DR MUHSEEN CHAPTER 18 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)
Www.bankinhausanovels.com.ng
📝Wuffffffff yayi saurin rufe mata baki da nashi,hakan yasa dole tayi shiru tana lumshe idonta.
Sun dade a haka kafin ya zare bakin shi yana mayar da numfashi,saurin juyamai baya tayi dan ji tayi tana jin kunyar hada ido da shi.
Murmushi yayi ganin yadda ta juya bayanta.saurin tashi yayi daga saman gadon jin motsi alamar wani zai shigo bedroom din.
“La’ila ha’illallahu muhammada rasu lillahi (S A W), Ohhhhhh ni maryama naga jaraba,Kai wannan yara baku da kunya yanzu mai gida daka shigo ko ni bazaka nema ba sai dai ka shigo ka hau lalube yarinya,Wallahi shiyasa yanzu haihuwar kwanika tayi yawa saboda ku jarabarku tayi yawa”maganar Kaka kenan da tayi tsaye jikin kofar bedroom tana surfa masifa.
Cikin sauri Seeyerma ta Kara saka kanta cikin filo tana boyewa,a ranta tana cewa “yanzu Shikenan ya jaman mitar yar tsohuwar nan,Kai ita kam gwmma ta koma part din Aunty Hajara nan zai fiyemata saukin zama”
Tsabar takaici yasa Muhseen yayi tsaye Yana kallon Hajiya Kaka da take kunfar baki.
Jin tayi shiru alamar ta idar da fadan.
Kallonta yayi murya cike da shagwaba ya ce “Ohhhh ni Matar wannan duk kishin ne,to kinsan dai ke tsohon jini ce,gwamma kiyi hakuri tunda nayi sabuwar mata to sai ki dau hakuri,Dan Ni bazan tafi ba sai kun bani matana kafin nabar garin nan”.
Rike baki Kaka tayi tana kallon wannan tijara ,kasa cewa komai tayi ganin ya sake haurawa saman gadon Yana kokarin tallabota.
Da sauri ta fice tana kunfar baki.
“Maigidan badai ni kake yiwa rashin kunya ba,to zan raba auren Naga ta kaniya, marassa kunya,itama munafika zata fito ta tadda ni,tana so tana kaiwa kasuwa”.
A falon ta zauna tana kunna kallo.
Yana ganin ta fita yayi saurin cewz “Dear zamu tafi Daura ko?kinga ko aikin bamu karasa ba na taho saboda farincikin dana ji na batun auren mu”.
Haushin maganar ta ji “wato ko dubata bazai yi ba kawai burin Shi ya tafi da ita,to ita babu inda zata bishi”Duk a zuciyata take wannan maganar.
Jin tayi shiru yasa ya rungumo West dinta Yana shinshina wuyanta,jin wani kanshi mai sanyi Yana tashi.
Ita dai bata ce komai ba,mikewa yayi ya fito falon.
Kusa da Kaka ya zauna Yana cewa “Kakata ta kaina Dan Allah ki bani fura na sha Ina jin kishirwa”.
“Au sai yanzu ka tuna da ni,ai nayi tunanin ta baka furar ka Sha”.cewar Kaka tana harar shi.
Murmushi yayi Yana mikewa saman kujerar.
A hankali ya ce “Ni dai bazanyi fishi dake ba,tunda kin bani mata kin gama min komai,dole zanyimaki kyauta mai tsoka”.
Itama murmushin tayi dan ta ji dadin maganar Kuma tayi alkawarin insha Allah Ummeey zata dawo gidan nan,dan jiya sunyi maganar da Unlce Yusuf akan zasu je Sudan cikin satin nan”.
Saida ta bashi furar ya Sha kafin ya wuce part din shi, zuciyar shi fal da farinciki.
Itako Seeyerma anan tayi bacci har gaf da sallar la’asar kafin ta farka.
Tunda su Hajiya Mariya suka koma gida Hajiya Balaraba ta shiga tashin hankali,lallai ta tabbatar Hajiya Maryama wato Kaka tafi karfinta,sai yanzu take ganin rashin kyautawarsu tabbas sunci amanarsu,domin Hajiya Maryama tayimata halacci dukda mijinta ba attajiri ba ne Amma ba laifi Yana da rufin asiri.
Da yammacin ranar ne falon Mama ya cika da yan’mata da samarin estate din,Wanda Seeyerma ma tana cikinsu,hira suke yi sosai sai su Khadijah da suke faman yimata dariyar Wai anyimata aure tana Yar karamarta,shikenan ba zata ci gaba da karatu ba .
Aiko danda nan Seeyerma ta rude jin Wai baza ci gaba da karatu ba.
Dakin Mama ta nufa,a gaban weardrop ta hangota tana gyara wasu Kaya,cikin alamun kuka ta karasa wurinta tana cewa “Mama kingani su dijah suna yiman dariya Wai tunda anyiman aure bazan yi karatu ba?”
Lalllashinta Mama ta fara yi,ta ce “ke kyalesu karya suke yi Zaki yi karatun ki kin ji”
Gyada kanta tayi alamar to kafin ta koma falon
Tana zuwa ta fara yimasu dariya “Yara Mama ta ce Nima zanyi karatuna,Sudan ma za’a Kai ni”.
Gaba dayansu Suka sakamata dariya jin wayon da aka yimata.suna cikin wannan dariyar Muhseen ya shigo part din.
Suna ganin shigowar shi kowa yayi cit suna faman gimtse dariyar,gudun kada ya fahimci dariyar da suke yi.
Gaishe shi suka fara yi.
Amsawa ya fara yi Yana kallon su one by one.
Hango Seeyerma yayi tayi rufda ciki saman kafet sai filo data dora kanta saman shi.
Cewa yayi Ina Mama.
Dakinta ya nufa bayan sun sanarmai tana bedroom.
Suna ganin shigewar shi suka fara silalewa daya bayan daya,saida ya rage daga Seeyerma sai kahdija da Aliyu .shima ya jira ne saboda akwai maganar da yake son yayima Ya Muhseen din.
A saman wata kujera ya zauna,saida ya fara gaishe da Mama kafin yayi shiru Yana nazarin ta inda zai fara sanarmata da tafiyar da yake son suyi da Seeyerma.
“Lafiya dai ko naji kayi shiru,alamu sun nuna akwai Magana a bakinka ko?”.
Bakar sumar kanshi yadan shafa Yana Kara yin kasa da kanshi kafin ya ce “Mama daman inaso ki yima su Uncle magana ne akan tarewar nan saboda cikin week din nan zan koma Daura”
Aje kayan tayi kafin ta zauna bakin gadon tana kallanshi.
Kasa ya Kara yi da kanshi ganin irin kallon da take jifan shi da shi.
“Wallahi Kai dai baka da kunya,to ai basai ka jira ankai maka ita ba kawai ka dauki kayanka ku tafi,ko jini bata gama ba Amma saboda rashin hakuri irin naka kake maganar tarewa”.
Nisawa tayi kafin ta dora da “to yanzu maganar dawo da Ummeey ake yi,saika jira idan mun dawo daga Sudan sai a baka ita kuje can ku karata,itama zata gane kuranta tunda Naga alamar ita ke Kara shishshigema.
Fuskarshi cikin fara’a ya ce “Alhamdlillah wallahi zanyi farinciki idan Ummeey ta dawo,Kai Allah na godemaka daka kawo sauyi a cikin wannan Familyn tabbas komai yayi farko zai yi karshe”.
Haka dai suka Kara tattatunawa kafin ya fito.
Bai tadda kowa a falon ba shima wucewa yayi Dan sunyi waya da Lameer akan ya same shi a gidansu zasu tattauna yadda za’a gudanar da Sha’anin bikin.
Bayan kwana biyu da faruwar wannan al’amari haka aka yankarma su Mama biza da Unlce Yusuf sai Aunty Hajara da Muhseen, sai Faruk Wanda dakyar ya yarda ya bisu saboda yadda Hindatu ta saka mai rigimar ba’inda zai je ya barta,Amma akan dole ta hakura.
Daman Sarki Abdulkareem yasan da zuwan su Dan haka aka hau shiryar tarbarsu.ranar Ummeey da Lailah saboda tsabar farinciki bakinsu kin rufuwa yayi,dukda ta wani bangaren bata so ta tafi tabar mahaifiyar tasu Amma tafiya ta zama dole domin aure ibada ne.
Karfe ukku na rana suka dira kasar Sudan inda muko anan ya kama karfe biyar na yamma.
Kusan motoci guda biyar sarki Abdulkareem ya tura domin dauko su daga fikin jirgin saman.
Da Lailah aka tafi aiko tunda ta gansu ta dafe ya Muhseen tana kukan farinciki haka ta rungume su Faruk da Aunty Hajara.sosai yarinyar ta basu tausayi.
Ajere Motocin suka nufo cikin masarautar.
Haka aka tarbesu cikin karramawa da kamala.part guda aka ware masu,kayan abinci iri daban-daban haka aka jeramasu.saida suka sauko farali kafin suka ci abincin.
Bayan sun huta sarki Abdulkareem ya shigo suka gaisa,bayan gaisuwa ne suka sanar da shi abinda yake tafe da su.
Sosai sarki Abdulkareem yayi murna domin shi daman bayyi fishi da su ba,saboda yasan wannan kaddara ce daga Allah,Amma yanzu tunda komai ya daidaita to sai muyiwa Allah godiya.
Haka Suka Kara gaisuwar yaushe gamo kafin ya koma part din Gimbiya zulaihat,sanar da ita yayi abinda ya kawo su,a zahiri nunawa tayi taji dadin hakan,Amma a zuciyarta bakinci ne fal dan Bata so wannan komawar ba.
Gaba dayansu suka dunguma zuwa part din Hajiya Aishatu inda anan Ummeey take zaune.
Sosai Ummeey fara’arta ta fadada ganin mutane mafi soyuwa a gareta har saida kwallar farinciki ta zubomata.
A babban falon suka zauna haka aka Kara gaisawa sosai Hajiya Aishatu taji dadin ganin anzo bikon Diyarta .A ranar suka bayar da sadakin komai da makudan kudade Koda Ummeey zata bukaci siyan wani abu.washe garin gari aka mayar da auren Alhaji Muhammad da Ummeey a babban masallacin dake cikin masarautar.
Ba wata hidima aka yi ba sai walima da sarki Abdulkareem ya gabartar Dan taya kanwarshi daya tilo farincin komawa gidan mijinta.haka aka ci aka sha cike da farinciki.
Da dare su Faruk suna part dinsu Ummeey ta shiga.gaisheta suka Kara yi kafin ta ce “Su Faruk ango ai jiya Jabeer ya Kira ni mun dade muna magana da shi,ya su Hindatun da Rukayya?”
Amsawa yayi da Duk” suna lafiya”.
Kallonta ta mayar kan Muhseen ta ce “Kai Kuma abinda nake son fadama kaga dai yadda abubuwa suka kasance yaci ace kin dauki wani darasi daga cikin wannan abubuwan da suka wakana,sannan inaso Dan Allah ka rike yarinyar nan da mutunci,sannan ya zama dole ka barta taci gaba da karantunta ka ji abinda na fadama ko?”
Cike da ladabi ya amsa da “insha Allah Ummeeyna bazan baku kunya ba”.
Sun dauki wasu mintuna suna hirarsu gwanin sha’awa kafin tayi masu sallama ta koma part din su kasancewar gobe zasu taho Nageria da karfe takwas jirginsu zai tashi.
A Nageria kuwa tunda Seeyerma ta samu labarin dawowar Ummeey ta cika da murna,domin tana kallon Ummeey a matsayin mahaifiyar ta,bazata taba iya manta irin zaman da suka yi da ita ba kafin tabar Nageria a part dinta ta fara zama lokacin da aka zo da ita haka yasa tafi shakuwa da Ummeey,tasan yadda San da Ummeey take yimata ko diyan data haifa sai haka.
Washe garin zasu taho haka ta je gidan Aunty Hindatu suka fara girke-girke domin tarbesu.
Haka Suma a Sudan tuni jirginsu ya lulo kasar Nageria,ya faruk, Uncle Yusuf, Muhseen,Aunty Hajara,Mama,sai Ummeey da Laila,cike da kewa Ummeey ta rabu da danginta ta biyo Diyanta da dangin Mijinta Wanda ta daukesu tamkar Yan’uwanta na jini.
Karfe shabiyu da Yan mintuna na rana jirginsu yayi landing a Usman na gwaggo Airport dake tsakiyar garin katsina.
Alhaji Muhammad da Dady Bishir sune a motar farko,sai motar Jabeerr na biye da su a baya Aunty Aliya ita ce a baya sai Khadija,Motar da Aliyu yake tukowa wacce ita ce ta ukku a gefenshi akwai sadik sai Seeyerma da take mazaunin baya tana ta kalle-kalle kamar bakuwa.
Isma’il shi yake tuka motar ya Muhseen a gefenshi Lameer ne Wanda shima yazo taya wannan Family farinciki.
Tunda suka shigo cikin Airport din kallo ya dawo kansu domin kowa yasan motocin *GIDAN FULANI* ne babban familyn dake ji da kudi da tsantsar kyawu,dukda ana jin haushin yadda Basu auren bare sai yan’uwansu Amma dukda haka ana kaunarsu saboda yadda suke da Foundation na taimakon marayu da gajiyayyu.
A hankali suka fara faka motocin su,one by one masu saukowa daga jirgin suke fitowa.su Unlce Yusuf sune a gaba,sai Mama data ruko hannun Ummeey,ita ko Lalah tana makale jikin ya Faruk.
Su Muhseen sune karshen fitowa,tunda ya fara taka matakalar benen ya fara hango ahalin nasu suna jingine jikin motoci suna kallon masu tahowa.
Caraf ya hango sahibar tashi tasha marum din abaya mai stone a jiki,ba wani makeup tayi ba Amma kallo daya zaka yimata ka fahimci tsantsar kyawun data mallaka.
Haka suka karaso suna tarbar juna.tsaye yayi Yana kallon yadda ta rungume Ummeey tana faman murmushi.gaba daya hankalin shi ya tafi kanta bai luraba saida ya ji Lameer ya rungumo shi kafin ya dawo hayyacin shi.
Cikin yin kasa da murya Lameer ya ce “Ya dai mutumin irin wannan kallo haka kadafa ka kasa control din kanka tun kafin ka jika a babbar fada”Yana yimai dariya.
Baice komai ba sai murmushin da yayi Yana sosa keyar shi ganin mama tana kallonsu.
Haka suka shishshiga motocin Suka kama hanya.duk yadda yaso ya shiga motar da Seeyerma take Amma bai samu damar hakan ba,domin tana makale da Ummeey a tare suka tafi.
Sauran wadanda aka Bari a cikin estate din gaba daya sun fito gaban part din Hajiya Kaka suna jiran karasowarsu kowanne fuskar shi dauk da tsantsar farinciki,musamman Hajiya Kaka da tafi kowa jin shauki domin ita harga Allah tana alfari da Ummeey a matsayin sirikarta bawai dan tafi kowa ba,a a kawai kauna ce daga Allah.
Haka motocin suka fara danno Kai cikin estate din.
Gaban part din suka fara fakawa kafin kowa ya fara kokarin fitowa.
Haka akayi ta rungume Ummeey wasu harda hawayen farinciki.
Dunguma Suka yi zuwa cikin falon,anan aka baje manya da yara ana Kara gaisawa kafin su Uncle Yusuf suka fita dan zuwa masallaci ganin time din salla ya karaso.
Abincin da aka kawo daga part din su Aunty Hindatu da Rukayya shi aka fara zuzzubawa,abinci ne kusan kala goma kowanne da kalarshi.anan tsakiyar falon aka baje kayan abincin dasu lemuka masu sanyi,sai kayan marmari a yayyanke cikin katon bowel gasu laimun kankana da ba abarba.
Kasancewar kowa ya kama nashi abincin Dan su Aunty Hindatu da Rukayya duk sun zubawa su Mama da Aunty Hajara Kuma sun zubama mazajensu.su Aliyu kuwa da kansu Suka zuba.
Ya rage daga Faruk sai Lameer .
Cike da jin haushi ya kalli Aunty Hindatu Yana cewa “Wato saboda kun raina ni ko ni bazaku zubaman abincin ba,sai Iyayenku da mazajenku kadai kuka zubawa,to mu bari mu mutu kawai tunda kun tsane mu”
Sosai yaba su Aunty Hajara dariya,haka suka dara.cike da zolaya Hindatu tace “yoooo Yaya ga matarka kiri-kiri tana kallonmu ko tayamu zubawa bata yi ba,kaima taka matar ta zuba maka”.
Shima cikin dariyar ya ce “to Alhamdlillah yau na wuce gori,dadin abinma Ina da matar yanzu ni ba gairo ne ba,ballantana a yiman gori”.
Ita dai Seeyerma lamo tayi a jikin Ummeey tana sauraren diramar tasu.
Saida Aunty Hajara ta fahimci bata da niyyar tashi ta zuba masu kafin ta daka Mata tsawar saida Muhseen ya ji ba dadi a ranshi.
“Seeyerma wannan wane irin sakalci ne,bazaki tashi ki zubamasu abincin ba,saina bata maki rai anan wurin”.
Cikin kakkarwa ta nufi inda aka aje kulolin ta fara kokarin zubawa,ganin haka yasa Rukayya taimaka mata suka zuba,da daddaya ta fara dauka tana ajewa a gabansu harta karasa jerawa kafin ta koma mazauninta tana kwalkwal da ido kaman zata yi kuka.
Cike da zolaya Jabeer ya ce “Wallahi ya Muhseen wannan matar taka daga gani raguwa ce,tun yanzu zata fara ragwancin tun a wurin zuba abinci”.
Kasa kasa Lameer yake dariya Dan yasan Muhseen ya kule da wannan maganar tunda ya ji yayi shiru bai tanka ba.
Da haka kowa ya kammala cin abincin Suka fara fita daga falon dan zuwa masallaci.
Su Aunty Hajara saida suka huta kafin suka wuce da Ummeey sabon part din da aka gyaramata Wanda ya sha gyara da tiles komai na part din sabo ne aka zuba,hatta kayan kitchen sabbi ne aka saka.
Ummeey bata yi mamaki ba Dan tasan irin San da Dadyn du Lailah yake yimata.
Bayan sun kaita kowa ya wuce part din shi.inda su Khadija Safna da sauran yanmatan suma suka wuce part din Mama madaddalarsu.
Kai Ummeey a wannan ranar taga soyayya a wurin tsohon Mai gidan nata,Dan ba laifi an tsinki fure 🌺🏵️ 🔥🤣.
Bayan kwana biyar haka Muhseen yayi ta zuba ido da kunnuwa Yana sauraren jin ance ga ranar da za’a bashi matarshi Amma ji kake shiru tamkar an aiki bawa garinsu, kwata-kwata ma Aunty Hajara ta hanashi ganin Seeyerma koda ya je part din korarshi take yi Wai gyarata ake yi,ranar daya gaji cewa yayi “shi dai ko ba’a gyara ba a bashi abinshi Yana so a haka,tunda dai ya biya kudin gyaran shikenan”
Kudin gyarama dubu dari biyar ya Basu da sauran abubuwa,lefe kuwa su Aunty Aliya aka tura London suka hado lefe na gani na fada,tamkar diyar gwamna.
Kai karshe kullun Muhseen dakyar yake bacci haka Lameer yake tasa shi a gaba yayi ta yimai dariya idan ya sanarmai.
Karshema da abin ya isheshi safiyar wata labara tunda sanyin safiya ya hada kayanshi ya fice Daura ba tare da sanin kowa ba,Dan gwamma yayi nesa da su duk ranar da suka shirya bashi to sun nemeshi.saboda hakurinshi ya kusa gazawa.
Seeyerma ko saboda tsabar kyau kamar ka tabata jini ya fito,gaba daya halittarta ta sauya saboda gyaran data ke damu,musamman aka dauko Mai gyara daga cikin gari,makudan kudade aka bata tare da waremasu daki guda anan ake gyarata,ciki da waje take shan gyara hakan yaba yarintarta damar Kara baiyana tayi Shar abinta tamkar ka saceta ka gudu………….³⁷