DR MUHSEEN CHAPTER 3 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)

DR MUHSEEN CHAPTER 3 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)



                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

sai akan jikin Muhseen,gaba daya tea din ya zube a kayan shi.jin wani zafi ya ratsa shi yayi saurin mikewa tsaye Yana nunata da yatsa cikin zaro ido,kokarin magana yake yi Amma bakin shi yaki budewa ballantana ya furta abinda yayi niyya.jin karar faduwar seeyerma yasa ya kalli inda Aunty Hajara take zaune,wadda sai a sannan tayi yunkurin tashi.gaba dayansu kanta suka nufa jin ta saki wani uban Kara mai rikitarwa,cikin lokaci daya jikinta ya saki babu alamar numfashi a tare da ita.”Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un,Hasbunallahu wani’imal wakil,ohhhh ni Hajara mezan gani haka,Soja dauko ruwan sanyi a shafa Mata”saboda tsabar rudewa da yayi kasa tashi yayi daga gurin.saida Aunty Hajara ta Kara maimaitawa kafin ya mike.tunani ne ya cika zuciyar shi,”kada dai ace yarinyar nan ta tsorata da abinda nayimata,idan ko

hakane to na bani nikam”harya kawo ruwan Yana tunani da wasi-wasin abun a ranshi.gefe daya ya koma ganin Uncle Yusuf ya shigo.fara tambayar su yayi “lafiya meye ya sameta”Aunty Hajara ce ta fadamai abinda ya faru tana faman shafa Mata ruwa a fuska.ganin haryanzu bata farka ba yasaka Uncle Yusuf ansar kofin ruwan ya fara tofa addu’o’i a ciki.saida ya dau tsawon lokaci Yana yi,kafin ya watsa Mata a fuska.sai dai abinda ya Kara tsorata su cikin Kara ji ta farka.tana kankame hannun Uncle Yusuf ta kasa bude idonta sai cewa take “Dan Allah ku raba Ni da shi,wallahi shi ne Wanda nake gani a mafarki na,kamani zai yi”addu’o’i sukayi ta tofamata har tadan lafa daga fisge-fisgen da take yi,sai faman ajiyar zuciya take yi.shidai Muhseen Yana gefe daya ko motsin kirki ya kasa yi.sai tunani daya addabi rayuwar shi.kallo shi Uncle Yusuf yayi Yana cewa kaje ka canza kayanka daman muna san ganinku a part din Kaka yanzu akan maganar da mukayi daku da su Faruk.cikin sanyi ya amsa da “To”kafin ya fice daga gidan.Ajiyar zuciya Aunty Hajara ta Kara saukewa ta ce “Ni wallahi abin ya bani mamaki,lafiya lau muke zaune da ita saita shiga kitchen tana cewa tea zata sha,shi ne fa bayan ta fito kaman taga wani abu,kawai tana ganin Soja sai gani mukayi ta saki cup din ta zube a kasa”

“Allah ya kauta cewar Uncle Yusuf”bayan ya mike tsaye”kada ku tasheta tunda ta samu bacci,zance nayima Kaka bayani kafin ta farka sai musan abinyi,dan jiyama sunce ta saida ta suma,to Yana da kyau a ce an gano matsalar tun kafin tayi nisa”.

“To Allah ya Kara karemu gaba daya”cewar Aunty Hajara.Amsawa yayi da Amin kafin ya juya zuwa part din kaka.haka Aunty Hajara tayi ta tofamata addu’o’i,ba tare data matsa daga kusa da ita ba.

A Sudan kuwa daidai lokacin Kaka tana kitchen dan girkama Mahaifiyar su abinci,Wanda ka’idar tace Bata yadda da kowa yayi masu girki ba .aiki take yi Amma hankalinta gaba daya ya tafi gurin tunanin halin da dannata zai da Yar marainiyar yarinyar da Bata da uwa bata da uba zasu kasance tun bayan tahowarta .jin motsin mutim a bayanta yasa tayi saurin juyawa dan ganin kowaye.Gimbiya Zulaihat ce jingine jikin kofa ta hakince tana yimata kallon sama da kasa.ita dai Ummey juyawa tayi tana cigaba da aikinta Dan tasan fitina ce ta kawota.cikin takama Gimbiya Zulaihat ta ce “Aikin banza anki zaman gidan miji,saina iyaye ai duk Wanda bai ji Bari ba ya ji hoho,a to”tana gama fada ta zuya kuyangunta na take Mata baya ta nufi part dinta.jin alamun ta tafi yasa Ummey sanyan gefen doguwar rigarta ta goge siraran hawayen da suka zubomata.a hankali ta juye dankalin data soya a karamin plate ta nufi dakin mahaifiyar tasu.a zaune ta tadda su bakin gado ita da Laila suna labari.akan wani dan karamin table ta aje race “Ummahmu ga shi na kawo maki”da to tsohuwar ta amsa tana fadada murmushin ta,ganin yanayin Diyarta ta ya canza alamar tayi kuka yasa tace “ki kasance mai juriya da hakuri kamar yadda nasan ki,duk mimuni na duniya sai Allah ya jarabce shi ta hanyoyi da dama,kada kiyi sake hakurin ki ya kasa,insha Allah diyata zakiyi farinciki mai dorewa”sosai Ummey ta ji dadin nasihar mahaifiyar tasu,shiyasa akoda yaushe take alfahari da samunta a mazaunin uwa a garesu.daga haka sukayi shiru taci gaba da cin dankalin.Laila kuwa tuni ta fice wurin Inna Asabe mai yimasu hidima Dan nane wurin hirarta.sun Jima a haka kafin ta fara jiyo Karan wayarta yana tashi wakar larabawa ce,cikin kidan taushi da sanyaya zuciya.cikin sauri ta dauko wayar ganin sunan Son dinta yasa ta fadada fara”arta,a ranta tace Lallai al”amura sun fara warwarewa tunda har yarona Yana kokarin kirana.da sauri ta daga tana cewa “Assalamu Alaikum Dana abin alfahari na”shima cikin Kamala ya amsa sallamarta dukda muryar shi ya nuna akwai damuwa.cikin yaren larabci ya ce “Ummeyna Ina Lailata da Yar tsohuwa”saida ta kalli inda mahaifiyar tasu take zaune kafin tace “Duk suna cikin koshin lafiya,Amma muryarka ta nuna akwai damuwa,Dana ka sanar Dani meye yake damunka”saida ya furzar da wata siririyar iska daga bakinshi ,Yana kokarin rufe part din kafin ya ce “Seeyerma”da sauri ta ce “Ya subahallah meya sameta ,kada kace itama cutar da ita zasu yi,Dan Allah son kada ka Bari wani abu ya samu marainiyar Allah,wallahi tunda na taho hankali na ya kasa konciya”jin tayi shiru tana sheshekar kuka yasa ya ce “kiyi hakuri Ummeyna haryanzu bamusan meye ya sameta ba,Amma zuwa anjima insha Allah zamu Kira Malam Muttaka yayi Mata karatu,Insha Allah komai zaizo karshe ki kontar da hankalin ki,Ina Yar tsohuwa bata wayar na gaisheta”mikawa Mahaifiyar ta wayar tayi tana goge gunyun kollar daya zubomata .duk maganar da suke yi Hajiya Aishatu tana jinsu.saida ta tabbatar ta saita wayar a kunnenta kafin ta ce “Kai dai akwai ja’irin yaro,idan kasan danka rinka sakaman ita kuka ka Kira to mun yafe Kiran”cikin taushi yayi Yar dariya tare da cewa “tsohuwa mai ran karfe ,da Ina addu’ar kiga matana,Amma tunda kince haka shikenan bazanyi aure ba sai idan kin tafi”Yana kunshe dariyar shi Dan yasan yanzu zata hau sama.Aiko sai ji yayi tana cewa “yooooo karkayi kayi ta zama da tazurancinka nidai nasan duk wacce zaka auro bazata kaini kyau ba”sosai ta bashi dariya.”Haba tsohuwa ni yarinya zan auro mai sabon jini keko ai sai a…….”tarar numfashin shi tayi da cewa “ita zatama tsufa kamar ni,kilama saita fini tsufa”.haka dai sukayi ta barkonci kafin yayi masu sallama akan zai Kara Kiran su zuwa da dare .Bayan ya katse Kiran shige gidan Kaka jin wani farinciki ya lullube shi,Yana son tsohuwar Dan akwaita da barkonci.Ansar wayar Ummeey tayi tana murmushi.kakama murmushin tayi tana ceamat “Kinga ikon Allah ko,to mu Kara dagewa da Addu’a insha Allah komai zai daidaita”da Amen Ummeey ta amsa ana sukaci gaba da tattaunawa akan yadda al’amarin ya kasance a shekarun baya harzuwa yanzu da komai ya fara daidaituwa. 

       Yana shiga falon kakar tasu ya tadda Iyayen nasu maza a zazzaune sun saka tsohuwar gaba suna sauraren ta.Akalla sunkai su takwas.sallamar shi ta katsewa Kaka maganar da take yi.Dukansu kallon shi sukayi.A hankali ya karaso falon kusa da kafafun Uncle Ahmed ya zauna.cikin ladabi ya Kara gaishe su,kafin ya gaishe da Kaka.amsawa sukayi banda mutum daya da yake ta faman huci da bata rai,Uncle Umar kenan.shidai Muhseen ko kallon shi bayyi ba ya mayar da hankay shi gun Kaka da take cewa “ka Kira Malam Muttaka  ko”?gyada kanshi yayi ya amsa da “eh yace gashi nan zuwa nan da Yan mintuna”.da haka wasu daga cikinsu suka fice daga part din ya rage daga Uncle Yusuf sai Uncle Ahmed da muhseen sai Kuma Kaka da take Kara basu shawara akan yadda ya kamata su gudanar da taron a sati mai zuwa.Sakeena ce da Ameerah suka yi sallama.gaishe fa su suka yi kafin Suka shiga uwar dakin na Kaka.

Karfe biyu da Yan mintuna  na rana a daidai wannan lokacin kuwa su Zahara’u ne suke kokarin fitowa daga cikin Hospital na sojoji dan komawa gida.sunyi weekend duty ne.zahara’u kallon Fadila tayi tana tabe baki cikin jin haushi ta ce “ke dakata ki ji idan har ba zaki bani shawarar yadda zan cimma burina na samun Dr muhseen ba to,kada ki bani shawarar rabuwa da shi,Dan bazan iya rayuwa babu shi ba.kinsan adadin tsawon lokacin dana dauka Ina dakon soyayyar shi,wallahi duk wadda tayi min shamaki da shi to zan iya kawar da ita kowacece”cikin mamaki Fadila ta juyo tana kallon kawarta ta jin irin furicin da tayi,batayi mamaki ba,Amma ita tasan abu ne mai matukar wahala ta samu Dr muhseen.”hmmmm to nidai abinda zance ki dage da Addu’a,idan har rabonki ne to zaki same shi”cewar Fadila tana tsayar masu da mai napep saboda har sun karaso bakin titi.da haka Suka nufi cikin garin daura.Fadila aka fara saukewa kofar gidan su dake cikin unguwar sha’iskawa kafin ya wuce da Zahara’u cikin unguwar Dole.

Shiko Muhseen a tare suka jero da Uncle  Yusuf bayan sun baro part din kaka.har zuwa wannan lokacin Seeyerma bata farka ba daga dogon baccin daya dauketa.wayar Muhseen ta dau Kara ganin sunan Malam Muttaka yasa ya fito waje Dan shigowa da shi.a wurin parking ya tadda shi Suka karasa bayan ya rufe motar shi.

         A kujera suka yimai masauki bayan sun gaisa ,Dan zuwa wannan lokacin Aunty Hajara ta sakamata hijaf a jikinta.Addu’o’i ya fara karantowa hakan yasa seeyerma ta farka da wani mugun Kara tana nuna Dr muhseen cewa take yi “wallahi shi ne,kada ku Bari ya tafi da ni, wayyooooooo Allah na bani”sai kawai gani sukayi luuuuuuuuuuuuuu……Ta Kara zubewa a sume.cikin jimami malam Muttaka ya mayar da kallon shi ga Uncle Yusuf “gaskiya akwai matsala koma meye yake tsorata ta to tabbas a jikin Muhseen take ganin shi,Amma mafi kyau ya nisanta da ita kafin muyi kokarin ganin mun gano matsalar” da sauri Muhseen ya dubi Malam jin abinda ya furta.ba tare daya ce komai ba ya fice daga part din,ganin lokacin salla yayi yasa ya taka a kafa dan zuwa masallaci.

Malam Muttaka Bayan fitar Muhseen ya dauko wani magani na ruwa a 
n wata Yar karamar kwalba ya Kara matsawa inda take konce jikin Aunty Hajara.A tafin hannun shi ya zuba ruwan maganin kafin ya watsa shi saman fuskarta.kawai sai gani sukayi tayi wata mikewa tana faman kakkafewa.cikin nutsuwa ta fara karatun alkur’ani cikin suratul jinn daga Aya ta farko zuwa ta biyar,Yana idarwa ya kamo suratul kafirun itama har zuwa karshe.haka yayi ta karatun cikin nutsuwa da bama kowane harafi hakkin shi.Amma cikin ikon Allah sai abin ya lafa.nan take bacci ya Kara daukarta.ganin haka yasaka malam Muttaka dakatawa da karatun kafin ya koma wurin zamanshi bayan ya mayar da maganin.
“To Alhamdlillah sai muyi addu’ar Allah ya kiyaye,Amma ga dukkan alamu akwai matsalar sihiri a cikin lamarin nan,tunda sunki yin magana to tabbas na ture ne”cewar Malam Muttaka nisawa yayi kafin ya ci gaba da cewa “yanzu zan bata magunguna a tabbatar tana amfani da su kafin zuwa wani dan lokaci muga abinda Allah zaiyi”
“To Allah ya yayemana wahala”cewar Aunty Hajara tana Kara gyarama Seeyerma dankwalin ta.
A tare suka fito da Uncle Yusuf.suma masallacin Suka nufa.
A bayan sun fito ne suka Kara gaisawa da muhseen sai su Faruk da Jabeer wadanda sai a lokacin suke jin abinda yake faruwa.
Sosai Faruk ya rude dan harga Allah Yana jin yarinyar har zuciyar shi da bargon jikinshi.sunyi sallama da Malam bayan ya jaddada masu zuwa anjima da yamma a tura wani ya amso magani a cemest din shi da yake a cikin unguwar kwado.akan haka Suka rabu bayan sunyimai godiya.
 Gaba dayan su  cikin estate din suka nufo a jere gwanim sha’awa, Uncle Yusuf shi ne a tsakiyar su Yana Kara kontar masu da hankali,ganin yadda duk Suka damu.duk maganganun da suke yi shi dai Muhseen bai ce kala ba sai sauraren su day kunne.dan shi Yanzu abu daya ne yake damun shi ya Kuma daure mai Kai,shi ne yadda Seeyerma ta rinka nuna shi a daidai lokacin da ta farka daga dogon suman da tayi.da wannan tunanin Suka Karaso kofar gidan kaka.bayan shigar su anan Suka tarad da Uncle Ahmed .cikin karfin hali Uncle Yusuf yayima Kaka bayanin abinda ya faru.sosai take kallon Muhseen da shima ita yake kallo.har zuwa wannan lokacin bata furta komai ba,sai dogon nazari da take yi akan al’amarin.
Muhseen ne ya mike Yana cewa “Uncle ni zan wuce Dan Ina tunanin yanzu zan tafi Daura”
Basu hanashi tafiya ba,saboda sunsan Yana cikin rudani na abinda ya faru Amma Dole ne su bashi time ya samu nisanta da dasu.Addu’a sukayimai da fatan Allah ya kaishi lafiya.da Amin ya amsa Yana ficewa daga part din.
Suma su Faruk da Jabeer fita sukayi kafin Kaka ta mayar da hankalinta ga yarannata guda biyu ta fara magana kamar haka “Bana son abinda zai kawo rabuwar kanku Koda ace bayan nabar duniyar nan,A kullun addu’a ta Allah ya Kara hada kawunan ku dana iyalan ku,Amma a wannan karon na fuskanci akwai matsala mai tarin yawa da rudani,baya da shekarun baya rudani ya riskemu Wanda har izuwa yau da nake maganar nan bai karasa warwarewa ba,to inasan sanar da ku duk Wanda yasan Yana kullace da Dan uwan shi a cikin ranshi to ya gaggauta gogewa”saida ta nisa ta saka bantalen goro a bakinta tana taunawa kafin taci gaba da cewa “magana ta biyu inaso ranar da zaku yi taron dangi na karshen wannan satin to a tabbatar an fitar da wadanda za’a auras nan da wata ukku masu zuwa ciki kuwa harda takwarata”kusan duk a lokaci daya Suka yi saurin dago kansu suna duban mahaifiyar tasu,sosai kalamanta suka taba zuciyar Uncle Yusuf Wanda kusan dukkannin kulawar Yarinyar tana karkashin su biyu shida Muhseen sai Kuma Faruk da yake taimaka masu.
Kasa Uncle Yusuf ya Kara yi da muryar shi,bayan jin mahaifiyar tasu tayi shiru ya dora da ” kiyi hakuri Hajiya bawai zanyi musu da Umarnin ki ba,Amma ni inaga kamar abar yarinyar nan ta fara karatu sai musan meya kamata muyi akan lamarin”shiru yayi Dan jin me mahaifiyar tasu zata ce .
Sun dau tsawon lokaci a haka ba Wanda ya Kara cewa komai.
Jikin tuntun dake gefen kafarta ta jingina kafin ta dubi yaran nata ta ce “nasan a halin yanzu duk irin fitinar da za’a hada to marainiyar nan za’a yiwa,bayan anyi sanadin rasuwar iyayenta to itama nasan bazasu kyaleta ba,Amma kuje kuyi yadda na ce nan da kwana biyu,idan kin yanke shawara kuda sauran Yan uwanku to kuzo ku sanar da ni domin na ji yadda kuka yanke hukuncin”amsawa sukayi da to kafin suka fita daga part din.
Muhseen kuwa Yana shiga part din shi ya fara harhada wasu abubuwan bukata Wanda zai tafi da su.sai wayoyin shi daya dauka ya rufe part din.wurin parking ya nufa.yana kokarin bude murfin motar daga bayan shi ya ji ana magana.juyawa yayi dan ganin mai yimashi maganar.ganin Aliyu ne yasa ya mayar da kofar ya rufe.mikamasa hannu yayi suka yi musabaha.cikin sakin fuska Aliyu ya ce “Yaya Amma badai har tafiya zakayi ba”?
Shima murmushin ya mayar mai da shi kafin ya amsa da “wallahi kuwa kanina komawa zanyi gobe Ina da ayyuka a office,Amma Insha Allah next week zan zo ranar Juma’a saboda family meeting, before na dawo ku tabbatar kun ansomana dinkunan,tun jiya nayi magana da tailor ya ce zuwa ranar talata zai karasa gamawa,Suma na yaran nan ku ansomasu”Yana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunshi,Dan so yake yi yayi sallar la’asar a Daura.
Aliyu Amsawa yayi da “to insha Allah zamuyi yadda ka ce,Allah ya kiyaye hanya”
Amsawa yayi da Amin bayan ya zauna a cikin motar.jakar kayan shi ya jefa bayan motar kafin yayi addu’a Yana tayar da motar.harya fice daga gate din farko Aliyu na faman daga mai hannu.saida yaga ya daina ganin shi kafin ya nufi part din su Yana ta doka murmushi.har zuciyar shi yake Kara kaunar Dr muhseen Dan Yana kula da su.ta wani fannin Kuma yakan ji tausayin shi.dan tun baya da watanni da wata kaddara ta same su duk ya koma so silent.ba kamar da ba daya kasance mutum mai fara’a da son mutane,Amma yanzu ko doguwar magana baya San yi.
A Sudan kuwa da dare Hajiya Aishatu ce zaune a falon part dinta sai Ummeey dake yimata tausa,Lailah kuwa tuni tayi bacci.
Cikin kallon tausayi ta dubi Diyarta ta ganin yadda tayi shiru tasan tunanin da take yi Dan haka tayi saurin cewa “Wallahi ko idan kika yi sake to zaki rasa damar ki,Ina mai Kara jaddda maki aduk lokacin da wani al’amari ya girmama a gareka to kada ka manta da ambaton Allah,dukda nasan ke ba baya ce ba a wannan fannin to Amma anaso kada mutum ya daina harsai bukatar shi ta biya,Koda ta biya to kada ka dakata sai kaci gaba da neman tsari”
Ita dai Ummeey Kara yin kasa tayi da kanta ba tare data ce komai ba.
Hajiya Aishatu ci gaba tayi da cewa “A kullun ita nasara tana tare da mai hakuri,Amma hakurin shi ne mai matukar wahala,mafi yawancin lokutta Dan Adam yakan ji bazai iya jurewa ba,Amma idan harya jure to watarana zai samu farinciki mai dorewa,kisani yake diyata babu nasarar da take samuwa ba tare da anyi hakuri ba,kafin zuwan wannan shekarun nasha gwagwarmayar rayuwa da makiya na fili dana boye,Amma cikin ikon Allah Dana yi hakuri sai gashi na dafa tudun nasara Wanda har zuwa wannan lokacin wannan hakurin shi nake ciki”daga haka tayi shiru tana ganin yadda diyarta ta take faman shatatar da hawaye.
Cikin sanyi Ummeey ta dubi mahaifiyar tasu ta ce “Wallahi ba komai nake tunawa ba sai marainiyar Allah wacce nasan bazasu kyaleta ba,a kullun burin su suga sun tarwatsa wannan ahalin,Amma abin mamaki an kasa gano ko su suwaye,Hajiya Mariya ita kadaice a lokacin baya muke zargi Amma zuwa yanzu nafi tunanin akwai makusantan wannan ahali,Wanda dasu ake hada Kai wurin ganin an cutar da mu”kukan taci gaba da yi.wanda Hajiya Aishatu bata yi yunkurin hanata ba sai janye kafafunta da tayi tana gyara konciyar ta.
Ummeey saida ta gaji da kukan kafin tayi shiru tana sharen hawayenta.
Cikin sauri ta nufi dakin su.wannan hotu nan ta Kara daukowa tana ci gaba da kukanta.
Jin kamar motsin Lalaih zata farka yasata saurin yin shiru tana sauke ajiyar zuciya.
Tunda ya karaso bakin gate din bareak ta sojojin ya ji damuwar shi ta Kara daduwa,tunowa da halin daya bar yarinyar .sama sama ya gaisa da wadanda suke duty a gate kafin ya nufi ciki.ganin lokacin sallar la’asar yayi yasa yayi parking jikin masallaci yayi arwallah,jam’i yabi kafin ya nufi cikin gidajen nasu.tafiyar minti biyar ta kaishi gaban wani babban block mai hawa ukku sosai wurin ya kayatu ga shuke-shuken filawowi masu kyau da tsari sunyima gidajen kawanya.inda ya saba ajiye motar shi yayi Parking dinta kafin ya dauki jakar kayan shi da wayoyin shi ya haura saman benen.saida yakai hawa na biyu daki na ukku daga hannun dama kafin naga ya saka key ya bude.harya saka kafar shi guda cikin tsoro da al’ajabi yayi saurin dawowa da baya Yana furta Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un jin wani………………

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *