DR TAHEER CHAPTER 10 BY UMMU ASHRAF

DR TAHEER CHAPTER 10 BY UMMU ASHRAF

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

Idan baku mantaba I once told you Nafeesa da Mijinta Awwal were cousins..so kar wasu su fara tunanin me zai kawo Ramla Dutse..itama family dinta ne..da mahaifinsu da mahaifin Awwal uwa daya uba daya suke.Wata yarinya ce tazo wucewa ta gabanshi yayi saurin tsaidata Yana nuna mata Layla da hannunshi yace”kin San waccen?..”yarinyar ta kalli inda yake nuna matan snn tace”eh na santa mana..Layla ce”…da sauri Taheer yace”yawwa dn Allah kawai ce Mata zakiyi tazo Ina kiranta”…tace”inji wa zance?..”yace”kawai ki nuno mata ni zata gane”.. yarinyan tace toh snn ta nufi wurin da su Laylan suke…Saida taje har kusa da Laylan snn ta nuno Mata shi da hannunta kmr dai yanda yace tayi tace”kinga wancan mutumin ne yace inyi mai mgn dake”…Layla ta daga idanu tana kallon Wanda yarinyan ke nuna Mata…sai ta zare idanu da sauri hadda su dafa kirji tace”daddy”…yarinyan tace mata”eh shi yace in kiraki..kin sanshi ne”…Layla da batama jin abinda yarinyan ke fada kawai sai ta nufi wurin da yake..gabanta sai dukan tara tara yake..tasan da kyar idan basu rikici dashi ba yanzu..amma ya akai ya taho yau shida yace sai gobe zaizo…

Taheer na ganin ta kusa karasowa inda yake sai ya juya tareda fita daga cikin hall din…Layla na binshi da kallo itama ta fita da ciki…tana fitowa taji an kama hanunta da kyau snn an shiga janta suna tafiya daga wurin…tayi tsit kawai tana ganin yanda yake janta kmr zasu tashi sama…bakin titi taga sun fito…har ta fara hawaye tace”daddy listen to me dn Allah..ka tsaya kaji bayanin da zanyi maka”…bai tanka mata ba..ya tsare musu taxi..ya dan risina saitin mai taxi din yace”nearby hotel nakeso ka kaimu..baki ne mu..so bamu San kan garin ba”…mai taxi din yace”ba damuwa ku shiga muje”…ya bude motar ya turata ciki snn ya zagaya shima ya shiga..Layla dake kuka wiwi tace”daddy ka saurareni dn Allah..kar kayi haka daddy su ummi zasu yita nemana..dn Allah ka maidani”…ke da kike karatu idan kin amsa to shima Taheer ya amsa…Yana dafe da kanshi kawai yanajin yanda har yanxu zuciyarshi batayi sanyi ba…duk ya rufe ido sai ya hangota tana rawa tana dariya a cikin maza duk suna kallonta..shi gani yake yau babu kalar namijin da bai kare mata kallo ba…sunyi tafiya kusan na 11 mins kafin su isa hotel din…ya kama hanunta suka fita daga motan..ya biya mai taxi kudinshi snn suka shiga ciki…har yanxu Layla bata bar kuka tana rokon yayi hakur ya maidata ba amma kmr da dutse take mgn don ko kallon inda take baiyi ba…suna shiga reception yayi musu booking daki..aka fada mashi room number snn ya amsa key suka tafi zuwa dakin…ganin yanda take tirjewa tanaso ta tara mai jama’a kawai sai ya sunkuya ya dauketa cak snn yaci gaba da tafiya har zuwa kofar dakin…ya matseta da hannu daya snn ya bude kofan dakin da daya hannun…yana shiga ciki ya sake maida kofan ya kulle snn karasa cikin dakin tareda ajiyeta kan gado…fuskan nn nashi a daure yace mata”stop crying”…da sauri ta hadiye kukan nata tana gyada kai alaman ta dena…shi kuma ya haura kan gadon tareda kwanciya yana sake lumshe idanunshi…Layla ta matso kusa dashi a hankali tace”daddy am sorry”…ya bude idanun nashi da kyar yace mata”kinyi min wani laifi ne..why are you apologizing”…tana girgiza Kai da sauri ta sake cewa”I know..ba sai ka fada ba..nasan nayi maka laifi amma dn Allah ka tsaya ka saurareni…anty Ramla da Ya Ma’u ne  suka dage sai anyi min..wlh daddy Saida nace musu banaso anty Ramla tace ai ba yau zakazo ba wai dole sai anyi min..am telling you the truth daddy kuma ka tambayi Anty Ramla zata fada maka”..Taheer ya mike zaune da kyar yana fuskantarta yace”you have no idea how jealous I am baby..da kin San yanda nake kishinki da duk bazakiyi wnn abubuwan ba…look at how beautiful you are..kikayi make up baby..kika sa mayafi snn kika fito da gashi kika shiga cikin taron maza kina rawa kina musu dariya baby is that fair..kinsan yanda naji dana ganki kuwa..kinsan zuciyata ta kusa bugawa”.. ya karasa mgnr yana girgiza kai tareda sake lumshe idanun shi..har yanxu bai bar takaicin wnn abu ba…Layla tasa hannu tana share hawayenta tace”na sani daddy..dn Allah kayi hakuri..wlh ba laifina bane..am so sorry ka yafemin”…ya bude idanuwanshi tareda zubasu a kanta…ganin yanda take hawaye wani kan wani sai yasa hannunshi ya janyota jikinshi…ya rungumeta sosae murya a hankali yace”you have no idea how much I love you baby..Ina sonki sosae..kimin alkawai bazaki taba barina ba in future..I will be nothing without you..I love you so very much”…Layla ta saki murmushin jin dadi kafin tace”baka ce ka yafemin ba daddy”…tana rufe baki yace”na yafe maki babyna..kawai dai inada kishi ne..amma bazan iya daukan fushi dake for so long ba kin sani..so ki kiyaye gaba kinji”…tasa hannun tayi hugging dinshi itama tace”nagode sosae daddy..I love so much”…yana murmushi yayi kissing kanta snn ya dago face dinta yana kallo yace”you look so gorgeous baby”…itama dagowa tayi tana kallonshi with a smile tace”you also look handsome hubby..and I love you for that”…Taheer ya dago face dinta yana kallo yace mata”I like that name”…sai ya matso da face din nata dab da nashi ya hade..hancinshi na gogan nata hakama lips dinsu…Saida ya lumshe idanunshi kafin yace”baby please”..Layla ta bude ido tana kallonshi sai kuma ta sake maidasu ta rufe tanajin yanda heart dinta ke beating at a faster rate…Taheer ya sake matso da face dinshi jikin nata yayi kasa da murya yace”baby dan Allah kinji..ki tausaya min plss”…da sauri Layla ta bude idanunta don sai yanxu ta fahimci abinda yake nufi…ta shiga ja baya da sauri tana girgiza kai tace”no daddy..dn Allah kayi hakuri”…yai azaman dawo da ita jikinshi still murya a kasa yace”dn Allah baby kiyi hakuri..I can’t..ki taimaka min kinji”..tana kuka tace”daddy ni tsoro nakeji..dan Allah ka maidani kar su ummi suyita nemana basu ganni ba dn Allah”…yana girgiza kai shima yace”nace maki bazakiji zafi ba baby..kiyi hakuri ko 10 mins ne kinji..I promise I’ll be gentle”.. daga haka bai sake bata space din mgn ba ya hade bakin nasu wuri daya…

(Asha kuka lfy🏃🏻‍♀️😹)

STORY CONTINUES BELOW

A can wurin dinner kuwa su ummi duk basu lura Layla bata wurin ba..don akwai mutane sosae a wajen so ko da basu ganta ba sunyi tunanin maybe tana wurin wasu family members din suna hira or something like that…

Saida aka tashi daga dinnern mutane sun fara watsewa snn hankulansu ya dawo kanta..ummi na duban Al’ameen tace”kai tashi kuje ku nemo Layla..kuce mata wucewa zamuyi zaman me takeyi Kuma”…su Al’ameen suka mike shida Ramadhan suka tafi neman Layla…suka ringa shiga lungu da saqo suna nemanta amma basu ganta ba..har premises din wurin suka fita suka duba ko Ina Amma ba Layla babu alamarta…suka dawo suka shaida musu sun duba ko Ina Amma ba Layla…”to fah”..shine mgnrda umma ta fada yayinda take duba cikin hall din kusan duk kowa ya watse su kadaine suka rage…a hankali suka mike suma suka fita daga cikin hall din..nan ma dai ba mutane sosae a wajen don da yawa sun tafi…ummi ta dubi Ramla tace”ke wai ba tare kuke bane tun dazu..ya zaayi a nemeta a rasa all of a sudden”…Ramla tace”ummi nifa tunda ta bar wurin likin nn ban sake ganinta ba..duk a tunanina wajenku tazo shiyasa ban nemeta ba”…”innalillahi ummi ta fada har karshe ta Dora da fadin”to Ina Kuma ta shiga ni Maryama”…umma tace”gsky dai abun da mamaki..ita ba karamar yarinya ba balle ace ko wani ne yai Mata wayo ya tafi da ita”..ummi tace”shine abinda na gani Aisha..ynxu idan bamu ganta ba ya zamuyi ni Maryam”..Nafeesa ta dafa kafadan ummi tace”ummi karki damu kanki dn Allah..zaa ganta InshaAllah..Bari in sake Kiran wayan nata”…tana gama mgn ta shiga dialing number Layla da taketa Kira tun dazu ana ce mata switch off..ta sauke wayan daga kunnenta a hankali..tana dubansu tace”har yanxu wayanta a kashe yake wlh”…gaba daya hankalinsu ya sake tashi…umma ce ta zaro wayanta daga jaka tareda Kiran number Taheer amma har ya gama ringing dinshi baa dauka ba…Saida ta jera mai 3 missed calls snn ta hakura..haka nn jikinta ya bata shine yazo ya tafi da ita..dukda yace sai gobe zaizo tasan halin kayanta tsaf zai iya cewa bazai iya bari sai gobn ba ya taho yau..amma gashi tanata Kiran wayanshi baya picking…Ganin mutane kalilan ya rage a wurin..umma tace su samu su karasa gidan bikin maybe tabi motan wasu ta tafi tare dasu…hakan kuwa sukayi..duk suka shiga mota suka koma zuwa gidan.

A canma dai duk binciken duniya sunyi amma ba Wanda yaga Layla…yarinyan da Taheer yasa ta kirata dazu..da taji ana nemanta tace wani mutumi ne yace ta Kira mishi ita..Kuma ta tabbata taga lokacinda ta tafi wurin mutumin…ummi ta rushe da kuka tana”innalillahi wainna ilaihi rajiun..wane mutumi ne wnn zaizo ya dauketa ni Maryam..me yake nema a wurinmu”…umma ce tayi karfin halin tambayan ta ko ya fada Mata sunanshi…yarinyan tace bai fada Mata ba Amma taji Layla ta kirashi da daddy…cak ummi ta tsaya da matsar hawayen da takeyi tareda kewayo da idanunta kan yarinyan…tana kallonta da kyau tace”me kikace ta kirashi”…yarinyan ta sake cewa”daddy”…ummi tayi wani kwafa tana fadin”aiko sai naci ubanshi wlh..mu zai rainawa hankali yazo ya sace yarinya ana cikin biki kawai sbd ya daga mana hankali”..umma da ko kadan batayi mamakin jin shi ya dauketa ba ta danyi dariya kawai..dama tasan da kyar idan bashi din bane..gashi kuwa zarginta ya zama gsky…ko Ina Kuma ya kaita yanxu sai Allah…Nafeesa ma dariya ta danyi kasa kasa cikin ranta tana ayyano rigimar da zaa sha da ummi idan ya dawo da ita…Sam ita bataga laifinshi ba tunda dama tun asali ya nuna baiso a taho mai da ita amma ummi ta dage..yanxu kuwa ko Abuja ya maida ita bazata taba ganin laifinshi ba…

A haka suka koma part din da aka saukesu..hankalinsu dai yanxu ya kwance tunda sun san tana wurinshi…ummi ce kawai taketa faman mita tun dazu..wai yaki dawo da ita ko gidan ubanwa ya kaita oho..Ramla na dariya tace”to ummi koma Ina ya kaita ba matarsa bace..ya gaji da abinda kike mai ne shiyasa kawai ya silalo yazo ya dauke kayarshi suka tafi..maybe ma zuwa yanxu sun sauka Abuja”…ummi ta maka Mata wani harara tana cewa”aiko da ya jama kanshi wlh..don sai tayi wata hudu a gida bata koma gidan nashi ba..sai inga karewan iskanci”…Ramla ta sake cewa”ummi baa shiga tsakanin ma’aurata fa..kilan yanada bukatar matarsh..”bata karasa abinda zata fada ba ummi ta buge mata bakin tana ce Mata”rufema mutane baki da Allah..kema da yake ba kunyan ne ya isheki ba zakizo ki cikani zancen banza”..gum Ramla tayi tana shafa bakinda ummi ta kaima duka…Nafeesa na zaune gefensu duk tana sauraron abinda suke fada tanata kokarin boye dariyarta amma sai daya fito…ummi ta dubeta baki bude tace”kici gaba da dariya kema..zakisha mamakina wlh..bazaku maidani tsohuwar banza ba”…

A can hotel din kuwa tana kwance a jikinshi tayi luf da idonta kmr tana bacci…a hankali ya yaye blanket da suka lullube dashi snn ya dauketa suka shiga bayi…ba tareda ta bude idanun nata ba tace”daddy ka tafi dn Allah..ni zanyi wakana da kaina”…Saida ya manna Mata kiss a Kumatu snn yace”no baby tare nakeso muyi wankan yau”…ta bude idanun nata da sauri sai Kuma ta sake maidasu still da sauri don batasan ba Kaya a jikinshi ba…ta kwabe fuska kmr zatasa kuka tace”nidai dn Allah daddy kaje ka kyaleni zanyi ni kadai”…Taheer yasa hannu tareda kamo kumatunta yadan ja snn yace mata”to mu sake komawa kan gadon idan muka Kara another round sai in bari kiyi wankanki ke kadai”…fuskan ta sake kwabewa tana makale kafada tace mishi”ah ah”…ya janyota kusa dashi tareda hade bare skin dinshi da nata..ya sunkuya saitin kunnenta yace”to ya zamuyi knn..kindai san bazanyi maki alfarman abubuwa har guda biyu ba koh”…tana hawaye Kuma still idanun a kulle tace”to ka sa kayanka”… murmushi mai sauti ya saki before saying”kin taba ganin inda mutum yayi wanka da Kaya a jikinshi”…tana turo baki tace”to nidai bazan bude idona ba”…ya juyo da ita saitinshi yace”come on baby open your eyes dn Allah..am all yours so ba wani abu bane idan kin kalleni”…ta sake makale kafada tace mai”No”… shi Kuma bai sake mgn ba ya dagata sama kawai sai jinsu tayi cikin bathtub…ya cikashi taf da ruwa…a haka ya farayi Mata wankan tun tana rufe idon har Saida ta hakura ta bude..saidai taki kallon side din da yake..ita a dole bazata kalleshi ba kayaba…shi Kuma Saida ya tabbatar da ta kalla din snn ya saurara Mata…

Saida suka gama lalacewarsu a toilet din kafin suyi wankan su fito…Yana daukeda ita a hanunshi kmr jaririya…ya ajiyeta kan gadon snn shima ya zauna..tana tsuke bakinta tace”daddy dn Allah ka maidani gida…su ummi fa basu san na taho ba”…ya dauki wayanshi yana dubawa yace”ai ke da ganin su ummi sai gobe Kuma”…Layla ta wara idanu tace”hope bada gaske kake ba”.. ya dago kanshi daga kallon wayan da yakeyi yace”da gaske nake wlh..sai gobe da safe zamu koma”.. yana rufe baki tace”dn Allah daddy kar kayi haka..zasu shiga damuwa wlh dn Allah mu koma can kaji”…Taheer baiyi Mata mgn ba sai wayarshi da taga ya Kara a kunne alaman Kira zaiyi… ringing biyu umma ta daga tana fadin”sannu shugaban marasa kunya”…ya shiga shafa kanshi Yana murmushi yace”umma kinsan dai ba laifina bane koh”…tace”ba laifinka bane ai laifina ne”…yace”no umma ba haka nake nufi ba..sai da na fada maku kar ku tafimin da matata amma kuka dage Saida kuka zo..shine nima nazo kawai na dauke abata yanxu haka mun koma Abuja ma”…umma tace”ai shknn Kai da Yaya ai..zakayi Mata bayani”…Yana dariya yace”umma wasa nake wlh..Muna nn cikin Dutse bamu tafi ba”….”cikin Dutse a Ina Taheer..dama kasan wani wurin ne”… yace”aah umma..Muna hotel..amma umma dn Allah kuyi hakuri Nima ba laifina bane wlh..kawai zuwa nayi na ganta taci uban kwalliya tanata rawa shine ni Kuma na dauketa daga wurin gaba daya..am sorry kinji ummata”….umma tace”Ai shknn Taheer..yanxu sai ka dakkota ka dawo da ita tunda ka gama abinda kakeso”…Taheer ya zare idanu sosae jin abinda umma ta fada…sai kuma yai kasa da murya yace”umma ai..sai..gobe..zamu dawo”…ya fada words din a rarrabe…umma bata sake yunkurin mgn ba kawai tayi hanging call din…Layla ta matso jikinshi da sauri tana cewa”daddy dn Allah muje gida..kaga umma ma bata yadda ba..dn Allah mu koma gida kaji”…Saida ya ajiye wayanshi yace Mata”babu inda zamuje sai gobe…yanxu bari in fita samo maki abunda Zaki sa”…banza tayi dashi tana binshi da harara..ya fara shiryawa a gurguje snn yasa kayanshi…ya dau key din dakin tareda wallet dinshi snn ya fita daga dakin.

After like 15 mins ya dawo daukeda leda a hanunshi…ya karasa kusa da ita yaga har tayi bacci ma..ya dauko rigan daya siyo mata snn ya zauna a hankali ya zira mata rigan a jikinta.. ya rage kayan jikinshi shima snn ya kwanta tareda sanyata sosae a jikinshi feeling extraordinary happy.

Washegari ma Saida suka sake another round snn sukayi wanka suka fara Shirin tafiya can gidan don Taheer zaije daurin aure 11…Layla sai kumbure kumbure take ita a dole ya bata Mata rai…da kanshi ya dauko abayan daya siyo Mata jiya ya zura Mata a jiki..sai Kuma ya rungumeta yana fadin”nace am sorry fa baby..bazaki hakura ba ne..kuma mace maki ban karawa sai da kanki kince mn kinaso”…tana turo bakinta tace”ai nasan ba denawa zakayi ba..kawai kasa duk jikina yanamin ciwo”..sai ta fara hawaye…Taheer yace”come on baby mene abun kuka Kuma..na fada maki as time goes on zaki dena jin zafin..kiyi hakuri kinji”…da kyar ya samu ya lallabata ta karasa shiryawa suka tafi bayan shima ya shirya…dama tun jiya daya fita yaje ya taho da kayanshi ba tareda kowa ya ganshi ba.

Cikin mintina qalilan suka isa gidan..Taheer ya ba mai taxi daya kawosu kudinshi snn ya kama hanunta suka shiga ciki…kirjinshi sai dukan tara tara yake..bai san wane irin rikici xasuyi da ummi ba..Kai tsaye part din da aka saukesu suka nufa..ita kanta Layla zuwa yanxu gabanta faduwa yakeyi sosae..a haka suka shiga ciki..Ramla ce zaune a parlor tana daurama Hibba dan kwali..su Al’ameen Kuma na zaune a gefenta..suk sunyi shirinsu na tafiya daurin aure suma..abbansu kawai suke jira..Taheer ya karasa cikin parlon hanunshi cikin na Layla snn suka zauna…suna zama din Kuma sai ga umma ta fito cikin shirinta itama…da sauri Taheer ya mike daga inda ya zauna ya karasa inda umma ta zauna..Saida ya zauna kusa da ita snn yayi making pity face yace”umma dn Allah kuyi hakuri wlh ba laifina bane”…umma na girgiza kai tace”wai nace kayi laifi ne Taheer..ai ba laifinda kayi..kawai ka jira hakuduwanku da Yaya”…ta karasa mgnr tana dariya kasa kasa don tasan drama ne zaa Shashi tsakaninshi da ummi…tana rufe baki kuwa abun kmr hadin baki saiga ummin itama ta fito tareda Nafeesa..dama suna niyyan shiga cikin gidan ne tunda time na daurin aure ya kusa…ummi na ganin Taheer a parlon ta daure fuska tamau snn ta karaso ciki tana duban umma tace”Aisha ya kikazo kika zauna Kuma..muda zamu shiga cikin gidan yanxu”..tana gama mgn Taheer da kanshi ke kasa yace”ummi Ina kwana”..ta juyo a fusace tana kallonshi tace mai”rike gaisuwarka banaso..badai ni ka maida mutuniyar banza ba..ka tsalallako Taheer har wajen biki kaje ka sace ‘yar mutane snn ka kama gabanka da ita..sbd tsabar Wulakanci Kuma ko ka kiramu ka sanar Kuna tareda ita..haka kasa mukayita neman yarinya hankalinmu duk a tashe..kuma tsabar rashin kunya sai da kuka kwana a waje snn kake dawo mana da ita..wai yaushe ka zama tantiri ne haka ban saniba”..shidai Taheer shiru yayi yana sauraronta..sai da ta gama snn yace”dn Allah ummi kiyi hakuri..wlh banzo da niyyan in dauketa daga wurin ba kawai gani nayi tayi make up Kuma tanata rawa shine na dauketa..amma dn Allah ummi am sorry kinji wlh baa son raina bane”…yana rufe baki ummi ta sake cewa”to idan batayi kwalliya ba Taheer ya kakeso tayi..haka kakeso ta tafi wajen bikin fuskanta kmr dusa..yarinya da kuruciyanta da kyanta Kuma sai a hana Mata kwalliya kawai sbd kafi uban kowa kishi…kai daka tsinci dami a kala ma ai kamata yayi ka ringa lallaba yarinyar nn tunda dai kasan tafi karfinka..amma shine zaka fara iskanci sbd kana ga ai ka riga ka sameta koh..to baka isaba wlh..kuma idan baka shiga hankalinka daniba ranka zaiyi mummunan baci kaji n gaya maka”…murya a sanyaye Taheer ya sake cewa”to ummi naji Kuma na karba laifina dn Allah kiyi hakuri kinji”..tabe baki ummi tayi tana gyara zaman mayafinta tace”shikena Kuma ai..dama ni rashin kunya ne banso..duk ka sake irin wnn abun Kuma wlh kaji na rantse sai tayi wata hudu bata gidan naka..sai inga karewan iskanci”.. tana rufe baki Taheer yace”InshaAllah ma bazaa Kara ba ummi..thank you”…ita kuma ummi duban Layla tayi tace Mata”je ki sako kayanki sai ki samemu a cikin gidan”..a hankali Layla ta mike tana takawa a hankali ta nufi daki…su Kuma su ummi suka fita daga dakin don don zuwa main hause din…Taheer ya kama hannun su Al’ameen suka tafi wurin daurin auren tare tunda a kofar gidan zaayi daurin auren.+
12 daidai suka dawo daga daurin auren…tare suka shigo gidan da Awwal da Kuma su Ramadhan..gaba daya Taheer sai yaji wani nauyinshi yakeji duk ya kasa sakewa dashi kmr da..dukda hiran da yake ta janshi dashi amma ya kasa sakewa har suka shiga part din dasu ummi suke…daidai lokacin suma duk suka dawo ciki…bayan sun zauna a parlor Awwal ya gaishesu with respect…ummi nata tsokanan Hibba da taje jikinshi ta lafe…
Nafeesa da Ramla suka kawo musu abinci kala kala da drinks suka ajiye musu…Taheer dama mikewa yayi don bazai iya cin abinci tare dashi ba…ganin zai fita sai umma tasa aka hada mai nashi daban..tasa aka Kai mai wani dakin…to anan ne ya Dan samu yaci dukda dai ba mai yawa ba yaci ba..
Bayan Sallhn Isha aka tafi Kai amarya…gaba daya su ummi sun tafi raka amaryan Layla ce kadai bata jeba..tana kwance cikin daki tana rama baccinda Taheer bai bari ta samuyi sosae ba jiya wayanta ya shiga ringing…cikin magagain bacci ta dauko wayan tareda picking call din..sai taji voice din Hanna na cewa”mutanen Jigawa”..Layla ta Dan bude idonta tareda mikewa zaune..a hankali tace”mama unborn how far..ya jikin naki”…Hanna tace”ganinan dai kawai Jakada abun baa cewa komai..tun jiya da dare nake Kiran wayan naki switch off”…Layla tace”wlh Hanna daddy ne ya kashemin wayan..ni banma saniba sai da safe na duba naga ashe tun jiya ma a kashe take”…Hanna tasa dariya sosae kafin tace”su love birds kice ana can ana fama..to Allah yasa ku dawo mana da baby”…tsaki Layla ta saki tace mata”ni matsala na dake akwai ki da donkey letter..wane irin mu dawo da baby kuma ana zaune qlou”…Hanna tace”kmr yanda kikaji na fada dai hakan nake nufi..ynxu dai ba wnn ba..kinsan dalilinda yasa na kiraki”…da sauri Layla tace”aah”..Hanna tacigaba”AY Gambo ne yazo yayi test wlh jiya..kuma yace shine C.A dinmu and bazai yima kowa make up ba..shine naketa kiranki tun jiyan in fada maki ko zaki samu kimai mgn idan yaga kece maybe zai hakura yayi miki mk up din”…shiru Layla tayi tana jinjina al’amarin a cikin ranta..bata taba tunanin zaiyi C.A dinshi yanxu ba dukda dama can yace musu shi unannounced C.A yakeyi…a wani bangaren Kuma tana tunanin da kyar idan Taheer zai bari ta sake mgn dashi…Saida ta sauke numfashi snn tace”shknn Hanna nagode..zanyi mgn da daddy duk abinda yace shknn”..Hanna tace”to Allah ya doraki a kanshi..ni zan kwanta Saida safe”…cikeda tsokana Layla tace”as’habul Kahfi iyayen bacci”…itama Hannan tace”eh ba komai..kema naki turn din yana nn zuwa”…da haka sukayi sallama… Layla tayi shiru tana tunanin da kyar Taheer zai bari tayi mgn da AY Gambo..amma abune Wanda ya zama dole don haka babu yanda zaiyi dole haka zatayi mgn dashi din..
STORY CONTINUES BELOW
Tun tana jiran su ummi su dawo har batasan time din da bacci ya dauketa ba…lokacin da suka dawo Kuma ba Wanda ya tasheta..sukayi Shirin baccinsu suma suka kwanta.
Shiko Taheer dama tun yamma ya koma hotel din da yayi lodging jiya..zai sake kwana a can amma gobe Sunday dai yake son  komawa Abuja…Allah yasa suma su ummin gobe zasu tafi don baiso baby tayi missing school da yawa.
Washegari suka fara shirin tafiya kano..don daga can zasu tafi…
Basu bar cikin Dutse ba sai around 2..bayan sunyi sallama da kowa snn an cikasu da kayan biki kala kala..driver dinsu na nn dama..don haka tare dashi suka tafi…
Tun safe Layla ke zuba idon ganin Taheer amma ko mai kama dashi bata ganiba…tayita Kiran wayanshi Kuma no answer…haka har suka tafi kano bata ganshi ba..umma ma tayita Kiran wayan nashi don ta fada mishi sun wuce kano amma still no answer.
Shiko Taheer bacci ne ya daukeshi mai nauyi sosae..har bai san time ya kure haka ba…lokacinda ya tashi yayi mamaki sosae da yaga har 3 ya kusa…ya fada bathroom da sauki yayo alwala ya fito..a nn cikin dakin yai sallahn zuhr snn ya shiga bathroom din yayi wanka ya sake fitowa..a gurguje yaketa shiri don bai San ko su ummi yau zasu tafi ba…Yana daukan wayanshi ya taradda 10 missed calls from Layla..sai 4 missed calls na umma…a gaggauce ya gama shiryawa snn ya dauki kayanshi ya tafi..Saida yai clearing bill dinshi na hotel din snn ya maida musu key dinsu ya tafi…Yana zuwa can gidan aka ce mai ai sun tafi kano…wani haushi ya kamashi sosae…har zasu tafi amma ba Wanda ya nemeshi..ko da yake sun nemeshi wayan nashi ne a silent shi Kuma yanacan yana bacci..
Shatan mota ya dauka shima direct suka nufi Birnin Dabo..
Karfe 4 saura su ummi suka shiga Kano..Kai tsaye Janbulo suka wuce inda gidan umma yake…bayan sun huta sun watsa ruwa…sai suka zauna parlor suna Dan taba hira…da a yau sukaso wucewa Abuja amma ganin yamma ya riga yayi sai suka fasa sai gobe su sakeyin sammako su tafi…
Har yanxu umma bata dena Kiran wayan Taheer ba amma still baya answering…sai Kuma ta shiga tunanin ko dai ba lfy yake ba..inba hakaba ya zaayita Kiran waya Yana gani yaki dagawa.
Itama Layla a nata bangaren bata dena Kiran wayan nashi ba…duk hankalinta yaki kwanciya gani take kmr wani abu ne ya sameshi..gashi Kuma tanaso suyi mgnr AY Gambo da akace yayi test dashi..don tana tsoron taje tayi mgn dashi Kai tsaye idan Taheer din ya samu lbri tasan he’s going to be mad..ko su ummi har yanxu bata fada musu cewa anyi test a school bata nn ba.
Taheer bai sauka garin Kano ba sai after 5…direct shima ya dauki drop din napep ya kaishi gidan umma don yasan for sure zai samesu a can tunda yamma yayi so baya tunanin zasu kama hanyan Abuja..yasan ummi bata son tafiyan dare Sam.
Yana shiga duk suka bishi da kallon mamaki..don ita ummi duk a tunaninta ya riga ya koma Abuja..umma ce tace dashi”Kai meya samu wayanka ne tun safe naketa kiranka amma baka dauka”…Taheer ya karasa cikin dakin ya zauna snn yace mata”wlh umma bacci ne ya daukeni..Kuma wayan a silent yake shiyasa ban ji Kiran naki ba”…umma tace”to da kaga missed call kuma meya hanaka Kira”…Kai ya langabe snn yace”umma sauri nakeyi in taho shiyasa..am sorry”…ummi tace”Kai daya kamata ka wuce direct Abuja meya kawoka Kano Kuma”…yace”zan tafi ummi..8 jirginmu zai tashi”…daga hak ummi bata sake mgn ba…
Layla dake daki kwance taji kmr muryanshi a parlor..don haka sai ta fito parlon don ta ga ko shidin ne…aiko tana ganin shine ta karasa inda yake tana washe baki tace”daddy sannu da zuwa..yaushe kazo..daddy tun dazu nake Kiran wayanka baka dauka..what happened”…Taheer ya kama hanunta yana murmushi shima yace Mata”duk wnn tambayoyin haka baby..wayan nawa ne a silent ni kuma ina can Ina bacci”…tace”dama ancemin anyi test ne a school jiya”…Taheer na dubanta da kyau yace”test Kuma”…tana daga kai da sauri tace”eh daddy..AY Gambo..Kuma yace wai bazaima kowa mk up ba”…shiru Taheer tayi for some seconds sai kuma yace”you see..yanxu kinga dalilinda yasa na dage kan bazakiyi missing school ba..amma kika dage ke sai kinzo..yanxu ya kikeso ayi”…yana rufe baki tace”daddy Hanna tace wai idan nayi mishi mgn da kaina zai yadda..kilan ta dalilina kaga suma Wanda sukayi missing test din yayi Mana make up din tare”…Taheer ya kalleta da wani expression kan fuskanshi snn yace”ummhum Ina jinki”…a hankali tace”daddy dn Allah inyi mgn dashi?..”tana rufe baki yace mata”No…idan kika kuskura kikai mgn dashi Kuma you will see the other side of me”…Layla har ta fara hawaye..tana kokarin yin mgn ummi tace”ban gane kar tayi mgn dashi ba Taheer..ba malaminsu bane”…ranshi a bace yace”ummi malaminsu ne..amma nidai ban yadda taje tayi mgn dashi ba..ba da yawuna ba”…da mamki sosae duk suke kallonshi…banda umma da tasan dalilin da yace haka…Layla ta sake matsawa jikinshi murya a raunane tace”daddy dn Allah kayi hakuri ka barni inyi mgn dashi”…a takaice ya sake ce Mata”I said no”…tace”but daddy why”…kmr jira yake tana rufe bakinta yace”because he loves you”…tana girgiza kai tace”daddy ba mun gama da wnn mgnr ba Kuma..ya riga ya zama past tense”…”idan ke ya zama past tense a wurinki to ni a wurina bai zamaba…idan Kuma kina tunanin ya dena sonki ne you are mistaken…he loves you so much..I saw it in his eyes sbd haka ban amince kiyi mgn dashi ba…Ni zanyi mai mgn dakaina..zan rokeshi yayi maki test dinda kikai missing amma baby ko a bayan idona ban yadda kiyi mgn dashi ba..I mean it”…Taheer na gama mgn sai ta fada jikinshi tana goge hawayenta tace”na gode sosae daddy..thank you”…a hankali yasa hannunshi ya janyeta daga jikin nashi don ganin duk hankalinsu su ummi na kansu…Nafeesa da Ramla kuwa mikewa sukai suka bar parlon…ita Nafee kunyar rungumar da Layla tayi mai ne yasata barin parlon..bata San me yasa takejin nauyin hakan ba yanxu dukda ba yanxu ya fara hugging dinta a gabanta ba…ita Kuma Ramla nauyin Taheer din takeji tunda ba wani sabawa sukai dashi ba…tsakaninta dashi gaisuwa ne kawai..bai sakewa da yara sbd baya son raini…Layla ce kadai dama tun tana karama yake sakewa da ita fiyeda kowa…ashe Kuma kauna ce tsakaninsu basu saniba…
Ummi kuma na dubanshi da kyau tace”ni duk ban fahimci me kuke cewa ba..waye yake sonta Kuma”…sai yanzu umma ta fara bata lbrin duk abubuwan da suka faru…ummi tayi mamki sosae..sai Kuma tace”Amma dai wnn yarinya akwai Mara mutunci…taketa kulla makirci haka kan kankanuwan yarinya ‘yar cikinta..to Allah ya kiyaye gaba..ita Kuma Allah ya shiryeta”
Karfe 7:30 daidai Taheer yayi sallama dasu snn ya tafi airport…duk ranshi a bace yake sbd bazasu koma yau ba…knn hakan na nufin Layla zata sake missing zuwa school gobe Monday..yanayin mgn Kuma yasan ummi zata hau shi da fada..
Washegari suma karfe 7 suka kama hanya…sunaso su isa Abuja da wuri sbd Nafeesa da yara jirgin 6 zasubi zuwa porthacourt tunda yaran basu samu hutun makaranta ba.
Basu suka isa Abuja ba sai ana sallahn azhr..bayan sun karasa gida kowa ya kama dakinshi don ya dan huta… already dama mama Hauwa tayi musu girki don haka suna gamawa suka fito cin abinci…bayan sun gama sai suka koma parlor…Taheer ya Kira umma take sanar dashi sun sauka…yace zai zo gidan idan ya baro clinic.
Karfe 5 ya baro clinci ya nufo gidan..dama already su Nafee sun gama shiryawa daukansu kawai yayi bayan sun gama sallama da su ummi snn suka nufi airport…kafin su shiga jirgi Nafeesa ta samu ta janyo Layla gefe snn ta bude hand bag dinta tareda dauko wani leda a ciki ta mikama Laylan…ba musu Layla ta amsa tana kokarin tambayan menene Nafeesan tace Mata”ki ringa damawa da madara kullum kinasha safe da yamma..tun tuni nakeso in baki to ban samu kebewa dake bane…da akwai tsumi shima yanada kyau sosae zan aiko dashi gidan Ramla sai kije can ki amsa..Kuma ki tabbata kina amfani da ruwan zafi and ki yawaita Shan fruits don naga mijin nn naki chewing gum ne”…cikeda kunya layl tayi kasa da kanta jin abinda mamin tace…Nafeesa tasa hannu tareda dago fuskan nata tace”ke ba kunya tsakanina dake wnn shine kadai gatan da zan iya yi maki..kuma dn Allah Layla kiyi kokari ki ringa amfani da shawarwarin da Muka baki kinji…Ina Kara jaddada maki banda raki banda gudun miji Layla sai kin dage sosae inba hakaba duk wnn soyayyan da ake maki zaa dena..duk magungunan dana aiko maki dasu Kuma ki tabbata kina amfani dasu yanda ya kamata..Allah ya karo zmn lfy ya kawo zuri’a dayyiba”…tana rufe baki sai kawai taji Layla tayi hugging dinta tana hawayen farin ciki tace”thank you so much Mami..I love you”…Nafeesa ta dagota tana murmushi itama tace Mata”I love you more sarkin kuka..yanzubari mu tafi sai munyi waya”…Layla ta daga Mata kai har yanxu bata dena murmushi ba…ganin su Al’ameen na nufo inda suke Nafee tace”yi maza kisa wnn abun a jaka..Kuma ba cewa nai kije kiyita sha a gabanshi ba..karma ki kuskura yasan kinashan wani mgni kina nija”…Layla tasa maganin a hand bag dinta tareda daga Mata Kai…daidai su Al’ameen suka karaso nn ta akam hannun hibba suka nufi jrigin da zasu shiga..dama sun riga sunyi sallama da Taheer din…ita Kuma Layla juyawa tayi zuwa inda yake jiranta..ta bude mota ta shiga shima ya shiga snn suka dauki hanyan gidansu don sun riga sunyi sallama dasu ummi…
A kan hanya yake fada Mata yayi mgn da AY Gambo ya Kuma amince zaiyi Mata make up din..bama ita kadaiba duk Wanda sukai missing test din zaiyi musu…gobe idan sunje school zai fada musu date da Kuma time da zasuyi…Layla taji dadi sosae har batasan time din da ta matsa jikinshi tareda manna mai kiss a kumatunshi ba…Taheer na murmushi yace Mata”Allah baby idan kikasa mukai accident ba ruwana..bakisan effect din wnn kiss din naki ba koh”..Layla na smiling har yanxu ta juya idanunta tana cewa”Kai daddy..yanxu dan wnn peck din ne zaisa muyi accident”…tana rufe baki Taheer yace”bazaki gane bane baby..komai naki is special..komai naki is different..shiyasa dan abu kadan zakiyi ya kaimin karo..sbd haka a taimaka a dena juyamin idanun nn ki bari idan muka isa gida sai ayi duk abinda zaayi..har kiss dinma yau sai kin koya mn”…ya karasa mgnr  tareda kashe mata ido…ita Kuma ta saki murmushi mai sauti snn ta maida hankalinta kan titi..har cikin ranta taji dadin mgnr daya fada..wai Abu kadan zatayi yake kaimai karo…hmmm gsky daddy sai a barshi…Haka kwanaki sukai ta gangarawa suna zama satika..satika Kuma suna komawa watanni…yayinda tuni Layla sun gama exams sunyi hutun 3 weeks har sun sake juyawa second Semester wanda itama tana gab da karewa.. karatu sukeyi ka’in da na’in don Layla gani takeyi da kmr ma ba karatun sukayi ba…+
Friendship dinsu da Hanna kuwa kullum Kara karfi yakeyi…cikin hutun da sukayi Hanna tazo gidanta..itama Kuma taje nata gidan don basu taba zuwa gidan juna ba.
Tsakaninta da Taheer kam zaace Alhamdulillah don soyayyane mai karfi ya sake shiga tsakaninsu..yana kulawa da ita sosae itama Kuma tana tattalin kayanta..duk abinda yakeso tana iya bakin kokarinta taga tayi mai shi…snn ta dena kin amincewa dashi..zuwa yanxu tasan dadin harkan sosae saidai shagwaban ne dai har yanxu ana nn ana tabawa…suna concentrating kan junansu sosae wanda hakan ke sake karfafa kaunar dake tsakaninsu..
A bangaren girki sai Hamdala don zuwa yanxu zaa iya kiranta very good cook sbd yanda ta maida hankali sosae da sosae..Kuma Alhamdulillah yanxu ba kalan abincin da bazata iya yiba..dama komai na duniya saidai mutum baisa kanshi zai koya ba.
Yau ya Sunday gaba dayansu suna gida..shi Taheer yana parlon sama yana aiki cikin laptop dinshi ita kuma daga shiga daki ta dauko wayanta kawai ta bigire a wurin tana bacci…Taheer ya ajiye system dinshi ya nufi dakin nata don gani abinda ya hanata fitowa tun daxu…da mamaki sosae yayi tsaye yana kallon yanda take baccin hani’an…rabin kafanta na kan gado sauran rabin Kuma na kasa…ya karasa kusa da ita a hankali tareda zaunawa kusa da ita…a hankali ya kamo hanunta daya ya rike cikin nashi…idanunshi Kuma nata aikin zagaye face dinta da kallo…hannunta dake cikin nashi ya saki snn yasa hannun ya dagota daga kwancen da take tareda dorata kan laps dinshi…ta bude idanun a hankali tana kallonshi sai Kuma ta turo baki tana fadin”bacci nakeji plss”…yana girgiza mata kai yace”bazan bari kiyi bacci ba da yamman nn baby..tashi muje parlor in  kunna maki movie ki kalla”…a hankali ta sake turo bakin tace”nidai aah pls..I want to sleep”…Taheer yayi shiru yana kare Mata kallo kawai…lokaci daya Kuma sai ya saki murmushi snn ya mike zuwa closet dinta ya dauko Mata zumbulelen hijab ya dawo inda take ya shiga sa Mata hijab din…Saida ya gama sa Mata snn ya dagata cak yayi waje da ita…ya sauka downstairs snn ya fita waje…ya bude mota ya sanyata ciki snn ya sake komawa ya kulle gidan snn ya koma wurin motan shima ya shiga…har yanxu kuma Layla bacci take…shiko yana driving yana juyowa yana kallonta..har yanxu murmushi yakasa barin face dinshi…addu’a yake Allah sa abinda yake zato ya zama gsky…
Saida ya isa clinic dinshi snn yayi parking…ya juyo yana kallonta tareda kamo hanunta guda daya ya manna mai kiss..sai ta shiga bude idonta a hankali…sai Kuma ta mike zaune tana kalle kallen wurin tace”daddy inane nan?..”a nutse yace daita”Clinic”…ta sake turo baki tace mishi”daddy ni ka kaini mu siyo ice cream din da kace zaka siya mn..yunwa nakeji”…Taheer ya lumshe ido tareda dora dayan hannunshi kan flat tummy dinta yace”no more Shan ice cream baby..I can’t risk loosing my child”…ta sake turo bakin tace”I promise you won’t loose me daddy..kawai inaso insha ne”…dariya sosae Taheer ya saki jin abinda ta fada..wato ita batama fuskanci abinda yake nufi ba knn…Saida yayi me isarshi snn yace mata”kiyi hakuri baby  Shan ice cream ya Kare”…kmr zatasa kuka tace”why daddy”…yace”na fada maki bazan iya bari wani abu ya samu child dina ba”…tace”to daddy tun da can da nakesha wani abu bai sameni ba sai yanxu”…Taheer ya lumshe ido ya bude yace Mata”wacece ke a wurina”….a hankali tace”your baby”…yana shafa cheeks dinta yana murmushi ya Kai bakinshi daidai kunnenta snn yace”yes you are my baby and not my child..am talking about my very own flesh and blood”…lokaci daya Layla ta zare idanu tana kallonshi tace”ban gane ba daddy”….Taheer ya kai both hands dinshi ya dora kan cikinta..idonshi cikin nata yace” I think you are pregnant”…sake zare idanun tayi tana girgiza kai tace”kmr ya pregnant daddy..ni wlh ban gane ba”…Saida ya saki murmushi mai sauti kafin yace Mata”I mean you are carrying my child..my own blood”…yana rufe baki Layla ta fashe da wani irin kuka hadda dora hanu a kai tana fadin”na shiga uku na lalace..shknn yanxu bazan samu daman cigaba da karatuna ba..wayyo Allah na wayyo Mami wayyo ummi wayyo umma wayyo dan Allah ku taimakeni”…Taheer yayi azaman sanyata jikinshi gamida toshe mata baki..yana dariya kasa kasa gamida bubbuga bayanta da daya hanunshi yace mata”menene abun kuka Kuma baby..what’s the meaning of wnn ihun da kikeyi”…yana gama mgn tace”daddy ciki hana karatu yakeyi wlh”… yace”how do you know?..”tace”friend dita Hanna tunda ta samu ciki har yanxu bata iya yin karatu sosae..kullum cikin rashin lfy take nasan nima shknn nawa karatun yazo karshe”…Taheer na murmushi yace”come on baby ya kike mgn kmr ba medical personnel ba..laulayi ai kowa da irin nashi..maybe ma ke bazakiyi laulayin ba..kuma ana fita daga first Trimester ake samun sauki ai”…tace”dukda haka daddy nidai am scared”…ya dagota daga jikinshi tareda cupping fuskanta yace mata”don’t be scared..abin da ma bamu tabbatar da cikin ba..shiyasa na kawoki clinic sbd ayi test mu gani”…ya fada mata kawai don hankalinta ya kwanta amma for sure yasan ya hango karamin ciki a tattare da ita(kunji sai kace maye😹da gaske doctors nada wnn talent din..akwai wani doc da na taba aiki dashi a wani asibiti..irin yana duba out patient sai wata Mata ta shigo itama mara lfy ce amma ko complaint dinta bai gama saurara ba yace a rakata ward a bata gado..idan yazo yin ward round da safe zai dubata..matar tana fita doc din yace min”she will die”nidai bance komai ba sbd inaga kmr he’s lying..wlh the next day Ina shigowa ward din naga ana fitar da gawa..nace wace ta mutu akace patient din Dr.Ishaq yayi admitting jiya😹nayi mamaki sosae..so da gaske doctors are amazing🥰suna iya gane Abu without conducting any test)
STORY CONTINUES BELOW
A haka ya bude mota ya fita snn itama ya bude mata ta fito..ya kama hanunta cikin nashi suka shiga clinic din…mutanen dake cikin asibitin sukaita kallonsu suna ‘yan kuskus dinsu..wasu sun san ya aureta wasu Kuma basu sani ba…har suka shiga elevator hanunta na cikin nashi…suna fita daga ciki Kuma suka shiga office dinshi…ya zaunar da ita kan 3 seater snn yayi using landline dake office din ya kira Central Lab kan su aiko mai da Sample bottle akwai test da yakeso ayi mashi emergency…ba bata lokaci kuwa daya daga cikin ma’aikatan lab din nashi yazo da sample bottle hadda su tourniquet da 5cc syringe Wanda zaiyi amfani dasu wajen daukan sample din…Taheer da kanshi ya karba snn ya dauki blood sample din nata da kanshi…tanata rusa kuka kmr wanda akaima operation…shi Kuma Taheer ya bada sample din yace PT yakeso ayi yanxu yanxun nn…ba musu guy din ya karba snn ya fita tareda komawa lab din..
Shi Kuma Taheer ya karasa kusa daita ya zauna tareda sanyata jikinshi..yana shafa bayanta yace”am sorry kukan ya isa haka”…yana rufe baki tace”daddy wlh akwai zafi”…yana dariya gamida girgiza kai yace”wnn idan akazo labour ban San ya zaayi ba”…aiko ta sake rushewa da kuka hadda su bubbuga kafafu…ya kama kafan nata da sauri shima kmr zaisa kukan yace mata”baby mana..don’t harm our baby da wnn buga kafafun da kikeyi”…itadai tana cigaba da kukanta..sai ya rungumeta gam ya shiga hura Mata iska cikin kunnenta kafin yace”to am sorry kiyi hakuri kinji..am so sorry bar kukan”
After like one hour aka kawo mai result din..ya karba snn ya shiga bude papern a hankali..idanunshi suka sauka kan inda aka rubuta Positive sai daga kasa Kuma aka rubuta 2/12 Amenorrhea…rungume takardan yayi sosae lokaci daya Kuma hawayen farin ciki suka wanke mai fuska..yanxu shine zaiyi Dan kanshi..baby zata Haifa mai ‘da…”Alhamdulillah ya Allah.. Astagfirulla…Subhnallah… MashaAllah…La’ilaha illallah”…abubuwan da yaketa maimatawa knn kmr zautacce..duk addu’an dayazo bakinshi yi yake Kuma har yanxu yana rungume da papern yana hawaye…Layla dai na zaune gefe tana kallon ikon Allah..sam batayi tunanin kukan farin ciki bane ita a tunaninta cikin ne babu shiyasa yake wnn kukan…shi kuma Taheer mikewa yayi da sauri tareda zagayowa tsakiyan office din ya fuskanci Qibla kawai sai ya durkusa ya fara sujoodushshukhoor…yi yake yana karawa har yanxu Kuma bakinshi bai bar furta Hamdala da salati ba…Saida ya gama snn ya mike tareda karasowa inda take ya mikar da ita tsaye kawai sai taji yayi hugging dinta so tight kmr zai maidata cikinshi..hawayenshi na sauka kan kafadanta yake cewa”baby it’s positive..it’s positive baby you are two months pregnant..you are carrying my own child baby thank you so much.. thank you so much baby I love you very much”…sai Kuma ya saketa da sauri tareda durkusawa nan kasa..a hankali yakai hannu tareda daga riganta sama…ya shiga mannawa cikin nata kisses all over har yanxu Kuma bai bar hawayeba..he just can’t believe shine zaiyi ‘dan kanshi from this loving soul..wato a duniya samun ‘da ko ‘ya from the woman da kake mugun so a rayuwanka is blessing..he can’t thank Allah enough for all these..He’s forever grateful…Saida ya gama kisses din nashi snn ya kama cikin da duka hannayenshi..fuska daukeda tsantsan farin ciki yace”your Papa loves you so much..I can’t wait to hold you…inaso ki zama good girl okay.. this mummy of yours is somehow stubborn..I want you to be a good girl kar ki ringa hanata yin karatu kinji”..sai Kuma ya sake kissing cikin nata yana”I love you so much”…Layla dai tsuru tayi tareda zubawa sarautan Allah ido…zuwa yanxu ko baa fada ba tasan the result was positive…ganin yanda yake mgn da cikin da Kuma hawayen da yake yatabbatar Mata he’s very Happy…at this point itama sai taji she’s happy..duk abinda zai sanyashi farin ciki haka ba karamin Abu bane..kuma tana son duk abinda yakeso don haka itama sai taji tana kaunar cikin..she just can’t wait ta haihu taga dawa babyn zaiyi kama…ta daga ido tana kallonshi with a smile tace”wane yace maka it’s a girl..ni baby boy nakeso wanda zaiyi kama dakai”…tana rufe baki Taheer ya sake hugging nata yana cewa”no baby InshaAllah it’s a girl..I want a baby girl just like you..I want to pamper and spoil her kmr yanda nayi maki”…dariya kawai ta saki without saying a thing…shi Kuma ya mike tareda kama hanunta yace let’s go dama abinda ya kawo mu knn…ba musu ba bishi a baya..Saida yayi locking office din snn suka shiga elevator da zai maidasu 1st floor…suna fita ya sake kama hanunta har cikin mota…ya bude motan ya shiga bayan itama ya sanyata a ciki…har zai tada motan Kuma yaji bazai iya tafiya without telling umma wnn good news ba…don haka ya zaro phone dinshi tareda dialing number dinta…tana picking yace Mata”Ummata Albishirinki”…a daya bangaren umma tace”goro”..yace”am going to become a father soon”…umma ta dan wara ido sai Kuma tace”ban fahimceka bafa”…yace”Umma baby is pregnant.. two months pregnant..we are going to become parets umma ki tayamu farin ciki”…Umma da lokaci daya farin ciki da jin dadi suka lullubeta tace”Taheer are you serious..banason wasa fa”…yace”wlh umma da gaske nake…ai bazan taba maki irin wnn wasan ba”…umma tace”Alhamdulillah Alhamdulillah..Allah ya raba lfy Taheer ubangiji Allah yayi mai albarka ita kuma Laylan Allah ya bata lfy”… yace”Ameen Umma”…kafin ya sakeyin mgn tace mai”Kai kyaleni inje in bama Yaya good news..I will get back to you”.. daga haka ta kaste Kiran..shima Taheer ya ajiye wayan nashi har yanxu yana murmushi snn ya tada mota suka tafi…
Saida suka hau kan titi snn yace Mata”baby me kikeso kici..name it..ko menene dole ma in nemo maki shi”…Layla ta rausaya Kai snn tace mai”ni ice cream nakeso”…ya shiga girgiza kai yace”banda ice cream plss..ki fada wani abun dai”…tayi raurau da ido alaman zata sa kuka tace”nidai shi nakeso”…kai ya sake girgizawa yace”dn Allah baby ki fadi wani abun..banda ice cream plss..I don’t want my baby to catch cold tun bata zo duniya ba”…yana rufe baki sai ta rufe face dinta da hannayenta ta shiga rera mai kuka…da sauri ya gangara gefen titi yayi parking tareda kamota jikinshi…a tausashe yace mata”baby dan Allah stop..why zaki fara kuka kan such a minor issue”…tana cigaba da kukan tace”it’s not minor..ni ice cream kadai nakeso kuma idan baka siya min ba bazanci abinci ba wal”..tun kafin ta karasa ya rufe mata baki da hannunshi…kmr zaisa mata kukan shima yace”baby na shiga uku..why zakice baza kici abinci ba..do you want to sterve my child”…ta dan dakatar da kukan da takeyi tana turo bakinta kmr zai bar muhallinshi tace”nidai ka siya min ice cream dina”…tana rufe baki yace”zan siya maki baby amma karami..Kuma daga yau karma ki sake cemin zakisha ice cream don bazaki sha ba..bazan bari kiyita dirkama yarinyata sanyi tun tana cikin ciki ba”…tace”to nidai muje a siyo min”…Saida ya maidata seat dinta snn shima ya koma nashi yaci gaba da driving..yanayi yana kallonta…
A Cold Stone suka fara tsayawa don siyan ice cream din..bayan sun shiga ciki ya juya yana kallonta yace”which flavour kikeso?..”da sauri tace”inason chocolate da vanilla..snn inason strawberry and daddy dn Allah ko 5 Scoops ne  banason Dan kadan plss”…baice mata komai ba kawai ya zaro atm dinshi…shi Kuma mutumin dake wurin ya shiga hada mata flavours din da tace tanaso…bayan an gama hada mata anyi packaging Taheer ya amsa..snn suka fita daga wurin bayan sun cire kudinsu through his card…tun a mota ta bude ice cream din ta fara sha kmr Wanda ta dade basa komai a bakinta ba…Taheer dake driving sai juyowa yake yana kallonta..Sam baa son ranshi take Shan wnn ice cream dinba..gani yake kmr sanyin zaiyi affecting babynshi..baison komai ya samu babynshi..he wants her to stay strong and healthy in her mother’s womb..Sam bai son abinda zaisa yayi risking life din child dinshi amma baby is trying to be stubborn..
Saida suka sake tsayawa a chicken republic ya sai mata burger da pizza kmr yanda ta lissafa mai snn suka kama hanyan gida…har yanxu bai dena godema Allah kan such a very huge blessing da yayi mashi ba…sai nanata Alhamdulillah yakeyi yanajin tsantsar farin ciki na sake ratsa kowace kafa ta jikinshi.
Umma suna gama waya da Taheer ta nufi dakin ummi da saurinta…sukaci karo da ummin tana Shirin fitowa parlon itama..saura kadan umma ta bugeta sai Kuma tayi saurin ja da baya..she’s very happy that bata lurada ummin ba saida suka kusa bugan juna…ummi na dubanta tace”lfy kike kuwa Aisha..tunanin me kikeyi haka har kika kusa kaini kasa baki saniba”…umma ta saki dariya jin abinda ummin ta fada..wai ta kusa kaita kasa…ta kamo hannayen ummi tareda rikesu gam cikin nata…fuskanta dauke da farin cikin daya mamayeta tace”Alhamdulillah Yaya mun kusa samun karuwa..jikarki dai cikine da ita”…ummi ta dan tabe baki kafin tace”jikata Kuma Aisha..wacce jikar tawa daga ciki”…da sauri umma tace”Yaya wace jika kike daita mai aure Wanda ta wuce Layla..yanxun Taheer ya kirani yake fadamin she is two months pregnant”…wani irin sandarewa ummi tayi a wurin baki a bude…tsananin mamaki da Kuma farin ciki da zumudi suka baibayeta lokaci guda…bawai tana mamaki da ikon Allah bane..aah kawai dai tana mamakin yanda basu taba kawo Layla zata samu ciki yanxu ba Kuma sai gashi Allah ya kawo…a hankali ta cire hanun umma dake cikin nata…sai ta durkusa nn kasa itama tayi sujoodushshukhoor…bayan ta gamata dago tana duba umma cikeda tsantsar farin ciki tace”Allah mungode maka..Allah Alhamdulillah..kai wnn kyakykyawan albishir ne Aisha..Allah ya zaunar da cikin nn lfy Allah rabasu lfy..kema da kika fada mn Allah ya biya maki bukatunki duniya da lahira..Allah mun gode maka”…tana gama mgn Kuma sai tayi hugging umma tana kokarin maida hawayen farin ciki dake kokarin zubo Mata..bata taba tunanin Layla na iya samun ciki nan kusa ba..Ashe akwai ranar da zatazo ta riski wnn abun farin cikin..Ashe akwai ranarda zataga gudan jinin Taheer..her only son…kai Allah abun godia….sun dauki tsawon lokaci rungume da juna kafin suyi breaking hug din…still ummi na dariya tace”Ashe akwai rabo a tsakanin yaran nn shiyasa duk yanda nayi kar aurensu ya yiwu sai da akayi..kice dana zura jiki ma karshenta wnn rabon sai ya kasheni kuma snn ayi bikin..Allah mun gode maka”…umma itama nata murmushi tace”wlh fa rabone Yaya..Allah ya nuna mana lokacin haihuwarta lfy..Allah Kuma ya rabasu lfy”…ummi ta amsa da ameen..cikin ranta tana tunanin da kyar idan ba dauko Layla zatayi ta dawo da ita nn gabanta ta ringa kulawa da ita ba..gani takeyi Taheer Sam bai San yanda zai na kula da ita da kuma bayn cikin dake jikinta ba.(Hajia Ummi badai karfin hali ba😂)
Suna karasawa gida Layla ta baje kayan daya siyo mata a nn parlor ta fara cin kayanta…Taheer yana daga zaune gefe yana kallonta with adoration..kawai yana imagining ta Haifa mashi very cute baby kmrta..he just can’t wait for this day.. Allah ya bashi tsawon rai da zaiyi witnessing wnn rana…Kiran sallah da akai ne ya tasheshi a wurin..ya shiga bathroom ya dauro alwala snn ya tafi masallaci.+
Lokacin da ya dawo bai sameta a parlon ba sai ya wuce zuwa dakinta..tana zaune kan sallaya itama ta idar da sallah knn ya shigo dakin..ya karasa ciki ya zauna yana kallon yanda take addu’a..Saida ta gama ya tayata shafawa snn ta mike daga inda take tareda maida sallaya ta ajiye inda yake..ta cire hijab din jikinta shima ta ajiye..ya rage daga ita sai kayan baccin da tasa…Taheer ya Mika Mata hannunshi ta kama snn ya zaunar da ita kusa dashi..ya dora hannunshi kan cikinta..idanunshi kuma na kallon fuskan ta yace”har kin koshi da abincin?..”a hankali ta daga kanta alaman ta koshi…ya sake janyota jikinshi kafin yace”kin tabbata kin koshi baby..ban so kina barin babyna da yunwa ne”…ta murguda mai baki tareda cire hannunshi daga kan cikin nata tace mai”ni ka kyaleni”..tana gama mgnr Kuma ta juya tareda kwanciya kan gadon… Taheer ya matso ta sosae yana cewa”Hey ki ringa bi a hankali fa kar wnn juyin da kike yayi affecting babyna”…a fusace ta sake mikewa zaune..ta shiga tureshi har ta fara hawaye tana cewa”leave me alone..ai dama kafi son cikinka dani..nima ka kyaleni”…ta juya zata koma ta kwanta Taheer ya matseta a jikinshi gam..Allah ya sani har cikin ranshi yakejin wnn juye juyen da takeyi gani yake kmr idan tayi kwakkwaran motsi wani abu zai samu babynshi…a hankali ya shiga shafa kanta yana cewa”baby am sorry..pardon my manners kinji..I love you both..you two are my family so ina sonku equal”…yana rufe baki tace”Allah kafi son cikin nn a kaina..gashi nn tun yanxu ka fara dena damuwa dani”…Taheer ya dafa goshi kafin yace mata”na fada maki duk ku biyun are my babies..ki dena wnn kukan pls”..ba musu ta share hawayenta..shi kuma yaja dogon hancinta yana murmushi yace”that’s my good girl”
Washegari sukayi Shirin fita tun safe..shi zaije Clinic ita Kuma zataje school..Allah ya sani ji yake kmr ya hanata zuwa makarantan nn..gani yake kmr idan tasha wahala wani abu zai samu cikinshi..yasan yanxu yana cewa ta hakura da zuwa school ballo ma kanshi ruwa zaiyi..don idan ta fara kuka har sai ya gaji da lallashi zata hakura…a haka ya gama shiryata da kanshi..duk yanda taso ya barta tayi Shirin da kanta kin yadda yayi..ko breakfast ma a waje ya siyo musu don baiso tana yin aiki mai yawa sbd babynshi…bayan ya sa mata Hijab dinta ya dauka hand bag dinta snn ya kama hanunta suka fita…ya bude mota ya sata ciki snn shima ya zagaya ya shiga ya tada motan suka tafi…Saida suka fara tafiya snn yace”baby ba wani abun da kikeso?..”ta daga kanta kawai don ta gaji da bashi wnn amsan..tunda garin Allah ya waye yake tambayanta Kuma tace mai batason komai…shima sai yayi shiru da mgnr ganin yanda ta daure fuska..yasan idan ya matsa zatace ai dama yafison cikinshi akanta..shi bai taba ganin rigimammiya irin baby ba wlh..
Bayan sun isa school din yayi parking..sai ya juya yana facing dinta ya kamo hanunta ya rike snn yace Mata”Kun tabbata ba abinda kukeso koh”…Layla na dubanshi da alamar tambaya tace”Ni da wa Kuma?..”Saida ya saki murmushi snn yayi pointing chest dinta yace”this baby”..sai Kuma ya sake pointing cikinta yace”and this baby”…ta tura baki tana hararanshi tace”ai saidai ku nemi wani sunan kuma badai baby ba wlh”…Taheer ya wara idanu still smiling yace Mata”why..ba babyna bace itama?..tace”to nidai baka isa ka kirata da sunan da kake kirana dashi ba..itama kuma bata isa tace zata kiraka da daddy ba”.. ta karasa mgnr tareda murguda mai dan bakinta…Saida ya lumshe ido yayi kissing bakin snn yace”itama fa ‘yata ce baby..dole zan kirata da baby mana..she is your younger sister”…yana rufe baki tace”she is not my younger sister”…still Taheer na murmushi yace”why..kema ba ‘yata bace”…tace”ka taba ganin inda uba ya auri ‘yarshi ne”…yace mata”of course ba gashi kin gani a kanmu ba..you are my baby..itama kuma she’s my baby”… Layla bata san lokacinda murmushi ya subuce Mata ba jin abinda ya fada…ta danja gemunshi dake dab da face dinta tace”haka kawai ka gama rainona wai kuma daga baya  kazo kace zaka aureni..ni ban taba ganin inda akayi haka ba”…yace”kuma tun Ina rainon naki Allah ya dora min sonki ba..Ina sonki tun bakisan waye ke ba..gashi kuma yanxu na gama rainonki zan fara rainon sister dinki”…tadan harareshi snn tace”nifa she’s not my sister..she is my kid..kuma na fada maka baka isa kace zaka kirata da baby ba..wnn sunana ne ni kadai”…Saida ya dora hannunshi kan cikinta kafin yace”baby sbd me wai..ba dai kishi zakiyi da itaba..kinsan dai ita bazai taba yiwuwa inzo ince Ina sonta daga baya ba”…Layla ta saki dariya tana cewa”to wa ya sani daddy..ni din ma ai ba wanda ya taba tunanin zakace kana son nawa kuma ka fada”…tana rufe baki yace”ai ita she’s my blood”…tace”umhhh su blood manya..nidai yanxu kar barni in tafi kar inyi missing class”…yayi kissing goshinta snn yace”you can go..amma da kinji kinason cin wani abu just give me a call zan bar duk me nakeyi in kawo maki  kinji”…tana murmushi ta daga mai kai tana cewa”toh”…shi Kuma ya shiga binta da kallo fuska daukeda murmushi har ta fita daga motan..saida ta bacema ganinshi snn ya tada motan shima ya tafi.
STORY CONTINUES BELOW
A bangaren Ummi da Umma kuwa farin ciki baa mgn..tun a jiya ummi ta kira Nafee da kanta take sanar da ita lbrin cikin…ita kanta tayi farin ciki fiyeda tunanin mai karatu..Allah ya sani tana masifar son union din Layla da Taheer..kuma samun karuwa daga garesu ba karamin karfafa zumunchi dake tsakaninsu zaiyi ba…bayan Nafee ummi duk Saida ta kira duk Wanda take ganin sun Dace su San da mgnr cikin ta fada musu..she’s over excited zata samu jika from her only son..da kuma grand child dinta data raineta tamkar ‘yarta.
Wajen karfe 10 ta shiga kiran wayan Taheer..lokacin yana office dinshi yana duba outpatients Kiran nata ya shigo…baiyi picking ba Saida ya sallami patient dake gabanshi snn ya kirata back..Yana shiga unmi tayi picking..Taheer yace mata”Ina kwana ummi”..tace”lfy qlou Taheer ya aikin”…yace”Alhamdulillah ummi”..tace”Congratulations naji good news a wajen Aisha..Allah ya raya manashi Allah ya kawo manashi lfy”…cikeda farin ciki yace”Ameen Ameen Ummi”…ummi Kuma tace”yanxu Ina Laylan take”…yace”tana school”…tace”to idan ka daukota daga school din ka kawota nan gida Ina son ganinta”…yace”ba matsala InshaAllah zan kawota”..daga nn sukayi sallama..
Ita Kam Hajia Layla tana shiga class dinsu taji ana announcing Lecturer din da zai shigo musu yanxu yace suyi hakuri bazai samu zuwaba..amma zaiyi fixing wani time din…ana fadan haka mutane suka fara fita daga class din..kowa Yana tafiya sabgar gabanshi…ita kuwa Layla karasawa tayi inda Hanna ke zaune itama ta zauna..tana dubanta cikeda tsokana tace”sannu mai ciki”.. Hanna ta galla Mata harara itama tace”masu ciki dai..ko kina tunanin duk boye boyenki ban gane kinada ciki bane”…Layla tace”gsky kinada sa ido..to ni kaina ban San da cikin ba sai jiya..haka kawai daddy ya daukeni mukaje clinic akayi test sai gashi har two months”…Hanna na dariya tace”Ni dama wlh naga alama..kinga yanxu sai ki denamin iskanchi kema gashi nn kin gamu..gara ma ni yanxu wata na 6 nake ke kuwa yanxu ma zaki fara”…Layla ta girgiza kai kawai kafin tace”amma nifa bana rashin lfy..ko zazzabi ban tabayi ba wlh..saidai kwadayi da Kuma bacci shima ba sosae ba”…Hanna tace”aikam Allah ya taimakeki don laulayi bashida dadi kwata kwata..yanxu zuwa next session duk mun zama mommies..oh I can’t wait”…dariya Layla tayi sosae kafin tace”gsky Hanna bakida kunya..wato har wani lissafi ma kike”…tana rufe baki Hanna tace”Kai kinsan dadin ‘da kuwa..Tabb ai wlh ni na matsu ma in haihu ko don in ringa kallon ‘dana ko ‘yata inajin dadi..ai haihuwa tayi a rayuwa..in inada ‘da ko miji ne ya batamin rai banjin haushi..ina kallon ‘dana zanji duk damuwana ta yaye..Allah kada ka jarabcemu da rashin haihuwa alfarmar Annabi da Alqur’ani”…Layla na murmushi tace”Ameen Ya Allah”…sai Kuma ta fara tunanin farin cikin data gani tattareda Taheer jiya..ta tuna yanda ya ringa hawaye yana maganganu kmr mara hankali..mgnr Hanna gsky ne..haihuwa tayi..Hakika duk Wanda Allah ya jarabceshi da rashin haihuwa Yana ganin babban jarabawa a rayuwarshi..Allah kayi mana tsari da jarabtar rashin haihuwa..ubangiji ka azurtamu da ‘ya’yaye na gari ba don halayen mu ba..”
Shiko Taheer yana clinic amma daidai da second daya hankalinshi bai bar kanta ba..bini bini ya kirata a waya”baby are you alright..kina bukatan wani abu..ba inda ke maki ciwo..ki kulamin da kanki da my little one plss”…Layla har Saida ta gaji da bashi amsoshin wdan nn tambayoyin..daga safe zuwa yanxu ya kirata kusan sau 20 Kuma duk mgn dayace yaketa nanata Mata har ta gaji da daukan wayan nashi ma..
Tana gama lectures ta kirashi don ta fada mai ta gama sai kawai yace mata ai yana cikin school dinma tun dazu yana jiranta…haka ta nufi inda tasan zata sameshi tana mamaki..ko wa ya barowa aikin nashi oho.
Tana karasaw inda yake dama already ya fito ya bude mota..yana tsaye wurin ta karaso tana kokarin shiga motan kawai taji ya sanyata a jikinshi…ta zame jikinta da sauri tana kalle kalle tace”haba daddy..yanxu idan wani ya ganmu fa”…Saida ya sata cikin mota snn yace”I don’t care..koma wane zai gani ya gani..you are my wife afterall..so inada right din inyi hugging dinki ko a inane”..ya rufe motan snn shima ya zaga ya shiga..maimakon ya tada motan su tafi sai ya sake matsowa jikinta a hankali ya dage hijab dinta da Kuma rigar jikinta..cikinta dake nn a shafe ya bayyana…ya lumshe idanu snn ya dora hannayenshi kan cikin..Saida ya manna kiss a wurin snn yace”your Papa missed you alot”…Layla dai binshi kawai takeyi da ido..har yanzu bata dena mamakin wnn kauna da yakema cikin nn ba…shi kuwa yana gamawa sai ya koma seat dinshi snn ya tada motan suka tafi…tadan daure fuska tana kallonshi tace”shine ni bakace kayi missing dina ba sai cikinka koh”…yace”shiyasa na farayi maki naki tun a waje sbd nasan zakice nayi son kai amma duk da haka ban tsira ba”…ta murguda baki tace”ai ni bakace kayi missing dinaba sai ita..I mean sai shi”…Saida yadan juyo ya kalleta fuska daukeda murmushi yace”ai na fada maki InshaAllah it’s a girl..so kima dena alakanta min ita da namiji”…yana rufe baki tace”aiko in Allah ya yadda namiji zan Haifa..sai muga ta tsiya”…Taheer ya fashe da dariya yana cewa”ko namijin nema ai ba kinshi zanyiba baby..I will love them equally..kawai dai nafiso in fara da mace ne sbd tana fara girma inyi mata aure in samu jikoki..and I want to spoil her kmr yanda nayi spoiling dinki..shknn”…murguda bakin nata ta sakeyi tareda juyar da kanta tana kallon titi…shi kuma yayi murmushi Yana cigaba da driving dinshi.
Suna isa kofar gidan yayi horn aka bude mashi gate snn ya shiga ciki…ya samu wuri yayi parking snn ya fito..ya zaga ya fitoda ita itama snn suka nufi cikin gidan…suna shiga parlor ummi ta taso da sauri ta rungume Layla a jikinta tanata sambada mata albarka…Taheer ya karasa ciki ta zauna kusa da umma yana murmushi…itama ummi ta kama hanun Laylan suka zauna snn Taheer ya gaishesu..itama Laylan ta gaishesu for the very first time taji kunyansu takeji duka..yanxu shknn da ance tanada ciki kowa yasan yanda akayi aka samu cikin..Gosh wnn abun kunya da yawa yake..ummi na duban Taheer tace”sai ka biyota da kayanta ko zuwa gobe ne”…Taheer ya buda ido sosae kafin yace”ban gane in biyota da kayanta ba ummi..me zatayi da Kaya a nn gidan kuma”?..”ummi tace”ai ba komawa zatayi ba Taheer..zata zauna a nan don mu ringa kulawa da ita da abin dake cikinta sosae..idanma an barka da ita ba wani iya kula dasu zakayi sosae ba”…tana rufe baki Taheer ya shiga girgiza kai yana cewa”ummi kar kimin haka dn Allah..ya zakice bazan iya kula dasu ba..ni likita nefa ummi nasan duk abinda ya kamaceta da Wanda bai kamaceta ba..dn girman Allah ummi kar kice zaki rabani da matata nidai zan iya kula dasu wlh”…shiru ummi tayi tana kallon wnn magiya da yake Mata haka..kafin tayi mgn umma tace”don Allah Yaya kiyi hakuri ki kyaleshi kawai ya kulada matarsa..nasan zai iya wlh..ai shi ba yaro bane snn yanada ilimin da zai iya kulawa dasu sosae..ki barsu suje inyaso idan cikin ya tsufa sosae a ta dawo nn din sbd haihuwa koh”…ummi dai har yanxu shiru tana tunani cikin ranta..gani tayi mgnr da umma ta fada gsky ne..sai tace”shknn..amma duk take bukatan wani abu sai ka Kira ka fada..shi sha’anin mai ciki bada wasa ake daukansa ba”…Taheer ya sauke ajiyan zuciya a boye before yace”yawwa ummina ko kefa.. thank you so much”…harara ummi ta watsa mai tana cewa”bakada kunya wlh..Ni ban san time din da ka lalace haka ba”..dukkaninsu suka sa dariya.
Basu suka bar gidan ba sai around 10..suna komawa gida Kuma kowa yayi shirin bacci snn suka kwanta tunda already sunci abinci a can kafin su taho…suna kwanciyan Kuma bacci yayi gaba da Layla..shi kuwa Saida ya dade yana nn zaune yana kallonta yana Kuma mgn da cikinta kmr tababbe kafin shima baccin ya silola yazo yayi gaba dashi.
Haka rayuwa yacigaba da tafiya Layla na samun kulawa sosae..ba bangaren su Ummi ba..ba kuma ga bangaren daddyn nata ba..wasu lokutan har tausayi yake bata yanda taga Yana kaunar cikin nn..sai yasa cikin a gaba yaita surutunshi shi kadai yana murmushi shi bai yadda ba yana mgn da babynshi…kullum zai kaita school snn zai maidata gida…duk take sha’awan cin wani abu kuwa tana kiranshi duk inda yake Kuma duk abinda yake haka zai bari yazo ya kawo Mata…suna rainon cikinsu sosae Kuma bai hanata karatunta tunda ba wani laulayi takeyi sosae ba..+
Kayan babies Kam Taheer na siyansu tamkar bai San zafin neman kudi ba…duk abun da ya gani yai mishi kyau sai yayi order indai abindaya danganci yara ne…banda Wanda kusan kullum sai ya dauketa sunje shopping Kuma duk siyayyan na kayan babies ne…duk abinda zai siya kuma na Mata yake dauka…Layla tayi tayi dashi akan su ringa daukan unisex yanda ko ba mace ta Haifa ba zasuyi amfani dashi amma inaa…kullum cewa yake shi jikinshi na bashi mace zata Haifa dukda scanning din da sukai guda biyu duk namiji yake nunawa..
Lokacin da cikin nata ya isa antenal kuwa da kanshi yakeyi Mata komai…duk wasu tests da akeyi yana Mata…har su urinalysis Yana zuwa da Combi9 dinshi har gida yayi Mata…sauran tests din Kuma irinsu PCV..VDRL da bazasu yiwu a gida ba sai ya dauketa suje clinic dinshi ayi Mata…Layla dai na ganin tsabar soyayya da kulawa a wurin Taheer..at times har tunani take kilan tana haihuwa zai dena sonta ya dena kulawa da ita..sbd yanda taga yake bala’in son cikin nn abin har mamaki yake bata..
A bangaren su Ummi ma Kam baa barsu a baya wajen kulawa da ita ba…time to time ummi zatayi Mata girki irin na gargajiya Wanda tasan mai ciki zataso snn suje har gidan su Kai Mata..watarana Kuma su aika driver yakai ko Kuma Taheer din yaje ya amsan Mata…babu abinda zatace ma Allah daya wuce Alhamdulillah.. kullum cikin godiyan Allah take for such a blessing…fatanta Allah ya sauketa lfy itama taga me zata Haifa..tanaso taga babyn da ita zaiyi kama koda babanshi..
Lokacinda Hanna ta haihu cikin Layla nada watanni 5 ciff a duniya…zuwa lokacin Kuma cikin nata ya fito sosae…haka sukasha suna da katoton cikinta abunta…yarinya taci sunan mum din mahaifinta Aisha..zasuna kiranta da Hanan…
Bayan haihuwan nata da kadan Kuma sukayi exams na second semester…wnn karon zasuyi hutun 4 weeks kafin su juya another session…haka rayuwa yacigaba da tafiya musu har zuwa yanxu da cikinta ke wata takwas…yana shiga na takwas din dama ummi ta dage kan lallai sai Taheer ya maidota gida don ba iya kulawa da ita zaiyi ba..haka ya hada kayanta da nashi snn suka tattara suka koma gidan…shima hankalinshi zaifi kwanciya idan tana tare dasu don sau tari idan zaije clinic hankalinshi bai kwanciya ya barta ita kadai a gida..yanxu kuwa ko bai nan yasan zasu kula mai da ita sosae.
Dukda suna gidan kuma bai fasa kulawa da itan ba..duk abubuwan da yake Mata a baya ba Wanda ya bari..ko abinci indai yana gida saidai ya bata a baki..wasu lokutan har kin zuwa aiki yakeyi sbd ita..daidai da wanka saiya taimaka mata tun ummi na fada har ta hakura ta zuba musu idanu kawai…yanda yake rawan jiki kan cikin nn har mamaki yake bata..sai kace a kanshi zaa fara haihuwa..ita kuwa umma sam bata mamaki don ta riga tasan irin kaunar da Taheer din kema Layla..dn haka dolene tasan yaso cikin nn fiyeda komai…
Nafeesa kam har yanxu bata samu zuwa Abuja ba sbd karatun yara..tanata so tazo ko kwana biyu ne suyi sbd ta samu taga Layla amma umma tace suyi zamansu kawai..idan Allah ya sauketa lfy sai suzo..saidai suna wayan kusan kullum da ita…haka su Al’ameen ma duk sun kagu ta haihu suzo suga babynsu…
Yau Saturday da wuri Taheer ya baro clinic zuwa gida..tun da ta fita bai samu yin waya da itaba as yanata Kiran wayan nata bata answering..gaba daya sai hankalinshi ya tashi don yana tunanin ko wani abun ne ya sameta amma daya Kira umma sai ta tabbatar mai da cewa lfy Lou take saidai tun dazu tana daki tanata bacci…dukda haka shidai baiji hankalinshi ya kwanta ba don haka ya dawo gidan don yaga hakinda take ciki.
STORY CONTINUES BELOW
Su ummi suna parlor suna duba uban kayan babies da sukai order tun last two weeks shine yanxu akayi delivering dinsu…ya gaisa dasu a gurguje snn ya wuce zuwa dakinta don gaba daya hankalinshi na kanta…tana zaune tsakiyar gado ta dora kanta a kan kafafunta tana rere kuka a hankali…da sauri ya karasa gareta hankali a matukar tashe yace”baby what is it?..bakida lfy ne?..”Layla banza tayi dashi tana ci gaba da kukanta…yasa hannunshi ya dagata cak snn ya zauna gefen gadon tareda dorata a kan cinyanshi…ya riko face dinta da hannayenshi yace mata”baby please..what is wrong with you”…a hankali ta dora tiny hands dinta kan nashi tace”daddy am tired plss..ka cire mn cikin nn don Allah..wlh na gaji daddy kullum bana samu inyi bacci..bana iya yima kaina komai dubi fa ko zip din rigana kasa zugewa nayi..nidai na gaji wlh”…Taheer lumshe ido yayi tareda sauke nannauyan ajiyan zuciya..duk a tunaninshi ko batajin dadi ne…ya dora kanta a chest dinshi yana shafa gashinta har yanxu Kuma idanunshi na rufe yace mata”baby ba mun gama da mgnr nn ba..na fada maki saura kadan ki Kara hakuri kinji..nasan kina kokari amma dn Allah ki kara akan Wanda kike dashi..edd dinki na cika zanyi maki Cs in ciro abuna da kaina so ki dan kara hakuri kinji koh”…ta sake yin luf da kanta dake kirjinshi tace”daddy kullum sai yaita kicking dina yana hanani yin bacci..ko juyawa yayi sai naji zafi wlh”…ta karasa mgnr hadda su guntun hawaye a idonta…Taheer ya bude idanunshi dake rufe ya dago kan nata yana kallonta a hankali yace mata”kiyi hakuri kinji..lfy zaku rabu InshaAllah”…yana gama mgnr ya kama zip din maternity gown dake jikinta ya zuge Mata shi snn ya sake dago face dinta yana kallo yace”kinci abinci”…a hankali ta girgiza kanta…ya dora hannu kan cikinta a hankali yace”to me zakici”?…”ta wani kwabe fuska kmr zatasa kuka tace”Fish”…Taheer ya dan wara idanu yana kallonta kafin yace”kifi dai baby?..”still fuskanta a kwabe ta daga mishi Kai…Taheer ya sauke numfashi before yace”alright bari in fita yanxun nn in samo maki shi”…da sauri tace mai”daddy ni zan bika”…yai shiru yana kallonta kmr bazai ce komai ba sai Kuma yace Mata”to tashi muje”…ba musu ta mike tsaye shima ya mike..ya dauko hijab dinta ya sa mata snn ya kama hanunta suka fita daga dakin..
Su ummi sun gama dudduba kayansu har sun maidasu daki…ummi na ganin Layla da hijabi a jiki tace”Kai badai wani wajen zaka kaita ba koh”…yace”kifi zamuje siyowa ummi”…ummi tace”wane irin kifi kuma ni Maryama..da tsohon cikin zaka wani kwasheta kuje siyan kifi”…Layla na turo baki tace”ummi nifa so nake in bishi..na gaji da zaman wuri daya”…daga haka ummi bata sake mgn ba…umma ce tace”to yanxu ta Ina zaku fara neman wani kifi Taheer”..yace”to umma tace shi takeso..dole haka zamu fita mu nema nasan InshaAllah bazamu rasa ba”…umma tace”Ay shknn sai Kun dawo”…yace”Ameen”snn suka fita suka tafi.
Saida sukai yawo sosae don Saida suka fara fita outskirt din Abuja snn Allah ya taimakesu suka samo kifin…tun a hanya ta faraci…
Suna isa wani super market yayi parking snn ya fita daga motan yace mata he’s coming…taci gaba da cin kifinta shi Kuma ya shiga ciki da sauri…sharp sharp ya dauko abinda yake bukata snn yazo ya biya kudin…Yana Shirin fita suka kusa cin karo da Sameera…yaja baya da sauri yana dauke kanshi daga gareta…ita Kuma sai ta saki dan smile tana cewa”doctor dama ana ganinku”…Taheer yayi mata banza yana kakarin fita daga wurin ta sake Shan gabanshi tace”dn Allah doctor duk abinda ya faru kayi hakuri..Sharrin shaidan ne wlh amma InshaAllah hakan bazai sake faruwa ba…ka yafemin”…Taheer ya matsu ta gama surutunta ta bashi hanya ya wuce yace”naji..now bani hanya in wuce”…da sauri tace”ai bakace ka yafemin ba doctor”…Taheer ya dafa goshi ganin tana neman bata mai lokaci yace”dn Allah ki bani hanya in wuce..da ban yafe maki ba kinsan baki isa in tsaya ma Ina sauraranki ba..so ki bani hanya in wuce before I loose my temper”
A cikin mota Kam Layla dake cin kifinta taga har yanxu bai fitoba sai ta bude motan ta fita…ita batama san abinda ya tsayar dashi a nn wurin ba…tana sa kai tun ma kafin ta shiga ciki idanunta suka hango Mata shi yana tsaye da Sameera..zuciyarta taji yayi wani irin bugawa da karfi..batasan lokacinda ta saki wayanta dake hannunta ba…lokaci daya Sameera da Taheer suka juyo jin karan faduwan abu a bayansu…daidai lokacin Kuma Layla ta juya tareda barin wurin da sauri kmr zata tashi sama…shima Taheer da saurin yabi bayanta yana kiranta amma batada alaman slowing down…Saida ya dauki wayanta da tayi wurgi dashi nn wurin sai yasa gudu snn ya iya kamo inda take…ya kamo hannunta ya rikeshi da karfi..idanunshi har sunyi jajawur yace mata”baby are you mad..kina haukane zaki fara irin wnn saurin bayan kinsan condition dinki..do you want to harm my child?..”a hankali Layla ta lumshe idanu wasu hawaye masu zafi suka wanke mata fuska..wato shi baima ga girman laifinda ya aikata ba…ta danshi kawai yakeyi..bai damu da ko ita wani abun zai iya samunta ba…kawai sai ta kwace hannunta dake cikin nashi da karfi…kafin yayi yunkurin sake rike hanun nata ta sake juyawa da sauri wnn karon har tana hadawa da dan gudu ta doshi gate din wurin…ya sake binta da gudu yanajin yanda duk taku daya idan tayi jinshi yake har cikin ranshi don baison abinda zaiyi affecting ita ko cikin da yake jikinta…yana karasawa inda take kawai sai yayi hugging dinta gam..bai damu da yanda mutanen wurin keta kallonsu ba…idanunshi har sun ciko da kwalla yace”baby please…ki taimaka min ki dena gudun nn don Allah..mutuwa zanyi idan kika bari wani abu ya samu cikin nn..ki tausaya mn dn Allah..wlh ba abinda kike tunani bane”…ita dai idanunta na rufe ruf tanajin abinda yake fada sai zuciyarta ya sake dagulewa…ta shiga kokawa dashi tanason freeing kanta a hanunshi amma ta kasa…shi Kuma Taheer kawai sai ya dagata ya koma wurin motarshi da ita…duk yanda taketa dukan chest dinshi tana ya ajiyeta bai ajiyetan ba har sai daya karasa inda motar shi take ya sanyata a ciki snn ya zagaya da sauri shima ya shiga snn ya tada motar suka bar wurin.
Ko a hanya Banda kuka ba abinda takeyi Kuma mgnr da yake Mata har yanzu bata bashi amsan ko guda daya ba…a hankali ya gangara gefen titi yayi parking yana kallonta da idanuwanshi dake dab da fitar da kwalla yace mata”baby please..dn Allah kiyi hakuri ki tsaya ki saurareni..wlh ba abinda kike tunani bane..roko na takeyi in yafe mata ni Kuma nace na riga na yafe Mata..dn Allah ki dena kukan nn kinsan condition dinki…banason wani abin ya sameki ko ya samu unborn dina ki dena plsss”..idan ke da kike karatu kin tanka to Layla ma ta tanka…Taheer ya hada kanshi da starring motan yanajin yanda wani mashahurin zafi ke baibaye ko wace kafa ta heart dinshi…a hankali hawayen dake makale a idanunshi tun dazu suka samu damar zubowa a kan fuskanshi…Allah ya sani duk wnn kukan da take..da guje gujen da takeyi gani yake kmr zai iya affecting cikinta…shi kuma baison abinda zai sameta ko ya samu cikin nn kwata kwata..a hankali yasa hannu tareda goge tears din da suka zubo mai snn ya dago fuskan nashi yana kallonta…ya bude baki zaiyi mgn tace mai”na gaji..ka kaini gida in huta”…ba musu ya tada motan suka cigaba da tafiya…saidai gaba daya hankalinshi yana kanta…jin kukan nn nata yakeyi har tsakiyar kwakwawarshi…bai San me zai fada Mata ta yadda dashi ba Kuma..
Suna isa gida ko parking din kirki baiyi ba ta bude motan ta fita da saurinta…Taheer ya bita da kallo har ta shiga ciki…da kyar ya bude motan shima ya fita ya nufi entrance din gidan.
Umma ce kadai a parlor itama tana kokarin shiga kitchen sai ga Layla ta shigo a sukwane ta wuce dakinta tana sharan hawaye…umma ta bita da kallon mamaki ganin yanda take uban sauri ko nauyin jikinta bataji..sai kace ba mai ciki ba…ta sake juyawa zata shiga kitchen din sai Kuma ga Taheer ma ya shigo..sai ta dawo cikin parlon tana kallonshi da kyau tace mishi”Kai lfy..meyake faruwa?..”a hankali Taheer ya zauna kan kujera yana sauke numfashi..itama umma ta zauna kusa dashi snn tace”Ina tambayanka kayimin shiru Taheer..baa samu kifin bane ko Yaya?..”ya dago weak and tired eyes dinshi ya dorasu kan umma…murya a raunane yace Mata”Umma fushi takeyi dani..kawai sbd ta ganni da Sameera..Kuma taki tsayawa ta saurari bayanin da nakeso inyi Mata”…umma ta daure fuska snn tace”shine Kai Kuma ka sata a gaba kana Mata kuka ko mene..wai ace yarinya karama kmr Layla ta ringa juyaka Taheer..da girmanka da komai kanaso ka zama solo6iyon namiji wanda kejin tsoron matarshi koh”…tana rufe baki Taheer yace”umma ba haka bane wlh..ni banyi kuka a gabanta ba..Kuma umma ni ba tsoronta nakeji ba kawai ni damuwana kar wani abu ya samesu..kinsan condition din da take ciki baa son tana bacin rai haka..yanda take saurin nn Allah umma sai naji kmr akan zuciyata take tafiya”…baki umma ta tabe kafin tace”ai sai ka bata sarari duk ta gama iskancin nata ta sauko sai kayi mata bayanin tunda yanxu bata sonji”…Taheer na girgiza kai yace”wlh bazan iyaba umma..bazan iya barinta a wnn halin da take ciki ba..idan wani abu ya sameta ko unborn dina fa”…umma bata sake mgn ba Saida ta mike ta kama hanyar kitchen snn tace”ai sai kai tayi..haka kawai ka zauna yarinya karama tana maka iskanci iri iri kuma kana biye mata”..daga haka ta shiga kitchen abinta…shi Kuma Taheer mikewa yayi a hankali ya nufi dakin nata…a zaune ya sameta a gefen gado..tayi tagumi da duk hannayenta tana ta sharar kuka…ya karasa ciki da sauri tareda zaunawa kusa da ita…yasa hannunshi ya cire nata hannayen da tayi tagumi dasu…ya shiga girgiza mata kai murya a raunane yace”baby dn Allah..dn Annabi..kiyi hakuri ki tsaya kiji bayanin da zan miki”..Yana rufe baki Layla tace”ai dama kana sane ka shiga wajen..maybe dama Kun gama hada appointment dinku zaku hadu a wurin..shine ka tafi ka barni inata zaman jiranka a cikin mota”…ta karasa mgnr wasu sabbin hawaye na sake zubowa kan face dinta… Taheer ya kamo face dinta da duk hannayenshi…a hankali ya matsa da nashi fuskan ya hade da nata…yana kallon idanunta dake lumshe yace”yanxu baby zargin da kikemn knn..baki yadda dani ba dama”…a fusace ta bude idanunta tana zabga mai harara…ta daddage ta mike daga kusa dashi tana kokarin fita daga dakin ya dawo da ita jikin nashi da sauri…ta shiga dukan chest dinshi tana jujjuya Kanta tana cewa”ni ka sakeni..let go of me right now”…ai bata karasa mgnr ba Taheer ya hade bakinshi da nata…taci gaba da dukanshi tana kokarin kwace bakinta amma Taheer ya kamashi gam kmr magnet…a hankali yasa hannayenshi tareda rungumeta ga jikinshi sosae har yanajin tudun cikinta a jikin nashi…ya makaleta tsaf yanda ko motsin kirki ta kasayi..har yanxu kuma bai cire bakinshi a nata ba..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *