DR MUHSEEN CHAPTER 16 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)
Www.bankinhausanovels.com.ng
📝………………..Amma ki sani aure a tsakanin Seeyerma da mai gida babu fashi,dukda Ina ganin kanwata Balaraba zataga nayimata rashin adalci,Amma hakan bazai hana ni yanke wannan hukuncin ba”shiru tayi tana sauraren diyan nata ko akwai Wanda zaice wani abu.jin sunyi shiru yasa ta dora da “Inaso wannan ya zama sirri a tsakanina da ku,sannan ba yanzu za’a daura aurensu ba harsai ranar data haihu,sannna banbaku izinin zubar da cikin ba,banaso ayi kisan kai kun ji abinda na fadamaku”.
Kowa jinjina kanshi yayi alamar sunji,kafin suka fara fita da daidaya.ya rage daga Aunty Hajara sai Aunty Aliya,mama ma fita tayi.
A hankali Aunty Hajara ta matsa kusa da tsohuwar ta ce “Hajiya inaso ki bani izini anjima Zan saka akai Seeyerma cikin gari gidan kawata harsai wannan kwaramniyar ta wuce kafin ta dawo”.
Kallonta Hajiya Kaka tayi kafin ta bata amsa da “Idan kina ganin hakan bazai haifar da matsala ba to na baki izini,Allah dai ya Kara rufamana asiri”
Gaba dayansu Suka amsa da “Amin”kafin suka fice daga part din.
Haka ko Aunty Hajara tayi tana fita ta sanar da wata aminiyarta abinda yake faruwa,nan take ta amince.
Wayar Faruk ta Kira cewar tana son ganinshi yanzu,bayan ta katse Kiran derect dakin da su Seeyerma suke ta nufa.a zazzaune ta taddasu wasu na chart wasu na hira.ganin Seeyerma da kwanon danwake a gabanta tana ci sai faman shhhhh take yi tana shan yaji.
Ba tace da su komai ba sai drower ta daga ta fara zuba kayan Seeyerma a cikin troly.saida ta kammala tsaf kafin ta kamo hannunta suka nufi dakinta tana janye da akwatin.sakata tayi ta wanke hannunta.
Shigowar Faruk yasa ta sakamata hijaf tana mikar da ita tsaye,ita dai Seeyerma kallonsu kawai take yi Dan ta kasa cewa komai.
“Gata nan Faruk yi sauri ka kaita yanzu Allah ya kiyaye hanya”cewar Aunty Hajara tana damkata hannun Faruk.
Tare suka fito Yana janye da troly suka shiga motar daya ajeta a kofar gidan.cikin sauri ya tashi motar suka doshi gate.
Safna ce ta kalli inda Khadijah take zaune tana cewa “Wai Ina za’a Kai Seeyerma ne?”.
Caraf Aunty Rukayya ta bata amsa da “To Ina ruwanku magulmata,Aunty Hajara ya kamata ku tambaya saita baku amsa ko?”.
Jin haka yasa Safna ta tsuke bakinta bata Kara cewa uffan ba sukaci gaba da hira.
A daki kuwa suna fita Aunty Hajara ta sauke ajiyar zuciya tana zama bakin gadon.ganin Maigidan nata ya fito daga toilet yasa ta kalli inda yake tana sanar da shi inda ta tura Seeyerma.bai ji komai ba saboda yasan halin Matar shi mutuniyar kirkice.
Tunda suka fita daga estate din cikinsu ba Wanda yayi magana har suka haura babban titin da zai sada su da unguwar GRA,sai a sannan ta kalli ya Faruk tana cewa “Wai ya Faruk Ina zaku Kaini ne?kodai ya tabbata ni ba ahalinku ce ba?”.
Da sauri ya dora yatsar shi saman bakinshi yana shiiiiiiiiii.
Da sauri tayi shiru tana sadda kanta jin yadda gabanta yake faduwa.
Saida taji ya tsaya alamar sun zo kafin ta dago kanta,Bata yi mamaki ba ganinsu a kofar gate din gidan su Hajiya karimatu tasan gidan sosai,domin duk lokacin data aiko ya Faruk gidan to ita take rakoshi,hakan yasa tasan Yan gidan farin sanima kuwa.
Tana wannan zancen zucin ta ji ya bude site din da take Yana cewa fito mu shiga.
Haka ta fito sororo kamar wacce aka cirewa lakka.
Gate din ya konkwasa aka bude,har cikin falon Suka shiga da sallama dauke a bakinsu.
Hajiya Karimatu da saurinta ta taresu suka zauna saman kujerar.cike da ladabi suka fara gaisheta,cikin sakin fuska itama ta amsa tana tambayar yan gidan.
Bayan sun gama gaisawa ya mike zai tafi itama Seeyerma ta tashi zata bishi.karshe dai dakyar suka rabu akan gobe zai zo ya tafi da ita.haka tana ji tana gani ya Faruk ya tafi ya barta.
Kayanta Hajiya Karimatu ta dauka tare da kama hannunta suka nufi wani daki anan kasan falon.
Wata kyakykyawar yarinya ce saman gadon tana latsa system,tana jin alamar shigowa ta juyo tana kallonsu,ai da gudu ta kwasa tana rungume Seeyerma cike da farinciki ta ce ke “seeyama yau kece a gidanmu?
Itama Seeyerma dandanan ta fadada fara’arta ganin Seeham tana nan.
Haka Hajiya Karimatu ta aje turolyn ta barsu nan suna farincikin ganin juna.
Tun a daren Seeyerma ta saki jikinta Suka sha hira da Seeham kafin Suka konta bacci.
Washe gari haka aka gudanar da walima a cikin babban holl din nasu,sosai aka wa’azantar da amaren harma da matan auren dake wurin,haka Suma yan’mata an tabo fanninsu.sosai Ameerah tayi dana sanin irin rayuwar da tayi a shekarun baya,Amma tana tuba ga mahaliccinta akan yadda tayi ta Saba mai.karfe shida aka rufe taro da Addu’a,inda aka raba manyan jukkuna dauke da lemuka da kayan malakushe dangin su cincin da donot,meat five da sauransu.haka kowa ya watse cike da farinciki Amma banda Ameerah dan zuwa yanzu ta fara jin tsoro na rashin zuwan Ya Muhseen,tana jin faduwar gaba tabbas tasan akwai abinda yake shirin faruwa.haka dai ta daure bata sanar da Hajiya Mariya ba har washe garin ranar Asabar.
A GRA kuwa Seeyerma tayi zamanta hankalinta konce,Bata da wata damuwa domin komai na bukatar rayuwa akwai shi a gidan saidai kewar su ya Faruk tana damunta.
Tunda safe da Maheer ya shigo cikin gidan nasu dan yin breakfast ya kyallara idonshi akan Seeyerma aiko nantake ya rude ganin wannan kyakykyawar halitta har a cikin gidansu.
Duk yadda Hajiya Karimatu taso ta takama dannata birki akan maganar Amma abin ya gagara.yana ganin Dadynsu ya sauko kasa aiko ya sanarmai.Dady cewa yayi ya kontar da hankalin shi insha Allah zai nemomai aurenta.
A estate kuwa da misalin karfe sha biyu na rana a babban masallacinnsu al’umma suka shaida daurin auren Faruk da Hindatu sai Jabeer da Rukayya,akan sadaki mafi karanta domin neman albarkar aure.
Sosai mutane suka yi mamaki jin ba’a daura auren su Muhseen ba,Alhaji Muhammad baice komai ba kasancewar kannen shi sunyimai bayanin abinda yake faruwa,bai tayar da hankalin shi ba saboda yanzu asirin da Hajiya Mariya tayimai ya fara sakinshi,Wanda idan a watannin baya ne to da sai yayi rigima da Yan”uwanshi.suma su Uncle Yusuf sunyi mamaki.
Itako Ummeey da Aunty Hajara ta sanar da ita a waya batayi mamaki ba domin haka al’amarin Allah yake yakan anshi addu’ar bawansa a lokacin da bai tsammata ba.Amma tagirgiza jin cikin dake jikin Seeyerma saidai Basu da yadda zasu yi haka Allah ya kaddara masu dole su anshi kaddarar rayuwar su.
Tun bayan an idar da daurin aure Faruk ya Kira Muhseen Yana sanar da shi yadda al’amari ya kasance.tsabar jin dadin abun cewa yayi “Insha Allah nasan Seeyerma ita ce Mata ta”
Sosai yaba Faruk dariya ya fara janshi da wasa Yana cewa “Idanfa wani ya rigaka fa?”.
Da sauri ya amsa da
“Kaga banason iskanci ka ji ko,yauwa Dan Allah kacema Aunty Hajara ta turoman nomber Hajiya Karimatu inason jin muryar Dear”cewar Muhseen Yana jin wani sabon farinci ya lullube shi.
Da haka Suka katse call din zuciyar kowa fes.
A part din Hajiya Mariya kuwa lokacin da wannan labari ya riskesu ita da Ameerah haukane kawai Basu yi ba,musamman Ameerah da aka caba Mata ado ga kawayenta suna tare da ita.haka ta dinga ihu da birgima tana cewa “Shikenan sun raba Ni da shi,sun tonaman asiri ni Ameerah ya zanyi da rayuwata?”karshe dai haka ta rinka Suma ana faman yayyafa Mata ruwa.
Itama mahaifiyar Ameerah ta shiga damuwa,musamman data fahimci irin kawayen da diyarta take mu’amulla da su,anan ta fahimci diyarta tayi gadonta a yawan bin maza.sai a ranar ta ji nadamar abinda ta aikata ta kamata,sosai ta boye kanta a wani daki tasha kukanta.
A part din Kaka kuwa sosai danginta Suka ji dadin faruwar wannan al’amari,domin sun Dade da sanin cewar Balaba bata kaunar Ahalin Hajiya kaka,ko Auren Hajiya Mariya da Dadyn Muhseen sunsan wani minafirci ne aka hada,Amma Allah ya fisu da sannu zai kubutar da su daga sharrinsu.
Haka wannan estate ya kasance a ranar part din Mama,Aunty Hajara da part din Kaka anata hidimar biki hankalinsu konce,Amma bangaren su Hajiya Mariya tamkar ana zaman makoki haka suka koma,wasunsu duk sun koma gidajen su,daga ita sai Mahaifiyar Ameerah.
Itama Ameerah wasu kawayen nata duk sun gudu,Daman ganin kwakwaf ya kawo su Kuma sun bawa idonsu abinci.
Ya rage daga ita sai Nazla da abokiyar harkarsu Ihsan,wacce sudai sunji dadin faruwar hakan domin daman basuso tayi aure ta barsu anan.dan sunyi alkawarin Koda tayi aure to ba zasu fasa bibiyarta ba.
Nan sukayi ta yimata hudubar shedan akan ta kontar da hankalinta tunda da kuruciyarta kada ta wani damu,kwai ta saki jikinta ta mori rayuwarta Koda daga bayane ta samu miji sai tayi aurenta kawai.
Haka sukayi ta zama har bayan magriba kafin suka yimata sallama suka tafi.
Kai a wannan ranar Ameerah taga takaicin duniya,Koda tayi ta Kiran wayar Muhseen kin yin picking yayi,a karshema daya gaji da yawan Kiran sai yayi switchup na wayar yayi konciyar shi.
Haka Ameerah ta konta tana ta kukan takaici yadda lokaci daya komai ya tsaya Mata chak.
Da misalin karfe takwas da rabi aka Mika amaren gidajensu bayan sunsha nasiha daga iyayen nasu . Nan gidajen suke a cikin estate din.can layin baya suke gidajen su a jere gwanin sha’awa.gininma iri daya ne,harta kayan daki da komai iri daya aka yimasu.part din da za’a Kai Ameerah kuwa sai rufeshi aka yi…………….
..Bayan kwana biyu da Kai amare gidajensu duk sauran yan biki kowa ya koma gidajenshi lafiya,sai wadanda baza’a rasaba an barsu da gyaran gida da sauran ayyuka.
Faruk ne ya shigo part din Auntyn Hajara da basket a hannunshu.
Su Khadijah ne ya tadda da Safna suna breakfast.
Cike da girmamawa suka gaishe shi,saida ya zauna kafin ya amsa gaisuwar.
Cike da gulma khadijah ta bakinta saitin kunnen Safna ta radamata “ki kalli ya Faruk yadda yayi wani fresh da shi,kwana biyu da angoncewa kamar ba shi ba ne yake wani fiskewa irin bayaso din nan”.
A hankali suka saka dariya,duk abinda suke Yana kallonsu ta kasan idonshi Kuma ya fahimci gulmar shi ce suka yi.
Cikin tsawarwa ya ce “ke uban me kuke cewa ne? Munafikan yara”.
Fiki-fiki sukayi da idanuwa alamar rashin gaskiya,suna gimtse dariyar su.
“Ku baceman da gani Kona Zane ku yanzun nan,Yan jarirai da ku Amma kun iya gulma da cigididi”
Ai tun kafin ya rufe bakinshi Suka kwasa da gudu dakinsu suna sakin dariya.
Shima murmushi yayi Yana shafa dan madaidaicin bakin sajen shi Wanda yake bala’in birge Hindatu,Dan indai suna tare to tayi ta tabawa,takance batason wata ta kwacemata shi saboda tasan sajenshi yana daukar hankalin yan’mata.
Da sauri ya juyo Yana kallon Aunty Hajara da take kokarin fitowa daga kitchen.
“A lallai Faruk shi ne ka fito da kanka maimakon ka bari su Khadijah su kawomaku”.
Daidai tana aje wani basket din a kusa da shi.
“Kodan gwamma da kazo da kanka dan Khadija sunce bazasu Kara zuwa ba,Wai korosu kayi”
Sosai yayi dariya jin sharrin da khadijah tayimai.kawai fa sunyita knowking ne yaki budewa saboda lokacin suna soyewarsu,saida yazo ta bude yaga sun zunbiri Baki shi ne suka ki shigowa.
“Hmmmm Aunty khale deeejah tsegumi ne da ita”cewar shi Yana mikewa tsaye,basket din ya dauka Yana Kara cewa “Aunty yaushe zan dauko Seeyerma ne”.
“To Faruk bari anjima na Kira Hajiya kaltume idan munyi magana na sanarma,Dan jiya Son ya Kira yake cewa a bari ya dawo sai ya daukota”.
Amsawa yayi da “to ba matsala,Allah ya dawo da shi lafiya”.
Amsawa tayi da “Amin”
Shi Kuma ya fice dan kaimasu kayan breakfast.
tun karfe takwas su Hajiya Mariya suka fita daga estate din ita da Ameerah da mahaifiyar Ameerah.sunyi alkawarin tarwatsa wannan Familyn tunda har su aka yiwa wulakanci irin haka,dansun fahimci Daman an shirya wulakantasu.ita dai Ameerah jinsu kawai take yi domin kuwa tasan ta riga data rasa ya Muhseen har abada,Daman ba kaunarta yake yi ba Yanzu addu’arta Allah yasa ta samu Wanda yake sonta itako zata aure shi,danta fahimci su Nazla ba kaunarta suke yi ba tunda suke bata shawar banza.
Tana cikin wannan zancen zucin ta ji motarsu tayi parking.
Dago kanta tayi dan ganin garin da suka zo.wani kunkurimin daji ne ta gani mai dauke da dogayen bishiyoyi.ganin duk sun fita daga ita sai Driver ya rage da motar shiyasa itama cikin sanyin jiki ta bude murfin motar ta fito.
Bayansu tabi ganin sun doshi wata siririyar hanya Mai cike da yashi.
Haka sukayi ta tafiya bamai cewa kowa komai har suka kawo bakin wani bukka mai dauke da rufin zana irin na mutanen kauye.gidan shi kadai ne a cikin dajin.
Tun kafin su shiga Suka fara jiyo Amon wata katuwar murya tana tashi.nan take tsoro ta fara kama Ameerah a ranta ta ce “oh ni Ameerah yau inane muka zo”ji tayi ana cewa su shiga.
Tunda suka shiga Ameerah ta rabe jikin Hajiya Mariya tana rufe idonta saboda bata son tana kallon wannan mummunar fuskar ta wannan mutumin.
Mahaifiyar Ameerah ta bude baki zata fara yimai bayani yayi saurin dakatar da ita Yana cewa “nasan abinda ke tafe da ku,to zan sanar da ku gaskiya kodan ku samu damar aurar da diyarku ga wani,Amma ba wannan yaronba Sam ba mijinta ba ne,baya sonta Kuma babu aure a tsakaninsu”Yana Kai karshen maganar ya saka wata muguwar dariya mai tsoratarwa.da sauri Ameerah ta kwakume Hajiya Mariya tana jin faduwar gaba,a ranta ita Daman ta hakura da ya Muhseen.
Cikin sauri Hajiya Mariya ta ce “to boka so nake yi a raba shi da waccen shegiyar yarinyar,tunda har diyarmu bazata aure shi ba to ya zama dole ya rabu da waccan”.
Wata kwarta ya janyo Yana zagaye hannunshi tare da yin wasu kalamai Wanda bazaka iya fahimtar abinda yake fada ba.
Cikin kakkausar murya ya na dubansu ya ce “yarinyar da kuke magana akanta yanzu haka tana dauke da ciki Wanda kuma wannan cikin na shi yaron ne”kwayar dake gabanshi ya turamasu.lekawa sukayi ganin Seeyerma tana fesa turare.
“Amma yarinyar bata gidan”cewar Hajiya Mariya tana duban gidan Dan tasan wannan ba cikin estate ne ba.
“Yanzu zata sauko kasa daga saman benen nan,Dan haka ku fadi abinda kuke so ayimata”.
Cike da cin haushi Hajiya Mariya ta ce “kawai so nake yi a kasheta,ko nawa ne Zan baka kada ka damu burina nidai na daina ganinta”.
Cike da kwadewa ya fara wasu surutai Yana wani abu.kallon kwayar kawai suke yi.
A GRA kuwa kasancewar da asuba dakyar Seeyerma ta tashi ta gabatar da sallar Asuba saboda yadda take ta faman yin hamma ,Jin wani nauyin bacci daya saukomata.
Tana idarwa ta haye bisa gadon ko doguwar addu’a kasa yi tayi saboda yadda idonta yake rufewa.
Itace bata farka ba sai around 11,cikin sauri-sauri tayi wanka ko mai bata tsaya shafawa ba sai turare data fesa,doguwar riga ta saka marar nauyi ta nufo hanyar kada zata sadata da falon kasa.
Tunda ta taho ta matakalar benen yake kallonta,kur yayi da idonshi Yana yimata kallon kurulla Wanda ita sam bata lura da hakan ba .
A daidai wannan lokacin ne boka ya buga wani karfe a ciki ruwan kwaryar dake gabansu,Wanda su Hajiya Mariya suna ganin komai akan idonsu.
Kanshin da taji ya daki hancinta yasa ta daga kanta tana kokarin hango dinning table din.tuni yawunta sun tsinke,Amma kafin ta hango sai ji tayi gaba daya ta taho kasa da kanta,haka ta fara mirginowa daga saman benen tana gangarowa kasa.
Maher ya fara tsabura da sauri ya rugo wurin,daidai lokacin ta saki wani Kara mai rikitarwa jin ta fado kasa a rufda ciki.
Kaicho Maher cike da tausayi ya rungumota jikinshi,ko jinin dake zuba ta kasanta bai gani ba haka ya kwakumeta cikin jikinshi.
Daidai nan su Hajiya karimatu suka karaso wurin,Dadyn majer ne yayi saurin cewa “Daukota bari na janyo mota muje asibiti”ya fice daga falon.
Seeham kuwa banda kuka babu abinda take yi.sosai ta tsorata kada dai ace yarinyar mutane ta mutu a hannunsu.
Maganar Dady ta dawo dasu,cike da azama Maher ya dagata cak suka nufi bakin motar.
Shida Hajiya Karimatu Suka shiga sit din baya suna rungume da ita.
Sai Dady ya zauna mazaunin direver Seeham tana gefen shi.
Saida sukaga fitar du daga gidan kafin ruwan dake cikin kwayar ya dawo wani hayaki yake tashi daga cikinta.
Wani hadadden privet Hospital suka nufa.cikin gagagwa aka shiga bata taimako.haka suka zauna a waje sai Hajiya Karimatu da take faman Kai komo a gaban kijerun ,gaba dayanta a rude take ita dai addu’ar ta Allah yasa kada yarinyar nan ta rasa ranta Dan Bata san ya zata sanar da Aunty Hajara ba.
Gaba dayan su suka nufo Doctor din data fito daga dakin da aka shigar da Seeyerma da alamun damuwa dauke a fuskarta.
Rige-rigen tambayar ta suke yi wane hali take ciki.
Cikin jimami Doctor din ta kallesu ta fara da cewa “please and please kuyi hakuri Allah ya……………..?³³