DIYAM CHAPTER 5

DIYAM CHAPTER 5

Ranar da mukayi hutu a ranar Mama ta aiko babban danta yaya Mukhtar wanda kusan sa’an Sadauki ne yazo tare da drivern su ya dauke mu. Lokacin Sadauki bayanan sun tafi gidan yaya Ladi shida Ummah, haka na shirya raina duk babu dadi ga yaya Mukhtar yana tayi min jaraba wai in yi sauri ina bata masa lokaci ni kuma Allah Allah nake su Sadauki su dawo kafin mu tafi dan muyi sallama amma ina, haka ya tasa keyar mu yana ta rankwashi na muka shiga mota ina ta waigen ta inda Sadauki zai billo amma har muka sha kwana babu shi babu alamar sa.+ Tun daga nan fa shikenan na turbune fuska kamar an aiko min da mutuwa. Da muka je gidan ma da kyar na gaishe da Mama, ta harare ni tace “ke kuma me akayi miki kike wannan bacin ran?” Nan take hawaye ya fara zubo min, na saka bayan hannu na ina gogewa nace “ni gidan mu zan koma” yaya Mukhtar ya dungure min kai yace “yi mana shiru anan, shagwababbiya kawai” ai kuwa nan take na bare baki “wayyo Allah na wayyo Sadauki” Mama ta tafa hannu tana salati “wayyo Sadauki? Dama abinda duk Adda take fada gaskiya ne? To zaki ci ubanki ne ke da sadaukin, babu inda zaki je muna nan dake a gidan nan”. Mama yayanta biyar, yaya Mukhtar ne babba sai yaya Abdullahi sannan Rumaisa wadda take sa’a ta kuma a lokacin kusan itace best friend dina bayan Sadauki sannan Muhsina sai Rufaida yar auta kuma sa’ar Asma’u. Tunda muka je gidan, ga dai kayan wasa nan iri iri saboda babansu mai budi ne amma ni sam basa gabana, sai in ringa tunanin ina ma tare da Sadauki muka zo, nasan da zai so video game din su Abdullahi. Mama tayi fadan har ta gaji ta rabu dani tace “shegen taurin kai irin na uba” ni dai nayi tagumi ina kallonta. Da Rumaisa kadai muke dan yin hira, shima kuma duk kusan hirar sa ce dan ita din ma mutuniyarsa ce saboda ni, duk sanda taje gidan mu yana yi mata wasa sosai. Ranar nan muna backyard,su yaya Mukhtar suna ball mu kuma muna kallon su. Nayi tagumi sam hankali na baya tare dasu ban sani ba ashe hawaye ne suke bin kumatu na, kawai sai jin saukar ball nayi a goshina, na hantsila na fada bayan bench din da muke zaune, nan take sai ga jini yana zuba daga hancina. Rumaisa ta zagayo tana yi min sannu, na mike ina kallon yaya Mukhtar da yake yi min dariyar mugunta alamar shine ya buga min ball din yace “yanzu sai kiyi kukan mai dalili ai” murya can kasa nace “Allah ya isa na kuma sai na gayawa Sadauki” ai kuwa a guje ya bini har bayan Mama, ta rike shi tana tambayar abinda ya hada mu ga hancina da jini, ni dai ban tsaya bin ta kansu ba na shige daki na rufe kofa. A daddafe mukayi sati biyu, a ranar da muka cika sati biyu kuwa sai ga Baffa ya sako Sadauki a gaban mota sunzo daukar mu. Ina fita maimakon in tafi gurin Baffa sai na wuce shi na tafi gurin sadauki. Mama ta fito ta gaishe da Baffa tana mita “hutun nasu fa bai kare ba, ni ai ba’a gaya min yau za’azo daukar su ba gashi ko dinkunan su ba’a karbo a gurin tailor ba” Baffa ya daga Asma’u da tazo gurinsa da gudu yace “in an gama dinkin a aika musu dashi gida”. Tun a mota na fara zayyanawa Sadauki duk irin cin zalin da yaya Mukhtar yayi min, tun daga dungemin kan da yayi har zuwa doka min ball da yayi a ka. Baice komai ba sai ya mulmula min goshin kamar yanzu akayi dukan. Bamu kuma tayar da maganar ba ni har na manta ma sai kawai rannan Mama ta aiko yaya Mukhtar ya kawo mana dunkunan da tayi mana ni da Asma’u. Sai da muka gama gwaggadawa muna ta murna ya fito Inna ta biyo bayansa tana bashi sakon godiya zuwa ga Mama, bai yi aune ba sai jin saukar ball yayi a goshinsa, ya hantsila ya fadi a gaban Inna jini yana bin hancinsa. Muka daga kai cike da mamaki sai ga Sadauki yana saukowa daga stairs din saman dakin Baffa, ya tsaya a gaban Mukhtar yace “gobe ma in Diyam ta kara zuwa gidan ku ka sake buga mata ball aka”. Inna tayi kukan kura ta riko shi, amma sai nayi sauri na rike hannunta har ya samu ya zame ya fice da gudu, ai kuwa sai tayo kaina, na ruga sai dakin Baffa na rufe kofa ina leken ta taga. Tayi ta banbamin fada tana debe wa Sadauki albarka “bakin mugu mai bakar zuciya. Allah ya isan sa, idan ya dake ta ina ruwanka? Dan uwanta ne, kai kuma fa? Marar asali” tayi tayi dai babu wanda ya kula ta, ta tashi Mukhtar ta bashi ruwa ya wanke fuskarsa amma sai ya kasa fita wai tsoro yake kar Sadauki ya kuma kamashi a waje. Haka ya koma daki har sai da na fito nace “kayi tafiyarka, babu abinda zaiyi maka ai ya ramamin”. Kuma haka ya fita a tsorace amma Sadauki yana kan mota ko kallonsa baiyi ba. Tun daga ranar ko kallon banza yaya Mukhtar bai kara yi min ba. Yana daga al’adata kullum da daddare dakin Ummah nake zuwa inyi kallo. Inna ta hana amma sai Baffa ya daure min gindi yace “ai homework Sadauki yake koya mata a can din. In kuma kin iya sai ke kike yi mata a daki” Inna bata yi makaranta ba dan haka dole ta hakura. Yes, muna yin homework din in mun gama kuma muyi kallo muyi hira ko Ummah tayi mana tatsuniya. Inna dai ba’a san ranta ba. Wannan yasa ta dage sai data samo mana islamiyyar dare duk kuwa da cewa muna yin ta assuba sannan muyi ta yamma. Baffa yayi magana tace “ai ilimi baya yawa” haka ina ji ina gani kullum nake tafiya islamiyya da daddare. Ni raina baya son islamiyyar nan musamman saboda malaman akwai cin zali kullum zaka gansu suna yawo da doguwar bulala ni kuma babu abinda bana so irin a taba lafiya ta. Ga prefects suma da shegiyar mugunta. Kullum sai Sadauki ya tabbatar naje da wuri saboda kar a dake ni, in lokacin tashi yayi kuma shi zaije ya taho dani saboda kar wani ya tare ni a hanya yaci zalina. Ranar nan sai na kasa bada hadda. Yasaiyadi ya ware mu ya kira monitan aji uku yace ya zane mu. Haka aka zazzabga min dorina a baya na, gurin ya tashi yayi rudu rudu. Tun da aka dake ni nake kuka har aka tashi Sadauki yazo tafiya dani. Ina fita kuwa na gaya masa duk abinda ya faru, yace in nuna masa wanda ya dake nin a nuna masa muka taho gida. Dama ranar laraba ne, ban san yadda akayi ba sai ranar assabar na tafi makaranta wata yar ajinmu ta tare ni a hanya tace “Diyam, wallahi kar ki je makaranta yau, ana nan an ciro bulalai ance yau sai an zane ki, wai yayanki Sadauki ya tare monitan daya dake ki rannan ya zane shi shida kaninsa. Wallahi yasaiyadi uku ne suke jiranki a makaranta” nan take cikina ya duri ruwa, na juya da sauri sai gida, ina shiga na lallaba na wuce dakin Inna na shige dakin Ummah, nayi sa’a itama bata nan tana dakin Baffa sai Sadauki yana kallo. Na dora hannu aka ina kuka na gaya masa abinda ya faru, yace “zauna. Kin daina zuwa islamiyyar daga yau. Ai ba jakarsu bace ke da zasu saka ki a gaba suna duka kamar ganga. Ina nan zaune a kusa dashi har Ummah ta dawo, ita ta dauka har na taso daga islamiyyar ne dan haka tace “Diyam ki tafi gurin innar ki kar tazo tana nemanki”. Washegari ina kallon Sadauki yana ta yan aiyukansa a saman rufin dakin Baffa, da Baffa yayi masa magana sai yace “Baffa zafi ake yi, hawa zanke yi sama ina shan iska da daddare” yana gama wa sai ya kira ni gefe yace min “idan Inna tace ki tafi islamiyya da daddare ki hau sama kiyi kwanciyarki” shikenan nayi graduating daga islamiyyar dare. Kullum da dare in lokacin islamiyya yayi sai in lallaba in hayewa ta sama inyi kwanciya ta akan katifar da Sadauki ya shimfida min. Daga baya sai Sadauki shima ya fara biyo ni, yazo muyi ta hirar mu muna dariya, ko kuma yazo mana da games din Chess, Watt ko ludo muyi tayin kayanmu. Amma duk kanin mu munsan cewa duk wanda ya juri zuwa rafi to kuwa tabbas watarana zai fasa tulunsa. Ina ajin karshe a primary Sadauki shi kuma yana ajin karshe a secondary. Mu nan wai muma mun girma a ajin mu sai ake yin irin soyayyar nan ta yarinta. Kowa da saurayinta, amma ni banda ni. Wannan abin yana kona min rai kullum ina ganin ana rubutowa kawayena love letter su karanta suyi replying amma ni babu wanda yake rubutomin.+ Akwai seat mate dina lubabatu kuma itace headgirl, ita head boy din mu yake so, kuma dan rainin hankali ni yake bawa wasika in bata wai kunyarta yake jiba zai iya bata ba, ita ma kuma inta rubuta reply ni take bawa in bashi, su basu san haushi suke bani ba gabadayan su. Ranar nan, ina koro yara aji an gama breakfast sai muka hadu dashi. Muka gaisa yana ta sosa keya ni kuma na fahimci me yake so na bata rai nace “kar ma ka tambaye ni, ni bansan inda take ba” yace “ni fa ba cewa nayi ina neman lubabatu ba, yanzu ba zamu gaisa ba sai kinyi tunanin wani abu?” Nayi gaba nace “oho dai, kai kasani” ya biyoni “dan Allah Halima kina ji ba? Ki ce mata bata bani amsar jiya ba fa” nayi kamar ban jishi ba nayi tafiyata. Bayan naje na zauna a aji na ganta tana ta faman zanen flower a jikin plain sheet, nayi tsaki nace “rashin aikin yi, wai soyayya? Yar karama dake har kin ita rubuta wa saurayi wasika. Allah ya sawake, kuma in baki daina ba sai naje gidan ku na fada” ta harare ni tace “Allah yaso ma dai ni wasika kawai nake rubutawa saurayi na, ke kuma fa? Da kullum kuke yawo ke da naki saurayin?” Nayi galala ina kallonta ina tunanin waye take nufin saurayi na, sai kuma nayi dariya nace “wai Sadauki kike nufi? Bafa saurayi na bane ba, yayana ne to” ta harare ni tace “in yayan ki ne to ya akayi ke fara shi baki? Kuma ai munsan ba babarku daya ba kuma baban ku ma ba daya ba” naji haushin maganar ta na dauki jakata na bar mata seat din na koma wani. Amma kuma sai maganar ta ta tsaya min a raina, wai Sadauki ne saurayina. Ina nan zaune har aka tashi. Ana ta zuwa daukan dalibai sai ga wata sa’adatu yar A ta leko ta window tace da karfi “Halima Usman ki fito ga wannan saurayin naki yana nemanki” Lubabatu ta juyo tana yi min dariya ni kuma na kara kulewa, na dauki jakata na fita. Kamar hadin baki sai gashi washegari muka je gidan Mama tare da Inna, muna ta harkokin mu dasu Rumaisa su Inna kuma suna hira, sai naji kamar sun ambaci sunan Sadauki sai na saurara ina jin abinda suke cewa. Inna tace “mtsw, Hafsa ba zaki gane abinda nake nufi ba, ni nake zaune da yaran nan ni kuma nake ganin abinda nake gani wallahi. Ina jin tsoro Hafsa. Bana son abinda nake gudu ya kasance” Mama tace “wai gani kike in sun girma zai iya cewa yana son aurenta?” Inna tace “sosai ma kuwa, ya riga ya shanye ta kamar yadda na fada miki, kuma alamu sun riga sun gama nunawa. Tsoro na Allah tsoro na kar ya furta abinda nake tunani saboda kinsan halin baban su, wallahi indai yaron nan yace yana son yarinyar nan bashi ita zaiyi” Mama tace “chafdi. Kice tsugunne bata kare ba kenan. Allah yaji kan inno, da tana raye wallahi da tuni ta fatattaki yaron nan daga gidan nan. Ni babban tashin hankali na shine rashin sanin asalin sa. Ga tambarin da uwarsa take dashi. Yanzu menene abinyi?” Mama tace “ni so nake kije ki kai maganar nan gidan Alhaji Babba, shi kadai ne zaiyi min maganin fitinar nan wallahi” Mama tace “wanne Alhaji Babba? Alhaji Babba ba zai iya yi miki maganin komai ba saboda kinsan halin mijinki ba lallai ne in Alhaji Babba ya gaya masa magana ya dauka ba. Ke dai addu’a zamuyi tayi, idan har Allah ya rubuta aure a tsakanin su to Allah ya daidaita lamarin” Inna tayi saurin girgiza kanta tace “babu, insha Allah babu, da wanne zanji? So kike zuciya ta ta buga?” Mama tace “ni Adda ba sanin yaron nan nayi sosai ba, gaya min, bayan rashin sanin ubansa da ba’ayi ba yana da wani aibun ne?” Inna ta bude bakinta ta rufe, ta kasa tuna wani laifi da Sadauki yayi mata wanda zata bayar da misali da shi. Duk a cikin hirar su Inna kalma biyu ce ta tsaya min a raina. “So” da kuma “Sadauki” nayi ta kuya kalmomin a raina ina tunanin ma’anar su. Wai soyayya muke yi ni da Sadauki? Sai kawai naji wani excitement ya lullube ni. I can’t wait in bawa Sadauki wannan labarin. Magrib tana yi inna ta ce mu nemo hijaban mu da takalman mu mu tafi gida “kunga yau na jawo muku kunyi fashin makarantar yamma, gwara mu tafi da wuri kar Diyam ta rasa ta daren itama” sannan ta bawa Mama labarin dalilin da yasa ta saka ni a islamiyyar dare. Mama tana ta dariya muka taho. Muna zuwa gida sallar isha nayi kawai na saka hijab dina na dauki jakar islamiyya ta, Inna ta bani kudi wai ko zanga yara suna siyan wani abu. Nayi mata sallama na fita amma ina fita sai nayi hanyar kofa kamar na tafi sai nacire takalmana na dawo da baya na zagaya ta kofar dakin Baffa na hare saman bene. Ina zuwa na zubar da takalma na a gefe na cire hijab dina na ninke dan kar yayi squeezing na kwanta rigingine na rufe idona ina jin dadin iskar da take kadawa a gurin. Na jima a haka ni ba bacci ba ba kuma ido biyu ba. Sai naji a jikina kamar ana kallona. Nayi murmushi na bude idona a hankali na sauke su a cikin na Sadauki daya zauna ya saka ni a gaba ya zuba tagumi yana kallona cikin hasken farin wata. Yayi murmushin daya bayyana kyawawan jerarrun hakoransa Yace “wato kinji dadin iska ko? Shine har da bacci?” Nayi dariya kawai, nace masa “ya garage din yau, mota nawa ka gyara yau?” Ya bata rai yace “daya” nace “kawai?” Yace “kinsan irin lalacewar da motar nan tayi kuwa?” Nan ya fara bani labarin irin parts na motar da suka lalace da irin yadda ya gyara su, ni kuma nayi shiru ina sauraronsa duk kuwa da cewa ba ganewa nake yi ba, sai daya gama sannan yace “to ya gidan Maman” nace “lafiya lau” sai kuma na bata rai nace “ina sweet dina?” Yayi murmushi ya saka hannu a aljihu ya dauko alawar splash guda biyu ya miko min, na karba nayi masa godiya sai kuma na bare daya na mika masa dayar kuma na jefa a baki. Sai ya zagaya bayan pillow na shima ya kwanta rigingine ya dora kansa akan pillown da nake kwance akai, sai ya kasance shi a kasa yake ba’a kan katifar da nake ba. Yayi shiru kamar bacci yakeyi amma ni nasan ba bacci yake yi ba, nasan kallon sky yake yi kamar yadda nima nakeyi. Can kuma sai naji yace “Diyam? Yau sky tayi kyau sosai” nayi murmushi ina kallon yadda wata ya cika very full, ga stars ba adadi sun cika sararin samaniya. Sai na juya nayi rub da ciki na tallafe fuskata da hannayena, wannan yasa dankwali na ya zame saboda santsin gashi, gashin ya zubo a fuskar Sadauki, ya saka hannu ya tattare su gefe yana kallona, direct nace masa “Sadauki wai kai saurayi na ne?” Sai ya kware da alawar da yake sha, ya mike zaune yana tari yana bubbuga kirjinsa sannan ya kalle ni da mamaki yace “what?” Na daga kafada nace “nima haka naji ana cewa” ya kwanta rub da ciki irin yadda nayi yayi tagumi da hannayen sa yana kallona fuskarsa cike da mamaki yace “a ina kika ji ana fada?” Na bashi labarin abinda ya faru a school, ya ja hancina har yanzu da dariya a fuskarsa yace “ke kuma me kika ce? Are you my girlfriend?” Na juya na koma rigingine nace “oho” yace “oho? Baki sani ba?” Nace “eh, to kaga ai kai baka rubuta min letter da kalaman soyayya” yayi dariya sai kuma ya rufe bakin sa dan kar ajiyo dariyar tasa daga waje yace “kalaman soyayya Diyam? Naga ta kaina ni Aliyu, Diyam a ina kika san kalaman soyayya?” Nace “a makaranta mana. Ka ga lubabatu headgirl din mu to head boy ne saurayinta, kuma kullum sai ya rubuto mata letter ya bani na bata” yace “ohh, wato abinda kuke yi kenan ko? Head boy saurayin headgirl, ke kuma assistant head girl ke ce budurwar assistant head boy ko?” Nace “lah, ni me zanyi da wannan kazamin?” Ya koma ya kwanta, sannan yace “to ni yanzu me zanyi kenan in ina so in zama saurayinki?” Na daga kafada nace “wasika zaka rubuto min” yace “to ni ban iya ba, ki koya min” nace “kaga, plain sheet zaka samu, sai kayi zanen flowers da pencil, sai kazo ka zana heart da arrow yayi crossing heart din ka rubuta sunan ka a sama nawa a kasa, sai ka rubuta I love You Diyam a saman takardar, a ciki kuma sai ka rubuta min kalaman soyayya shikenan” yayi murmushi mai sauti yace “to ni ai ban iya kalaman soyayyar ba” na bata rai nace “ni ma ban iya ba ai” muka yi shiru gaba-daya muna kallon sky. Can sai naji yace “Diyam. Look at the stars, kinga yawansu ko? To zabi daya wadda kike ganin a idonki kamar tafi sauran dukka haske. Concentrate on it kiyi ta kallonta ita kadai ki manta da sauran, ki saka a ranki kamar babu sauran kowanne star a sky din nan sai wannan wadda kike kallo. A hankali zaki ga sauran sunyi disappearing, zaki ga ba kya ganin komai asararin samaniya sai wannan star din guda daya” nayi exactly yadda yace, sai naga komai ya bace a idona sai star guda daya, yace “do you get it Diyam?” Na gyada kaina da sauri ina murmushi, yace “to haka nake ganin ki a idona, ke kadai kike haske a duniya ta, duk sauran mutane da duhu nake ganin su. You are the only star in my sky” nayi murmushi na maimaita “You Are the only star in my sky” yace “that’s right. Ki rike wannan a ranki, ko mai tsanani, komai shudewar zamani, ke kadai ke zaki kasance a raina har gaban abadan” nayi dariya nace “wallahi ka iya ashe. Yayi dadi sosai” yace “to shikenan na zama saurayinki?” Sai kawai naji wata kunya ta lullube ni, nayi sauri na rufe idona da hannayena guda biyu, yace “au wai kunyata kike ji kuma? Bude idon ki gani” na makale kafada, yace “kinga wani abu” nace “naki wayon” sai yakama hannu na da niyyar bude fuskar ni kuma sai na tashi da gudu na fara sauka daga stairs, shaf na manta da cewa buya nayi, na manta cewa gudun makaranta nayi, sai da naji muryarsa a bayana yace “Diyam!!, Come back!!” A daidai lokacin ne kuma idona ya fada cikin na Inna a tsaye a tsakar gida da tray din tea a hannunta. Muka tsaya muna kallon kallo, cike da mamaki tace “Diyam?” Adaidai lokacin da Sadauki yayi appearing a bayana. Ta saki trayn hannunta ya fadi cike da karar data jawo hankalin Baffa da Ummah suka fito a tare kowa daga dakinsa.2 Cikin hanzari Inna ta juya ta koma daki, baya yi second uku ba sai gata ta fito da sharfadediyar dorinar da ta siyo ta ajiye danyi min barazana a duk lokacin dana ki jin maganarta. Da sauri na zagaya na koma bayan Sadauki, na kusa fuskata a bayansa zuciya ta tana aiyana min cewa yau kwanana ya kare, na tabbatar da cewa yana iya jin bugun zuciya ta a bayansa. Cikin tsananin zafin rai Inna ta karaso inda muke tsaye amma sai Sadauki ya sake tura ni baya ya hadani da jikin bango shi kuma ya tokare ni da jikinsa. Nan Inna ta fara dukansa da iyakacin karfinta da wannan dorinar ta hannunta amma ko gezau baiyi ba, shi kawai kokarinsa shine ya kare duk dukan kar wani ya sameni.+ Sai da dorinar hannunta ta kakkarye sannan ta yar da ita ta shiga kitchen ta dauko muciyar tuwo, a lokacin ne Baffa yayi sauri ya rike hannunta, sai kuma ta saka kuka tadora fuskarta a kafadar Baffa. Sai kuma yaja hannunta a hankali ya shige da ita zuwa dakinta. Umma ce ta taho itama zuwa inda muke tsaye ta sauke kyakykyawan mari a kuncin Sadauki, kafin ya dago kai ta kuma marin daya side din sannan kuma cikin sassarfa ta wuce dakinta, Sadauki ya bita da sauri yana kiran sunanta “Ummah ta, Ummah ta. Ummah dan Allah kiyi hakuri”. Sai ya kasance an barni ni kadai a tsakar gidan. Na durkushe a gurin ina jin kafafuwana suna rawa, sai kuma na dafa bango na mike da niyyar komawa sama in dauko kayana, a lokacin Baffa ya fito daga dakin Inna, nayi saurin komawa na dunkule a guri daya ina cewa “wayyo Allah Baffa kayi hakuri. Na tuba, bazan sake kin zuwa islamiyya ba” yazo ya tsaya a gaba na ya miko min hannunsa yace “zo uwata” na sake ja da baya, ya kama hannuna yace “zo Diyam, ba dukan ki zanyi ba, magana zamuyi kawai” na mike a darare amma sai naga yayi min murmushi.1 Dakin sa ya jani muka tafi, ya zaunar dani akan kujera sannan shima ya zauna a kusa dani yana kallon yadda jikina yake karkarwa yace “share hawayenki ki daina kuka, ni ba dukanki zanyi ba kuma bazan bari innar ki ta dake ki ba in dai har kika gaya min gaskiya. In kuwa kika yi min karya, zan zaneki sannan bazan hana innar ki dukan ki ba kuma sauran ke da Allah, kinsan baya son mai karya ballantana mai yiwa iyayensa karya” na gyada kai ina jin dadi a raina tunda yace ba za’a dake ni ba sai in nayi karya, ni kuwa yadda nake ji da jikin nan nawa me zai saka inyi karya? Yace “me yasa innarki ta tura ki islamiyya kika ki zuwa kika buya?” Na share hawayen tunowa da laifi na na islamiyya sannan nace “dukana za’ayi in naje” yace “me kika yi zasu dake ki?” Na bashi labarin abinda Sadauki yayiwa monitan aji uku. Ya jinjina kai yace “to me yasa da akayi haka baki zo kin gaya min ko kumako gayawa innarki ta gaya min in yaso ni sai inje makarantar in basu hakuri shi kuma Sadauki inyi masa fada ba?” Na sunkuyar da kaina ina wasa da hannuna ina tambayar kaina me yasa? Ni da abin ya faru ma it never occurred to me cewa in gaya wa inna, in na gaya mata gani nake fada zata yi min ko kuma ma ta dake ni, besides, bana so ayi wa Sadauki fada akan me yasa ya daki wancan yaron. Yace “to Sadauki ne yace kike buya a sama?” Na gyada kaina, yace “kuma sai shima yake zuwa kuke zama tare a saman?” Na kuma cewa “eh” yace “to me kuke yi a saman?” Nace “games muke yi” yace “wanne irin game?” Nace “ko chess ko lido ko whot ko kuma….” Sai kuma nayi shiru, Yace “ko kuma me? Kinsan dai kinyi min alkawarin zaki gaya min gaskiya ko?” Nace “ko kuma muyi ta labari” yace “wanne irin labari?” Nace “ko ya bani labarin gareji ko makarantar su nima sai in bashi labarin makarantar mu da kawayena” yayi shiru yana jinjina kai sannan yace “to yanzu ina dankalinki da hijab dinki?” Na nuna sama da hannuna, yace “ya akayi kika cire su?” Nace “hijabin cirewa nayi dan kar yayi squeezing, dankwalin kuma bansan ya zame ba” yace “to me yasa kika sauko da gudu dazu, fada kukayi?” Na girgiza kaina sai kuma nayi murmushi ina tuno kalaman sadauki, Baffa ya sake maimaita tambayarsa yana nazarina, nace “na fada mukayi ba, kunyarsa nake ji shine na rufe idona shi kuma yace sai na bude masa yagani” Baffa ya dan bata fuska yace “me yasa kike jin kunyarsa?” Na dan rufe fuskata alamar kunya Nace “cewa yayi I am the only star in his sky” Baffa ya bude baki da mamaki yace “shi Sadaukin?” Na gyada kaina ina murmushi. Ya jima yana kallona sannan yace “to sai wanne wasan kuma kukeyi a saman?” Innocently na daga hannuna nace “shikenan” ya kuma yin shiru yana kallon na, sai kuma ya gyada kai yace “to yanzu kingakinyi wa innarki dani baffan ki laifi, an tura ki islamiyya kinki zuwa, me zaki ce mana?” Na durkusa a gabansa nace “Baffa kayi hakuri” ya kama hannuna yace “na hakura, saura Inna”.2 A zaune muka sameta, idonta akan tv amma daga gani ba kallon take yi ba, hallonta daya akan Asma’u tana shafa kanta a hankali ita kuma tana bacci. Na rakube daga bakin kofa ina kallonta, Baffa yaje ya zauna akan kujerar da take kusa da ita sannan ya kirawo ni da hannu yace “me kika cewa innarki?” Na durkusa nace “Inna kiyi hakuri, na tuba, bazan kara buya ba inkin kuma tura ni islamiyya” ta watsa min harara tace “kuma ba zaki kara kula Sadauki ba?” Na sunkuyar da kaina nayi shiru. Baffa yace “tashi ki tafi dakin ku ki kwanta” na tashi babu musu na shiga na kwanta, sai kawai naji ina tunanin koya Sadauki yake ji a jikinsa? Dan nasan ba karamin dokuwa yayi a gurin Inna ba. A palo bayan na wuce Inna tace “shikenan? Shikenan maganar nan ta wuce? Shikenan ba zaka dauki mataki akan yaron nan da yake neman ya lalata maka yarinya ba?” Baffa yace “nayi magana da Diyam, abinda kike tunani ba haka bane ba. Tabbas shi ya hanata zuwa makaranta saboda wai ance za’a dake ta in taje akan laifin da shine ya aikata ba ita ba. Tabbas Sadauki yayi laifi kuma zan zauna inyi magana dashi kamar yadda nayi da Diyam. Zan fahimci inda yake da kuskure in nusar dashi, inda kuma yayi laifi inyi masa fada” hawaye ya zubo daga idon inna tace “shikenan abinda zakayi masa?” Yace “to gaya min me kike so inyi masa?” Tace “ka mayar dashi gidan ubansa tun kafin yalalata mana yarinya ya cuce mu” ya girgiza kansa yace “Sadauki ba zai lalata Diyam ba, in ma hakan ta faru to mune zamu kasance masu laifi fiye dashi. Yanzu in tambayeki? Me yasa da Diyam ta gudo daga makaranta batazo gurinki a matsayin ki na mahaifiyarta ba sai ta tafi gurin Sadauki?” Da sauri inna tace”saboda ya cinye kurwarta bata ganin kan kowa da gashi sai nashi” Baffa ya girgiza kai yace “saboda a gurinsa take ganin zata samu maslaha in ta zo gurinki problem zata karawa kanta. Yarinyar nan dududu shekarunta goma da watanni a duniya, yanzu ne ya kamata ace kin kara jawo ta jikin ki kin koyar da ita lamurran duniya, amma me? Diyam tsoron ki take ji, komai tayi gani takeyi kamar laifi zatayi a gurinki. Yanzu da ace ma lalata tan yakeyi kamar yadda kika yi tunani ta yaya zaki sani? Kince ba kya son taje dakin Zainab, amma ke kin gaza yi mata abinda Zainab din take yi mata har take nacin zuwa dakin nata, wasa da dariya, kulawa, nuna soyayya, wannan shine kadai abinda Diyam take bukata daga gurinki a wannan lokacin. Ke kika haife ta, dan haka in kika sakar mata fuska zakiyi mamakin yadda zata sake dake itama”. Inna ta kalleshi tace “dama na sani, nasan duk yadda zakayi ka juya maganar nan ta koma kamar laifina ce sai kayi, ni kumana riga na sani, nasan cewa kafi son Sadauki akan Diyam, kafi son agola akan yar data fito daga jikin ka, kamar yadda ka fi son zainabu akai na ni uwargidan ka kuma yar uwarka ta jin, kuma uwar yayanka na gaskiyai” Baffa ya mike tsaye yana girgiza kai yace “Diyam ni na haifeta, Sadauki kuma nina rike shi tun yana cikin tsumman sa dan haka dukkan su yaya nane, babu banbanci. Maganar tsakanin ki da Zainab kuma ke kike ganin haka, ke kika saka haka a ranki. Amma ina son ki bude idonki ki kalli gabanki sosai zaki fahimci ke kadai kike fadanki babu wanda yake amsa miki” Har ya kai bakin kofa tace “ina neman alfarma guda daya a gurinka” ya juyo amma bai ce komai ba, tace “ina son idan Diyam ta kammala primary a kaita boarding school” yace “Allah ya nuna mana lokacin”.2

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *