DR TAHEER CHAPTER 12 KARSHE BY UMMU ASHRAF

DR TAHEER CHAPTER 12 KARSHE BY UMMU ASHRAF

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

End

Saura sati daya su Layla suyi arba’in ummi ta turasu porthacourt sukayi sati daya snn suka dawo..bayan sun dawo Kuma ta sake cewa zasuje Kano snn suje Dutse suna dawowa kuma sai su koma gida..amma Sam Taheer bai yadda ba..da taimakon umma suka samu suka lallabata tace idan Layla ta samu hutun makaranta sai suje…daga nan Kuma sai aka fara yi Mata gyaran komawa gidanta..gyara takesha sosae ta ko wanne bangare..ita kanta sai dataji canji a jikinta..

Yau ne zasu koma gidansu..Taheer jin kanshi yake tamkar a sararin samaniya sbd farin ciki..tun safe yake sintiri a part dinsu wai ko ummi zata ce ya dauketa su tafi yanxu amma shiru kakeji..dama tun jiya da aka gama hada kayansu ya dauka ya kai musu can..snn an gyara musu gidan tsaf dawowansu kawai yake jira..

Karfe 5 ya dawo daga clinic..ko part dinshi bai shigaba ya nufi nasu..Yana shiga ummi tace ba yanxu zasu tafi ba sai after magrib..haka nan ya hakura ya koma part dinshi yayi wanka snn ya tafi masjid..bai dawo gidan ba Saida yayi sallahn Ishaa..yana komawa Kuma bayan sun gama sallama ya daukeki Nawal ya fita waje..su ummi suka rakosu har mota snn suka tafi..ko a hanya yana driving yana juyawa Yana kallonsu time to time..ya kagara su isa gida sbd farin cikin da yake ciki…Saida ya tsaya ya siya musu kaji ya hada da soft drinks snn suka tafi..Layla dai sai kallon yanda yake nishadi kawai take..tasan yau kam dole taji a jikinta..dama tunda taga ya siya kaji tasan babu sauki sai na Allah knn..har yanxu bata manta first night dinsu ba.. exactly kmr haka sun dawo daga gida..saidai wnn karon su uku ne a madadin su biyu…

A takaice dai wnn daren Layla ta tabbatar da babu wata macen da Taheer zaiso a duniyar nn bayan ita..ya gwada Mata soyayya ne fiyeda tunaninta..ta Kuma tabbatar da missing dinta da take cewa yayi ba karya bane da gaske yake..indeed wnn daren yana daga cikin daren da bazasu taba mantawa dashi ba har abada.

Shima a nashi bangaren bazai taba mancewa da wnn daren ba..bazai taba manta irin care din data bashi a wnn daren ba..shi yasan har ya mutu bazai taba samun mace kmr Layla ba..ko ya samu dinma yasan bazai taba son wata diya mace kmr yanda yake sonta ba..indeed she is a blessing and darling..

