DAWUUD
CHAPTER 10
suna sauka direct masauki suka nufa sbd sai washe gari zasu asibitin dama aleeyar amatse take da akai ta kwanta jiri da wani irin rashin sukunin zuciya l take ji sosai dan haka suna isa nana ta taimaka mata tayi sallah a zaune ta kwanta aka rufeta da bargo ko abinci bata iya ciba suna ganin rasamu bacci suka barta dan yanada wuya tasamu bacci.
mum daga airport drop ta dauka asibitin ta nufa kai tsaye suna isa bata sallami mai taxi dinba tace yajirata tukuna ta nufi cikin asibitin tana kallo da mamakin millions of nairas daya kashe gurin ginawa sbd asibitin takai kamar a germany.
reception ta tsaya tareda kallon receptionist din dake gurin sanye da bluee kaya da sunan asibitin ajiki tace,
excuse me..
yes maam hw may i help you?
i’m here to see dr dawood assiddeq.
kallonta ladyn tayi gaso taga kamarsu da dr dawood amma saitace,
do you u have an appointment ne or….
cikin takaici mum ta katseta da cewa,
i’m his mother you idiot,,just tell me ina zangansa before i lose my patience hia.
cikin rawar jiki da sauri tace,
sorry maa rashin sanine dr dawood jst left wit dr jass ko 30min basuyiba.
dafe goshi mum tayi cikin takaici da matsuwar son ganinsa jitake kaman zata zare sbd son ganinsa kasa hkr tayi takalli receptionist din tace,
yaushe kike tunanin dawowarsa?
i dont know maa and yanada wuya yadawo idan yafita irin wannan time din saidai idan da akwai emergency.
give his address its urgent ina buqatar ganinsa yanxu.
kallonta ladyn tayi tace,
sorry maa i cant give you his address banmasan address na gidansa ba…
zaro waya mum tayi ta nemo hotonta inda take da dawood da taheer ta nuna mata cikin zafi tace,
kingani idanma baki yarda yanxu kingani zakiban address dinsa kokuwa saina saka ancire uniform din jikinki.
da sauri ta girgiza mata kai ta tareda rubuta mata address din tamiqa mata tace,
have a gud day maa.
ko kallonta mum batayiba ta qarbe takardar ta wuce tana duba takardar.
miqawa mai taxi din tayi bayan tashiga yana dubawa yagane anguwar da street din ya tayarda mota suka tafi.
basu wani sha wahala sosaiba gurin gano gidan nan tafito ya fito mata da qaramar luggage dinta ta bude jakarta tabasa kudi masu yawa ya wuce ta kalli makeken gate din gidan tareda kallon shirgegen maigadin dake zaune.
kallo daya yayi mata yaga tsananin kamarta da dr da sauri yataso yana mata sannu da zuwa,
mota biyu tagani harabar gidan nan takalli flat hudu dake jere komai nasu iri daya kowanne da sunan mai flat din aqofa,
na farko ne taga sunan maska ajiki saitaji jikinta yayi sanyi na biyun ne taga sunan dawood kobaa fadaba tasan sauran biyun na jass da sufyaan ne ta qarasa jikin na dawood bata tsaya komaiba tayi knocking gabanta na faduwa sbd tasan dole dawood ma bayason ganinta yanxu tunda haryazo yabude sabuwar rayuwa anan batareda yata6a nemanta kosau dayaba.
kwance take apalon bacci takeyi sosai abincin ranama daqyar da lalla6awa yabata fruit tasha yasake fita yabarta nan bacci yasake dauketa.
cikin bacci taji knocking ta motsa daqyar tareda tashi zaune tana duba agogo tana la’asar ta wuce ta miqe tsaye tana saka room slippers dinta ta nufi qofar tana lumshe ido sbd baccin bai isheta ba……
Story continues below

katsewa hammarta tayi wasu yawu suka sarqeta tayi baya da sauri tana tari dosai jikinta na rawa.
mum ma kasa gasgata idanuwanta tayi ta shigo ciki tareda murxa idanuwanta da qarfi tana cewa,
nashiga uku ya allah nafara mugun gani babu alheri atafiyarnan tawa.
tari take sosai kamar zata fita hayyacinta ta zube qasa tanayi nan take idanuwanta suka canxa ga tashin hankali ga tarin yaqi tsayawa kamar daga sama ya diro gidan dan dama tunda yakoma asibiti nuraaat tace mum dinsa tazo tabata address dinsa ya juyo arikice sbd bayajin zai daukarwa mum wata masifar yanxu koba komai baiso kowa yasan inda sukeba saisunxo dakansu.
ganin halinda take ciki yasashi qarasowa da sauri ya dauko ruwa a fridge mai sanyi kadan ya bude tareda dagota jikinsa yabata yana mata sannu kamar yaciro tarin ya kashe,
saidata sha sosai tarin yalafa numfashinta yafara dawowa daidai yana shafa bayanta ahankali yana jera mata sannu cikin wani irin sauti mai kashe jiki.
kasa daukarta qafafuwanta sukayi ta ba shiri ta xube a sofa tana qoqarin daidaita numfashi da nutsuwarta sbd tasamu damar fahimtar abunda ke faruwa akan idonta murya na rawa,
takalli fuskar dawood daya cira matarsa sama yayi bedroom da ita takira sunansa baiko waiwayoba saidaya kaita toilet yayo mata wanka yashirya cikin kaya marasa nauyi ya kwantar yana sake kwantar mata da hankali ganin nutsuwarta na barin jikinta sbd sosai ta firgita da ganin mum har lokacin jikinta rawa yakeyi sosai.
saidaya lalla6ata tadan nutsu yafito gurin mum yatararda ita tana kuka rigis harda shesheka saikuma yaji jikinsa yayi sanyi tsananin so da qaunar mahaifiyarsa tareda tausayinta na taso masa ya tsaya yana qoqarin hana kansa sake mata amma sosai kukanta ke shigarsa ya qaraso ahankali tareda zama kusada ita ya riqo hannunta ta juyo da sauri tareda rungumesa tasaki wani sabon kuka tana qanqamesa.
ganin kukan na neman yawa yasashi dagota yana share mata hawaye yace,
mum please kinsan banason koke koken nan ya isa haka,
girgiza masa kai tayi tareda kallonsa murya a hargitse tace,
mi’amor wacece wannan dakakai daki kamar layla?
ajiyar zuciya yasake ahankali ba kwana kwana kai tsaye yace,
mum layla ce and she’s my wife now…..
arikice ta wanka masa wani gigitaccen mari cikin zaro ido tace,
matar dan uwanka ce fa na shiga uku ni faraah wannan wane irin masiface ta afkomin nida zuriata….
tashi yayi idanuwansa jajir yace,
wannan shine babban problem dinki mum,baki ta6a tsayawa sauraron uzurin mutum koyaushe kedai me mutane zasuce akan the famous faraah assiddeq damien,
farko kinrabani da farin cikina kinsakani auren wadda dagani har ita rayuwarmu ta lalace babu kyakkyawan abun qwarai acikinta,
dan uwana ya auri matarda bata sonsa waninsa takeso suma sunyi rayuwar aure mara maana da qunci qarshe yakusa rasa rasuwarsa duk kece sila mum and still baki sadudaba kina kiran aurena da disgrace mum kinasona kuwa?
riqosa tayi da sauri tana hawaye tace,
my love wlh kaine farin cikina duk wani farin cikinka ina sonsa na gane kuskurena kawai nakasa fahimtar abunda nake ganine yanxu layla matar tahee…..
‘dan uwanka ne wani akan mace?
mum….
shigowarsu sufyaan ne yasashi yin shiru zuciyarsa ba dadi ya wuce bedroom adan hasale.
qurawa jass da sufyaan ido tayi tareda dafe goshi itakam yau tana ganin abubuwan firgitarwa da tsoro tareda ban mamaki,
ganin ta gurgiza sosai da ganinsu sufyaan ya matso tareda zaunarda ita yana qoqarin kwantar mata da hankali ta hanyar kar6ar ruwanda jass ya miqo masa yabata tasha tafara jero ajiyar zuciya.
riqo hannayensu tayi su duka hawayen farin ciki suka gangaro mata na ganin suna raye sbd har cikin ranta take qaunarsu kamar yayanta musammman maska.
cikin sanyin murya datasha kuka tacewa sufyaan,
meyasa idanuwansa suka rufe yakasa fahimtar abinda nakeson fahimtar dashi?
mum kece kika kasa tsayawa ki fahimcesa,
ahankali yafada mata komai nan kunya da sanyin jiki suka hanata ko motsi sbd tasan ta cutatarda layla saidai kam zata koyardasu saraah mugun darasinda bazasu mantataba.
ganin haka jass da kansa yaja kayanta zuwa daya daga cikin bedrooms din palon yakaita yace,
mum have some rest kisamu nutsuwa zuwa anjima tukuna.
ficewa sukai daga palon zuwa nasu
daqyar tayi wanka ta kwanta tayi shiru cikin tunanin abubuwan saikace a film saidai harcikin ranta yanxukam tayi farincikin kasancewar mi’amor dinta da wadda yakeso kuma zata rufe ido ta tsaya tsayin dakan ganin bai sake rasataba saidai ace tayi sonkai amma bazata ta6a bari danta yasake rasa nur ba sbd tagani ta tabbatarda itace farin cikinsa aleeya kam gskia saidai tayi hkr tunda dama yasaketa basuda aure.
da daddare koda sukayo musu ordern dinner daqyar ya lalla6ota ta iya fitowa palon sbd tsoro da fargaba sbd gabaki daya hankalinta yatashi gida take tsananin son zuwa ta fuskanci masifar data riga ta afka mata.
suna fitowa tayi saurin zame hannunta daga nasa ta sunkuyar dakai idanuwanta na cikowa da hawaye.
kallonta yayi zai jawota jikinsa tayi saurin duqawa qasa hawayenta na gangarowa.
mum dake zaune dining ta taso ahankali tareda tayar daita tsaye ta rungumeta cikin tsananin qaunarta tace,
kicire damuwa ina taredaku insha allah komai zaizo da sauqi da fahimta.
janta tayi har dining sukaci abinci kowa hankali kwance cikin farin ciki banda ita da kwata kwata hankalinta yariga yagama tashi zuwa gida da abunda zai biyo baya.
kasacin komai tayi duk yanda dawood dasu mum sukayi saidai tasha ruwa kawai.
mum harda kanta tashiga kicin ta dafo mata noodles da egg amma takasa ci dasuka matsa mata ma kawai sai amai tayita kelayawa nan hankalinsu yafara tashi sbd sunsan tariga tasawa kanta damuwa da fargabane.
hakanan ya lalla6ata sukai sabon wanka suka kwanta yana shafa bayanta.
daqyar yasamu bacci ya dauketa shima sama sama yayi baccin sbd jin jikinta yayi zafi sosai alamar zazza6i mai qarfi yashigeta.
da asuba zazza6in ya sauka sosai sukai sallah ya jawota jikinsa ya zare mata hijabin datai sallah yakalli fuskarta data qara masa kyau ya shafo fuskar zuwa wuyanta qirjinta har zuwa cikinta ya sauke numfashi ahankali.
lumshe idanu tayi ahankali tareda dagowa ta kalli fuskarsa yasakar mata kasalallan murmushi qasa qasa ahankali yace,
i love you my angel.
lumshe ido tayi sbd yanda zuciyarta ta kar6i zancen,
hade fuskokinsu yayi yana goga hancinsu ahankali kafin ya hade bakinsu yafara kissing dinta cikin sanyi.
sosai yayi making love da ita cikin farin ciki da jin dadi dakuma sabuwar soyayyarta da kullum ke qara shigarsa musamman yanxu dayake jin alamar jininsa atareda ita.
wanka sukayi ya shiryata shima ya shirya sbd tare zasu asibitin zazza6inta yadawo dakuma jiri datakeji yanxun,
mum ma shiryawa tayi suka nufi asibitin tare bayan sunyi breakfst duk da dai still bata iyacin komaiba sbd sosai takejin rashin sukuni da fargaba.
shiya bude mata mota tashiga ya
rufe ya budewa mum itama ta shiga suka fice motarsu jass na bayansu.
suna isa kowannensu office tun a receiption aketa kawo gaisuwa sbd mum da kuma matarsa dakowa ke muradin gani sbd sunanta dake jikin asibitin,
wani emergency aka kirasa yakalli dr divya data qaraso yayi mata bayanin dubamasa matarsa dazatai ya wuce da sauri bayan yayiwa mum sidehug.
babban office din dr divyan suka shiga nanta kawowa mum drink daga fridge takoma ta zauna tana facin nur dake zaune kan kujerarda take duba patien tafara yimata tambayoyi cikin sakewar fuska.
sunjima tana dubata kafin qarshe tayi mata scanning cikin tsananin farin ciki mum ke kallon tvn takasa rufe bakinta dr divya na qara yimata bayani cikin tayasu murna.
duk inda tashin hankali da furgici yake tashigesa jin cikine ajikinta
jikinta har wani rawa yakeyi ta tashi zaune mum data lurada halinda take ciki tayi saurin riqota suka zauna tafara qoqarin kwantar mata hankali amma ina tayi nisa sosai take neman rikice mata dole saida suka hada da kiran dawood.
tunda suka shigo asibitin gabanta yayi mugun faduwa dr aqeel dakansa yafito yashigo dasu suka nufi office dinsa kamar gixo taga giftawar wani kaman dawood ta rufe idonta ta bude taga tabbas kamar shi dinne ta zame hannunta cikin na ammy ta nufi inda taga yabi tana tafiya ahankali sbd rashin qwarin jiki abba da dr aqeel tuni suka shige office ammy da nana suka bita da sauri,
a hanzarce ya qaraso office din suka hade a qofa dr divyan zata fita wani emergency call fuska cikeda farin ciki ta miqa masa hannu cikin dariya tace,
congratulations dr your wife is pregnant.
hannu ya miqa mata cikin tsananin farin ciki yace,
thank you dr.
wucewa tayi tana cewa,
tun yanxu angel dinka tafara tsoron haihuwa fa.
wani mummunan jirine ya dibi aleeya dake tsaye bayansa jin abinda dr tafadawa dawood.
bude office din yayi yaga mum nata faman bata baki yasan gaban mum zataji nauyi ya jawo hannunta yana cewa,
two minutes mum.
suna fitowa ya jawota jikinsa yana murmushi yakai fuskarsa daf da tata tareda kamo face dinta…..
ALEEYAAAA”” sukaji anfada bayansu da qarfi,
a firgice suka juya kusan atare idanuwanta suka sauka kan ammy da nana dake qoqarin riqo aleeyar.
zame jikinta tayi daga nasa jikinta na wata irin rawa,
ammy da nana riqe kawai sukeda aleeyar amma laylar suke kallo cikin tsananin mamaki da tashin hankali daqyar ammy ta iya bude baki murya na rawa tace,
la…y..la,
hawayen idanuwanta dasukai jajir ne suka sauko ta daga qafarta daqyar zata matso aleeya tayi saurin qwacewa dagasu ammy tayi baya tana kallon dawood dake qoqarin riqo hannun layla ganin tana tangadi fuxge hannunta tayi tana kallon fuskar aleeya dake qoqarin juyawa.
riqota ammy tayi tana cewa,
aleeya kinmanta bakida lafiyane kibi ahankali,
fixge hannunta tayi zuciyarta na wani irin zafi da tafarfasa gaba daya ta dainajin ciwon datakeji sbd quna da zafin da zuciyarta ke mata tasake juyawa zata bar gurin tun kafin ta 6aci tsakaninta da layla sbd batason tacigaba dajin zafin datakeji akanta,
ammy ta riqota da qarfi tace,
aleeya ki nutsu mana ina zaki jiri na dibarki haka…..
cikin zafi ta juyo tareda qwace jikinta afusace tace,
mezan saurarawa?
ciwon danazo dashi ajikina wanda nakeyi sbd wainda basusan inayiba ko kuwa wannan abun dayake faruwa gabana yanxu zan saurarawa?
layla da dawood nakewa wannan ciwon ammy,
na rasata anawa tunanin,
shikuma bansan wane halin yake ciki ba sbd hakan ne muke asibiti yanxu dan haka saimu koma gida tunda gashinan munga suna lafiya cikin kwanciyar hankali ciwona ya qare daga yanxu…..
wani irin kuka mara sauti layla tasaki jikinta na tsananta rawa ta qaraso gaban aleeyar da sauri aleeya tayi saurin rintse idanuwanta tareda juyawa tabar gurin da sauri sauri gudu gudu tana qoqarin danne kukanta dake son faso qirjinta sbd azabar zafi.
da gudu ta isa jikin motarsu bilal na ganinta ya fito da sauri ya riqeta ta qanqamesa jikinta na rawa tace,
bilal fitar dani daganan yanxunan numfashina zai bar zuciyana..
da sauri yasakata mota yatayar suka fice layla na qarasowa suna barin gurin taxi ta tsayar tafada tabi bayansu idanuwan na qara rinewa jajir sbd kukanma ya tsaya sai radadi idanuwan kemata har lokacin jikinta rawa yake sosai aleeya kawai takeson ta fahimceta sbd bazata iya daukar ganin tsanarta a idon aleeyaba.
suna isa gida ta fito motar da sauri ko gani batayi sosai tayi ciki ta fada daki tareda rufewa ra sulale qasa tareda sakin kuka mai qarfi kozataji abinda ya tsaya mata aqirji ya fada,
tana shigowa harabar gidan su ammy da nana nashigowa bilal na ganinta ya qaraso da sauri cikeda tsoro da tsananin mamaki da fargaba harzai ta6ata ya tsaya cak tareda qura mata ido sbd tuno halinda aleeya ke ciki hakan na nufin layla tagani shima wani zafi yaji azuciyarsa ya juya cikin tsananin jin zafin laylar yabar gurin batareda ya tsaya sauraron kiran da ammy ke masa cikin tashin hankaliba,
sake shiga sabon tashin hankali tayi ganin halinda take shirin shiga yasa ammy riqota suna shiga dakin aleeya ta miqar da aleeya tsaye tareda kallonta cikin tsananin fargabar halinda taga aleeyar tashiga lokaci daya tabbas tasan layla takai qololuwar aikata babban laifi saidai bazata nuna hakanba yanxu sbd aleeya tadau zafi idan itama ta nuna nata zafin lalacewa kawai abun zaiyi cikin daga murya tace,
aleeya duka wannan abun mu tsaya muji komai tukuna…..
cikin zafi da daga murya ta miqe tareda kallon ammyn tace,
Story continues below

mekikeson naji ammy ne?
i’ve suffered enough,,abu daya kawai nakeson ji yanxu shine meyasa kikeson na saurara ammyn bayan komai yazo qarshe.
ba haka bane aleeya NUR DA DAWOOD sunason juna tun kafin aurenku dawood shine dr dawood din layla….
wani sabon kallo aleeya tasakarwa ammy kamar zautacciya qwaqwalwarta na juyawa tanaci gaba da jin sauran bayanan ammy tun farko har qarshe sai kawai taji wani mugun jiri ya de6eta layla tayi saurin riqota tana juyowa bata tsaya komaiba ta saukewa laylar wani gigitaccen marinda yasatayin baya daidai isowar dawood yayi sauri riqota tareda bude baki afusace zaiyi magana cikin wani irin karaji da fushi aleeya ta nunasa da hannu tace,
stay out of this wannan is between me and her nobody will interfare tana buqatar amsa dukkanin tambayoyina ayau sbd daga yau THERES NO MORE ALEEYA AND LAYLAH,,,,
afirgice kowa yakalleta layla kuwa kuka tasaki na tashin hankali tareda matsowa jikinta na tsananta rawa cikin wani irin yanayi takalli laylar tace,
meyasa kika za6i ki rusa rayuwata ta hanyar bari na auri wanda baya sona bita6a sonaba,kinta6a tunanin rayuwar qanqancin dazanyi idan na auri wanda wata yakeso baniba….
cikin tsananin kuka layla murya na fita daqyar tace,
duk abinda zanyi sbd farin cikinki nakeyinsa……
wasu hawayen takaicine suka saukowa aleeya tace,
abinda baki saniba shine kin rusa duk wata rayuwar farin cikina laylah,
wlh kozan rasa raina bazan bari ki auri wanda nasan bazakiyi daraja agurinsaba koda kina sonsa sbd qaunar danake miki tafi haka,
amma me kikayi ta hanyar 6oyemin kina kallo na auri wanda zanyi rayuwar qunci agidansa har abada sbd babu so,
qarin abin haushinma ashe duk wannan quncin danakeyi kina sane da mafitarsa kika za6i ganina acikinsa shin wace irin muguwar qiyayya da qaddara tafi asaki mace ranarda aka kaita gidan aurenta
amma ni aleeya sbd tawa qaddarar daban take tasakani tsananin son mutane biyu dabasu cancantaba
adaran da aka kaini adaren aka sakeni sbd ke NUR,
nayi kuka agabanki nayi abayanki,
nayi rayuwar qunci agabanki nayi abayanki kina saneda akwai mafutar quncina kika za6i kiyita ganina ahaka menayi na cancanci haka NUR karki cemin sadaukarwa ce sbd sam babuta anan……
tsawa ammy ta daka mata ta tsayarda ammyn da cewa,
ammy ayau babu mai magana nice zanyi magana sbd nice aka taru aka rusawa rayuwa,
menayi dana cancanci haka daga wainda nakeso fiyeda komai….
meyasa kika za6i dawood akaina layla meyasa,,,,
meyasa zuciyata ta ringa azabatardani akan wainda suka za6i junansu akaina shin dama so yana zama haka,,
riqota bilal yayi da sauri ganin yanda take kuka sosai kamar numfashinta zai bar jikinta hawayen tausayinta yakeyi sbd tabbas ancutatarda ita ta hanyar qyalewa ta auri wanda baya ko qaunarta shima harcikin ransa ayanxu jin zafin layla yakeyi,
qanqamesa tayi tana tsananta sautin kukanta sbd wani irin radadi da zafi takeji cikin ranta akan layla,
kukanda layla keyi shiya daga hankalin mum da dawood sukayo kanta ganin yanda take jan nunfashi tana kuka
ammy ma hawayen takeyi ga nana dake kuka sosai na tausayinsu su dukan,
rarrafowa tayi gaban aleeya cikin tsananin rudani da kuka tace,
aleeya karki rabu dani kiyimin hukunci daidai yanda zuciyarki zata huce amma wlh banta6a fatar qunci ko damuwa ba ko akan takalminki bare ke,
aleeya narabu da dawood har abada idan hakan zaisa kifahimci banida niyar quntata miki bazan qara ganinsaba na….
wata mahaukaciyar tsawa ya daka mata cikin tashin hankali da tsoron abinda take fada yace,
har abada babu mai raba dawood da nur duk maison fahimtar hakan ya fahimta wanda bayason fahimta dole zai hkr meyasa kunkasa fahimtar abinda nakeso……
wani kallon baqin ciki da takaici aleeya tasakar masa zuciyarta na qara zafi tabbas sone yasa aka dade ana cimata fuska tazama wata wawuya atsakani amma anyi angama koda kuwa sonsu zai kasheta cikin yanayi na rakaici ta katsesa da cewa,
kallon cikin idonta layla tayi da sauri aleeyar ta juya ta fada bedroom tareda rufowa ta sulale qasa tasaki wani irin kuka mai tsananin qarfi daya daga hankalinsu ammy da mum da bilal dakejin quncinta harcikin ransa sbd tamkar uwa daya uba daya yakejin qaunar aleeya ajininsa.
kuka takeyi da qarfi sosai sbd bata ta6ajin zafin datakejiba a qirjinta yanxu jitakeyi kaman ta hadiyi zuciya ta mutu,,
sonsu su biyun ajininta yake saidai har abada ta yafesu sbd suba alherineba arayuwarta they hurt her so deeply morethan she can take,
kukan datake duk iya qarfinta ya daqa hankalin kowa cikin wani irin mugun yanayi layla ta miqe cikin wani irin mugun yanayi ta fice gidan dawood yabi bayanta da sauri saidai yana fita tana shigewa texi ‘dinda ta tsayar sukabar gurin da gudu.
arkice ya juya ya shiga motarsa yabi bayansu jikinsa na wata irin rawa sbd tuni zuciyarsa tafara bugawa da qarfi.
wani irin mahaukacin gudu yakeyi yana duba gabansa sosai sbd sosai motarsu tayi masa nisa yana kaiwa round trafficlight ta tsayar dashi kota kanta baibiba ya wuce da gudu daidai lokacinda aka sako wasu motocin nantake sukai wani irin karo kankace me tuni gurin ya rikice da holdup wasu nata zaginsa bai tsaya sauraronsuba ya bude motar da sauri yafito yana kukkutsasu harya fice cikinsu yaga ko alamar motarsu laylan ya dafe goshinsa tareda rufe ido cikin wani irin mugun yanayi na tsoro da fargaba.
wani police ne yazo ya tsaya agabansa yanata faman zuba masa fada akan holdup daya hada ahankali ya juya yashigar motar yafara matsawa har hanya tafara samuwa nan gurin yafara sakewa yasamu hanya ya dauki hanyar gidansu da gudu,
yana isa su sufyaan na harabar gidan sunata faman kiransa,
yanayin shigowarsa da parking dinsa yatabbatar musu da babu lafiya nufarsa sukayi kowanne na qoqarin tambayarsa amma baimasan sunayiba saidai ya nufi flat dinsu ahargitse ya dudduba koina bata nan yafito harabar gidan yana qoqarin sake fita jass ya riqesa cikin daga murya yace,
wai bakajine,menene yake faruwa ka kasa fadamana duk kasa hankalinmu yatashi?
kallonsu yayi da jajayen idanuwansa wani irin zafi na tasowa daga zuciyarsa yace,
dafe goshinsa yayi yana sakejin ciwo cikin ransa,
ganin kamar yana buqatar taimakonsune yasa suka dunguma yawon duk wani motopark da stations nemanta amma babuta babu mai kamada ita nan hankali ya qara tashi mum tun tana daurewa kasawa tayi ta miqe ta fita nema itama sbd harga allah tasamo danta ya daidaitu daqyar bata fatar akoma inda aka fito,
ta yarda tabi sai layla.
har dare suna abu daya amma babu alamar zaa ganta,
hankalinsu bai qara tashiba saida sukaga dawood na neman shiga wani hali babban abinda yafi jijjiga duniyarsa shine sabon sonta da dansa ko yarsa dake cikinta,
duk yanda sukaso dawowa gida har gobe qiyayi haka suka raba tsakiyar dare suna nema shiga tashin hankali,
asubar fari dole suka dawo gida jiran kira daga stations dinda suka bayarda reports reports,
duk yanda mum taso ko ruwan coffee yasha yakasa sha gashi har wani jiri jiri yake gani daqyar yayi sallar asuba ya sulale yaqara ficewa basu saniba.
duk yanda taso bawa zuciyarta dangana da rarrashi saitaji takasa sbd mutane biyune data fifita qaunarsu fiyeda komai suka taru suka karya zuciyarta da yardarta akansu,
tanason dawood so mai tsanani data za6i zaman rayuwar qunci agidansa sbd sonsa kuma ta shirya hakan har qarshen rayuwarta saidai duk sonda take masa tafison laylanta fiyedashi meyasa layla taza6i 6oye mata komai?
zata iya bawa layla jininta da qodarta bare abinda takeso amma suka za6i baqanta mata fiyeda fada mata komai tun farko,
dafe zuciyarta tayi tana cigaba da rero kukanta sbd qunci da zafi takeji sosai cikin ranta idan har haka ake sadaukarwa to itakam tata batazo mata a dadiba don kuwa nata cutatarwane,ancuceta anbarta tana jinyar banza abanxa.
tun tana kukan da qarfi harta koma ta lafe saidai hawaye,
abba daya dawo yana fada sosai akan sunbarosa asibiti batareda anyi abinda akaje yiba cikin sanyin murya da fargabar yanda zai dauki zancen ta zayyane masa komai,
shiru yayi yana jujjuya zancen cikin zuciyarsa kafin yasake ajiyar zuciya yakalli ammy cikin sanyin murya yace,
wannan alamari tabbas qaddarane sbd matar mutum hausawa sunxe kabarinsa ce saidai duk muduka amatsayinmu na iyaye munyi kuskure musamman keda kike uwa mace kuma kinsan komai amma kika qyale,
datun farko kin fadamin koda baki fadawa aleeyarba saimu samu mafitarda zata 6ulle bakamar irin wannanba,
Story continues below

share hawaye aleeyar tayi tareda zamewa ta kwanta jikin ammy murya na rawa tacigaba da cewa,
har cikin raina bana buqatar layla ayanxu ina buqatar zuciyata tasamu sarari tukuna sbd ganinta yanxu naqarawa ciwukan zuciyata zafi.
shafa kanta ammy tayi cikin muryar banhkr tace,
aleeya ki yarda babu wata qauna ko soyayya aduniyarnan datafiki agurin layla,
layla namiki qauna irin wadda kike mata sbd tun asali komai datayi tayine sbd taza6i rabuwa da wanda take tsananin so sbd ke,
ta za6i yarda da auren qaninsa sbd ta haramtawa kanta wanda takeso duk sbd kene,
wannan cikin na jikinta isharane sbd allah yayi da akwai rabo atsakaninsu koda aure kobabu aure dole zaa samesa tunda allah ya qaddara to maixai hana mu taru mu rungumi qaddarar gabaki daya.
shiru tayi tareda rufe idanuwanta ahankali zuciyarta na qara nauyi.
ammy anan ta kwana gurinta tana qara fahimrarda ita kuskuren dasuka taru suduka suka tafka.
baidawo gidaba saida su jass suka fita nemansa hankali ba kwanceba,
koda suka dawo gida wahala da yunwa tafara zabgesa wuni guda,
mum kuwa tayi jimamin tayi kukan zuci acikin kwana na uku tuni kukan fili yafara bayyanar mata sbd masifar data hangowa kanta kan ‘danta,
duk iya nema da bincike anyi babu nur babu labarinta tun abu na sauqi sauqi haryayi zafi abba dakansa yafara nasa aikin sawa nemanta hankali tashe
ammy ma kam rashin hankali yadawo sabo ganindai ta tabbata ba’aga laylaba ta 6ata,
duk yanda aleeya takaiga daurewa abin cinta yake cikin ranta da jikinta sbd wata irin rama da lafiya data fara qaurace mata babu layla ga dawood kwance sosai babu lafiya,
bilal kam kallo daya zakayi masa kasan baya cikin kwanciyar hankalin 6atan yar uwarsa ga aleeya ma dayake gani yana rage kewar layla batada walwala kwata kwata yanxu kullum tana daki,
cikin sati biyu alamari yayi tsanani kullum cikin yiwa dawood allurar bacci ake har taso fara ta6a masa qwaqwalwa suka daina yimasa aikuwa nan take ciwo yadawo sabo babban abinda yafi daga musu hankali shine mugun ciwon cikin dayakeyi sosai nan suka duqufa bincike suka gano giyar dayayishace abaya ta ta6a masa qoda nan suka duqufa magani amma kamar basayi,
sannu ahankali damuwa da quncin dasuka fito yafara dawowa kamar da,
mum duk ita inda tashin hankali yakai tana ciki tayi kuka har idanuwanta sun rikide
lokacinda abun yayi tsanani hankalinsu jass yatashi suka sanarda dad da taheer halinda ake ciki nan take dad ya shiryo zuwa yazo duk yanda mum taso yaqi bari tagansa yayi iya kwanakinsa suka wuceda dawood din sbd aikin dazai masa acan.
bayan tafiyarsu kullum ammy agidan take wuni itada nana suna rage mata damuwa,
aleeya sosai take jinyar kanta amma haka ta daure tashirya taje gurin mum din aranar data dawo gida tayi kuka sbd ganin ko yanxu rayuwar mutane da dama na neman lalacewa ta sanadin rashin layla to idan wancan karon laifin layla ne yanxu nawaye?
anyi masa aiki cikin nasara saidai sosai yadaga musu hankali gida yakeso su koma kar layla tadawo bayanan,
hakanan suka tattaro suka dawo dashi aka dora jinyar anan,
sannu ahankali ciwo ke cinsa babu abinda yake fata ayanxu irin mutuwa sbd yatabbarda soyayyar layla itace ajalinsa,
zafi da ciwo mara sassauci yakeji cikin zuciyarsa matuqa,babu abinda yakeson gani irin laylarsa sbd duk inda take ayanxu ta haife cikin dake jikinta da wata daya,
rufe idanuwansa yayi ahankali yabudesu ciki azabar ciwo wasu irin hawaye masu dumi suka gangaro masa tabbas nur itace rayuwarsa.
tari yayi ahankali mum tamiqa masa tissue yarufe baki yana tarin yana dago tissuen ahankali yaga jini ya lumshe idanuwansa daqyar cikin azaba tareda 6oye tissuen kar mum ko su jass sugani,
hankalinsu baqaramin tashi yayiba ranarda yaringa kwararo aman jini nan suka kwashesa sukai asibitinsu,
lokacinda sukaga result din bincikensu akansa kuka sosai jass yazauna yanayi sufyaan na qoqarin danne nasa gurin lallashinsa sbd sun sadaqar da shima rasashi zasuyi kamar yanda suka rasa maska tabbas dasun tabbata marayu idan babu maska babu dawood.
tsawon wata hudu da dawowarsu babu siyama babu dalilinta ga ummanta ta daga musu hankali da koke koken nemanta nan hankalin ammy yasake tashi ga abba sosai hankalinsa ke tashe gurin ganin ansamo inda layla take kusan shekara kenan babu labari,
tareda abba ayau suka sauka porthrct direct headquatr suka nufa gurin jin bayaninda akakirashi akansa cewar antsinci gawar wata mata da jariri sabo.
wata mummunar sarawa kan aleeya yayi tayi saurin jada baya tana qoqarin zubewa daidai kawowarsa shima ya iso hankali tashe jin kiranda akai musu kan case din nur.
fado masa tayi idanuwanta na qoqarin rufewa jikinta nason saki,
riqeta yayi dakyau tareda cewa abasa ruwa masu dan sanyi,
miqo masa abba yayi jikinsa na rawa,
kadan ya zuba mata amma ko alamar motsi babu atareda ita nan abba ya rude suka kwasa asibiti hankali tashe,
bayansu yabi da kallo ahankali tareda kallon qaramin gyalan doguwar rigar dake jikinta da akabari ajikinsa,
nauyi yaji azuciyarsa akaro na farko daya ta6ajin hakan ya dafa zuciyarsa ahankali tareda qurawa gyalen ido yana sauraron abinda ake fada masa kan gawar daaka tsinta,
shiro yayi cikin tsananin tashin hankali yafito yanufi gida yana tsoron fadar zancen kar dawood yaji gashi tun jiya yana asibiti jikin yatashi sosai cikin dare,
yana isa asibiti kallon sufyaan dake daurawa dawood jini yayi ya girgiza kai idanuwansa na cikowa da hawaye.
lokacinda ta farfado kuka takesonyi amma yaqi zuwa tsabar tashin hankali da firgicin datake ciki.
zaidai jajir da idanuwanta sukai lokacinda abba zaije dubo gawar saidai yakaita gurin mum dan harlokacin bata dawo daidaiba,
kallo daya sukaiwa juna itada mum suka tausayawa kansu nana datuni aka barwa mum ita ita tayita fama dasu ko ruwa daqyar sukesha har abba yakira yasanardasu ba gawar nu bace,
washe gari aka dawo da dawood gida ana shigowa dashi palon idanuwanta acikin na jass suka fara sauka kusan atare suka dauke fuska kowanne babu walwala,
shikuwa dawood baisan wayene akansaba harlokacin,
ganin halinda yake ciki yasake girgixa kwanyarta tayi kuka adaren da ita da mum ba’asan mai rarrashin waniba bare da tsakiyar dare abin yataso yayita aman jini tuni suka fitarda rai akansa banda kukansu su duka nabu abinda kd tashi,
sannu ahankali yafara gane wainda ke kansa nan aleeya tayi masa alqawarin nemo masa nur da kanta takawo masa da wannan alqawarin suka dan fara sabawa itace ke kulada cinsa da maganinsa,
ahaka harsuka sake shekara babu nur duk wata rayuwarta ayanxu ta tattarane gurin kula dashi,
bata iya barci kullum kwana take azaune,
mum ma ahankali tafara ciwo nan abubuwa suka taru sukai mata yawa musamman yanxu da ciwon dawood yake sake gangarawa dan yanxu kam yafi wata akwance ko motsi bayayi tun ranarda ya kwana yana aman jini,
kallonta ammy tayi cikin hawaye tana cewa,
aleeya mukoma gida kiyi jinya wlh kema bakida lafiya ji yanda kika kashe rayuwarki gurin jinya.
share hawayenta tayi da dogayen yatsunta dasuka rame murya a sanyaye tace,
ko ayanxu na mutu nasan wannan danakeyi shi ake kira sadaukarwa babu cutatarwa babu 6oyo da zuciya daya nakeyi kuma wlh komai danakeyi inayine damin layla bazan ta6a bari abinda takeso ya wulaqantaba,
ni layla da dawood sune tawa qaddarar.
shuru ammy tayi tana fidda qaramin sautin kuka ahankali sbd gabaki daya aleeyar ta canxa tamafi wanda ke jinyar lalacewa sbd abin ita a zuciyarta yake cinta.
wannan wace irin soyayyace allah ya jarabci aleeyar da ita akan dawood da layla.
kuka sosai ammy tayi na tausayin yarta haka takoma sbd aleeyar taqi yarda tabita,
bayan tafiyar ammy mum tayi sabon kuka dan tabbas gskia ta fada aleeyar na buqatar kulawa fiyeda ita sbd ita kanta tana hango qunci da tsananin ciwon zuci da aleeyar ke fama dashi.
aranar da suka dawo gida da dawood tazauna takallesa taga yanda ciwo yamayar dashi sai aranar tasamu kuka yazo mata tun bayan tsawon lokaci,
bude idanuwansa yayi daqyar tareda lumshesu cikin azabar ciwo yace,
thank you aleeya.
giegiza masa kai tayi cikin tsananin kuka ko mgn bata iyayi,
sake bude baki yayi daqyar yace,
duk ranarda kikaga nur da abinda ta haifa nabaki amanarsu and pls forgive me aleeyaaa””’ya qarasa fada cikin wata irin azaba tareda fara tari
tsananta kukanta yayi kamar zata shide,
mum ce tashigo ta tarardasu ahaka arikice ta qaraso ganin jini fiyeda na kullum salati tasaki mai qarfi jikinta na rawa nan aleeya ta dago tana ganinsa tafuta cikin tsananin firgici daidai isowarsu sufyaan da kwalayen drip drip suna ganin yanda yaks suka watsarda komai aka kwashesa suka koma asibiti cikin sabon tashin hankali.
****
DAWOWA LBR
zama taji anyi kusada ita shiyasata dauke jajaye idonta dagakan sunan asibitin ta sunkuyar dakai qasa,
anty aleeya””’taji ankira sunanta murya na rawa,
kobata dagoba tasan muryar bilal ne sai kawai ta share hawayen dasuka sauko mata ta dago ahankali,
taheer tagani tsaye bayan bilal yana kallonta cikin tsananin tausayawa sbd tabbas ta jarabtu,
kama hannunta bilal yayi yana kallon tsakiyar red swollen eyes dinta yasaka mata takarda cikin hannunta yace,
anty aleeya hawaye da damuwar danake gani cikin idanuwanki har abada bazasu barni na zauna cikin sukuniba,
layla da dawood ne farin cikinki tuntuni nayi alqawarin dawo miki da farin cikinki,
ban nemo laylaba sbd tana yar uwata na nemotane sbd ke.
kallonsa tayi da sauri idanuwanta na cikowa yace,
layla itace warakar dawood insha allah ke kuma warakarsa da ganinta itace taki ina fatan komai yazo qarshe.
kallon takardar tayi hawayenta na saukowa kafin tadago tasake kallon bilal din da sauri ta fada jikinsa tareda sakin wani irin kuka.
saidatayi kamar bazata bariba kafin ya miqar da ita tashiga dakin dawood taquara masa zuciyarta na karaya tsawon lokaci ta sake kallon takardar hannunta ta juya ahankali ta fuce tareda sake waiwayarsa.
tan fitowa sukaci karo da jass zaishigo kallon juna sukayi kowanne ya wuce,
kallonta taheer yayi yace,
muje nizan kaiki lets finish this today insha allah.
gyada masa kai tayi hawaye na gangaro mata suka wuce kosu mum basu saniba.
airport taga sun nufa takalli bilal daya hana tasa rayuwar sukuni sbd su,
tabbas tasan yana tsananin kewar yar uwarsa saidai yana qoqarin dannewane yanuna mata kulawarsa dan kusan duk sati saiyazo prthct dubata shi sam baya son dawood arayuwarsa sbd shine silar komai daya samesu yake gani.
jirgi suka shiga itada bilal din da taheer kowannensu shiru da abinda yake saqawa shi kansa taheer zuciyarsa bugawa takeyi da qarfi ta yanda zai kalli macen dayafi komai so amatsayin matar dan uwansa harda qaruwa tabbas bazai ta6a iya qara zama akusadasuba zaicigaba da rayuwarsa acan inda yafara ayanxu.
bilal kuwa zurfi yayi cikin tunanin yanda sukasha baqar wuya shida taheer kafin suka samu inda take,
lokacinda suka fara nemanta a porthrct basu samuba duk iya kashe kudi da bincike taheer da dad sunyi amma babu alamarta nan taheer ya yanke shawarar mayarda binciken abuja,
canma tsawon lokaci babu wani alamar zaaganta anan nan ya yanke shawarar komawa lagos,
komawarsa lagos yasa dole ya nemi bilal sbd jin ko akwai guraren dayake tunanin zata iya zuwa maana acan rayuwarsu ta baya nandai suka fara bincike a 6oye shida bilal din da bincike da dubara har qauyensu baffa dahiru sukaje amma babuta nan shima baffan hankalinsa yatashi sosai musamman dayaji kusan tsawon shekara da 6acewarta.
shiru yayi cikin nazari kafin ya dago yace,
suje har adamawa inda komai yasamo asali sugani.
aranar suka koma abuja washe gari suka sauka adamawa,
lokacinda suka fara bincike daqyar bilal yagano unguwar dasukai rayuwarsu tada sbd canje canje da gyara da gurare suka samu,
saida suka share sati biyu babu wani cigaba suka tattara suka koma aranar dazasu koma a airport yahadu da wata matashiyar mace da yaranta biyu duka maza,
gudu sukeyi sukayo gurinsa suka boye mamar tabiyosu cikin fada tana cewa,
kuxo muje mana kokuwa so kuke sai ALEEYA tayita jiranku harta gaji.
da sauri suka fito sukayo gurinta kowannensu na cewa,
ummy nine anty zata bawa aleeya idan na girma.
dariya tayi tareda dagowa ta kalli bilal din dake kallonsu tace,
sorry sunxo sun damuqeka…
no its ok yarane ai koba komai naji sunada yar uwa mai sunan tawa yar uwar danake jida ita.
kallonsa tayi tasake kallonsa zuciyarta nadan rawa sbd kamar dayake mata da fuskar sani duk da dai ya girma sosai yazama saurayi amma kamannin still sunanan,,,bilal ta furta ahankali ga mamakinta saitaga ya juyo yace,
kinkirani ne?
baki ta rufe cikin tsananin mamaki da farin ciki tace,
bilal din laylah?
dawowa yayi da sauri shida taheer harsuna hada baki gurin cewa eh shine.
murmushin farin ciki tasaki tace,
Story continues below

bilal kaine ashe kaima zanganka raheenatu ce damukai zama tare tun baabanku nada rai katuna kuwa?
tabbas ya tuna da ita sbd itakadaice mai nuna musu qauna da kulawa tun wancan lokacin qawar layla ce jiyayi jikinsa yayi sanyi sbd ya dauka watace daban tasan inda laylan take,
sakin murmushin yaqe yayi cikin qarfin hali yace,
allah sarki nakuwa tuna duk da kamannin sun canza.
dariya tayi tace,
gaskia ne kam saidai ina kuka shiga tsawon lokaci haka.
shafa fuskarsa yayi cikin yanayi na damuwa yace,
abubuwa da dama sunfaru babban ciki shine nur muke nema yanxu tsawon lokaci mai tsayi anata nema amma haryanxu shiru bamuda tabbacin tana raye ko tana….
katsesa tayi da cewa,
nur nanan raye saidai…..
ganin irin zaburowar da su biyun sukayo yasata saurin rufe bakinta tareda rintse ido cikin jin zafin subutar bakinda tayi saidai ita kanta dama tanason sanin inda su bilal da aleeyar suke sbd kawo qarshen komai tun kafin aleeya tafara tambayarsu ina daddynta dan ana gaf da fara hakan.
juyawa tayi da sauri zatabar gurin sukasha gabanta atare bilal baisan lokacinda ya zube qasaba cikin sanyin murya yace,
dan allah ki taimaka rayuwar mutane da dama na cikin wani hali sbd ita ka sanardamu inda take idan kinsani..
kallonsu tayi cikin yanayi na tausayawa tace,
kubani numbernku zan kiraku na sanardaku idan na isa gida kuje kurage damuwa layla na taredani tun ranarda tabaro gida aranar muka hadu.
jiki na rawa suka rubuta mata numbibinsu sbd dagewar datayi bazata iyayi musu komaiba ayanxu.
da wannan suka fasa tafuya suna zaman jiran kiranta shiru shiru babu bayani suka tattaro suka dawo aranarda suka sauka lagos aranar tayo musu txt na address din gidanta dake adamawa kuma aranar sukayo porthcrt suka damqawa aleeya address din.
juyowa yayi ya kalleta lokacinda jirginsu ya sauka yaga har lokacin idanuwanta na rufe.
saukowa sukayi babu 6ata lokaci suka dauki drop zuwa address din.
kallon tangamemiyar gate din gidan tayi taja numfashinta dake fita da sauri ahankali tanajin wani irin qarfi da jarumta azuciyarta duk da sosai takejin nauyi aciki,
mai gadi bai hanasu shigaba sbd madam dinsa ta sanardashi zuwansu suka shigo kowanne da kalar bugunda zuciyarsa keyi,
suna gaf da shiga palon taji ankira sunanta,,
ALEEYAH..
cak ta tsaya tareda jan numfashi kafin ta juyowa ahanki bugun zuciyarta na tsanan,
yarinyace fara sosai kyakkyawa dabata baro ko yatsa daya na mahaifintaba da kakarta dan har jajayen lips dinsa saidata dauko da kalar tafiyarsa cikin sanyi,
sanye takeda riga da wando red an gyara mata gashinta andaure,
qurawa yarinyar ido tayi jin yaron yasake kiranta da aleeyah.
rufe bakinta tayi da duka hannayenta biyu sbd kukan dakeson zuwar mata zuciyarta na karyewa,
basai anfada mataba tasan wannan itace ‘yar dawood da layla kuma sunanta laylanta tasawa yarinyar batasan lokacinda hawayenta suka saukoba lokaci daya taji quncinta yafara gushewa ganin yarinyar sbd mutanen datafi sone suka sameta,
dafata raheenatu data fito tayi tana kallon little aleeyah tace,
aleeyah zoga mummy aleeyaan ummynki.
juyowa yarinyar tayi suna hada ido da aleeya tazo da gudu ta fada jikin aleeya cikin wani irin shauqi aleeya ta rungumeta sabbin hawaye na gangaro mata,
bilal da taheer ma daurewa kawai sukai basuyi hawaye ba daqyar suka qarasa palon little aleeya na damqe ahannun aleeya sbd kobada laylaba yanxukam tasan little zata kawo sauqi arayuwarsu insha allah,
zama sukayi aka kawo musu ruwa amma babu wanda keda nutsuwar kallon ruwan amatse suke dasuji inda layla take,
cikin sanyin murya tace,
mijina ya rasu yabarni da yarana biyu a porthct daga baya na shirya tareda tattara duk wata dukiyar damuka gada nida yayana nayi shirin dawowa gida adamawa
aranarda layla tabar gida aranar cikin qaddarawar allah nice na bugeta da mota a porthct kuma bugu sosai dan kuwa qaddarawa da ikon allah kawai yasa cikin dake jikinta ya tsaya bayan doguwar wahalar jinyar datasha kafin daga baya muka dawo adamawa tare muka cigaba da jinya tsaqon lokaci harta haihu,
haihuwarma tazo da babbar matsala saida muka koma jinyar uwa da jaririyar bayan haihuwa kafin daga baya komai ya daidaita ga jaririyar inda da kanta ta6arwa yarta sunan aleeyah saidai haryanzu ita babu wani sauqi sai agurin allah,
layla tafada mini komai sbd acewarta duk ranarda ta rasu nakai little aleeya gareki aleeya sbd tanasakaran bazata sake ganinkuba arayuwarta,
tuntuni naso mu nemoku sbd halinda take ciki amma tasani alqawarin rshin yin hakan saidai kullum da fargaba nake kwana da ita nake tashi sbd gudun karta rasa ranta ahaka cikin damuwa da qunci shin mezai hana ataru anemi mafita wa wannan alamari sbd sam wannan bashine hanya mai 6ullewa ba,
little aleeyah ta taso da tsananin qaunarson ganinki aleeya sbd mahaifiyarta data cusa mata qaunarki mai tsanani aranta ta hanyar yimata maganarki kullum duk da tanacikin mawuyacin hali.
zubewa qasa raheenat tayi cikin yanayin na hawaye tace,
na roqeki aleeya ji yafewa layla abinda tayi sbd hakan yasa takasa cire damuwa aranta harya zamar mata ciwo ki yafe mata kodan darajar qaunar dakike mata,
ki yafe mata sbd kashe kanta takeyi ahankali batareda tasaniba.
kasa dagowa aleeya tayi sbd tsananin kukan dayafi qarfinta wannanwace irin rayuwace sukeyi mara tsari da tawakkali,
kallon aleeya tayi tareda cewa,
bismillah muje nakaiki gurinta,
miqewa sukayi wannan karon qafafuwanta har rawa sukeyi sbd bugawar da zuciyarta keyi suka nufi sama zuwa wani daki.
bude qofar raheenat tayi tareda matsawa gefe aleeyar tasaka qofa tashiga dakin itakuma ta fito tafeda ja musu qofar,
tsayawa cak tayi tsakiyar dakin tareda qurawa nur din dake zaune qarshen gado ta takure,
wasu irin hawaye masu zafi da ciwone suka gangaro mata ganin yanda laylar takoma,
mezata gani haka layla takoma kamar wanda tayi shekara goma tana jinya,
LAYLAHH””’ta furta muryarta na wata irin rawa,
kamar amafarki taji muryar aleeyar ta dago kai ahankali ta dorawa fuskar aleeyar ta sake dubawa dakyau taga itace
sai kawai ta sunkuyar dakai ahankali hawayen datafi shekaru dason yinsu sai yau suka ciko idanuwanta amma basu saukoba sai rawa da jikinta yafara dauka,
qarasowa ahankali aleeya tayi tareda zama kusada ita tayi irin zamanta suna fuskantar juna cikin rawar murya aleeya tace,
i miss you like hell my laylah.
rintse ido layla tayi sai kawai kuka ya qwace mata suka rungume juna da sauri kowannensu na sakin kukan daya jima baiyi irinsaba raheenat dake qofa takoma palo tasanardasu taheer nan suka sauke wata irin wahalalliyar ajiyar zuciya atare tareda roqon allah yasa iyakacin wahalar kenan.
little aleeya kuwa murna takeyi yau zatabi mummy aleeyarta sutafi.
kuka sukai sosai saida suka gamsarda zukatansu kafin suka saki juna aleeya ta miqa mata hannu tace,
lets go home.
kallonta layla tayi da jajayen udanuwanta zatai magana aleeya ta katseta da cewa,
wlh har abada babu dawood cikin zuciyata yanxu,
komai ya isa hakanan namiki alqawarin inganta rayuwata matuqar zakimin alqawarin kulada dawood harya samu cikakkiyar lafiyarsa,
nabar dawood nikuma kimin alqawarin kinbarmin little aleeyah.
gangarowa hawayenta sukayi murya a shaqe tace,
aleeya takice har abada kece uwarta saidai nima babu abinda zanyi arayuwar dawoo….
baki gaji da ganinmu cikin wannan halinba kenan tun farko arayuwa taurin kankine yake jawo mana matsala dan haka daga yanxu kingama yanke kowane hukunci idanhar nice aleeyarki nice zan yanke hukunci daga yanxu,
and we are goin back home today.
tana fada ta miqe zuciyarta na daci sbd taurin kan layla yafara zama wani abin..
riqota layla tayi da sauri tareda goge hawayenta tace,
karkiyi fushi dani aleeyah konan gaba dan allah.
dawowa tayi ta rungumeta tana cewa,
har abada bazan qaraba insha allah idan har bazaki qara 6oyemin komaiba.
bazan qaraba i promise.
daqyar suka lallashi juna ta riqota suka sauko qasa bilal na ganin yar uwarsa kasa hkr yayi yataso da sauri suka rungume juna cikin tsananin qauna da kewar junansu.
taheer daqyar ta iya kallonsa suka gaisa qasa qasa sbd ko kallonsa takasayi.
duk yanda raheenat taso su kwana kasawa sukayi abincima daqyar suka samu cusawa suka juya da layla da little aleeya sbd amatse suke dasuga sun kai nur din gaban gadon dawood.
suna sauka airport direct asibiti suka nufa jikin layla nan take yafara rawa idanuwanta suka canxa ahankali aleeya ta riqo hannunta tareda girgixa mata kai tana sakar mata murmushin bata qwarin gwiwa gwara suyi facing komai once and for all kowa ya huta.
hannunta aleeya ta riqo tareda janta suka shiga,
tun daga nesa mum ta hangosu takasa yarda da abinda idanuwanta ke gane mata ta ta6a sufyaan dake kusada ita ta nuna masa murya na rawa tace,
NURRR,
miqewa sukayi dukkaninsu atare shida mum sbd jass na ciki yana cirewa dawood din jinin daaka daura masa ya qare,
karaf idanuwan mum suka sauka kan little aleeya dake hannun taheer daya dauketa,
murza idanuwanta tayi cikin wani irin yanayi da shauqi kobaa fada mataba tasan wannan jinintace gudan jinin sweetboy dinta wata irin murna da hawaye tafara lokaci daya da sauri ta kar6eta daga hannun taheer ta qanqame jikinta kota kan laylar bata farabiba saidai sufyaan ne yayita yiwa allah godia idanuwansa na cikowa da hawayen farin cikin samun cikar burin dawood dinsu,
Nana kuwa rungume layla tayi tana hawayen farin ciki sbd ita kanta tasan tana tsananin qaunar layla har cikin ranta,
daqyar mum tabari sufyaan ya kar6i little tareda rungumeta dakyau wata irin qaunarta mai tsanani na shigarsa don kuwa jiyakeyi kamar gudan jininsace aka haifo koba komai suma sun zama dadys daga yanxu,,,alhamdulillah ya allah”””ya furta ahankali tareda sakarwa little din murmushi yana cewa,
welcom dadys princess mai iyaye da yawa.
cikin ‘doki da zumudin farin ciki Nana ta matso zata kar6eta ahannunsa hannuwansu suka hadu wani irin tsigar jiki yaji da sauri ya dago ya kalleta itama kallonsa tayi tareda sunkuyar dakai ta kar6i little din ta juya yabi bayanta da kallo kafin ya kalli tsigar jikinsa data tashi,
rungume layla mum tayi takasa mgn sai hkr take bata tana roqonta karta sake barinsu,
jijjiga kai tayi tana share hawayenta babu wadda takeson gani yanxu kamar ammynsu tasan itama tana cikin hali na tausayi da damuwa,
ahankali aleeya ta miqe ta shige dakinda dawood din yake daidai shikuma ya juyo ganin waye yashigo,
cikin idanuwan juna idanunsu suka sauka ta dauke kanta tana kallon dawood din cikin farin cikinta daya kasa 6oyuwa afuskarta,
qura mata blue eyes dinsa yayi akaro na farko dayaga murmushi kan fuskarta jiyayi kuzarinsa na ragewa ya juyarda kai cikeda mamakin abinda yasata farin ciki suna cikin wannan halin,
cikin wata irin murya tace,
kanasaran zai farfado nan kusa i mean yaushe kuke sakaran farkawarsa?
dan juyowa yayi ya kalleta yace,
anytime soon tunda jinin yagama shiga.
juyawa tayi tafice batareda taqara wata maganarba wannan ne karo na farko da magana doguwa irin wannan tashiga tsakaninsu.
tana fitowa takalli layla dake sharewa mum hawaye tariqo hannunta tareda miqar da ita tace,
nida mum munyi namu now its your turn zaki kulada mijinki mukuma zamu koma gida muyi jinyar kanmu…..
katseta mum tayi da cewa,
no aleeya ina zata iya jinyarsa itama fama takeyi da kanta..
murmushi aleeya tayi tana cigaba dajan layla zuwa dakin tace,
mum na tabbatarda ciwon laylana ya warke alokacinda muka hadu da juna abinda ya rage aciwon dr dawood zai qarasa warkar dashi.
kallonta layla tayi da sauri saikawai taji kunya da nauyin zancen meyasa tabari sonda takeyiwa dawood ya bayyana har haka aleeya tagane.
sake tura qofar tayi ahankali wannan karon jass yana juyowa da little yafaracin karo yaquramata ido kafin yayi mgn idanuwansa suka sauka kan nur da sauri yamaida kallonsa kan little aleeya kafin yakalli aleeya dake kallonsa ta gyada masa kai cikin murmushin farin ciki tace,
yes she’s our little princess my little….
yes i’m a father now nima inada ‘ya yanxu,,,,
murmushi aleeya tayi tana kallon yanda yake nunawa aleeya wata irin qauna kamar zai hadiyeta yace,
nine zanzama real dad naki sweethrt kowa ya hakura nixa’abarwa….
matsowa aleeya tayi gabansa tareda ‘dan tamke fuska ta miqa masa hannu alamar yaba ita tace,
sorry dr amma she’s my already so…….
dariyar daya manta rabon dayayi yayi tareda saurin ficewa dakin sbd tunowa dayayi akwai patien da sauri tabi bayansa tana cewa,
ji wannan dan qarfin halin.
tunda suka shigo idanuwanta suka sauka kansa tayi saurin dafa gado sbd wani irin mummunan jiri daya ‘dibeta,
rawa jikinta yakejyi sosai da qyar ta qarasa bakin godon ta zube qabansa tareda sakin wani irin kuka mai ciwo ahankali,
tabbas bazata ta6a yafewa kantaba tunda tasaka dawood cikin wannan masifar tayi tunanin rashinta zaisa ya dangana ya rungumi aleeya amatsayin abokiyar rayuwa amma ga abinda hakan ya jawo,
tabbas koyaushe bin ra’ayinta ba alkhairi bane daga yanxu tadaina bin tunaninta sbd kullum shiyake kaisu ga masifu irin haka,
daqyar ta iya tsaida kukanta ta dago tareda qurawa fuskarsa ido ta lumshe idanuwa ahankali tanajin tsananin tausayinsa nabin jijiyoyinta duk yanda take tunanin cirewa ko danne soyayyar dawood azuciyarta wannan abune dabazai ta6a yiyuwa agaretaba duk kuwa baqar wuyar datake sha gurin gwada yin hakan,
hannunta ta dago ahankali yana rawa ta doro kan nasa dake kan cikinsa tasaki wata irin wahalalliyar ajiyar xuciya kafin takai kanta ahankali ta kwantar gefen guskarsa numfashinta na fita zuwa cikin kunnensa.
awaje kuwa abu soyayi yazamarwa jass da aleeya fada qarshe dai dole yabata sbd gida dazasu dukkaninsu shida sufyaan ne kawai zaa bari a asibitin sbd kar dawood ya farfado babusu akusa dan sunasaka ran farkawarsa koyaushe sbd jinin daaka saka masa.