DR MUHSEEN CHAPTER 6 BY RUKAYYA IDRIS BALAH (AUTAH)
Www.bankinhausanovels.com.ng
📝……………..Dr muhseen harya Kai bakin kofar fita daga cikin Holl din,yayi saurin dawowa da baya jin kamar an ambaci sunan shi.baikai ga karasa tunanin shi ba yaji Uncle Yusuf ya Kara maimaita kalmar.
“Muhseen da Ameerah,wandan mutanen su shida sune za’a gabatar da daurin auren su nan da watanni ukku masu zuwa insha Allah,sai a fara shirye-shirye daga wadannan bangarori, sai shues na gaba akan maganar karatun Seeyerma da khadija ne Wanda Hajiya Kaka ta damka nauyin karatun su a hannun Muhseen………….
Da sauri Dr muhseen ya karasa ficewa daga wurin ba tare daya bari yaji karshen bayanin ba.
Wani makirin murmushi Ameerah ta saki jin burin su Yana gaf da cika a cikin wannan ahalin.cikin sauri ta rubuta sako akan wayarta ta turama wata nomber tana Kara jin wani farinciki ya mamaye zuciyar ta.
Jabeer ne ya dubi ya Faruk cikin kidima da tunanin wannan mirdadden al’amari.ganin tun dazu kanshi yake duke a kasa yasa ya dubi Aliyu,shima Ya Faruk yake kallo.gani sukayi ya mike tsaye idonshi saboda tsananin bacin rai yayi kaman garwashi gaba daya ya fice daga Holl din suna kallon shi,ba Wanda yayi yunkurin hanashi.
Da sauri itama Seeyerma tabi bayan shi hartana hadawa da dan gudu saboda yayimata nisa.
“Jar uban can”cewar Hindatu da ta matsa jikin kujerar da Ameerah take zaune.
“Ameerah Kinga abinda idona ya ganoman kuwa”
Inji Hindatu.
Saida Ameerah ta Kara fuskantar Hindatu cikin kasaita da yanga tace “kisani wannan wani babban yaki ne zaki tunkara idan har kika jajirce to zaki iya zama jaruma a fagen yaki,da zaran kuwa kin sanya kasawa da rashin juriya to za’a iyayin nasara a kanki akowane lokaci,Dan haka zabi ya rage naki”
Jinjina Kai Hindatu tayi,tana ji a ranta ai ta samu kwarin guywar da zata mallaki zuciyar ya Faruk cikin sauki.
A bangaren iyaye maza ba Wanda yayi magana,Amma Alhaji Muhammad zuciyar shi ta cika da al’ajabin sauyin da aka samu,domin ko a jiya da dare ba haka rubutun takaddar yake ba,sunan su Muhseen da Seeyerma shi ne farko,kafin Jabeer da Rukayya,sai Kuma Faruk da Hindatu,tabbas akwai munaficcin da ake kokarin hadawa tunda har aka canza wannan tsarin”nisawa yayi kafin a hankali ya furta ya Allah ka ceci rayuwar Muhseen da Seeyerma kodan maraicin yarinyar nan.
Haka a bangaren iyaye Mata Banda tunani ba abinda Aunty Hajara take yi,tunawa tayi da maganar da sukayi da Faruk a wasu lokutta can baya,inda yake cemata “Wallahi Aunty duk makircin da ake hadawa a cikin wannan estate din akwai wadanda nake zargi,burinsu su mamaye dukiyarmu su saka rikici a tsakanin mu da yan’uwanmu,Amma nayi alkawarin kosu waye insha Allah zamu gano su ta a ranar da za’ayi hadin aure,saka mutane biyu cikin ahalinmu shizai tabbatar da zargin da nake yimasu”.
Dagowa tayi tana hango mijinta Wanda shi ne yake bayani akan fannin kiwo da kasuwanci na familyn.
Da haka taro ya tashi bayan cin abinci da hotuna.
Hajiya Mariya ce zaune a room dinta.cikin jin dadi ta fashe da wata mahaukaciyar dariya bayan data gama karanta sakon daya shigo wayarta.cikin tsantsar farinciki ta ce “Kowa taci tuwo da ni to Miya ya Sha,duk sai kun gane Kuranku ni zan nunamaki ni cikakkiyar bakatsiniya ce ,da ace na tashi a banza to gwamma asirin kowa ya tonu”haka tayi ta surutun ta Wanda na kasa gane inda suka dosa.
“Ummeey wallahi bansan yazanyi ba,idan har nabar Seeyerma a cikin wadannan azzaluman mutanen to itama zasu iya kasheta,koni Allah ne yake tsare ni da bansan mezasu yiman ba”lumshe idon shi yayi bayan ya jingina jikin shi da wata bishiya.
A hankali ya Kara furta “zanbi duk shawararki, addu’a ta Allah yasa Kaka ta amince da maganata,to indai mukayi nisa da su nasan insha Allah zamuyi nasara”da haka sukaci gaba da tattaunawa saida yaga dukansu sun fice daga Holl din kafin ya nufi jikin motar shi.
Harzai shiga cikin motar ya jiyo da sauri jin alamun tahowar mutane,Faruk ya gani da Seeyerma suna fitowa daga bayan Holl din.bai tankasu ba ganin yadda Seeyerma take kuka,jin bazai iya cigaba da kallonsu ba yayi saurin shigewa ya fice daga wurin zuciyar shi fal da tunanin maganganun Ummeeyn shi,hakan yana nufin Ummeey ta gano wadanda suke munafintar su kenan?….
*ASALIN GIDAN FULANI*
Hajiya Kaka da mai gidanta Alhaji Abubakar haifafun fulanin ajiwa ne ta cikin jihar katsina,sun fito daga wani kauye da ake Kira da Kanto,fulanine sosai gasu kyawawa kasancewar su makiyaya yasa suke da tarin dukiya kama daga shanu,rakumma,awaki,kaji,harma da dawakai a wannan lokacin Alhaji Abubakar yakan shigo garin katsina dan sarin kayan masarufi ya zuba a shagon shi da haka kasuwar shi ta kankama harya dawo cikin birnin katsina da zama,kasancewar mahaifin shi ya rasu Yana zaune da mahaifiyar shi ne da yan’uwan Baban shi.Bayan dawowar shi da shekara biyu ya koma garinsu aka auramasa Hajiya kaka, Suka dawo gari da mahaifiyar shi anan cikin kwado ya siyamasu gida mai dauke da dakuna guda ukku da bayi sai dan karamin kitchen,a shafe yake sumul da suminti gwanin sha’awa.
Bayan wasu watanni Alhaji Abubakar ya koma kauyen Kanto inda ya tattara dukiyar shi wacce ya barma abokinshi Amana,haka ya siyar da komai ya tattaro ya dawo katsina.ya kama kasuwanci da dama yakan siya fili ya Gina shi saiya sayar ga masu so ya samu riba,haka cikin kasuwa ya zuba Kaya masu yawa a cikin shagonshi sai yaran shi da suke tallafa mai.
Ana cikin haka Alhaji Abubakar ya ci gaba da karatun shi,kasancewar yayi secondary School a ajiwa,saiya jona Diploma anan F C E part time.cikin ikon Allah kafin wani lokaci yakai matsayin aji biyu.
A wannan shekarar Hajiya Kaka ta haifi danta namiji yaci sunan Muhammad (shi ne Dadyn Muhseen kenan).suna zaune lafiya da mahaifiyar Alhaji Abubakar cikin biyayya da mutinta juna.
Bayan ta yaye Muhammad ta haifi danta na biyu inda yaci sunan Jafar,sai Ahemd,Bishir,saifudden,A Mata kuwa tana da Aliya sai Fatima,sai Uncle Yusuf Wanda shi ne karamin su.
Haka sukaci gaba da rayuwa arzikin Alhaji Abubakar Yana Kara habaka,tuni ya ginamasu katon gida gaba kadan da toshon gidan su.haka suka saka yaransu a islamiyya da boko,lokaci zuwa lokaci suna ziyartar mutanen kauyen Kanto sukan yimasu tsaraba da shatara na arziki.
Lokacin da Muhammad yakai aji shida a secondary a wannan shekarar Allah yayiwa mahaifiyar Alhaji Abubakar rasuwa,sunci kukan rabuwa da Yar tsohuwar saboda sunyi maraici.sosai Yan Kanto suka zo ta’aziyya yan’uwa da abokan arziki har tsawon sati daya kafin kowa ya koma gidan shi.inda Hajiya Kaka aka kawomata kanwarta mai suna Balaraba, wacce suke uba daya da ita.domin Kaka ita kadai ce a wurin mahaifiyar ta.Ankawota ne danta tayata kula da su Muhammad .cikin ikon Allah wata rana Alhaji Abubakar ya zo da abokin shi mai suna Nazifi,daga kasuwa suke ya biyoshi jin Kaka ta aikamai cewar Dansu Bishir baya da lafiya,to anan Nazifi yaga Balaraba ya nuna ra’ayin shi akanta.dukda Yana da Mata Amma haka ta amince.Ba tare da daukar wani lokaciba akayi bikin Nazifi da Balaraba.
Bayan wasu shekaru Balaraba ta haifi yaranta guda biyu Mariya ita ce ta farko sai mai bimata Aminu.
Inda Hajiya Kaka kuwa yaranta biyu suka rasu da saifudden da Fatima.Haka taci gaba da rainon sauran yaranta.zuwa wannan lokacin kuwa Alhaji Abubakar ya fara fita kasashen ketare harkar kasuwancin shi.kuma tundaga Hajiya Kaka bai Kara yin Aure ba.watarana Balaraba takanzo gidan yayarta Hajiya Kaka ita da Diyanta Mariya da Aminu,saisu yini a gidan idan zasu tafi saita hadamasu Kaya sosai saboda Alhaji Abubakar yafi Nazifi arziki.ashe wannan abu Yana damun Balarab a kullun idan ta bude idonta taga mijinta shine baya takanji ciwo a zuciyarta,harma takanji Daman ita ce ta Auri Alhaji Abubakar .
*GIDAN FULANI* sun gado kyau ne a gun Hajiya Kaka da Alhaji Abubakar,tamkar Larabawa haka Allah yayimasu tsabar kyau da cikar haiba,sai yaransu suke kama da su sosai.
Tunda Muhammad ya taso a rayuwar shi ya tsani kanwar mahaifiyar tashi wato Inna Balaraba,ganin yadda take da kwadayi da son abin duniya,wani lokacin idan yaga tazo gidan to shi idan ta fita baya dawowa harsai ya tabbatar data tafi kafin ya dawo.
Bayan wasu shekaru Muhammad ya dawo daga London inda ya kammala digreen shi na farko a fanni Business,Dan Alhaji Abubakar da kanshi ya zabamai Course din duba da yadda ya fara manyanta.sai Jafar da yake a matakin karshe a England inda shima Business yake karanta.sai su Bishir,Ahmed,Yusuf,da Aliya da kowanne Yana karatu cikin jin dadi da konciyar hankali,Dan Alhaji Abubakar akwai kokarin nema gashi Yana kyautatawa yan’uwansu na kauyen Kanto.
Wata rana kwatsam Balaraba tazo gidan yayarta tana kuka,dandanan Hajiya Kaka ta rude tayi tunanin ko Baffansu ne ya rasu.jin wani batu na daban da take fadamata yasa Hajiya Kaka yin shiru tana kallon kanwarta ta.
“To Balaraba bawai naki batunki ba,Amma ita Mariya tana son shi Muhammad din,Dan idan har bata sanshi to baza’ayi Mata Dole ba”cewar Hajiya kaka. Tana kallon kanwarta ta.
“Ahhhh Yaya kada kiji komai na tambayeta ta tabbatar min data amince da shi”inji Balaraba tana marairaicewa.
A hankali Hajiya Kaka ta nisa kafin tace “to kada ki damu idan Abbansu ya dawo daga London cikin satin nan insha Allah zamu tatatuana maganar da shi,nasan bazaiki Amincewa ba”da haka suka rabu ta saka Driver ya mayar da ita gida.
Bayan wani lokaci akayi Auren Mariya da Muhammad (Hajiya Mariya kenan da Uncle Muhammad Dadyn Muhseen)Ina fatan kun gano inda labarin ya fara 🤣🥰 Aunty Saudat kar kuce fa na rudaku 😃.
………..Anyi auren su da wasu shekaru Amma har zuwa wannan lokacin Allah bai basu haihuwa ba.sosai Hajiya Mariya da mahaifiyarta Balaraba suka shiga damuwa dan sunsan idan har Mariya bata haihuba a wannan gidan to tabbas Alhaji Muhammad saiya Kara aure.
Hakance kuwa ta kasance, wata rana kwatsam Business yakai Alhaji Muhammad Sudan inda yake wakiltar mahaifin su Alhaji Abubakar akan wata mahimmiyar tattaunawa da za’ayi da wani companyn takalma na kasar Sudan.sosai yaga tarba ta mutunci da karramawa.
A wannan lokacin company mallakar sarki Abdulkareem ne.dan haka a gidan sarki aka sauki Alhaji Muhammad.
Part guda aka bashi harna tsawon sati daya,inda Ummeey ita ce ke kaimasa abinci da abinsha.sosai yaji dadi ganin yarinyar Bata da matsala,ga nutsuwa da tarbiya.
A ranar da zai tafi ya nunawa sarki Abdulkareem Yana ra’ayin a bashi auren Ummeey dukda ba dan kasarsu ne ba,haka sarki Abdulkareem ya sanar da Mahaifiyar su Wato Hajiya Aishatu.tunda Ummeey taji labarin wani sabon Farinciki ya kamata,Dan harga Allah tunda taga wannan bakon zuciyarta ta kamu da kaunar shi ,Ashe Allah yasa rabonta ne,Ance Yan Nigeria bakaken fatane Amma shi taga kamar ba dan canba,kasancewar da yaren turanci yake yimasu magana hakan yasa Basu taba ji yayi Hausa ba.
Kafin Alhaji Muhammad ya tafi saida suka tattauna komai,akan dazaran ya koma gida zasu zo da yan’uwan shi a daura aure.tun Yana can ya sanar da Hajiya Kaka,sosai taji dadi Dan tanaso ta fara ganin yan jikokinta.
Bayan Alhaji Muhammad ya dawo Hajiya Mariya ta samu labarin Karin Auren da zaiyi aiko ranar hauka ne kawai batayi ba a gidan,sosai tayi ta masifa tana cewa ai Hajiya ta saka shi Kara auren,haka tayima Hajiya Kaka rashin kunya da Alhaji Muhammad ya ce zai saketa ta hana shi saboda bata so zuminci ya baci.
Aiko su Hajiya Mariya da mahaifiyarta Balaraba ba zama (Wai ansaci zanan mahaikaciya 🤣)haka sukayi ta yawo cikin garin katsina da kauyika suna rabawa malamai da bokaye kudi dan ganin an lalata maganar auren,Amma abu ya gagara,wasu idan sunje sukan sanar da su gaskiyar cewa aure babu fashi sai anyishi.
A karshe dai dole suka hakura aka dauro auren Ummeey da Alhaji Muhammad.haka akayi ta fafatawa yau da dadi gobe ba dadin.har Allah yaba Ummeey cikin Muhseen.tofa anan Ummeey tasha bakar wahala.dan hatta abinci sai a part din Hajiya Kaka takoma tana ci,saboda Hajiya Mariya sunsha Alwashin ganin sai sun zubar da wannan ciki.
Cikin ikon Allah ranar da cikinta ya cika wata tara da kwana tara,A ranar da dare nakuda ta kamata,Allah yasa Alhaji Muhammad a dakinta yake,cikin gaggawa ya fitar da mota suka nufi wani pravet Hospital aka ansheta.cikin awa daya ta haifo danta kyakykyawa mai kama da larabawa,sai da asuba aka sallamesu suka dawo gida.
Da safe ya buga waya kasar Sudan ya sanar da su,sunyi farinciki da jin wannan albishir.
Wayyyyyyo Hajiya Mariya Ina wuta ta saka Ummeey da jaririnta,saboda takaici har kuka saida tayi.
Haka dai ta daure har ranar suna ta zagayo yaro aka radamai Muhammad Amma suna Kiran shi da Muhseen kasancewar sunan Baban su Alhaji Muhammad kenan.
Sosai Ummeey take samun kulawa daga fannin Hajiya Kaka,gasu Jafar,Yusuf da Aliya suna kaunar Muhseen Sai dai kwata-kwata basu shiri da Ahmed saboda yadda yake yimata rashin kunya,ko danta baya daukar shi.
A lokacin Aliya ta karasa secondary School dinta inda ta samu miji Dan abokin kasuwancin Alhaji Abubakar ne,haka aka daura aurensu ta tare a gidanta dake unguwar filin samji.
Haka suma Jafar da Bishir kaka ta turasu kauyen kanta suka samo matan aure,Dan tace bazata Bari su karayin aure a cikin katsina ba,gwamma su auro danginta suma suzo suci arziki.Haka Jafar ya Auro Zinatu wacce suke Kira da Mama (Mama kenan wacce Yan Mata da samarin gidan suke a part dinta ita ce matar Uncle Jafar😃).
Shiko Bishir ya auro Bintu wacce suke Kira da Momy (Momy matar Uncle Ahmed kenan).
A lokacin Aliya sau biyu tana yin bari na ciki,Daganan Allah bai bata haihuwaba har tsawon wani lokaci.inda zuwa sannan Matan su Uncle Jafar da Uncle Ahmed sun haihu.(matar Uncle Jafar Mama kenan ta haifi danta namiji mai suna Faruk,kun gano mahaifiyar Faruk ko?😘)
Sai Bintu (momy kenan matar Uncle Ahmed) ta haifi yaronta yaci sunan Jabeer.tserayyarsu da Faruk bata da yawa hakan yasa suke kaman sa’anin juna inda Muhseen ya basu kusan shekar Biyu a haife,Dan shi Muhseen a lokacin Yana gudunshi koina.
Sai matar Uncle Bishir da suke mazauna Legos suna da yara guda biyu Bishir shi ne babba wato yaci sunan mahifin shi,sai karamar Fatima wacce ta samu sunan Fatima wacce ta mutu Diyar Hajiya Kaka baya da wasu shekaru (idan kun tuna diyan Hajiya Kaka biyu suka rasu da Saifudden da Fatima)👌.
Haka rayuwar taci gaba da juyawa inda Aliya ta haifi Diyanta Mace mai suna Hindatu da Saifudden,a Kuma wannan shekarar ne Allah yayima mahaifin su Alhaji Muhammad rasuwa.wato Alhaji Abubakar kenan Mijin ga Hajiya Kaka.
Sosai wannan Familyn sukaji wannan rasuwa Dan Alhaji Abubakar mutumne na mutane,sukansu Yan kauyen kanta sunji ba dadi,Dan Alhaji Abubakar ya gidana masu islamiyoyi da masallatai ya wadatasu da ruwan fanfo,Dan haka sunyi jimamin rasuwar wannan tsohon tare da yimashi addu’ar samun rahamar Ubangiji.(to Nima dai nace Allah ya jikan dan tsoho Alhaji Abubakar da sauran yan’uwa Musulmai).
Zuwa wannan shekarun Muhseen ya fara zama saurayi,gidan kuwa ya Kara samun karuwar iyali.inda Mama matar Uncle Jafar ta Kara haihuwar yara biyu Bayan ta yaye Faruk ta haifi Aliyu da Rukayya, sai karamar su Ameenatu.
Matar Uncle Ahmed wato Momy kenan, bayan ta yaye Jabeer ta Kara haihuwar Nura da isma’il sai karamar su Safna.
Sai Uncle Yusuf shima Hajiya Kaka ta turashi kauyen Kanto inda ya auro Aunty Hajara,a cikin dangin mahaifiyar Hajiya Kaka kenan.
Bayan auren su Suma Allah ya Basu yara guda ukku,wato sadik, Halimatu,sai Auta Khadija.
Haka wannan ahali sukaci gaba da rayuwa wani lokaci akan haihu Amma sai yaron ya Mutu musamman Ummeey,Dan bayan danta Muhseen ya fara zama saurayi kusan sau ukku ta haihu Amma yaran ko suna ba’ayi suke mutuwa wasu ko kwana biyu basa yi.hakan yasa suka Dan tsagaita haihuwar.
A lokacin Hajiya Mariya ta dauko wata Diyar kanwarta a matsayin ruko mai Suna Ameeerah (Ina fatan kun fahimci Ameerah ba haifafiyar gidan ce ba,daukota akayi ruko)jikar Balaraba ce mahaifiyar Hajiya Mariya .ba Wanda yayi yunkurin hanata saboda ana ganin hakan zai iya debemata kewar rashin yara da bata da su.
Da haka itama Ameerah ta zama Yar gidan,Dan hatta dinki idan za’ayimasu to gaba dayansu ake yiwa,to duk cikinsu Ameerah ita ce kamaninnta Suka dan banbanta da iyalan gidan dukda itama jinin Hajiya Kaka ce…………….¹³