DR MUHSEEN CHAPTER 19 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)

DR MUHSEEN CHAPTER 19 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)

 

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

             📝…………….. Muhseen saida yayi kwana biyu da tafi ba tare da kowa ya sani ba,Kaka da taga ya daina shigowa tasaka Khadijah a gaba akan ta Kira shi a waya ta ji ko lafiya,domin tana gudun kada ya kulle kanshi a daki tasan halin shi sarai idan yayi zuciya abin ba kyau.

   Haka Khadijah tayi ta faman Kiran wayar shi,Amma is not reachable kasancewar cikin asibitin su wasu wuraren babu network.

   Karshe dakyar suka samu ta shiga,lokacin Yana office din C O dinsu suna tattaunawa akan wasu takaddu da za’a tura Bauchi,Karan wayar da ya ji yasa yayi saurin dubawa ganin nomber Hajiya Kaka yasa ya ceman ogan nasu 

“Parmition sir”.

 

  “Ok”

Cewar C O Nursing.

    

    Yana dagawa yayi sallama.

  Saida ta amsa kafin ta ce “Yanzu mai gida shi ne ka tafi baka sanar da mu ba ko? Saboda mun hanaka wannan yarinyar mai kama da cokali”.

 

   Dariya ta kusan kufcemai Wai mai kama da chakali,Kai wannan tsohuwa da Jan rigima take.

   “Kiyi hakuri matar Zan Kira ki,yanzu Ina office din ogana idan na koma gida zan Kira sai mu yi magana ko?”

  Amsawa tayi da “to ba damuwa Allah ya taimaka ka gaishe da shi”.

   Saida ya amsa kafin ya katse Kiran Yana duban ogan nasu.

Shima duban shi yayi Yan cewa “Daga ji wannan ita ce Hajiya kaka,Dan na gane hakan yadda na ji tana janka”cewar C O Nursing fuskarshi dauke da murmushi dan duk cikin ma’aikatan su Yana jin dadin mu’amulla da Dr muhseen,kasancewar Yana da dunbin ilimi ga natsuwa da girmama manyan shi.

  Sosai Muhseen ya fadada fara’ar shi Yana sanar da shi ta ce tana gaishe shi.

    Cewa yayi “Ina amsawa insha Allah idan munje biki zan shiga na gaishe da ita”.

   Sosai ya ji ogan nasu Yana Kara shiga ranshi ganin yadda yake nuna kulawa ga familyn Shi.

   Haka suka ci gaba da tattaunawa kafin ya koma office din shi .

  A bangarin Hajiya Kaka sai a lokacin ta ji sanyin a ranta,jin muryar babban jikan nata.

   Da dare misalin karfe tara da Yan mintuna Yana bedroom din shi.system ce a gaban shi Yana dubawa.wayar shi ya ciro daga jikin charge kafin ya saka kati daga account din shi.

    Nomber Hajiya Kaka ya fara Kira.

   Ita ko lokacin tana zaune a falo ita da Jabeer kular dafaffiyar kaza ce ya kawo mata,Rukayya ce ta dafo mata,sosai ta ji dadin Naman kazar ganin yadda daguwar tayi romo ga taushi,tana ci suna hira da Jabeer akan al’amuran familyn nasu,da irin yadda kasuwancin yake tafiya.

      Jin wayar ta dauki Kara ya lalubota Yana duba mai Kiran,Maigida yaga an rubuta yasan Muhseen ne.

   Saida ya danna picking call kafin ya mikamata wayar.

   Karawa tayi a kunne tana cewa “yanzu mai gida sai yanzu ka shirya Kira na,tun dazu nake ta jiran ganin Kiran ka,to Daman dan nayima albishir ne na kazo ka tafi da matarka,Amma tunda baka so muma mun fasa baka”

   Ai Muhseen Yana jin haka da a konce yake yayi saurin tashi zaune ya fara zuba mata kirari “Haba kakata ta kaina,tsohuwa mai ran karfe,makiyanki sun buga da ke sun barki,kowa ya ja da ke to wallahi saiya fadi kasa,uwar gida daya tilo a gidan Alhaji Abubakar tubalin GIDAN FULANI,kece hasken ahalin fulani,Allah yaja da ran bafulatanar usili masu asalin kyawu da dukiyar shanu,asalin mutanen kanto.”.

   Jin tsohuwar ta saka dariya yasaka shi sakatawa shima Yana dariyar.

  Jabeer ma dariyar ya saka saboda Yana jin su kasancewar wayar a hansfree take.

  “Kai amma mai gidan ka iya godalo da neman a baka mata,irin wannan kirari haka sai ka saka na ji kamar zan Kara shekaru talatin a duniyar nan,sai dai kash nasan dole wata rana mutuwa zata dauke ni daga cikin ku”nan take Hajiya Kaka ta saka kuka tunowa da tayi babu mai gidanta sannan babu yaranta guda biyu wato Fatima da Jalaludden.

Sosai take kuka harda sharbe majina.

  Cikin yaren fulatanci Muhseen ya fara kokarin ganin ya kontarmata da hankali,sosai ta dan samu nutsuwa kafin suka dan taba hira.

Bayan sunyi sallama akan gobe da safe gashi nan zuwa katsinar kafin ta mikama Jabeer wayar tana goge gunyun hawayen daya rage a fuskarta.

   “Kai wallahi Ya Muhseen Kai dai Allah ya shirya ka”cewar Jabeer bayan ya Kara wayar a kunnen shi.

    “Ka sakamana Yar tsohuwa kuka ko?to Zan wallahi zan hana su Unlce su baka matar inga ta tsiya”.

   Sosai Muhseen ya saka dariya Yana cewa “Ai wallahi yaro baka isaba,wato saboda Kai kasan ka kama taka a hannu baka da sauran wata matsala ni shi ne kake so ka kashe ni ko?to gobe tun kafin ku tashi a bacci zan diro garin ko ku bani matana ko Kuma na dauka da kaina eheee,Kai harka samu bakin magana ko saboda kayi aure kasan dadinshi ko?to ni Mata hudu zan yi nan gaba”Yana Kai karshen zancen kit kake ji ya katse call din.

   Sosai Jaberr yayi ta dariya a ranshi Yana cewa “Kai wallahi Muhseen tantiri ne,Ashe shiyasa Seeyerma take cemai DAN BARIKI saboda shakiyancin shi,baiwar Allah harta bani tausayi Dan wannan kam nasan bazai daga Mata kafa ba”.  

  Aje wayar yayi ya mike bayan yayiwa Kaka sallama ya wuce part din matar shi.

  Shiko Muhseen bayan ya katse Kiran wayar Aunty Hajara ya Kira.

Lokacin suna zaune da Seeyerma ta tasata a gaba dole saita shanye tsumin data kawomata cike da wani dan madaidaicin cup.

   Itako sai faman shagwaba take yi taki sha,saboda yadda ta ji baurin abun.

Suna a haka wayar Aunty Hajara ta dauki tsuwwa.

   Ganin My son yasa ta aje wayar tana cewa “Wallahi idan baki Sha ba zan bata maki rai,wannan jarababben mijin naki daga gani bazai barki ki huta ba,Amma saboda rashin wayo irin naki ba zaki gane ba,Ana so ayimaki gata kada ya rainaki ke saboda sakalci kin kasa ganewa”.

   Jin Karan wayar ya sake tashi a karo na biyu yasa ta daga tana Kara cemata “wallahi kafin na karasa wayar nan Naga kin shanye shi tas ko ranki ya baci”.

  Tunda ya ji yasan da Seeyerma ne,shikam ya kasa gane wannan dure-duren da ake yimata Kona meye ne,sai yayi magana ace Wai gyarata ake yi,shiman Ina ruwan shi da wani gyara indai zai ji shi sakayau ai shikenan.

   Jin muryarta tana cewa “idan bazaka yi magana ba zan kashe wayana”.

    Da sauri ya ce “Aunty Ina yini”

  A takaice ta amsa da “Lafiya”Dan Seeyerma ta bata Mata rai.

   Ji yayi jikin shi yayi sanyi,a hankali ya ce “ehm Daman gobe zan zo insha Allah”.

   “Allah ya kaimu,nasan me kake yiwa wannan Kiran to ka zo ka dauketa ku tafi,duk ranar daka gama raraketa ta gane kuranta ita Yar dadi miji,gatan da ake kokarin yimata bata so to ni na gaji kazo ku tafi nayi iya bakin kokarina,randa taji ta zama kamar dusa ta nema da kanta ta gyara”.

   Cikin sauri Seeyerma ta shanyen tsumin ta aje cup din tana Jin wani iri saboda baurin maganin.

   Shidai Muhseen shiru yayi jin yadda Aunty Hajara take faman fada kamar ta ari baki.

   A karshe dai jin yayi shiru yasa ta ce “wato kaida ita kun dauke ni sakarai ko,idan nayi magana zaku yi shi”.

   Bawan Allah zuciyar shi cike da tsoro ya ce “Dan Allah kiyi hakuri Aunty wallahi ba laifina ne ba,kiyi hakuri idan ranki ya baci”shidai Addu’ar shi Allah yasa su bashi matar shi,idan ya taho da ita to sai bayan ta haihu kafin ya kaita katsina su ganta,duk wannan wulakancin da suke yimai saiya rama saboda sunga a matse yake shiyasa suke Jan ranshi.

   “Anshi wayar ni kafin na masge ki marar kunyar karya”cewar Aunty Hajara bayan ta mikamata wayar.

   Cike da tsoro Seeyerma ta anshi wayar,Dan bata taba sanin Aunty Hajara nada fada ba sai yau.

    Saida taga ta fita daga dakin kafin ta dannan hansfree ta dora wayar saman cinyarta ta saka kuka tamkar Yana ganinta.

   Runtse idonshi yayi jin yadda sautin kukan yake dukan zuciyar shi.

   Sosai take kukan shiko ya rasa mezai ce mata,sai ajiyar zuciya da yake saukewa.

     Sunyi kusan two minutes a haka tana aikin kukan kamar wacce ake duka, kafin yayi karfin halin cewa

 “Please sorry my wife,Dan Allah kiyi shiru muyi magana,kinsan bana son wannan sautin kukan ko?so kike ki tayarman da hankali?kina kallon yadda nake fama da su,sannan kema ki karaman wata damuwar duk fa kokarin da nake yi na mu kasance tare da juna ne,Dan Allah ki saurari abinda zance kin ji”.

  Jin haka yasa Seeyerma ta dan tsagaita da kukan tana Jan ajiyar zuciya.

    Katse Kiran yayi Yana cewa sorry Bari na Kira ki.

Vedio call ya Kira,tana dagawa ya wani lumshe idon shi Jin wani sabon al’amari ya tsarga jikin shi.

   Tar ya bude su a kanta,itako tama manta dressing din dake jikinta.

Wata yaloluwar rigar bacci ce mai hannun best,sai gidan bra da aka yiwa rigar da Kan karamin zip manne jikin Brest cup din,hakan yaba farar fatarta bayyana sai kyalli take yi da daukar ido,kusan rabin kirjinta a waje suke saboda yadda rigar tayi Mata kadan,tsawontama ko bakin guywarta ta tsaya.sai santala santalan kwaurinta daya bayyana.

  Kanta ko hula babu sai kwantaccen gashinta mai kyau da santsi.

    Ji yayi gaba daya waya muguwar kasala ta rufeshi,Dan danan idanuwanshi suka kankance tare da fara sauya kala.

   Ita kuwa Seeyerma saurin kawar da kanta tayi gefe daya ganin ko riga babu a jikin shi.

Murmushi yayi Yana shafa sumar kanshi a ranshi ya ce “Haba yarinya zaki shigo hannuna,sai kin gane ni DAN BARIKI ne,Ashe rashin kunyar taki ta karya ce”.

   Ganin taki ta kalle shi ya ce “idan baki kallo ni ba ko wallahi idan na kama ki saina cinye ki,ok na gane sai yanzu kike jin tsorona da can da kike ceman katon tazuru bakiyi tunanin zamu zama abu guda ba ko?hmmmm yanzu dai kifadaman me kike yiwa kuka”.

   Jin haka yasa cike da yarinya ta ce “Nidai Dan Allah kacema su Uncle ka fasa auren wallahi bana so tsoro nake ji”.

  Ganin yadda tayi maganar cike da sakalci yasa yayi saurin cewa “Tsoran me kike yi”.

    “Uhmm uhmm Ni dai Dan Allah kace ka fasa wallahi tsoro nake ji”.

  Sosai ta bashi dariya ganin duk maganar da take yi fa idonta a rufe suke.shiko hakan yasa ya samu damar kallon kirjinta da suke tamfats tamkar zasu tsone mai ido.

  Wasu yawu ya hadiye mukuuuuuut Yana jin yadda girman shi take kokarin tonamai asiri.

   “To zan fadamasu but sai kin bude idonki munyi magana kafin na sanar masu”.

Itako saboda tsabar yarinta bata san wayo ne zai yimata ba tayi saurin budewa tana cewa “to wallahi na bude Dan Allah ka ce ka………

  Da sauri ta katse Kiran tana sakin Kara jin wani abu Yana yimata yawo a kwakwalwarta.saurin katse Kiran tayi tana kwalalo idanuwanta waje saboda tsorota da tayi.

Kashe wayar tayi gaba daya kafin ta dafe kanta tana cewa “Ohhhhhh ni maryama na shiga uku Kai wannan mutumin baya da kunya ko kadan,Kai nikam Naga ta kaina,Allah kasa ya sake ni na huta wallahi Dan Ni bazan iya zama da wannan katon ba”

(Niko Autah na ce ba Amin ba,muda muke so mu je cin kazar amarci🤣🤣).

 Shiko sosai Yarinyar ta bashi dariya,ga tsoro ga Jan fada,kamar ba ita ce take cemai katon garjejen tazuru ba.

A fili ya furta “Zaki ji yadda katon garjejen tazuru yake daga ranar dana damke ki sai kin yabawa aya zakinta”.

   Da haka ya fada toilet Dan yasan dole saiya sake wanka saboda yadda yaji wani Yana yi na daban yasan an samu matsala.

 Ita ko tana wannan tunanin na abinda ta gani hannuwanta dafe da kai,Aunty Hajara ta dawo dakin.

  Da sauri ta dago tana Yan kame-kame ganin haryanzu ran Auntyn nasu kamar a bace yake.

   Saida ta karemata kallo tsaf kafin ta ce “Bani wayata,Kuma wallahi idan baki rinka ja mai aji ba rainaki zai yi,kullum ya rinka lalube ki,daga ranar da kika kwararrarbe to wata zai aure keko kina nan kin zama bola”

  Da sauri Seeyerma ta dago Kai tana kallon Aunty Hajara idonta harya ciko da kwalla,cikin tsoro ta ce “Aunty dan Allah ku raba Ni da shi,wallahi na fasa auren bana sanshi ya je ya auri Aunty Ameerah Kuma ni yafi karfina kinga girman abun…………….sai Kuma tayi saurin rufe bakinta da tafin hannuwanta tana yin kasa da kanta jin irin sakin layin da take kokarin yi.

   Sosai Aunty Hajara ta ji kunya ta kamata,itakam ta bani da wannan yaran, Seeyerma ba wayo shi Kuma Yana abu kamar ba babba ba,yanzu da wasu ta fadawa haka ai an samu matsala.

   A hankali ta zauna kusa da ita ta dafa kafadarta tare da Kiran sunanta Seeyerma! Seeyerma!! Seeyerma!!har saida ta kirata sau ukku kafin ta ci gaba da cewa “Seeyama kada na Kara jin kin fadawa kowa wannan maganar kin ji, wannan sirri ne tsakanin ke da shi kin ji ko?”

   Ita dai Seeyerma ba baka sai kunne,gyada kanta tayi alamar to.

  “Sannan daga yau ko me zai yimaki ko ya fada maki to kada ki kuskura ki sanarma da wani,Koda su Hindatu ne inhar ba neman shawara kike yi ba kin ji,sannan ita rayuwar Aure sirri ce,ki kasance mai rikon sirrin rayuwar auren ku,Kuma ki kasance mai juriya da hakuri,na fahimci mijinki ba mabukaci ne dukda Ina da tabbacin ba mazinaci ne ba,abinda ya faru tsakaninku ma Allah ne ya kaddara bamu da yadda zamu yi,to dole sai kina bashi kulawa idan Baki so wata ta kwace maki shi,ko kinaso ya yimaki kishiya ne, ko matan waje su janyemaki shi?”

  Cikin sauri Seeyerma tayi girgiza kanta.

  Murmushi Aunty Hajara tayi irin nasu na manya kafin ta ce “to meyasa kike cewa a raba auren ku?”.

Kasa magana tayi sai kwalkwal da tayi da ido kamar zata fara kuka.

   “To na fahimce ki,Amma bari ki ji idan har aka warware wannan auren to bazai saka ki a makaranta ba,sannan Zaki bar nan estate din a mayar dake gidan Aunty Aliya,kin amince da haka?”.

  Da sauri ta girgiza kanta tana cewa “A a Aunty kuyi hakuri na daina cewa bana so,zan zauna da shi Kuma wallahi nayi alkawarin duk abinda ya ce nayi zan yi mai,nidai ya saka ni a School”.

Sosai taba Aunty Hajara tausayi,Dan haka tayi ta kontar Mata da hankali,har saida taga ta sakata dariya kafin ta rufemata dakin bayan ta bata wani hadin zuma ta shanye.

  Bayan ta fita Seeyerma ta dade bata yi bacci ba tana tunanin maganganun da suka yi da Aunty Hajara tabbas akwai abinda take son ganowa akan alakarta da Aunty Aliya,meya ake cewa zata koma gurinta da zama?tunda ta baro Sudan bata Kara komawa ba har zuwa wannan lokacin,Kuma bata Kara ganin iyayenta ba sai cewa aka yi sunyi hadari a jirgin sama sun mutu,Amma tayi alkawarin zata tambayi Yaya Faruk tasan shi zai fadamata abinda ya faru.

  Da wannan tunanin bacci ya dauketa Mai cike da mafarkin ya Muhseen.

  Itama Aunty Hajara data koma bedroom wurin Uncle Yusuf anan take sanarmai rigimar Seeyerma shima murmushi yayi ya ce “Yarinta ce wata rana zata daina”.

   Dan Muhseen kuwa dakyar ya samu bacci barawo ya sace shi da tunanin gobe tayi ya damki hanyar katsina.

      Washe gari tun karfe bawkai da mintuna ya baro garin Daura.

Cikin mintuna talatin ya shigo estate din.

 Darect part din Mama ta nufa,shiru gidajen suke duk suna bacci.

   A kitchen ya tadda Mama tana soyamai Arish da kwai,kasantuwar ya sanar da ita zuwan shi.

Ganin bata karasa ba ya ce “Bari na je na shirya a part dina,akaikan kayan break din”.

     Ya juya zuwa part din shi.

   Sosai Mama ta ji tausayin yaron ganin yadda duk yayi dan wuya,danma Yana da kyau da sai an gane ramar shi.

Karfe goma saura ya kammala shiryawa.Safna ce da Khadijah suka yi knowking a bakin part din nashi.

Tasowa tayi ya bude,ganin sune yasa ya matsa gefe,kayan suka aje saman dinning kafin Suka ce “Ya ina kwana”

   “Lafiya Lau”.

  Juyawa suka yi Suka fita.safna part din Mama ta koma ita ko Khadijah part din Aunty Hajara ta nufa dan kaiwa Seeyerma labarin zuwan angon nata.

  

     A cikin blanket ta risketa tana ta sharar bacci saboda raba dare da tayi bata yi bacci ba.

Saida ya yaye blanket din kafin ta daka Mata duka a saman cinya.

   Seeyerma zabura tayi tana lalube ganin yadda take ganin wani duhu a cikin  idonta.

“Yarinya kina nan kina aikin bacci,tun karfe bawkai ya Muhseen ya shigo estate din nan,yau zamu Mika ki hannun shi gwamma ki tashi tun kafin Aunty Hajara ta shigo”.

  Mitstsike ido Seeyerma ta fara yi jin abinda Dijah ya ce.

   Cikin mutuwar jiki ta fara kokarin sauka daga gadon take ta ce “Allah ya isana da kika tashe ni a bacci na,Kuma saina fadawa ya Faruk tunda kema kin fara tsanata”.

  Da haka ta shige toilet tana faman gunguni.

   Gadon Khadijah ta hau gyarawa tana dariyar mugunta a fili ta ce “Yarinyar duk wannan rashin kunyar taki sai kin dainata idan kika ji maza”.

   Saida ya kammala break din kafin ya fito cikin dakakkiyar milk din shadda dinkin zamani sosai ta Kara fitar da kyawun shi, kalamin shi mai kyau da tsada,shi ba ma’abocin saka hula ne ba,sai Yar yaloluwar sumar shi da ya gyara,agogon silver ne daure da tsintsiyar hannunshi sai wayar shi kirar kamfanin iPhone 12 sabuwar yayi.

   Cike da takun mazantaka ya fara takawa zuwa part din Hajiya Kaka.

     Ba kowa a falon sai Karan fanka da A/c suke kadawa.bedroom din ya nufa da sallama dauke a bakin shi.

   Tsohuwar amsawa tayi tana kallon shi,daidai ya shigo dakin.

  Saman gadon ya zauna Yana cewa “Tsohuwa mai ran karfe kin tashi lafiya”.

  Saida ta aje cup cin dake hannunta kafin ta ce “Lafiya Lau na tashi saima karfi na daya karu,sannan wannan uban safkon daka dakomana dukna meye?”

Murmushi kawai yayi Yana duban kwanon dake gabanta ganin kayan marmari a yayyanke yasaka ya dauki yankan kankana daya,saida ya shanye kafin ya ce “Ai wallahi kunsan bazan kyaleku ku huta ba har  sai kun bani matana,Ina dalili hakuri na ya kusan Karewa ku ko tausayi na bakwa ji,ga yadda su Faruk Suka yi kiba hankalinsu konce Niko sai reto nake yi kamar nayima sarki karya”.

   Mahicin dake gefenta ta cillamai ya fice da gudu Yana dariya.

Part din Ummeey ya nufa.

Saida yayi knowking kafin Lailah tazo ta nude kofar.da gudu ta dafe shi tana “oyoyoooo yayana Ina ka tafi Ina ta kewarka”.

  Domin tun randa Suka dawo daga  dauko su Ummeey bai Kara shiga part din ba.

  Tana kafadar shi ya karasa cikin falon.saman kujerar ya zauna kafin ya zaunar da ita saman cinyar shi.

  “Autah Ina Ummeey take?”

   “Bari na kirata tana kitchen”da gudu ta nufi kitchen din dake cikin falon.

Jim kadan sai gasu sun dawo tare tana rike da hannunta.

Saida ta zauna kafin ya ce “Ummeey Ina kwana”.

   “Lafiya Lau,Ai nayi tunanin bazaka dawo ba tunda ka tafi babu sanin kowa,Kai mai zuciya ko?

  Shiru yayi a ranshi Yan cewa “Ni shikenan kullun ni ne Mai laifi”.

    “To yanzu meya dawo da Kai?”.

   Nanma dai shoru yayi Yana Kara sadda kanshi.

  Maganar Dady suka ji Yana cewa “wallahi Ummeeyn su ku fita a idona in rufe,duk kunbi kun tasoman yaro a gaba da takura ko?to dake da Auntyn su da Maman su Faruk yau idan baku ba yaron nan matar shi ba ranku zai baci,haka ake yi ki duba kiga yadda yayi dan wuya ku haka aka yimaku ne?ka kontar da hankalinka my son insha Allah yau zaka anshi matarka anjima su Yusuf da kansu zasu kaita dakinka,nidai rokona ka riketa da Amana ka ji “.

  Yana daga kafadar Muhseen din.

  Cike da jin dadi Muhseen ya ce “Nagode Dady Allah ya Kara daukaka da nisan kwana”.

   “Amen ya Allah “Dady ya amsa Bayan ya mike tsaye.

A tare suka fito,itako Ummeey ganin haka yasa ta koma kitchen tana cigaba da ayyukanta. 

   

    A ranar da dare misalin karfe takwas da Yan mintuna Seeyerma tana daki suna ta fira da Khadijah da safna,sai dariya take kwasa.

  Shigowa su Mama da Aunty Hajara yasa tayi saurin hadiye dariyarta tana wurga ido.

   Mama ta riko hannunta tana cewa “ku tashi hakanan hirar ta isa,sai gobe”.

Hanyar toilet ta nufa da ita.cikin tsoro Seeyerma ta ce “Mama wallahi zazzabi ne a jikina,kaina Yana ciwo ga kuguna ya rike”tana tirjewa alamar ta saketa.

   Cak Mama ta tsaya tana yimata kallon kin rainani.

   Sim-sim Seeyerma ta shiga toilet din,kafin Mama ta bita a baya.

Sauran kayanta Aunty Hajara tasaka su Khadijah kimtsawa a cikin wata troly tasa Suka Kai cikin Motar Uncle Yusuf.

  

Ruwa ta hada mata masu turaren wanka na kanshi irin na larabawa Wanda Ummeey ce ta bada gudummawa.

  Haka ta tsareta tayi wankan, Seeyerma tana faman jin kunya haka tayi wankan.wata bona ta turare ta kunna haka tasata ta tsuguna turaren Yana ratsata.ta Dade a haka kafin ta kyaleta.

  Tunda ta fito ake shiryata,a gogamata wancan a bata wancan ta shafa kafin aka kammala,kwalliya Aunty Hindatu ta tsaramata mai kyau.

Suna cikin haka Ummeey tayi sallama tare da karasa shigowa.

Kilar data shigo da su day wani dogon cup Rukayya ta amsa suna gaishe da ita.

   A hankali Seeyerma ta ce “Ina yini”.

  “Lafiya Lau Doghter”.

   

  Cike da zolaya Rukayya ta ce

 “gaskiya Ummeey kina ji da wannan yaran naki,irin wannan tsimi haka kadafa ya kassara Mana Yar kanwar tamu,Daman Ina ga lafiyar kura ballantana tayi zawo”suna dariya ita da Hindatu.

  Ita dai Ummeey murmushi kawai tayi sai Aunty Hajara ce tace “Gwamma dai ya kassaratan tunda ita Bata san ciwon kanta ba…..”

Saurin duba wayarta tayi jin alamun ana kira ganin sunan Son yasa ta Kara cewa “Gaskiya Hindatu wannan yayan naku sai ayimai addu’a ya hanani na huta,yau idan aka bashi yarinyar nan to ni kaina nayi har nayi bacci da minshari,tunda ya zo yake faman kirana,a kalla yayiman Kira ya kusa talatin a yau kadai”.

  Dariya su Aunty Hindatu suka saka suna cewa “to Aunty Kinga laifin shi,ai wallahi yayi hakuri ma,da wani ne tuni da kun damka mai,Amma shi bawan Allah Dan kunsan Yana da hakuri shiyasa kuke ta gwara shi,to ku sani saiya rama akanta”.

   Ita dai Ummeey fita falo tayi jin kunya ta kamata,Mama ma shiru tayi sai Aunty Hajara ce ta ce “kuyiman shitu marassa kunya,Kuma nan zaku Nuna Mana kunsam yadda aure yake ko?”.

  Da haka suka kammala shiryata.kular da Ummeey ta kawo Aunty Hindatu ta buda tana dorawa bisa cinyar Seeyerma.

   Ta gane abinda take nufi Dan haka Dan danan ta fara raba ido,itakam ta gaji da wannan abun so suke yi ya kasheta kawai.

   Ji tayi Aunty Rukayya tana yimata rada a kunnenta,Danda nan ta fara ci da spoon.

   Kallon Hindatu tayi suka yi murmushi a tare.

   Itama Aunty Hajara falo ta koma,danta fahimci akwai maganar da suke San fadama Yar kanwar tasu.

  Aiko kamar jira suke yi suna ganin ta fita,suka akama kofar key kafin suka zauna a gefenta ya zama tana tsakiyar su.

   Sosai suka fara yimata lectures da yadda zata ba Mai gidan nata kulawa,ita dai tana jinsu duk kunya ta gama rufeta,Kai ashe suma su Aunty Hindatu Basu da kunya?.

   Saida suka saka ta cinye dahuwar tantabarun tas ta shanye tsumin kafin suka kyaleta.

Ji take kamar tayi amai Amma dole haka ta daure,saboda sunce Mata idan tana cin irin wadannan abubuwan to bazai yimata komai ba,itako ta amince da haka shiyasa duk abinda aka mikomata take saurin shanyewa.

   Sai karfe tara da rabi su Uncle Yusuf da Unlce Ahmed suka zo tafiya da ita.

  Aiko anan Seeyerma ta fara ihun kuka ganin fa da gaske tafiya za’ayi a kaita.

Haka duk sukayi cirko-cirko a dakin, Ummeey kuwa tuni ta gudu part dinta,sai su Aunty Hajara da Mama ta bari.

Jin shiru sun Dade basu fito da ita ba,yasa su Uncle  Yusuf suka shigo dakin.

Baiyi mamaki ba ganin irin kukan da take rafzawa.

Cewa yayi su saketa.sakinta Suka yi duk suka fito daga dakin.

Cikin tausayin yarinyar ya ce Seeyerma bani hannunki,saboda yasan kowacce yarinya zata rabu da iyayenta dole zata yi kuka.

  Jin muryar Uncle din yasa ta tsagaita kukan tana sauke ajiyar zuciya.

A hankali ya kamo hannunta suka fito, Uncle Ahmed Yana biye a bayansu.

  Mama ta biyosu da Hijaf a jikinta.

Bayan motar Suka sakata sai Mama ta shiga gefenta,su Kuma Suka shiga gaba Uncle Yusuf ya tayar da motar Suka doshi sabon gidan da aka mallaka masu.

    Bayan tashin Motar su Kiran Muhseen ya Kara shigowa wayar Aunty Hajara a karo na ba adadi.

  Cike da zolaya tayi picking call din cikin hade rai ta ce “Kai Wai bazaka daina kirana ba,su Uncle dinku sunce bazasu baka ita ba,ka rubuto takardarta ka kawomana,Dan yarinya tace ita bata sanka ta fasa aurenka,Dan haka kada ka Kara kirana”kit ta katse Kiran suna dariya.

   Gaba daya yaji duniyar tana jiyamai,lokacin Yana part din shi shida Faruk da Lameer.

  Sosai Faruk ya tsorata ganin Yana neman sume masu.wayar shi ya lalubo ya fara Kiran Hindatu.

Cikin dariya ta daga Kiran tana cewa “Gaskiya Yaya Muhseen sai a slow”.

  Cikin tsoro ya ce “pls Dear tell me da gaske an fasa auren?wallahi Kinga ya tsorata Suma yake kokarin yi”.

  Tana jin haka tayi saurin cewa “wallahi Dear wasa muke yi tun dazu su Unlce Ahmed suka tafi su kaita,kada ya damu wallahi da wasa muke yi”.

Kasancewar wayar a hansfree take yasa Muhseen ya Dan bude idanuwan shi Jin kanshi ya Dan saki daga nauyin da yayi mai.

     Tunda Seeyerma ta ji motar tayi parking alamun an karaso gidan ta saka wani sabon kukan.

Saida Unlce Ahmed ya daka Mata tsawar kafin tayi shiru tana makale jikin Mama.

  Unlce Yusuf da kanshi ya kama hannunta su Mama na biye da shi a baya,saida ya shigar da ita har bedroom ya zaunar da ita a bakin gado tare da Kara yimata Yar takaitacciyar nasiha kafin Suka fito.

Ita kadai aka bari duk yadda ta rungume mama tana kuka dole ta saketa saboda tsawar da Uncle Ahmed yayimata haka ta konta saman bed din tana kuka mai tsuma zuciya,suko Suka shiga mota suka aje Mama a kofar part dinta kafin shima Uncle Ahmed ya sauka,kafin shima ya wuce gidan shi.

   Su Hindatu suna ganin dawowar Unlce Yusuf Suma Suka Kira mazajensu akan su zo su tafi.

  Cikin mintuna kadan kowa ya koma gidan shi,a lokacin karfe shadaya ta kusa.

Ai Muhseen Yana warewa ya ce Lameer shima ya tafi baya bukatar rakiyar kowa shi kadai zai tafi.

Haka Lameer ya tafi gidan su.

   A kalla ta dau tsawon rabin awa tana wannan kukan kafin taji motsi alamun za’a shigo dakin.

Ita dai Bata motsaba daga koncen da take harya shigo  dakin hannunshi dauke da ledoji……………….

………Tsaye yayi a bakin kofar yana kallon yadda ta kudundine guri daya.sosai ya ji ta bashi tausayi ya Jima a haka kafin ya karaso jikin gadon.Duk abinda yake yi Seeyama tana kallonshi ta kasan idonta.

Royal bed ne Mai kyau gefenshi hadadden weardrop ne, mirrorn kanshi abin kallo ne.

Kalar papules ne hatta labulayen kalar kayan ne,sai kafet Mai kyau da aka shimfida shi gaban gadon.my fns jost kuyi emargen tsarin haduwar gidan .

Akan wata kujera ya aje ledar kafin ya Kara dawowa kusa da ita.

A hankali ya saka hannunshi yana dagota,tana jin haka ta Kara langwabewa a jikin shi.

Mayafin da aka rufe kanta da shi yake kokarin yayewa Amma gam ta rike shi.

Cike da sanyin jiki ya ce “Dear kiyi hakuri ki tashi muyi salla domin mika godiyar mu ga Allah subahanahu wata’ala daya nuna mana wannan rana mai albarka”.Yana Kara leka fuskarta ta cikin mayafin.yasan ba bacci take yi ba kawai pretending ne da tsoro,Dan Yana jin yadda zuciyarta take bugawa da sauri.

  

  Cike da shagwaba ta ce “kaina yake ciwo da cikina”

 Sannu ya yimata kafin ya fita daga dakin zuwa wani daban Wanda suke kusa da juna.

  Tana ganin ya fita tayi saurin sakama kofar key tana sauke ajiyar zuciya.

Toilet ta shiga jin yadda mararta ta cika da fitsari.ta dan Jima a ciki kafin ta fito.turus tayi ganin shi zaune saman bakin gado yana amsa waya.

    Weardrop ta bude,wata doguwar rigar bacci ta dauko tare da saban pant ta koma toilet din.bayanta yabi da kallo Yana jin mod dinshi ya canza.

    Wanka ta sake yi da sabulu Mai kanshi,a cikin toilet din ta kimtsa jikinta kasancewar shi wadatacce.

   Yana gama wayar ya sake fita zuwa dakin da nake tunanin mallakin shi ne,wanka yayi tare da canza Kaya zuwa milk din jallabiya Mai gajeren hannu.sosai ya gyara sumar kanshi Bayan ya dauro alwala.wasu turarika Naga ya dauko masu kanshi ya shafe jikinshi da su.

Nasihar da Ummeey tayimai ta Kara fadowa ranshi

 “Son ka rike yarinyar mutane da Amana,duk ranar daka yimata gori akan mutincinta banyafe maka ba,sannan kasan haryanzu Seeyerma yarinya ce dole Sai kana hakuri da ita,Kuma kada kasa ta kasa da bukatarka,wasu lokuttan sai kana hakuri da ita ta hakane zaka Samar da zaman lafiya a tsakaniku”

  Kanshi ya dan shafa jin wata kunya ta Kara kama shi,a lokacin da tana yimai nasihar kasa motsawa yayi saboda yadda ya ji kunyar maganar.

    Wayoyinshi ya kwasa ya nufi hanyar dakin nata zuciyar shi cike da fargabar kada taki amincewa da shi.

   

     A hankali ya tura kofar,can kuryar faffadan gadon ya hangota ta rufe duka jikinta da blanket.

   Hasken wayar shi ya kunna ganin dakin yayi duhu.ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cire takalman kafar shi ya fara haurawa saman gadon.

  Sosai ta ji tsinkewar zuciya,a ranta kuwa cewa take “Yau nikam nasan na mutu,da safe sai dai a dauki gawata”Bata idar da tunanin ba ta ji ya dagata sama cak ya nufi hanyar toilet da ita Bayan ya kunna  light haske ya gauraye dakin.

     Bai tsaya a ko’ina ba sai a cikin toilet din kafin ya direta tare da cewa “Oya yi alwala,Dan na fahimci kin fara raina ni saboda Kinga girma na ko?to idan kina so mu shirya dole kina bin umarni na”.

   Haka ta fara alwalar badan ranta ya so ba.koda ta idar haka ya sake daukarta zuwa dakin.abin salla ya shimfida kafin ya ciromata hijaf da zani.akan rigar ta daura kafin ta saka hijaf din.

Haka ya jasu suka yi salla raka biyu kafin ya dafa kanta sosai yayi ta kwararo addu’o’i Dan neman zaman lafiya da zuri’a dayyi ba.

   A ranta ta rinka mamakin Ashe Yana da zurfin ilimi haka,tunawa tayi da Kaka tace Mata tun Yana da shekara Sha biyar yayi sauka.

   Plate ya dauko da spoon a kitchen sai cup .

Inda ya barta anan ya dawo ya tadda ita,bai Kara kallon inda take ba saida ya zuye soyayyan Naman kazar ya ciyaya leman holandia a cup kafin ya matso gabanta.

Cikin natsuwa ya ciremata hijaf din,zanen ya warware ya aje gefe daya kafin ya ciro Naman ya nufo bakinta da shi Yana cewa “haaaaaa”irin na yara.

Kasa ta Kara yi da kanta tana jin takaici na Wai yau itace aka yima aure Kuma babu dinner ba events ko daya.

  Maganar shi ta Kara dawo da ita daga duniyar data Lula.

“Wallahi ko yau nida ke ne a gidan nan,Kuma kinsan bana son gaddama ko?Dan haka idan baki amsa ba to bazan bari kiyi bacci ba”.

  Tana jin haka da sauri ta bude bakinta saboda yadda idonta yake rufewa saboda tsabar gajiya da baccin da take ji.

   Haka ya ciyar da ita saida ta koshi kafin ta girgiza kanta alamar ta koshi.cup din ya dora saman bakinta shima saida ta kusan shanyewa kafin ya cire shi.kadan shima yaci kafin ya kama 

Hannuwanta ya mikar da ita tsaye ya nufi toilet da ita

ruwa ya zuba Mata ta kiskure bakinta kafin suka dawo.ita dai tana biye da shi kamar jela.

    Cak ya sungumeta suka haura saman gadon.ai ko tuni Seeyerma jikinta ya fara kakkarwa.

Gyara mata konciyarta yayi ya rufe kafafunta da blanket kafin ya Kara Mata gudun A/C.

   Sai a sannan ta sauke ajiyar zuciya jin Yana cewa “konta kiyi baccin ki saida safe kin ji?”.

     A hankali ta fara rufe idonta dukda bata ji dadi a ranta ba ganin kamar ranshi ya baci.

    Kayan da suka ci abincin ya dauke ya mayar dasu kitchen,kafin ya wuce dakin shi.

    Saida ta tabbatar ya fita kafin bacci ya fara daukarta.

  Shiko Muhseen system dinshi ya janyo Yana duba wasu sakonni.ganin wayarshi ta kawo haske ya janyota Dan ganin mai Kiran shi a irin wannan lokacin.

Baiyyi mamaki ba ganin nomber Lameer.

Picking yayi Yana cewa “Wallahi Kai dai Lameer Dan iska ne,yanzu saboda bakinciki ka rinka kirana a irin wannan time din?”.

   Cikin dariya Lameer ya ce “sorry man Kira nayi indai tunamaka kada ka kashemasu yarinya,Dan yau nasan shekarun daka kwashe kana tazurancinka saika fanshe su”.

   “Mtssssss banza ka katse Kiran nan kafin na ci Ubanka,kada ka tayarman da wife tana bacci”.

  Jin haka yasa kit Lameer ya katse Kiran Yana dariyar mugunta.

  Agogo ya duba ganin kusan karfe daya saura tayi ya rufe system din ya dauki wayarshi guda ya nufi dakin nata cike da shaukin San kasancewa da abar kaunar tashi,Dan tunda ya zauna surarta kwai take yimai gizo a idanuwanshi.

   A hankali ya tura kofar ya shiga.hasken wayar shi ya kunna ya karasa bakin gadon.gani yayi ta Kara kyau beautiful sleep.

Dim light ya kunna kafin ya aje wayar shi gefen drower.

Cike da natsuwa ya daga blanket tare da  shigewa ciki.

Motsawa ta fara yi jin kamar ana tabata ganin zata farka yayi saurin saka hannun shi cikin………………….³⁹

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *