DR BOBBY CHAPTER 3 BY AISHA RANO

Kai tsaye office dinshi ya wuce yanata faman tsaki domin har cikin zuciyarshi wani tukuki yakeji..a zahirin gaskia ba iya mgnr da Nur ya fada ne ya bata ranshi kadai ba hadda wnn yarinyar Lamido take ko Gidado…last time daya ganta a clinic sam ba wani tsayawa yayi ya kalleta ba amma dazu despite baya so saida ya kare mata kallo tsaf..kuma a iya kallon da yayi mata ya tabbatar da ta hada jini da fulani…shi sai yanxu ma ya tuna Nur ya taba fada mishi cewar ‘yar Gombe ce…lokaci daya yaji gaba daya tsanar yarinyar ya samu matsuguni a zuciyarshi…da yasan bafulatana ce kuma ‘yar Gombe da babu dalilinda zaisa ya dauki hannunshi mai daraja yayi mata allura dashi sbd gaba daya Fulani basuyi deserving help ko kuma pity dinshi ba a rayuwa…they are all not worthy of his kindness especially wanda suka fito daga Gombe ya tsanesu..ya tsanesu fiyeda komai..baisan meyasa ganin yarinyar kadai ya dawo mishi da abubuwan da suka faru tsakaninsu da dangin mahaifinsu ba…baisan meyasa tun farkon ganinshi da ita baiyi realising cewa bafulatana bace kuma ‘yar Gombe ba har saida yayi mata allura…ya dafe kanshi yasan har abada da ciwon wnn abun zai mutu…yanada riko a rayuwa shiyasa har yanxun ya kasa mance abubuwan da suka faru tsakaninsu da ‘yan uwan daddy kimanin shekaru biyar da suka wuce…sam baiji dadin taimakon da yayi mata ba kuma da ace yasan ‘yan Gombe zasuzo su cika mashi makaranta da baiyi attempting bude makarantan bama at the first place..haka kuma da yanada damar da zaiyi banning ‘yan Gombe and all Fulani from studying at his college da yayi hakan saidai it can never be possible…wnn yarinyan kuwa ji yake kaman yaje ya korata this instant ta bar mashi college dinshi…duk zuciyarshi ta cunkushe ga kuma takaicin da Nuruddeen ya sake dirka mashi duk sun taru suna barazanar fasa mashi zuciya..a fili ya furta”the fool..har wani tunani yake ni inje in zama lecturer dinsu..what nonsense!..”ya karasa mgnr yana dukan table dake gabanshi…haka dai ya karasa yini ranan bai tsinana uwar komi ba a office din…one nayi ya shiga toilet dinshi yayo alwala snn ya fita dan zuwa sallahn jumu’a…driver ya bude mishi kofa ya shiga shima ya zagaya ya shiga saidai kafin ya tayar da motar Nur ya fado cikinta da wani irin sauri kaman wanda aka biyoshi…Bobby bai ce mishi komai sai dan tsaki daya saki tareda kawar da kanshi gefe..shi kuma Nur ya saki hadadden murmushi yana kallonshi yace”i don’t mind having a drive with my friend”…da sauri Bobby ya juyo yana kallonshi shima fuska tamke yace”well am not going for a drive as you can see..am going for prayer.. jumu’at prayer sbd haka get out of my car immediately”..kara sakin wani smile Nur yayi yana wani shafa gemunshi yace”i still don’t mind going for prayer with my friend and we better get going idan bakaso muyi latti”..tsaki Bobby ya saki yana sakan mishi wani harara murya can kasa yanda driver bazai jiba yace”Fool”..da sauri Nur yace”godia nake my friend..i love you too”..watsa mishi harara kawai Bobby yayi tareda dauke kanshi dan yaga alama idan yaci gabada biyema Nur zai maidashi mahaukaci ne a gaban driver dinshi…shi kuwa Nuru murmushin cin nasara ya kara saki cikin ranshi yace”zakaga rashin mutunchi ai..badai Lamido kayima wulakanci ba dazun?..”tayar da motar driver yayi suka fita daga makarantar…koda suka isa masallacin saida Nur ya sake dirka mashi wani abun haushin..kallon suit dake jikinshi yayi sai ya dan saki tsaki yana girgiza kai yace”yau Friday dinma mutum bazai sa manyan kaya ba..some people need to grow up wlh..basu ajiye komai ba sai shegen zafin rai”…ko kallon inda yake Bobby baiyi ba amma ya shaka iya shaka.😂

Karfe biyu daidai suka baro masallaci…Bobby ba tareda ya dubi Nur dake zaune gefenshi ba yace”a ina zamuyi dropping dinka kasan ba komawa college zanyi ba ni..am going home”..da fara’a Nuru yace”don’t worry muje gidan..dama mun kwana biyu bamu gaisa da Mummy ba”..Bobby bai sake yi mishi mgn ba har suka karasa gida…driver na gama parking ko jira ya fito ya bude mishi motan baiyi ba ya bude ya fita abunshi..shi kuma ya dauko briefcase dinshi yabishi a baya…shima Nur fitowa yayi zuwa cikin gidan yana daria kasa kasa gamida girgiza kai dan masifar Bobby daria yake bashi wlh…babu kowa central palor as usual suka wuce parlon Mummy…tana zaune da wasu yammata guda biyu da kallo daya Bobby yayi musu ya wani sake tamke fuska…a hankali ya karasa kusada Mummy ya zauna yanata wani basarwa cikin igbo yace”mummy sannu da gida”…tana murmushi  tace”sannu Bobby ya aiki?..”can kasa kasa yace”fine..”Mummy ta maida dubanta ga Nuruddeen daya karaso shima ya zauna kusada Bobby tace”yau an tuna damu knn Nuru”..murmushi yake ya shiga shafa kanshi yace”wlh aiki ne kemin yawa Mummy…duk Bobby ya gama sakar min komai ko taimaka min bayayi”..girgiza kai kawai Mummy tayi tace”to ya aikin?..yasu Mom dinka?..”yace”duk suna lafia Mummy..ina auta?..”tace”auta bai dade da fita ba wai zasuje dubiyan wani abokinsu”..gyada kai Nur yayi alaman gamsuwa…sai yanxu yammatan dake zaune suka samu daman gaishesu…Nur kadai ne ya amsa Bobby kam saima sake tamke fuska da yayi…kallonshi Mummy tayi tace”Bobby bakaga Rayhan bane?..”fuskan nan ba sarari yace”na ganta Mummy”..tace”kuma baka iya amsa gaisuwa ba koh?..”a karkace ya juya yana kallon inda suke murya a dakile yace”lafia lau”..daga haka ya mike ya kama hanyar flat dinshi Mummy ta bishi da kallo kawai tana girgiza kai..cikin ranta take cewa”Ya Allah ka shiryamin Bobby”…shima Nur mikewa yayi yana duban Mummy yace”Mummy bari in shiga ciki”..kai kawai ta iya daga mishi dan Bobby ba karamin sanyayar mata da jiki yayi ba..ya juya kenan zai tafi aunty sumy da Miemie suka shigo parlon suma…dakatawa yayi da tafiyar tareda wara idanu sosai akan Miemie yace”hey pretty!..”murmushi ta saki itama ta karasa kusa dashi tace”Uncle Nur good evening”yace”evening pretty how are you..how was school?..”tace”Alhamdulillah”…juyawa yayi ga aunty sumy da har ta karasa kusa dasu Mummy ya wani daga hannunshi alamar salute yace”Allah ya taimaki babbar yaya..barka da rana”..aunty sumy na daria tace”barka dai Nur kwana biyu..ya aiki”..yace”normal normal aunty ya naki aikin?..”dan tabe baki tayi kafin tace” babu dadi wlh..duk Bobby ya sakar min komai ni kadai”..daria ya saki yace”nima haka nake fama dashi aunty..saidai hakuri kawai”..yana rufe baki Mummy tace”to ka wuce ka tafi Miemie zata kawo maku abinci yanxun nan”..bai sake mgn ba kuwa ya kama hanyar flat din Bobby…itama aunty sumy mikewa tayi bayan sun gaisa da baqin Mummy ta kama hanyar nata flat din itama…Miemie kuma Mummy tace taje ta cire uniform sai ta kai musu abinci…ba musu ta juya itama zuwa flat din mamanta.

Yana shiga ya fada bathroom ko kayan jikinshi ma sai a bathroom din ya ciresu…ruwan sanyi sosai ya sakar ma kanshi wai ko zai samu yaje inda yake son yaje wala’alla ya samu saukin abunda yakeji amma inaa…shi abubuwan ma sun mishi yawa baisan da wanne ya kamata yaji ba..na farko waccan bafulatanar yarinyar da yakejin ya tsaneta sama da komai a dunia…sai kuma Nur da kalan iskancin da yayi koma yake kan yi mishi..yanxu kuma ga wnn jarababbiyar yarinyar itama tazo zata kara mashi akan wanda yake ciki already…shi ya rasa wnn masifa da bazata hakura ta kyaleshi ba tunda tasan ba sonta yakeyi ba..wlh ko yanada niyyar yin soyayya baiga dalilinda zai sashi kula mace marar class irin wnn ba..ace mace kaman chewing gum sai nanikewa kike ana koranki amma bazaki hakura ba..wnn wace irin rayuwa ce?.

Koda Nuru ya shigo yanajin alaman yana bathroom sai ya nemi kan sofa ya zauna yana pressing wayarshi…after like 7 minutes Bobby ya fito daure da towel a waist dinshi…dagowa Nur yayi yana kallon pure white skin dinshi da ruwa ke tsere akai as result of wankan da yayi snn ya saki wani murmushi…murya can kasa ya furta”what a hottie!..”sarai Bobby yaji abunda ya fada amma bai kulashi ba ya karasa gaban mirror ya fara shafa cream dinshi…shima Nur sake juyawa yayi yana facing inda yake hadda su yin tagumi yana cigaba da kallonshi…kawai ayyana baiwar kyau da Allah yayi mishi yake…gani yake kaman Bobby is the most cutest and hottest guy alive…baisan why ba amma shi kam kyawunshi na burgeshi sosai…cikin ranshi yake ayyana idan shi da yake namiji yana admiring kyawun Bobby yammata kuwa ai kilan sai sunyi hauka akanshi cox yanada wani irin kyau da a kallon farko zaka fahimci hakan…ko dan kasancewarshi ruwa biyu ne oho?..dama ai ance duk dunia babu wanda yakai halfcast kyau so maybe shiyasa duk yan gidansu Bobby keda kyau tunda Mom dinsu igbo ce Daddy kuma Fulani…ta cikin mirror Bobby yaga yanda Nur ya sake juyowa yana zuba mishi ido kaman wanda bai sanshi ba dan haka ya dan saki tsaki tareda juyawa yana dubanshi yace”malam what is the look for?..haka nan ka kafa min ido kana starring..are you sick?..”numfashi Nur ya saki tareda sauke hannunshi  daga tagumin da yayi before saying”kawai ina kallon hottie ne…the only cute and sexy man around..guy ba dole yammata suyita hauka kanka ba..ga Rayhan can ma tunda na ganta nasan zuwa tayi kuyi zance”…wani kululun baqin ciki yaji ya sake tokareshi just by mentioning Rayhan’s name…Goodness he hates that girl with passion…he hates her like hell and not only Rayhan he hates duk matan dake kawo mishi kansu…he hates classless women…sbd tsabar baqin ciki ma kasa cewa komai yayi kawai ya juya zuwa closet dinshi ya shiga ciki ya sako white crazy jean da wata black polo snn ya fito fuskan nan ba fus…gefen bed dinshi ya zauna ya dauki wayanshi knn Miemie ta shigo dakin rikeda tray da aka dora transparent glass jug mai daukeda pineapple juice a ciki…kan dan table dake tsakiyan sofas din ta ajiye snn ta mike…tun kafin ta juya Bobby ya daka mata wani tsawa”Miemie bakida hankali koh?..kina hauka zaki shigomin bedroom without my permission?.. “jikinta har ya dauki rawa tace” Uncle Bobby nayi sallama f..”bai bari ta karasa ba ya shiga nuna mata kofa yace”leave immediately”…ba musu ta juya tana turo baki ta fita daga dakin…Nur ya juya yana dubanshi yace”kaidai bakayi ba wlh…baka ajiye komai ba sai shegen masifa mara amfani”…ya bude baki zaiyi mgn aka sake turo kofan dakin wnn karon Rayhan ce ta shigo daukeda tray din abinci…wani azababben zafi yaji ya faraji all over his body kaman ba yanxun ya fito daga wanka ba…like how dare this girl enter his bedroom like this…how dare she…Nur na ganin yanda yanayinshi ya sauya ya saki murmushi cikin ranshi yace”Allah ya kara”..a fili kuma kallon Rayhan data ajiye trayn hannunta yayi yace”sannu da aiki fa”..tana murmushi ta daga mishi kai…shi kuma ya mike yayi pouring juice da Miemie ta shigo dashi a cup snn ya fita palor yana sipping juice din yace”bari in baku space”…Bobby ya bishi da wani uban harara kaman idanunshi zasu fado kasa…idanuwan Rayhan a kanshi kaman zata cinyeshi itama…bata taba ganin wanda harara yayi mishi kyau kaman shi ba…rai a bace ya juyo da idanunshi gareta voice dinshi har bai fita sosai sbd bacin ran da yake ciki yace”how dare you?..how dare you enter my bedroom without my permission?..”a hankali tace”am sorry..Mummy tace in kawo maka abinci”..tun kafin ta karasa yace”Mummy tace ki kawo ko kuma kikace zaki kawo..wato bazaki fita harkana ba koh?..”a hankali tace”bazan iya fita harkanka ba because i love you”…daga mata hannunshi yayi yana fadin”hold it there…wai how many times do i have to push you away ne?..don’t you get tired?..”nan da nan hawaye ya kawo idanunta tace”Uncle Bobby please!..wlh i love y..”still bai bari takai karshe ba yace”who’s ur uncle anan?..stop calling me that am not ur Uncle”..ya karasa mgn yana kawar da kanshi daga gareta kaman wanda yaga poopoo…baisan why duk ta ce mishi Uncle Bobby yakejin wani iri ba…duk Miemie ce ta cuceshi tasa mishi wnn sunan shknn yanxu kowa ke kiranshi haka…hatta Sab da yake brother dinshi shima ta koya mishi kiranshi da Uncle Bobby and now wnn super glue din ma ta kama…hannu Rayhan takai ta goge tears dinta…wlh da tanada yanda zatayi ta cireshi daga ranta da tayi ko don sbd wulakancin da yake mata amma bazata iyaba ita kanta ta sani…mikewa tayi bayan ta gama wiping tears din nata tace”zan tafi..amma dan Allah Uncle Bobby ka dinga picking call dina ko sau daya ne a rana please”…baice mata komai ba sai kanshi daya daga ita kuma ta juya a hankali ta fita tana cigaba da share hawaye…Nuru na ganin ta fita ya dawo dakin rikeda empty cup daya shanye juice din ciki…kai tsaye warmers data shigo dasu ya shiga budewa kobi takan Oga Bobby baiyi ba…ya wani lumshe ido yana smelling aroma din abincin hadda su girgiza kai…serving kanshi yayi ya fara cin abincin…su Uncle Bobby dai har yanxun ana zaune dafe da kai feeling extra hot inside.

Saida Dr Nuru ya gama cinye abincinshi tas ya kora da juice snn ya dawo da hankalinshi kan Bobby da har yanxun ke zaune kaman statue yace”Man if bakaci abincin nan ba kayi missing wlh..na tabbata wnn handwork din Mummy ne for the food taste good”…banza Bobby yayi dashi dan abunda ya dameshi ma ya isheshi…shi kuwa Nur ya sake zuba juice dinshi a cup snn ya mike yana sipping abunshi ya fita daga dakin…parlon Mummy ya koma ya samu tana sallama dasu Rayhan zasu tafi sai Miemie dake zaune dinning tana cin abinci…karasawa yayi ciki shima ya zauna idanunshi kan Miemie kafin Mummy ta dawo cikin parlon itama…Nur ya gyara zama yana fuskantarta yace”Mummy karan abokina na kawo fa”…juyawa itama tayi gareshi tace”wai Bobby?..meya hadaku kuma?..”saida ya sauke ajiyar zuciya snn yace”akan college ne wlh…malamar da take daukan reproductive health ne ta tafi maternity leave and su biyu dama mukeda a wnn bangaren shi kuma Umar yanada classes da yawa da yake attending shine nace Bobby ya taimaka ya danyi covering yaran ko na 1 week ne before we employ new staff amma sam yace bazaiyi ba..that shi ba lecturer bane kuma Mummy na tabbata ba wanda zai iya koyar dasu kamanshi tunda field dinshi ne amma yaki amincewa and in the next 3 to 4 weeks students zasu fara exam bansan me yakeso su rubuta a course dinba tunda duk wnn semester baifi lectures din 1 month suka samu ba shine naga i have to talk to you ko zakiyi mishi mgn ya taimaka musu plss”…if you see yanda ya karashe mgnr da wani puppy eyes zakayi tunanin mutumin kwarai ne😂Mummy na gama sauraranshi tace”amma Bobby bai kyauta ba gaskia..don’t worry zanyi mgn dashi ai bai kamata a bar students a haka sunata wasting time dinsu a banza ba..i’ll speak to him”…Mummy na fadin haka ya saki wani murmushi yana shafa kanshi yace”yauwa Mummy thank you…thank you sosai”…murmushi itama tayi tareda gyada mishi kai…Aunty Sumy ta shigo parlon sanyeda dogon riga mara nauyi da alama tayi wanka ne…ta karaso ciki ta zauna tareda umartan Miemie data kawo mata abinci…ba musu ta mike zuwa kitchen tunda ta gama cin nata already…zubowa tayi ta kawo mata snn ta nemi wuri ta zaune kusada Mummy…Aunty Sumy data fara cin abincin tace”Mummy yanxu mukai waya da Hafsa tace zasu dawoda Ilham gobe”…Mummy na gyada kai tace”to Allah ya kaimu goben..nasan da kyar idan ba halin nata tayi musu ba tunda zasu dawo da ita da wuri”…Aunty Sumy tace”nima nayi tunanin haka..ai tama dade wnn karon yau satinta daya fa”…sauke ajiyar zuciya Mummy tayi kafin ta sake fadin”Allah ya kaimu goben toh”..Aunty Sumy tace”Ameen”…Miemie da har yanxun ke zaune kusada Mummy tace”Allah ya kaimu dama na matsu ta dawo wlh..duk gidan ba dadi idan bata nan”..murmushi Nur yayi yana kallonta yace”to mai ‘yar uwa”..murmushin itama kawai tayi mishi..shi kuma ya sake kafa idanu a kanta..yarinyar na burgeshi sosai…ana haka Sabeer ma ya shigo parlon sanyeda yadi milk…dogo ne sosai shima dan kusan tsayinsu iri daya dana Bobby saidai Bobby yafishi da kadan…kai tsaye jikin Mummy yayi masauki yana wani kwabe fuskanshi kaman dan yaye yace”Mummy yunwa”..shafa cikinshi Mummy tayi tace”shiyasa nace ka tsayi kaci abinci kafin ka fita amma kaki…nasan ba abincin waje kake iya ci ba..Miemie tashi ki kawo mai abinci”..ta karasa mgnr referring to Miemie dake zaune…batayi musu ba ta mike zuwa kitchen tana kunkuni…itafa ta dena kula Uncle Sab a gidan nan sun kasa fahimta…Nur da yaga yanda Sabeer ke sake lafewa jikin Mummy sai ya saki daria yana fadin”haba Oga ASP da girmanka?..irin wnn shagwaba ai na civilians ne irinmu mu bana officers ba”…cikeda yar kunya ya dago daga jikin Mummyn yana wani shafa kanshi yace”Uncle Nur barka da zuwa..ashe kana nan wlh ban lura da kai ba”…Nuru na girgiza kanshi yace”dama ya zaayi ka lura dani Sab kana irin wnn shagwaba haka..wai kai auta koh?..”daria kawai Sab yayi yana sunkuyar da kai…Miemie ta dawo da abincin nashi ta ajiye tana kokarin zaunawa yace”Mummy kinga bata kawomun spoon ba kuma idan na gama ci wane ruwa takeso nasha?..”kafin ma Mummy tayi mgn Aunty Sumy tabi Miemie da wani kallo tace”haka ake kawo abinci?..”dan turo baki tayi tace”shine fa dazu da safe hadda cemin skeleton”…a fusace Aunty ta sake cewa”sbd ya fada maki haka shine zaki rama yanxu koh?..wai yaushe kika raina Sab ne haka a gidan nan?..abokin wasanki ne shi?..”bata ce mata komai ba sai mikewa da tayi zuwa kitchen da dauko spoon din hade da ruwa ta kawo mishi..ya faki idon su Mummy yayi mata gwalo ita kuma ta kwabe fuska tana duban Mamanta tace”Aunty kinga yanamin daria koh?..”tsaki Aunty Sumy ta saki tareda tura mata plate data gama cin abinci dashi tace”C’mon dauka ki kai kitchen”…da gudu ta mike ta dauki plate din tayi kitchen…tana ajiyewa ta sake fitowa a guje tayi dakinta rai duk a bace kaman zatasa kuka…Mummy ta bita da kallo tana girgiza kai…ta fuskanci wnn rigiman nasu hali ne a kokon rai dole sai sunyi shi…hakan kuma baya hana duk daya baya nan dayan yayita kewar dayan ba…dan ma akwai Bobby da suke tsoro ai da kilan rikicin nasu sai yafi haka.

Suna zaune Bobby ya shigo rikeda waya a hannunshi kai tsaye ya karaso ciki tareda mikama Aunty Sumy wayan yace”Its your call”…ba musu tasa hannu ta amsa wayan tareda karawa kunnenta tayi sallama…a daya bangaren Hafsa tace”wa’alaiki salam Maman Miemie..inata kiran wayanki no answer shine nace bari inyi trying na Bobby in gani sai gashi kuma ya shiga..Ilham ce ta dameni wai tanason mgn daku”..Aunty Sumy ta dan saki murmushi tace”oh Hafsa wai kece?..dama kinada Number Bobby knn?..”Hafsa tace”bani dashi wlh Ilham din ce ta bani wai tunda naki baki dauka shi a kirashi..gata kuyi mgn”..daga haka ta mikama ilham dake zaune kusada ita wayan…yarinyan da bazata haura 8 to 9 years ba ta amsa wayan full of happines tace”Auntyyy”..aunty sumy ta saki daria jin yanda taja sunan nata tace”na’am ‘yar gidan aunty ya kike?..”tace”am fine aunty just missing you..i want to come back home”..aunty sumy tace”hope dai ba rigima kikema aunty hafsa ba koh?..”tace”bana rigima aunty kullum sai mun fita yawo..yau ma saida aka kaimu shopping dasu fadeel”..aunty sumy tace”inyee ‘yan gidan aunty hafsa..ilham banda fitina kinji?..kuma banda kiriniya banda sa aunty hafsa magana”…daria ta saki sosai kaman wata babba tace”aunty i want to speak to everyone please..where is my Uncle Bobby?..”Aunty sumy tayi putting nata on speaker snn tace”your uncle bobby is here”..cikin excitement ilham tace”my uncle bobby”..yace”yes my mummy how are you?..”tace”am fine uncle bobby ya aiki?..”yace”aiki fine ilham gobe zaki dawo ba?..”tace”yes..kasan me na siyo muku daxu da mukaje shopping?..”yace”sai kin fada mummy”..suna jin yanda ta danyi kasa da murya snn tace”na siyo maka cheesy na siyoma uncle sab sweet na siyoma yaya chocolate snn na siyoma Mummy da aunty biscuits”..dan bata rai Bobby yayi yace” seriously ilham?..of all abubuwan dake wajen ki rasa abunda zaki siyomin sai cheesy?..”daria ta saki sosai tace”to ba kace min kana son cheesy ba..shknn zan sake maka wani yanxu ka bama Mummy da uncle sab muyi mgn”..bai sake mgn ba ya mikama Mummy wayan..nan ma hira suka sha sosai sai kace wata babba snn sab ya karba shima aka sha hiran dashi…miemie ce karshe aka kai mata wayan har daki nan ma suka dora daga inda suka tsaya…Bobby na duban Mummy in a serious tone yace”Mummy nidai kada a sake bari wani daga cikin mutanen nan yazo yace zai dauki yaran nan bana so wlh..after duk abubuwan da suka yi mana yanxub zasu ringa wani zagayowa suna daukan yara sbd mu yadda dasu?..”girgiza kai Mummy tace”kaidai ka fiya riko wlh Bobby..baka manta abu komai qanqantarshi…abun daya faru ya riga ya faru saidai a kiyaye gaba”..aunty sumy tace”kuma Mummy duk abubuwan da suka faru babu ruwan hafsa a ciki..lokacin ma tana england komai ya faru so bazan iya hanata ba muddin ta nuna tanason daukansu koba komai qanwar mahaifinsu ce”..wani kallo Bobby yayi mata yace”sbd tana qanwar mahaifinsu bashi zai daman zuwa koda yaushe tace zata daukesu ba..idan abun da gaske ne meyasa shi baban nasu ya kasa nemansu duk tsayin wadan nan shekarun sai ita?..”dafe goshi kawai Mummy tayi dan tasan kome zaa fada bazai yadda ba tunda ya riga ya dauki zafi haka…itama aunty sumy sanin halinshi yasa taja bakinta ta tsuke tunda it’s of no use trying to explain things to him bazai taba fahimta ba..ya mike zai koma flat dinshi Mummy ta kira sunanshi…ba musu ya dawo ya zauna yana fuskantarta…itama tana dubanshi tace”wane magana kukayi da Nuru dazu kace bazaka iyaba?..”da sauri ya kalli Nur da yayi wani kasa da kai sai kace mutumin kirki…wato ma karanshi yazo ya kawowa Mummy sbd yasan ita kadai zata iya mishi dole koh…rai a dan bace Mummy tace”bada Bobby nake mgn bane?..”a hankali yace”Mummy lecturing fa yakeso inje inyi..sbd Allah Mummy ta ina zan wani fara shiga class ince zanyi lecture bayan ba tabayi nayi ba..idan tsakani da Allah ne shi meya hana bazai je ya koya musu da kanshi ba”..yana rufe baki Nur yace”amma kasan da field dina ne ba abunda zaisa ma in tambayeka sbd nasan 6atamun lokaci zakayi..kaine gynaecologist dan haka kai ya kamata ka koya musu ba ni ba”…wani irin daci yaji yana taso mishi tun daga throat dinshi zuwa bakinshi..gaba daya sai ya zama speechless a wurin..nan take Mummy tace yaje ya  taimaka musu koda na one or two days ne…as usual ya amsa mata da toh snn ya mike zuwa flat dinshi…Nur ya bishi da kallo yana kunshe daria…sallama yayi dasu Mummy snn ya mike zuwa flat din Bobby ya sameshi kwance kan three seater a parlor idanunshi lumshe yayi pillow da hannayenshi…murmushi ya saki tareda sunkuyawa saitin kunnenshi yace”this is your punishment for making Lamido cry”…Bobby da yaji mgnr kaman daga sama baisan lokacinda ya mike zaune da sauri yana kallonshi ba…mamaki ne karara a fuskanshi jin abunda yace…shi kuwa Nur juyawa yayi ya fita daga parlon yana daria kasa kasa yasan yanxu komai taurin kanshi dole yayi abunda yakeso tunda Mummy tasa baki…Bobby kam sbd tsabar takaici baisan time daya dunkule hannunshi tareda naushin kujeran da yake kai ba yana fadin”Fuck you Nur”.

Har washegari Saturday ranshi bai dena 6aci kan abunda Nur yayi mishi ba..neman hanyan da zai rama kawai yake amma ya rasa…mikewa yayi daga karshe ya bude wata kofa ta cikin parlonshi sai gashi wajen wani tafkeken swimming pool daga gefenshi kuma gymnasium dinshi ne daya cikashi taf da kayan motsa jiki…kai tsaye gym din ya nufa dan a al’adanshi every Saturday and Sunday sai yayi training kafin yayi komai dan haka yana shiga ya fara training dinshi…ya 6ata lokaci sosai yanayi dan bai baro gym din ba sai da ya hada gumi sharkaf snn ya bude fridge dake ciki ya dauki chilled water ya bude yasha snn ya fito daga gym din yana cigaba da sipping a hankali…direct bedroom dinshi ya wuce bai kobi takan wayanshi da yaga yana haske ba ya fada bathroom…wanka yayi a tsanake snn ya fito yana goge jiki da towel..ya isa gaban mirror yayo shafe shafenshi snn ya shiga closet dinshi ya sako kaya ya fito snn ya isa ga wayanshi da har yanxu bai dene haske ba alamun ana kira knn…missed calls ya gani har 8 biyu na wata Nurse dake Hospital dinshi,biyu na Nuru sai ragowan hudun kuma gaba daya na Rayhan ne…baibi ta kan natan ba ya fara kiran Nurse din..bayan sun gaisa tace”Sir dama da akwai emergency ne kuma Dr Isaac baya nan”..yace”doc Vivian fa?..”tace “itama bata nan Sir”.. kmr bazaiyi mgn sai daga baya kuma yace”alright i will be coming”.. ta amsa da” ohk sir”..snn ta kashe wayan…suna gamawa ya shiga kiran Nur shima bai dade yana ringing ba yayi picking yana fadin”Bob ina ka shiga naketa kira baka picking?..”ba tareda ya bashi amsan tambayan ba yace”what’s the call for?..”da sauri Nur yace”wlh yanxun ake kirana daga Hostel wai wuta tayi spark a wani apartment kuma baa san me yayi causing ba shine naga ya kamata muje mu duba to make sure ba wani babban matsala bane”..shiru Bobby yayi yana sararonshi har ya gama snn yace”yanxun Hospital zanje munada emergency sadai in na gama da can in shigo”..da sauri Nur yace”No problem kana gamawan ka shigo i’ll wait for you”..bai sake cewa komai ba ya kashe wayan…karasawa gaban mirror yayi ya sake feshe jikinshi da turaruka snn ya dauki dayan phone dinshi ya fita daga dakin…kai tsaye parlon Mummy ya shiga bai sameta ciki ba dan haka ya wuce bedroom…tana zaune kan sallaya sanye da hijab a jikinta tana azhkar ya shigo…ya nemi wuri ya zauna saida ta gama azhkar din ta juyo tana kallonshi tace”Bobby”..yace”Mummy ina kwana”..tace”lafia lau..in zakaje haka da sassafe?..”yace”Hospital zanje wa there is emergency..daga can kuma zan shiga college amma ba jimawa zanyi ba”..Mummy ta mike daga inda tace”to muje kayi breakfast “..tana rufe baki yace” Mummy am ok plss..bana jin yunwa”..zaunawa tayi kusa dashi tareda kamo hannunshi a hankali tace”wai sbd maganan jiya ne kaketa 6acin rai haka?..”ya dan turo bakinshi yace”Mummy nifa ba ta6a lecturing nayi ba kin sani..kawai sa inje in wani ce su zauna zanyi musu lectures “..murmushi Mummy ta saki tareda gyara zama tace” ko da baka ta6ayi ba am 💯 sure you can do it..besides taimakawa zakayi Bobby dududu baifi kuyi na two or three days ba zaa samu wani..ko kana ganin as the proprietor bazaka iya shiga class ka koyar dasu ba?..”da sauri ya girgiza mata kai yace”that’s not what i mean”..tace”to ka kwantar da hankalinka nasan you can do it..and believe me zaka kara qima a idonsu idan sukaga har ka shiga class dinsu da kanka ka koyar dasu so relax”kasa ce mata komai yayi sai dan murmushi daya saki…murmushin itama tayi masa tareda mikewa ta kama hannunshi suka fita zuwa dinning…da kanta tayi serving dinshi baiyi musu ba ya shiga cin abincin…jin shiru da yayi gidan yace”wai duk ba wanda ya tashi?..”Mummy tace”kasan weekend ai dama ba tashi da wuri suke ba..kowa yana ramuwar bacci”…gyada kanshi yayi yace”amma shi Sab ramuwar baccin uban me yake shida ba fita ko ina yake ba?..wai yaushe ne ma zasuyi resuming school?..”tace”nan da two weeks ina tunanin”..yace”Allh ya kaimu..gara ya koma ko don sbd mu huta da rigimarsu da Miemie..kullum cikin cin zalinta yake”harara Mummy ta maka mashi kafin tace”bayanta kake goyo sbd ita ‘yarka ce koh?.”ya dan saki murmushi yace”aah Mummy gaskia dai nake fada”..tace”to rike gaskiyan naka baa son ji dan bazan bari ka dorama d’ana laifi ba”…murmushi kawai ya sakeyi baice komai ba…saida ya gama cin abincin ya mike Mummy ta rakashi har centarl parlor tana mishi addu’a..yayi mata side hug tareda fadin”Ameen Mummyna..bari inga aunty Sumy kafin na fita”…gyada mishi kai kawai tayi snn ta juya ta koma ciki shi kuma ya nufi flat din yayar tashi…Miemie ce kadai kwance a palor tana kallon wani Series ya shigo..ta mike zaune da sauri tana gaisheshi yace”lafia..bata tashi bane?..”tace”ta tashi tun dazu tana daki”..bai sake mgn ba ya nufi bedroom dinta..zaune ya sameta a kan gado tayi tagumi tareda zubama wayanta dake rike a hannunta ido sai kace zata gano wani abu a jiki…ya karasa ya zauna kusada ita yana kallon wayan nata snn ya kalleta yace”Aunty Sumy lafia kuwa?..”firgigit ta dago tana kallonshi dan batasan ya shigo ba…ta boye wayan hannunta da sauri tana kakalo murmushi tace”yaushe ka shigo?..”maimakon ya amsa sai cewa yayi”lafia wai?..meya faru naga kin zubama waya ido haka?..did somebody called?..” girgiza kai ta shiga yi da sauri tace”b..ba wanda ya kirani”…bai sake cewa komai ba yakai hannu ya amsa wayan daga hannunta..direct call log ya shiga aikuwa yaci karo da wata international number..yayi tsai yana karema number kallo nan take kuma ya gane number England ce…ya dago yana kallonta fuskanshi har ya sauya sbd 6acin rai yace”why did he called?..”murya a sanyaye tace”don’t know..maybe sbd kids dinshi”..bata rufe baki ba cikin tsananin 6acin rai yace”but how dare he called you?..a ina ma ya samu numberki koda yake nasan qanwarshi ce zata bashi..wnn shine dalilinda yasa nace maku bana son mu’amala da mutanen nn..idan ba munafurci ba all these years meyasa bai ta6a kira ya tambayi kids din nashi ba sai yanxu?..after all what he’s done to us har yanada guts din dazai daga waya ya kiraki?..is he Maddd?..”shiru kawai Aunty Sumy tayi tana kallon yanda ya rufeta da masifa as if shine yayanta..tasan duk wnn abun da yake yanayi ne akan gaskiyarshi and bazata ta6a ganin laifinshi ba..ita kanta kusan mutuwar tsaye tayi da taji voice dinshi ta  kuma tabbatar da cewa Ismail nefa da gaske ya kirata after 5 long years…to me zai fada mata?..me xai fada wanda bai fada mata shi a lokacinda zasu rabu ba?…a hankali tace”ka kwantar da hankalinka plss”..bai bari ta karasa ba yace”i will have to deal with him myself”..bata ce komai ba tana gani yayi blocking number snn ya mika mata yace”he might use another number to call..yana kira ki fadamin”..a hankali ta gyada mishi kai shi kuma ya mike ya fita sbd 6acin rai ko mgnr daya kawoshi bai fada mata ba…sauke ajiyar zuicya tayi bayan ya fita ta koma ta kwanta kan gado tana sake sake..ita kanta tasan idan yaji anyi blocking dinshi zaiyi using wani number ya kira..idan ya kira din kuma batasan me zata fada masa ba as gabaki daya kanta a daure yake yanxun..ga kuma Bobby da tasan muddin ya samu labarin ya sake kira din shima ba karamin rikici zaayi dashi ba..she knows how stubborn he can be and ko kadan bata blaming dinshi because duk abunda yakeyi yanayi ne sbd su..tasan yanda yakejin ciwon abubuwan da suka faru a baya shiyasa har yanxun ya kasa mancewa…yanada son ‘yan uwanshi sosai shiyasa duk wani abu daya shafesu yake bashi muhimmanci…ta lumshe idonta ta bude data tuna yanda yake dawainiya dasu Miemie tamkar shi ya haifesu..bama su kadai ba hatta ita kanta Bobby shine komai nata a yanxu..tun daga kan Mummy,Sab,Miemie da Ilham zuwa ita kanta shine ya zama tamkar mahaifi a garesu…duk tsawon shekarun nan bai ta6a bari sunyi missing wani abu ba ya zama gatansu sosai…kusan duk neman kudin da yakeyi a kansu yake karewa tunda shine komai nasu…kuma da yake Allah ba azzalumin sarki bane sai yake buda mishi a harkokinshi sosai kuma mishi albarka business dinshi har ya kawo level din da yake a yanxu…tayi nisa cikin tunani har batasan time din da ta fara hawaye ba..tausaya ma kansu takeyi yanda basu da kowa sai junansu a yanxu sai few daga familyn Mummy da suka rage..yanda familyn dad dinsu dana baban yaranta sukayi abandoning dinsu kawai sbd kasancewar Mummy ba bahaushiya ba…yanda sukayita truggling su kadai har Allah yasa suka yanxu…zuwa yanxu kuka takeyi sosai shiyasa bata cika son tana tunawa da past dinsu ba domin yin hakan yana dawo mata da baya gaba ne..gashi duk yanda takai da kokarin dakatar da kanta abun ya gagareta haka taci kukanta sosai ta godema Allah har 6arawon bacci ya lalla6o yayi gaba da ita.

Kai tsaye yana fita parking space ya nufa…driver na ganinshi ya mike da sauri yazo ya gaisheshi tareda tambayanshi motan da zasu fita…Bobby bai iya cewa komai ba sai juyawa da yayi yana kallon motocin..idonshi ya sauka kan wata Benz dinshi daya dade bai hau ba dan haka yace a fito da ita kawai..cikin hanzari Mr.Obi yayi clearing motan dukda dama ba wani datti ke gareta ba cox ana yawan wankesu snn ya fito da ita..ya bude back seat da kanshi ya shiga snn driver yaja motar bayan ya gama warming dinta suka fita daga gidan..kai tsaye yace ya fara kaishi Hospital.

Bai baro asibitin ba sai after 11 kai tsaye kuma suka wuce College…suna hanya ya kira Nur yace gashi nan zuwa shima yace dama already yana cikin college din shi yake jira…da yake akwai dan nisa tsakanin Hospital da College din basu suka isaba sai 12…bai fito daga mota ba ya kira Nur sai gashi ya fito daga office hihi ma ya da cikin motan nasu suka shiga Hostel din…as always sukayi parking daidai second gate snn suka fito zuwa ciki…daya daga cikin Matrons dake kula dasu tayi musu jagora har cikin apartment da abun ya faru..wutar apartment din ya dauke gaba daya..Nuru yace”amma daga wane room abun ya fara?..”ba musu Matron ta kaisu har cikin dakin..babu kowa ciki kasancewar an riga an sanar dasu cewa Provost zai shigo dan basu san har proprietor zaa zo ba…karema dakin kallo suka hau yi idanun Bobby ya sauka kan gadon Lamido da har yanxun ke shimfide da bedsheets na Man Utd..ya kalli gadon da kyau sai kuma ya ta6e baki cikin ranshi yana mamakin wai mace da football…duk iya dubansu basuga wani alama na wani abu ba har sun juya zasu fita ta fito daga kitchen hannunta rike da plate din indomie tana cewa”Billy you need to taste this…”magananta ya makale sakamakon mutanen data gani a dakin…yau ma dai kaman ko yaushe jessy ne a jikinta fara na Manchester sai wandon jessyn daya tsaya mata iya guiwa…gaba daya tsayawa sukai suna kallonta…ita kanta mutuwar tsaye tayo a wurin don kwata kwata batasan suna cikin dakin ba…juyawa tayi da sauri tana zazzare idanu kaman wanda tayi ma sarki karya…idanunshi ya sauka bayan rigan nata da aka rubuta POGBA da capital letters sai a kasa kuma aka zana katoton number 6…wani haushi yaji ya sake turnukeshi…ita kuma kaman wanda aka tsikara ta bude wardrobe da sauri ta rarumo hijab din Billy ta zura a jikinta…sai a yanxu Nur ya samu baki mgn”Lamifo is this your room?..”tana kokarin kakalo smile tace”yes sir..good afternoon “..yace” afternoon amma garin ya wuta yayi spark a nan?..”tayi kasa da kanta ganin irin kallon da Bobby ke mata tace”muma bamu saniba sir..kawai muna zaune sai mukaji wani kara”..bata rufe baki ba Bobby ya juya ga Matron data rakosu yace”waye dayan wanda suke tare a dakin?..”da sauri matar tace”bari a kirata Bilkisu ce”..daga haka ta fita sai gasu sun dawo tareda Billy da tayi kasa da idanu sbd idanun Dr.Bobby da ko kusa bata kaunar ya zuba mata su…sumi sumi ta karaso cikin dakin tareda tsayawa kusada Lamido da itama nata tun dazun yake kasa…shi kuma ya shiga binsu da kallon da suka tsana ya ganeta sarai itace ta rakata Clinic ranan da ya mata allura..baisan meyasa jikinshi ke bashi akwai dalilin yin spark din ba..kuma as far s Lamido is concern yasan abunda yafi haka ma zata iya aikatawa cox a dan ganin da yayi mata yaga alaman ba karamar fitinanniya bace..cikin voice din daya sake tsoratar dasu yace”now tell me..waye ya kusa haddasa min gobara a building?..”sukayi shiru ba mai kwarin guiwar yin mgn cikinsu…ya daka musu wani tsawa yace”are the two of you deaf?..”jiki na rawa Billy tace”Sir itace ta jona iron ta barshi a jiki”..tana rufe baki itama Aysha tace”Sir karya ne itace ta jona iron din ta tafi tayi bacc..”ragowar mgnr nata ya makale sakamakon idanu data hada dashi…wani irin kulululu taji cikinta nayi kaman zataje toilet..Allah ya zubama idanun nan nashi wani kwarjini na musamman dake sa mutum ya shiga taitayinshi da zaran ya hada ido dashi…shi kuwa Bobby da gayya yayi hakan don yasan duk iskancinta ta kalli cikin idonshi saita saduda…lokaci guda wasu hawaye suka ciko idanun nata gashi har yanxu ya kafeta dasu ko blinking bayayi…hatta Bilkisu da nata idanun ke kasa ji take kaman ana wura mata wuta a cikinta tsabar tashin hankali…maimakon ya dauke idanun nashi sai ya shiga takawa a hankali har zuwa inda take…ya tsaya dab da ita hannayenshi zube cikin pockets dinshi cikin wani stern masculine voice dinshi yace”Now speak”..idanunta ta lumshe hawayen dake ciki suka cigaba da gangarowa cikin ranta ko duk addu’an da yazo bakinta yi take dan yanda taji kaman an daureta da sarqoqi ne an kuma jefata a cikin kurkuku tsabar rudanin data shiga…ganin halin data shiga Nur yayi saurin matsowa inda suke saidai kafin yayi magana Bobby ya daga mishi alaman he shouldn’t say a thing..ba yanda ya iya haka ya koma baya tareda rungume hannu yana binsu da kallo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *