DANGIN JUNA BOOK 1 CHAPTER 7 BY SA,ADATU WAZIRI GOMBE

DANGIN JUNA BOOK 1 CHAPTER 7 BY SA,ADATU WAZIRI GOMBE

 

 

yadda ka hadu kuwa? Ai sai ka sa ‘yan mata karo

Gaba daya aka kwashe da dariya. “Fati ai ba karo ba, ko tunkure-tunkure ne ni na mace daya ne”

Cik in sauri ta kalle shi, “Who’s that lucky girl?”

“Kar ki damu za kiji koma wace ce

Abba ne ya katse hirar ya tambayi “Shin wai ina Faruk ne?”Cikin hanzari Fati ta juya, “Dama da shi aka z0?”

Umma ta amsa “Tare muka zo, sai dai dama ya yi fushi dake don kin taho bai sani ba”.

Cikin doki fati ta sake tambaya, “To ina yake in je in ba shi hakuri?” Mohd ya yi karaf ya ce, “Na ganshi dazu a waje a bakin swimming pool na kofar gida yana zaune shi daya”.Ba ta saurari komai ba ta nufi waje da mugun gudu, ita ma ta rasa me yasa take son ganin shi.

Tsaye yake bakin ruwa ya harde hannuwansa a Kirji idanuwansa sunyi ja, sai dai boye yake cikin farin glass dinsa. Bakar T. Shirt ce da bakin jeans, duk wanda ya hango shi a yadda yake sai ya yi masifar sha’awarsa saboda tsabar kyau da yayi da gurin, da kuma yanayin gurin.Sai dai kallo daya zaka ma kwayar idonsa ka tabbatar yana dauke da buhu-buhu na damuwa. Da mugun gudu ta isa ta ba shi kyakkyawan runguma ta baya, ya yin da Kirjinshi ya ci gaba da bugawa a tunaninsa mafarki yake ko jikinsa ke zolayarsa.

Fati rungume da shi da sauri ya juyo suka

Kurawa juna ido, ya yin da dukkansu suka sakarwa juna murmushi. Lokacin da ya kuma murmushin ya koma kuka.

Cikin sanyin murya mai cike da kuka ta soma magana, «Yaya Faruk na tayaka mura da Karuwar da muka samu, Allah raya Faruk.

Sannan yaya ka yi hakuri saboda tahowa da na yi ban gaya maka ba” Murmushi da kallon da ya mata ya tabbatar mata ya huce. Yana shirin fadar wani abu Amin ya iso yace Sorry for the interruption

Fati ce ta jawo hannun shi, “Haba yaya

Bature kai ma sai ka shigo ayi hirar da kai, dama ina bawa babban yaya hakuri ne

Al’amin yace Gara ki ba shi hakuri don kin yi laifi

Ta ce, “Yanzu kam ya huce”.

Dariya suka yi duka, ya yin da shi dai

Faruk dariyar ta dole ya yi, don gaskiya ya tsani ganin Fati kusa da Amin. Ita kuma ya lura ta fiye shisshige mashi.Al’amin ya kalli Faruk yace Babban yaya yau na yanke shawarar gaya muku yarinyar da nake so”

Faruk ya yi murmushi, “Ina jinka”.

“Wato yaya Faruk ina son yarinyar sosai, but I’m not sure ko tana sona?”Fati ta yi dariya ta ce,Kar ka damu

Yayana, she will love u. Ka san ka hadu kuwa?” “Fati ai ba kyau ne ko wani abu ke sa so ba, wannan daga Allah ne kin gane?”Haka ne

Faruk ya kalli Al’amin yace “Kar ka yadda ka fada soyayya mai tsanani da mace”.Amin ya kalle shi ya ce, “Why?” Ya amsa masa, “Does who fall in luv shed

tears”Amin ya kalli Fati Wai haka ne kanwata?”

Murmushi ta yi, “Ban sani ba yaya, amma shi da bamu ga yana sharar…..Karaf ya amsa mata,

“Kema kin san na zub da hawaye har hawayena sun kafe, har na koma na zuci. Yayin da na zucin ma yake kokarin kafewa” Amin ya ce, “Amma na ga tamkar kanwar tawa ba ta baka ciwon kai”

“Manta ka ji Al’amin, amma ai har ciwon hawan jini tasa min. Amma fa tsakanin mu ne, ni dai shawara ce duk wadda za ka so ka so ta daidai, don zai yiwu tana sonka kana sonta wani abu ya hana auren kagane?”Haka ne yaya”. Fati ta sake jeho magana karo na biyu. “Yaya Faruk ka manta soyayya bata sallama ba ta neman izini, kawai mutum tsintar kansa zai yi a ciki, kuma dama haka soyayya take”.

Faruk ya amsa “Lallai my dear kin yi magana”

Kura mata ido ya yi tamkar bai taba ganin ta ba. Ganin haka yasa Fati ta ce, “Amin ya kamata ka gaya mana saboda mu shirya, in kuma ba a so na ji sai na shiga ciki”Amin ya amsa, “Ina, ai kece mai ji ma.

Wato Yaya Faruk a tun lokacin da nake gida kafin na tafi cos waje na tsinci kaina da tsananin son Fati

Dago kanta ta yi da sauri ta kura mishi ido alamun mamaki bayyane a fuskarta. Faruk tunda yake a rayuwarshi bai taba jin maganar da ta fadar mishi da gaba irin wannan ba.

Nan take wani gumi ya yanko mishi ya

Tsinci kansa a wani irin bakin ciki da bai ta6a jin irinsa ba, bacin rai ya ziyarci zuciyarsa, wani irin bala’in kishi ya kama shi, nan take jikinshi ya

Hmmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *