DR MUHSEEN CHAPTER 17 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)
Www.bankinhausanovels.com.ng
📝………………Cikin jimami Doctor din ta kallesu ta fara da cewa “please and please kuyi hakuri Allah yayiwa cikin jikinta zubewa ita kuma muna kokarin ceto rayuwarta insha Allah zata farfado”.
Da karfi Hajiya Karimatu ta sauke ajiyar zuciya jin bayanin da Doctorn tayi.
Da sauri Maheer ya kalli momyn tashi fuskarshi dauke da mamaki.a ranshi yake mamakin wannan yarinya za’ace tana da ciki,no onder shiyasa yaga kyawunta yayi yawa.
Saman kujerun suka koma.sosai Seeham taji dadi jin kawarta tana da rai.
Sai a sannan Hankali Hajiya Karimatu ya dawo jikinta ta tuna ta baro wayarta da zata sanar Aunty Hajara halin da ake ciki.
Lokacin su Hajiya Mariya harsun juyo garin katsina.ita dai Ameerah duk a tsorace take sai yanzu take jin babu dadi da suka saka aka kashe Seeyerma.har suka shigo estate din kuka kawai take yi.
Akalla su Momy sun dauki tsawon awa guda suna zaman jiran likitocin dan jin halin da yarinyar mutane take ciki,cike da tsoro ta kalli Maheer ta ce mai “Son yi sauri kaje gida ka daukoman jakata da waya,ya zama dole na sanar da iyayenta somin suzo kada wani abu ya faru”.
Cike da ladabi ya amsa kafin ya fice.
Bai dauki wani tsawon lokaci ba ya dawo,kasancewar tare suka fita da Dady ya aje su a company saboda suna da meeting.
Nan take Momy ta Kira Aunty Hajara ta fara sanar da ita halin da ake ciki.
Tashin hankali Wanda ba’a saka masa rana, danda nan Aunty Hajara ta rude.katse Kiran tayi bayan ta tambayeta asibitin da suke.
Wayarta ta dauke da jaka sai tana saka hijaf dinta da sauri ta nufi part din Mama tana zubar da kwalla.
A tare suka fito da Mama bayan ta Kira wayar Faruk da Jabeer.
Su hudu suka dunguma zuwa asibitin a bisa Umarnin Uncle Yusuf da yace su je gasunan zuwa.
Ba Wanda ya sanar da Kaka saboda Yana yin jikinta,any time hawan jininta yana iya tashi.
A reseption suka tadda
Momyn su Maheer tana ganinsu suka mike tsaye.dukda Aunty Hajara aminiyarta ce Amma bata ji dadin faruwar wannan al’amari ba.
Ya Faruk ya fara cewa “Momy Allah yasa ta farfado,ya akayi haka ta faru?”.
Cikin damuwa Momy take yimasu bayani abinda ya faru.suna cikin tattauna maganar ne Doctors din suka fito suna goge zufa saboda dadewar da suka yi a kanta.
Dukansu sukayi saurin tarar su,cike da sauri Doctor din yake tafiya Yana sanar dasu su same shi a office zai yi magana da su yayi gaba.
Bayanshi suka bi zuwa office din.
Saida ya kammala rubuce rubuce a file din kafin dago kanshi bayan ya cire glass din dake manne jikin idonshi.
“Ehm Masha Allah cikin ikon Allah munyi nasarar samota,sai dai an rasa cikin dake jikinta,sannan tana bukatar hutu da kulawa kafin zuwa wasu kwanaki,yanzu da mun sakamata Karin jini kada Wanda ya shiga inda take sai bayan ta farka,but kuna iya aje mutum daya Wanda zai kula da ita”.
Sosai suka yi hamdala ga Allah subahanahu wata’ala daya ceto rayuwar marainiyar Allah.
Faruk, Mama,Aunty Hajara sosai Suka ji dadi jin wannan kaddararren ciki ya zube finally yanzu komai zai daidaita insha Allah.
Haka suka fita Dan komawa gida kafin da yamma su dawo.
Faruk ne zai biya kudin magunguna Hajiya Karimatu ta hana su suka biya kafin suka wuce.bayan anbar Aunty Hajara domin ta kula da ita.
Direct Mama part din Kaka ta nufa bayan motarsu ta tsaya a parking space.
A Falo ta tadda ita tana dama fura a cikin silba.
Kallo daya Hajiya kaka tayiwa Mama ta fahimci akwai abinda ke faruwa.
Gaishe da ita ta fara yi kafin cikin tsoro take sanar da ita abinda ya faru.
Da farko Hajiya Kaka hamdala ta yi jin labarin zubewar cikin,domin tasan halin Hajara mutuniyar kirki ce baza’a hada baki da ita ba har ayi sanadin zubar da shi.tasancewa wannan mukaddari ne daga Allah.
“Ba komai sai muyi addu’ar Allah ya bata lafiya ya tashi kafadunta”cewar Hajiya kaka.ta Kara da cewa “Anjima Jabeer yazo ya kaini na dubota,idan an sallameta Ina so a dawo da ita nan”.
Cike da ladabi Mama ta ce “to insha Allah za’a dawo da ita”.
Da haka ta koma part dinta dan yin girkin da zasu koma asibitin da shi.
Su Faruk da Jabeer kuwa tun shigowar su a masallaci suka sauka dan gabatar da sallar azahar.sai Bayan sun koma gidajen su suka sanarma da matansu rashin lafiyar Seeyerma sosai su Hindatu suka yi jimamin lamarin.
Zuka hau shirin zuwa dubiya.
Saida Seeyerma ta kwashe awa daya ba tare da tasan inda kanta yake ba kafin ta fara alamun motsawa.A hankali ta fara motsa yatsun kafarta tana jin kanta yayimata nauyi.
Da Aunty Hajara ta fara lura da yadda take motsa kafarta,cikin sauri ta Kara matso da kujerarta jikin gadon,cike da kulawa ta ruko hannunta Wanda babu kanula a jikin shi ta kuramata ido ganin yadda fuskarta tayi fayau alamar tana jin jiki.
Tana fara bude idonta tayi saurin rufesu ganin yadda take ganin wani dishi-dishi kamar Yana ta rufemata ganinta.
Cikin sanyi Aunty Hajara ta fara Kiran sunanta Seeyerma! Seeyerma!!
Cikin kasa buda bakinta tayi sai “Uhhmm”kawai data ce.
Bacci ta Kara komawa jin bazata iya tashi ba.
Iskan fankar ta karamata ganin yadda take zufa……. Aunty Hajara ta dade a zaune tana kallonta ganin yadda duk fuskarta tayi wani fayau ta Kara haske.
Bayan ta gabatar da sallah ta fara kokarin Kiran wayar Muhseen,Amma sai ace babu service hakura tayi tana jin babu dadi a ranta kamar zai ga anki sanar da shi.
Tana nan zaune ta ji motsi alamun za’a bude kofa.bakin kofar take kallo ganin su Mama ne suka shigo yasa ta mike tana janyomasu kujreru.
Tambayar ta Suka yi ya jikin nata,ta amsa “Da sauki Amma tunda ta farka saita Kara komawa”
Sallamar wata Doctor yasa dukansu suka juya tare da amsa sallamar.
Karin ruwan ta ciremata tare da yimasu bayanin yadda zasu bata magungunan.
Bayan fitar Doctor din Seeyerma ta Kara farkawa,a wannan karon sosai ta ji idonta ya bude tana ganin mutane.hakan yasa ta fada kokarin tashi zaune,da sauri Faruk ya tallafota ya zaunar da ita tare da saka Mata filo a bayanta yadda zata jingina.
Kasa kallonsu tayi sai sadda kanta kasa da tayi tana jin yadda mararta take murdawa.sannu suka yimata,Amma sai dai ta gyada kanta.
Aunty Hajara ta shiga toilet ta hadamata ruwan wanka masu dan gumi ta ajemata makilin da brosh sai sabon pant da part danta kintsa jikinta.
Kamata tayi a hankali suke takawa zuwa cikin toilet din,saida ta shigar da ita kafin ta dawo.
Sama-sama suke dan taba hira tsakanin Mama da Aunty Hajara akan irin boren da Hajiya Mariya taje tayi a part din Hajiya Kaka na Wai ba’a sansu tana nunamsu Yan ubanci danba daki daya suka fito da Mahaifiyar su ba.haka dai sukayi rashin kunya abun babu dadin ji.shi dai Faruk baice komai ba Dan hankalin shi Yana Kan matar shi yasan yanzu ta idar da abincin shi take jira su taho tare.
Cike da ladabi yake tambayar su Aunty Hajara cewar “ko an sanar da Muhseen dan yau sauran sati biyu su dawo daga mai duguri,Kuma dareta gida zai taho”
“Wallahi kaga tun dazu nake faman Kiran wayar shi bata shiga”cewar Aunty Hajara.
“Tau ba matsala bari na je zan dauko Hindatu,zanyi tray nomber ta shi idan ta shiga zan sanar mai”
Bayan sun amsa mai kafin ya fice ya nufi gida.
Ita ko Seeyerma tunda Aunty Hajara ta barota a toilet din take tsunne,dakyar ta samu tayi wankan jin yadda ruwan yake da gumi,brosh tayi kafin ta gyara jikinta da kayan da ta gani a ratayi jikin karfen.
A hankali take daga kafarta harta fito daga toilet din.cikin sauri Aunty Hajara ta kamota ta zaunar da ita bisa gadon tana Kara yimata sannu.
Basket din da Mama ta shigo da shi ta fara dagawa,ganin farfesun Naman kaza ne yasa ta dauko dan madaidaicin plate ta juyomata shi.gabanta ta janyo kurjera tana mikamata plate din kazar.
Ita take bata a baki tun tana jin babu dadi haka dai ta daure take ci,sosai ta ji dadin dahuwar jin yadda ya ji tarugun da tafannuwa sai kanshi ke tashi.
Girgiza kanta tayi jin takoshi.
Lemun abarba ta tsiyaya Mata a cup ta mikamata.
Shima ta Sha sosai saboda yadda yake sa sanyi.
Da kadan kadan ta rinka bata maganin saida ta Sha kowanne kafin ta gyara mata zamanta.
Zuwa bayan la’asar dakin ya cika da dangi,haka Suma su Momyn Maher sunzo da kayan abinci hadi da kayan marmari.
Suna cikin hirar wayar Aunty Hajara ta dauki ringing,ganin sunan Muhseen yasa ta fita waje saboda yadda dakin ya kaure da sururtu ganin Seeyerma ta saki jikinta kasancewar daman bata ji jiki ba,kawai jini ne data zubar shima yanzu tunda aka Kara Mata wani ta ji karfin jikinta sosai.
“A a son bana so ka tayar da hankalin ka,yanzu ta samu sauki hirama ake yi da ita zuwa lokacin da zaka dawo insha Allah komai ya daidaita”cewar Aunty Hajara da take tsaye gaban barandar block din da aka kontar da Seeyerma.
Yadai amsa da to,Amma shi harga Allah hankalin shi bai konta ba,zai Kira Hajiya Kaka yasan ita ce zata zartar da hukunci yasan Kuma shi Dan gaban goshinta ne.
Cewa yayi ta ba Seeyerma wayar suyi magana.
Amsawa tayi da to ta juya zuwa cikin dakin.
A kunnenta ta karamata wayar tana cewa “Anshi zaya duba ki”
Turo Dan karamin bakinta tayi tana kallon Maher ganin yadda shima ya tsareta da idanuwa.
Lumshe idonta tayi jin sassanyar voice dinshi ya daki kunnenta.
“Dear ya jikin naki”
Kasa cewa komai tayi sai lumshe ido da take faman yi.
Cike da so da kauna ya sake cewa “Wallahi ko Idan Ina magana kina yiman shiru to zan hukunta ki,Kuma kinsan hukuncin da zanyimaki”
Tar tayi saurin bude idonta still haryanzu idon Maher Yana kanta.
Cike da sanyi ta ce “Da sauki”
Daga haka tayi shiru tana sauraren shi.
Harya kammala maganganun shi bata Kara cewa komai ba,yasan zuwa yanzu kila haushin shi take ji,Amma Bari yayi mata uziri shi zai koyar da ita yadda zata so shi.
Katse Kiran yayi Yana kallon yaran shi da ya shigo dakin nashi.
Uniform din daya kawo mai ya amsa.
Jin ya katse Kiran ta aje wayar tana Kara yin kasa da kanta.
A cikin kwana biyu Seeyerma ta ji sauki sosai, yan’uwa duk sun zo dubata ciki harda Kaka wadda Jabeer ne ya kawota.
A washe garin rana ta ukku ne da yamma aka sallame ta suka koma gida.
A part din Hajiya Kaka aka ajeta sai dai Aunty Hajara takan zo ta bata abinci da maganinta.
Ranar da aka maidota washe garin ranar juma’a bayan an idar da sallar juma’a mutane suka shaida daurin auren Muhseen da Seeyerma bisa Umarnin Hajiya Kaka. akan sadaki mafi karanta domin neman albarkar aure.
Wasu sunyi mamaki wadanda suka San da maganar kuwa hakan bai basu mamaki ba.
Innalillahi zo kuga tashin hankali da jaraba a gurin su Hajiya Mariya,wato sai yanzu suka fahimci munaficcin da aka hadamasu,su sun dauka Seeyerma mutuwa tayi jin ance tana asibiti rai a hannun Allah,wato su za’a ha’inta a munaficcesu.
Haka Hajiya Mariya ta ja hannun Ameerah Suka nufi part din Hajiya Kaka.rashin kunya suka yi ta zubamata ba Wanda ya ce da su kala.saida Suka gama tas kafin suka juya dan fita daga falon.
Turus suka yi ganin Dadyn Muhseen a tsaye Yana kallon su.
Rai cike da bakin ciki ya ce “Daga yau babu ni babu ke tunda har bazaki iya daratta mahauciyarmu ba to ki je na sake ki saki ukku”.
Ai nan take Hajiya Mariya ta zube a sume itako Ameerah kururuwa ta saka ganin marikiyarta a kasa rai a hannun Allah.
Wayarta ta dauko ta Kira Hajiya Balaraba ta sanar da ita halin da suke ciki.bayan ta gama wayar haka ta dauko ruwa tana yayyafa Mata kafin ta samu ta farfado.
Haka suna kuka suna komai suka koma zuwa part din su Dan tattara kayansu.
Bayan sun fita ne Alhaji Muhammad ya kalli mahaifiyar tasu ya fara cewa “kiyi hakuri Allah yasa hakan da nayi bai bata ranki ba,saboda yadda na yanke hukunci ba tare da izinin ki ba”.
Cike da jin dadin yadda babban Dan nata ya sauya alamu sun nuna sihirin da suka yimai ya karye.
Dauke da murmushi ta kalleshi ta ce “Kada ka damu Dana Allah yayimaku albarka hakan da kayi shi ne ya kamata kowane da yayi a lokacin da aka wulakanta mahaifan shi,Dan haka sai muci gaba da Addu’ar neman tsari tsakaninmu da makiyanmu”.
Gaba dayansu suka amsa da “Ameen”.
A part din su Hajiya Mariya kuwa suna kuka Suka hada kayansu,motar da Alhaji Muhammad ya siyamata suka hau,gidan Hajiya Balaraba suka nufa,zuciyarsu cike da bakinciki.
Washe garin ranar Asabar da yammaci sosai Seeyerma tana konce a bedroom din Hajiya Kaka wayar Ya Faruk ce a hannunta tana game,tunda ya shigo ta amsa saboda ta gaji da kallo a tv,kasancewar Kaka ta nufi cikin garin ita da shi zai kaita wani Islamic center Dan amso magunguna da nata dana Seeyerma .
Motsi ta fara ji a falon tayi tunanin su Khadijah ne Dan haka ta ci gaba da game dinta tana jin Nishadi.
Shiko Muhseen da yanzu ya shigo falon,fura ya fara daukowa a fread kafin ya nufi cikin bedroom din,Dan a tunanin shi Kaka tana ciki.
A hankali ya tura kofar dakin zuciyar shi cike da farinciki,Dan tun jiya da Faruk ya sanar da shi batun daura auren shi da Dear tun daga nan hankalin shi ya dawo gida,ko bacci kasa yi yayi shiyasa ya biyo jirgin karfe Sha daya ya taho gida.
Tsayawa yayi Yana kallon mazaunanta da suke cike cikin siket din, rufda ciki take tana danna waya alamar kacokan hankalinta baya wurin.
furar ya aje kafin ya fara nufar bakin gadon cikin tafiyar shi ta kasaita,bakin danyan boyal ne a jikin shi wanda yake kalli da daukar ido,bai saka hula ba sai sumar shi data sha gyara tana faman daukar ido.
Cike da natsuwa ya sadda jikinshi samanta Yana sauke ajiyar zuciya.
Cikin firgici Seeyerma tayi saurin juyowa,Amma kasawa tayi saboda jin yadda yayi saurin sakarmata nauyi.lamo tayi tana mayar da numfashi.
A hankali ya birkito da ita ya zama suna fuskantar juna.waro eyes dinta tayi ganin ya Muhseen ne,cike da mamaki ta bude da niyyar cewa yaushe ka zo.amma sai wuffffffff………….