DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 4 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI
Www.bankinhausanovels.com.ng
Mun tsaya
Ta ce, “Bari in asubancin zuwa garin mu in sanar da dangina da duk wanda na san zai zamar min shaida, kuma su sa ni a cikin addu’a, domin abin ya fi karfin mu sai dai mu zubawa Sarautar Allah idanu”.
Da ta sanar da malam Bala ya ce, “Haka ne, kinyi tunani mai kyau. Ni zan je can garin namu, amma ki zauna ki samu nutsuwa”.
Ta ce, “Zan je gidan Haj. Hadiza, domin
dan uwa shi ne mai jin tausayin ka, ko magana mai
dadi ta fada min zan ji sanyi”.
Ya ce, “Shi kenan, a dawo lafiya”.
Alpha ne ya iso gidan su Mubarak, tsugune
ya same shi a kofar gida ya saka hannu biyu ya kama haba, har Alpha ya fito daga mota ya tsaya a gaban sa yana masa sallama sam bai ji shi ba, domin tunanin sa yayi zurfi. Sai da ya zungure shi ya firgita, ya kalle shi yana kakalo murmushi, kai
da ganin murmushin ka san na dole ne. Ya ce, “A’a, Alpha aminin Mustapha”.
“Sannu abokin Mustapha”.
Haka suke kiran junan su, ya ce. “Na zo na same ka cikin wani irin yanayi mara dadi, dazu munyi waya da abokin ka na ce kana nema na, ya ce inzo inyi maka kowanne irin taimako ka nema, ka san Amini na ya fi karfin komai”.
Ya yi murmushi ya ce, “Mu shiga dakina Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, “Bisimillah”.Suka shiga ciki, Alpha ya ce.
“Ina Mah?”Ya ce, “Ta je gidan yayar ta”.
Ya ce, “Me ya hana ka zuwa office? Can na je aka ce wai ka kwana biyu ba ka zuwa, ko lafiya?”
Ya ce, “Ina tunanin barin aiki da kamfanin su Mustapha, yanzu haka neman aiki nake kowanne iri ne, wanda zan rike iyaye na”.
“Ko zan san dalilin barin ka aiki?”
Ya ce, “Ya zama dole, ka sani don na
fahimci kana son Mustapha tsakani da Allah”. Murmushi Alpha ya yi, ya ce. “Mustapha Amini na ne, amma ai ka kwace
min shi”.Duka suka yi dariya, ya ce.
“Ai yanzu na bar maka kayan ka, ‘don nayi nadamar sanin Mustapha a rayuwa ta. Tunda iyaye na suke wani bai taba kai karata ta fatar baki gurin su ba, amma yau iyayen Mustapha sun yi karar iyaye na”.
Sai yanzu hawaye ya rinka zubo masa, kuka sosai Mubarak ya rinka yi. Shi kam Alpha tsayawa yayi yana kallon sa, bai hana shi kukan ba don ya san dole in yayi kukan yaji sanyi a zuciyar sa.
Lallai akwai magana, kada zancen da ya tsinta agun Furaira mai aikin gidan su Mustapha gaskiya ne? Don ‘yar uwar su ce da aurenta ya mutu ta taho gidan su, Momi na neman ‘yar aiki Furaira ta ce zata yi, shi ne dalilin da yasa ta zama ‘yar aikin Momi, kuma a can take kwana, yanzu ta koma gidan su.
Sai da yayi kukan sa ya ishe shi, sannan yace Akwai matsala Alpha”.Ya ce, “Wacce iri?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya ce, “Na san kai lauya ne, shi yasa nayi tunanin ko zaman tare zai sa ka taimaka min. Ka sani iyayena talakawa ne, kuma sun bani dukkanin kulawa, ba na iya hada kowa da su…”.
Nan ya warwarewa Alpha komai, Alpha yace.
“Iko sai Allah. Mami rudaddiyar mace ce, ba ta son zaman lafiya ko kadan, shi kansa d’anta ta kwarzabe shi. Sai dai ita shari’a sabanin hankali ce, za ta iya zuwa ajuye, amma ni ba zan iya tsaya maka ba sai dai zan taimaka maka ta hanyar hada ka da wani lauyan. Kaga bai kamata in goyi bayan ka ba, amma zan iya baka duk wata kulawa, kuma zanyi bincike sosai don in san a ina aka haife ka? Su waye suka karbi haihuwar ka? Ungozomar ka? Karfe nawa aka haife ka? A gida ko a asibiti? In a asibiti ne katin yana nan? Sannan za’a yi gwajin jini”.
Mubarak ya yi murmushi, “Shi kenan Alpha, zan ba ku goyon bayan da zaku yi bincike har garin mu Panda”.”Shi kenan”.
Nan suka yi sallama har inda ya ajiye motar sa ya raka shi, ya shiga ya tafi cike da takaicin Momi.
Suhaila da Momin ta suna zaune falo, domin tunda aka yi bikin ta bata samu damar zuwa ba sai jiya da yamma ita da dan mijin ta Khalid suka iso a jirgi.
Muryar Baba Halima ta ji, ta mike tare da daka tsalle ta ce.
“Mah, sannu da zuwa”. Ta kalli Suhaila tayi kiba, tayi kyau abinta,
da gani ka san a huce take.Ta ce, “Oyoyo Mah, kina raina wallahi, cewa nayi da yamma zan je gidan ki”. Hajiya Hadiza ta kalle ta, ta ce.”Yau a gari? Inji maki mako”.
Ta ce, “Ai ba kya nema na”. Ta ce, “To ai gaki kin zo ko?”
Suhaila ta ce, “Mah, ina Barek?”
“Yana nan”.
“Mah, me nayi miki kika ki zuwa biki na?” Ta ce, “Suhaila ba a gayyace ni ba, saboda bani da muhimmancin zuwa bikin ki, kin san bani da abin da zan kawo…”.
“Dakata”. Inji Hajiya Hadiza.Zuwa kika yi kiyi min iskanci har cikin gida na? Ko so kike ki bata min rai?”
“A’a ko daya, amma naji haushi bikin sai bayan anyi abin naji, uwa daya uba Www.bankinhausanovels.com.ng
“Haka ne”. “Amma ba a sanar dani ba? Shi kenan,
Uhanghyt Allah Yasa anyi a sa’a, Allah Yasa mutu ka rabaAmin in da gaske kike”. Tayi murmushi, Suhaila ta ce.
“Mah, duk kin rame kamar mara lafiya”.Ta ce, “Lafiya ta kalau, sai dai bani da kwanciyar hankali”.
“Lafiya?” Haj. Hadiza ta ce. Hawaye suka zubowa Mah, ta warware “Jakar uba!”. Haj. Hadiza ta ce.
abinda ke damun ta.”Kai ana abu a duniya, to ba su isa ba, ai dan mutum ba dan yar tsana bane, wallahi mu zuba, dan halak ka fasa. Kinji min abu kamar wasa? Lallai ana abu a duniya”.Ta dauki waya ta kira danta Al’ameen ta sanar da shi tana son ganin sa, ya ce.Momi, kin manta na tafi Sulga?” Ta ce, “Oho, kaina ya dauki zafi”.
Ta kira Mukhtar, shi kuma ya ce yana zuwa. Suhaila tace, “Mah, kada ki damu, da fatan kina do takardansa na haibuwa?”
Ta ce, “Hatta katin da naje haihuwa yana nan, ko ciwo Mubarak yayi ba na yar da katin, yana ajiye. Duk takardun sa duk suna ajiye, wannan na san wata kaddara ce daga Allah, amma taya zan haifi da wata ta ganshi sama tace danta ne don taga bani da kudi, bani da gata ta karbe min dana
Suhaila tace “Ai ko danta ne ya kwatu, bare babu abinda zai ci gawayi”.
Sai ga Mukhtar ya shigo, sukas gaisa, ya ce.
“Baba Halima, kwana biyu? Ina Mubarak?” Ta ce, “Yana nan”.
Ya ce, “Ai rannan mun hadu da shi da wani abokin sa, shi kuma abokin nasa kamfanin baban sa muke aiki”.
Momi ta ce, “Kaji wata tatsuniya, wai karar su aka kai akan Mubarak wai dan wata mace ne”. A zaune yake, ya yi saurin mikewa, ya ce.”Kai! Rigima”.
A nan ta warware masa komai, ya ce. “To kada ta damu, insha Allahu komai zai(settling)”.
Dan uwa kenan rigar kaya, gashi dai Haj. Hadiza duk ta rude, ta gigice. Shi yasa aka ce duk dadin ka da bare dan uwa ya fi shi.
Weediyan ta tsaya akan Momin Musty, tace.
“Ina so ki fada min shi Mustapha DAN WAYE? Tunda kin ce ba danki bane, rayuwa zata yiwu ace baka san darajar dan Adam bane? Wallahi ko Musty daga sama ya fado ni ina son sa”.
Haj. Lami ta ce, “Wai me ke damun kanki ne Weediyan?”
Ta ce, “Ba dole in damu ba, don mijinta na da kudi sai a kyaleta ta ringa abubuwa? Saboda Momin Musty nake burin sai na auri mai kudi, saboda in taimaki kowa”. Www.ba
nkinhausanovels.com.ng
“Kije ki auri Karuna mana”. Inji Haj.Saratu.
Weediyan ta ce, “Hakika kin zama azzalumar uwa, kuma insha Allah sai Allah Ya sakawa Mustapha, don na fahimci shi kike son
tozartawa, kuma wanda Allah Ya daukaka babu wanda ya isa ya komar dashi baya. In ba ki sonsa me yasa kika haife shi? Ni da ban san ina son Mustapha ba sai yanzu”.
“To tunda kina son sa ai sai ki aure shi, ko ki zamar masa gurbina”.
Weesal ta shigo, ta ce.
“Ke Weediyan, me yasa baki da kunya?” “Sai ki tambaye ta me yasa bata da imani da tausayi?”
Weesal ta ce, “Hajiya, kina jinta fa, yayar maman mu take yiwa fitsara akan wanda bamu da tabbas din jinin mu ne? Ai uwa ta fi kowa son danta, kila wani mugun abin ne ke da shi taga bari ta sake shi”.
Haj. Saratu ta ce, “Ko kadan, in kuna yi masa tunanin mugun abu to ku daina, Mustapha yana da kirki da girmama duk wanda ya dangance shi ko Alhaji, kawai ni dai naji shi din ba dana bane”.
“To ai sai ki kashe shi, in da nine Mustapha har abada ba ni ba ke wallahi, kuma sai kin neme ni. Amma wai ba ki da lafiya shi ne duk inda yaji me magani ya je, yayi tayi miki karatu, amma a banza. Kai duniya da kallo, wata sakayyar sai a lahira”. Haj. Saratu ta ce, “Weediyan, ki fita idona in ba haka ba zan saɓa miki, kuma ke baki isa ki dirke ni kina rashin mutunci ba, ko uwar ki bata isa ba balle ke”.”Eh, ita ai ‘yar uwarki ce, amma ni fa?”
Haj. Lami ta bata mari, ta ce. “To tabbatacciya, ya isa, bana son dibaralbarka”.
Weesal ta kamo ta tayi daki da ita, ta ce.
“Haba ‘yar uwata, na kula da ke duk kin sauya, wai me ke faruwa dake?” Ta ce, “Nima ban sani ba, nayi takaici da ba
karatun likita nayi ba, amma duk da haka ina da
(right) din da zan watsawa duniya wannan labarin”.
Ta zaro mata ido, ta ce, “Haba Weediyan, saboda me za ki yi haka?”
Ta ce, “Allah sai na watsawa duniya labarin da zarar an fara shiga kotu, kuma zan je in “Allah Ya kyauta miki”.
Alh. Abdulmajid duk abin duniya ya hadu yayi masa yawa, ga dai matar sa ta tafi saboda zurmewar zuciya, ga dansu ya bar kasar ba ki daya. Takaicin sa daya, sunan sa da matar sa take neman bata masa, taya ma za a yarda da ita a cikin wannan murdadden lamari?
Tausayin Mustapha ya kama shi, nan take yaji zazzafar kaunar sa ta kama shi, saboda haka kawai sai ya dauki wayar sa ya kira shi, amma har tayi (ringing) ta gama ba a dauka ba, sai kawai ya ajiye. Www.bankinhausanovels.com.ng
Shiru yayi yana tunani, ko asibitin masu tabin kwakwalwa za a kai Haj. Saratu? Ko ya lallaba ta su wuce kasashen waje a gwada masa kwakwalwar ta?
Ji yayi wayar sa tana neman agaji, ya dauka, dansa ne Mustapha, ya ce.Ya aka yi Boy?”
Mustapha yayi murmushi, “Barka da yiniDaddy”.
Ya ce, “Sai yau ka tuna dani?” Ya ce, “Na isa Daddy? Wane ni? Ko kamanta dazu ma munyi waya?” Ya ce, “Haka ne, tsokanar ka nake yi”.
Ya ce, “Daddy, dama dazu mantawa nayi, ya kamata aje gidan iyayen Izzat ko? Na fada
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG