DR MUHSEEN CHAPTER 13 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)

DR MUHSEEN CHAPTER 13 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

            📝……………..Dear ba gaisu?kiyi hakuri kin ji nasan dole abin zai dame ki,Amma inaso ki sani kowane dan Adam a duniyar to da irin rubutacciyar kaddarar da take zuwa cikin rayuwar shi,duk mumuni na duniya sai Allah ya jarabce shi ko a lafiyar shi,ko a cikin imanin shi,ko akan iyalinshi,ko Kuma akan dukiyar shi”

     Nisawa yayi Yana kallon yadda take zubar da kolla tamkar ruwan fanfo.

    Cikin taushin murya yaci gaba da cewa “Zanyi maki alkawari Dear Amma bazan yimaki dole ba idan harkin amince da ni to zan sanar da Unlce Yusuf ya daura aurena da ke,Daman ita Hindatu tana da Wanda take so,ta amince da hadinsu ne Dan kada suga ta bijirema umarninsu,Amm…………..

     Sauran maganar ce ta makale a bakinshi sakamakon banko kyaren kofar da akayi.

      Dukansu ita da Faruk suka mike tsaye suna kallanshi.

      Sosai jikinta ya fara kakkarwa da zufa,Bayan Faruk ta labe tana sauke ajiyar zuciya ganin irin kallon da yake yimasu.

     Cike da takama cikar haiba,cikin takun shi na cikkakkun maza ya fara tako kafar shi cikin tsakiyar dakin.

       Faruk ya tsare da idonshi Yana yimai wani irin kallo mai cike da ma’anoni da dama.

     Har zuwa wannan lokacin suma su Faruk a tsaye suke,itako Seeyerma baiwar Allah sai Kara runtse idonta take yi ji take kamar ita yazo lamawa.

            

           Saida yayi kasa da muryar shi kafin ya fara cewa “ok sai yanzu na fahimceka Faruk,Ashe wannan dalilin yasa kake ta faman likemata tun fil’azal ko?to bari ka ji na sanar da Kai da babbar murya Seeyerma ba matarka ba ce,wannan abun Kuma daya faru kaddara ce da Allah ya jarabcemu da ita………”

        “Dole zaka ce kaddara mutumin banza mutumin wofi,Kai yanzu saboda baka da kunyar harka iya tako kafarka inda muke saboda ka daukemu bamusan me muke yi ba,to idanma kana tunanin hakan da kayi shizai saka na baka aurenta to kayi kuskure,tuni nayi mata miji Dan haka ka gaggauta ficeman daga site dina tun kafin ranka ya baci”Cewar Unlce Yusuf cikin muryar bacin rai,daidai ya karasa shigowa dakin sai Aunty Hajara da take biye a bayanshi.

     Muhseen ji yake kamar kasa ta tsage ya shige saboda wata muguwar kunya data kamashi,baiyi tunanin Yan gidan suna nan ba jin lokacin daya shigo cit kamar ba kowa.

      A hankali ya nufi bakin kofar a zuciyar shi Yana jin babu dadi yanzufa duk laifinshi suke gani,dazu harsaida Lameer ya ce mai yayi zaman shi a gidansu saboda Yana bukatar hutu,dukda bai sanar da shi damuwar shi ba,Amma ya tausayamai ganin yadda duk yabi ya zabge.

     Harya fice daga dakin Seeyerma na makale bayan Faruk saida ta ji alamun yabar dakin kafin ta koma bakin gadon tayi konciyar ta.

    Fita Uncle Yusuf yayi Faruk yabi bayan shi.

    Karasowa Aunty y tayi tana Kara yimata sannu.

       Tunda ya fita daga part din yake jin kafafuwan shi duk sunyi wani sanyi,sosai yake ganin jiri saka kafarshi kawai yake yi Amma baisan Ina ne ya nufa ba .

    Tun daga nesa Jabeer ya hangoshi.ganin kamar zai fadi yayi saurin karasawa wurin shi Yana tambayar shi “Yaya Muhseen lafiya?meyake damunka haka”?

   Kamashi yayi Suka karasa part din Kaka,ganin sunfi kusa da wurin.

       Tana uwar daga Dan haka ya wuce da shi ciki.

     Hajiya Kaka ganin an ruko babban jikan nata yasa ta rude tana tambayar Jabeer abinda ya sameshi.

    Sanar da ita yayi shima bai saniba a nan waje ta ganshi Yana kokarin faduwa.

   Kontar da shi yayi saman bed din dakin ya zauna kusa da shi.

     Tasowa tayi kusa da shi tana taba jikin shi,zafi taji sosai a jikinshi.

      “Maigida baka da lafiya ne?Kai Jabeeru kiramin wayar Yusufa yazo da likita a dubashi” 

    Tana mikawa Jabeer wayarta

     “Ace mutum baida lafiya Amma bazai fadi ba sai kace ba likita ba”haka tayi ta faman mitar ta.

   Shidai Muhseen baiko kulata ba,saboda shi kadai yasan yadda yake ji a jikinshi.

      A Sudan kuwa Lalaih ce a jikin Yar tsohuwa Hajiya Aishatu tana rera kukanta,murya cike da yarinya ta fara magana”nidai wallahi zanje na sanarma sarki a kaini Nageria inaso Naga Yaya Muhseen da su Aunty Seeyerma,kullun sai nayi mafarkinsu”ta karashe maganar cikin saka kuka.

    Ummeey ce ta daga Mata tsawa lokacin da take shigowa dakin.

 Cikin Kara valume din kukanta ta fice daga dakin.wurin mai aikinsu ta nufa tana cigaba da rera kukanta.

       Bayan ta fita Ummeey ta zauna kusa da mahaifiyarsu ta ce “wallahi ni kaina hankalina ya kasa kontawa duk cikin kwanakin nan Ina yawan yin mugun mafarki akan yaran nan,dazu har Unlce dinsu na Kira Amma ceman yayi lafiyar su kalau babu abinda ya same su”.

     “Kiyi hakuri Diyata yanzu koma meye to addu’ar ki suke bukata,insha Allah madamar kin dage da yimasu addu’a to koma meye Allah zai kawo shi da sauki”cewar Hajiya Aishatu tana rike da hannun Ummeey.

    

       A gida Nageria kuwa haka Jabeer yayi ta faman Kiran Unlce Yusuf Amma baiyi picking ba saboda tun bayan fitar Muhseen daga part din shima ya koma kasuwa,Daman yayi mantuwa ne shiyasa ya dawo.

     Nomber Doctorn tasa aka kirmata,cikin kankanin lokaci yayi pecking.bayan an sanar da shi ya amsa da gashi nan zuwa.

      Mintuna shabiyar a tsakani sai gashi ya karaso.

     Saida aka dauramai karin ruwa saboda yadda ya shiga damuwa.

Magunguna ya rubuta dandanan Jabeer ya je ya siyo.haka yayi teriteng dinshi kafin ya tafi.

     Tunanin Hajiya Kaka ta fara yi towai meyake faruwa ne?ance Seeyerma bata da lafiya to shima wannan gashi a konce tabbas akwai abinda su Yusufa suke boyemata.

     A haka har bayan kwana biyu Muhseen Yana part din Hajiya Kaka,saidai ya ji sauki sosai har ana iya labari da shi.tunda ya sanar da commander a waya ya bashi left na kwana biyar harsai ya warke kafin ya dawo.

     Sosai Seeyerma ta ji jikinta ya warke sau biyu Doctor yana zuwa dubata,wurin dinkin ya warke tas.Aunty Hajara tana kula da ita sosai kama daga magungunan gyaran jiki da yanayin abinci mai gina jiki.

      Cikin wannan satin Seeyerma tayi bul abunta gwanin sha’awa,ta Kara haske da kiba dukda haryanzu tunani abin yaki barin zuciyar ta.

Shiko Muhseen tuni ta warware harya koma bakin aikinshi,tundaga wannan lokacin ne bai Kara zuwa katsina ba tunda ya tafi,saidai yayi waya da su Hajiya Kaka da Jabeer,dukda hankalin shi Yana ga yarinyar Amma Koda wasa bai taba tambayar tana Ina ba.kokarin ganin ya mayar da hankalin shi bisa aikin Shi yake yi.

       Ranar wata juma’a da yammaci Faruk ya dauketa suka fita zaga gari,saboda ta ce ta gaji da zaman wuri daya.

   Sosai suke yawo wuraren shakatawa ya kaita wurin shan accreem,sosai ya siyamata kayan malakushe su dangin Cakulet.

   Sai gab da magriba suka shigo cikin estate din.a wurin parking lot suka ga Kamar motar Ya Muhseen Amma basuyi tunanin shi ne ba,Dan yayi kusan sati biyu raboda ya zo katsina.

    Shiko Yana ciki tun shigowar motar su ya gane su,kasancewar motar shi akwai tintek hakan yasa basu ganshi ba.

    Cikin farinciki suka fito daga motar ya dauki leda daya itama ta dauki dayar.

   Harsun wuce wurin motocin ta tuna da tayi mantuwa,da sauri ta dawo jikin Motar ya Faruk bayan ta bude take kokarin dauko abinda ta manta.

 Shiko ya Faruk tuni ya shige part din Hajiya Kaka Dan shi ne mafi kusa da wurin aje motocin.

    Cikin sanda ya fito dag motar shi,ta bayanta ya tsaya Yana kallonta ganin yadda ta Kara zama cikakiyar budurwa ga wani kyalli da fatar jikinta yake yi.

  Cike da gajiya ta juyo da nifin ta karasa cikin gidajen leda dauke a hannunta.

Gaba daya cak taji anyi sama da ita tare da rufe Mata Baki da wani kyalle.

Da kafarshi ya rufe kofar,ya juya da ita zuwa cikin motar shi.

      Bayan motar ya sakata Daman a bude take.shima zama yayi kusa da ita bayan ya ciremata kyallen daya rufe bakinta da shi.

    Da sauri ta daga Baki da zummar zata kwala kara,lura da hakan yayi sai wuffffffff yayi saurin rufe Mata baki da nashi………………Wufffff yayi saurin rufe mata baki da nashi,dukda yasan Koda tayi ihu bamai jinta ballantana wani ya ceceta.sosai yake tsotse bakinta,itako sai faman tureshi take yi Amma yaki sakinta.hannunshi yake kokarin kaiwa Kan kirjinta tayi saurin bige hannun tana Kara tureshi.still yaki cire bakinshi daga cikin nata.

        Cike da jin haushi ta mintsile shi a bayanshi Amma shikam Muhseen baisan tana yiba.saida ya gaji da kanshi kafin ya saketa Yana mayar da numfashi tamkar Wanda tayi gudu.

    Da sauri ta Kara matsawa karshen sit din ganin yadda ya kureta da kallo.

 Saida ya Kara matsawa kusa da ita kafin yayi kasa da muryar shi ya ce “shawara daya ce idan har kinaso na kyale ki to sai kin amince da bukata ta”

   Cike da tsoro ta dago manyan idanuwanta tana Kara kallonshi.jin abinda ya fada.

    Turo dan madaidaicin bakinta tayi tana gunguni.alamar tana son fadar wani abu.

     Cikin wani irin salo da murya Mai cike da amo yaci gaba da cewa “kada ki dauka abinda ya faru tsakanina da ke Ina sane a lokacin da abin ya faru, A a ke kika jawoma kanki nasan ke a nufinki zaki rama abinda nayimaki ko,to bari kiji duk lokacin da kika yi yunkurin ramawa to sai dai ki rame,sannan abu na karshe zan baki zabi guda biyu na farko kodai ki amince ki aure ni,ma’ana ki sanarma da su Unlce Yusuf ni kike so ki aure,ko Kuma kina biyamin bukata ta duk time din Dana bukaci hakan,bazanso jutar dake ba,dukda ba halina ne ba,Amma tunda na dandanaki na kasa jurewa kullun da tunainki nake kwana da shi nake tashi.dukda dai kina kwaila da ke Amma hakanan zanna maleji”

        Cike da mamaki take kallonshi jin irin kalaman da suke fitowa daga bakinshi.a ranta ta ce “Lallai wannan mutumin dan guguwa ne,zanko nunamaka na fika iskanci harni kake fadama haka saboda ka gama sani na ko,Uhmm duk laifina ne”bata karasa tunanin ba taji Yana huramata iskar bakinshi saman fuskarta.

   Runtse idonta tayi ta budesu tar akan fuskar shi.murya cike da tsiwa ta ce “Uhmmm harka bani dariya wallahi to Banda abinka kai kam mezaka yi da kwaila kamata?Ai gani nake yi kwaila ai sai daidai ita,nifa bari ka ji wallahi na tsane ka,Kuma bazan taba sanka ba har abada”

      Saurin taryar numfashinta yayi da cewar “Karya kike yi Seeyama wallahi babu Wanda kike so sai ni,ke bari ki ji nine abokin rayuwarki babu Wanda ya isa ya zauna da ke sai ni”.

Ganin tana kokarin bude murfin motar yayi saurin rungumota jikinshi.yana buga bayanta,cikin cool voice ya ce “Yanzu ba zaki gane abinda nake nufi ba,wallahi Seeyerma bazan iya rayuwa ba saida ke,tun kina karama nake dawainiya da sonki cikin zuciyata,duk abinda zakiga nayi wallahi saboda ke nake yi,ban taba tunanin haka zata faru tsakanina dake ba,Amma kaddara ta riga fata,Dan Allah ki tsaremin kanki kada ki zubar da mutincin ki Dan Allah na rokeki”

    Ji tayi gabanta ya fadi jin zubar hawayen shi saman jikinta.

Dagowa tayi tana kallon shi ganin yadda yake zubar da kolla tamkar karamin yaro.

   A hankali ta ji tausayin shi Yana ratsa bargon jikinta,ita kam tasan wannan itace kaddarar su,Basu da yadda zasu yi sai hakuri.hannu ta saka tana gogemai hawayen .

Gani tayi yayi murmushi har dimple din shi suka lotsa.yatsarta ta saka cikin ramin tana juyawa.

Sosai ta bashi dariya,saiya tuna lokacin tana karama tun bayan an dawo da ita Nageria duk inda zai je tana makale da shi,haka idan zai koma Daura to ranar tayi ya aikin koka harsai tayi rashin lafiya.cikin so da kauna ya manna Mata kiss a goshi Yana bude murfin motar.

   A tare suka fito suka jera zuwa cikin gidan.turus tayi ganin ya Faruk a gaban par din Yana kallonsu.wani haushi ne ya ji Yana tasomai a zuciyar shi ya ce “Lallai na yarda Mata rauni garesu,yanzu nan shikenan har yayi Mata zakin baki,Dukda Seeyey tayi mai bayanin cewa laifinta ne,Amma Koda itama tana son Muhseen to ya kamata ta dan wahalar da shi kafin ta amince da tarensu”ta gefen su ya raba ya wucewar shi.da kallo Suka bishi kafin suka karasa part din.

Jin ana Kiran salla yasa Faruk wucewa zuwa masallaci.

    Ganin sun shigo tare yasa Kaka cika da dinbin mamaki,Dan ita dai taga yayi kusan sati biyu rabonda ya zo garin Koda sunyi waya saidai ya ce zaizo.

  Zaunar da Seeyerma yayi kafin ya wuce zuwa masallaci dan sauke farali.

Yana fita itama ta wuce part din Aunty Hajara.

      “Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un na shiga ukku ni Ameerah wallahi mutuwa zanyi,Ni akeso a wulakanta Aunty Mariya Dan Allah ki taimake ni,wallahi yanzu na Kara tabbatarwa da ita yake so,Kinga fa tunda ya sakata cikin motar shi sun Dade sai yanzu suka fito hannunsu sarke da juna,Niko ko wayata baya dagawa idan na Kira shi saboda kiyayya,Anya kuwa Aunty wannan malamin Yana yimana aikin nan”cewar Ameerah da take durkushe a kasa gaban marikiyarta wato Hajiya Mariya.

    Sororo tayi tana kallonta ganin yadda ta dage bilhakki tana ihun kuka tamkar wacce aka ce uwarta ta mutu.

    Saida tayi kuka mai isarta kafin tayi shiru jin har yanzu Hajiya Mariya batace ko uffan ba.saima aikin Danna waya da take yi.

    Murya cike da fada ta ce “wallahi kedai akwai sakarai,to da kin dauka rabashi da wannan yarinyar abune mai saukin gaske?ko kin manta abinda malam ya fada ne,kaunarta a cikin jikinshi take Yana yimata San dako kanshi baya yiwa.sannan ki sani bake kadai kike harin ganin kin mallaki zuciyar Muhseen ba,akwai wasu,sannan wasu burinsu suga rayuwarshi ta salwanta,to ta hakan kike ganin zakiyi nasara ba tare da kinsha wahala ba?,to bari kiji ni a ganina gwamma ki hakura cikin kwartayen naki ki fitar da guda daya a auramaki,Dan duk ranka kika Kara kwaso cikin shege to sai dai ki haifeshi kinji dai na fadamaki tunda ke bakisan ciwon kanki ba,yooo mazan wannan zamanin kuka biyemasu ba saidai ki lalata jikinki ba,da zarar sunga kin zama bola to zasu tsallake ki su koma wurin wata”,

     Sosai Ameerah taji jikinta yayi sanyi,sai yanzu take ganin wautar da tayi na sakarma kowane sakarai jikinta kamar wata tinkiya, tabbas hakane ita rayuwar bariki bata da wani rana a rayuwa sai dinbin asara da nadama marar amfani,Kuma abin takaicin duk cikin samarin nata babu mai yimata so na gaskiya,ko a watannin baya duk Wanda tace ya fito to zai dai ya zame Yana yimata karyar baiyi kaza ba shiyasa bazai yi aure yanzu ba,runtse idonta tayi tunawa da yadda Suka kwashe da Nurah akan shekaran jiya ta ganshi da wata budurwa a hotel,data yimai magana haka ya zage babu kunya yayimata rashin mutunci harda cewa ai ya gano bada shi kadai take mu’amulla ba to daga yau karta sake ta Kara neman shi tunda ta zama karuwa.

 Da sauri ta runtse idonta tunowa da tayi irin munanan kalaman daya rinka jifarta da su.sai yanzu ta fara gane illar rayuwar bariki,gashi dai yanzu yaci moriyar ganga ya yada koranta.kuma ita ta tashi a tutar babu tunda babu abinda ta karu da shi sai lalata mata rayuwa da yayi.

Sun dade a haka babu Wanda ya sake cewa komai.ita Hajiya Mariya chat take yi da kawayenta itako Ameerah ta fada kogon tunanin yadda rayuwarta ta fara lalacewa baya da wasu shekaru.

Tunda ta hadu da nura a hanyarta ta zuwa gidan wata freind dinta mai suna Nazla, yarinyar sosai Babanta yake da kudi ya taba rike mukanin Dan majalissa na jaha a shekarun baya,Kuma fitaccen Dan kasuwa ne a school suka hadu har suka kulla abota.tundaga nan suka zama kayawaye,da farko tayi tunanin Nazla yarinyar kirkice sai daga baya ta fahimci yarinyar ta kware a wurin bin samari hotel,sai tayi kwana biyu bata koma gidansu ba,dukda bata Shan komai na kayan maye,Amma kullu tana tare da maza wannan dalilin yasa Ameerah ta fara yin baya da tarensu.ganin haka yasa Nazla janyo Ameerah jikinta ta hanyar fara yimata hidima da kudi,kamar hauka haka take yimata barin kudi.ita ko Ameerah tuni ta saki jikinta ganin tana kyautata Mata.

Wata rana sun tashi daga school Nazla ta bukaci Ameerah ta rakata gidan su wata kawarta Bata kawo komai a ranta ba ta bita Suka tafi.

Tunda suka je gidan taga kamar babu mutane a gidan.wata kyakykyawar budurwa ce ta fito tana yimasu oyoyo.cike da murna ta rungumesu tana farincikin ganinsu.

        Cikin falon Suka karasa,anan suka zauna suna hira abinci ta gabatar masu da abin sha.saida Suka gama kafin Wannan kawar ta Nazla ta yimata bayanin bukatar abinda suke nema a wurinta,sosai Ameerah ta tsorata da jin abinda suka fada.

     Jiki na kakkarwa ta mike tsaye tana nuna Nazla da hannunta ta ce “Nazla ashe iskancin ki ba a iya maza ya tsata ba? To ni bazan iya rayuwar wannan kazantar ba Kuma daga yau babu ni babu ke”….kafin ta Kara cewa komai taji Nazla ta watsamata wani abu a fuskarta.

Kafin tayi wani yunkurin ta tafi luuuuuuu ta zube saman kujera.

   A tare suka saka dariya da karfi suna tafawa.

Yarinya an gayamaki Zaki ci kudinmu a banza ne,ai baki isa ba dole Zaki biya abinda kika ci.

    Daga haka Suka ciccibe zuwa bedroom,haka Ameerah tana kallonsu suka gama lalata mata rayuwa bata iya daga Koda dan yatsarta.

   Tun daga ranar Suka sakata a kungiyarsu,wani lokacin takan bi samarinta ko kawayenta.

   Cikin zubar da kolla ta wuce bedroom dinta tana jin takaicin irin wannan rayuwar,lokutta da dama sai taji tana son dainawa Amma da ankwana biyu zasu Kara janyota.addu’a tayi Allah ya shiryesu da duk masu aikata irin wannan rayuwar.

    Tunda ta shigo part din Aunty Hajara take kallonta ganin yadda take faman doga murmushi.

Saman kujerar falon ta zube tana cire mayafin kanta.cike da gajiya ta fara bude ledojin tana nunama Aunty Hajara.ita tayata murmushin tayi ganin yadda take cike da farinciki.

 Cike da tsokana ta ce “Uhmm ni kodai dana ne zai zama sirikin namu,irin wannan hidima haka gaskiya Seeyerma Faruk Yana yimaki so na gaskiya,gafa dukda haka ta faru Amma bai canza komai ba daga kulawar da yake baki saima Kara ninkuwa da tayi fiye da baya”.

      Cike da fara’a Seeyerma ta ce “A a Aunty nifa ba shi ne nake ²⁷

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *