khairiyya tsaf sannan suka soma haramar tafiya ana igobe zasu tafi Sabira ta haihu nan fa tace tafasa tafiya dakyar ya lallabata suka tafi bayan sunje asibiti sun dubata ita da babyn yace zasu dawo ana igobe suna.

Tunda cikin halima ya tsufa Aliyu ya maida hankali wurin bata ruwan addu’a tana sha da dabino, kullum safe da yamma sai yabata domin samun sassaukar nakuda, wani fresh tayi lokacin duk da cikin dake jikinta gashi baya daga mata kafa indai a fannin bukatarsa ne shiyasa wani sa’ilin sai sunyi fada dashi suke daidaitawa yauma da la’asar sakaliya yasata agaba da neman magana, yunkurawa tayi ta tashi zaune,

“Ya Ali, idan kana kaunar Allah ka rabu dani inhuta…”

“To naji zan barki amma nikuma tawa bukatar inyi yaya da ita?”

“Kayi aure…. Ni wallahi ka kara aure”

Dariya tabashi nan yayi mai isarshi yana kallonta,

“Wato harma kin fara gajiya dani kenan ko?”

“Ni ba gajiya nayi dakai ba Darling brother”

“To yaya ne….?”

“Ni wallahi bana sone….”

“Baki so zaman lafiya ba to”

Buntsuro baki tayi tana harararshi.

Zama tayi asaman gado ta janyo wani dan madaidaicin akwati pink colour tasoma duba kayan ciki,

Aliyu ne yashigo yana kokarin cire rigar jikinshi, zama yayi kusa da ita yasaka hannunshi cikin akwatin dake gabanta, mamakine ya lullubeshi domin gaba daya kayan jarirai mata ne aciki harda su abun hannu da barima kala daban daban,

“Wannan kayan fa….?”

“Kayan baby nane mana ko baka ganiba”

Dariya yayi ya janyo wata hula blue mai kyau,

“Ke waya fada miki mace zaki Haifa?, keda zaki haifi namiji”

Harara ta watsa masa ta fara tattara kayanta,

“Ni daina taba min kayana Malam, ni mace zan haifa kuma…”

Matsawa jikinta yayi ya kanainayeta yana dariyar tsokana,

“Haba Maman Aslam… Baki son ki cika min burina? Sofa nake mafarkina ya zama gaskiya…”

Bata sake saurararshi ba ta harhada kayanta ta dauki akwatin taje ta ajiye a maboyarta, binta da kallo yayi yana murmushi domin ko kadan bai san da wannan akwatin ba baima san lokacin da take siya ba,kamo hannunta yayi,

“Haba maman baby…. Menene abin fushin ne? Mace zaki haifa ni wasa nake”

Sai lokacin tayi murmushi ta zauna saman cinyarshi,

“To ko kaifa yaya nah…”

Sosai ya sata nishadi sai fara’a take domin jin yana yimata addu’ar ta haifi ya mace,sun jima suna hutawa har yamma, da daddare suna tsaka da bacci yaji tana dan nishi sama sama dama tunda watan haihuwarta ya kama Aliyu baya bacci sosai, tashi yayi ya kunna wuta ganinta yayi tana cije lebe tana nishi, ganin yanda takeyi ya fahimci cewar haihuwar ce, riga ya kawo mata tasaka ta cire ta bacci tasa hijab ya taimaka mata suka fita, dakyar ya samu key din motarshi suka tafi asibiti, hankalinshi atashe yayi parking ya fito da ita nan aka shiga labour room da ita, da addu’a abakinshi ya rakasu da ido,cikin ikon Allah ko minti biyar ba ayiba da shiga da ita ta haifi yaronta katon gaske fari tass Aliyu yana waje yanata kaiwa da kawowa sai ga nurse tazo tayi masa albishir, dukkan kulawar da mai haihuwa ke bukata anbawa halima ita domin asibitin kudi ne, saida aka gama gyarasu tsaf itada jaririnta sannan Aliyu ya samu ganinsu, fadin irin farin cikin da yake ciki yau bata bakine domin daga halima har jaririn suna cikin koshin lafiya, shine yarinka zirga zirga wurin kawo duk abubuwan da ake bukata zuwa safiya aka sallamesu saida suka koma gida sannan ya kira su Abba ya fada musu, suna komawa ya hada mata ruwan zafi domin tayi wanka shi da kansa ya gasata suna yi suna kokawa daga karshe ya fita yabarta aciki ta karasa, Aslam yaje ya dauka wanda ke sanye cikin kayan sanyi blue and white, komai na yaron irin nashi ne banda launin fatarshi wannan kam yasan ko ba afada masa ba halima ya dauko tunda shi baki ne,

Aranar yayiwa jaririn huduba da sunan da yajima yana yiwa yaronsa tanadi, kafin 11 nasafe su umma suka karaso gaba dayansu harda baba tabawa wacce zata zauna domin yan aikace aikacen da ba arasa ba, Abba ne yafara daukar jaririn yasa masa albarka sannan umma ita kam ummi sai daga karshe ta daukeshi bayan su faruk sun gama kokawar daukarshi, cikeda farin ciki kowa yake domin babu wanda zaiga halima ya tsammaci itace ta haihu saboda dass da ita kuma rass tasha wankanta da kwalliyarta cikin doguwar riga, sai bayan sun jima da zuwa sannan Aliyu ya dawo daga companyn shi domin motocin da yayi order ankawo masa su ayau wannan dalilinne yasa yafita ba wai dan yaso ba, kowa sai san barka yake masa tareda addu’ar Allah ya raya, ummi kam cewa tayi gobe ko jibi sai su tattara gaba daya su tafi Zaria ayi suna acan inyaso bayan arba’in sai halima ta dawo, da kamar yayi shiru sai kuma yaga idan yayi shiru zai cutu dan haka yacewa Ummi a’a shi basai anje Zaria ba domin dama bashida ra’ayin yin taron suna, kallonsa halima tayi ta harareshi aranta tana cewa “me hali baya fasa halinsa…”,
Ummi nunawa tayi bata yarda ba amma Abba sai ya goyi bayan Aliyu yace tabarshi yayi yanda yake so tunda iyalinshi ce wannan dalilinne yasa ummi ta hakura tayi shiru. Aranar aka gyarawa Aliyu dakin kusa da na halima sannan suma su ummi suka gyara daya domin suna nan Abba ne kawai yatafi, Aliyu abin baiyi masa dadiba domin bai taba raba daki da halima ba sai wannan lokacin haka ya hakura saboda yana jin kunyar su umma, dakansa ya harhado dukkan kayan da yasan mai jego na bukata domin gyara kanta nan baba tabawa ta shiga kula masa da matar tasa tareda tallafin su umma, ana saura kwana biyu suna Sabira da khairiyya suka zo,dariya suka rinka yiwa halima domin idan zata bawa jaririn nono sai ta rufe jikinta ko ta gudu dakin Aliyu tabashi acan, haka akayi suna sulu domin babu wani taro da akayi amma duk da haka Aliyu yakashe kudi ba kadanba sannan ansha bushasha, bayan suna da kwana biyu su umma suka koma Zaria suka bar halima da baba tabawa dan tana kula da ita tareda sauran yan abubuwan da yadace irinsu yiwa jariri wanka da renonsa da kuma yiwa ita kanta haliman. Lokaci kankani tun kafin suyi arba’in sukayi bul bul dasu, satinsu uku yau da suna, tana sallar la’asar Aliyu yashigo bedroom dinta yana dauke da aslam ahannunshi,

“Wai dama kina salla shine baki sanar daniba?”

Shafa addu’ar da take tayi ta juya ta kalleshi,

“Tunfa sati biyu ya dauke….”

“Alhamdulillah… Cewa zakiyi banida matsala ashe”

“Akan me? Tab ina fama da kaina, gaskiya a’a”

“Lallai…., to abisa dukkan alamu baki san abinda me akhdari yafada ba ko acikin littafinsa?”

“Uhmm” tace dashi tana zama gefenshi,

“Cewa yayi ko aranar da mace ta haihu mutukar jini ya dauke mata to tayi salla tayi azumi sannan mijinta yaje mata”

Dariya tayi ta karbi aslam tasoma shayar dashi,

“To mudai sai munyi arba’in”

“Ai kuwa wasa kike wlhi”

Ita duk atunaninta dawasa yake ashe har zuciyarsa dagaske ne shiyasa ya kafa mata naci har saida ya cimma burinsa. Ko wata biyar aslam baiyi ba tafara laulayi haka tayita fama da raino da laulayi wanda ba karamin dadin hakan Aliyu yajiba,ahaka ta cigaba da rainon aslam tana hada masa da madara shiyasa sam bai rame ya lalace ba saima uban kiba da yake hadawa, yana wata tara yafara tafiya lokacin cikinta ya tsufa amma duk da haka bata yayeshi ba har saida watan haihuwarta ya kama lokacin ne Aliyu ya daukeshi ya kaishi Zaria wurin su ummi, ko sati biyu ba ayiba da yaye aslam din ta haihu wannan haihuwar ma cikin sauki da nasara ta zo mata kamar waccan kuma yanzun ma baby boy ta haifa mai kamada aslam fitik, kamar wancan karon wannan haihuwar ma Aliyu yayi bajinta sosai ranar suna yaro yaci Asif,da baba tabawa da wata yarinya Umma ta samo mata domin su zauna tare da ita tunda shi Aliyu baya bari taje Zaria wanka, aslam kuwa fur yaki zama a abuja sai Zaria yasake bin su umma,Kamar amafarki wannan karonma halima tun kafin tayi arba’in ta samu wani cikin, duk da tana kaunar haihuwar ji tayi tafara tsoron Aliyu domin taga kamar baiwarshi anan take, yanda tayiwa aslam haka tayiwa Asif saida ta kusa haihuwa sannan ta yaye shi, tun daga nan kuma haka ta rinka jera haihuwa babu hutu tana haihuwar wannan zata dauki cikin wani da haka saida ta haifi yara shida duk maza, kai idan kagansu zaka zaci yan biyune domin kowanne kansu daya shida mai bi masa Aslam da Asif komansu daya haka Bilal da Ashraf, Ahmad da Sahal suma kansu daya ko kayane iri daya ake siya musu, gashi duk haihuwar da zata yi sai ta lodo kayan mata sai kuma ta haifi namiji yanzu haka da take dauke da ciki na wata bakwai siyayyar wasu kayan matan take kara yi,yauma daga asibiti wani boutique ta wuce ta iyo siyayya sannan ta dawo gida, gidan babu kowa sai ita kadai domin yaran duk suna Zaria kowa daga an kaishi yaye sai yaki dawowa yayi zamansa acan,tsakaninsu da yaransu sai dai idan anyi hutu su zo musu ko kuma su idan sunje Zaria su gansu, yanzu ne ma da Aliyu ya siya musu waya yasa musu sim sannan yake tura musu credit shine suke samun damar gaisawa da yaran duk da halima bata goyon bayan siyawa su aslam wayar da yayi domin babbar waya ya siya musu mai tsada amma yasa mata security babu abinda zasu iya yi da ita sai iya waya da games. tana zaune dirsham tana sake duba kayan data siyo ya fito daga bedroom da alama yatashi daga baccin da yakeyi domin ta barshi yana bacci sakamakon ciwon da kanshi keyi, zama yayi akan kujera yana fuskantarta,

“Wai har yanzu baki gama hada kayan nan ba? Ko kayan aure kike hadawa sai haka uwar biyu…”

“Uwar biyu ko uwar bakwai… Wai kamar almara nice da yara shida ga na bakwai zan haifa, nidai agama haihuwar nan haka”

“Keda ko rabi bakiyi ba, dozen fa nake so…”

Kayan ta soma mayarwa cikin leda,

“Ka karo aure sai amaryar tayi maka dozen din”

Dariya yayi ya mike akan kujera,

“Lokacin da bamu yi aure ba da nake fada miki duk shekara zaki rinka haihuwa jina kawai kike to yanzu fa?”

Yunkurawa tayi zata tashi ta kasa har saida yazo ya dagata,

“Nidai kaga tafiyata daki, ka shigo min da kayan ciki”

Saida yakaita har bedroom din sannan ya fito ya shigar mata da kayan.Wannan haihuwar halima ta danyi doguwar nakuda dan tafi awa uku daga bisani ta haifi yarta mace mai kamada ita sai yanzu ta samu wadda ta dauko kamanninta amma sauran duk kamannin Aliyu ne, sosai Aliyu yabata mamaki domin ranar suna halimatus Sadiya ya sakawa yarinyar suna kiranta da mima, bayan sunyi arba’in tarkatasu yayi gaba daya suka nufi kasa mai tsarki domin yin umarah harda su faruk duk suka tafi, satinsu biyu awata ranar juma’a bayan sun dawo daga masallaci suka bar yaran a masauki sukuma suka fita shopping, a kantin wani Balarabe suna siyayyar turaruka wata yar Nigeria ta shigo yin siyayya itama, kurawa Aliyu ido tayi tana murmushi shi sam bai ganta ba amma halima na sane da abinda ke faruwa, sun gama siyayyar suna kokarin fita matar takira Aliyu, koda ya juyo yaganta sai yamanta a inda ya taba ganin fuskarta, murmushi tayi tace,

“Karma ka wahalar da kanka, sunana Teenah wadda tayi alkawarin auranka mutukar tana numfashi….”

Tabbas yanzu ya tunata, duk da halima ta rage zazzafan kishi akanshi amma yau kam sai ahankali domin gabanta faduwa ya shiga yi kamar me, kama hannunta taji teenah tayi cikin tausassan lafazi tace,

“Nasan kece matarsa, na rokeki ki taimakeni kibar mijinki ya aureni…”

Duk da hajijiyar dake kokarin daukarta hakan bai hanata yin jarumtar kakaro murmushi ba sannan itama ta runtse hannun teenah cikin nata,

“Karki damu yar uwa indai tanine bakida matsala wallahi nayarda kuma na amince…”

Aliyu baiko sauraresu ba yayi gaba abinsa yana rike da memah a hannunshi, shi fushi ma yasoma da halima, ita kam bata baro wurin teenah ba saida sukayi exchanging numbers dinsu.

Fushi sosai Aliyu ya dauka har suka karasa masauki fushin da bai taba yi da itaba wai danme zata cewa teenah ta amince, kenan yanzu bata sonshi tagaji dashi,dakyar ta rarrasheshi ta shawo kansa ya sauko amma sai da ya goge number din teenah wacce ta bata, saida suka gama zagaya gari bayan sun gama umarar su sannan suka dawo Nigeria wannan karon kam tun a saudiyya halima ta fahimci tana da ciki nan ta soma boye boye wai kar Aliyu yagane shi kuwa ya rigada ya jima da ganewa kawai rabuwa yayi da ita ya kau da kai, duk lokacin da ta zauna ta rinka mita kenan wai mutum yayita kunika kamar a kauye domin kusan kullum sai khairiyya ko Sabira sun yi mata tsiya wai sun rigata fara haihuwa amma gashi tazo tayi musu overtaking ta wucesu domin duk cikinsu babu mai yara biyar har yanzu duk yaransu uku uku ita kuma gashi tana shirin ajiye na takwas, duk lokacin da ta sakashi agaba da wannan mitar cemata yake yi tsananin son da yake yi matane dalili domin duk matar da take irin haka to yar gatan miji ce kuma miji yana ji da ita,wani lokacin ta yarda wani lokacin kuma tace bahaka bane, kamar yadda ta saba cikinta na wata na tara ta yaye mimah Aliyu yakaita Zaria wurin su Aslam tuni itama ta ware taki dawowa ta shiga cikin yan uwanta dama kuma halima ta canfasu tace duk wanda yaje Zaria ayaran babu wanda yake dawowa kowa zamansa yake yi acan hankali kwance tunda akwai yara agidan. Ranar da edd dinta ya cika aranar ta haifo kyakkyawar yarta amma kuma kamar Aliyu jaririyar ta iyo, yana gefenta agadon asibiti rike da jaririyar bayan ya gama bata ruwan zamzam halima ta mintsineshi,

“Itama wannan ji duk kamarku ce kamar su aslam…”

“To ai jinina yafi naki karfi one love kinga dole yarana suyi kamata,amma kibari next time sai ki haifo mai kama dake mai kamar memah”

Kafadarshi ta dan buga,

“Wai na goma? Tabdijam wallahi ban isaba, hutawa kuma zanyi insha Allah”

Dariya yayi yasake gyara rikon jaririyar a hannunshi,

“Har kin bata a lissafin fa, yanzu ta takwas kika haifa sauranki hudu…”

Zamewa tayi tai kwanciyarta tana fadin,

“Bakinka ya sari danyen…… Insha Allah hutawa zanyi, hutu daga Allah”.

Ranar suna ansha shagali domin yan uwa duk sun halatta nan yarinya taci sunata Ummu ssalama,duk inda halima ta wuce sai an kalleta ankara domin tayi kyau na musamman ga yaranta duk sunsha kwalliya kowa shida mai bi masa ansaka musu kaya iri daya shiyasa babu wanda zai ganta yace ita ta haifi wadannan yaran sai wanda yasani,tun daga ranar sunan halima ke addu’ar Allah ya tsallakar da ita wannan karon karta sake samun ciki da wuri cikin ikon Allah kuwa sai taji shiru duk da Aliyu bai daga kafaba kamar yadda yasaba amma wannan lokacin kam harta kusan yaye ummussalma babu alamun ciki ganin haka yasata ta saki jikinta itama sannan har yanzu tana nan da dabi’arta na guduwa dakin Aliyu idan zata bawa jariri nono bata taba badawa a idon mutane tun su Sabira na daukar abin nata a matsayin sabon shiga har suka gane dagaske take domin ko agaban su umma lulluba take ko ta gudu, daga karshe da suka dameta da tsokana cemusu tayi Aliyu take boyewa kayanshi kar wani ya gane masa, bata taba goyo irin wannan ba domin saida yarta ta shekara biyu cif sannan ta yayeta itama tabi yan uwanta Zaria shikenan gida yadawo sai ita da Aliyu kadai, tsit take koda yaushe sai dai awaya idan ta kirasu ko su sun kira.

Yau kusan wata shida da yaye ummussalma tana kwance afalo tarasa abinda ke yimata dadi saboda kadaici domin shima yatafi wurin aiki, tanata saka da warwarewa sai gashi ya dawo, fuskarta da alamun damuwa ta karbeshi ta kawo masa abinci yau ko hirar ma da suka saba yi tareda tsokanar juna bata samuba, tisata agaba yayi da tambaya bayan yagama cin abincin kan saita fada masa menene damuwarta,budar bakinta sai cewa tayi,

“Nidai gaskiya ka mayar dani Zaria wurin yarana, nan kullum saini daya kwal kamar mayya daga ni sai halina kowa yatafi baya son dawowa, kaga ummussalama itama taki dawowa…”

Murmushi yayi yazaro wayarshi,

“To idan kin tafi to nikuma fa?”

“Waya sani, idan bazaka zauna kai daya ba sai kayi aure”

Dariya yayi kamar me sannan ya shiga rarrashinta daga karshe yajata suka fita cikin gari acan suka hadu da teenah itada angonta wanda aka daura musu aure watanni biyu da suka gabata. Acikin satin suka bar kasar Nigeria suka tafi kasar Cyprus inda sukayi karatu shekarun baya domin kawai shakatawa, basu tafi da yaronsu ko daya ba domin yaran sunfi son zaman gidansu umma, to sai muce adawo lafiya.

 

ALHAMDULILLAH

Anan nakawo karshen wannan littafi mai suna Dan halak, Allah yasa mu amfana da abunda ke ciki ya yafe mana kura kuranmu, jinjina da fatan alkhairi ga masoya wadanda suka bibiyi labarin tun daga farkonshi har zuwa karshe nagode babu adadi, sai mun hadu a wani labarin taku ahar kullum Ummi A’isha.

*_Ummi Shatu_*👌🏻

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *