DANGIN JUNA BOOK 1 CHAPTER 3 BY SA,ADATU WAZIRI GOMBE
Da Kyar Umma ta rarrashe shi suka fito
falo, amma duk da haka rokon ta yake Umma
don Allah ki gayawa Abba ya aura min Fatina.
“To Faruk na ji, amma yanzu kaje gida
zamu yi maganar da Abba Umma za a aura min ita?” Ta ce, Za a aura ma Da kyar ya samu direba ya mai da shi, don a gaskiya barin shi ya yi tuki ba karamin hatsari bane. Ya yin da ta koma ta samu Fati kwance Kudundune alamar sanyi take ji. Umma ta isa gare ta da sauri.
“Fati me ya same ki?”Umma kaina ke ciwo”
Umma ta taba kanta zafi, nan da nan ta
debo ruwa da wani farin karamin tawukl ta
dinga goge mata jiki da goshi, cikin sa°a ta ji
sauki. Ranar dai haka Umma ta kasance da ita
har safiya.Faruk kuwa yana isa gida dakin shi ya
zarce, ya yin da hotonan Fati ke baje a gun, nan
ya dinga ganin hotunan Fati a zama mashi Fati. Faruk fa ya rude, hatta kujera ganin ta yake
kamar Fati Maryam ganin shiru har yanzu Faruk bai Ieko ta ba yasa ta fita ta duba shi, don kuwa
kullum yana zuwa duba ta kafin ya kwanta, duk
da ba abin da ke hadasu amma haqqinta kam ba
wanda baya ba ta. Jin motsin tana zuwa yasa
Faruk tashi da wuri ya tare ta don kuwa in ta
shigo dakinsa komai zai iya dagulewa.
Kura mata ido ya yi, sanye take da rigar
bacci irin ta Fati, sai ya dinga ganin Maryam na
zama Fati. Ita kuma ganin yana kallon ta yasa ta
dan yi murmushi ta ce,Dama na dauka baka
dawo bane?”sai ta juya. Faruk ya bita da ido har
yanzu a fati yake ganin ta, sai ya isinci kanshi da
binta. Maryam na kwance kawai taga Faruk
kwance bayanta tamkar an jeho shi, mamaki ya
kama ta ganin ya matso kusa har ya yi kokarin…
Can Faruk ya dawo hayyacinsa, hankalinshi ya tashi ganin Maryam kwance a Kirjinshi kuma dukkansu a yanayi na ma’aurata. Ya yi saurin tashi zumbur tamkar wanda aka mintsine shi. Fati ya kira sunan da Karfi, yayin da Maryam ta Kura mashi ido. Don kawar da zargi a zuciyar Maryam, Faruq ya yi murmushin dole ya fice daga dakin.
Bayan gida ya nufa ya sakarwa kanshi
shawa, ya yin da ba za ka gane wanne yafi ” gudu
tsakanin ruwan shawan da hawayen Faruk ba. Ba
abin da ke idonsa da ransa illa tsananin bakin
ciki da bacin rai, wannan yana
nufin yaci amanar Fati, shi da ya yi alkawari jikinshi bai taba wata mace sai Fati, shine yau ya karya alkawari.Karfe goma Fati ta yi shirin tafiya Kano da iyayenta, don jirgin Karfe daya za ta bi zuwa London karatu, ita da Umma da Abba za su tafi, ya yin da sauran yan rakiya za su yi.
Faruk na zaune a falo a bangarensa,
Maryam ta shigo ta gaishe shi, ya amsa ba tare
da ya kalle ta ba. Ta ce,Ga can break fast a
table””To”Ya ce mata kawai ta fice, ta zauna a
dinin table din tana jiran shi, ya yin data kifa
kanta ta dinga tunani barkatai. To ko Faruk din baya sonta ne? To meke damun shi, ko akwai wadda yake so ne aka hana shi? Haka ta yi ta tunani kala-kala. Can ya fito yana dai zaune a kujera, amma bashi da niyar cin komai.
Maryam tace Asa mane?”Barshi kawai nama koshi” Tana shirin fadar wani abu ne
wayar hannunta ta yi kara, ya yin da shi kuma ya yi shirin tashi. Cak ya tsaya saboda sunan da ya ji
Maryam ta kira.Fati kina ina? Haba Fati ashe kin san yau za ki tafì shi ne ko ki gaya min , ba wani Abba.ke dai kawai shi kenan ba zan yi hakurin ba, ki tuna Nigeria gaba daya zaki tsallake shine bara
kizo mu yi sallama ba, ni da kin gaya min da naZo ba komai Kanwata na yafe miki baki min
komai ba, na yi hakuri. To zai ji, zamu kawo
miki ziyara. O.h good luck and bye-bye”
Jawota ya yi da Karfi,Ina Fati za taje?”
Nan Maryam ta labarta mashi.
Oh my God!” Ya fada da Karfi ya yin da
ya zari key ya fita da mugun gudu. Maryam ta
bishi da ido.Faruk ya dinga sharara gudu a titi tamkar zai tashi sama, awa biyu cikakku suka sada shi da Kano. Karfe daya saura minti goma ya isa airport, ya yin da ya shiga neman su Fati shiru bai gansu ba har karfe daya ta cika, lokacin ya ji ana announcin matafiya su zo su tafi.
Lokacin ne ya dinga raba ido. Can kuwa
ya hango su suna shirin shiga zuwa gun asali,
inda jirgin yake. Kwala mata kira ya yi ta yi,
dukkansu suka tsaya cak! Yayin da Faruk ya iso
inda suke, bai damu da iyayensu dake tsaye ba
kawai fisgar Fati ya yi.Haba Fati, me yasa za ki min haka, ya ma za ayi ba shawarata kawai za ki tafi? Ya ma za a yi ki tafi ki barni?”
Abba ne ya katse shi ya buga mashi isawa,
“Sake ta na ce
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe