DR MUHSEEN CHAPTER 11 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)

DR MUHSEEN CHAPTER 11 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

          📝………….Kusan a tare suka mike tsaye jin wani gigitaccen Kara daya karade illahirin cikin gidan.dakin Seeyerma suka nufa harsuna na rigen shiga.taddata sukayi tana ta fisge-fisge zata cire Karin ruwan da Doctor ya jona Mata.

Cikin zafin nama Aunty Hajara ta riketa murya cike da tausayi ta ce “sorry Seeyerma ki dakata kada ki Kara yima kanki illa”.

Sosai ta saka matsanancin kuka jin an riketa.

A hankali Uncle Yusuf ya fara tofamata addu’o’i har zuwa wasu lokutta kafin ta fara samun nutsuwa.

Gaba daya ta kontar da kanta bisa kafadar Aunty Hajara wani bacci mai nauyi ya Kara yin gaba da ita.kontar da ita tayi ta Kara ragemata iskan fanka kafin suka fito ta rufomata kofar.

      Anan bisa kujerun falon Suka sauna kowa da abinda yake tunani a cikin zuciyar shi.

     Sundau tsawon wani lokaci a haka kafin Aunty Hajara tayi ajiyar zuciya tana Kai dubanta ga mai gidan nata jin baice komai ba ta fara cewa 

“Gaskiya Abban su Khadija akwai matsala fa,kasan daman dakyar aka samu ta samu sauki a rashin lafiyar da tayi kwanaki,Wanda nafi tunanin kamar turen aljani ne aka yimata”.

     Sai a lokacin ya dawo daga duniyar tunanin daya Lula.

“Ki kontar da hankalin ki yanzuma zata warke insha Allah,saidai Ina Kara gyammaki kada kowa ya ji wannan batun…….”bai karasa maganar ba jin sallamar Faruk a bakin kofar shigowa falon.

Bayan sun amsa ya karaso ciki Yana mikamasu magungunan daya siyo.

Aunty Hajara ta amsa bayan yayi Mata bayanin duk yadda za’ayi amfani da su.

    Cikin sanyin jiki ya fice daga falon Bayan yayi masu sallama, zuciyar shi cike da damuwa yarinya marainiyar Allah hakan ta faru gareta,lallai nasan daga yau dole Seeyerma zata tsani Muhseen tsana marar iyaka.

Da wannan tunanin ya karasa part din shi saida yayi sallar isha’i kafin ya konta,Amma ya gagara yin bacci saboda yadda abin ya tsaya a ranshi.

        Haka Suma a bangaren su Aunty Hajara,ranar a dakin Seeyerma ta konta,cikin dare ta farka misalin 1:30 na dare.da kuka ta farka Dan haka Aunty Hajara ta ciremata Karin ruwan ganin ya Kare,Dan kafin Doctor ya tafi saida ya nunamata yadda zata cire.

Ruwa ta hada Mata masu zafi ta taimaka Mata zuwa toilet,dawowa tayi ta canza bedsheet din ta Kara gyara wurin.

Ta jima a zaune tana jiran fitowarta bayan ta hado Mata tea mai kauri a cup.jin shiru bata da niyyar fitowa yasa ta leka toilet din ganinta durkushe ta saka kanta a tsakanin cinyoyinta tana kuka yasa ta karasa ciki.

Tsaye ta mikar da ita bayan ta Kara hada wasu ruwan.

Tana sakata tako saki wani ihu saboda zabar da taji tana ratsata.da haka tayi ta rarrashin ta harsaida ta tabbatar ta gasu kafin ta kyaleta.wasu ruwan ta hadamata kafin ta fito tana bata Umarnin fa tsarkake jikinta kafin ta dauro alwala.

       Dakyar ta samu ta karasa wankan tana yi tana zubar da hawaye.

Doguwar riga ta bata ta saka marar nauyi mai gajeran hannu da dogon hijaf.

Saida ta shimfida Mata abin salla kafin ta bata Umarnin ta rama sallolin da ake binta.

A zaune tayi saboda jin bazata iya tsayuwar ba.tana salla tana kuka.data idar saida ta roki Allah ya bata ikon cinye wannan jarabawa.

      Tea din ta mikomata,a hankali take kubar shi Dan ji take kamar madaci  ne take Sha saboda komai baya yimata dadi.da haka ta ballo Mata magunguna ta bata ta sha.kamata tayi zuwa saman gadon ta kontar da ita.kafin ta rufeta da blanket.

    Ajiyar zuciya tayi ta saukewa har bacci yayi awon gaba da ita.kafin itama Aunty Hajara ta konta.

    Wuraren karfe 2:00 na dare Muhseen ya farka sakamakon wani mugun mafarki da yayi da shi da Seeyerma sunata gudu a da ji wasu mutane na biye da su da wukake  zasu kashe su.da sauri ya dafe kanshi jin wani mugun ciwo daya fara yimai.

    Ganin dare baiyi ba sosai yasa ya dauro alwala ya kabbara sallar nafila,Dan shi kam tunda yake baitaba aikata zina ba a rayuwar shi,ko a bareak  Yana kallon yadda wasu daga cikin abokan aikin Shi suna fantamawa yadda suke so,Amma baya shiga cikin su.

Tabbas yasan wannan ita ce kaddarar su,Kuma Yana addu’ar Allah ya Basu ikon cinye wannan jarabawa .

Da haka yayi ta addu’o’i da istigifari Yana Kara neman yafiyar a gurin  mahaliccinmu.kafin ya shima ya konta….A washe garin ranar Asabar Muhseen ko masallaci kasa zuwa yayi saboda tsananin kunyar familyn da yake ji.sai wuraren karfe bakwai saura kafin ya Kira wayar Lameer,tana fara ringing yaji yayi picking.

Ko sallama bai tsaya yi ba cikin sanyi ya ce “Lameer ka same ni a gida yanzu,zuwa anjima nake son komawa Daura”.

        “Lafiya Muhseen kake son ganina a irin wannan lokacin?ko baka da lafiya ne?”.cewar Lameer Yana tunanin babu lafiya tunda yaji muryar abokin nashi ta canza.

      Cikin kasa da murya tamkar Wanda baya son buda Baki ya ce “kayi abinda nacema malam banason yawan sururtu”

Kit ya katse Kiran Yana mayar da kanshi jikin filo.tunani yake yi a ranshi ko Yaya jikin Seeyerma soyake ya ganota Amma Yana jin tsoro.

     A part din su Aunty Hajara kuwa tunda aka kwalla Kiran sallar farko ta tashi.saida tayi nafila har aka fara salla tana bisa abin salla tana Kai kukanta ga Alllah subahanahu wata’ala akan faruwar wannan lamari.

       Kallon gadon da Seeyerma take tayi ganin yadda take ta faman juye-juye alamar bata jin dadin baccin.

   A hankali ta haura bisa gadon ta fara tayar da ita.cikin magagin bacci taji ana Kiran sunanta.

A hankali ta fara bude idonta saboda yadda ta ji duk sunyimata nauyi.

Ajiyar zuciya ta sauke tana ganin Aunty Hajara ce ke tashinta.

      Yunkurawa tayi danta sauka daga gadon,Amma da sauri ta koma ta konta jin yadda wurin yake yimata zafi.

     “Seeyerma tashi kiyi salla kinji,lokaci yayi”cewar Aunty Hajara tana kokarin tayar da ita zaune.

     Da taimakonta ta kaita toilet ita ta taimaka Mata tayi alwala.

      Akan abin salla ta ajeta kafin ta juya cikin toilet din.

ruwa ta Kara hadamata masu zafi.bayan sun idar da sallah ta umarceta da ta Kara yin wanka kota ji karfi-karfi a jikinta.

     Bayan ta shiga ita Kuma kitchen ta wuce.ruwan tea ta hadomata mai kyau da ya jikayan yaji sai kanshi yake yi.sai farfesun kayan ciki data hadamata masu romo ya ji tarugu da tafannuwa.

     A konce ta tadda ita.kasan kafet din ta sauko da ita.ta zubamata farfesun.da farko kin ci tayi saida tayi Mata da gaske kafin ta fara ci,harzuwa lokacin nan sharar kolla take yi.

      Yana konce yaji ana danna door bell.fitowa yayi hannunshi dafe da goshin shi jin yadda jiri yake neman kayar da shi.

Yana budewa yaga Lameer a tsaye Yana kallon shi.

“Shigo Mana ka wani tsare ni da kallo”cewar Muhseen Yana wani bata rai.

Murmushi Lameer yayi kafin ya raba ta gefen shi ya shiga cikin falon.

Shima rufe kofar yayi ya bi bayan shi.beedroom din suka nufa.

Lameer saman wata doguwar kujera ya zauna,shi Kuma ya haura bisa gado yayi rufda ciki Yana jin yadda zuciyar shi take bugawa da sauri da sauri .

Sun dau tsawon wani lokaci a haka kafin da Lameer yaji shirun tayi yawa ya kalleshi ganin hankalin shi baya jikin shi ya ce “kaifa wallahi dan rainim hankali ne,ka Kira ni Kuma kayi wani forget da ni”

     Shidai Muhseen ko uffan ya kasa ce sai kolla da tskfy silalowa daga cikin idanuwan shi.

      Shima kyale shi yayi yaci gaba da chat din shi.

     Seeyerma tas ta shanye farfesun jin yadda ya ji yaji sai kanshi yake yi,magunguna ta mikamata ta sha kafin ta lumshe idonta tana tuno abinda ya faru da rayuwar ta,da tana cikin farinci Amma sai gashi daga jiya zuwa wayewar gari duhu ya lullube wannan farincikin.

      Sakamakon maganin data sha taji wani bacci mai nauyi ya fara daukarta.cikin sanyin jiki ta cire hijaf din jikinta tana mikewa tsaye.yanzu ji tayi ciwon yadan ragu sai kadan-kadan take ji.

    Saman gadon ta koma tana konta tana lumshe idanuwanta da Suka yimata nauyi.

     Ganin bacci ya dauketa yasa Aunty Hajara sauke ajiyar zuciya ta fice daga dakin.

     “Lameer!Lameer!!”

Da sauri Lameer ya juyo jin Yana Kiran sunan shi.

      “Ya akayi ka shirya sanar da ni matsalar ka ko?”

   Saida ya tashi zaune kafin ya ce “ka kiraman Aliyu ya ansoman kayan break a part din Mama”.

    Haryanzu hannun shi Yana saman goshin shi Jin yadda jijiyoyin wurin suke kokarin fitowa.

    Baice komaiba sai wayar Muhseen daya dauka Ya fara kokarin Kiran nomber Aliyu.

    Aliyu da yake konce a part dinsu na samarin gidan yayi saurin duba wayar jin Kira ya shigo.sosai yayi mamaki ganin Kiran yayan nasu a irin wannan lokacin sadik ya kalla Yana cewa “kaga soja ne yake kirana ko lafiya”

     “To ka daga Mana kada ta katse kaji ko wani abin ne”cewar sadik da yake chat.

   Sallama yayi bayan yayi picking call din.

A dayan bangaren yaji an amsa,Amma ba muryar ya Muhseen ba ne.

Gaishe shi yayi,jin abinda yake cewa yasa ya amsa da to kafin ya katse Kiran.

   “Hmmm kaji Wai kayan break zan amsomasu a part din Mama taso muje ka rakani “cewar Aliyu Yana mikewa tsaye.

   A tare suka fita zuwa part din Mama.

    Bayan an kawo masu kayan break din Suka fara karyawa, Muhseen kadan ya kurbi tea din yaji ya koshi.shiko Lameer saida yayi taf kafin ya tashi.saida yayi wanka ya shirya kafin suka fito daga part din.harzuwa wannan lokacin Muhseen baice komai ba akan maganar.

     Cikin gari suka nufa gidan wani freind dinsu mai suna Rabi’u…………..²³

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *