DR MUHSEEN CHAPTER 22 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)
Www.bankinhausanovels.com.ng
📝…………….Haka rayuwar su Muhseen da Seeyerma ta kasance cikin farinciki basu da wata damuwa, abinci kuwa daga kowane part ake kawomasu.Ba laifi Seeyerma tana kokari dan ganin ta sauke hakkin auren shi dake kanta,shima fahimtar hakan da yayi yasa yake dan daga mata kafa dan karta gajiya da bukatar shi.
A karshen sati ranar wata lahadi da yamma suka shirya kayansu kama daga kayan sakawa da sauran abubuwan bukata,Basu dauki kayan cikin gida ba, kasancewar gidan da yake a bareak ya saka masu komai na bukata.
Saida suka shiga kowane part dan yimasu sallamar tafiya.da suka shiga part din Ummeey sosai Seeyerma ta ji kunya tun bayan daura aurensu sau daya tazo gaisheta shima da dare ne ya kawota.
Da sauri Ummeey ta rungumeta cike da farinciki ganin yadda yarinyarta tayi gwanin kyau, Bayan sun zauna ta durkusa kasa ta gaishe da Ummeey cike da farinciki ta amsa tana sakamasu albarka.
Muhseen ganin sun manta da shi yasa ya kalli Ummeey yana langabar da Kai gefe daya ya ce “Ni gaskiya ban yarda ba shikenan daga ganinta ni duk an wani manta da ni”
Yana yin yadda yayi maganar cikin shagwaba shi zai baka dariya.
“Kai yanzu ai ka girma”cewar Ummeey tana rike da hannun Seeyerma suka nufi bedroom dinta.
Da kallo ya bisu yana murmushin jin dadi,ganin yadda kowa yake kaunar su.
Wasu ledoji ne masu kyau Ummeey taba Seeyerma kafin suka fito tana cewa “Zan turama son sako ta watarshi saita Baki ki karanta kin ji,sannan nayi mai magana akan ya siyamaki waya saboda ki rinka debe kewa”
Gyada kanta tayi Seeyerma alamar to kafin suka fito,har bakin kofar falon ta rako su kafin ta koma.
Daga nan part din Hajiya Kaka suka nufa.anan suka tarad da yan’mata gidan suna hira a falo.Direct cikin uwar dakan ya nufa,ita Kuma Seeyerma ta tsaya gaisawa da su safna.khadijah sai zuzuta kyawunta take yi tana Santi,ita dai bata cewa komai sai dai ta kallesu tayi murmushi.
Cikin muryar rada kahdija ta ce “Gaskiya Seeyerma daga ganin sojanmu yana Jan Kaya, kunyi wani fresh da ku,To yanzu ya kika ji da garjejen tazuru Kuma?”tana rufe bakinta alamun zata iya saka dariya.
Cikin turo baki Seeyerma ta ce “To magulaciya Ina ruwanki koma dai me yanzu ai mijina ne,sai dai idan kece tazuru eheee”ta shigewarta dakin Kaka ta barsu anan sake da baki suna mamaki.
“Uhmm su miji manya”cewar Safna tana rike habarta alamun mamaki.
Koda ta shiga a saman kafet ta taras da kaka,Dan haka ta matsa jikinta tana cewa “Kakata ta kaina duk fishin ne haka kika kyale ni”
“Uhm oh ni maryama yaran nan Baku da kunya,wato sai yanzu Zaki zo inda nake ko?shima danbanza tunda yaga ya kamaki a hannu ya manta da ni,ko irin dahuwar nan baza’a Kawoman ba”.
Sosai ta basu dariya Kaka kenan mai bakin cin dadi,ita dai ta ci abu mai dadi shi ne burinta.
Sun dade a part dinta suna Shan hira kafin Suka fito tana yima Muhseen gargadin ya bi yarinyar mutane a hankali.
Da haka suka karasa inda yayi parking motar shi su sadik na biye da su a baya,ganin an loda kayan a but yasa ya ciro kudi Yana bawa matasan kannen na shi kafin Suka shiga motar ya tayar.
Tunda suka fito daga cikin gari ta fara bacci Yana rike da hannunta guda,dayan Kuma Yana tuki jefi-jefi yakan juyo ya kalleta ganin yadda baccin ya karamata kyau tamkar wata cute baby.
Sanyin AC ya Kara masu ganin ta fara zufa.
Anan kiraye-kirayen sallar magriba suka shigo cikin bareak din.Bayan ya dan yi tafiya mai nisa kafin ya karaso block dinsu.
Sai a lokacin ta dan motsa.
Saida ya fito kafin ya haura saman dakin shi ya bude gidan.
Koda ya dawo bata farka ba,kawai ya nade hannun rigar shaddar dake jikin shi cak ya dauke ya manneta da jikin shi.A hankali ya tura kofar kafin ya shimfidar da ita saman doguwar kujera Yana mannamata kiss a libs dinta.
Yana fitowa yaga wani sojansu zai wuce shiya taya shi ya shigo da kayan kafin ya rufe kofar.ganinta yayi zaune tana lumshe ido alamar baccin bai isheta ba.
Tashi kiyi sallah ya ce kafin shima ya shiga toilet din dake cikin falon.fes yaga gidan saboda ya sanar da abokinshi zuwansu shi ne ya saka aka gyara.
*BAYAN WATA HUDU*
Sosai masoyana suke durzar soyayyar su ba tare da wata damuwa ba,tun zuwansu da kwana biyu ya siyomata wata kamfanin Samsung Mai tsada.hakan yasa ta ji gwanin dadi tana waya da su Aunty Hindatu da kaka.koda bata Kira duk bayan kwana biyu sai Aunty Hajara ta Kira dan ta ji lafiyar su.
Ta bude WhatsApp aka sakata group dinsu na family.Amma ta ji haushi da Muhseen ya hana su je family meeting Wanda za’a gabatar nan da sati daya .saboda Yana da ayyuka.Amma taci alwashin yau zata lallaba shi harya amince dan tana kewar yan’uwan nata dukda suna waya,Amma tana so ta ganta a cikinsu.
Ranar Muhseen suna da yawan ayyuka a office hakan yasa bai dawo ba sai karfe ukku na rana,haka ta kammala abincin rana ta tsala wankanta da kwalliya tana jiran gogan nata Dan tasan yau sai sun sha dabir da shi,Daman Yana jin haushin yadda take kin yarda da shi,saboda cikin dake jikinta lokutta da dama sai ta ji Bata so ya kusanceta.
Koda ya dawo ta taimaka mai ya kimtsa jikin shi,suna zaune saman dinning Yana cin dambun shinkafa da miyar albasa da tayi masu.kallan shi tayi ganin yadda duk ya wani hade rai shi nan Wai yana fishi kamar ba karamin yaro yake komawaba idan ya haye jirgin dadi.
Saida ta langabar da Kai cikin shagwaba ta ce “Please Sojana ka amince muje meeting din nan,wallahi Ina kewar su Dijah”tana kwalkwal da idonta alamun zata yi kuka.
Kamar ya ce bai amince ba,Amma sai wata dabara ta fadomai.Nan ta ke ya ce “Ok ba matsala na amince”
Cike da farinciki ta dawo saman cinyarshi tana yimai kiss saboda ta ji dadin yadda ya amince.A ranshi ya ce “Uhmm yarinyar anjima zamu hade sai kin raina kanki tunda nabi dake ta sanyi kinki bani hakki ne,sai kin bani kafin kije katsina”.
Haka ranar ta wuni cikin farinciki da ya ce tayi Mai abu zata yi sauri ta yi.
Da magriba ta je masallaci shi ne bai dawo ba sai bayan sallar isha’i.
Anan falo suka ci abincin dare kafin suka dan taba kallo duk tana like jikin Shi,shiko daurewa kawai yake yi.saida karfe shadaya tayi kafin suka nufi bedroom.
Bayan sun konta har bacci ya fara daukarta ta ji alamun yana lalubarta,sosai gabanta ya fadi dan tunda tayi sati daya rabonta da shi harta Kara Yar kiba,Danta fahimci baya gajiya.
Cikin alamun kuka ta ce “uhmm kayi hakuri bacci nake ji kaina Yana ciwo”.
Jin haka yayi saurin tura bakinshi cikin nata Yana canza akalar wasan na shi.ganinfa da gaske bazata bashi ba ya ce “wallahi idan baki bani ba to ba ke ba zuwa katsina sai bayan kin haihu”tana jin haka ta tsorata dan ta tabbatar da gaske yake yi tsaf zai iya hanata zuwa”Bata da yadda zata yi dole ta biyemai.Aiko ta gane kuranta dan saida ta galabaita.koda asuba dakayar ta tashi.
Haka wannan sati yayi ta tafiya daya matsu saiya ce daitay amince kafin ya kaita katsina,da haka ya fake Yana ta kwasar gara abinshi.
Da ranar Asabar ta zo tunda asuba ta fara shiri,bayan ya dawo daga masallacin yayi kicin-kicin da fuska ganin haka yasa ta saka mai kuka,A karshe dai saida ya samu ya dan Kara sacond round kafin suka yi wanka suka kama hanyar katsina.
Sosai jikinta yake ciwo dan duk wannan satin ta amshi wuta ba laifi.
Suna shigowa Derect part din Hajiya Kaka suka sauka,shi Kuma ya wuce tsohon part din shi,Dan yayi ta kwakwar ta bishi ta kiya saboda tasan bazai kyaleta ba.
Haka ya karasa badan ranshi ya so ba.
Cike da murna suke rungume juna ganin Seeyerma ta ta zo.
Aunty Hindatu dake zaune da tsohon cikin ta ta ce “Kai Dan Allah ku saketa kada ku jamana asara”Da sauri su Khadijah suka saketa suna mamakin Wai Seeyerma ce da ciki.
Anan suka baje suna ta fira ana shan dariya.
Da rana ta yi ta ce ita zogala take so a kwada mata.
“To sai ki nemi Wanda yayi maki cikin,Amma mu nan ba bayin ke bane”cewar Safna.
Aiko Seeyermar kamar jira take yi ta fara Kiran wayar Muhseen.tana jin ya daga ta saka mai kuka harda sheshsheka.
Sosai ya rude yana tambayarta meya faru.
Cikin kukan take sanarmai.cewa yayi kada ta damu yanzu sadik zai kawomata.
Yana aje wayar su Khadijah suna ta mamaki Wai ta Muhseen ne yake rudewa akan Seeyerma lallai namiji idan ya je hannun mace ba komai ne ba.
Ko minti ashirin ba’ayi ba saiga Sadik ya shigo da ledar zogala a hannunshi.
Saida ya aje kafin ya kallo Seeyama Yana cewa “Wallahi kedai kin shiga ukku haka kike yimai Yana ta kakkarwa akan ki,haka ya rude yana ta faman kwadamin Kira nayi tunanin wanine ya Mutu,wai saida na zo na ji Yana cewa na siyomaki zogala”ya karashe maganar Yana harararta.
Cike da jin haushi ya fita.
Sosai ya Basu dariya ganin yadda ya zage Yana ta faman fada.
Haka ta kwada abinta ta ci ta koshi tabi lafiyar gadon Kaka tabar su Safna suna hira.
Da yammaci haka aka gudanar da family meeting cike da tsari.komai ya gudana yadda ake so anci ansha an gabatar da sabbin tsare-tsaren estate.
Da dare suna part din Aunty Hajara hira suke yi a Falo da su Khadijah.kiran shi ta gani taki dagawa,haka tana kallo yayi ta faman Kira ta kyale shi.koda ya Kira Kaka ta ce suna part din Aunty Hajara Haka ya nufi part din ranshi a bace.tana ganin shigowar shi tayi saurin rufe idonta alamun bacci take daman saman doguwar kujera take konce.
Yana zuwa yaga bacci take yi ya juya ya shiga dakin Aunty Hajara.
Da sallama ya shiga Bayan sun gaisa yayi shiru Yana sosa keya.kyale shi tayi tana cigaba da tura sako a wayarta.ya Dade a haka kafin ya ce “Bari na je saida safe”
Amsawa tayi da “Allah ya kaimu”kafin ya fice.
Bai tsaya a falon ba ya koma part dinsu Yana jin ranshi a bace ga wani mugun feeling da yake neman hanashi konciyar hankali.
Bayan ya fita Aunty Hajara ta fito falon haninta zaune suna falls labari yasa ta ce “Seeyerma tashi ki tafi part dinki hirar ta isa haka”
Kwalkwal tayi da ido tana San yin kuka.Aunty Hajara gaba tayi tana cewa “Kada ki bari na fito na tadda ke,Kuma idan Naga kin nufi wani part din sai ranki ya baci”.
Ba yadda zata yi Dan dole ta saka mayafinta tana kunkuni ta fita su Khadija suna yimata dariya.
Safna ta ce “Yarinya gwamma ki je ki amso darasi”Tana jinsu ta kyalesu tayi gaba.
A hankali ta tura kofar falon wani sanyi ta ji ya ratsata ta lumshe idonta.
Anan saman kujera ta konta,duk abinda take yi duk Yana kallonta.saida ya Bari ta fara bacci kafin yazo ya sungumeta suka nufi bedroom.Saman gadon ya azata yabi samanta Yana sakarmata nauyin shi.
Cikin gagan bacci ta ce “wayyyooo cikina mutuwa zan……..”
Ruf yayi saurin rufemata baki da nashi Yana gyara Mata konciyarta saman kirjinshi……………Ruf yayi saurin rufemata baki da nashi Yana Kara gyara mata konciya bisa saman kirjinshi,hakan yasa tayi luf tana sauraren yadda yake sarrafa.
Da asuba anan tayi wanka tayi salla shi Kuma ya wuce masallaci.
Bacci Suka Kara komawa saboda gajiya da take ji.sune basu farka ba sai wuraren karfe shadaya saura,shima Kiran wayar da ake yi ne ya tayar da shi.ganin haryanzu baccin take yi yasa ya zare jikin shi ya fada toilet.
Har saida ya gama shiryawa bata tashi ba.A hankali ya dagota tare da Kiran sunanta.
Dakyar take bude idonta saboda baccin daya addabeta,Dan dole ta tashi.
Kafin ta karasa shiryawa an kawo masu kayan break.hadamasu tayi bayan ta Kara kimtsa dakin.Bayan sun ci break din ta ce part din Hajiya Kaka zata je.Bai hanata ba dan haka ta hijaf dinta ta fita.
Shima cikin gari ya nufa.
Da yamma shiya dauketa a Mota suka nufi gidan Aunty Aliya.
Sosai tayi masu tarba Mai kyau,Bayan sun gaisa ta kalli Muhseen tana tambayar shi
“Yanzu son tunda aka yi biki sai yau kukaga damar zuwa,to banda Aunty Hajara ta Kira ka may be bazaku zo ba ko?”
Kasa yayi da kanshi Yana Jin babu dadi a ranshi Aunty Aliya ta cika korafi.
“Kiyi hakuri Aunty kinsan yanayin aikina wallahi bana samun time sosai ko yanzu nayi niyar muyi two days Amma babu hali dole zamu koma gobe insha Allah”.
“Allah ya kaimu”cewar Aunty Aliya tana mayar da hankalinta gurin Seeyerma.
Ita dai Bata ce komai ba Dan tasan Auntyn nasu fada ne da ita,yanzu ta ce tayi laifi.
Sun dan Jima a gidan kafin Suka ce zasu tafi.
Bedroom ta kama hannun Seeyerma suka shiga.
Saida ta zaunar da ita a bakin gado kafin ta daga weardrop.wata leda ta dauko ta bata.kafin suka fito.
Har wurin parking ta rakasu,saida taga tashin motarsu kafin ta juya cikin gidan zuciyarta cike tab da kaunar yarinyar Dan idan ta kalleta tana tunamata da abubuwa da yawa.
Ba tare da bata lokaci ba su Seeyerma a washe gari suka koma Daura badan ta so ba,saboda ji take kamar kada ta rabu da Yan’uwanta.
Satin daya zagayo a cikin shi ne aka daura auren Ameerah da Nurah bisa sadaki dubu dari ba wata hidima aka yi ba,saboda idan kaga Seeyerma gaba daya ta sauya tamkar ba ita,duk tayi sanyi.
Wasu daga cikin family gidan fulani sunje Amma daga Uncle Yusuf sai su Aunty Hajara Wanda abisa Umarnin Kaka ne ta tilasta zuwa.
A ranar da aka Kai Amarya ta Sha kuka,Dan tun Bayan tafiyar abokanshi yake yimata rashin mutunci da wulakanci,haka Suka kwana Dan ya ce shi fa baiga abinda zai amsaba bayan ta gama mu’amulla da wasu banzaye hadda mata,Dan abinda ta rinkayi Yana da masaniya Akan shi.
Tunda safe ta Kira Hajiya Mariya ta fadamata,hakuri ta bata akan wata rana zai daina yimata.
Haka rayuwar su tayi ta tafiya badan tana jin dadin zama da shi ba,saidan Bata da yadda zata yi idan ta tafi to shima zawarcin wani tashin hankali ne na musamman.
*BAYAN WATA BIYU*
Su Aunty Hindatu da Rukayya sun sauka lafiya,yaransu duk maza ne daya yaci sunan Kaka Muhammad wato Dadyn Muhseen,sai Dan gidan Rukayya ya ci sunan Uncle Yusuf.
Dakyar Muhseen ya yadda ya kawo Seeyerma ranar ya gobe suna itama da tsohon cikinta Wanda take gaf da haihuwa.
Ranar suna ansha bidiri inda Suka yi ankon leshin Mai kyau da tsada.
Dakayr Seeyerma ta saka rigar saboda yadda cikinta yayi girma duk kafafu sun kunbira.
Bayan suna ya ce ta shirya su tafi Aunty Hajara ta hana tafiso saita haihu kafin ya tafi da ita.
Ansha dabir da Muhseen daya ga dai anfi karfin shi dole ya hakura ya tafi ya barta badan ranshi ya so ba…….⁴⁵