DOCTOR EYSHA CHAPTER 1 BY FANAN_A.A

DOCTOR EYSHA CHAPTER 1 BY FANAN_A.A

Www.bankinhausanovels.com.ng 

( *BOOK 1*)

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI, INA KARA YIWA ALLAH GODIYA DAYA BANI IKON WALLAFA WANNAN LITTAFIN MAI SUNA *DOCTOR EYSHA* WANNAN LITTAFIN KIRKIRARRAN LABARI NE DUK WACCA LABARIN TA KO HALI YAZO DAYA TOHM INA BATA HAKURI SABODA KATARI NE AKAYI. 

*ZANYI AMFANI DA WANNAN DAMAR DOMIN MIKA GAISUWA TA GA YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI ❤️*

*PAGE* 0️⃣1️⃣➡️0️⃣2️⃣

Taron mutane ne a wajen sosai dalilin hadarin daya auko a wajen, Duk yawancin mutanen wajen suna cikin wani yanayi domin hadarin da suka tsinci kansu, ga kuma Taron ambulance din dake tare da likitoci, domin bada taimakon gagggawa. ‘

kutsawa nayi Dan na dauko maku labarin abinda ke faruwa Dan nasanku da son Labari. 

Ko wani likita ‘ko’kari yake yaga ya shawu kan patient din dake gaban sa, wasu kuma ana daukar su ana saka wa a ambulance domin a samu damar kai su asibiti Dan Kuwa mutanen da hatsaren ya afka dasu suna da yawan gaske, 

Wata motar asibiti ce ta iso itama, wani wawan burki suka ja domin kowanne a cikin likitocin burin sa ya fito, likitoci biyu ne suka fito ko Wanne na ‘ko’karin ganin ya nafi cikin majinyatan domin basu taimakon gagggawa, 

“Masha Allah” na fada saboda wata kyakkyawar surar danaci karo da ita, 

Kyawun ta ya isa Dan Kuwa babu babu mutumin da zai ganta koda Kuwa yar uwar ta mace ce bata yaba da kyaun surar taba, *DOCTOR EYSHA* kenan bara na barku tare da ta ida Baku labarin. 

Saukowata daga mota kenan cikin hanzari na fita domin yadda nake jin ihun mutane yana Tashi wasu iyayen sun rasu sai yaran su suna ta kuka, Ni nama rasa ina zan dusa Dan Kuwa a wannan wajen Kowa na bukatar taimako, nishin Dana ji ne taga baya na ya saka Ni saurin juyawa, 

” taimako Dan Allah wani ya taimaka man”

Muryar yarinyar da bata wuce shekara biyar Naji daga baya na, sauri nayi naje wajen domin Kuwa nasan dole ne tana bukatar taimakon, 

Cikin sa’a Kuwa na same ta cikin wata mota da glass din motar ke rufe, babu yadda na iya saidai kawai na fasa glass din Dan yarinyar tana cikin mawuyacin hali, 

“ina lillahi wa ina ilaihir rajuun ” na shiga furtawa saboda Tashin hankalin da na gani, yarinya ce kwance cikin jin dalilin karfen daya shiga tsakiyar kirjin ta, sauri nayi na fiddo ta domin tana cikin wani hali nayi saurin ajjiye ta a wani kebabben waje saboda cunkuson mutane da yake a wajen bazai bani damar saka ta a ambulance ba. 

” Nagode sosai yar uwa ta saboda mutane Basa son taimako na duk likitan daya zo zai dubani mutane Basa barin sa ya duba Ni acewar su tunda iyaye nane suka ja wu wannan hadarin saidai na mutu, yar uwa Kiyi mani alkawarin baza ki barni ba na mutu saboda ina jin zafi sosai ” yarinyar ta fada. 

Rike hannun ta nayi sannan na sakar mata murmushi ina cewa” nayi maki alkawarin zanyi iya bakin ‘ko’kari na wajen ganin Kin samu lafia inshallahu ” na fada ina ‘kokarin nayi wani Abu domin Ceto ran wannan karamar yarinyar wacca bata San komai ba. 

” ya kamata ace mun tafi da ita domin Kuwa tana bukatar jini sosai kuma muna da bukatar mata surgery domin Ceto rayuwar ta “. 

Mutumin dayake baya nane ya fad’i wannan maganar, juyawa nayi domin ko a mafarki nasan mai wannan muryar Dan Kuwa nasan ba Kuwa bane illa 

doctor Aryan. 

” Doctor Aryan kaine Anan ya akayi kazo nan bayan kuma anyi suspending dinka? “. 

” Kiyi hakuri yanzu ba lokacin wannan maganar bace domin Kuwa rayuwar yarinyar nan tana cikin hatsari ” ya fada yana ‘ko’karin daukar ta, yayi gaba ina biye dashi. 

Hankalin mutanen wajen ne ya fara Dawowa kan mu cikin harguwa suka fara cewa” Babu wanda zai taimaki wannan yarinyar saboda iyayen ta ne suka saka Kuwa a cikin wannan halin, dole ku kyale ta Anan ta mutu “. 

‘ko’kari nake naga na shiga da ita ambulance Amma mutane sun hana sai ihu suke suna nuna baza’a taimaki wannan yarinyar ba, da kokarin jami’an tsaro na muka samu damar saka ta ambulance directly *KASHMIR* Nifa domin bata taimakon gagggawa. 

Muna isa asibitin Ta ‘barauniyar hanya muka shiga da ita saboda dalilin mutanen da sukayi curko curko a wajen, 

Direct *OT* na nufa da ita domin gabatar da surgery din ta tare da taimakon doctor Aryan, cikin rashin sa’a wata mata ta hango mu zamu wuce mu shige hospital din, 

Babu bata lokaci ta bayyana ma sauran mutanen abunda ta gani a, babu bata lokaci Kuwa wajen ya hargitse da hayaniya, nan take Yan jarida suka shigo wajen suka sha gaban mu ta yadda bamu da yadda zamu tsere masu, ai Kuwa babu bata lokaci daya daga cikin su ta fara Magana 

“mun Samu rahoton cewa Anan asibitin ana so a taimaka wa diyar mutanen da suka hada hatsari a airport road, *DOCTOR EYSHA* me zaki iya cewa a kan wannan lamarin. 

Shuru nayi ina cira idanu domin Kuwa Ni yanzu banda abinda zance Dan sai yanzu na lura Doctor Aryan ya bar wajen, Shuru nayi domin bani da abinda zan iya cewa. 

Kamar a mafarki Naji muryar doctor kaseem yana cewa ” Aikin likita shine ya ceci ran al’umma bawai suyi sakaci dashi ba, ina tunanin indai mutane zasu dugara da likita har su Basa yadda akan zai iya Ceton rayuwa tohm ya kamata ace Likita ya zage damtse Dan ganin ya taimaki rayuwar al’umma, iyayen tane sukayi laifi ba ita ba Dan haka babu inda zata ge sai munyi mata aiki an Ceto rayuwata ” takai karshen zancen dai dai lokacin da ya iso inda nake. 

Tafi mutanen wajen suka shiga yi masa Dan Kuwa har ga Allah zancen sa ya shiga kunnen su. 

” ki taho mu tafi saboda bamu da lokaci mai yawa “. 

Babu musu na biyo sa Amma kuma abinda ya bani mamaki dashi shine Kwata Kwata ba hanyar *OT* muka nufa ba……….. 

*FATEEMA A. A🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *