DIYAM CHAPTER 3
Tun daga ranar Diyam da Bassam suka hade, kullum a school suna tare duk ya daina kula friends dinsa ita kuma dama bata dasu, daga school kuma zai wuce gurin aikinsa, anan zai samu kudin kashewa gobe. Sosai yake jin dadinsa hankalinsa kwance as if bashi da wani problem.+ Ranar Thursday suna lunch a cafeteria kamar kullum, Diyam ta tambaye shi “can you tell me about that not laughing situation da kace kana ciki? Because I can see yanzu kana dariyar” dariyar yayi sannan kuma ya hade rai yana jujjuya abincin gabansa yace “I got fired” ta zaro ido tana mamaki, fuskanta cike da concern tace “daga gurin aikinka? When?” Yace “no, ba daga gurin aikina ba, I got fired from my family” ta hade rai tace “your family? Ta yaya za’ayi familyn mutum su kore shi? Me kayi Bassam? What happened?” muryarta tana breaking kamar zata yi kuka ta tambaye shi, ba tare daya kalleta ba yace “nayi laifi, babban laifi, maimakon in tsaya in fuskanci hukunci na kuma sai na gudu na kama daki a hotel nayi zamana. When I did that na saka ran kwana biyu ba zasu wuce ba mami na da Daddy na zasu zo kasar nan, nayi tsammanin zasu zo har dakin da nake, nayi tsammanin karbar wadansu kyawawan mari daga Daddy na kuma yi tsammanin in samu nasiha daga mami amma shiru, basu zo ba ballantana su fada min cewa nayi ba dai dai ba ballantana su kaini gurin Aunty na da nayi wa laifi su saka ni in bata hakuri” ya dago ido yana kallonta cikin ido yace “basu zo ba ba kuma su kira ni ba, they just cut me up, basu zo ba ballantana suyi min maganin problem dina, at least ko shawara ce su bani”. Tana kallonsa tace “wanne problem ne kenan? Your smoking problem?” Ya girgiza kai yace “basu san wannan ba ai” sai kuma ya bata labarin feelings dinsa for Khausar, da kuma yadda ya tarar tana dating cousin dinsa Ayan, tun daya fara bata ce komai ba har sai daya gama sannan tace “how old are you Bassam? You know nothing about love, do you? That girl doesn’t love you, cigaba da jan magana tsakanin ka da ita ba abinda zai yi sai bata zumuncin dake tsakanin ku. Kuma ni a fahimtata familyn ka ba wai cutting dinka off suka yi ba, suna keeping tabs on you tabbas tunda su suka haife ka and they love you. They just want you to grow up, they want you to make the right decision by yourself daga nan sai su san hukuncin da zasu yanke maka. Kafin Mami da Daddy su zo su baka shawara ni ga tawa, ka koma gurin auntyn ka wadda kayi wa laifi kaje ka bata hakuri on your on ba wai sai ance maka kaje ba, ka bawa cousin dinka hakuri kuyi shaking hands kabar maganar Khausar, you don’t know what God has planned for you”. Yayi murmushi yace “I guess you are right, maybe wadda zan samu nan gaba tafi Khausar komai” ya karashe maganar yana kashe mata ido daya. Tayi saurin dauke kanta tana jin zuciyarta tana bugawa da karfi. A take taji abincin ya fita daga kanta, ta ture plate din ta mike tace masa zata je class in ya gama ya same ta a can, ya bita da kallo har ta fita yana mamakin me ya chanja mata mood. A ranar haka ta wuni tana jin ranta babu dadi, kar dai abinda take tunani akan Bassam haka ne, kar dai he is developing feelings for her, kar dai abinda Murjanatu ta fada rannan gaskiya ne, cewa she is playing with fire. Tana zuwa gida ta tarar da abinda yafi wannan daga mata hankali. Murjanatu ta gani zaune ta zuba uban tagumi, ya yarda jakar hannun ta ta zauna a gabanta cike da concern tace “Fanna? Lfy?” Ta dago tana kallonta tace “yaya ya kira yanzu, wai in gayawa Judith ta hada kayanta ta bar gidan nan kafin weekend” Diyam ta mike “au wai har yanzu bai bar maganar Judith ba? Me ta tsare masa? Akanshi take zaune? Ni ba zan iya korar Judith ba tunda babu abinda tayi min, dama baki gaya masa sakona na ranar nan ba?” Murjanatu tace “ni na ce miki bazan iya gaya masa ba Diyam tsoro nake ji” Diyam tace “mala’ikan mutuwa ne shi da zaki ke tsoronsa?” Daga haka ta figo wayarta daga cikin jaka and for the first time tun zuwan ta kasar ta danna number dinsa, bugu daya ya dauka, bata ko saurare shi ba ta fara zazzaga bala’i “wanne irin mutum ne kai wai? When will you stop playing god? When will you stop making decisions a rayuwar mutane? This is my life and I asked you to stay out of it” I nutse yace “Diyam….” Ta katse shi “kar ma ka gwada yimin dadin baki, bazan kori Judith ba and that is final” yace “am sorry dear, I was just trying to..” tace “trying to protect me? To kayi hakuri but I don’t need your protection” ya sake cewa “I was just trying to…..to provoke you into calling me” sai ya kyalkyale da dariya. Ta tsaya tana kallon wayar da mamaki, sannan ta kalli Murjanatu taga ta durkushe a kujera tana ta kyalkyala dariya harda rike ciki, sannan tayi realising abinda ya faru. Ta jefar da wayar kamar wadda aka ciza sannan ta dafe kanta da hannu biyu tace “oh God, Murjanatu what have you done?” Da gudu Murjanatu ta mike ta shige daki tana dariya ta rufo kofa. Diyam ta zauna akan kujera ta dauki wayar da har yanzu take a kunne tace “this is cheating” har yanzu da dariya a muryarsa yace “kin tuna abinda kika ce min ranar da zaki bar Nigeria? Kin tuna alkawarin da muka yi dake cewa in dai kika dauki waya da hannunki kika kira ni to nayi winning, zan yanke duk hukuncin dana ga dama” ta sake cewa cikin raunanniyar murya, “but this is cheating” yace “in life, my dear, cheating is allowed once in a while” sannan ya kuma dariya yace “see you on Saturday” ya katse wayar. Ta kife kanta a kujera tana jin hawayenta yana jika kujerar, sai da tayi kukanta ta gama sannan ta dago ta dauki wayarta ta tura masa message “You always claimed that you play your games fair and square, but this is not fair” Bayan yan mintina reply ya shigo mata “Nothing is fair my dear, life in itself is not fair, you just have to be smart and have eyes like an eagle’s so that you won’t get cheated on. My regards to your lips”.Ta jima a kwance a gurin, har Judith ta dawo ta shiga kitchen ta fara hada musu dinner, sannan ta tashi ta shiga daki tayi sallar magrib ta kwanta, ita ba bacci ba ita ba ido biyu ba tana ta saka da warwara. Allah ya gani bata son wannan zuwan nashi dan tasan ba zasu kare da dadi ba, zuwa zaiyi suyi ta rigima kuma rigimar da babu inda zata kai su. A nesa nesa dai sai sunfi samun kwanciyar hankali, wannan shi yasa ta zabi tahowa karatu nan kasar dan tayi baya dashi har abubuwa su warware. She don’t want to keep hurting herself and she don’t want to hurt others. Bassam ne ya fado mata a rai. Poor innocent Bassam, daga ganinsa tasan is from a wealthy family amma duk da haka bata son involving dinsa a wannan drama din, kuma she is afraid that he is already involved saboda irin kallon da yake mata kwana biyun nan. Kar dai ace ya fara son tane. She will have to put a stop to their relationship. Har daki Judith ta kawo mata dinner kuma ta matsa mata sai data ci, tana ta tambayar ta abinda yake damunta amma sai tace mata family issue ne kawai. Washegari tana shiga class ta hango Bassam a seat din kusa da inda take zama, sai tayi sauri ta dauke kanta ta samu front seat ta zauna. Bata jima da zama ba taji kamshin turarensa a kusa da ita, bata dago kai ba yace “Are we changing seat?” Still bata kalle shi ba tace “I am” ya koma baya, ana jimawa sai gashi ya dawo da takardun sa ya zauna a seat din kusa da ita. Bata ce masa komai ba ta dauko littafi tana karantawa, shima ya dauko nasa yana flipping through the pages, can ya ajiye yace “can we go and eat? Ni fa yunwa nake ji” bata kalle shi ba tace “you can. Am okay” yace “me kika ci?” Sai ta mike zumbur ta rataya jakarta, yace “ina kuma zakije?” Tace “somewhere quiet” ya bita da kallo baki bude har ta fice daga ajin. Ya ajiye littafin hannunsa yana tunanin a inda yayi laifi. Har aka fara lecture bata dawo ba. Sai a lokacin yayi realizing cewa bashi da number dinta, dan haka hankalinsa gaba-daya yana gurinta har akayi lecture din aka gama. She never misses her lectures tunda ya santa sai yau. Ya fara tunanin ko bata da lafiya ne? Lecturer din yana fita shima ya fita ya fara nemanta, duk inda suke zuwa tare sai daya je amma bata nan har lokacin wata lecture din yayi sannan ya dawo wai ko zata zo wannan amma itama shiru har aka gama. Ana gama wa ya tafi department din su Murjanatu ya tarar yau sam basu da lecture ma dan haka bata zo ba. Yana futowa ya tare cab sai block dinsu. Ya hau lift har apartment dinsu yayi ringing bell, daga ciki ya jiyo muryar Diyam ta amsa “who is there?” yace “thank God. Bassam ne, Diyam?” shiru tayi bata bude ba, har yayi kamar zai sake danna bell din kuma sai ta bude, fuskarta a hade ta tsaya tana kallonsa kawai bata ce komai ba, ya tsafa kansa yace “You skipped your class and I was worried and thought ko baki da lfy ne” direct tace masa “lfy ta kalau as you can see” tana ganin yadda expression din fuskarsa ya chanja, daga gani tasan bai ji dadin abinda tayi masa ba amma sai kawai ta juya zata koma ciki ba tare data kara cewa komai ba, yace “Diyam?” ta dakata amma bata juyo ba, yace “in kina so in daina kula ki ne just say so ba sai kin tsaya kwana kwana ba, but please don’t skip your classes because of me” daga haka taji motsin tafiyarsa. Ta juyo tana kallon kofar duk ranta babu dadi, sam bata ji dadin bata wa Bassam rai da tayi ba but wani abun ya zama dole ne, laifin tane tun farko data fara zama involved with him amma ai a lokacin bata yi tunanin zai yi attaching wasu strings a relationship din nasu ba. Ta dawo ta rufe kofar sannan takoma ta kwanta a doguwar kujera ta rufe idonta tana lissafin yadda next weekend din zai kasance. Haka ta ringa jera tsaki ita kadai a kwance har taji motsi a hanyar corridor din dakunansu, ta daga kai taga Murjanatu a tsaye tana kallonta, nan take ta kara bata rai ta juya bayanta. Murjanatu ta karaso ta zauna a gefenta tace a hankali “Diyam” Diyam ta mike ta dauki wayarta ta shige ciki ta barta a zaune. Bassam tunda ya bar gidan su Diyam ya saka hannayensa a cikin aljihunsa ya fara tafiya, wani irin zafi yake ji a ransa yana jin zuciyarsa tana kara karyewa, tambayar da yake ta maimaitawa kansa itace me yayi mata? Duk iya tunanin sa in ya dawo da hirarrakinsu baya sai yaga babu inda yagaya mata ko da kuwa wata magana ce marar dadi. Shi akwai wanda ya samu power over him a rayuwarsa irin Diyam? Tun farkon haduwar su baya iya mayar mata da magana, to me ya faru? Babu abinda ya kai ayi maka hukunci ba tare da kasan laifin me kayi ba ciwo. Yana isa kofar hotel dinsa sako ya shigo cikin wayarsa. Ya dauko yana dubawa, for the first time in weeks ya samu sako daga gida, daga brother dinsa, yaji heart dinsa tana racing kafin ya bude amma yana bude wa sai ya tarar babu ko kalma daya a cikin sakon sai hoto, hoton flight ticket. Yayi ajjiyar zuciya ya jingina da bango, wato babu wata magana kenan a tsakanin su sai yaje gida. Abinda suke bukata dashi shine ya kai kansa gida ya karbi laifinsa. Yayi ajjiyar zuciya ya mayar da wayar aljihu a ransa yace “not now brother” dan bayajin zai bar kasar har sai yayi straightening tsakanin sa da Diyam. Ya tuno da shawarar da Diyam ta bashi na cewa ya je gurin Aunty Hafsat ya bata hakuri sannan ya tafi gida ya kai kanshi. Wani tunani ya fado masa a game da Diyam, anya ba wannan ne dalilin da yasa ta juya masa baya ba? Washegari Friday, da sassafe Diyam taje school dan ko breakfast bata tsaya tayi ba saboda bata ma son abinda zai hada ta magana da Murjanatu har sai tayi deciding inda zatayi placing dinta. Ta jima a class tana duba takardunta amma a can kasan zuciyarta tana duba ta inda Bassam zai bullo. Tana nan a zaune har aka zo aka sanar cewa lecturer din ba zai samu zuwa ba, a dai dai nan Bassam ya shigo, suna hada ido tayi saurin dauke kanta amma ta kasan idonta ta hango shi straight ya taho gurinta, ta fara kokarin harhada takardunta pretending to be busy har yazo daf da seat dinta ya tsaya, da dan karfi yace “why? Menene dalilinki na cutting dina off? Laifin me nayi?” Bata ce komai ba amma sai taji wani abu ya rike a tsakiyar cikinta kamar mai jin yunwa, nan take jikinta ya kama karkarwa har takardun hannunta suka zame suka zube a kasa, ta sunkuya tana kwashewa shima ya sunkuyo yana taya ta, sunkuyon da tayi yasa rolling din veil dinta ya kunce gashinta ya zubo ya rufe mata fuska ya sauka akan hannayensa. Still yayi yana kallon tsaho, baki da santsin gashin, ya daga hannunsa ya mayar mata da gashin bayanta tare da bude mata fuskarta, a lokacin ya lura da how red fuskarta da idonta sukayi, sai kawai yaji tashi zuciyar tayi melting, yaji kamar bai kyauta ba da ya daga mata murya har ya bata mata rai. Ta mike ta warce papers din hannunsa ta ajiye a gefe tana gyara veil dinta yace “am sorry Diyam but dan Allah ki gaya min abinda nayi miki” ta dauki takardun ta ta zagaye shi zata wuce ya rike jakarta yace “saboda na fada miki am in trouble da family na shine zaki juya min baya?” Da sauri ta juyo tana sauke manyan idanuwanta da suka yi ja a kansa, she looked shocked, bata taba zaton zai yi linking wannan abin da labarin sa ba, ta warce jakarta tace “is that what you are thinking? tunanin da kake yi a kaina kenan?” Ya daga kafada yace “then tell me otherwise, me nayi miki” tace “babu abinda kayi min Bassam” ta danyi shiru kamar mai tunani sannan cikin karyayyiyar murya tace “am just not who you think I am. Am sorry” ta juya da sauri saboda hawayen da taji yana taho mata. Kafin ta kai kofa ya kuma rike jakarta, ta juyo ta zuba masa jajayen idanuwanta yace shima da raunanniyar murya “ko ba zaki cigaba da kulani ba, at least give me your number yadda zan ke jin halin da kike ciki ko a waya ne, ko physically ba zamuyi magana ba at least…..” “Number?” Ta katse shi “wacce number zan baka Bassam? Ohhh I have so many numbers a cikin wannan kan nawa” ta fara lissafa masa da yatsun hannunta “kaga na farko 24 itace number din shekaru na, 3 itace number adadin yayan dana haifa a duniya, 2 itace number of times I was divorced, 8 itace shekarun yar karamar yarinya ta, infinity shine number of times my heart was broken and 0 is the tolerance I have for other hear breaks. So tell me, wacce number zan baka a cikin wadannan?”14 A hankali jakarta ta zame daga hannunsa saboda yadda gaba-daya jikinsa ya saki, tamkar numfashin sa aka zare gaba daya. Ta tako zuwa dai dai fuskarsa tace “like I said, am not who you think I am”. Har ta fita daga ajin bai motsa daga inda yake ba.4 You did not see that coming, did you?7 Tabbas maganar da Diyam ta fada wa Bassam bashi kadai ta taba ba, har ita. Tana fita daga ajin taji kanta yana wani irin juyawa kamar zata fadi, duk reality din rayuwar ta yana dawo mata. Tun da tazo UK take living in a dream yanzu kuma ta farka, gobe kuma zata kara farkawa tunda gobe zai zo bata san kuma da wacce zai zo ba. As far as he is concerned yayi winning over her dan haka zata bi abinda yace kenan. Ta samu jikin wata bishiya ta jingina tana mayar da numfashi, a nan taji karar shigowar text wayarta, ta dauko a jaka ta bude taga wanda take tunanin ne ya aiko mata da message+ “Tell him I say hi, kafin inzo mu gaisa gobe”1 Ta sake karantawa, ta nanata amma ta kasa making sense of it. “Him?” who is him?. Wata karamar murya a can kasan zuciyarta tace “Bassam” ta zame ta durkushe a gurin, so he knows about Bassam? Abinda take ta gudu kenan gashi nan bata yi escaping ba. Amma ta yaya yasan labarin Bassam? “Murjanatu” muryar ta sake fada mata. Ta mike and for the first time ta tari cab saboda yadda take ji ba zata iya tafiya a kafa ba. A motar ma dunkule wa tayi dan ba zata iya zama straight ba saboda wannan abin daya dunkule mata a ciki har yanzu bai saki ba, sai da drivern yayi mata magana sannan ta san sunzo, ta bashi kudinsa ta shiga ciki. Tana bude kofa idonta ya sauka akan Murjanatu a zaune tana facing kofa, suna hada ido Diyam tayi realising gaskiya, ba Murjanatu ce ta gaya masa ba. Murjanatu ta mike tana twisting hannunta tace “Diyam, yaya yasan kuna tare da wannan yaron” Diyam ta bita da kallo bata ce komai ba, Murjanatu ta cigaba “wallahi bani na gaya masa ba, I wanted to tell you tun jiya ya kira ni ya tambayeni wai waye kuke yawo tare dashi a school nace masa ni bansan kina yawo da kowa ba, he said in bangaya masa ba in yazo sai na sani. To dazu kuma ya kira yace min nayi masa karya kuma sai na gane kure na” still Diyam bata ce komai ba, kallonta take kawai tana lura da yadda tsoro ya fito baro baro a kyakykyawar fuskarta. Ta taho ta zagaye ta zata shiga corridor Murjanatu ta mike ta rike hannunta tace “Diyam am sorry akan maganar shekaran jiya, wallahi bansan betting kuka yi a kan wani abu ba, ni kawai cewa yayi min zamuyi playing game, yana so in nuna miki da gaske yake zai kori Judith, please Diyam kiyi hakuri bana son alakar mu ta baci a saboda wannan” ba tare da Diyam tace komai ba ta zare hannunta daga na Murjanatu ta shige dakinta ta rufe kofa. Direct toilet ta shiga, ta cire kayanta gaba-daya ta shiga shower ta kunnawa kanta ruwan dumi. Ta lumshe idonta tana jin dadin yadda ruwan yake sauka a kanta, tana jin duminsa yana narkar da daskararriyar zuciyarta, tana jin jijiyoyinta suna warewa suna aikawa da sakonni kwakwalwarta. Ta tuno abinda Murjanatu tace “a game” of course it is all a game, shi komai a gurin sa ai game ne. Ta tuno wata magana daya taba fada mata shekaru da dama da suka wuce1 “Diyam, life is like a game of chess, the secret to winning is to observe the movements of your opponent, think deeply and make your move” Amma abinda ya kasa ganewa shine a yanzu bashi da opponent din, shi kadai yake buga game dinsa, kuma ya kasa realizing cewa a haka zai zo yayi hurting others, innocent mutane kamar Bassam. Ya kasa realizing cewa duk abinda take yi tana yi ne for him not against him. Shi kawai burinsa yayi winning, no matter the cost. Ita kuma burinta shine ya ajiye wannan game din ya duba reality, ita bata son wannan game din nasa mai ban tsoro, dan last game din da ya buga didn’t end well, it ended with someone in jail for life, someone very important to her.5 Ta kashe shower din ta fito ta daura dogon towel sannan ta dauki karami tana goge fuskarta da dogon gashinta dashi, a ranta tana kokarin placing kanta in his place daga nan sai taga menene next move dinsa. Amma duk iya kokarinta ta kasa guessing menene zaiyi a next move dinsa. Ta fito ta dauki wayarta data ajiye tana dubawa, sai a lokacin tayi realising cewa for the first time tun zuwanta kasar yau ne rana ta farko da bai kira ta ba, hakan yana nufin yayi fushi da ita, fushi kuwa mai tsanani. Ita dai tasan har ga Allah bata fara kula Bassam saboda wani abu ba, ta fara kula shine saboda maganganu marasa dadi data fada masa a farkon fara maganar su, wannan yasa ta sauko da niyyar ta wanke kanta a gurin sa kuma sai abota ta shiga tsakaninsu. Ita tasan ko da da digon zarra bata jin wani feeling a kan Bassam wanda ya wuce na mutumta juna da aminci.1 STORY CONTINUES BELOW Ta shirya cikin doguwar rigar zaman gida, ta kwanta ta dauki pillow ta dora akan cikinta ta rungume, sai a sannan ta tuna cewa ko breakfast bata yi ba amma kuma yunwa is the last thing a mind dinta. She just want to know wanne mataki zai dauka, she just want to make sure ba zaiyi hurting kowa ba akanta. Tana nan kwance ita ba bacci ba ita ba ido biyu ba har lokacin sallar zuhr yayi, tayi alwala ta sauke farali sannan ta fito parlor, babu kowa dan haka tashiga kitchen ta dafa noodle ta zauna akan stool taci sannan ta wanke plate da tukunyar data bata ta dauki bottled water ta fito parlor ta zauna tana sha. Dai dai nan Murjanatu ta fito itama da shirin tafiya school. Ta dan zauna a gefen Diyam amma bata ce komai ba. Diyam ta mike ta shiga daki ta dauko dogon hijab ta saka tayi hanyar waje, har ta taba kofa taji Murjanatu tace “Diyam” sai ta juyo ta dawo kusa da ita ta zauna ta rike hannayenta a cikin nata tace “don’t worry. He won’t hurt you, not while am here”. Sai kuma ta tashi ta fita da sauri. Tana fita ta tari cab, since ta kasa sanin wanne mataki zai dauka ita zata dauki nata matakin da kanta. Bata san hotel din da Bassam yake ba dan haka direct mall din da yake aiki ta tafi. Tana kallon irin kallon da mutanen gurin suke yi mata kuma tasan yana da alaka da dogon hijab din da ta saka amma bata kula su ba ta cigaba da harkokin gabanta. Customer care ta tafi ta tambayi matar gurin agame da ma’aikacin su mai suna Sadiq Abubakar Sadiq. Daga farko kin bata wani information tayi a kansa for security reason, sai da tayi mata karyar ita friend dinsa ce ta yi loosing phone dinta ne kuma tana nemansa emergency concerning harkar karatunsu, sai da matar tayi checking taga sunan makarantar da kuma department din da Diyam din ta gaya mata yayi tallying da information din Bassam sannan ta gaya mata cewa bai shigo yau ba, amma ta gaya mata sunan hotel dinsa. Godiya Diyam tayi mata ta fita ta nufi address din da aka bata. A reception ta tsaya tasake yi musu bayani irin yadda tayi wa waccan matar amma suma suka hana ta hawa sama instead sai suka kira dakinsa through intercom, yana dauka Diyam ta karbi phone din tace “Bassam? Diyam ce. Can you come down for a minute? Ina son magana da kai please” daga can barin Bassam bai ce komai ba dan ji yake kamar in yayi maganar ma voice dinsa ba zai fito ba, sai kawai ya ajiye wayar. Diyam ta ajiye itama a ranta tana kissima cewa yayi fushi ne shima. Amma sai ta kasa fita, sai ta samu guri ta zauna tayi folding hannayenta ta zuba idanunta akan kofar lifter da take ta sunturin kai mutane sama da sauko dasu. Tafi minti sha biyar a zaune sannan ta mike cikin sanyin jiki da niyyar fita, a lokacin ne kofar lifter ta bude ya fito. Sweater ce a jikinsa mai hade da hula wacce ya jawo ya rufe kusan rabin fuskarsa dan haka ta kasa karantar emotions dinsa amma sai taga a idonta kamar ya dan rame kadan. Ya tsaya a gabanta ba tare daya ce komai ba, tana jujjuya hannayenta tace “Bassam magana nake so muyi please in babu damuwa” ya danyi gyaran murya sannan direct yace “are you married? A yanzu nake nufi” da sauri ta girgiza kanta tace “of cause am not” ya gingina kai sannan yayi hanyar waje ba tare daya kuma cewa komai ba ita kuma ta bishi a baya.1 Baya suka zagaya, suka jera suna tafiya a tare, suna taka kafafuwansu a tare, amma daga ka gansu kasan akwai tension a tsakanin su. Wani garden suka shiga sannan suka je cikin wata rumfa suka zauna, gurin very quite duk da cewa akwai mutane jefi jefi suna hutawa a gurin, can kuma dan nesa dasu kadan swimming pool ne a zagaye ta fitulu mutane suna wanka a ciki. Ta daga ido tana kallonsa taga shima itan yake kallo, suna hada ido yace “uhumm? Ina jin ki, kince kina son magana dani” tayi kasa da nata idon tace “Bassam am so sorry ban gaya maka all these before ba, nayi haka ne saboda banyi tunanin da akwai bukatar in gaya maka din ba, yanzu kuma nace zan gaya maka ne saboda ka fahimci dalilina na daina kula ka, kasan cewa am doing it for you” ya katse ta “for me? How is that so?” Ta bude baki zata yi magana wayar ta tayi kara. Ta dauka tana dubawa wa, “Inna” ta danyi murmushin takaici ta ajite wayar, of cause Inna, of cause gurin Inna zashi ya shirya mata wata dramar kuma, tun dazu abinda take tunani ga amsar ta bayyana yanzu. Tasan wannan ba kiran Inna ba ne ba dan tun da tazo kasar nan Inna bata kiranta dan tace ita bata gane wannan lissafin lokutan dan haka sai dai ita Diyam ta rinka kiransu ko kuma in Asma’u tana gida sai ta kira. Har wayar ta katse bata dauka ba a take kuma aka sake kira, Bassam ne ya daga wayar ya ga sunan da yake kira yace mata “ain’t this important? Ba innar ki bace?” Ta karbi wayar ta daga kiran, sai kuma ta saka a handsfree yadda Bassam zaiji abinda ake cewa, maybe abinda zai ji ya taimaka masa wajan fahimtar ta. Tayi sallama, daga daya barin inna tace “Haleema ya karatun? Ya ‘yar’uwar taki?” Diyam tace “lfy lau muke inna ya kuke?” Inna tace “uhmm. Ni ina naga lfy kuwa? Kullum hankalina a tashe, ni dai har yanzu zuciyata bata kwanta da wannan karatun naki a kasar turawa ba Diyam” Diyam ta lumshe idonta tace “Inna ba mun gama wannan maganar ba tun kafin in taho? Inna ke da bakinki kika nuna hakan da nayi shine dai dai, yaushe kuma kika chanza ra’ayinki ” Inna tace “zancen lokacin da na chanza ra’ayi duk ba shine mai muhimmanci ba, abu mai muhimmanci shine na chanja ra’ayin nawa. Ni ban yarda da zamanki a kasar waje ke kadai babu miji ba, dan haka cikin biyu zaki zabi daya, ko dai ki hakura da karatun ki dawo gida ki zauna a gaba na ina kallonki har lokacin da kuka shirya auren naku ko kuma a daura auren yanzu in yaso ya taho kuyi ta zaman tare, tunda shima yana da nasa harkokin a nan kasar”. Diyam ta shafa fuskarta ta taji ta dauki zafi kamar mai zazzabi, ta kalli Bassam taga ita yake kallo shima fuskarsa cike da tambayoyi. Inna tace “kina jina shine kika yi shiru ko?” Diyam tace “Inna bashi wayar muyi magana” Inna tace “wa?” Diyam tace “nasan yana nan a gabanki Inna saboda kalmomin da kika fada ba kalmomin ki bane ba, nasa ne, shi yazo ya gaya miki su, to gwara ni ya gaya min a kunne na inji” Inna tace “au, wato abinda Ingilan ta koya miki kenan? Tun yanzu Diyam?” sai kuma suka ji muryar wani a background, can kuma sai ga muryarsa fes ta fito, very deep and very clear, yace “yes, I am here” Diyam ta hadiye wani abu a makogoronta cikin rarrauniyar murya tace “this is not the agreement, ba haka muka yi alkawari ba” yace “ba haka mukayi alkawari ba and yet you broke the promise” da sauri tace “I didn’t, believe me I didn’t” yace “we will see about that, tomorrow” daga nan suka ji shiru ya kashe wayar. 8