DEEMAH CHAPTER 3 BY ZAHRATEEY
“Rayuwa tana faruwa wucewa take kamar ba’ayi ba, duniyar ma nawa take komai me karewa ne, idan yau kaine gobe ba kai bane, kayi mai kyau a tuna da alkairinka, kayi mara kyau a dinga yama d’id’i da sharrinka, shi duniya ba madawwama bace, gurine na kazo nazo kamar kasuwa sai kaga har anci an tafi wasu sunzo suma sunci sun tafi, ka fuskanci lahirar ka sai komai yazo maka da sauki, kai ba kowa bane kuma ba d’an kowa ba face d’an adam wanda Allah ya halitta da ta6o, kazo duniya sirara zaka koma sirara, kazo hanu rabbana zaka koma da dayan biyu ko hannu rabbana ko hannu mai cike da haske da tarin alkairai, abin fa za6a akeyi ko ka bar son zuciya ka d’auke haske ko kuma ka biyewa son zuciya ka za6i duhu, shi duniya kamar rawar yan mata ne na gaba yayi baya, kuma ba’a shuka shinkafa a kasa a girbi masara, lamari na rayuwa inka duba ai tana da sauki amma fa idan ka bi Allah da manzosa, sai kaga komai dai-dai ko da kafi kowa talauci sai ka rinka jin wani farin ciki from no where yana ta mamaye zuciyarka” d’an gyara tsayuwata nayi, na cigaba da cewa “Yanzu kai _Baba K_ Allah na tuba ko mutuwa kayi ai bazaka dace ba, kai ba salla akan lokaci ba, kai ba azumi kake ba ka fake da ulcer, kai ba kula da tarbiyyan mu ba, kai ba kula da cin mu da shan mu ba, kai ba kula da matayenka ba, rayuwa muke a gidanka kamar a zamanin jahiliyya, sam-sam ma baka tsoron ka tashi da shanyayyen 6ari d’aya a ranar gobe kiyama saboda yanayin rashin adalcin ka ga matan ka, am _Baba K_ kar kace fa nayi rashin kunya amma a gaskiya auren mata har
hud’u na jaruman maza ne ba na ragwage ba, kai ko masu mata biyu ana buk’atan jarumin wanda suka san Allah da manzonsa amma ba dai irin ku irin ku ba, dan haka ko ka shirya gyara lahiranka ta hanyar gyara duniyarka ko kuma ka cigaba da lalata lahiran ta hanyar bakanta duniyar ka, shi dai duniya ba gurin zama ba kamar yanda na fad’a maka, yo kai da aka d’auke wa yara har biyar ai kafi kowa sanin ba gurin zama bane” ina gama fad’awa _Baba K_ abin da nayi tunanin zai fisheshi nayi gaba na barshi da cizon yatsa.
+
Wani irin d’aki nakeji a mak’ogoro na, shikenan munyi rashin yan uwan mu ta dalilin son zuciya irin na mahaifin mu? Mun sani cewa mutuwa na kan kowa kuma idan dai lokaci yayi babu tsimi babu dabara mutum zai tafi, amma wani lokacin silar itace abu mai cin rai da wuyar mancewa, balle irin namu da ake kisar walakanci, ga rad’ad’in fitan rai ga azabar gangan jiki da ake gana musu, tir da irin wannan rayuwa me cike da son abin duniya, tir da irin wannan rayuwa me cike da dimbin laifuffuka marasa dadi, ba dan dai Allah, Allah bane da tuni ya kifar da duniyar baki d’aya saboda tsa6onsa da yayi yawa, amma da yake Allahu gafurur rahim ne mai tausayi da jin kai me gafara da kuma arawa dan adam lokaci sai abubuwa suka zo da sauki, toh amma lahiran da ya zama final gurin zaman d’an adam shi ne ya dace a nema guri me kyau a ciki ba wai a duniya ba. D’aki na shiga na kwanta ina ta tunanin rayuwa, kamar ihu nake jiyowa a cikin gidan amma nayi kunnin uwar shegu dasu ko in fita, gyara kwanciya ta nayi, na cigaba da tunani kala-kala _Kisma_ ce ta shigo tace _Mama Qudi_ na kirana, tashi nayi na share hawaye na sannan na d’auki hulla na saka a kaina, kamar zan kira ta in tambayeta meke faruwa sai kuma na share, a cikin falo na samu _Mama Qudi_ ranta a 6ace sosai, zama nayi a d’an nesa da ita sannan nace mata “gani” sai data karemin kallo na wasu sekonni kafin tace “me kika je kikayi a gurin babanku har kika sa ya taramu yaci cicci mana mutunci, kin sani sarai ni sam-sam bana son shiga sha’aninki musanman a lamarinki da mahaifinku, dama _Inna Suwaiba_ jira takeyi ayi wani abin ta samu ta sauke abin da yake cinta a rai, ban san dai abin da kika aikata ba amma yau kin jawo anyi musayar yawu tsakanin matan babanku da shi baban naku, babban ma abin tashin hankalin dai shine iyayenku sunyi wa babanku duka gashi chan harda karaya a hannu da k’afa, _Ya Kolo_ ce kawai bata shiga ba tana daga gefe, ina jiye miki wani fitinar tsakaninki da yan uwanki domin idan suka san kece silar da akayi wa babanku duka abin ba zai yi kyau ba” tana gama maganarta tayi shigewa d’aki, ni kuma na fita dan tabbatar da gaskiyar lamari, ai kuwa abu ya tabbata yau _Baba K_ ya taro match, dukan mutuwa suka mishi, duk fuskarshi ya sha tabo, ga hannu duka biyu a d’aure kafa ma haka duk ya zama kamar robot, maimakon inji tausayin shi sai ma abin ya bani dariya, yanzu menene abin kiran matansa akan maganar mu dashi, ga shi ai ya janyo bala’i a kansa.
Kaf cikin matan gidan mu hatta _Mama Qudi_ babu wanda yayi jinyarsa, mazan gidan mu nema suka kokarta sukayi jinyar nasa, cikin watanni biyu da yake kwance gidan yayi mugun dadi, ga abinci a wadace, sai wanda mutum yaso dafawa ga shi babu zancen iya kud’in ka iya shagalinka, kawai d’iba zakayi a 6agas, _Baba K_ bakin ciki kamar ya mutu, sai na tuna ranar da muka yanka kajinsa akayi ferfesu kuma aka shimfid’a babban tabarma akaci a gabansa, sosai yayi kuka harda majina, ranar mun sha zagi har mun gode Allah, kuma ko a kolar rigarmu, mu dai munci kuma munji dadi.
A yanzu haka munata shirye-shiryen bikin su _Kursiyya_ dan saura sati d’aya da kwana uku, ga shi har mun fara bak’i daga ko wani 6angare, yayyin mu maza sun d’au nauyin kayan falo na yan matan da za’a aurar, su kawunan mu kuma sun d’au nauyin kayan d’aki wasu kuma abincin da za’a ci a ranar biki, kayan kitchen kuma kowa mahaifiyarta keyi mata, a namu d’akin yan uwan _Mama Qudi_ har sunyi wa amare komai sai dai d’an abin da ba za’a a rasa ba, nima nayi wa amaren kayan humra da turaren wuta da kulacca, sosai _Mama Qudi_ taji dadin hakan, dan dama bata son wariya tsakanin mu da yan uban mu, sai kuma lace da atamfa mai kyau dana saya musu akayi musu anko, ko wacce na saya mata kalar da tafi so, sai dai Pattern din kayan iya d’aya ne, _Goggo Fulera_ har 6angaren mu tazo tayi min godiya bayan na aikawa amaryan d’akinta nata sakon, ni kaina naji dadin abin da nayi ba laifi kuma an yaba min, duk da cewa ban fasa asusu na ba amma yan kud’in dake hannuna har yanzu basu kare ba, da dubu hamsin din dana samu a hannun _Iya Loja_ nayi amfani, sai wasu kudad’e da bansa a asusu ba, da kuma gudumawar da _Iya Loja_ ta bani na dubu ishirin wai ayi hidimar biki.
Sosai muka shirya wa bikin dan har walima muka had’a da sisters day, komai ya tafi dai-dai yan uwana maza suma na basu kyautan dubu goma goma, sosai sukaji dadin hakan kuma suka nuna yabawarsu, _Baba K_ kuwa har yanzu yana kwance bai gama warkewa ba sai dai yana d’an takawa, ko kwandala bai bayar ba da sunan ayi wani hidima dashi, _Inna Suwaiba_ ma ta bada nata gudumawar duk da cewa babu yaranta a cikin wadanda za’a aurar, duk wasu yan uwa na nesa dana kusa sun zo kuma sun bada gudumawarsu amma banda uban amare da angwaye.
Rana bata karya sai dai uwar d’iya taji kunya, a yau ake bikin yan uwana maza da mata yayyi na da kanne na, cikin ikon Allah aka d’aura aure lafiya kuma akayi taro lafiya aka watse ba tare da wani kananun magana ba, domin iyayen mu sosai suka shirya wa bikin, sukayi komai a wadace tare da fitar da juna kunya.
Duka amare a cikin bauchi gidajensu yake, mijin
_Kursiyya_ shine me karfi acikinsu, yana aikin banki, sai mijin _Kursum_ shi kuma direban gida ne, sai kuma mijin _Khalimah_ masinja a wani kamfani, sai dai duk gidajen kansu ne ko wanne d’aki biyu da kewaye a ciki, sai falo da kitchen dinsu, kuma duk anyi musu kaya dai-dai gwargwado babu na kushewa abin dai cikin rufin asiri. Duk naki yi musu rakiya amma nayi musu alkawarin zanje har gida in duba su, daker muka rabu suna kuka ni kuma ina daurewa dan kar in karya musu zuciya, mazan kuma sai da aka kawo matan nasu gidan mu kafin aka kaisu gidajensu, suma ba laifi iyayensu sunyi musu kaya dai-dai misali, sai dai muce Allah ya had’e kansu ya basu zaman lafiya.
Kyaun tafiya dawowa, duk wad’anda suka zo biki sun koma gida lafiya cikin koshin lafiya, Duk fa hidimannan da akayi _Baba K_ bai kula kowa ba, har yanzu yana fushi da yan gidan akan abin da aka mishi karfa kuce wai dukan daya sha a’a kajinshi da kayan abinci da mukaci, abin ya mishi zafi sosai har wani y’ar rama yayi kamar me ciwon aids.
Yau sati guda kenan da yan biki suka watse, gidan mu ya zama shuru kuma yan gidan sun karo walakanci da iya shege dan yanzu ba’a sayan kayan abincin _Baba K_ sai dai kawai a d’iba a dafa, karshe ma _Inna Suwaiba_ tasa yayyin mu maza suka raba abincin gida hudu ko wacce aka kai mata store din dake cikin 6angarenta, ya zama store din_Baba K_ babu ko hatsi, bayan anyi rabiya kowa ta koma yin girki a 6angarenta, babu ruwan wani da wani sai dai idan sun had’u su gaisa, _Baba K_ kam sai da aka had’a da kai shi asibiti domin ranar suma ya dinga yi yana farfad’o wa, yana cewa an kashe shi an kwashe mishi arziki, gashi yanzu tsoro yakeji yayi magana dan kar a sake mazge shi, kwanan shi uku a asibiti yasha karin ruwa har leda biyar da allurai sannan aka sallamo shi, kuka iya kuka yayi daya sake duba store yaga babu komai, saura garken dabbobinsa, hakan yasa ya tattara keyar dabbobin ya sayar yasa kud’in a aljuhu dan kar ma acinye mishi a banza, kuma ba kud’i kad’an ya samu ba daya sayar da dabbobin, amma maimakon yayi amfani dasu ta hanyar kula da iyalansa sai ya koma cin abinci a teburin me shayi yana cin bredi da kwai da shayi me kauri wataran kuma indomie da kwai da gasheshen kaji ko nama
.Yau bani da aiki, so ina gida ina hutawa, “kizo ana sallama dake” shine abin da _Mama Qudi_ ta fad’a daga bakin k’ofar d’akina, abin ma yaso ya sani dariya, yo wani me karar kwanan ne yazo gurina? Bani da amsar tambayan da nayiwa kai na, tashi nayi na d’auki mayafi me d’an girma saboda yanda kayan ya d’an kamani, a bakin kofar falo na ajiye slippers din, sannan na d’auki wani takalmi a waje na fita.
+
Lek’awa nayi naga ba kowa, toh ba kowa mana dan gurin shuru yan zaman kashe wando duk an tafi makaranta, sauran kuma suna hutawa kafin yamma yayi su cigaba daga inda suka tsaya, “Assalamu Alaikum” naji an fad’a daga k’asa, to daga k’asa zance ai dan yaron befi tsawon _Kisma_ ba da alamu ma kila ta girme shi, amsa sallamar nayi ina cewa “yaro wa kake nema, naga dai duk gidanmu babu yara balle ince kazo wasa, sai dai kuma idan aiko ka akayi gurin yan gidan” murmushi yayi sannan ya gyara tsayuwarsa kafin yace “eh toh nine na aika a kiraki, kuma wajenki nazo” rainin wayo kenan ai, wani wai wajena yazo “astagfirullah, nace aiko ka mutumin yayi ko kuma dai an aiko ka cikin gidan ne, yo kazo gurina a matsayinka na wa? kace min me ince maka me? toh a kaddara ma mun tsaya tare toh a matsayin suwa kenan mu din? Ni ba sa’ar ka bace dan haka kar kayi wasa dani, ka fad’amin sak’on wanda ya aiko ka ko kuma ka k’arawa manka wuta” na fad’a ina nuna mishi hanya, yo Allah na tuba mu jera dashi ace d’ana ko k’anina? Wani d’an guntu ne fa, ko ince yaro, ga fuskar yara, ga shi d’an karami, ga siranta, ina ni ina shi fisabilillahi, nafi shi tsawo na fishi jiki nesa ma ba kusa ba, dan nayi shi uku, mutum kamar igiyar shanya, wallahi Allah ya isa na daya zo da sunan gurina yazo.
“Tauraruwata kenan, ni da kika ganni shekaruna talatin da uku a duniya” nace “a hakan?” Yace “kwarai, ni ba yaro bane, kuma inada aure da yara uku, na ganki a shagon _Iya Loja_ ne kuma naji kin min kin kwanta min a cikin k’ok’on zuciyata, naji duk duniya idan bake ba bazan iya had’a matata da wata ba, sai dai ke d’in domin kin tafi da zuciyata da kuma komai nawa, ina matukar kaunarki, dan Allah ki bani dama mu zanta nan da d’an lokaci kankani sai muyi aure” ya fad’a yana had’e hannayensa guri guda, ni kuwa shaye da mamaki nake kallonsa, wai a haka har da yara, kuma duk cikin garinnan ya rasa dai-dai da shi sai ni, eh ba shakka dai-dai kenan su marigayi da neman aure, cikin gida na shiga na barshi a gurin, ina zuwa d’aki na fara kukan bakin ciki, yanzu ni a rasa me zuwa gurina se sa’an kanwata kuma yazo yana raina min wayo, yo ina abin yake wai shi har ya kai aure, kuka nayi sosai kamar ance _Baba K_ ya fad’a a rijiya.
Washe gari sai ga _Baba K_ ya aika a kirani, sosai nayi mamaki, ina zuwa na samu _Inna Abu_ a zaune, kamar bazan gaisheta ba sai kuma na daure nayi gaisuwar, ta amsa tana d’auke kai daga gurina, kallon shi nayi nace “gani nazo” yace ai ya ganni, wani murya naji yana min sannu, wai sannu kamar ance mishi ina jinya, yaron jiyane, kallonsa nayi da kyau dan jiya tsaban haushi da 6acin rai ban tsaya na karanci gaskiya game dashi ba, tabbas yana da aure kamar yanda yace harda yara, kuma yana aiki a kamfanin gidan mai na _A&S Oil & Gas_ sannan yayi bincike akan gidan mu ya samu rahotanni da yawa ciki harda son kudi irin na _Baba K_ sai yayi amfani da wannan dama yazo gurin _Baba K_ ya bashi kud’i domin ya samu ganawa dani, “dama ka kar6i kud’in ka, ka adana ko kuma ince dama baka 6ata kud’in ka a barza da wofi ba domin kaci karya ka kwana da yunwa wallahi, ni nan nafi karfinka, nafi karfin wanda ya tsaya maka, gwara ma ka kara gaba domin ko a bakin farcena bazan iya d’auraka ba, in rasa mijin aure sai me cusa kai ta hanyar iyayena yana basu kud’i dan samun biyan bukata, ga yar kwadayayyu ko, sai na aureka kazo kana min gorin halin ubana, to a kara gaba a kai kasuwa nan ba’a bukatan sayar da d’iya kamata” ina gama fad’a mishi haka na tashi nayi gaba, ban shiga 6angaren mu bama kawai na fita daga gidan baki d’aya domin raina ya gama 6aci.
STORY CONTINUES BELOW
Tafiya nayi me tsawo ba tare da sanin takamanman ina zanje ba, na dad’e ina tafiya ina share hawaye kafin na samu gurin wani dutse na zauna, tunda nake ban ta6a samun masoyi na kwarai ba, duk masu zuwa gurina gasunan dai ne kawai, kuma wani abin mamaki duk wanda suka nuna suna sona sati guda kawai sukeyi a duniya sai labarin mutuwarsu, ni kaina ina son inga nayi auren ba wai a son raina ne nake zaman gida ba, ba a son raina kannena sukayi suka barni ba, da alama _Kisma_ ma ta samu masoyi domin naji tana yawan hira a waya, ban san meke damuna ba, bani da sa’a a rayuwa, ba uba na gari ba, ba uwa data damu da rayuwata ba, ba yan uwa da suka damu da lamarina ba, komai nawa a juye yake, tabbas na tabbata ba mutum ba, ko kuma me shafar aljanu, idan ba hakan ba, me zai sa duk saurayin daya zo gurina baya wuce sati guda a duniya, “Ya Allah ka jikan _Mamita_ me sona, me kaunata, me sharemin hawayena, me nunamin cewa rayuwata zatayi kyau nan gaba, nayi rashin yar uwa wacce take sanyani farin ciki, take sanyani nishadi, na rasa annurina tunda na rasa ta, domin duk wani dariya da nakeyi bayan rashin _Mamita_ babu wanda ya kai zuciya, ya Allah ka kawomin d’auki ka kawomin agaji, ka samamin mafita a cikin rayuwata” na fad’a ina kara rushewa da kuka.
Bani na bar gurin ba sai da akayi azahar sannan na kama hanyar gida, ina tafiya ina tunani, duk ma hankalina baya tare dani, ina zuwa dai-dai junction din gidan mu naji wani abu ya bugeni da karfi, nayi sama sai kuma naji ni a k’asa tim kamar bishiya ya fad’a, daganan ban sake sanin duniyar da nake ba.
A hankali nake bud’e ido na, dishi-dishi nake gani hakan yasa na sake rufe idona ruf, kaina wani irin ciwo yakeyi ga wani irin nauyi da naji kan yanayi, sake gwada bud’e idon nayi amma duk da haka ba sosai nake g
ani na, rufewa nayi kawai barci ya kwasheni, sai bayan magriba na farka, yanzu kam ina ganin ko ina da kyau, d’akin da nake dai ya min kama da asibiti, hakan yasa na tuno da abin da ya faru, ta6a kai na nayi naji bandeji, wai irin goggoron da akayi wa _Baba K_ sak, ina cikin ta6a kan nawa sai ga yan gidan mu sun shigo, kowa yana min sannu ina amsawa da kai saboda bakina yayi min nauyi, amare ma sunzo, duk sun k’ara kyau da girma gwanin ban sha’awa, wani 6angare na zuciya na ayyana cewa inama da nice, da sauri na kawar da tunanin daga raina dan kar ya samun damuwa
Bayan sun yimin ya jiki sai suka tafi, aka barni da _Ya Kolo_ sai amaren yayyina da kuma kanne na amare, sun jima sosai kafin suka tafi, inaji suna hira a tsakanin su, da alamu har sun saba, bayan tafiyarsu ne na samu na rama sallolin da ake bina, bayan na idar _Ya Kolo_ ta bani tea me kauri na sha da kuma tsire wanda _Baba K_ ya daure ya sayo, lailai na cire tuta, duk da cewa bai fi yanka bakwai ba, guda biyar naci na barwa _Ya Kolo_ ladar ganin ido. Zuwa dare aka kawomin ferfesun kayan ciki da tuwon shinkafa daga gidan babban yayanmu, matarsa Anty Hassana akwai iya abinci, sosai naci har sai da nayi gyatsa, _Ya Kolo_ ma taci amma bame yawa ba kasancewarta mutum mara son cin abinci da yawa, gashi ita ba kiba ba sai dai ba za’a ce da ita siririya ba.
Kwana mu uku a asibiti sannan aka sallame ni, matar data bugeni wai sau biyu tana zuwa ina barci, amma da gani tana ji da naira dan asibitin _A&S_ ta kaina, bayan ta kaina sai ta kira yan gidan mu ta wayana data tsinta a kasa ta sanar musu. Shi kuma yaron da yaje gidan mu ko ince mutumin ashe bana Allah bane dan kwace kud’insa yayi a hannun _Baba K_ bayan na fita, yace ba zai yi asara ba, ni duk wannan be dameni ba, tausayinsa ma nakeji domin nasan kwana uku masu zuwa ya zama marigayi, dama ya bar kud’in a matsayin sadaka ga _Baba K_.
Muna zuwa gida yan uwana suka rinka shigowa dubani, har amare sai da suka sake zuwa, daganan kuma aka cigaba da rayuwa daga inda aka tsaya. Ranar da sati guda ya cika mukaji labarin mutuwar yaron nan, Allah sarki sai da nayi kwalla, duk da cewa lokacinsa ne yayi amma zuwa gurina ne sanadi, shiyasa sam bana son magana da mazan da ba muharramai na ba, idan aka cire _Sani_ direba da d’an _Iya Loja_ babu wani wanda nake sakewa fuska saboda gudun irin abubuwan da suke faruwa.
Ba’a gama da _Habu_ ba an haifi _Bukar_ angulu ta koma gidanta na tsamiya, _Baba K_ dai kud’i sun kare ya zama ba ko sisi sai dai yanzu abin ya juye, sai yayi wa matan gidan mu aiki suke bashi abinci, sam banyi tsammanin haka ba, abin harda su _Mama Qudi_ sai ya gyara mata d’aki take tsakura masa a plate, _Inna Suwaiba_ kuwa ta karo walakaci dan shike mata wanke wanke, ni bansan me matan gidan mu suke son zama ba, duk kuma _Baba K_ ne ya jawo, dan yanzu sun bala’in raina shi, da ace ya tsaya a matsayin tsayayyen namiji a cikin gidansa da ba’a kai ga hakan ba, to yanzu wa gari ya waya, ya zama house boy a cikin gidansa, abin sai wanda ya gani, gwanin ban tausayi.
Muna zaune a tsakar gida sai ga wasu mutane sun shigo, maza uku mace d’aya, “baiwar Allah lafiya zaku shigo mana gida babu neman izini balle ku tsaya ace ku shigo?” _Goggo Fulera_ ts tambaya cike da mamaki, muma dai abin ya d’aure mana kai, sai dai kafin muyi wani abin sai ga _Baba K_ ya fito yana cewa ” yauwa Hajiya har kun k’araso kenan, shiyasa nace da kunzo ku shigo dan yan sa idon cikin unguwa jira sukeyi ayi wani abu su fara k’ananun maganganu, kinga gidan dai, ga kuma 6angaren da zaki sauna” ya fad’a yana gaba ita kuma tana biye dashi tare da samari ukun da suka rufa musu baya.
Da walakin goro a miya, Ashe shi yace su shigo mana kai tsaye, ikon Allah, to bama wannan ba, haya zai bata ne naga yana cewa taga gidan kuma ta shigo ta duba? No wonder naga jiya yana kwashe komai nashi zuwa 6angaren su _Khalil_ ashe abin da ya shirya kenan! lailai akwai kallo a gidannan..
Ya tabbata _Baba K_ ya bada hayan 6angarensa, babban abin takaicin ma shine fitinar da ya jawo wa kansa, matar dilar kayan maye ce, kuma dama haka takeyi idan ta samu gara sai ta wanke shi, ba zan dai fad’a muku abin da zatayi ba amma ku cigaba da bin labarina zakuji yanda komai zai faru.
_Atika_ sunanta, yaranta maza uku, mijinta ya dad’e da rasuwa, uwar miji kuma ta sako ta a gaba akan sai ta bar cikin gidan d’an ta tunda bada ita suka had’a kudi suka gina gidan ba, ita kuma data fita rashin mutunci sai ta sayar gidan tunda dama gadon yaranta ne, sai ta samu wani guri tayi musu gini na zamani, sannan tayi amfani da kud’in ta gurin fara business, duk irin business d’in da takeyi babu wanda ya kar6e ta kamar dealer d’in kayan maye, hakan yasa ta fara babu kama hannun yaro, yaranta ma ko da suka girma sai suka cigaba da taimaka mata, gashi su ba karatun zamani ba, babu arabi ba boko kamar dai _Baba K_ kan duk babu komai sai harkan neman kud’i kota halin yaya, gwara su abin ya na musu kyau duk da cewa Allah yana ara musu lokaci ne, amma _Baba K_ duk sanda ya gwada harkan neman kud’i sai dai ya kare a ha’ula’i.
Daga baya da harka ta bud’e musu sai suka koma damfara, zasu duba gidajen da idan an sayar zasu ci kud’i sosai, sai suje da sunan neman haya, idan sunci sa’a sun samu sai su zauna na mako biyu ko uku, daga nan dama akwai police d’in da suke aiki dashi, sai yazo da sunan bincike, sai a samu kayan maya a 6angaren masu gida, idan an tafi case su kuma sai su sai da gida a dillalinsu, sai a barka da cizon yatsa, to yanzu ma abin da suka zo yi kenan a gidan mu, ni kam bazance komai ba ina so in gani ko zai yi hankali ya fuskanci gaskiya.
Bayan sun tare a cikin 6angaren _Baba K_ sai shi kuma ya koma side d’in su _Khalil_ a hankali mata me wayo take jan _Baba K_ a jiki, haka zata dafa d’a’amun yaji kayan had’i ga dijaja zako zako a kai yana maka sallama, zata gayyoto _Baba K_ ta ba shi yaci ya koshi yana yada habaici wa matansa, ni nawa dariya harda hawaye domin ni nasan ana mishi iya kud’insa iya shagalinsa, kafin dai su wanke shi ai zasu barshi yayi kuzari saboda idan ya tashi figewa kar yayi yanda za’a d’auka k’anjamau ne ya mishi illa. Sosai yake kwasan gara6asar kudin gidansa da _Atika_ take shirin saidawa, har ga Allah ina tunanin me zai faru kuma a ina zamu zauna, amma ni burina _Baba K_ ya gane gaskiya ya kama Allah da manzonsa, ko ba komai idan ya shiryu zamu fi jin dadin rayuwa. Nasan dai ko gidan _Inna Abu_ ne ba zamu rasa guri ba dan gidan ba laifi yana da d’akuna kusan biyar ga boys quarters me d’aki biyu, zamu iya maneji a ciki.
Kamar kullun yau ma sun shimfid’a tabarma a gaban 6angaren nasu, sun bararraje harda _Baba K_ suna cin tuwon sakwara da miyar egusi wanda yaki namomi har da 6omo, _Baba K_ ya dage sai cisgar kud’insa yakeyi, ita kuwa sai murmushin mugunta take mishi. Ina fitowa _Baba K_ ya wurgamin harara, juyawa nayi tare da d’aukan takalmina, ina jin yaron matar yana cewa shi fa idan babu damuwa yana son a ba shi izinin yimin magana, tsaki naja da karfi nayi gaba.
Bayan dawowa ta daga shagon _Iya Loja_ still na same su a gurin tare da _Baba K_ “ke zonan” naji _Baba K_ yana fad’a, k’in kulashi nayi kawai nayi tafiyata “Khadeemah ba dake nakeyi ba?” Kallon _Inna Suwaiba_ nayi da take kokarin fitowa daga 6angaren mu nace mata ” _Mama Qudi_ tana ciki ne?” Dan tace zata fita kuma bana son yin abin da na shirya yau a gaban idonta, amsamin tayi da cewa “a’a bata dawo ba, nima na shiga duba jikin _Kisma_ ne kuma tace bata dawo ba” _Kisma_ da shegen raki idan tana ciwon abin harda shagwa6a ma yake damunta.
Gurinsu _Baba K_ na nufa bayan na wanke hannu na, zama nayi a gefensa sannan nace _Gani_ tare da d’aukan plate d’aya na fara zuba abinci, tuwon suka sakeyi da yamman nan, biski sukayi da miyar taushe ya sha man shanu, zubawa nayi iya yanda cikina zai d’auka na watsa dijaja kusan guda biyar a kai sannan nayi bismillah na fara aikawa cikina, ko kallo basu isheni ba, mamaki na basu daga su har _Baba K_ ina ga
mawa nayi gyatsa tare da cewa “Alhamdulillah, yauwa _Baba K_ gani kace inzo kuma har yanzu shuru kamar ka shuka dusa ba kace min komai bafa” na fad’a ina gyara zamana dan abincin ya sauka da kyau da kyau, ganin ya kasa magana yasa na musu sannu sannan na sake slippers nayi wucewa ta.
Tun daga ranar nima na karo walakaci kusan kwana uku nayi ina jera musu irin wannan rashin mutunci, _Baba K_ yaci nima inci kuma babu halin yayi magana, bayan kwana ukun da nayi ina cinye musu abinci suka dai na fitowa tsakar gida suka koma ci a cikin falonsu, dama ni abin da nake so kenan su dai na tsokalo wa yan gidan kwad’ayi.
Satin su biyu a gidan basu sake gigin cin abinci a waje ba, shima yaron daya ce zai yi min magana sai naji shuru bai tunkareni ba, ashe a waje ya samu labarin duk wanda ya tsaya dani da sunan soyayya ga abin da yake samun shi, shine yayi wa kansa fad’a ya kame bakinsa, ashe dai yana tsaron mutuwa a nan kusa.
A sati na uku mai aikuwa ya auku, shi na _Baba K_ ba wai sharrin sayar da kayan maye suka mishi ba, ce mishi sukayi, akwai wani me kud’i da yakeson ya sayi gida naira miliyan goma, kuma zai bayar cash, kasancewar shi idan dai abu da kud’i ne an gama da rayuwarsa sai ya zauna ya auna riban da zai samu, ya gina a miliyan biyar ya samu goma, zai iya sake irin ginin a unguwar masu kud’i, har ma ya bud’e shago, bayan kwana biyu yaje yace mata ya amince, tace mishi abin da za’a yi yanzu akwai wani gida na dubu dari biyar sai ya saya mu koma ciki saboda idan mutumin yazo yaji dadin ganin gidan da kyau, in yaso idan ya ba shi kud’in sai yayi wani abin da shi, haka kuwa akayi ta bashi dubu dari biyar ya sayi gida a hannun dillalinta, gidan na wani ne daya saya yayi tafiya ya bari a gyara mishi kafin ya dawo, kunga kenan sun bashi kud’i sun kar6e kud’insu, tare da had’a mishi takardun bogi. Haka rana tsaka muka tattara muka koma gidan, gashi gidan me kyau sosai kuma gidan sama da kasa d’akuna biyar a sama uku a kasa sai boys quarter d’aki biyu, duk me hankali ba zai yarda cewa gidan dubu dari biyar bane amma dake son kudi ya rufe idon _Baba K_ sai ya yarda, Su kuma suka sayarda gidan mu suka kara gaba suka barshi a cikin bala’i ba tare daya sani ba, sun kuma yi akan cewa da zaran mutumin ya dawo daga kasar waje zasu kawo shi, har lambar k’arya suka bashi na wani dan karya haka kullun yake k’ara saka _Baba K_ a ruwa, ga gida iya gida yana ciki kullun yana shan AC, nida na san dawar garin ban wani sake jikina ba, matan gidan mu kuma sun koyo ladabi yayin da _Baba K_ ya karo walakanci. _Atika_ kuwa tuni sun bar garin bauchi bayan sun sayar da gidan mu.