DIYAM CHAPTER 10
Kafin mu cigaba please let us all take a moment and pray for Maryam Sanda and then pray for ourselves. Allah ya sa wannan hukuncin da aka yanke mata ya zamar mata alkhairi a duniya da kuma a lahirar ta, mu kuma Allah ya kare mu daga mummunar kaddara, Allah ya kare mu daga sharrin shaidan da sharrin zuciya, Allah yasa mu fi karfin zukatan mu a kodayaushe.11 Bayan haka ina kira ga matan aure manyan mu da kananan mu, please idan kin tabbatar your marriage is not working, idan kin tabbatar kin je limit dinki na hakuri a gidan auren ki, please walk out of the marriage. Allah ya halatta saki for a reason, wani lokacin rabiwar tafi alkhairi akan cigaba da zaman. It is better a kiraki da bazawara then ki kasance in maryam sanda’s shoes.4 Sannan iyayen mu dan Allah ku dube mu da idon rahama, ku tausaya mana, dan Allah idan yarinya tazo gida tace ta gaji da zaman auren ta please ku bincika sosai, idan tana da gaskiya kuyi supporting dinta, kar ku tura yarku ga halaka, karku tura yarku zuwa wuta.1 Now, let’s continue with labarin Diyam maybe anan ma da akwai darasin da zamu dauka. Da mamaki karara fuskarsa yake kallona, maybe bai taba tsammanin zan iya mayar masa da magana haka ba. Yace “ke? Kin san dawa kike magana kuwa? Ni din ne ma kike cewa za’a makala miki?” Na cigaba da kallon sa cikin ido duk a cikin kokari na na nuna masa cewa bana jin tsoronsa, amma zuciyata in banda lugude babu abinda take yi. Ya daga hannu da niyyar wanka min mari sai kuma ya kalli gidan inda hayaniya take fitowa daga tagogin sama, ya fahimci yana dukana zan tara masa jama’a dan haka sai ya dunkule hannunsa sannan ya sauke, ya nuna ni da dan yatsa yace “in kika sake kika shigo gidan nan sai na karya ki” na fusge hijab dina daga hannunsa nace “not today, kuma ni bani zan shiga gidan ka ba sai dai a shigo dani dan dole” na juya na tafi na barshi anan ina jin dadi a zuciyata, ashe dai Sadauki bai tafi da dukkan Strength din nawa ba, ko kuma maybe a time din wannan hug din ne yayi passing some of his strength and courage to me.4 Muna komawa gida na wuce direct zuwa dakin inna, na gaisheta tana ta washe baki tace “kun dawo? Ya gidan?” Na tashi ina ninke hijab din dana cire nace “lfy lau” tace “lfy lau? Shikenan abinda zaki ce? Bayanin gidan zaki yi min inji dame dame aka saka kuma menene ba’a saka ba” nace “Inna ban sani ba nikam, ban shiga ciki ba a waje na zauna” nan fa takama fada, ni kuma nayi shiru har saida ta gama sannan nace “Inna yace inna shiga gidan sa sai ya kashe ni” sai ta girgiza kai tace “fada kawai yake yi, shima fushi yake yi saboda an matsa masa akan maganar nan, daga ke har shi ba kwaso amma abinda mu iyayenku muka hango ku ba zaku hango shi yanzu ba sai nan gaba zaku fahimta”. Washegari ina kwance kamar kullum sai ga aike wai ana kiran Inna, ta tashi ta tafi can kuma ta dawo sai naga cards a hannunta. Ta miko min tana kallon fuskata har na karba na karanta. Katin daurin aure ne, sunana da sunan Saghir, date din kuma nan da kwana uku. Na ajiye su akan cinyata ina jin dan kuzarin dana samu jiya yana draining kawai sai hawaye na ya fara zuba akan cards din. Na tuno abinda Sadauki ya gaya min “how litres of hawaye zaki zubar ne acikin wata daya?” “Be strong” he said, sai na kara karfin kuka na, wanne Strength ne dani kuma bayan bani da gata? Bayan ana so ayi amfani dafarinciki na gurin faranta wa wanda yake da gata? Saboda namiji ne shi nikuma mace? Ko saboda yana da uba a duniya ni bani da? Sai Inna ta zauna a kusa dani ta kwantar da kaina a kafadarta tace “Alhaji yace za’a hada daurin auren da addu’ar kwanaki arba’in din baffan ku, sai bayan daurin aure da sati daya sannan zaki tare, saboda ki samu damar gayyatar kawayenki da sauran shirye shirye”. Na dago kai ina sake kallon date din, sai nayi realizing shine date din da za’a yi resuming school. Tun daga lokacin taste din abinci ya dauke daga bakina, nayi kuka kamar idona zai cire har bana gani sosai, nayi addu’a na gaya wa Allah, kullum kuma sai na gaya wa Inna “Inna bana son auren Saghir” amma kamar busa sarewa nake yi, babu wanda ya dube ni, babu wanda ya mayar da damuwa ta wani abu mai muhimmanci ba kowa sai yace “zata daina ne, daga anyi auren shikenan ai ita mace mai rauni ce” ni kuwa jinsu kawai nake yi dan bana tunanin akwai ranar da zata zo wadda zan ji ina son Saghir. STORY CONTINUES BELOW Ranar Lahadi, 28 September aka daura aure na da Saghir. Ranar tun dana tashi da assuba na shiga toilet na rufe kaina na kwanta kan tiles nake kuka har aka gama daurin auren ban fito ba. Sai da Mama tazo sannan da kyar na bude mata kofar toilet din ta shigo ta fito dani, ta kori duk wadanda suke dakin ta zaunar dani akan gado ta bani Alqur’ani tace “kiyi ta karantawa zaki ji sauki a zuciyarki. Kiyi ta ambaton innalillahi wa inna ilaihir rajiun Allah zai sanyaya miki zuciyarki kuma yasa hakan ya zamo abu mafi alkhairi a gare ki” itama sai ta dauko Alqur’ani ta zauna muke karantawa tare, har sai da hawayen fuskata ya tsaya. Ranar daga ni sai ita muka zauna a dakin, ta saka ni a dole naci abinci duk da cewa da kyar yake sauka cikina. Sai kuma na cigaba da karatun ina jin nutsuwa tana samu na, ina jin karfin guiwar karbar kaddara ta, sannan kuma na gabatar da adduoi ga Baffa da Ummah, sannan na yiwa Sadauki addu’ar fatan alkhairi a duk inda yake. Na kuma samu kaina da tambayar kaina ko ya sani? Ko ya san an daura min aure da Saghir yau?2 Kwanakin da suka biyo bayan nan shirye shirye ne kawai akeyi na biki. Hajiya Babba baki har kunne sai shiga take yi tana fita tana ta tsare tsare. Inna babu abinda take yi, gaba-daya tayi wani irin shiru da ita sai dai ta saka ni a gaba tayi ta kallo. Ni kuma na zama kamar mutum mutumi, bana kuka amma bana uhm bana uhm uhm. Mama ce tazo ta debi wasu daga cikin kayan lefe na ta kai aka dinka min, sannan ta yiwa Asma’u itama dinkuna tare dasu Rufaida. Sai tace min “Diyam babu wani abin da zaki shirya ne? Ko yar walima haka ke da kawayenki?” Ban kalle ta ba nace “Mama kawayena ai duk sun koma makaranta, ss1 zasu shiga, ni kuma gidan miji zan shiga, waye zai bar karatunsa yazo bikina?” Sai tayi shiru bata bani amsa ba amma tana komawa gida sai ga yaya Mukhtar ya kawo Rumaisa, Rufaida da Muhsina sun taho da kayansu zasu zauna har sai an gama bikin. Hajiya Yalwati ta saka aka ware mana daki saboda yan uwan mu da zasu zo daga Kollere zasu sauka a dakin Inna. Ranar Rumaisa ta kawo min waɗansu littattafai guda biyu ‘rayuwar aure a musulunci’ na daya dana biyu tace “ki karanta zaki samu idea akan zaman aure” na karba kawai nace “Nagode” sai kuma tayi dariya tace “ni ban san me kike yiwa fushi haka ba. Mijinki kyakykyawa, kinsan da ina da crush akan hamma Saghir amma yanzu na hakura tunda ya zama mijinki” na tabe baki kawai a raina ina cewa ina ma dai zamu iya chanjen place da ita? Ita ta zama matar tasa ni in koma ita? Ana gobe kamu Aunty Fatima tazo da mai kunshi zata yi mana, ranar sunga taurin kaina dan da kyar na zauna akayi min dan haka duk wanda baisan bana son auren ba sai daya sani a ranar. Ana gama wa kuma na saka hannu da gangan duk na damalmala kunshin ya chabe. Aunty Fatima kamar ta rufeni da duka dan haushi amma a haka ta kyale ni. Da daddare tace muje saloon sai na saka mata kuka a dole ta kyale ni kar in tara mata jama’a. Ranar kamu sai da inna tazo ta sakani a gaba sannan na tsaya akayi min kyalliya. Mun zo zamu tafi gurin da aka shirya dan yin kamun kenan naji wata tayi comment “kunga amaryar kuwa? Yar mitsitsiya” ai kuwa ina jin haka na juya na koma daki a dole sai mai kamun ce ta bini dakin ta kama ni a can. Ranar yini kuwa ni wuni nayi da zazzabi dan haka suka dai suka sha bidirin su. Washegari kai amarya, tunda safe Mama tazo, yau ne kadai na ganta tun da aka fara bikin. Tana zuwa yau ma duk ta kori su Rumaisa da dama duk sun addabeni, ta saka ni a gaba yau ma muka yi ta karatu kamar ranar nan, tare muka ci abinci mukayi sallah tare kuma sam bata yi min wata magana data danganci aure ba har magrib tayi sannan ta saka ni nayi wanka ta dauko min wani lace fari tas tace in saka. Ta gyara min fuskata simple make up sannan ta saka min sarka da dan kunne tayafa min farin mayafi ta kuma feshe ni da turare. Na zauna a bakin gado ta rufe min fuskata da mayafin sannan ta mike zata fita, na rike rigarta nayi mata tambayar da ta jima tana yawo a zuciyata, nace “Mama Sadauki ya sani? Ya san an daura min aure?” Ta dauke kai tace “ban sani ba Diyam, na kira layinsa baya shiga maybe ya chanza layi ne” sai ta fita, an jima suka dawo tare da wata matar dana fahimci daga baya cewa kanwar Hajiya Babba ce. Tana zuwa ta bude fuskata tace “Masha Allah. Tubarkallah. Lallai Sagjir yayi dace da kyakykyawar mata. Allah ya baku zaman lafiya, Allah yayi muku albarka, Allah ya baku zuri’a ta gari” Mama tace “ameen”. Sai suka kamani a tare suka fita dani. Sam ji nayi zuciya ta dake bana jin wani kuka kuma. Muka shiga dakin Inna anan na tarar da ita tana kwance ashe wai bata da lafiya tun safe. Na durkusa a gabanta tace “Allah yayi miki albarka Halima, biyayyar da kika yiwa iyayen ki Allah yasa kema naki yayan suyi miki. Allah yasa wannan auren shine mafi alkhairi” muka ce ameen muka tashi. Zamu tafi part din Alhaji Babba aka ce mana wai baya nan ya fita tun safe. A raina sai naji ina kewar Baffa, ba zai taba fita ba ranar da yasan zan bar gida in tafi gidan miji. Gidan kawu Isa muka shiga yayi min fada shima, sannan muka shiga mota muka tafi sauran motocin suna biye damu.1 Har muka je gidan banyi kuka ba. Muka shiga ciki sannan naji mun fara gawa stairs sannan muka shiga wani palo sai kuma wani daki. Aka zaunar dani akan gado Mama ta rufo kofa tazo ta zauna a kusa dani ta rike hannuna ta fara magana a hankali “Diyam ki saurare ni sosai kiji abinda zan gaya miki. Yanzu kin zama matar aure, kin bar karkashin iyayenki kin koma karkashin mijinki haka zalika aljannar ki ta koma karkashin mijinki. Bauta zakiyi, amma ki saka a ranki cewa ba Saghir zaki bautawa ba Allah zaki bautawa. Auren Saghir shine kaddararki, shine jarabawarki. Biyayyar Saghir a yanzu ita ce gaba da komai a gurinki in banda addinin ki. Na sami cewa ba’ayi miki adalci ba, na sani cewa iyayen Saghir basu kyauta ba sun kasa tankwara yaron su tun yana danye har sai daya bushe tukunna sannan kuma suka dora hakkin tankwara shi a kanki, duk da kasancewarki mai kankantar shekaru amma ni nasan zaki iya, in dai har zaki yi masa biyayya, ki kula da cikinsa da shimfidarsa, ki kasance mai tsafta mai hakuri da juriya da kawar da kai a lamuransa, to kuwa duk girman kansa sai kin mayar dashi tamkar rakumi da akala musamman tunda kina da kyau kuma shine abinda aza da yawa a yanzu suke so”. Ta jima tana yi min nasihohin hanyoyin da take ganin zan bi in jawo hankalin Saghir ya soni, ni kuma sai nayi wa kaina tambayar “ta yaya zan saka wanda bana so ya soni? Biyayya ga abinda baka so is extra hard right?”2 Ta mike zata fita sai na rike zanin ta na kifa fuskata a cinyarta na fara kuka mai tsuma zuciya amma sai tasa hannunta ta cire hannuna daga zaninta ta juya ta fita. Na rufe fuska ta da hannayena ina kuka, ji nake kamar wannan auren shine karshen rayuwata, ji nake ina ma mala’ikan mutuwa yazo ya dauki raina, anya kuwa zan iya yiwa Saghir biyayyar aure kamar yadda ya kamata? Kuma gashi aljanna ta tana defending on wannan auren alakakai din and I so much want to go to jannat idan na mutu, wannan yasa na fara addu’ar Allah yasa in mutu a wannan ranar. Ina cikin kuka na su murja suka shigo suka zagaye ni, Rumaisa tace “ke baki san yanzu an daina kukan aure bane ba wai? Wannan ai sai ki bada mu in abokan ango suka zo” murja tace “suka zo ina? Wai nan gidan? To ni kam bada ni ba babu wani siyan baki da zan zauna yi yazo ya hada mu ni da amaryar ya huce haushin sa akan mu” Rumaisa tace “ke dan Allah ki daina fadar haka ai sai ki saka taji tsoro”. Suna ta hirarrakin su ni dai na mike nayo alwala na gabatar da sallar isha ina kaiwa Allah kuka na. Ina nan kan sallayar sai na jiyo muryar yaya Mukhtar daga palo, sai ga Rufaida ta shigo tace “wallahi yaya Mukhtar yace duk ku fito mu tafi in ba haka ba sai dai ku kai kanku gida dan shi tafiya zaiyi. Wannan unguwar tasu kuwa ba abin hawa zaku samu ba, angon kuwa in ya zo ko suma kuke ba zai kaiku gida ba” kusan duk a tare suka mike suna harhada kayansu. Na kalle su da kumburarrun idanuna nace “yanzu tafiya zaku yi ku barni ni kadai a gidan nan?” Rumaisa tace “da anjima angonki zai zo, kuma ai naga kuna da maigadi” Murja tace “idan yayi tafiya kiyi min waya sai inzo in taya ki zama, amma in yana nan ba zan zo ba”. Yaya Mukhtar ya sake kwala musu kira dan haka suka fice da sauri. Ina jinsu suka sauka daga bene, ina jinsu suka fita daga palon kasa suka rufe kofa sannan naji sun shiga mota an bude musu gate sun fita, na tashi da sauri na leka ta window na hango hasken motar su har sun dau hanya. Sai kuma na tsaya ina kare wa unguwar kallo, babu gidaje sosai sai kwangwaye wannan ya kara wa unguwar duhu. A bakin gate naga mai gadi a zaune akan benchi da radiyo a gefensa. Sai naji wani irin loneliness sannan kuma naji wani irin tsoro. Na haye kan gado da sauri sai kuma wani tunani yazo min sai na tashi da sauri na bude kofa na fita. Sai na ganni a cikin wani palo madaidaici wanda aka kawata da kujeru da kayan kallo da adon frames a bango da sauran tarkace. Kofofi uku ne a palon, na fara bude su daya bayan daya ina neman kitchen amma sai naji daya a rufe take dayar kuma wani bedroom din ne kudan irin wanda na fito daga ciki sai banbancin colors. Na sauka daga bene da sauri shima palon ne amma yafi na sama girma da tsaruwa, sai wadansu kananan bedrooms guda biyu da dining room mai hade da katon kitchen. Ban tsaya kallon komai ba saboda yadda jikina yake karkarwa saboda tsoro, na shiga kitchen din na fara bude drawers ina neman abinda ya kawo ni, can naga set dinsu, wukake, na dauki wadda naga tafi kowacce girma na boye a rigata na sake fita da sauri na haye sama. Dakin da aka kaini na koma na tura kofa da niyyar locking amma sai na ga babu key a jiki. Na fara fara neme neme cikin lockers din dakin amma babu key babu alamarsa. Na shiga toilet na duba nan ma babu. Sai na dawo na zauna akan gado kamar zanyi kuka amma tears din sun tsaya, maybe sun kare. A hankali nace “Sadauki, Please come and take me away from here”.2 Sai na kwanta na dunkule a guri daya, na jima a haka sannan bacci ya fara fusgata ina yi ina farkawa a tsorace cike da mafarkai, wani mafarkin wai Sadauki tazo yace in tashi mu gudu, wani kuma wai Saghir yazo ya zare belt dinsa yace ba yace kar in sake inzo gidan nan ba? Cikin baccin naji karar bude gate, na tashi zaune a tsorace, sai nayi sauri naje na kashe fitilar dakin sannan nazo na leka window, mota naga ta shigo tayi packing, sai kuma ya fito yana tafiya unsteadily. Ina lura da maiigadi yana gaishe shi amma bai ko kalle shi ba ya taho cikin gidan. Nayi sauri na tura kofar dakin da na ke ciki sannan na dauki wukata na tafi can lokon gado na kudunduna a cikin duvet, naji ya bude kofar palo ya shigo amma banji ya rufe ba, najiyo shi yana hawowa sama sannan naji ya bude kofar dakin da yake kusa da inda nake, sai kuma takunsa yana tahowa sannan naji ya bude dakin da nake, na dauke numfashi na ina kara addu’ar Allah ya dauki raina. Ya kunna fitila sai can kuma naji ya kashe amma na tabbatar ya ganni, sai kuma naji ya karaso inda nake kudundune ya saka kafarsa mai sanye da takalmi ya dake ni da ita “ke!” Na dunkule hannuna a handle din wukata na mike da sauri ina nuna shi da ita, fuskata cike da hawaye nace cikin murya mai karkarwa “if you dare touch me!” Ya tsaya yana kallona ta kasan ido, da mamaki a fuskarsa sannan cikin wata irin murya da tafi yi min kama data yan maye yace “what? What will you do?” Na sake nuna shi da wukar “in ka kara wani takun kusa dani na rantse I will….” Ya tako step din without hesitation yace “you will what?” Gabadaya jikina karkarwa yake yi hatta wukar hannuna rawa take yi tana neman faduwa, hannu daya yasa ya doke hannun nawa sai wukar ta fadi. Na dunkule a kasa “don’t touch me please” sai yasa hannu ya kamo wuyan rigata ya mikar dani tsaye, ya hada ni da bango sannan ya kawo fuskarsa dai dai tawa, wani wari naji daga bakinsa, ba warin kazanta ba amma wani wari marar dadi, nayi saurin dauke kaina yace “mena gaya miki zanyi miki in kika sake kika shigo gidan nan? Kin dauka wasa nake yi dake ko?” Nace “wayyo Allah na, wayyo Sadauki” ya saki wuyana yana kallona “Sadauki? Sunan saurayin naki kenan? To yazo ya nuna sadaukan ta kar tasa in gani” nayi shiru a raina ina fatan zaizo din, yace yana kara matsowa jikina “bana ce miki karki zo gidan nan ba?” Na girgiza kai nace “nima kawo ni akayi, Bani nazo da kaina ba. Please ka mayar musu dani kace ba ka sona” yace “with pleasure. Amma kafin in mayar dake sai na yi musu proving abinda na gaya musu su kaki yarda. Kinyi min kankanta da aure” yana fadin haka sai ya saki wuyana, sannan ya hankada ni na fada kam gado kaina ya bugu da jikin frame din gadon. Na fara ganin dusu dusu a idona amma duk da haka sai nayi kokarin mikewa sai dai nauyin da naji a kaina ya sa na kasa ko motsi. Amma sai na takarkare tun karfi na zunduma ihun kiran Sadauki a lokacin da naji zani na ya bar jikina. Sai kuma naji wani piercing pain daya taho tun daga kasana ya dire har cikin kwakwalwata. Sai muryar ihun ta dauke, numfashi na ya dauke, naga wani haske a idona. The last thing da naji kafin hankali na ya barni shine muryar Sadauki lokacin da yake ce min “everything is going to be alright”.2 A short episode. But mu fara jajanta wannan lamarin tukunna. Dear parents, This might be what will happen to your daughter in kuka rufe idon ku kuka aura mata wannan lalataccen dan masu kudin da bata so, ko wannan alhajin da yake zuwa a babbar mota, ko kuma wannan dan uwan naku da yaki aure shekara da shekaru kukayi tunanin bara ku hada su dan inganta zumunci. It might not always be the right choice, especially idan wanda za’a hada ta da shi din ansan bashi da halayya mai kyau. Yaya amana ne a hannunmu, don’t trade them for wordly things please.3 Yes, addini ya yarda iyaye su taya ƴaƴansu zaben mijin aure, amma kuma bai ce a tirsasa musu ba. Akwai ingantaccen hadisin ma da ya nuna haramcin hakan.1 Allah ya sa mu dace.3 Sama sama nake jin maganganu a kusa dani, a hankali ake maganar amma sai naji tamkar wanda ake hayaniya saboda ciwon da kaina yake yi min. Na kai hannu a hankali na dafe goshina sai naki ance “sannu Diyam. Ta farka” naji muryar kamar na santa amma sai na kasa gane mai ita. Wannan yasa nayi kokarin bude ido na amma sai naji sunyi min nauyi. Na mayar dasu na rufe. Sannan na fara tunani where am I? What happened? A hankali pictures din abubuwan da suka faru suka fara yi min yawo a kaina. Mutuwar Baffa da Ummah, bankwana na da Sadauki, auren dolen da akayi min, abinda Saghir yayi min da daddare. Nayi saurin bude idona sannan nayi kokarin tashi zaune ina girgiza kaina hoping in ganni a gidan mu in ga cewa duk wannan wani mugun mafarki ne nayi. Amma wani irin azaba da naji daga kasana wadda cikin second daya ta gauraye duk sassan jikina ita tasa na koma da baya na kwanta, bana bukatar assurance, wannan ciwon ya tabbatar min cewa ba mafarki nayi ba, ya tabbatar min cewa Saghir raped me. Na runtse idona ina so hawaye yazo min amma yaki zuwa sai wata irin kuna da zuciyata take yi min. Na tuno alkawarin da Sadauki yayi min “ki saka a ranki cewa Sadauki zai kasance tare dake a koda yaushe, kome ya faru dake ko me kike yi ki saka a ranki cewa I will always be watching over you. This is my promise to you” sai nace “where were you Sadauki?” Duk sanda yayi min alƙawari yana cikawa amma ta gaza cika wannan. Na kai hannu zan taba inda nake jin tamkar anyi min tsarki da attaruhu sai naji an rike min hannu, na bude idona naga Adda Zubaida a zaune a bakin gado tana rike da hannuna, nabi dakin da kallo, bakin dakin nan ne dai da aka kawo ni jiya aka ajiye tamkar akuyar da akayi sacrificing dan a kama zaki, dakin da zakin kuma yazo ya karasa destroying rayuwata, ya karasa karbar dan sauran abinda nake rakama dashi.+ Na sauke idona kan Adda zubaida da fuskarta take nuna tsantsar tausayi na. Ta kara cewa “sannu Diyam” sai naji wata muryar kuma a gefe na itama tana yi min sannu, na juya naga wata mata da muke kira Uwani, kamar kanwa take a gurin hardo dan haka kamar kaka ce a gurin mu. Na kalli jikina naga doguwar riga ce yar kanti marar hannu. Na koma na kwanta a hankali nace “Adda ki kirawo min Inna dan Allah ki ce nace dan Allah tazo ta daukeni daga gidan nan” ta girgiza kai tace “Diyam ba zan iya ba, bazan iya gatawa innarki wannan mummunan labarin ba. Da wanne zata ji. Na dai gayawa su iyayen tantirin. Su san ga abinda dansu ya aikata” Uwani tace “to ya zasu yi? Sai addu’a” Adda tace “wallahi uwani duk abinda Saghir ya zama a duniya da sa hannun mahaifansa. Basa son laifinsa, soyayyar da suke yi masa ta rufe musu ido ko me yayi basa tsawatar masa. Duk dukiyar Alhaji fa ta salwanta a hannun Saghir kullum in ya di ba ya tafi sai sun kare zai dawo, in muka yi magana ace masa ai kasuwanci yake yi bayan mun san babu wani kasuwanci da yake yi sai iskanci. Sai yanzu kuma da lokaci ya gama kurewa sannan suke son su gyara shi. Yanzu kalli uban kudin da aka kashe aka sai masa auren nan aka sai masa gidan nan aka dauki kankanuwar yarinyar nan marainiyar Allah aka bashi amma dan iskanci shine a ranar da aka kawo ta yayi mata wannan wulakancin ya tattara kayansa ya gudu” uwani tace “au wai tafiya yayi? Ina ya tafi?” Adda tace “to wa sani ne. Da assubar fari ya kira wayata wai in taho gidansa Diyam zata mutu, ina jin gaka nasan yayi tsiyar. Haka nazo na samu Diyam tana numfashi da kyar maigadi ya gaya min tun assuba yaga ya saka akwati a mota ya fice, na sake kiran wayarsa bata shiga. Ni kuwa na kira uwar da uban nace to ga abinda Saghir ya aikata nan kuma ya gudu. Alhaji yayi ta salati, in ba sa’a muka ci ba in anjima kiji shi a asibiti hawan jini ya tashi, kuma hawan jinin mun san Saghir ne ya sama masa. Ita kuma Hajiya Babba saboda tsabar son kai ina gaya mata sai ta kama rokona wai dan Allah kar in gaya wa kowa mu bar maganar a tsakanin mu, in kai Diyam asibiti amma kar in gaya wa kowa. To ni wa zan iya gayawa wannan kayan takaicin ne?”. Uwani tace “hmmm, ni ina bacci ai taje ta same ni wai dan Allah in taho gidan nan in taimaka wa Diyam, ina ji nasan an yi aika aika kenan. Kuma dan dai ya saka mata karfi ne, amma in da a hankali ya bita babu abinda zai same ta” Adda tace “to ina zai bita a hankali? In yayi haka ai bai cika dan iska ba” sai tayi tsaki “ni ban ma san yadda zanyi ba wallahi. Na daiyi mata ruwan dimi na dan gasa ta, ni ba zan iya kaita asibiti ba wallahi wannan ai abin kunya ne, in je ince musu me? This is a rape case zasu iya cewa sai na dauko police” ta sake yim tsaki “Allah wadaran naka ya lalace. Amma ai duk wanda ya sai rariya dama yasan zata zubar da ruwa”. Sai kuma ta dauko waya tayi kira. “Hello, sister Asiya dan Allah in kina off ki taimaka min, wata kanwata ce akayi wa aure jiya kuma yar karama ce wallahi…..to kinsan halin maza… Dan Allah in baki address din kizo ki duba min ita” sai kuma tayi mata godiya ta katse, ta sake tsaki tace “this is very uncomfortable wallahi”. STORY CONTINUES BELOW Duk maganar da suke yi ina jin su amma na rufe idona kawai dan bazan iya tankawa ba. Addu’a kawai nake jerawa a cikin zuciya ta “ya Allah duk wanda yake da hannu akan wannan wulakancin da aka yi min ya Allah ka saka min. Ya Allah tafiyar nan da Saghir yayi Allah kasa yayi hatsarin mota ya mutu kar ya dawo. Ya Allah ka hada shi da yan fashi a hanya su sabauta shi kamar yadda ya sabauta ni. Ya Allah ka saka ginin gidan da zai sauka ya fado masa cikin dare ya tarwatsa shi kamar yadda ya tarwatsa rayuwata”.3 Ina nan kwance matar tazo, ina jinta suka gaisa da Adda zubaida da Uwani. Sannan ta zauna kusa dani tace “amarya” na bude ido na kalleta na rufe, tace “kar ki zama raguwa mana. Tashi tsaye mu gani” nayi saurin girgiza kaina sai ta kama kafafuwana tayi bending dinsu, nayi kara saboda jin cinyoyi na nayi kamar wadda nayi frog jump, ta bude rigata tana dubawa tace “babu tear, the place is just sore kuma akwai bruises” ta rufe rigar tace “zanyi mata allurar da zata rage mata pain sannan zan rubuta muku magani ku siyo mata. Sai take amfani da ruwan dumi sosai” Adda tayi mats godiya sai ta juyo tana kallona tace “ina angon? Yazo ya mayar dani gida” ita as a joke ta fada ni kuma kalmar angon ma bata min rai tayi. Har zata fita ta juyo ta sake kallona tace “amma yarinyar nan tayi kankanta da aure wallahi Zubaida. Wai dama har yanzu fulani kuna irin wannan auren?” Ban dai ji amsar da Adda ta bata ba suka fita.1 Ranar har dare Adda Zubaida tana guri na, kuma ta saka ni na shiga ruwan zafi sosai sannan kuma ta dafa min abinci mai kyau ta matsamin na ci. Sai kuma ta saka ni nayi tafiya wadda sanda ina yi ji nayi kafafuwana kamar ba’a jikina suke ba. Uwani ce ta zauna ta kwana a gurina washegari sai ga kayanta Alhaji Babba ya saka a aiko mata dasu yace ta zauna a gurina har sai Saghir ya dawo daga tafiyar da yayi. Sai da nayi kwana uku a sama ina jinyar kaina sannan na iya saukowa kasa, ina saukowa daga bene idona ya sauka akan katon hotonsa ya sha shadda army green wadda ta kara haska farar fatarsa, ya turo hular nan gaban goshi fuskarsa dauke da murmushi, sai a lokacin nayi tunanin kamar ban taba ganin murmushin sa ba. Na taka naje har gaban hoton na tsaya ina kare masa kallo sai kuma na saka hannu na ciro hoton na sauke shi kasa sannan na juya shi ya koma kallon bango. Jikina ya warke, amma tabon zuciyata yana nan kuma banajin zai warke har abada. Saghir kuma kullum zuciyata kara tsananta tsanarsa take yi. Ko mai irin sunansa baba son inji an ambata ballantana shi. Babu sallar da zanyi ba tare da nayi addu’ar neman sakayya tsakani na dashi da duk wanda ya aura min shi ba. Kullum kuma da fargabar dawowarsa nake kwana da ita naje tashi. Ko wani kwakwkwaran motsi uwani tayi sai na firgita ballantana in naji an taba gate. Muna da kayan abinci wadanda aka kawo da sunan kayan gara, kudi kuma duk karshen sati Alhaji yana aiko mana dashi shi dai kawai burinsa in zauna a gidan. Uwani tana tare dani, kuma duk weekend su murja ko su Rumaisa sukan zo su kwanar min biyu, wannan sosai yakan rage min kewa amma a zahiri a zuciyata kuwa empty nake jin heart dina. Kwanaki suka wuce haka satittika, sai watanni suka biyo baya har nayi wata uku a gidan Saghir amma babu shi babu alamar sa. A ranar da na cika wata ukun ne Hajiya Babba tace mu shirya muje gida mu kwana biyu. Da wuri driver yazo ya dauke mu muka tafi. Tun daga bakin gate na lura da yadda gidan ya chanja, ma’aikata sun ragu, motoci ma haka, gidan kuma yayi datti flowers sun mutu. A main palo muka samu Hajiya Babba, har da mikewar ta tsaye ta tarye mu da fara’a “sannunku da zuwa uwani” ta jawo ni jikinta zata rungume ni sai na zame na durkusa na gaisheta, ta amsa da fara’ar ta ni kuma na mike na nufi dakin inna ta ina jin missing dinta a raina, ina jin Hajiya Babba tana cewa “Masha Allah, lallai Diyam, wannan girma haka kamar ana hura ki?” Ina shiga na tarar da Inna tana ta murnar zuwa na itama. Na je na rungume ta tana ta dariya ta dan tura ni baya tace “Diyam kinyi girma haka? Alhamdulillah, naji dadin ganin ki sosai. Ni ina nan ina ta fargabar halin da kike ciki gashi Saghir ance yayi tafiya kasar waje business ya rike shi” na zauna akan gado ina rungume da Asma’u ina dariya. Ta zauna gefe na tana ta yi min tambayoyi game da halin da nake ciki ni kuma ina bata amsa a takaice. Tace “naso inyi miki girki tunda aka ce zaku zo, nasan kina son tuwo amma kinsan bana girki a gidan nan” na kalle ta sai na lura da yadda ta fada tayi baki bakinta duk ya bushe. Nace “inna ku ya kuke ciki? Lafiya dai ko?” Tace “hmm, lafiya lau” nayi shiru dai ina kallonta dan na fahimci ba karshen maganar ba kenan. Sai nace “Inna an saka Asma’u a makaranta kuwa?” Tace “eh an saka ta” sai ta sake shiru, ta jima kuma sannan tace “na jima inata faman bi akan zancen makarantar yarinyar nan, da kyar na samu aka saka ta amma wai ga makarantar da sauran yaran gidannan suke yi sai aka dauke ta aka saka a makarantar gwamnati. Tana kallon yaran zasu shiga mota a tafi dasu makaranta ita kuma sai dai ta tafi a kafa, har kuka sai da tayi min wai ita makarantar su siyama take so amma haka ba bata hakuri saboda babu yadda zanyi” Naji zuciyata tana zafi nace “to Inna ke ki saka ta ata kudin mana? Ina kudin da ake samu a garejin baffa duk wannan watannin ayi amfani dashi mana a saka Asma’u a makaranta mai kyau” tace “hmmm. Diyam kenan. Wanne gareji kuma kike magana? Tun a lokacin bikin ki nayi wa Alhaji maganar gare jin kinsan me yace min?” Na girgiza kaina tace “yace garejin shi aka siyar akayi miki kayan daki” na bude baki ina kallon ta nace “garejin? Da duk motocin da suke ciki?” Eh kawai tace, na sunkuyar da kaina sannan nace “filin Sadauki fa? An bashi kayansa?” A can kasa ta amsa tace “har dashi ya sayar”. Na tashi na shiga toilet na hada kaina da kofa, rabona da in kira sunan Sadauki tun ranar da aka kaini gidan Saghir amma ni kadai na san me nake ji a zuciyata, I missed him so badly dan tunda nazo duniya ban taba yin wannan dadewar ba tare dana ganshi ba yanzu kuma ambatar sunansa ya tayar min da mikin dake cikin zuciyata. Na tuna ranar da yaje school gurina da murnarsa yake bani labarin Baffa ya saya masa fili, kuma da kudinsa daya tara masa ya siya masa his hard earned money amma wai Alhaji Babba ya siyar. Ban roki Allah sakayya bama saboda nasan tabbas zai yi maybe slowly but surely.1 Bayan na dawo dakin ne uwani ta shigo suka gaisa da Inna ta kuma kawo min mangwaro na dana siya a hanya. Inna ta karba tana cewa “wannan mangwaron Diyam ai bai nuna ba aka baku shi” na karba na fara sha ina cewa “yafi dadi ai” sai ta tsaya tana kallona sannan ta juya ta kalli uwani tana girgiza kai sai naga uwani ta gyada mata kai, sai kuma suka juyo suna kallona a tare ina ta rasgar danyen mangwaro. A raina nace “su kuma wadannan menene naga suna magana da ka kamar kurame?”.2