DR MUHSEEN CHAPTER 24 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)

DR MUHSEEN CHAPTER 24 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

                📝……………..Tunda ya haura  motar shi saman titi yake faman sharara gudu,karfe bakwai da rabi ya iso garin katsina.Direct estate ya fara shiga ya wuce part dinsu saida ya Kara watsa ruka kafin ya fito,har zuwa wannan lokacin babu Wanda yasan da shigowar shi.part din Kaka ya shiga,shiru ya ji babu kowa sai iskan fankar dake kadawa. Bedroom din ya nufa bakinshi dauke da sallama.

Hajiya Kaka dake faman gyangyadi bisa abin salla tana rike da casbaha.jin sallamar yasa ta amsa tana kallan bakin kofar.

       Cike da mamaki ta rike habarta tana kallan shi.

 Saida ya zauna kafin ta ce “lallai Mai gida irin wannan safiya haka kamar Wanda za’a kwacema yaron?”

    Saida ya jingina kanshi da filon kujerar ya rufe idonshi kafin ya ce “Nidai ba wannan ba yanzu ki bani ruwan zafi na sha,asibitin zan wuce”.

   Da sauri ta kwala Kiran Asabe Mai yimata aiki.tana kitchen ta ji Kiran tsohuwar ta nufi dakin.

Saida ta gaishe da Muhseen kafin ta ce “Hajiya gani Mai kike da bukata?”

 

   “Ki hadomai ruwan tea Mai kauri da kayan yaji”

  Da “To” ta amsa kafin ta fita.

Jim kadan ta dawo hannunta rike da dan madaidaicin cup mai kyau.

Ajewa tayi kafin ta fita.

Ganin Yana da zafi yasa ya bari yadan sha iska.rabin cup din ya sha kafin ya mike Yana duban Kaka ya ce “Bari  na je anjima Zan dawo”ya fita daga dakin.

   Wurin da yayi parking motar shi ya nufa,Yana shiga ya nifi asibitin.

Daidai lokacin daya shiga daidai Seeyerma ta farka tana shan tea boy Yana hannun Aunty Hajara sai satar kallonshi take yi sak take kama da Muhseen.

   A hankali ya tura kofar dakin ya shiga fuskarshi cike da fara’a.

Gaba dayansu Suka mayar da kallonsu Kan kofar.Sosai Aunty Hajara ta cika da mamaki ganin shi ne yake shigowa.

    Cike da zumudi ya karaso cikin dakin,kujera ya ja gefen Seeyerma ya zauna Yana fuskantar.sai a sannan ya lura da Aunty Hajara dake gefe daya zaune tana kallanshi.

Dan shafa sumar kanshi yayi kafin ya saddar da kanshi kasa Yana cewa “Aunty Ina kwana?”

   Cike da fara’a ta amsa da “Lafiya Lau uban da,irin wannan sauko haka kamar zamu kwacema yaron”

  Shidai Muhseen baice komai ba,sai kasa da yayi da kanshi.yana so ya amso yaron Yana jin kunya.

Lura da hakan da Aunty Hajara tayi yasa ta mike ta doramai yaron saman cinyarshi,da sauri ya saka hannu biyu ya rike shi Yana Jin wani dadi a ranshi na yau shima ya zama Uba.

  Kiran salla yayima yaron a kunne kafin ya tofamai addu’o’i tare da radamai suna.ruwan zanzam Aunty Hajara ta mikomai da dabino ya tauna ya sakamai a baki.

  Duk abinda yake yi Seeyerma tana kallon shi ta kasan idonta.ji take tamkar ta rungume su dan dadi.

  Tuni Aunty Hajara ta fice daga dakin,waya ta Kira tana sanar da Yan Kanto da sauran yan’uwa.

Yana ganin ta fita yayi saurin ta shi ya zauna gefen gadon,ya hada da ita da boyn ya rungumo su jikinshi Yana sauke ajiyar zuciya.cike da jin dadi ya ce “Alhmdl Allah na godemaka daka azirta ni da Mata da yaro,Allah ka albarkaci rayuwar mu”

   Cike da so da kauna Seeyerma ta amsa da Amin.

Sun dade a haka kafin ya saketa Yana kallan kyakkyawar fuskar yaron.

   “Gimbiyata Kinga kama yake da ni ko?”

  Kasa magana tayi sai lumshe idonta tayi tana Jin kaunar su tana Kara tsaga jinin jikinta.

   Tunda Muhseen ya shigo ranar anan ya wuni,Duk Wanda ya zo anan ake taras da Shi.ranar yan’uwa da abokan arziki haka suka yi ta tururuwar zuwa dubata da ganin jariri.

   Kwanansu biyu tayi Shar abinta kamar ba ita ta haihuba,A ranar da yamma aka sallamesu suka dawo gida aka hau shirye-shiryen hidimar suna.

Sati na zagayowa yaro ya ci sunan Sarki Abdulkareem.

Anyi hidima ta gani ta fada,an ci an Sha.Anko kuwa anyi yakai kala bakwai kama daga leshin, material,Atamfa,shadda na manyan kudi.

   Boy Abdulkareem kuwa ya samu akwatina na Kaya da makudan kudade daga yan’uwa da abokan arziki.duk Wanda ya zo da abinda zai kawo na kayan suna.Raguna saida aka yanka manya guda ukku da shanu guda biyu.atamfofi aka rinka rabawa da kayan suna irin su butoci,robobi,da jaka masu kyau.musamman aka dauko Balancy photographer yayi ta kashesu da hotuna masu kayatarwa,Hadi da Vedios.

     Bayan suna da kwana biyu Yan nesa duk sun fara komawa gidajensu , sai wadanda baza’a rasaba.

Seeyerma kuwa tana part din Aunty Hajara ita ke kula da su da abincinsu Mai Gina jiki, Abdulkareem kuwa haka yake yini a hannun su Khadijah da Safna sai idan za’a bashi mama su kaimata shi, haka wataran zasu dauko yaran su Aunty Hindatu da Rukayya su yini a wurinsu.Tuni Aunty Aliya ta koma gidanta zuciyarta cike da wasi-wasin na abinda take kudirtawa a ranta.

Ranar da aka cika kwana na hudu da yin suna ranar Muhseen ya shirya komawa bakin aikin shi.

Koda ya shiga dakin su Seeyerma tana shan hadin kunu Mai dadi Wanda Ummeey ce ta aikomata shi ya ji kayan yaji sai tashin kanshi yake yi.

   Khadijah tana ganin ya shigo ta gaishe shi tana mikamai Abdulkareem kafin ta fita.

  Bakin gadon ya zauna Yana kallan yadda ta Kara wani irin kyau tamkar balarabiya.

  Addu’a ya Kara tofama yaron kafin ya dubeta Yana cewa “Ki daina bari ana jagula shi,jikin shi zai rinka ciwo,Kuma inaso ki shirya zamu tafi”

 Cike da mamaki ta aje cup din tana kallanshi, ganin yadda ya sha toka irin serious din nan.

   Saida ta muskuda gefe daya kafin ta ce “Uhm ka fadama Aunty Hajara kafin ka fadaman,kasan bazai yiwu ace na bika ba dole Ina bukatar kulawa”.

  Shiru yayi tamkar bai ji me ta ce ba,sai wasa yake yi da Abdulkareem Yana faman murmushi.

  Itama shiru tayi tana kallan ikon Allah,mutum kamar mai aljanu yanzu sai canza fuka.

  Saida ya ga yaron bacci ya dauke shi kafin ya shimfidar da shi cikin dan gadon shi irin na yara.

Kusa da ita ya dawo ya zauna Yana kamo hannunta.kiss ya mannamata a libs dinta kafin ya saka idonshi cikin nata Yana yimata wani irin kallo mai cike da  wata ma’ana.

Cike da kasala tayi saurin yin kasa da idonta jin bazata iya daure kallan kwayar idon shi ba.sun Dade a haka kafin ya mike Yana cewa “Zo muke mota na baki sako,inason na wuce yanzu yamma tana Kara yi”ya fadi haka bayan ta mike ya nufi hanyar fita daga dakin.

   Cikin sanyin jiki ta dauki mayafinta ta dora saman doguwar rigar leshin din tare da saka silifas tabi Bayan shi.

   Haka ta take Mai baya har bakin motar.Sit din driver ya bude ya zauna ya dauko wani kwali Yana mikamata tare da cewa “ki kularman da kanki,kuna yin arba’in zan zo na dauke ki kin ji”

   Gyada kanta ta Kara yi.

  “Ki yiman kiss Wanda zan na rinka tunawa,Kuma ki rinka rike wayan ki saboda zan rinka Kira ina jin lafiyar boy na”

  Hannunta ya kamo ya zaunar da ita saman cinyar shi Yana mannamata wani zazzafan kiss a gefen kuncinta.

Itama yimai tayi suna dariya cike da san mijin nata.Addu’a tayimai kafin ta fito daga motar bayan ta rufemai ya ja ya fara tafiya tana dagamai hannu harya fice daga gaban part din.

  Saida ta sauke ajiyar zuciya kafin ta kalli ledar daya bata ta juya y cikin gidan

………Bayan tafiyar Muhseen da sati biyu kullun saiya Kira a waya sun sha soyayya yakan ji kukan jenior idan yana rigima,har zuwa wannan lokacin a part din Aunty Hajara take wasu lokuttan takan je part din Hajiya Kaka su Sha hira da Yar tsohuwar.

       Haka rayuwa tayi ta tafiya jenior Yana Kara girma da wayo.

Inda aka yima Muhseen transfer zuwa bareak din Abuja,sosai ya ji ba dadi dan ya Saba da Daura Amma ba yadda zaiyyi shi aikin uniforms ya gaji haka.

Anyi haka da sati biyu ya zo katsina ranar wani weakend inda ya kwaso sauran kayan su daga nan zasu wuce garin Abuja,a Kuma ranar ne da yammaci su Hajiya Mariya da Ameerah suka shigo estate din.Direct part din Hajiya Kaka suka nufa.bata yi mamakin ganinsu ba domin tasan koba dade wannan ranar zata zo.

Nan take Ameerah ta saka kuka itama Hajiya Mariya ta fara kuka tana neman gafarar su Hajiya Kaka.Duk Wanda yake a zaune a falon saida suka bashi tausayi,Amma tuno da mugun hali irin na Hajiya Mariya yasa kowa ya kyaleta sai Ita Seeyerma ta ji tausayin su duba da yadda suka yi nadama,ta daga baki da niyyar yin magana ta ji Hajiya Mariya tana cewa “Dan Allah ku yafeman ni ce nayi sanadiyyar mutuwar Fatima da mijinta bayan dana gano tana raye,Amm……….”kafin ta karasa bayaninta Uncle Yusuf yayi saurin mikewa ya dauketa da mari cikin kakkarwa ya fara nunata da yatsa Yana cewa “Mariya ashe ke macuciya ce azzalima,duk yadda mahaifiyarmu ta dauke ku matsayin yan’uwa na jini ku ba hakane ba a bangaren ku,to ki sani bazamu taba yafemaki ba”Yana kaiwa nan cikin bacin rai ya fice daga falon Yana hici.

   Shima Dadyn Muhseen fita yayi Yana Kara jin tsanar Hajiya Mariya na ninkuwa a cikin zuciyar shi.

   Kuka suke sosai harda sheshsheka,ita ko Seeyerma tamkar gunki haka ta zama nan take abubuwan da suka faru a ranar suka fara dawomata tamkar a mafarki.

    Ranar 12 ga watan June a shekarar 2015 ranar juma’a da misalin karfe hudu na yammacin ranar ita da ya Muhseen da Khadijah a Mota suka nufi Air Force dan dauko Momynta da dadi Wanda saukarsu kenan daga Kasar Sudan,A ranar Seeyerma cikin farinciki take domin tunda ta dawo Nageria bata Kara ganin iyayenta ba,sai idan ya Muhseen ya Kira Momynta a vedion call saiya bata su gaisa.

Suna gaf da karasawa titin da zai sada su da Air Forte din A daidai wannan lokacin ne Hajiya Mariya ta Kira wayar Muhseen tana cewa su dawo gaya can ta saka Driver ya dauko su,hakan yasa suka juyo da Kan motar zuwa gida ba tare da tunanin komai ba,Bayan isowarsu da kamar mintuna goma aka Kira waya cewar motarsu tayi accident a daidai seterdio na ball sun rasa rayukan su,Amma shi drivern Yana asibiti,sosai hankalin mutanen estate din ya tashi nan take suka garzaya,inda aka taras da gawarwakin su a rufe.haka aka yi suturarsu,inda anan take Seeyerma tayi doguwar suma har tsawon kwana biyu bata san inda kanta yake ba.

  Da sauri Seeyerma ta mike tsaye hannunta daya dafe da kanta dayan Kuma tana nuna Hajiya Mariya cike da kakkarwa take ja da baya,ganin alamun zata fadi yasa kadija tayi saurin kamata ta zaunar da ita,a lokacin ne Muhseen ya shigo falon bakin shi dauke da sallama.

Da sauri ya karaso Yana kamota jikin shi tare da tambayar meke faruwa,kowa shiru yayi jin alamun kuka a gefen shi yasa ya juya Yana kallon su Hajiya Mariya.anan ya fahimci inda matsalar take,cak ya dauketa a hannun shi Yana cewa Khadijah ta taho da Jenior part din su.

  Bayan fitarsu Hajiya Mariya ta tsagaita da kukan kafin ta kalli Hajiya Kaka tana cigaba da cewa “Tabbas nasan mun kasance butulu,bamu yimaki adalci ba,mun cutar da ke,Amma Dan Allah Ina rokon ki da ki yafemana,yanzu haka Ameerah mijinta yayimata duka ya saketa gashi cikin dake jikinta ya ce ba nashi ba ne,Nima yanzu haka na rasa Mai aurena,Dan Allah ku ce kun yafemana ko mun samu saukin abinda yake bibiyarmu”ta aje maganar tana Mai share hawayen fuskarta.

    Kaka saida ta danyi shiru kamar bazata ce komai ba kafin ta nisa tana kallon Ummeey data dukar da kanta tana kukan zuci.

  Cike da tsufan Kamala ta ce  “Ummeey ya kamata ku fara neman yafiyarta somin kun cutar da ita,kun rabata da mijinta na tsawon wani lokaci”

  Baiwar Allah Ummeey da sauri ta ce “Ni na yafemasu,Allah ya yafemana gaba daya”.

   “To Nima na yafemaku,Amma ita Seeyerma ku bari ba yanzu ba,domin yanzu bata cikin natsuwarta”cewar Kaka.

  Sosai su Hajiya Mariya suka ji dadi,da haka suka koma gida inda suka tarar mahaifyar su Bata da lafiya Balaraba kenan kanwar Hajiya Kaka.

   Shiko Muhseen tunda ya fita da Seeyerma a hannun shi bai tsaya da ita ko Ina ba sai a bedroom na part dinsu, anan yayi ta faman rarrashinta da Kara bata hakuri, harya samu ta dan sauko Amma hoton wannan ranar yaki gogewa daga zuciyarta.⁴⁹

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *