DIYAM CHAPTER 17
A jikin kofar na zame na zauna ina jin zuciyata tana wani irin bugawa, ji nake yi kamar zan mutu, kaina yayi wani irin zafi kuma hawaye ya tsaya a ido na. Ban taba tunanin it’s possible ka tsani mutum kamar yadda naji na tsani Saghir a lokacin ba. Na fara girgiza kaina ina cewa “no no no” kamar mahaukaciya. I can’t even imagine komawa gidan Saghir a matsayin mijina, I can’t imagine him touching me again. I would rather die. Ina jiyo maganganu a palo kamar muryar inna amma bana gane me take cewa, sai naji ta taba kofar amma da yake ina jikin kofar sai ta kasa bude wa sai naji tana kiran Asma’u. Sai kuma naji ana knocking kofar. Da kyar na bude idona na matsa daga jikin kofar sai suka bude suka shigo su biyu sannan Subay’a ta shigo itama tana kallo na sai naga Asma’u tayi sauri ta dauke ta sun sake fita.+ Inna ta durkusa gabana tana taba wuyana tana magana a hankali amma ni bana jin ma me take cewa. Sai kuma naga ta kama ni ta mayar dani kan gado ta kwantar dani ta juya na riko rigarta sannan cikin muryar da naji kamar ba tawa ba nace “Inna bazan koma ba. In na koma mutuwa zanyi” ta juyo tana kallona sai ta zauna tace “komawa ina?” Sai kawai na bita da kallo, wato Saghir saboda bai daraja ta ba bai ma gaya mata cewa ya mayar dani ba? Sai ta gane me nake nufi tace “cewa yayi ya mayar dake?” Ban iya bata amsa ba sai kuka, sai ta mike tsaye “wannan wanne irin abu ne? Wanne irin ya mayar dake kuma? Suzo nan su kare mana cin mutumci sannan kuma ya mayar dake bayan babu wani mataki da aka dauka? To babu inda zaki koma. Yanzu fa Hafsa take bani labarin wai kawun ku Isa ya bashi Suwaiba” Suwaiba yar kawu Isa ce itama kuma kusan set din mu ce, mun dan girme ta kadan. Lokacin muna yara ita da Rumaisa ne suke crushing on hamma Saghir, murja tana yawan gayamin cewa har yanzu suwaiba tana son Saghir amma ni ban taba ko saka abin a raina ba. Inna tace “wato su suna can suna kokarin yi masa huce haushi shine shi kuma zai zo nan yace ya mayar dake? To ku biyu yake so ya hada a gida daya ko kuma ya yake so ayi? Ai indai kinga kin koma gidansa to ki tabbatar an zauna ne an hada ku anyi muku fada kowa an bashi laifin sa bawai kullum ace kece da laifi ba” tayi ta fadanta ni dai ina jinta kawai. Amma ni a raina nasan ko anyi mana fadan bana jin zan iya sake zama da Saghir, not after what he did today, not after what he said a gaban Sadauki. Tuni da Sadauki da nayi sai naji wata irin fargaba ta shige ni. Tsoro nake ji sosai, tsoron abinda Sadauki zai iya yi akan furucin da Saghir yayi a gaban sa. Ina tsoron zuciyar Sadauki, ina tsoron zafin sa, ina tsoron rashin tafiyar sa, considering abinda yaji da kuma yanayin da ya fita a ciki, bansan hukuncin da zai dauka ba. Sai na samu kaina dayi masa addu’ar Allah ya taushi zuciyarsa Allah ya hane shi ga aikata abinda zaizo yayi nadama. Sai magrib na tashi. Nayi alwala nayi sallah nayi kuka sosai a cikin sujjada ta na roki Allah ya kawo haske a cikin al’amura na. A lokacin ne Asma’u suka dawo ita da Subay’a. Subay’a ta taho gurina da gudu ta fada jikina tana kallona tace “Mommy kin daina kukan? Dazu naga kina kuka” nace mata “na daina subis” sai tayi dariya tace “Daddy ya tafi ko? Dama cewa yayi zai kawo ni gurinki in kwana biyu sai mu koma gidan mu tare” bance komai da akan wannan sai tace “Mommy kullum sai nayi kuka nace da Hajiya ta kawo ni gurinki ita kuma taki. Mommy dan Allah ni kar a mayar dani can gidan gwara in zauna a gurin ko kuma mj koma gidan Daddy na tare” sai na daga ta nace taje tayo alwala tayi sallah. Na lura ta rame, ta fada sosai tayi baki. Kamar ba’a kula da tsaftarta sosai sannan idonta ya nuna alamar damuwa. Sai na yanke wata shawarar, bawai ni kadai ce bazan koma gidan Saghir ba har da Subay’a ma ba zata koma ba, tazo kenan. Da dare ina jin Inna tana cewa Asma’u ta kira mata Sadauki, kamar tasan ina son in tabbayda lafiyar sa. Asma’u ta kira switched off, a raina nace nasan za’a rina, amma ban furta komai ba nayi shiru kawai. Nan fa hankalin Inna ya tashi tace “wai me ya faru ne mai zafi a tsakanin su? Ni sam banji dadin yadda naga Sadauki ba tunda kuma ya fita hankalina yana kansa wallahi” ta juyo tana kallona tace “me Saghir din ya gaya masa me zafi haka?” Na sunkuyar da kaina kawai, ni ba zan iya gaya mata kalaman Saghir ba. Jin nayi shiru sai tayi ajjiyar zuciya tace “Allah ya kyauta”. STORY CONTINUES BELOW Washegari babu kunya babu tsoron Allah sai ga Aunty Fatima nan da Hajiya Yalwati da kanwar Hajiya Babba wai Alhaji Babba ya turo su su gaya wa Inna cewa Saghir ya mayar dani, a gaya min in shirya sai mu saka rana ni da Saghir din sai yazo ya dauke ni. Ni kawai kallon su na tsaya ina yi cike da mamaki. Inna tace “yanzu Fatima har da ke? Har dake za’a ci amanar marigayi dan bashi da rai?” Aunty Fatima tace “me akayi Amina? Yanzu mayar da auren shine cin amana?” Inna tace “ba mayar da aure ne cin amana ba, rashin kulawa da nuna son kai shine cin amana” sai ta lissafa musu dukkan laifuffukan Saghir wanda ni na gaya mata tace “ni ba wai goyon bayan Diyam nake yi ba ko kuma bana so ta koma dakinta ba, a’a, so nake a zaunar da Saghir shima ta fadi laifin Diyam din sai a hada su kowa ayi masa fada a bashi laifin sa. A ja masa kunne akan dukanta dan ni abinda yafi komai daga min hankali kenan” sai Aunty Fatima ta nuna itama bata ji dadin abin ba tace “ni duk fa bansan wannan ba, ni cemin sukayi Diyam tana kula Sadauki shi kuma Saghir yaji haushi ya saketa. Kema yadda muke dake ai kamata yayi duk abinda ya faru ki kira ni ki gaya min. Da Diyam da Saghir duk yayana ne ai”. Amma ita kanwar Hajiya sai ta kama fada, ita wai lallai nayi wa Saghir sharri “babu wani shayeshaye da yake yi balle neman mata” sukayi ta bugawa da inna har tayi zuciya ta tashi ta tafi Aunty Fatima ma ta tafi sai Hajiya Yalwati ta zauna tace sai anjima zata taho. Daga jin haka nasan tsegumi ta zauna yi. Tace “wallahi Amina karki mayar da yarinyar nan. Yaron nan fa bawai gyaruwa yayi ba. To yaron da baiji kan iyayensa ba ina zaiji kan wani. Shaye shayen nan fa munsan yanayi amma sai a rufe ido ace bayayi. Neman matan nan kuwa yinsa yake yi kamar babu gobe. Ita kanta Fatima da take wannan maganar rannan a gaba na naji tanayiwa Minal yarta fadan kar ta kuma kula shi. Dama Suwaiba ce tasa kuma yanzu sunce sun bashi dan haka ku rabu dasu, in dai abinda Diyam ta fadi gaskiya ne in ya auri Suwaiban ai zasu gani” Inna tace “za kuwa su gani. Ai ni zanso ayi auren nan ma ko dan gaskiya ta bayyana” Hajiya Yalwati tace “gaskiya kam zata bayyana. Tun yanzu ba gashi nan muna gani yana zuwa yana daukan ta a mota ba? Ahau, lokaci kadai muke jira”. Har tana shirin tafiya kuma sai cewa tayi “ni Diyam kuma ta wani zubin banji dadin tahowar nan taki ba. Dama ke ce mai dan saka shi yana dan kawo mana abinci gidan. Yanzu kuwa shiru. Rannan har ya fara zancen aurar dasu murja yanzu kuwa yadda yake a rikicen nan nasan ba lallai ne yayi ba”. Inna ta dauki yan kudade ta bata tace ta siyawa yara sabulu. Da dare sai ga wayar Saghir. Na kalli wayar kawai na dauke kai. Yayi ta kira sai na saka a silent sai ya turo min message “ki shirya. Rana ita yau zan zo mu tafi”. Sai na kashe wayar gaba-daya na ajiye. Washegari wai dan rashin kunya sai ga Hajiya Babba da kanta. Ina ganin ta nayi wa Asma’u text. “Ki dauki Subay’a ku bar gidan nan, sai na kira ki zaku dawo”. Ina kallon su suka fice. Tazo ta saka inna a gaba “yanzu ya za’ayi ace kince ba zata koma gidan taba? Yanzu zumuncin kenan? Koma menene ya faru a tsakanin su shi ya hakura ita me yasa ba zata hakura ba?” Inna tace “tace ba zata koma ba. Ni kuma baxan matsa mata ba, matsantawar da nayi mata a wancan karon ma da ace zan iya dawo da hannun agogo baya da banyi ba”. Sai ta kama hannuna ta jani daki muka zauna a bakin gado tace “yanzu Diyam ke kinsan halin Saghir. Kinsan cewa ya chanja sosai saboda ke kuma ya chanja din. Yanzu da kika barshi Diyam Saghir duk ya koma yadda yake da koma fiye da haka. Me yasa ba zaki je ki karasa abinda kika fara ba? Ko dan saboda Subay’a” nace “Hajiya Saghir fa ba wai chanzawa yayi ba. Indai har da gaske ya chanza bai kamata ya koma ruwa ba dan bana tare da shi. Hakan yana nufin saboda ni ya chanza kenan ba wai saboda kansa ya chanza ba. To yanzu kuma in mutuwa nayi fa?” Tace “a hankali ai yake gyaruwar, in kin koma zai cigaba da gyaruwa ne” nace “Hajiya tun farko ba kwa ganin kamar akwai son zuciya da zalunci a cikin dora mim alhakin gyaran Saghir? Ku da kuka haife shi baku gyara shi ba tun yana danyensa ta yaya zaku bani shi bayan ya bushe kuma ku saka ran in kare rayuwata gurin gyaransa?” Tace “saboda munsan zaki iya. Kin fara kuma zaki iya karasawa” na girgiza kaina nace “bazan koma ba Hajiya” tace “saboda me?” Nace “saboda bana son shi Hajiya” sai ta tsaya tana kallona. Sai na tuno da ranar da Saghir yazo gaban inna yace baya son aure na. Hajiya tace “ba kya son sa fa kika ce min Diyam. Yanzu har idonki yayi budewar da zaki kalle ni kice ba kya son Saghir? Koma dai menene Saghir din nan, koma da gaske ne maganganun da kike fada still Saghir dai danuwan ki ne kuma duk kin da kike masa ba zaki taba cire jinin ki daga nasa ba. Mijinki ne kuma, tunda dai yace ya mayar dake Sannan uban yarki ne, ba zaki taba chanja mata uba ba” nace “Allah zai raya ta ko ba a gidan sa ba” sai ta mike da fushi ta fita, ina jinta tana cewa da Inna ina Subay’a zata tafi da ita, sai inna tace “Diyam tace Subay’a ba zata koma ba. Zata rike yarta” nan tayi ta bala’i “wallahi bata isa ba, ita tace ba zata koma ba sannan yar tasa ma ta hana shi? Da dare inna ta kuma saka Asma’u ta gwada number din Sadauki but still bata shiga. Inna ta kalleni tace “ke baki san inda yake zaune ba?” Na girgiza kai nace “ban sani ba Inna. Sai dai office dinsa na sani” Asma’u tace “ni dai nasan kamar a hotel yake zaune. Amma bansan wanne hotel din ba” Inna tace “to ko Asma’u zan tura office din nasa gobe ta gani? Ni duk zuciyata bata min dadi wallahi”. Washegari Asma’u tana dawowa daga school sai gashi ya kirata. Tace “Inna ga hamma yana kira” Inna tace “to kiyi sauri ki dauka mana kar ta katse kuma? Alhamdulillahi” Asma’u ta dauka tana gaishe shi sai naga ta kalleni tace “tana nan” sai kuma ta mike zata fita, Inna tace “ina kuma zaki je?” Sai Asma’u ta daga mata hannu ta fita kawai. Shiru shiru, ni dai ina zaune a kan kujera staring into nothingness har Asma’u ta dawo after like two hours. Ta zauna tace da Inna “yace ince miki yana lafiya kuma gobe zai shigo” Inna tace “shikenan? Duk wannan dadewar kuna waya shikenan abinda yace?” Asma’u tace “tambayoyi yayi ta yi min kawai. Akan Adda. Yanayin zamanta a gidan Saghir” Inna tace “ke kuma me kika ce masa?” Asma’u tace “everything. Duk abinda na sani na gaya masa sai dai kuma wanda ban sani ba. Abinda na fahimta shine duk shekarun nan shi ya dauka Adda lafiya take zaune a gidan mijinta” na dauke kai ina lissafin wanne ne abinda Asma’u ta sani wanne ne kuma wanda bata sani ba? Washegari da safe muna breakfast yazo. Fuskarsa babu annuri ko digo a cikinta ya gaishe da Inna muma muka gaishe shi. Ya kalli Subay’a yace da inna “an dauko tane?” Inna tace “tunda uban ya kawo ta Diyam tace ba zata koma ba” yace “good. Ba zata koma ba. Ita ma kuma Diyam din ba zata koma ba sai dai in har ita ce take son komawar” ya juyo ya kalle ni yace “kina son komawa gidan Saghir?” Na sunkuyar da kaina ina girgiza kaina da sauri, yace “good. Then ki dauki wayarki ki kira shi. Ki gaya masa ba kya sonsa ba zaki koma gidansa ba. In yana son rabuwa ta arziki to ya kawo miki takardar ki within the next three days, in kuma ba haka ba kice masa zaki kaishi kara in yaso alkali ya raba ku”.5 Ya juyo yana kallon Inna yace “Baffa uba ne a gurina. Dan yadda nake jinsa a zuciyata har yafi yadda nake jin shi kansa wanda ya haife ni saboda Baffa ya bani abinda shi din bai bani ba. Baffa ya bani soyayya, ya bani kulawa, ya bani tarbiyya. And he used his last breath a duniya to tell me in kula daku, and that’s what I have been trying to do, and that’s what I will continue to do sai inda karfi na ya kare”.Inna ta fara sharar hawaye, ita dama kwana biyun nan komai sai kaga ta fara hawaye. “Allah ya ji kan baffan ku. Babu abinda bai gaya min ba sai kace yasan abinda zai faru bayan babu shi. Abinda na wulakanta shine yanzu gatana ni da yayana, wadanda kuma na daukaka fiye da komai sune muka zama abin wulakanta wa a gurin su.” Sai Asma’u ta tashi ta koma kusa da ita tana rarrashinta, Sadauki ya mike tsaye yana kallona yace “ki kira shi yau. Gobe ki gaya min yadda kuka yi dashi”. Na gyada kaina sai ya juya ya fice.+ Ina kallonsu suka gama kukansu amma ni ko hawaye banji a idona ba, maybe ko kukan ya kare ne oho, nidai abu daya da na sani shine baxan koma gidan Saghir ba and that’s final. Sai yamma na samu courage din kiransa. Bugu daya ya dauka yace “ha! Finally. Kin shirya inzo mu tafi?” Na lumshe ido na na bude, ina bitar abinda Sadauki yace min nace “ba wannan dalilin da yasa na kira ka ba. Na kira ne in tabbatar maka da abinda na gayawa Hajiya sanda tazo. Aure na dakai ya kare Saghir. Ba zan koma gidan ka ba saboda rabuwa a tsakanin mu tafi alkhairi akan zaman. Ina neman ka sawwake min. Ka kawo ko kuma ka aiko min da takarda ta nan da kwana uku in kuma ba haka I will have no other choice than in kai karar ka alkali ya raba auren mu” ya yi shiru amma nasan bai ajiye ba, sai yace “are you threatening me Diyam?” Nace “ba threat bane ba, option ne na baka kamar yadda nima Allah ya bani option na ko in hakura in zauna da kai ko kuma in kai karar ka in baka kudin yin wani auren kai kuma ka sawake min” yace “ohh, abinda ya tsara miki kenan ko? Abinda yace ki gaya min kenan? To ki bude kunnen ki kiji sosai nima nawa sakon zuwa gurinsa. Kice masa nace bazan sake ki dinba, idan akwai abinda yafi court ya kai ni can. Amma kafin ku tafi court din bara in fara gaya muku abinda zai fari a can din. Muna zuwa zan zayyana wa alkalin cewa shi wanda ya taimaka miki kika kawo karar tawa tsohon manemin ki ne, na kama ku na hana ku harka shine kuka yi deciding kawo kara ta saboda in sakar masa ke. How about that?” Nace “kai kanka da kake fadar maganar kasan cewa ba gaskiya bane ba. Kuma duk inda alkali yake ai mutum ne mai ilimi wanda zai zai saurari kowa. Ni fa ƴa ce Saghir ba baiwa ba, tunda nace bana sonka set me free please” yace “in nayi haka Diyam ai na bashi abinda yake so kenan, na baku abinda kuke so. Ni kuma nayi alkawarin tunda kuka making fool of me for years sai na dauki fansa. Plus wulakancin da yasa police suka yi min. So here is another message to him. Tell him nace I want my job back, I am kind of out of money yanzu. In ba haka ba kuma zan fara spreading rumors a cikin ma’aikatan sa, and this time around I won’t be drunk yadda zanyi passing clear message har su fahimci wanene real Mr Abatcha, suma su fara boye matansu. Kuma harda gishiri zan kara wa maganar” ya karashe maganar yana dariya. Na cire wayar daga kunne na saboda yadda maganganun sa da dariyar sa suke kara huta ga already wutar da take ci a kirjina. Shin anya kuwa Saghir yana tsoron Allah? Shi karya bata yi masa wuya. Sanda ya dake ni a gida ya nuna yana zargina da Sadauki banji haushin sa ba kamar wanda naji akan maganganun da ya fada ranar nan akaina a gaban Sadauki, it shows cewa abinda yayi din ma bashi da remorse akan sa tunda har fada yake yi proudly a gaban third party. Yanzu kuma maganganun sa sun nuna min cewa ba wai ya mayar dani bane ba saboda yana son aurena ba, ya mayar dani ne to get back at Sadauki. Am not a toy, am a person with zuciya a kirjinta da kuma jini a jikinta. Am not going back. Da dare na gwada wayar Sadauki dan in gaya masa abinda Saghir yace amma naji har yanzu bata shiga. Haushi ya ishe ni na ajiye ta kawai. Amma sai na gayawa Inna duk abinda Saghir yace akan maganar Sadauki. Ta juya kai tace “wannan yaron baya kyautawa. Shi bai san hukuncin wanda yayi wa wani irin wannan sharrin ba? In kotun za’a je fa shine a kasa dan bashi da wata shaida” sai kuma tace “ni bana son zuwa kotun nan wallahi, zuciyata bata so, yan’uwan mu ne mutanen nan, so nake ayi sulhu a tsakani ba sai kowa yaji ba. Ba ga Suwaiba nan ba an bashi, kuma yana da wata matar a gida me yake nema kuma. In kudin yake so sai a bashi shima in dai za’a rabu lafiya. Ni kotun ce bana so, kuma bana so ya bata wa yaron nan suna a gurin mutanen da suke ganin girmansa”. STORY CONTINUES BELOW Nima kuma bana son court din, amma kuma bana son komawa gidan Saghir kuma bana son in watsawa Sadauki kasa a ido ince bazan je ba. Dan haka ranar sai naki bacci na kwana ina gayawa Allah. Kuma na tabbatar ya jini kuma na yarda da cewa zaiyi hukuncin da ya dace. Washegari da safe Asma’u ta tafi school ni kuma na koma na kwanta in danyi bacci sai naji karar wayata. Na dauka ina kallon number din Sadauki. Sai na jujjuya wayar a hannuna dan in tabbatar da cewa tawa ce bata Asma’u ba. Sai data kusa katsewa sannan na dauka da sallama na gaishe shi yace “ya kuka yi?” Sai da bashi labarin duk abinda Saghir ya fada. Sai kawai naji yayi dariya, yace “that man is so predictable. Ya fadi exactly abinda nake so ya fada. Tell him, na tsorata na tuba nace yayi hakuri kar ya zubar min da mutunci a gurin mutane, kice nace ya dawo ya cigaba da aikinsa ai dama ni ban kore shi ba shine ya daina zuwa. Sannan kice masa kema kin hakura ba kya son zuwa court dashi dan haka zaki koma gidan sa amma kina so please ya baki wata biyu saboda kina so ki shirya sosai” nayi saurin cewa “bazan koma ba” yace “I know. But just tell him that” nace “saboda me?” Yayi shiru sannan yace “do you trust me?” Nayi shiru nima ina lissafa lamarin sannan nace “yes, amma ina bukatar bayani” yace “okay, let me break it down for you. Bana son ke ko Inna ku shiga court dashi saboda kamar yadda Inna ta fada yan uwanku ne babu yadda zakuyi dasu. Sannan kuma ko an kaishi court din karshe kawai raba auren za’ayi and to get even that sai anyi ta faman cecekuce ana saka ki kina bayar da labari kina kara maimaita wa. I don’t want to put you through that emotional trauma. You have had enough of your share of emotions. Still kuma in nace zamuyi sueing dinsa for abinda ya fada a kunnena yayi, ba lallai ya samu wani sentence mai kyau ba saboda a lokacin da yayi din akwai aure a tsakanin ku dan haka iyayenki za’a jawo cikin case din for marrying you off that young. Bana son insa Inna cikin wannan maganar. So option dina shine ya zama tsakani na dashi ne kawai ku kuna gefe. And I promise you ba zaki koma ba but for that I need you to call him ki gaya masa abinda nace”. Nace “okay, zan gaya masa” yace “thank you. But please kar ki gayawa Inna. Let it be our little secret”. Ban gayawa Inna din ba kuma ban kira Saghir ba sai washegari. Ji nayi bana son kiran nasa dan haka sai na tura masa text message na fada masa abinda Sadauki yace in fada. Sai kuwa gashi nan ya kira ni na dauka da kyar, yace “it wasn’t so hard now was it? Dama nasan zamewa zaiyi ya barki. Ai mutane irin su babu abinda suke so irin su gyara public picture dinsu, ina komawa kuma zanyi requesting karin albashi kuma sai inga in zaiyi denying” yayi ta maganganun sa ni dai bance komai ba har ya gama sannan yace “and you? Mai zakiyi da wata biyu?” Nace “shiryawa nake so inyi sosai” yace “wacce irin shiryawa kuma? Ba kayanki kawai zaki zuba a akwati ba?” Nace “ina so in shirya emotionally, bayan abubuwan da ka fada ranar nan a gaban Sadauki ai you should be greatful da nace zan dawo din ma” sai na katse wayar kamar nayi fushi na kashe ta ma gaba daya. Daga nan komai ya lafa a bangaren mu. Two weeks after that Sadauki yazo yayi wa inna sallama yace zaiyi tafiya zuwa Canada. Yana shigowa Subay’a ta zagayo ta dawo bayan kujerar da nake zaune. Muka gaishe shi ya amsa sai ya mika mata hannu “Subis come here” sai ta makale. Yayi dariya yace “inna na kawo karar Subay’a, bata gaishe ni” Inna tace “ke! Ba zaki zo ki gaishe shi ba?” Still taki zuwa, zanyi mata fada yace in rabu da ita, yayi wa Inna bayani “dama family na na Maiduguri kusan duk suna Canada, zan danje in yi musu kwana biyu. In naje zan kira ku da number din da za ku same ni da ita should in case ko wani abun zai tashi” Sai Inna ta nuna irin bata ji dadin tafiyar tasa ba, Asma’u harda matsar kwalla yace “ko wata daya fa ba zanyi ba. Just hutawa nake so inyi saboda ina aiyuka da yawa a nan”. Yana fita Subay’a ta zagayo cinyata tace “Mommy bana son mutumin nan” Inna ta kwade ta da muhuci tace “kar in sake jin kince ba kya sonsa, kuma in na sake ganin yazo kin ki gaishe shi ni dake ne. Babanki ne shi, tunda yayan babarki ne”. Sai bayan tafiyar sa Inna ta tambayeni “wai ya kuke ciki ne maganar Saghir? Ni baki ce min komai ba” nace “na gaya masa abinda Sadauki yace in fada masa, shi kuma yace ba zai sake ni din ba sai dai aje court din. Shi kuma Sadauki yace vaya son muje court dasu” inna tace “nima bana so, to amma ai ba zaki yi ta zama da aure aka ba. Dole dai cikin biyu za’ayi daga. Bara ya dawo daga canadan muji”. Sati daya da tafiyar Sadauki muka je gidan Mama gabaki dayan mu. Anan ne muke samun labarin ashe rigima ake tayi a sharada tsakanin Alhaji Babba da kawu Isa. Kawu Isa yayi wa Saghir huce haushi na da suwaiba, har Saghir ya karba ya an fara shirye shirye sai kuma yaxo yace ya fasa ni zai mayar sai kawu Isa ya nuna cewa ba’a kyautawa yarinyar ba, amma as usual, Alhaji Babba ya goyi bayan dansa. Mama tace “ni tsoro nake ma Allah yasa bai lalata musu yarinya ba, dan labaran da muke ji basu da dadi”. Bayan dawowar mune nayi bakuwa. Fauziyya. Ni ban san ma tasan gidan mu ba sai yau. Na karbe ta sosai muka shiga daki nayi serving dinta abinci da drinks. Sannan tace “muna ta jira kuma har yanzu shiru” nayi dariya kawai, sai tace “ko sai za’a koma sabon gida sannan zaki dawo?” Nace “sabon gida kuma?” Tace “eh mana, ko bai gaya miki ba ya siya mana sabon gida? Sai ta fara yi min bayanin girma da kyan gidan “kowa da part dinshi, part din kowa yayi girman gidan da muke ciki. Yayi order komai na gidan next week za’a kawo su” sai ta nuna min key din mota “kinga ya siya min mota, kema ina jin kina komawa za’a siya miki taki. Shima ya sake wata” na gyara zama ina nazarin ta nace “why are you here Fauziyya?” Tace “ziyara na kawo miki mana. Kuma in gaya miki alkhairin da ya samu mijin mu dan in kwadaita miki komawa gidan. Hausawa sunce the devil you know is better than the angel you don’t know. Na zauna dake lafiya, gwara ko dawo akan a kawo min wata wadda ban sani ba”. Bayan tafiyar ta na zauna tunani. Kudi? Lokaci daya? Saghir? Ina ya samu kudi? And I remembered lokacin daya samu aiki yazo yake bani labari yace “financial secretary aka ce miki. Ni nake kula da duk harkokin shige da ficen kudi a companyn”.Sai naji tunani na ya tsaya. I just want to make a sense of wannan abin but na kasa believing abinda nake thinking. Is Saghir helping himself out of Sadauki’s money? Ko kuma yana blackmailing Sadauki ne akan wannan maganar? But anya Sadauki zaiyi paying Saghir irin wannan kudin saboda empty threats dinsa? Tun sanda yayi threat din ni ban ji ko alamar tsoro a voice din Sadauki ba. Menene ma kuma dalilin da yasa Sadauki ya mayar wa da Saghir aikinsa? In dai kuwa har Saghir kudin Sadauki yake dauka then he is dumber than I thought.5 Koma dai menene ni abinda na sani shine ya kamata inyi warning Sadauki akan ya kula da kudinsa tun kafin Saghir ya debi wanda zai kassara Sadauki ko kuma shi wanda ba zai iya biya ba. Kamar yadda na tabbatar zan mutu haka na tabbatar Sadauki ba zai bar masa ba.2 Wayar Asma’u na nemo na dauki number din da naga Sadauki ya kira ta rannan na saka a tawa wayar nayi dialing amma sai taki shiga, naji kamar in jefar da wayar saboda bakin ciki, wato a wannan number din ma sai da yayi blocking dina? Wai me yake tunanin kansa ne? Ni ma na damu, sai sune suyi tayi ai daga shi har Saghir din. Washegari Saghir yazo gidan. Ya ci kwalliya fiye da yadda yake da sai sheki yake yi kamar tarwada. Sai naga rashin kunyarsa da har zai iya shigowa palon Inna bayan duk abinda yayi mata da kuma sakinna da yayi a gabanta. Subay’a ta tafi da gudu ta rungume shi ya daga ta sama yana juya ta kamar yadda yake yi mata sanda muna gidansa. Asma’u tayi tsaki ta fita. Sai ya dan rissina ya gaida Inna ta amsa masa ba yabo ba fallasa. Sai ta dauki mayafinta tace min zata je unguwa. Ya zauna yana kallona yace “babu gaisuwa gimbiya” na kalle shi nace “yaushe babana ya zama sarki ballantana ni in zama gimbiya?” Yace “ai ba gimbiyar gari bace ba, gimbiya tace ni kadai. Kinsan cewa an bani kyautar budurwa naki karba saboda ke? Ke kinsan wanne irin so nake miki kuwa Diyam?” Nayi shiru ina tunanin irin maganganun daya fada a nan palon a gaban Sadauki, is that his version of love?+ Yace “wata biyun nan yayi min yawa please. Ki rage. Ko kuma ince na rage miki da kaina. Na sayi sabon gida, you are going to like it. Zanyi tafiya zanyi two weeks kafin nan komai na gidan ya kammala ina dawowa zamu tare. So, I want you to get ready kafin nan kafin lokacin dan har dake din zamu tare a lokaci daya. Kinga da kin koma ma da dake zamuyi tafiyar nan. Am taking Fauziyya to the honeymoon I promised her, but in kin koma kema sai muyi fixing time ki zabi kasar da kike so mu tafi” na gyada masa kai kawai a raina ina jin haushin Sadauki da yace ince da Saghir zan koma. I don’t like this idea at all. Ya fara duba kayan jikin Subay’a “wannan kayan duk sun tsufa a zubar dasu Diyam. Ga kaya nan na taho mata dasu suna mota sai ta cigaba da amfani dasu” sai ya dora ta akan cinyarta tana ta zuba masa surutu yana dariya, ina jinsu ya fada mata zaiyi tafiya ita kuma ta fara lissafo masa kayan da zai siyo mata. Sannan tace “Daddy dan Allah ka dawo da wuri mu koma gidan mu ni nafi son zama tarr da kai da Mommy” yayi pecking dinta a cheeks yace “ina dawowa zamu koma kinji princess? It is going to be sabuwar rayuwa for us”.2 Sai naji a raina cewa tunda har yanzu ni matarsa ce then it is my responsibility inji source din kudinsa. Sai nace “kudi ka samu ne masu yawa haka? A ina?” Sai ya watso min wani mugun kallo yace “matse ni sai in gaya miki, kinsan dai tunda kika sanni da arziki na kika san ni ko? Ko kin taba gani na ina gyaran matattun motoci? Wanda ya samu dukiya sama ta ka shi ake yiwa tambayar inda ya samu dan zata iya yiwuwa yankan kai ko fashi da makami yake yi”.3 Sai da yasa na raka shi har bakin kofa, ya fito da kayan Subay’a jaka guda ya mika min sannan yace “I will be seeing you soon, sweet pie”.21 Washegari jirginsu ya daga shi da Fauziyya, I didn’t even know ina suka tafi sai ya suka sauka ya kira ni yace min sun sauka a Miami, yace in ajiye number din saboda zai ke kira na da ita. Bayan tafiyar Saghir ne Asma’u ta kammala jarabawarta, tayi candy, sannan kuma hakan yazo dai dai dayin saukar Alqur’anin ta. Wannan yasa ta shirya walima a nan gidan mu ita da kawayenta. Inna ta aika wa duk yan’uwa aka gayyato su kuma ga mamakin mu sai gasu sunzo, sai dai abinda muka lura dashi shine babu jituwa tsakanin iyalin Alhaji Babba da kawu Isa. Aka gabatar musu da abinci iri iri wanda su kansu sai da sukayi mamaki, daga abincin da aka ci har zuwa sutturar da muka saka daga mu har Inna duk sun nuna cewa ba a cikin kunci muke ba. Su Murja sai tambayata suke yi “yaushe zaki koma gidan hamma?” Murja ta jani gefe “dan Allah Diyam in baki koma bama kiyi masa magana ko zaiji maganar ki. Kinga maganar auren nan fa ta tsaya duk uban kudin da yake samu kwanan nan amma yace ba zaiyi ba. Shi kuma kawu isa da muke tunanin tura masa samarin mu shi kuma gashi yanzu ko magana basa yi da Alhaji” nace “wai me ya hadasu ne?” Ta rufe baki tace “ba za’aji a baki na ba”. STORY CONTINUES BELOW Kwana biyu da yin walimar Asma’u sai ga Kawu Isa a gidan mu. Mamaki ya ishe ni na tuna ranar da yace sun cire mu a cikin zuri’a ranar da sagjir ya sake ni a gabansu amma yanzu gashi few months after ya dawo da kafafuwansa. Muka gaishe shi ni da Asma’u muka fita muka basu guri da inna. Sun jima suna maganganu kafin muji ya fita sannan muka dawo dakin. Asma’u ta saka Inna a gaba da tambaya “me yace? Me ya faru” Inna tace “ina ruwanki? Suda mai bakin magana” Sai da Asma’u ta tafi islamiyya sannan inna ta bani labari. “Zuwa yayi yace min wai dan Allah duk yadda za’ayi kar mu mayar dake gidan Saghir. Ashe abinda Yalwati take fada min rannan gaskiya ne, Suwaiba dai har da cikin Saghir a jikinta. Alhaji Babba yace shi lallai sharri aka yiwa dansa, shi ma kuma Saghir din yace ba nashi vane ba kuma yama fasa aurenta ke zai mayar. Shine shi kuma hamma Isa yazo yace kar mu mayar masa da ke in yaso yayi biyu babu kenan. Su yanzu likitan da zai cire cikin suke nema”. Nayi shiru ina jin hawaye yana bin fuskata. Na tuno zafin da naji sanda Saghir yayi min sharri a gaban yan’uwan mahaifina amma duk babu wanda yayi komai a kai. Ga zina nan ta kare a gabansu, yanzu sai su ware ni da Saghir waye mazinaci. Bayan sati ya kuma zagayowa sai ga malam iliya maigadin gidan Saghir ya kirani hankali a tashe. Na tambayeshi sai yace “yan NDLE ne suka zo gidan, sun yi filla filla da komai na gidan wai suna neman kayan maye” cikin tashin hankali na tambayeshi sun samu sai yace “sun samu, a dakin mai gidan sukayi ta fitowa dasu sannan suka samu wasu kuma a motarsa. Yanzu tafiyarsu kenan nima guduwa nayi da ina jin dani zasu hada. Shine na kira ki tunda su basa nan in gaya miki halin da ake ciki” nayi masa godiya na kashe wayar, ina kokarin bawa inna labari sai ga kira ya shigo wayarta daga Hajiya Yalwati tana ta kuka “Amina mun shiga uku. Wai yan drugs ne suka zo zasu tafi da Alhaji. Alhaji Babba fa? Me ya hada shi da shaye shaye?”. Nan take Inna ta rikirkice ta saka mu muka shirya muka tafi gidan gaba daya, muna zuwa muka tarar har an tafi dashi ga yan gidan nan sun fito sunyi chirko cirko masu kuka nayi masu salati nayi, yan unguwa kuma ana tsaye ana kallo. Mukayi ta basu baki muna mayar dasu cikin gida har muka samu suka koma ciki sannan aka fara tunanin ta inda za’a bullowa lamarin. Ni dai na fada musu abinda mai gadin gidan Saghir ya fada, dan haka sai muka fahimci cewa neman Saghir suke yi shi yasa suka kama Alhaji. Aka kira Kawu Isa aka gaya masa amma yace shi babu ruwansa “tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka”. Dan abin kunya sai surukan gidan aka nema, ciki harda wanda yake neman auren Murja, su sukayi ta zirga zirga Inna kuma ta saka Asma’u taje ta ciro kudi a account a bawa wancan cin hanci a bawa wancan amma sai da Alhaji Babba ya kwana biyu a garkame sannan suka sake shi da yarjejeniyar Saghir yana shigowa kasar zai danka musu shi a hannun su. Ranar da Alhaji ya dawo gida haka ya zauna yana ta kuka kamar karamin yaro “ban taba ganin cin mutumci irin wannan ba, wannan yaro mai ya janyo min haka ni Muhammadu. Ankwa hannu da kafa haka aka saka min ana jana a titi kamar wanda yayi kisan kai” sai kuma ya fara yiwa Inna godiya a kan kokarin ta da karfin ta da kudinta gurin ganin an fito dashi. Yana ta kuka har ciwonsa yana kokarin tashi dan haka akayi masa allurar bacci mu kuma muka tafi gida.5 What remains a mystery shine yadda akayi yan drugs suka yi suspecting Saghir yana ta’ammali da kayan maye har suka kaiwa gidansa ziyara. Two weeks after tafiyar Saghir sadauki ya dawo. A gurin Asma’u naji zancen dawowar tasa sai kuwa gashi nan yazo gidan. Ina jin shigowarsa na shige cikin daki na lulluba kamar mai bacci. Ina jin su suna ta hirar su a palo, ya kawowa Asma’u graduation gift na wata desighner handbag da takalmi, ya kawo wa Subay’a yar karamar computer ta yara mai kyau. Ta shigo da murna tana nuna min “Mommy kinga abinda wannan yayan naki ya kawo min, amma ke yace bai siyo miki komai ba” na karba ina dubawa nace “to kije kice kin gode madallah” ta fita na koma na kwanta. Ina ta so dai inyi masa maganar kudin companyn sa, amma bana son ganinsa dan haka bayan ya bar gidan sai na kara dauko waya ta ban kirashi ba dan nasan ba shiga zata yi ba amma sai na rubuta masa message. “Ka sa ido a kudaden kamfanin ka. I might be wrong. Just taking precautions”. Na tura masa. Na zauna da wayar a hannu ina jiran reply, shiru shiru babu. Har na gaji na ajiye ta na tashi na cigaba da harkoki na. Aka jima na sake dubawa babu reply, nayi tsaki a raina nace “ku kuka sani” Sai kuma nake jin haushin kaina for caring a inda ni ba’a damu dani ba.6 Saghir yakan kira ni sometimes, in ya kira sai in bawa Subay’a suyi magana. Ko da wasa ban bashi labarin case din drugs ba dan nasan ba karamin aikinsa bane ba yaki dawowa dan ba damuwa yayi da abinda za’ayiwa Alhaji in bai dawo din ba. Ranar nan ya kira na bawa Subay’a suka gama maganganun su sai yace ta bani, na karba yace min “jibi zamu dawo. Ina son ki kawo Subay’a airport ta tare mu. Tace tana son zuwa” nace “okay Allah ya kaimu jibin. Allah ya kawo ku lfy” yace “ameen. Hope kin gama shiryawa dan daga airport sabon gidazamu zarce” na sake cewa “Allah ya kaimu” na kashe. I didn’t have the energy or the patient to argue. Muna gama wayar sai naga Asma’u ta dauki tata wayar tayi kira sannan tace “jibi zai dawo” ta kashe. Ta kalleta nace “what was that?” Tace “Hamma yace in gaya masa ranar da Saghir zai dawo” na saki baki kawai ina kallonta. What was that about? Ranar dawowarsu na shirya Subay’a tana ta murna muka tafi malam Aminu Kano international airport. Muka tsaya a gurin da aka tanada dan taryar matafiya. Subay’a tana ta tsalle ta kasa tsayawa a guri daya yayin da ni kuma nake ta lissafe lissafen halin da nake ciki. Ni har yanzu ban gama fahimtar kudurin Sadauki na mayar da Saghir aiki sannan da kuma hanani gaya masa cewa ni ba zan koma gidansa ba. Na fahimci kamar yana buying time ne but for what? Me yasa kuma yake son jin lokacin dawowar Saghir?2 Muna tsaye akayi announcing saukar jirgin su Saghir, muna tsaye kuma har suka gama checking out suka fito. Na hango shi, as handsome as ever, hannunsa cikin na Fauziyya suna fitowa daga revolving door din gurin. Subay’a ta fara murna “Daddy, Daddy” ya dago mata hannu yana murmushi. And then as he steps his feet out of the door, police surrounded him. Police, not NDLE officers. Fauziyya ta matsa baya da sauri tana ihu, Subay’a ma ta fara ihun kiran Daddy yayinda shi kuma ya fara demanding dalilin kamashi. Na daga Subay’a na rungume ta a kirjina, muna kallo daga inda muke tsaye aka garkamawa Saghir ankwa a hannayensa aka wuce dashi police car da take gefe tana jira.3 Subay’a ta fara jera min tambayoyi “me yasa yan sanda suka tafi da Daddy na? Ina zasu kai shi?” A lokacin naji karar shigowar text cikin wayata. Na dauko ta na duba naga number din Sadauki. Sai yanzu yayi replying message dina. Na karanta “check up” it said. “Check up” na maimaita a fili. Nasan wannan kalmar amma a ina? Sai mind dina ta koma baya, back in time lokacin muna yara a gida muna playing game of cards ni da Sadauki a incomplete benen Baffa a lokacin da nake gudun islamiyya ya rama min duka ance in na koma sai an zane ni. A cikin game din ana cewa check up. And it means game over. Amma wanne game din ne over bayan ni bansan sanda game din ya fara ba? Ya akayi ya turo min wannan text din a dai dai wannan lokacin? Ko dai Sadauki yana da hannu ne gurin kama Saghir? Kamar ance min in juya baya sai na juya. And I saw him. Yana tsaye ya jingina da jikin motarsa with dark glasses a idonsa and a broad smile on his face yana kallon motar police din da aka saka Saghir a ciki, sai da yaga sun ja sun tafi sannan ya bude motarsa shima ya shiga shima ya tafi. Da sauri na koma taxi din da nayo shutter nace masa mubi bayan police car din data fita. A hanya drivern yake ta surutai “ai haka police suke yiwa irin wadannan bata garin, in sunyi abu sai su gudu su bar kasar sai a shammace su ranar da zasu dawo azo ayi gaba dasu. Ai wannan commissioner din baya wasa” jin ban kula shiba sai yayi shiru kuma muka cigaba da bin su a baya har na tabbatar cewa bompai zasu tafi dashi sannan nace da drivern ya kaini badawa layout, gidan Mama, muna zuwa na ajiye Subay’a na gayawa Mama briefly abinda ya faru, naci sa’a yaya Sadiq yana gida sai ta hadani dashi muka koma police station din dan muji takamaiman abinda ya faru, for what charges aka kama Saghir.+ But ni already jiki na ya gama bani charges din ina dai so ne in tabbatar da zargi na. Ina kuma bukatar wasu amsoshin daga Saghir. Da kyar muka samu desk officer din ya kula mu, amma da muka nemi ganin Saghir Muhammad da aka shigo dashi yanzu sai kawai yayi mana dariya irin mun ma bashi dariya din nan, yace “wannan ai ko uwarsa ce take son ganinsa sai dai ta hakura. Ku koma gida kuyi taja masa charbi dan yau ne za’ayi masa tambayar kabari ta duniya” ya fada yana dariyar mugunta. Nace “to zamu iya sanin dalilin da yasa aka kama shi?” Yace “ke wacece a gurinsa?” Nace “matarsa” yace “kinsan inda yake aiki?” Na hadiye wani abu a kirjina Nace “eh. Abatcha Motors” yace “to can zaki je ki tambayi abinda yayi, zasu yi miki bayani dalla dalla”. Haka muka hakura muka fito. Yaya Sadiq yana jan motar mama ni kuma ina gaba nayi shiru ina juta lamarin a raina. My deepest fear have come true, wannan case din bana drugs bane ba kuma wani ne daban, case din Sadauki ne, Saghir ya debi kudin companyn Sadauki yayi facaka dasu Sadauki kuma ya saka an kama shi. But what was Saghir thinking? Gidan Alhaji Babba nace Yaya Sadiq ya kaini, dole inje in fada musu halin da dansu yake ciki in yaso a hadu a san yadda za’ayi tackling lamarin. Ga kuma wancan case din NDLEA da yake jiran Saghir. Sai kawai naji ina jin tausayin iyaye da yan uwan Saghir.1 I also needed to talk with Sadauki. Bana ko raba daya da biyu nasan tarko ne Sadauki ya dana wa Saghir shi kuma ya fada head over heels. Wato wannan shine time din daya nema in yi masa buying kenan. Sai kuma na sake tambayar kaina “menene hadin Sadauki da case din NDLEA? I really do hope bashi da hannu a ciki.11 Da muka je gidan kuma sai na kasa gaya musu, musamman ganin da nayi suna ta fama da kansu, an dafa wake da shinkafa ana ta lissafin yadda za’a samu kudin mai, sai da naje na bayar aka siyo musu. Sai na ja Hajiya Yalwati gefe na labarta mata. Ta rike baki tana salati tace “gurin aikin sa kuma? Ba companyn Sadauki bane yake aikin ji nake ya kore shi?” Nace “bai kore shi ba, ga kuma abinda ya faru. Yanzu yana bompai. Naje an ma hanani ganinsa” haka na tafi na barta da jimami nace ta gayawa Alhaji da Hajiya. Ni ba zan iya ganin wannan heart break din ba. Daga nan gida yaya Sadiq ya kaini, na bar Subay’a gidan Mama in yaso gobe in na koma station din sai in biya in taho da ita saboda nasan yanzu in muka he gida ta saka ni a gaba kenan da tambayar ina daddyn ta? Ina police suka kai shi?. Ina shiga gidan Inna tana sallamar wani yaro da yazo siyan kankara ta gane something is wrong, sai data sallame shi tace min “lafiya? Ina Subay’a? Rigima kuka sake yi da Saghir?” na zauna ina cire hijab dina nace “inna Saghir yana bompai” ta saka salati tana tafa hannu tace “masu neman nasa ne suka kama shi? Dama sun san yau zai dawo?” Nace “basu bane ba Inna. Wani case din ne daban, basu gaya min menene ba amma sunce case ne daga gurin aikinsa” na fada ina kallonta cikin ido, nan da nan sai naga ta fahimta tace “Sadauki? Me ya kuma hada su kuma?” Na daga kafada nace “ban sani ba. Sai gobe zan sake komawa inji ko zasu yi min bayani” tace “to ki kira Sadaukin mana ki tambayeshi shi?” Na kwanta a kujera ina cewa “ba zai dauka ba Inna. Dama can baya daukar waya ta ballantana yanzu”. STORY CONTINUES BELOW Na jima kwance da idanuna a rufe har aka fara kiran magrib. Ni dai va bacci nake ba kawai ina ta lissafe lissafe ne, Sadauki should have just let me take Saghir to court shikenan a wuce gurin. In na rabu dashi ba dai shikenan ba? Ina ji da dare Inna ta saka Asma’u tana ta bugawa Sadauki waya amma yaki dauka, daga baya ma sai ya kashe wayar gabaki daya. A raina nace dai dai kenan. Washegari tun da wuri na tashi na shirya inna ma ta shirya tace gwara muje tare, muka bar Asma’u a gida muka tafi bompai amma muna zuwa muka tarar Hajiya Babba ta riga mu zuwa ita da wani kaninta. Idanunta sun kumbura alamar tayi kuka harta gode wa Allah. Muna shiga ta taho gurina da sauri “Diyam sharri yake masa wallahi, wallahi sharri yake yi masa ina yaron nan zai kai wadannan uban kudade?” Inna ta rike ta tana lallashinta ni kuma na karasa gurin desk officer din da yake on duty. Ya miko min wata takarda wacce take dauke da case statement na case din Saghir, a jiki naga bayanin cewa ya yi transfer din kudi ne daga account din company zuwa private account dinsa. Amount din dana gani sai daya saka kaina ya sara naji kamar zan fadi, mai Saghir yake tunani ne wai? A jiki kuma naga cewa Saghir din ya karbi laifinsa tun a jiyan da aka kawo shi dan haka har an fara shirin tura shi court. Na ajiye takardar nace da officer din “can I see him please” ya kalle ni da mamaki yace “are you sure? He went through some questioning so an dan sassama shi kadan” ya karasa yana grinning. Na juya na kalli inda Hajiya har yanzu take zaune tana kuka Inna tana rarrashinta. Nace “zan ganshi, amma ni kadai” sai ya miko min wani form yace in cike. Na karba na tafi gurin su Hajiya nace musu “sun hana ganinsa, gwara ku tafi gida kawai. Ni zan zauna in cike wasu takardu yanzu zan biyo ku” kamar ba zasu tafi ba sai kanin Hajiya wanda dama tunda muka zo naga yana ta nuna alamar ya gaji yace “in mun zauna ma babu abinda zasuyi mana fa, zasu iya wulakanta mu gwara mu koma gida sai asan yadda za’a bullowa lamarin” sai naci sa’a suka bishi suka tafi ni kuma na koma ciki na cike form din da aka bani, aka kaini wani daki na zauna ina jira, shiru shiru tun ina kallon agogo gar na fara zama frustrated ina jin tamkar na shekara a dakin sai aka bude kofa aka shigo. Saghir ne, amma kamar ba Saghir ba. Daga shi sai singlet da gajeren wando, fuskarsa babu inda bai kumbura ba dan idanuwansa da kyar suke budewa. Sai kawai naji zuciyata ta karye na rufe baki na kama kuka. Officer din daya shigo dashi yace “na gaya miki ai” sai ya zaunar da Saghir akan benchi ya juya ya fita. Na tsaya kawai muna kallon kallo. Sai can yace cikin wata irin murya “kinzo ne dan ki sakani a gaba kiyi ta kallo kina cewa Allah ya kara ko kuma kinzo ki karasa aikin da tsohon saurayinki ya fara?” Na zauna ina facing dinsa nace “Saghir me yasa ka daukar masa kudi? Why? In zaka dauki kudin kowa a duniya me yasa zaka taba na Sadauki bayan kasan abinda yake tsakanin ku?” Yace “menene a tsakanin mu din? Ke? Dan ke akayi min wannan abin na sani kuma yayi da dan halak. Sai na rama duk ranar da na bar gurin nan sai na chanja masa kamanni kamar yadda yasa aka chanja min nawa” na girgiza kai cike da takaici, he is still being arrogant, nace “ni so nake in tabbatar, ka daukar masa kudi ko ba ka daukar masa ba? Ina so insan gaskiyar maganar nan saboda in san ta inda zan bullo mata” ya dauke kai yace “I don’t need your help. Kiyi tafiyar ki kawai. Ki je ki gaya masa cewa tarkon daya kafa ya kama shaho” na girgiza kaina a raina nace ‘he have no idea how much trouble yake ciki’ sai na bashi labarin case dinsa da yan drugs. And that broke him down. Hannu biyu yasa ya dafe kansa, ya jima a haka sannan ya dago yana kallona yace “wannan duk yana cikin irin kiyayyar da kike yi min Diyam? Me yasa baki fada min ba kika barni na dawo kasar? Me yasa kika barni na fada tarkon da makiyana suka kafa min” naji tausayinsa har cikin raina, nace “Saghir, ko daya ba naki gaya maka ne saboda bana sonka ba, naki gaya maka ne saboda nasan in na gaya maka ba zaka dawo ba and that means trouble for Alhaji, wanda babanka ne shi mahaifi dan haka dawowarka yafi maka alkhairi akan kin dawowarka” yace “really? To case din Sadauki fa? Shima kamanin da yayi yafi min alkhairi akan rashin kamani? Waye ya gaya masa zan dawo da har yasa aka tare ni a airport?” Nace “duk abinda zan gaya maka ba lallai ka yarda ba. Amma duk da haka zan gaya maka. Bani da idea akan abinda ya faru tsakanin ka da Sadauki. Na san dai yana buying time for something but bansan menene ba. Kuma ina so kasan cewa zanyi iya kacin kokari na na ganin ka fita daga gurin nan but for that ina bukatar ka gaya min gaskiya. Ka dauki kudin Sadauki ko baka dauka ba? Drugs din da aka samu a dakin ka da motar ka, naka ne ko ba naka ne ba?”1 STORY CONTINUES BELOW Ya jima shiru kamar ba zaiyi magana ba sannan kuma sai ya danyi murmushi yace “that former boyfriend of yours is smart, na bashi credit anan. Tunda yaron nan ya dauke ni aiki, ina jin ma ai na taba gaya miki, babu aikin da nake yi. Sai ya dauki wani a matsayin assistant dina to duk aikin da ya taso shi ake bawa yake yi and I tot ‘huta roro’ tunda dai ana bani salary na mai kyau ai bani da problem. Shekara da shekaru, ko banje gurin aiki ba bani da matsala, I should have known tun a lokacin that something is off but ni ta constant monthly income dina nake yi. And then lokacin da na koma aiki, suddenly it was all work for me. A lokacin ne nasan ma how much money ne a cikin account din Company and it was a huge money. Kullum kudi suna shigowa wadansu suna fita, kudi masu yawa. Shi yayi tafiyar sa, and duk takardar da aka kawo zaiyi signing sai a kawo min ace yace inyi a maimakon sa. Duk kudin da za’a fitar ni za’a saka in fitar dasu haka duk kudin da za’a shigar. It was like cewa ake yi Saghir dauki kudin nan. And I saw my chance. Mutumin nan yaci amana ta yayi making fool of me for years, dan haka dole ce ta saka ni na cigaba da aiki under him saboda babu inda zanje in samu din. Dan haka sai na dauka as a revenge for what he did to me kuma dan in kafa kaina nima in daina aiki under him. Nasan zai gani amma kuma nasan yana tsoron kar in bata masa image dinsa with that scandal so I expected him to keep quiet. Da kudin na sayi gidan dana gaya miki na kuma saya mana motoci ni da ke da Fauziyya and I gave some part of the money to Kabir da niyyar zamu hada share muyi business tare. Sauran kuma dasu nayi wannan tafiyar wadansu kuma suna account dina da niyyar su zasu rike mu kafin business din da zan fara ya kankama”. A gyada kai, my mind already thinking ta yadda za’a harhado kan wadannan kudade. Ya cigaba: “Drugs kuma, wadanda aka samu a daki na, a kasan gadona, ba nawa bane ba. You know I don’t do drugs. Na Kabir ne ya bani ajjiya saboda yana da iyali karsu taba masa ni kuma tunda zanyi tafiya shine yace in ajiye masa, a mota ta kuma alcohol zasu samu”. Na gyada kai nace “so, where is Kabir now?” Ya daga kafada yace “ta yaya zan sani tunda ina nan a rufe?” Nace “but ta yaya akayi suka kai mamaye gidan ka?” Yace “I have no idea. Ask that smart boyfriend of yours maybe shi yana da idea”. Na mike tsaye nace “thanks for telling me the truth. Zan je gidan Alhaji zamu zauna muga ta yadda za’a bullowa lamarin. Insha Allah, you are getting out of here. Zamuyi reporting cewa stuffs din Kabir ne ba naka ba.” Na juya zan fita sai yace “why?” Na juyo ina kallonsa nace “why?” Yace “why are you trying to help me bayan duk abinda nayi miki? I tot ke celebrating zakiyi ma cewa you are finally getting rid of me” nace “kamar yadda Hajiya ta gaya min rannan. Kai dan’uwa na ne, mijina, kuma uban yata”. Daga bompai gidan Alhaji Babba na koma, a can na same su harda inna duk sunyi jigum jigum har aunty Fatima itama tazo. Na zauna na lissafa musu tas abinda ya faru. Saghir dai ya dauki kudi ba sharri ne akayi masa ba, ya kuma admitting to ajiye drugs a gidan sa amma yace ba nasa bane ba na Kabir abokin sa ne. Nan take Alhaji Babba ya dauko waya ya kira Alhaji Murtala mahaifin Kabir yana tambayarsa in yasan inda Kabir din yake amma sai yace shima nemansa yake yi bai san inda yake ba, ya dauka ma tare suka fita da Saghir, da yake duk halin daya ne. Nan fa hankalin Alhaji ya sake tashi. In ba’a samu Kabir ba Saghir ne a ruwa. Out of the confusion na fita waje na zauna a compound. Sai na dauko wayata nakira Fauziyya. Tunda na ganta a airport sanda aka kama Saghir ban kuma waiwatarta ba kuma babu wanda ya kuma kiranta. Bugu biyu ta dauka. “Halima ya ake ciki?” Naji haushin da bata kirani taji ya ake ciki ba sai yanzu? Amma sai nayi mata bayanin duk abinda na fahimta da kuma halin da ake ciki a yanzu. Sai ta tabbatar min da cewa tabbas taga sanda ya ajiye drugs din a day to tafiyarsu yace ajjiya aka bashi but bata san menene ba a lokacin kuma bata san waye ya bashi ajjiyar ba. Sai na ce mata ta shirya ta taho gidan Alhaji itama ayi komai da ita. STORY CONTINUES BELOW Sai can yamma ta zo, tana ta dari dari dan duk yan gidan ba sonta suke yi ba kar ma Hajiya taji labari, tace tsohuwar karuwa ce. Ita ta sake tabbatar musu da cewa Saghir shi ya ajiye drugs din da hannunsa, ta kuma gaya musu zancen gidan daya siya wanda su sam sam basu san da zancensa ba. Tace gidan yana unguwar rijiyar zaki dan haka muka yi shirin gobe zamuje a ga gidan sai kuma a nemi mai siya. Za’a karbi motarta da tasa a hada da wadda yace ya saya da sunana duk a siyar, sai a hada kudin da sauran kudin da yake account dinsa aga abinda za’a tayar kafin a nemi inda Kabir yake a dankashi a hannun NDLEA a kuma karbi kudin Saghir na hannunsa. Sauran kudaden kuma da Saghir ya riga ya kashe bansan inda za’a same su ba. Da Fauziyya zata tafi tace min “Mr Abatcha, ai yana jin maganar ki ko? Zaki iya sakawa ya saki Saghir ko?” And I didn’t answer her. Muna komawa gida na kira shi da wayar Asma’u tunda ba zai dauki tawa ba amma still sai yaki dauka, I guess yayi tunanin Inna ce take nemansa da gaske. Amma ita inna tunda taji zancen cewa Saghir ya dauki kudin Sadauki da gaske sai tayi shiru bata kuma cewa komai ba. But like I told Saghir, zanyi iyakacin kokari na gurin fito dashi so I decided to see Sadauki the next morning. Da safe muka sake komawa gidan Alhaji Babba, Fauziyya ma tazo za’a tafi sabon gidan Saghir sai nace musu suje kawai, na gaya musu inda zanje. Abatcha Motors. Na tarar da gurin kamar wancan zuwan nawa ana ta hada hada, sai dai yau kamar gurin yafi cika kuma motocin gurin sunfi nada yawa har bazan iya kirgasu ba, na samu receptionist din nace masa “ina son ganin ogan ku” sai ya tsaya yana kallona yadda na hade rai ya dauki waya yayi magana a ciki sai kuma ya kalle ni yace “ya ga shigowar ki ta CCTV. Yace kije office dinsa. In kika bi nan….” Na daga masa hannu nace “nasan inda office dinsa yake thank you” sai kuma na tafi inajin haushin kaina for being rude ga wanda bashi yayi min laifi ba. Na ga wannan kyakykyawar secretary din nasa, ta yi min sannu da zuwa sannan tazo ta bude min kofa kamar ranar nan na shiga but sai na bar kofar a bude na tsaya ina kallonsa a zaune yana kallona shima. Nace “let him go” sai ya taso ba tare daya ce min komai ba yawuce ni majestically ya rufe kofar dana bari a bude. Ya juyo ya samu kujera ya zauna yace “he took, or rather stole my money” nace “kudi, kudi, kudi dai? Shikenan abinda yake da muhimmanci a gurin ka kudi? Look at what you have, lokacin da naga amount din kudin da Saghir ya dauka I tot ya kassara ka but ni banga alamar anyiwa companyn nan ko da scratch ba” yayi murmushi yace “you are right. Amma dai ya dauka. So, dole zai biya in kuma ba zai iya biya ba sai ya tafi gidan maza har zuwa ranar da iyayensa zasu samu kudin da zasu biya masa” na tako nazo gaban table dinsa na tsaya, ina jin kamar in rufe shi da duka. Nace “me yasa? Tarko ne ka dana masa na sani but why? Me yasa? You could have just let me take him to court kamar yadda nayi niyya ya sake ni and that’ll be all. Zumuncin dama ai a lalace yake menene saura. Why do you feel the need to lock him up?” Yace “kamar yadda kika ce in kika kai shi court ya sake ki that will be all. Meaning duk abinda yayi miki yayi a banza kenan? What he did to you and said to my face shikenan yayi a banza kenan?” Ya fada with bitterness in his voice, ya cigaba “wannan abinda yayi, kuma ya gaya min yayi, shine greatest mistake dinsa a rayuwa kuma shine abinda zai paying for in prison for as long as possible” na zauna a kujerar da take facing dinsa nace “ni yayi wa, ba kai ba….” Yace “da ni yayi wa da sai abin yafi zuwa masa da sauki” naji zuciyata ta karye nace “Sadauki…..komai ya faru fa ya wuce. Ni duk na yafe kowa saboda a yanzu kowa yayi paying price dinsa. Tun daga ranar da aka kaini gidan Saghir nake addu’a cewa Allah ya saka min akan duk wanda ya zalinceni, kuma a yanzu bayan shekaru duk wadanda suka zalinceni din babu wanda bai karbi hukuncinsa ba. Inna, tun ranar da aka kaini gidan Saghir har yau Inna cikin regret take, har yau bata samu peace of mind ba saboda bana jin akwai abinda yafi ciwo irin ace uwa tayi destroying rayuwar yarta da kanta. Alhaji Babba a yanzu fa bashi da komai, ka tuna dukiya da izza irin ta Alhaji Babba amma yanzu rigar da zai saka ma sai in na debo na Saghir da baya sakawa na aika masa saboda shi ba zai bashi din ba. And Saghir, Saghir fa ta kare masa, ko da bakayi trapping dinsa ya daukar maka kudi ba Saghir already yana da case, NDLEA sun samu drugs a dakinsa dan haka suna nemansa. So you see? You don’t have to do anything Allah yana planning komai accordingly” yace “na yarda, kamar yadda na yarda cewa Allah yana using people to furnish other people. Alhaji Babba da kike magana fa har yanzu baiyi regret ba, ko ya taba kiranki ya baki hakuri akan abinda yayi? Har yau da zaki tambayeshi cewa zaiyi taimaka miki yayi ya aura miki Saghir, dukiyarsa kuma cewa zaiyi makiyane suka saka masa hannu. So dole ya cigaba da zama gida daya da kaji da raguna ya cigaba da having sleepless nights for as long as I had, which will be like forever tunda har yau ba baccin nake yi ba” Na mike tsaye ina jin haushinsa nace “how thick is your skull? In kana furnishing Alhaji su kuma iyalansa fa? Me sukayi maka? Makota fa? Me sukayi maka? Gidan gona tunda ka bawa Asma’u zan saka ta ta chanja masa guri. Batun Saghir kuma za’a biya ka kudinka, za’a siyar da duk abinda ya siya da kudaden sannan a nemo sauran a cika maka a baka kayanka ba shikenan ba?” Ya mike tsaye yana murmushi yace “me da me za’a siyar, gida da motoci? You are kind of late because I already bought the house and one car about two weeks ago” na juyo da sauri nace “what?” Ya gyada kai yace “bayan ya debi kudina I asked someone to track duk abinda zaiyi da kudin, naji ya sayi gida da motoci and I became worried cos zai iya siyar dasu ya biya ni. Luckily for me, sai ga report cewa one of his friends…” Ya duba wata takarda a gefe yace “Kabir, ya saka gidan da mota daya a kasuwa zai siyar, he was in a kind of hurry sai na taimaka masa na siya, yanzu har na zuba yan haya a gidan. Shi abokin daya siyar din yanzu ance min ya gudu ya bar kasar” ya sake murmushi “hard luck for him”.3 Na dafa kujera na zauna ina kallonsa. Na fahimci lissafin sa tsaf kuma na gane mai ya faru. Saghir ya saci kudi, Kabir set him up with the drugs sai ya siyar da gidan ya hada da sauran kudaden ya gudu. Meaning yanzu Saghir bashi da abinda zai biya ga kuma case din drugs a kansa. Sai na mike ba tare dana sake cewa komai ba har nayi hanyar waje kuma sai na tuna abinda ya faru rannan dan haka na juyo nace masa “open the door” yace “Please Diyam, stay out of it. Let him take the fall. He more than deserves it” na dawo gabansa nace “tell me something. Me yasa ka yafe wa Inna? Inna tafi kowa musguna maka a duniya amma ita mai yasa ka yafe mata?” Ya dago kai yana kallona yace “she gave birth to you”.Maganar ta daki kunnuwana sannan ta wuce har cikin zuciyata, sai naji tamkar ta kunno min emotions din dana ke ta kokarin dannewa a cikin zuciyata, sai hawaye yazo idanuna ya fara zuba kan kuncina a hankali na fara rera kuka sai ya taho inda nake da sauri yace “Diyam…..” sai kuma ya dakata ya juya ya koma bayan table dinsa ya danna button din bude kofa yace ba tare daya kalleni ba “good bye Halima”. Na juya nima da sauri na fita ina kokarin goge hawayen fuskata. Na sauka daga stairs din cikin sauri na fita daga building din. So nake kawai in samu seclusion din da zanyi kuka na son raina har in gode Allah. Na tsaya a bakin kenan naga mota tayi packing a gaba na sai driver din ya fito ya zagayo inda nake ya bude min kofar baya yace “oga yace ki shigo a kaiki gida” har nayi tunanin kin shiga sai kuma nayi lissafin gwara inyi kukana a cikin mota ni kadai da ac akan inyi a cikin napep mutane suna kallona.3 Na shiga ya rufe kofar ya zagayo gurin driver sannan na masa kwatancen gidan Alhaji Babba muka tafi. Na jawo hijab dina na rufe fuskata nayi kuka na na koshi amma ni kaina bansan kukan menene ba, kukan tausayin kaina ne ko na Sadauki? Kukan abinda ya faru da ne ko kuma wanda zai faru nan gaba? Ko kuma kukan abinda yake faruwa yanzu ne? Nayi bitar maganganun Sadauki ina son inyi placing dinsa a scale din dai dai da rashin dai dai. A iyakacin fahimta ta tun muna yara nasan kafiya da zuciya sune manyan flaws din Sadauki. And he seemed to be harder yanzu. Ya nutse sosai a cikin kogin revenge yadda har yana kokarin yayi loosing kansa, and I won’t allow that.5 Nasan duk abinda yayi akan gaskiyar sa yake, babu inda ya kaushe wa shari’a but still Allah da kansa yace yana son bayinsa masu hakuri ni kuma ina so Sadauki ya kasance a cikin jerin mutanen da Allah yake so. Muna zuwa gidan Alhaji Babba na sauka, drivern ya tambayeni in shikenan inda zai kaini na amsa masa da eh. A dakin Alhaji na same sun yi tsuru tsuru har da Fauziyya. Ina shiga Alhaji ya mike yana tambayata “ya kuka yi Diyam?” Na girgiza kaina kawai na zauna a raina ina cewa ‘you are in for a bad news’ duk da daga yanayin su na fahimci sunje gidan Saghir sun tarar da yan haya a ciki. Alhaji ya zauna shima, yanayinsa kawai ya isa ya saka mai raunanniyar zuciya kuka, yana cewa “wannan wacce irin mummunar kaddara ce ta afkawa yaron nan? Wallahi ni ko da wasa bai gaya min ya dauki wadannan kudade ba, ballantana ya gaya min ya karbi wannan ajiya. Ba wanda yake neman shawara a gurinsa shi kadai yake al’amarinsa shida abokansa. Yanzu gashi gidan munje mun tarar da mutane sunce su haya suke yi a hannun wani agent suka karba” sai na basu labarin duk abinda na fahimta da maganar, a lokacin da Saghir yake can yana honeymoon dinsa shi kuma babban abokinsa Kabir ya saka gidan da kuma motar da Saghir din ya siya da sunana a kasuwa, ya karbe kudaden ya hada dana wajensa ya gudu ya bar kasar bayan ya bawa Saghir ajjiyar drugs kuma yayi masa chunen NDLEA.1 Kowa yayi shiru a dakin har na gama bayani na, sannan na kara da cewa Sadauki yana kan bakansa na cewa sai an biya shi kudinsa. Har na gama babu wanda ya samu damar bani amsa. Sai dana gama sannan Hajiya Babba tace “Allah, Allah mun tuba. Allah in laifi muka yi maka ka dube mu ka yafe mana ka kawo mana sassaci a lamarin nan. Allah ka dubi yaron nan ka fitar dashi daga wannan matsala” ni dai nace “ameen” amma a raina nasan a inda matsalar take. Alhaji ne yayi deciding cewa zai je yaga Saghir kuma zai gaya masa halin da ake ciki. Sai naji dadi dan ni kam I wasn’t looking forward to breaking the news to Saghir cewa best friend dinsa ne yayi framing dinsa dan ya cinye masa kudi. Daga gidan Alhaji gidan Mama na tafi. Ina shiga Subay’a ta taho da gudu ta tarye ni tana cewa “Mommy ina daddy? Kin dauko shi daga gurin yan sandan?” Na jawo ta na rike fuskarta a hannuna nace “Daddy ya sake yin wata tafiyar, amma zai dawo very soon” sai ta saka kuka ita gurin Daddy zata je ita in kira mata shi a waya. Sai da Mama tayi barazanar dukanta sannan na samu tayi shiru. Muka zauna na bawa Mama labarin duk abinda ake ciki tace “ki fita cikin maganar nan Diyam. Ki barshi shi da iyayen sa suyi ta fama ai tsuntsun daya ja ruwa hausawa suka ce shi ruwa kan doka. Duk halin da Saghir yake ciki iyayen sa ne suka jawo masa dan haka ki barsu su girbi abinda suka shuka da hannun su” sai nayi shiru ina kallon Subay’a tana wasa ina tunanin ko zata daina tambayata daddyn ta? STORY CONTINUES BELOW Sai yamma sosai na shirya Subay’a muka koma gida, muna zuwa na tarar Inna itama dawowar ta kenan sai Asma’u take bamu labarin Sadauki yazo yiwa Inna sallama zai tafi ‘business trip’. Na kwanta kawai na rufe idona amma nasan babu wani business guduwa yayi dan kar inyi breaking dinsa. An saka ranar shari’a Saghir sati biyu bayan kama shi, na shirya na koma bompai gurinsa amma sai yaki yarda ya ganni, officer din yace “ya zama very emotional kwana biyun nan yace baya son ganin kowa” sai na fahimci cewa Alhaji yazo ya bashi labarin cin amanae da Kabir yayi masa, and it broke him, finally. Tun da aka saka ranar shari’ar Saghir ban zauna ba, nice gidan Alhaji, nice bompai, nice NDLEA, kuma nice kiran Sadauki. Kullum sai na kira shi da yawar Asma’u amma itama sai ya daina dagawa. Sai in zauna in tsara masa message, duk abinda nasan zai saka ya sauko in tura masa amma ko reply daya ban taba samu ba.1 During one of my visits to NDLEA ne na samu rannan suka saurare ni, nayi musu bayanin abinda ya faru nayi mentioning sunan Kabir and that cought their attention, ashe dama suna suspecting dinsa amma basu da hujjar kama shi dan haka sun yarda zai iya framing Saghir din but still there is a case, kuma dole someone has to take the fall, Saghir kenan, dole zasuyi convicting Saghir suyi sentencing dinsa har sai an kama Kabir ya kuma karbi laifinsa. I felt relieved, duk da ba wani important improvement bane ba but at least it was a step further. An siyar da gidan Saghir inda muka zauna, an siyar da tsohuwa da sabuwar motarsa sannan an siyar da motar daya siyawa Fauziyya itama. Sai aka hada da kudaden daya bari account din sa but all that only raised one third of kudin da ake binsa. A lokacin ne na kuma fahimtar cewa Saghir bashi da kowa, bashi da brother dama, cousins din kuma da brother in laws din duk babu wanda yayi zaman arziki dasu ballantana su tsaya masa, uncle din kuma yayi wa yarsa ciki dan haka ko sau daya bai taba shiga maganar ba, daga ni sai Hajiya da Alhaji, ga Alhaji babu isasshiyar lafiya ga kuma tsufa daya kara saukar masa. Yan uwan Hajiya ma duk sun zare hannayensu sunce wannan abin kunyar ba da su ba. Nima rannan na dawo gida a gajiye Inna ta kalleni tace “daga yau babu inda zaki kuma fita akan maganar nan. In dake ce wani abu irin wannan ya same ki da daga Saghir din har iyayensa babu wanda zai daga ko dan yatsa ne ya taimaka miki, dariya ma zasu yi miki” na zauna kawai nayi shiru, sai tace “ko kin chanja shawara kuma Saghir din zaki komawa?” Nayi saurin girgiza kaina. Bana son Saghir kuma na gama aurensa, that’s a fact, but still har yanzu mijina ne, nayi kurakurai da dama a rayuwar auren mu bab sani ba ko wannan kokarin da nake masa zai taimaka min wajen goge wadancan laifukan. Sannan kuma, Subay’a, bata da wani uban daya wuce Saghir duk wani wanda zai rike ta sai dai ya zama uban kara amma ba mahaifi ba, and I am not looking forward to telling her that babanta yana prison, what will happen kuma inta fahimci cewa Sadauki yayi playing role a saka babanta a prison din?12 Another dalilina kuma shine Sadauki. Sadauki loves me, for that bani da dobt, wannan kusan shine dalilin da yasa ya gudu saboda kar yaga na damu ya kasa abinda yayi niyya. And I love him, shima bani da dobt a kan wannan dan haka nake so in chanja ra’ayinsa zuwa forgiveness, for his sake, saboda ina gudar masa daukan alhakin wadanda basu da laifi, ina kuma gudar masa dana sani a nan gaba.1 Ranar sharia tazo and we all went to the court, na bar Subay’a a gida, wadda a ranar ma sai da tayi min complain din neman daddyn ta. Na samu seat a farko farko na zauna bracing myself for duk outcome din da za’a samu. Muna zaune aka shigo da Saghir, looking very down and defeated, ban taba ganin sa a haka ba. Ya zauna a gurin zaman accused looking down at his fingers. Sai aka fara gabatar da kara, aka lissafa all charges against him sai lawyers suka fara maganganun su da ba ganewa ake yi ba, nayi ta stressing ƙwaƙwalwa ta ina so in gane mai suke cewa amma sam bana fahimta sai dai in sunyi magana inga alkali ya gyada kai har suka gama. Sannan ya juyo yana kallon Saghir ya tambaye shi “how do you plead?” Ba tare daya kalle shi ba yace “guilty” and my heart went out to him. A take alkali ya yanke masa hukunci, for the crime of kudin Abatcha Motors daya ci, za’a rike shi a prison har sai familyn sa sun biya kudin, for the crime of drugs, shima zai zauna har sai an kama Kabir. In both cases he is doomed for life. Aka gama karanta masa sentence dinsa amma bai dago kansa ba, na fara jin koke koke a baya na. Na waiga naga Hajiya tana kuka ita da kanwarta, sai Fauziyya daga can gefe, sai su Murja sun hada kai ita da sauran yan’uwanta suna yin nasu, and then a can karshen room din na hango wadda banyi tunani ba. Suwaiba. Itama tana nata kukan. Sai aka taho dashi za’a wuce dashi, ya tsaya yana kare mana kallo daya bayan daya, sai muka hada ido and he smiled. Da sauri na mike na tari abin hawa zuwa gida.1 Ranar kwana nayi banyi bacci ba. Washegari Mama tazo suka wuni anan ita dasu Rufaida da Muhsina. Bayan sun tafi da yamma sai naga Subay’a ta shigo da banki irin na kasar nan na yara ta saka a kasan gadon Inna. Nace mata “Subay’a? Banki kika siyo mana?” Tace “eh, kudi zan ringa tarawa a ciki in biya wannan yayan naki kudin sa da yake bin Daddy na” I was stoned, nace “Subay’a? A ina kika ji wannan maganar?” Tace “Mama naji suna hirar da Inna, wai Daddy na yana gurin police sai an biya yayanki kudi sannan za’a fito dashi”.2 The next day na tashi da wuri na shirya, Inna ta tambayeni inda zanje sai nace “prison” sai ta shirya min abinci a basket tace “ki kai masa”. Da yake anan kano central prison yake, dan haka da kafa na tafi tunda babu nisa da gidan mu. Na jima ma’aikatan prison din suna ta ja min aji kafin su yarda zan ganshi. Sai suka kaini wani guri suka ce in zauna. After waiting for like eternity sai gashi sun fito dashi. He looked very different. Older but calmer. Suka zaunar dashi a kujerar gaban table din da nake sannan wanda ya kawo shi ya matsa baya but yana kallon mu. Na sunkuyar da kaina ina lissafa fingers dina shi kuma yana kallona yace “my God, you really are beautiful” na dago na kalle shi and he smiled. Nace “ga abinci nan inji Inna” yace “thank you. Dama kinga azumi nake yi” nayi shiru ina tunanin ban taba ganin Saghir yana azumi ba in ba Ramadan ba. Sai yace “ya kika ga sabon gida na? Yayi kyau?” Na kalli surrounding din gurin nace “nan ba gidan ka bane ba Saghir. I am going to get you out of here” yayi dariya yace “how? Zaki saka ni a jaka ne mu tafi gida tare?” Nayi shiru. Yace “nasan maybe, just maybe, zaki iya convincing your lover boy ya yafe min kudinsa, but zaki iya kamo Kabir ki danka shi a hannun hukuma ki saka yayi confessing cewa shi yayi framing dina?” Nace “maybe, just maybe, zan iya convincing Sadauki ya yafe maka, sannan in saka shi yayi amfani da power dinsa to get you out. Nigeria ce fa, with few phone calls an gama komai”.2 Yayi dariya “not even in your dreams. Ba zaiyi ba. Mutumin da yake son ganin baya na ta yaya zai taimaka min?” Nayi shiru, nima kaina bansan ta inda zan bullowa wannan lamari ba but i am going to try.1 Yace “I really did mess up ko? Nayi messing up auren mu. It would have been a great one” nace “not ‘you’ but ‘we’. Tare muka hadu muka rusa auren mu. Ina fatan kuma zaka yafe min my part of the mess” yace “oh, you mean the closed doors ko?” Nayi murmushi. Na juya hannunsa yace “na yafe” nace “thank you”. Sai ya saka hannu a aljihu ya fito da takardu guda biyu yana kallona sarcastically yace “ya sunan ki ma? Ke ce Halima ko kece Fauziyya?” Bance komai ba sai ya miko min daya, naga sunana baro baro a jiki na bude na karanta1 Ni Saghir Muhammad Kollere na saki matata Halima Usman Kollere saki daya, in ta samu miji tayi aure5 Na dago ina kallonsa yace “daya ne ba yawa, in kika hada da wancan sun zama biyu kenan. Ni kuma na rike daya a gurina with hope that maybe, just maybe, zaki zauna ki jira ni” nayi murmushi yace “not even in my weirdest dream ko? I will just have to keep hoping”.6 Mutumin daya rako shi ya matso yace “time up” na gyada kaina na mike kamar zan tafi sai kuma na dawo na tsaya a gabansa nace “For raping me, na yafe maka. For the twins, na yafe maka. For everything, na yafe maka. And I am going to get you out of here”7 Yayi murmushi yace “thank you. Goodbye Halima”.4 Sai na juya da sauri na fita daga gurin, na kuma fita daga cikin prison din, hannuna rike da takarda ta. Na fara tafiya a kafa ina jin iskar yanayin damina tana ratsani. Wani abu naji ya yaye daga ƙwaƙwalwa ta. I felt a sense of freedom wanda rabon da inji shi tun ranar da aka aura min Saghir. Hatta hanjin cikina ji nayi yana warwarewa tamkar da a nannade yake a guri daya, wani abu daya tokare a makogwarona naji ya sauka at last ina shaƙar numfashi freely.4 And I decided that I am going to do the right thing.