DR MUHSEEN CHAPTER 14 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)

DR MUHSEEN CHAPTER 14 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

  

          📝………………Cike da fara’a Seeyerma ta ce “A  a Aunty nifa ba shi nake nufi ba,Kuma ma ni ba yanzu zanyi aure ba”

   “To Seeyerma idan bakiyi aure ba me zakiyi?komai dadewa wata rana ai dole zaki rabu da mu”

   Zunburo bakinta tayi jin abinda Aunty Hajaran ta ce,ledar kayanta ta dauka ta shige dakin su,tana jin babu dadi a ranta.

Binta Aunty Hajara tayi da kallo tana Kara jin tausayin yarinyar har cikin zuciyarta.

    Tunda ya idar da sallar magriba ya koma part din Hajiya Kaka.Anan ya Kira wayar Ummeey Suka sha hirar su cikin harshen Larabci gwanin sha’awa,Idan Muhseen ya juya harshen shi saika rantse da Allah cikakken Balarabe ne saboda yadda yake kama da su.

      Haka yaba Hajiya Kaka wayar suka gaisa kafin yayimata sallama yana katse Kiran.

   Tundaga ranar ake wasan buya tsakanin Seeyerma da Muhseen, kwata-kwata taki yadda su hada hanya.shiko kullun burinshi ya sakata a idonshi Dan a Yan kwanakin nan so yake ya jita kusa da shi.

  

    Ranar lahadi ya kamata ya koma Amma kin tafiya yayi dukdan ya samu damar ganinta.

   Itako tana sane take boyewa,ko part din Hajiya Kaka ta daina zuwa saboda tasan can ne wurin zaman shi.

   A ranar lahadi ne da yammaci sosai Muhseen ya fito Dan zuwa part din Kaka,harya kusan shiga ya hango samarin kannen nashi suna wucewa zuwa part din Mama.A hankali shima ya juya akalar tafiyar tashi zuwa part din.tun a bakin kofar falon ya fara jiyo hayaniyar su cike da karadi suke ihu wasu na tafi.ga dukkan alamu dai kallo ne suke yi.cike da natsuwa ya tura kofar jikinshi sanye da riga da wando na shan iska masu shegen kyau da daukar ido.

    Babu Wanda ya lura da shigowar shi,sai Hindatu da take tsaye jikin kofar tana hango yadda suke ihu da murnar cin ball din da suka yi.

   Hannuwanshi ya harde a kirjinshi Yana kallonsu one by one,a kalla sunkai su kusan ashirin kama daga manya zuwa kanana,mazansu da matansu.Faruk,Jabeer,Aliyu,su ukku suke zaune a bisa doguwar kujera,sai Sadik,Nurah, isma’il wasu suna sauran kujerun.inda a bangaren mata duk suna zaune saman kyakykyawan kafet sai Zeenat da Rukayya da suke a Kan kujera mai cin mutum biyu.khadijah, Seeyerma dasu Safna duk sun baje kasa. 

    Sosai abin ya bashi mamaki hango Seeyerma da yayi tayi rashe-rashe tana shan icecream kaman wata Yar beby.

    Shiru Aunty Hindatu tayi ganin Yana yimata alamar tayi shiru,tanason yimasu alamar su  natsu, Amma ba yadda zata yi saboda Yana kallonta.

     Tsakiyar falon ya fara takawa cike da jin haushin yadda suka cika gidan da hayaniya kamar wani gidan biki.

     Babu Wanda ya lura da karasowar shi wurin kwatsam sai ganin mutum sukayi ya kashe tv gaba daya suka kalle shi.cike da azama Seeyerma ta nufi dakin Mama da gudu tana haki domin kuwa tasan cewa ita yake nema.tana gaf da saka kafarta ta ji an janyo gashin kanta da tayima dauri a tsakiyar Kai sai jelar da take yawo a bisa bayanta.

Gaba daya ta ji tayo baya alamun zata iya faduwa kasa cike da karfin hali ta fado kanshi.a tare suka sauke ajiyar zuciya,ita tayi ajiyar zuciya ne na jin bata fadi kasa ba,shiko jinta a saman kirjinshi ya saka shi saukewa nannauyar ajiyar zuciyar.

      Kunnenta ya ruko da karfi Wanda saboda zafin da taji saida ta saka Yar tsuwwa ,domin Seeyerma bata so a taba Mata kanta.

   Gaba daya matasan dake cikin falon ido suka zuba masu suna kallon wani sabon salon bariki Wanda sai wanda Suka san Kan soyayya kafin suka iya irin shi.banda Ameerah data runtse idonta jin yadda sautin bugun zuciyarta yake bugawa da sauri-sauri kamar wurin zai tsage.

      Aunty Hindatu saurin Juyawa tayi zuwa dakinsu ganin yadda ya kanainaye ta Yana kokarin yimata kiss,duk yadda taso ya saketa Amma ya kiya.shiko hango Yadda Ameerah take rufe ido yasaka shi yin wani abun.

   Cike da zolaya ya Jabeer ya taso ya ruko hannuwanta Yana cewa “sorry sojanmu ayimata hakuri hakanan,bazata sake ba”.

 Sakinta yayi Ya dungurin kanta tare da cewa “zan kamaki ne zaki gane kuranki”.

  Sakato ya Faruk yayi Yana kallonshi tamkar ba shi ne ya lalata rayuwarta ba,Amma yanzu har wani borin kunya yake yi da barin jiki,yasan karshen zancen zaice ne Yana son Aurenta,to shikam yayima kanshi alkawarin bazai bari haka ta faru ba,Dan yaga alamar Zaiba yarinyar wahala ne.

Tunda ta samu ya Jabeer ya kwaceta ta samu ta sadade tabar cikin falon,dakin Mama ta shige,ganin bata a falon yasa tayi konciyarta saman kujera tana shafa kanta jin yadda wurin yake yimata zafi.A saman labbanta ta furta “Dan bariki kawai,sai Allah ya sakaman,mutum sai mugunta ya iya kato da shi ya rinka cin zalin yara.

    Bayan Seeyerma ta shige dakin Mama shima fita yayi ya koma part din Hajiya Kaka.

Tunda ya koma aiki a washe garin litinin kenan bai Kara waiwayen estate dinba harna tsawon sati biyu.

   Bayan wata biyu,haka rayuwar tayi ta tafiya tana juyawa,dukda suna yawan yin waya da Ummeeyn shi Amma kullun addu’ar shi Allah ya dawo da ita gidan Dadyn shi.

A cikin sati biyu wasu abubuwan sun faru inda a bangare guda sauran sati hudu bikinsu Muhseen kamar yadda aka saka rana .

Wani abin mamaki yadda Seeyerma duk ta Kara zama big girl da ita.saboda irin konciyar hankalin data samu yasa ya saka ta murje abinda tayi shar gwanin kyau.ya Faruk cewa ya rinka yi sai ka ce ita ce Amarya,ita sai bata cewa komai saidai tayi dariya suk lokacin da taji ya ce Haka.

Cike da jarumta ya diro garin yayi dauke da alkawarin zaije ya tunkari Uncle Ahmed da batun ko Kuma ya Kira sarki Abdulkareem ya sanar mai abinda yake damushi danya fahimci Uncle Yusuf da gaske yake bazai bashi auren Seeyerma ba…………….

*Dan Allah kada ku fitar da shi wannan amanace a garemu da ni da ku, Ina fatan zaku kasance masu kishin aljihunku  .Gidan Unlce Yusuf ya fara sauka,ganin ba kowa a gidan sai Aunty Hajara da khadijah.

Ya Jima anan saida ya Sha kunun gyada mai dadi Wanda Aunty Hajara ce ta hama mai shi.

    Fuska cike da yanayin tausayi ya fara shedawa Aunty Hajara kudirinshi nasan a auramai Seeyerma.

Jin haka yasa Aunty Hajara bata yi mamaki ba,domin ta dade da sanin irin kaunar da yake yima yarinyar ko wannan abun daya faru daman ita bata dauki zafi da shi ba.koda taga Mai gidan nata yayi fishi da shi hakuri ta dingi bashi.

     Jin tayi shiru yasaka Muhseen Kara marairaicewa kamar wani karamin yaro.

   “Kayi hakuri Son inata kokarin ganin na fahimtar da Unlce din ku,Amma abin ya gagara to dole sai munbi abin a sannu duba da yadda makiya suke bibiyar rayuwarku,ko aurenka da Ameerah da aka hada akwai wata kullala a kasa,Amma nayima alkawarin insha Allah da Seeyerma za’a daura aurenka”cewar Aunty Hajara Dan tasan So na gaskiya yake yimata,sannan tana da yakinin bin matan banza ba halin shi ne ba.

       Da sauri Hajiya Mariya ta koma da baya jin kamar alamar motsi a kusa da inda take labe.

   Da sauri ta lalubo wayarta daga cikin riga ta fara Kiran wata nomber.

Tana jin an daga ta fara cewa “gaskiya Mama akwai matsala,anya wadannan mutanen zasu bari burinmu ya cika kowa?”

Banji me aka ce ba ta katse wayar,cikin sauri ta koma part dinta.

      Zarya ta fara yi a tsakiyar kayataccen bedroom din nata,Wanda ya Sha kyau harya gaji.

Tunani take yi idan har Muhseen ya fasa auren Ameerah hakan Yana nufin sun rasa damar su ta farko kenan,itama da tayi wannan tunanin Amma daga baya taga rashin dacewar hakan.

     Jin wayarta ta dauki ringing tayi saurin dubawa dan ganin mai kiranta.Hajiya Balaraba ce mahaifiyarta ita ce ta sake kiranta.

     Bayan ta daga Hajiya Balaraba taci gaba da yimata bayani akan yadda sukayi da bokansu na san ganin wannan auren ya kasance.

“Kina jina ko?”cewar Hajiya Balaraba .

“Ki sani ya ce dole mu kiyaye dokokin daya saka Mana inhar muna so aurensu ya tabbata”.

   Jinjina Kai Hajiya Mariya tayi tamkar tana gaban mahaifiyarta ta.

   Haka tayi ta koramata bayanin yadda zasu yi.ita ko sosai ta dauki shawarar mahaifiyarta ta.kafin kowa ya aje waya.

Cikin mintunan da basu gaza biyar ba ta Kira kawarta Laure.sosai Suka tattauna akan lamarin kafin ta sanar da ita zuwanta da yamma.

    Haka ko akayi Hajiya Mariya na fita daga gidan itama Ameerah ta wuce gidan da suke holewar su ita da su Nazla.

      Koda Muhseen ya koma part din Kaka nanma baiga gilmawar Seeyerma ba,harsaida ya gaji da zuba idanu kafin ta tambayi Kaka,inda take sanarmai ai sun fita ita da Faruku.

Wani kololon bakinciki yaji ya tsaya a makoshin shi,wato ya fara lura da take taken Faruk so yake ya dauke shi sakarai.shiko abinda yasa bayaso wani ya aureta idan ya auri Seeyerma to wata rana zai iya goranta mata.shiyasa yake so ta kasance tare da shi har abada.

Yana cikin wannan tunanin yaji sallamar su,Faruk ne a gaba sai Seeyerma na biye bayanshi.ledoji ne dauke a hannuwansu Wanda yake da tabbacin kayan zaki ne.

    Rai bace ya ce “Faruk ba na hanaka siyamata kayan Zaki ba?ko so kake yi ka lahanta ta?to wallahi ka kiyaye ni ka ji na fadama”fuuuuuuuu ya fice daga part din tamkar zai tashi sama.

   Kaka,Faruk dukansu da kallo Suka bishi da shi zuciyoyinsu cike da mamakin wannan lamarin.ajiyar zuciyar Hajiya Kaka ta sauke tana tuno wani abu a ranta.

Shima Faruk ko zama baiyiba ya fice daga estate din.itako Seeyerma uwar dakar Kaka ta shige tana jin babu dadi a ranta ganin yadda ya Muhseen ya dauki fishi da ita.wanka ta shiga saida ta dauro alwala kafin ta fito.

   Safna da khadijah ta gani a Kan gado suna hira.

Kaya ta canza kafin ta zauna tana bude ledojin data shigo da su.

Khadijah ta matsa kusa da ita ganin kayan zaki,Dan itama Khadijah akwai shan zaki.

    Jin Kiran salla yasa Suma su Khadija dauro alwala Suka tayar da salla.

Yau ya kama sauran sati biyu bikin su Faruk da Muhseen da Jabeer inda wasu suke murna,wasunsu ko akasin haka.cikisu kuwa hadda Seeyerma wacce ta rasa dalilinta na jin haushin wannan auren.ko anko cewa tayi bata so,sai Faruk ne ya lallabata kafin ta hakura.a cewarta za’a rabata da Yaya Faruk dinta.dan ita bata ya Muhseen take ba,saboda haryanzu bata Kara saka shi a idonta ba.

     “Wannan wace irin kaddara ce?”

Cewar Zahara’u da take kallon kawarta.d

“Uhm to ni Ina zan sani Banda ke ai kinsan Dr muhseen ya wuce da ajinki,ke bari ki ji dazu na shiga Admin Block office din su oga Haruna naji kamar ana cewa Wai sauran 2 weeks bikin shi”cewar kawar zahara’u Mai suna Aisha….

 Zahara’u da take konce saman wata kujera a cikin dan matsakaicin office din tayi saurin dirowa kasa tana zaro ido waje.

   Cike da tsoro ta mike tsaye tana Kara kallon kawartata da ita kadaice tasan sirrinta.

“Dan Allah kawata idan kinsan wasa ne kike yiman to ki daina,idan ko da gaske kike fada to kiyi gaggawar tayar da ni daga wannan mafalkin Mai cike da takaici”

    Cikin lokaci kalilan saiga hawaye sun wanke mata fuska,sosai damuwa ta bayyana akan fuskarta Wanda ta kasa daurewa har saida ta zubar da hawayen bakinciki..

       Sosai Aisha taji tausayin kawarta ta.domin tasan irin mugun son da take yima Dr muhseen.

Amma dukda haka Zahara’u bata karaya ba daga soyayyar da take yima Dr muhseen saima karuwa da take yi…………²⁹

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *