DANGIN JUNA BOOK 1 CHAPTER 10 BY SA,ADATU WAZIRI GOMBE

Wani setin sarka ya miqa mata na diamond da wani leda, turaruka ne a ciki sai key din mota dar blue ‘yar Karama mai bala’in kyau.

“Sanin ba abin da kika fi so a rayuwarki irin turare yasa na saya miki su. Sannan sarka na san baki cika son saka yan dan kunne ba, dama na siya da niyyar ranar bikinmu ki sa nasan za suyi miki kyau, to tunda Allah bai yi dani ba ina fatan zaki sa ranar bikin ki da Amin.

Mota kuma na ga kina sha”awar karamar mota shi yasa na saya,miki don taki babba ce”

Kúka take kamar ranta zai fita, “Yaya Faruk na gode da kyautar ka. Ina so ka sani wallahi Yaya Faruk duk duniya kai kadai nake go. Ina.,so kafin a daura min aure da Amin ka yadda da wanna ka kuma daina fadamin wai bana sonka. Yaya Faruk don Allah ka sa ma zuciyar ka hakári ka sassauta abin da kake wa Yaya” Maryam, wallahi Yaya Faruk ba ta da

laifi Fati ki yi hakuri ba yadda ban sarrafa

“zuciyata Ba don na so Maryam na kasa, wallahi fati nima ina tausaya mata, to amma ya zanyi an halicci zuciyata don son mutum daya.

Wallahi Pati sonki har ya min yawa, na rasa ya zanyi. Patina wallahi ina sonki ba zan daina ba sai na mutu. Pati ki min addu’a na mutu kafin gobe na ga daurin auren ki. Fati zan yi hauka in naga ranar nan. Fati don Allah ki aure ni kar ki sa na rasa ki. Fati me yasa baki so na aure ki? Wallahi zan miki komai a duniya, wallahi ba zan bata miki rai ba, kuma ba mai bata miki rai, kullum zan saki cikin farin ciki.

Wallahi zan na saki dariya, ba za ki yi girki ba bare shara, bare wanke-wanke, ko ba kya son masu aiki ni zan miki. Ko kin ce kar na je aiki zan zauna dake in ta saki dariya. Zan kai ki India ki ga Rani da Soni Nigam. Komai an miki, kullum zan kai ki ki ga Umma da kowa, zan kai ki Hajji da Umra.

Kai Fatina, komai zan miki muddin dan

Adam zai iyawa mutum ya sa shi farin ciki.

Wallahi Fati kar ki sa na rasa ki don Allah.

Patina kar ki sa na rasa ki, ba zaki tausayawa bawan Allah ba. Pati na ki aure ni?” Girgiza kai ta yi ta koma cikin mota, lallai duk mutumin da damuwa tai mai yawa har ya yi kuka samu ya yi. Don a gaskiya Pati kasa kuka tayi tsabar bakin cikin yai mata yawa, sai hawaye har sun kafe ta koma yin kukan zuci da ajiyar ruciya. Kasa magana ta yi, ya yin da shi kuma bai daina mata magiya ba. Yaya Faruk don Allah ka ja mota mu

tafi”Fati baki damu da halin da nake ciki ba ko?”

Nan ya je ya samu wata bishiya ya

Kankame yana kuka, kuka sosai da Karfinsa tamkar yaro yana surutai. Da sauri ta fito ta nufi gunshi,

Dafa shi ta yi ya juyo suka rungume juna tamkar zata koma jikinshi su zama daya, ga ta

“yar Karama a gabansa.

A hankali ya dagata ya dinga juyi da ita ya

Kara rungume ta, kai Faruk dai har ya rasa ina zai sa Fati don so da dadi da murna, ya rungume ta. Tunda suka soma soyayya bai taba rungume ta ba sai yau. A hankali ya sauke ta ya koma ya jingina da bishiya yana kuka yana kuma dariya. Pati kam kuka hawaye shine abin da ke fita daga idonta, hakika ita yanzu bayan son shi ma tausayin shi take sosai, to amma ya za tayi kalmar nan dai daya ce HAKURI.

A hankali ta isa gunshi, «Yaya Faruk mu tafi gida”

“My dear za ki aure ni?”

“Ka yi hakuri my dear ba zan aure ka ba”

“Ba za ki aure ni ba?’

Shiru ta yi ta nufi motar, ya yin da yazo ya figeta da karfi, Allah ne kadai ya kai su gida lafiya.

Washegari juma’ a aka daura auron Fati da Alamin a Rofar gidan Alh. Abubakar. Fati kam ta rasa mai ke mata dadi, duk duniya tai mata zafi, duk kyan abu ranar munin shi take gani, kallon mutane kawai take suna kai wa da kawowa wai sunzo taya ta murnar biki, maimakon su taya ta jimamin rasa masoyinta da ta yi. Ta kalli wasu kayayyaki da Kawayenta suka kawo mata wai congratulation na aure suke mata. Kayya! Ta san duk wanda yace bikin nan yazo ba sonta yake ba, ita yanzu ta san ba ta da sauran farin ciki, to amma abin da ya dame ta yanzu wani hali masoyinta yake ciki. Wayyo masoyina Faruk, Allah cika maka burinka ko a lahira ka aure ni matsayin mata, a duniya kam na san ka rasani har abada.

Duk wani programme da yayi Pati ta nuna ra’ayin ba ta son komai, walima kawai aka yi. Ya yin da su Umma, Yaya Maryam, Abida da sauransu aka tafi yiwa Fati jere. Giidansu na kallon juna da na su Faruk tamkar na iyayensu, haka nan su ma komai iri daya ne.

Fati kam ta sha kaya, Umma kam tayi rawar gani ta amsa sunanta uwar Fati, duk yadda mutane ke tsammani Umma ta wuce nan. Kayan Fati kam sai wanda ya gani.

Zaune take bakin dressing mirror tana kallon madubi, amma bisa ga dukkan alamu hankalinta baya ga madubin.

Hmmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *