DAN WAYE? CHAPTER 13 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

DAN WAYE? CHAPTER 13 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Da aka tambaye shi saboda me yayı haka? Cewa yayi, karen ya yi kama da karnukan garin su Laila”.
Gaba daya suka bushe da dariya, “Wato karen ma ba na Laila bane, kama yayi da na garin su Laila. Lallai ya yi zurfi”. Suka bushe da dariyaTo kun ce namiji ba ya zurfi, shi ya yayi?”
Su ai Larabawa ne”.
“Au, kuna so ku ce min Bahaushe bai san soyayya ba? Kuna nufin kuce iyayen mu ba a soyayya suka same mu ba?” “A’a, mu bamu ce ba, kiyi hakuri ki
kaddara Allah bai nufa Mubarak mijin ki bane”.

“Ban yarda ba, Momi bata so in aure Barek ne, insha Allah sai yayi arziki, sai Momi ta gano cewa dan uwanka duk lalacewar sa, duk talaucin sa dan uwanka ne”. “Kiyi hakuri”.
Mustapha damuwa biyu ce a gare shi, yadda soyayyar Izzat ke damun sa, ga shi kwanakin sa uku cikin asibiti amma bai ga idanun Momi ba, wai saboda me? Sai yaji idanun sa na yi masa yaji. Wai me yasa take watsi da lamarin sa?
Yana cikin wannan hali Mubarak da Mah da baban sa suka shigo, yana duban su sai yaji tamkar an wanke masa zuciya. Cikin fara’a ya ce.
“Mah?”ah Ta ce, “Yarona, me yake damunka haka ne?”
Ta karashe maganar cikin nuna
tausayawar sa. Tana son Mustapha kwatankwacin son da take yiwa Mubarak. “Ya jikin naka?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Malam Bala ya tambayi Mustapha.
“Da sauki Baba”.Mah ta ce, “Yaron ka da kai ina za ka
samu hawan jini? Komai ya samu bawa da sanin Allah, duk abinda kayi hakuri zai shige tamkar ba a yi ba, kada ka janyowa rayuwar ka nakasu tun kana yaro karami. Ka ganni nan babu abinda zan sanya shi a zuciya ta ya dame ni, in yini ko in kwana da bacin ransa. Don Allah ka zama mai tawakkali akan duk hukuncin da Allah Ya yi maka”.
Sai ya ji zuciyar sa ta karye, sai yaji hawaye na sakko masa, Mubarak ya dinga goge masa.Ya ce, “Mah na gode Allah da kuka shigo rayuwa ta, ina ji a jikina ku kun zamar min barin


jikina. Don Allah ku taya ni da addu’s Allah Yayi min maganin abinda yake damuna”.
To Malam Bala ya ce, “Zamu yi maka addu’a, amma sai ka saka tawakkali da juriya, ka kuma mai da komai ba komai ba”.
“Shi kenan”.
A lokacin Alpha da Alhajin Mustapha suka shigo, suka gaisa da malam Bala da Mah, Mustapha ya gabatar da su a matsayin iyayen Mubarak. Ba su dade ba suka koma, suka hau Adaidaita sabu ya kai su gida.
Mustapha ya dubi babansa, ya ce. “Daddy, yau kwana na uku a cikin asibiti
ban ga Momi ba, na rasa me na yi mata ba ta kauna ta. Daddy don Allah ka fada min gaskiya, ko indai ni ba danta bane?” Daddy ya yi murmushi, ya ce.
“Kai daya na haifa, ban taba son dan wani fiye da kai ba, ko ita uwarka na fi sonka da ita, don ita zan iya rabuwa da ita, kai fa?”
Ya ce, “Ina tunanin mahaifiyar ka ko tana da aljanu ne wadanda suke tunanin raba ta da kai, domin mun sha wuya kafin ta dauke ka bayan an haife ka, da kyar ta baka nono, kai daga karshe ba ka shekara ba ka daina sha, abin nan yana yi min ciwo. A lokacin abin yayi sauki, amma yanzu ya dawo, har yafi da. Ni ina ganin
kayi aure shi zai fi ma”. Mustapha ya dora kansa kan kafadar Www.bankinhausanovels.com.ng Daddy sai kuka. “Ya ba zanyi hawan jini ba, uwarka ta mai da kai abokin gabar ta? Ni kuma tawa kaddarar kenan”.”Hakuri zaka yi, nayi fushi, na raba dukiya ta biyu na mallaka maka rabi, lauyoyi na sun sa hannu, itama ta sa hannu, lauyoyin ka nake jira. Dangi na babu wanda ba ya sonka, ka san na birni da na kauye, burina ka kyautata musu. Yanda ta ce bata son ganin ka nima bana so ta ganka, wai a duk sanda ta ganka wani abu ke tsaya mata a cikin zuciyar ta. Idan na samu sukuni zan tafi Turkey inci gaba da rayuwa ta a can, tunda dama zama na a can ya fi na Nigeria
yawa”. Ya ce, “Shi kenan, yanzu gashin kanka za ka ci, nafi so komai naka kaji my Boy”.Ya yi murmushi, sam yanzu ba batun Izzat ne a gabansa ba, batun mahaifiyar sa ne a
gabansa. Ya taso cikin tsana da tsangwama da kyara a gurin ta, babu kulawa da tausayi, tun baya damuwa har ya damu.
Mijin ta da mahaifiyar ta sun yi bakin iyawar su, har sakinta anyi daga baya ta dawo. Mahaifiyar ta har rokon Allah take
Wani lokacin za ka gansu lafiya abin sha’awa, in abin ya motsa sai a (slow).Lamarin ne ya motsa, ga tsakanin sa da Izzat, abin ya zamar masa zafi biyu: To muna nemar masa saukin Allah.
Biki yayi biki, yau bikin na masu abin ne,
domin Sudan aka je aka dauko masu shirya
amarya su hada ta tayi kyau. An daura auren Suhaila akan sadaki dubu dari biyar da mota ‘yar ubansu.
Amarya cike take da kunci saboda bata samu cikar burinta ba. Kayan mata iri-iri mahaifiyarta ta dibga mata.
Anyi fati iri daban-daban, amma ita duk wannan bai burge ta ba, ita kawai a bata Mubarak dinta, ko dakinsa ne na soro su zauna kafin Allah Ya yi masa nasa.Ta ringa ware idon ta ga Mah amma ba ta ganta ba, kuma kafin bikin take tunawa Momi
kada tayi fushi da ‘yar uwarta”ki gayyace ta”. “Suhaila ba ki san halin Halima ba, muguwar yarinya ce ba wai hakuri ne da ita ba, tsabar iya munafurci ne. Haka tai ta hada ni da iyayen mu, sun fi sonta a kaina, ni da basu sogashi nan ni Allah Yafi so, don Ya bani arziki na kudi da ‘ya’ya, ita fa? Da daya ta haifa, ga talauci”.
Suhaila ta ce, “Momie, wannan duk daga Allah ne, ke dai ki rungume ta, babu wanda yasan gobe sai Allah, Allah Ya yiwa kowa arziki”.
“Ta ina zai yi arziki? Ai shi da arziki sai dai in mota ta auna shi ba ta buge shi ba ace ya auna arziki, ko an gaya miki haka siddan ake yin arzikin?”
“To naji Momie, ki daure ki sanar da ita, kinga kin fita hakkinta, bana so Allah Ya kama ki da hakkin ta”.Ta ce, “Zan aika mata”.
Ta ce, “Ko za ki bani in kai mata?”
“Ki kai mata ko dai kije gurin masoyin ki danta? Ke ko rabon kawayen ki na ce baza ki ba, shi yasa nasa miki tsaro kada ki ɓallo min ruwa”.
Suhaila ta dawo daga tunanin, tabbas Momie bata aika mata ba. Ai shi kenan, itama tayi alkawarin taimakon Baba Halima ko don kyawun halinta.Anyi casu sosai a bikin Suhaila, Naira tayi
kuka don maroka sun kwashi rabon su. An nufi birnin Tarayya, inda za a kai ta zauna. amarya, Suhaila Www.bankinhausanovels.com.ng
Mubarak yana zaune bakin gadon sa sanye yake da singileti da (3 quater), ya kunna t.v don ganin labaran tara. Ko minti daya ba a yi ba ya ga an hasko (Lovers night) din bikin Suhaila.
Wuta ce ta dauke masa, ashe so wani abu ne mai wuyar cirewa. Son gaskiya ba ya buya, ba ya dannuwa, tunda soyayya ce da aka dasa tun kuruciya. Sai gashi ya zube bisa gado, bai san iya
adadin lokacin da ya dauka ba, ya mike jiki babu kwari ya shiga gida, ya zube gaban Mah, ya ce. “Mah, me yasa ba ki sanar min anyi bikin”Wanne irin biki?”na Suhaila ba?” Ya ce, “Anyi bikin ta, yanzu na gani a tv
Ta ce, “Oh ni ‘yasu, wai me muka dauki dan uwa ne? ‘Yar uwata uwa daya uba daya, saboda tunanin ta bani da shi shi ne taki gayyata ta? Ai gugu ko bai yi tsoron komai ba yayi na igiya. Amma shi kenan, Allah Ya ba da zaman lafiya. Wallahi na r
abu da ita, sai sanda ta neme ni”.
Yace, “Ai in kinyi haka Mah kun zama daya, ai akwai bambanci tsakanin jahili da mai ilimi, haka akwai bambanci tsakanin mai hankali da mahaukaci, haka bambancin yake tsakanin babba da karami”.Ta ce, “To yanzu me kake nufi?”
“Ki bari sai bayan abin zan kai ki kiyi mata murna”.
Ta ce, “To shi kenan, ina rokon Allah Ya yi maka albarka, ya sauya maka da wacce ta fi ta alheri. Ni na san kai dan albarka ne, Allah Ya bude maka hanyoyin alheri, wanda muke tunani da wadanda tunanin mu bai zo kai ba”,
Ya ce, “Amin”. Ya mike jiki a sanyaye tamkar kazar da aka tsoma ta cikin ruwan zafi.
Hajiya Hadiza tana daga tawagar ‘yan kai amarya, don ta shige gaba abinta, ita ce akan harkokin ta. Kawayenta duk wayayyu ne, irin masu budewar idanun zamani, irin hajiyoyin da suka dauki rayuwa da zafi, irin mutanen da ba su dauki komai da wani muhimmanci ba, burinsu shi ne burin su ya cika ko da za su salwantar da rayuwar wasu. Sam ba su dauki ran dan Adam da daraja ba, su kam sai a hankali.
Hajiya Marka ta ce, “Ni tunda aka soma • biki ban ga Halima ba”. Ta ce, “Ba ta samu zuwa ba”.
Hajiya Laure ta ce, “Ya zata zo an hana danta auren tsaleliyar yarinya irin wannan? Ai mijin Suhaila ya more yarinya, ta hadu ta ko ina”.Ta ce, “Kema dai kin fada, haka ta so in
aurawa danta ‘yar don ya samu aiki, to albashin
nasa nawa ne? Wai har ya sai Lifan, naji ance ya sai fili ya soma gini”.
Suka fashe da dariya, “To banda abin Halima ai dai dai ruwa dai dai kurji”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Hajiya Marka ta ce, “Ni kuma inda ni ce ke zan janyo Halima a jikina in taimake ta, tana da kirki fa. Kuma sai naje har gidanta na ji dalilinta na kin zuwa bikin ‘yarta, mai sonta”. Hajiya Larai ta harari Marka, ta ce.”Ku dama ai sai a hankali, biki in naki ne ‘yan uwanki ne za su tsaya saboda kada mu handame, Hajiya Hadiza kawa tafi ‘yar uwa, abinda kawayen suka tara miki ‘yan uwan za su baki?”
Hajiya Marka ta ce, “Wallahi da ciwo, ko karayar arziki ta same ko babu mai tsaya miki sai naki, don ni ganau ce ba jiyau ba. Kawayen ma sai kina da shi kike mutum, in baki da shi babu mai rabar ki”.”To ai wannan abu haka yake, ko da kuwa ga ‘yan uwan ne”. “To ni batun ya ishe ni”. Inji Hajiya Marka.
“Kowa ya gyara ya sani, kowa ya bata ya sani. Kanwar taki guda daya in baki yi mata ba kiyiwa wa? Duk wanda za kiyiwa ba burge su zaki yi ba. Shi dan nata da kika hana kin san me zai zama?””To ki dauki ‘ya’yanki ki bashi”.
Tayi dariya, ta ce, “To inama ace Allah (S.W.T) Ya amsa bakin ki, kuma ya hadu da Weesal ko Weediyan, da na bashi”.”Wadannan yaran ‘yan feleke?”

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *