DAN WAYE? CHAPTER 12 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI
Mun tsaya
Ya shiga ya fito da kwandon abinci da wasu hadaddun kuloli a ciki, ya sanya a bayan mota, ya ce.
“Ma hadu Daddy, bari in dauko mota ta”. Ya ce, “Okey”. Ya ja ya tafi.
Maigadi ya bude masa yana cewa.
“A gai da mai jiki, ayi masa sannu.
Ubangiji Yasa kaffara ce”.Alhj Yace, “Amin”.
Ya nufi asibiti zuciyar sa cike da takaicin halin matar sa, ai ko dan riko aka dauko ba naka ba shakuwa wani abu ne.
Mustapha ya tara halaye na gari wanda jama’a ke yabon sa shi dai bai son raini, haka akwai shi da girmama duk wanda ya girmama shi. Matsalar sa daya rashin hakuri, amma dole ya kawo karshen wannan halin nasa, don yanzu hakurin sa ya kare akan irin wannan halin ko in kula da take nunawa gudan jinin nasu tal daya.
Har a lokacin bacci yake, ko da Alhaji ya shigo ya shafi kansa yana jin kaunar dan nasa, a lokacin Alpha ya shigo ya zauna.
Alhaji ya ce, “Wa zai zauna?” Ya ce, “Gani mana”.
Ya ce, “Office din fa?”Ya ce, “Nayi signning, kuma na nemi excuse”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya ce, “Zan wuce ina da (meeting) da wasu ma’aikata na, amma muna fitowa zan zo. Inaga anjima Hajiya za ta zo”. Ya fice.
Alpha ya kura masa ido, tausayin sa ya kama shi, don tun suna yara suke tare, babu wanda yasan tsakanin su sai Allah. Haduwar Mustapha da Mubarak ce tasa abotakar su tayi sanyi, don Alpha baya son yaga Mustapha ya fifita wani akan shi. Shi yasa shi ko shiga sabgar Mubarka baya yi, amma sai yaga Mubarak yana da kirki da kyan hali, shi yasa sai ya watsar aka zama duk abokai.
Alpha ya jima a zaune har Dr. Yaseen ya
shigo, suka gaisa, ya ce.Ya farka kuwa?”
Ya ce, “A’a, ni dai tunda na zo bacci yake”.
Ya ce, “Ai na sani, domin baccin muke buata yayi, domin zuciyar sa da kwakwalwar sa su huta. Amma na san daga yanzu zuwa wani lokacin zai iya farkawa, da zarar ya farka sai ka kira ni”.
Suka yi musabaha, Dr. Yaseen ya fita.
Sai biyu da kwata ya farka, ya bude idonsa yana kallon dakin. Ya gano a asibiti yake, ya zauna ya kalli Alpha yace
“Tun yaushe nake anan?” Ya ce, “Tun jiya”.
Ya mike tsaye ya ce, “Ina (brush) dina?”Ya tashi ya dauko masa, ya matsa masa makilin. Ya shiga ya watsa ruwa, ya sanya wando (3 quater) ya sa (T.shirt) ya sha (tea) din da Alpha ya hada masa, sannan mike yayi sallah.
Ya jima kan sallaya yana addu’o’insa, kamar jiru ake ya shafa akayi sallama. Yan gidan su Momin sa ne sun kai su takas har da kakar sa mai son sa, mai kaunar sa.
Ta karaso inda yake, kan sallaya, ta ce. “Mustapha, sannu da jiki, ance min baka ji dadi ba, na tashi hankali na, don ban shirya takaba ba”. Suka tuntsire da dariya, Alpha ya ce.
ow”Kaji Hajiya, shekaru dari biyu ma nan
gaba muke sa ran ki”.
“Ai kam da an gaji da ku”.
Ta ce, “Ni kam ko banza nayi asarar gerona na gumba”.
Alpha ya ce, “Baki yi asara ba, ki dama kunu kiyi sadaka”. Dai dai lokacin Faisal da Anwar suka shigo.”Wai, har naji dadi, Mamie tace kana asibiti duk mun tsure, ashe ma ka samu”.
A lokacin ya mike ya hau gefen gadon ya zauna, suka ci gaba da kwasar Hajiya suna dariya. Da yake sun saba duk Juma’a suke zuwa gidanta din dambu da danwake, ko tayi musu dashishi ko burabusko, har tubani ma yi musu take. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai la’asar ta ce, “To bari in koma gida, in an sallame ka shi kenan, in kuma ba a sallame ka ba sai gobe. Me zan taho maka da shi?”Ya ce, “Tuwon dawa miyar danyar kuɓewa”.
Ta ce, “To shi kenan”.Alpha ya ce, “Ni gaskiya Hajiya ba tuwo
ba”.To waye mara lafiyar? Abinda nake so shi za a kawo”.
“To waye mai jinyar? Mara lafiya ai baya cin abinci, mai jinya shi yake kwasar dadi”.
Hajiya tayi murmushi ta ce. “Kwa karata, ni kunga tafiya ta”.
Faisal ya ce, “Bari inzo in kai ki gida”.
Ta ce, “Ai ina tare da direba”.Ta kalli Mustapha ta ce, “Ina tunanin yau
kanwar ka Weesal za ta dawo”. ya dan yi murmushi, yayin da gaban sa ya ba da dam! Ya ce.
“Allah ya kawo ta lafiya”. Ta juya ta fita. Biyar na yamma ciwon kai irin na bari dayan nan ya damu Mustapha, ga abokai da ‘yan uwa wannan ya shigo wannan ya fita. Yana kwance yana jinsu hayaniyar su ta dame shi, a lokacin likitocin biyu suka shigo suka gaisa, duk matasan suka fita.Dr. Yaseen ya dubi Mustapha ya ce.
Ya jikin?”Ya runtse ido ya ce, “Alhamdu lillah”. Ya dafa kansa, “Me ke damun ka?”A
Ya ce, “Ciwon kai mai tsanani, bana son surutu duk sun dami mutane”.Okey, sannu ko?”Ya janyo V.p ya auna hawa jininsa yayi, di ya ce.Dr. Shuriem, dan duba ka gani ko idona ne bai gani dai ai ba”. Shi ma ya gwada, ya ja tsaki ya ce.”Mustapha, me yake damun ka wanda gashi har jinin ka yayi mugun hawa? Dole masu damun ka za mu hana kowa ganin ka, akan me za su hana ka kwanciyar hankali?”
Ya duba takardar jikin gadon sa wanda (case) dinsa ke rubuce, ya sake rubuce-rubuce. Ya fita ya dawo ya yi masa wasu allurai, sun jima suna yi masa tambayoyi har bacci yayi gaba da shi. A lokacin Alhajin ya shigo, suka gaisa, Dr. Yaseen ya ce.
“Alhaji, bamu bukatar ‘yan dubiya, domin jininsayayi irin hawan da bama so, da alama ya jima da damuwa a tare dashi, don ciwon yayi karfi”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Alhajin ya rangwadar da kai, ya ce. “To Allah Ya kawo sauki”.
Suka ce, “Ameen”.
Da likitocin da Alhaji tare suka fito, a lokacin Dr. Shuriem ya kalli Alpha ya ce.
“Alpha, da Allah a hakura da ‘yan dubiya, ko in sun zo ku zauna a waje, yana bukatar kadaici. Abokin ku yana fama da ciwo ku kuna ta hira, da tsautsayi sai y fadi ba ku sani ba”.Duk suka yi (shock) suka wuce su, dole sauran abokan suka wuce.
Alpha shi kadai ne a zaune, shi ma a waje.Alhaji yace “Alpha, wai me ke damun abokin ka?”
Ya yi shiru, ya ce, “Ina ga akan yarinyar nan da yake so ne, to amma ko ma meye Mubarak ya sani. Ni sai yanzu na tuno da shi, inaga bai sani ba, don da tuni ya zo”. Alhaji ya ce, “Bari inje gida, sai bayan isha”.Yana tafiya Alpha ya kirawo Barek a waya ya sanar da shi suna Nusshu hospital.
Suhaila ce zaune tana kallon su Yusrah suna ta faman zuba kayan rabo, manyan jakunkuna masu dauke da hoton ango da amaryar, kowacce jaka akwai saitin kayan kamshi da atamfa da agogon bango, duk mai dauke da hoton ango da amarya, sunyi mugun kyau.
Bafilatanin Gombe ne, yana da uku-uku irin na Gombawa, jikin sa a murje, dan gayu sosasi. Amma in har ka kare masa kallo hakikaza kasan ba na yau bane amma kallo daya ba zai bayyana maka shekarun sa ba.
Wasu jakunkunan set din silba ake zubawa da farantan tangaran, da jug. Yanayin yadda ake zuba kayan rabon zai nuna maka ‘yar masu kudi ce sosai, ahka shi ma mijin ma mai kudi ne.
Surayya Ibrahim ta shigo tana fadin. “Ina amaryar ne? Sai naji an daga Barek an dankara shi da kasa”.
Kawai sai Suhaila ta fashe da kuka, ta ce.
“Na ce bana son sa, Barek nake so, anki
yarda, za a hada ni da wannan tsohon”.Rukayya tayi wuri-wuri, don tana da tsoro sosai.
“A’a Suhaila, kada inzo ace ni na zuga ki, da can
baki yi kukan ba. Kiyi hakuri, kila Hajiyar ki ta gano miki alherin da ke ba ki hango shi ba. Iyaye fa babu yadda zasu yi su zaba maka abinda zai cuce ka, don Allah kada ki nunawa ‘yan (school) dinmu dole aka yi miki, kiyi hakuri”.
Ta share hawayen ta, ta ce.”Kowa za a bani bai kai kyan Barck ba, bai kai addinin sa ba, bai kaishi tsoron Allah ba, haka bai kai shi sona ba”.
“Wannan fa maganar da kike abu ne a duhu, babu wanda yasan gaskiya sai Allah. Bari in mike in tafi”.
Yusrah ta yi murmushi, ta ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Da ban yi niyyar sanya muku baki ba, amma yanzu Ruky ace mutum yaki ci yaki sha? Kina bata ranki kina bata na masoyan ki? Ki sani duk wanda ya yiwa iyayen sa biyayya ba zai fadi a banza ba, kema ‘ya’yan ki za suyi miki. Wanda kike abin nan akan sa ba ya saurarar ki, ba ya daukar wayar ki.
Kin san wani abu Ruky? Jiya na ganshi yayi jawur da shi, yayi kiba alamar babu abinda yake damun sa. Kuma Ruky ban taba ji ance namiji ya fada rijiya ko kashe kansa akan mace ba, sai dai mace tayi wannan shirmen. To su mazan tawakkali suka fimu? Ko biyayya suka fi mu? Ya kamata mata su farka daga wannan narnauyan baccin da suke yi”.Rukayya ta ce, “Gaskiya ne Yusrah, mace ta fi namiji zurfafa a soyayya. Kuma maganar ki tana kan hanya”.
Suhaila ta ce, “Ana samun namiji mai zurfi a soyayya, bari in tuna miki labarin Laila majnun. Yana cikin rukunin matafiya suna cikin tafiya yaga kare, ya sauka daga kan abin hawan sa ya kama karen ya rungume, yayi masa wankaya gyara shi. Da aka tambaye shi saboda me yayı haka? Cewa yayi, karen ya yi kama da karnukan garin su Laila”.
Gaba daya suka bushe da dariya, “Wato karen ma ba na Laila bane, kama yayi da na garin su Laila. Lallai ya yi zurfi”. Suka bushe da dariyaTo kun ce namiji ba ya zurfi, shi ya yayi?”
Su ai Larabawa ne”.
“Au, kuna so ku ce min Bahaushe bai san soyayya ba? Kuna nufin kuce iyayen mu ba a soyayya suka same mu ba?” “A’a, mu bamu ce ba, kiyi hakuri ki
kaddara Allah bai nufa Mubarak mijin ki bane”.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG