DANGIN JUNA BOOK 1 CHAPTER 6 BY SA,ADATU WAZIRI GOMBE
Shiru Amin din ya yi, alamun yana tunanin wani abu. Tunanin haka Faruk ya yi saurin katse shi, “Shin Amin wai yaushe za ka yi aure ne, ko sai ka tsufa ne a haka?” Yace Ni yaya Faruk nesa tazo kusa, don kuwa daf da yin aure nake, yanzu yardar yarinyar nake nema Faruk yace “Wacece haka?”Haba Yaya, in je in gaya maku taqi yadda ku min dariya?”Faruk yace”To in ta yi tsami ma ji
Kaf zuriyar gidan ba wanda ba ai wa biza ba, hatta Baba Iro da matarsa suma za suje gun Fati. Sannan Habib da Abida ma haka, yaya babba ne kawai ba za taba, nan ma dan ba ta da ishasshen lafiya ne A gaskiya sunyi niyar yiwa
• Fati bazata. Fati na yaune ta zuba uban tagumi sai hawaye, a gaskiya karatun ma ya : soma gagararta. Tunani barkatai take wanda ita kanta ta kasa barin kwakwalwarta ta yi tunani daya, na iyayenta ko na Ummúnta ko su Baba Iro da Abbanta, ko uwa uba Faruk. Nan take tasa hannu aka ganin
Kwakwalwarta na-juyi. Hajiya Aysha.ce ta dafa ta, “Lafiya Fati meke damun ki?”A gaskiya Hajiya Aysha ta tausaya mata duk da ba ta san meke damun ta ba. Ta ci gaba da. shafar kanta gami da rarrashi, »Yar gidan Umma me ya same ki? Ba zaki gaya min ba?”
Fashewa tayi da kuka ta ce, “Wallahi Momi ba ma abin da baya damu na, ni dai gida kawai zan koma” Lallashinta ta yi ta yi, “Ki yi hakuri kinga yanzu jarabawa kuke kun kusa hutu sai ki je gida ko baby na” Fati dai ta jita ne kawai ta amsa, amma a gaskiya tana ga ita kam ta ajiye karatu, damuwar da ke kanta ya fi karfin karatu.
Washegari da safe tana kwance kan gado
Tana sharbe, Momi ta riske ta,
“Tashi kiyi kwalliya na san dai kin yi wanka kuma ki canza kayanki” Nan taciro mata wasu navy blue riga da wando yan Dubai, sai dai rigar iya cinya ce ba doguwa bace Sannan wandon ta sama tsuke yake, sannan ta kasan a bude. A takaice dai an mai shape ya masifar mata kyau, ta yafa dan siririn gyale gami da sa takalmanta covers.Matsalar Fati na daya shi ne ba fara’a a fuskarta. Momi ta kalle ta, “Kin yi kyau fati amma saki fuska mana”.
Murmushin dole kawai ta yi suka fita, window suka nufa kasancewar gurin sanna rufe ma Fati ido ta yi sannan ta bude mata, hango family dinsu ta yi dukkansu tsaye banda mutum daya.
Wani irin kara ta saka mai firgita duk wata halitta dake gun, da mugun gudu ta sauko., gun
Umma ta wuce kai tsaye ta rungume ta sosai
“Ummana ni dai ba zaki tafi ki bani ba binki zanyi’
A hankali ta ji ana shafarta ta baya, •yaya Maryam ta gani suka rungume june. Dukkan su kuka suke, Maryam dai zamu iya cewa kikin murna take, amma ba mu san Fati ba. Dole tasa ya bar harabar gun, saboda yana tsananin kunyar hada ido da Fati. Yadda ya dinga nuna mata baya sha’awar auren Maryam shi ne ga shi har da da.
Dafata ta ji anyi ta juya da sauri, wanda ta gani tsaye bayanta yasa ta mika ma abu Faruk Junior da wuri ta mike, tsayawa ta yi tana kallon shi kallon mamaki. Yaya Bature yaushe ka dawo? Kai ne kuwa? Kai ne yayana? Shine kaje kaqi dawowa da wuri?”Ta juya ta dan tura baki, “Na yi fushi” Ya sha gabanta, “I’m sorry my sister”.
Nan take ta juyo suka rungumi juna suna tsananin murna. Zuciyar Faruk kam ta yi baki, ya yin da ta dinga bugawa tamkar za ta balle, nan take maganar Goggon Kirfi ya fado masa, da dan nan zai yadda sai ya auri Shubuna, wannan yasa bugun zuciyarsa ta tsananta. A take ya bar gun don idanunsa ba zasu jure ganin Fati rungume jikin wani ba. Sun dade suna hirar yaushe gamo. “A gaskiya Yaya Bature ka Kara kyau da fari, kaga