Bayan Shekara uku…

Da gudu Nawal ta fito daga dakin Layla zuwa dakin babanta..sukaci karo dashi a daidai kofa sukaci karo dashi shima zai fito..ya dagata sama yana kallon gashin kanta dake a barbaje kafin yace”Hey sweetheart gudun me kikeyi haka..what’s wrong,?..”Nawal ta kwabe fuska kmr zatasa kuka tace”Papa talk to maama plss..banaso tamin combing gashina I wat you to do it..ita nata da zafi takeyi”…Taheer na murmushi yaja kumatunta kafin yayi mgn Layla ta karaso inda suke..ta daure fuska kwarai tana hararansu kafin ta tsaida idonta kan Nawal dake hannunshi tace”ki sauko in taje maki gashin nn ko inci ubanki wlh..kullum sai kin bata min lokaci kinsa nayi lattin tafiya school kikejin dadi.. stupid girl kawai”…Layla na rufe bakinta Nawal ta fashe da kuka..Taheer ya rungumeta da sauri yana shafa kanta yake cewa”come on sweetheart stop crying okay..ni zan taje maki gashin da kaina kinji..just stop crying I promise bazan bari maama tayi maki da zafi ba”…tana cigaba da kukan tace”she called me a stupid girl”…Taheer ya dago face dinta yana kallonta yace”you are not stupid my dear..you are my good girl..kar maganan maama ya bata maki rai kinji..she didn’t meant it..wasa takeyi maki okay”…Yana rufe bakinshi Layla tayi wurgi da comb dake hannunta snn ta juya ta bar musu wurin..Taheer ya bita da kallo yana sauke ajiyan zuciya yasan rigima ne zai Shashi a wurinta itama..yanxu ya gama lallashin Nawal snn yaje itama ya lallasheta..oh Allah shikam babies din nn na bashi headache wlh..rigiman Nawal na daban ne ga Kuma Layla itama da har yanxu bata dena yin nata ba..kullum haka suke cikin rigima abu kadan Layla zatace ai dama yafi son Nawal akanta…jin Nawal na kokarin sauka daga hannunshi sai ya dawo dashi tunaninshi…ya koma dakinshi tareda dorata kan mirror snn ya dauko comb da Layla ta yarda a kasa kafin ya fara taje Mata gashin yanayi a hankali exactly yanda yakema Layla…wani murmushi yayi escaping lips dinshi daya tuna haka itama tana kuka zatazo tace mishi ita ba ummi ne zata taje Mata Kai ba shine..haka shi Kuma zai taje matan yanayi a hankali don kar taji zafin..sai Kuma wani murmushin ya sake kwace mai daya ga a yanda ta tafi ta barsu..shi mamaki take bashi da take kishi da Nawal..kumafa itama har yanzu ba iya taje kan nata takeyi da kanta ba duk gashinta yake a tsefe shike taje mata…amma yanxu yasan ba karamin daru zaasha ba kan zai tajema Nawal…Yana cikin taje Mata gashin at thesame time yana tunani yana Kuma sakin murmushi time to time kawai sai yaji Nawal tace”Papa jiya auntynmu Saida ta fada sunanka a school”…Taheer yadan wara idanu yace”Really..wane sunan nawa ta fada”…Saida ta wani tabe baki kmr babba snn tayi kasa murya tace”cewa tayi Jakada..Ni Kuma nace Mata karta sake fadan sunan Papa na”.. murmushi kawai yayi yana girgiza Kai..daidai lokacin Kuma ya gama taje Mata gashin ya dauketa suka fita yana ce mata”bai kamata ki fada Mata haka ba sweetheart ai she’s your teacher so kota fada sunana it’s nothing”…daidai nn suka karasa dinning yaja Mata kujera ta zauna snn shima ya zauna kuda da ita…Layla Kuma ta fito daga kitchen rikeda tea flask ta ajiyeshi nn dinning din snn taja kujera ta zauna…Taheer yadan saci kallonta yaga ta daure fuska tamau..sai ya maida kallonshi ga Nawal da tace”Papa knn sai in barta tayita fadan sunan babana”…Taheer ya kamo hannunta yace”come on sweetheart na fada maki it’s nothing.. beside duk sunanmu ne Jakadan ai har mom dinki ma haka ake kiranta a school don haka kar in sakeji kin fadama auntynku haka kinji”…a hankali ta daga mishi Kai…ita Kuma Layla tabe baki tayi kafin ta mike ta fara serving dinsu…bayan ta gama saita koma ta zauna..ita Kuma Nawal ta dauki nata abincin ta juye cikin nashi snn ta tashi daga seat dinta ta hau kan cinyanshi ta zauna..tana kallonshi da murmushi tace”Papa ni tare dakai nake sonci”…Taheer dake kallon tsananin Kamar da takeyi dashi yaja hancinta snn yace”alright sweetheart”…daga haka sai ya shiga hada musu tea…Nawal Kuma tayi shiru tana kallonshi can Kuma sai tace”daddy auntyn namu fa cewa tayi Taheer Jakada..wai ni daughter din Dr.Taheer ne”…Saida ya gama hada tea din da yake snn yace mata”eh mana baby ai na fada maki duk sunanmu ne..kinga ni Taheer Jakada…mom dinki Maryam Taheer Jakada kema Kuma”…tun kafin ya karasa da saurinta tace”Aisha Taheer Jakada”…sai yasa dariya tareda Mika Mata hannunshi Yana cewa”give me five”…itama tana dariya ta Mika mashi hannunta suka tafa…basuyi aune ba kawai sai jin karan kujera sukaji Layla ta mike tareda bar musu dinning din…lokaci daya hankalinsu ya dawo gareta sai suka bita da kallo…da sauri Taheer ya mike tareda ajiye Nawal kan kujera yace mata”sweetheart kici abincinki kinji..am coming back right away bari inyi mgn da mom dinki”…yana gama fadan haka ya haura sama zuwa dakin Layla…a bakin kofa yaci karo daita ta sanyo hijab ta dauko hand bag dinta da car key zata fita…sai ya dauketa cak ya maidata cikin dakin…tayi wani irin tsalle ta diro daga hanunshi…shi kuma ya kamata suka zauna yana kallonta da kyau yace Mata”baby yanxu wnn tsallen da kikeyi idan yayi affecting babyn cikinmu Kuma fa”…yana rufe baki ta shiga kokarin mikewa ta bar wurin amma ya riketa gam…sai kawai ya rungumeta yana shafa bayanta a hankali yace”baby am so sorry plss..nida sweetheart bamu kyauta ba amma kiyi mana hakuri kinji..plss kar ki bari wnn tsallen da kike yayi affecting babyna tun baizo duniya ba”…banza tayi dashi tana cigaba da kokarin kwatan kanta…shi Kuma ya matseta sosae ya sake cewa”baby I said we are sorry Mana..ya kamata ki hakura”…yana rufe baki a fusace tace”wai laifin me kukayi ne kake bani hakuri haka…did you hear me say kunyi min wani abun..kaje kuci gaba da cin abincinku ni am ok”…tana rufe baki kafin ta sake yin wani maganan Taheer ya hade bakinshi da nata ya shiga bata the hottest kiss of her life…ita Kuma tun tana kokarin kwatan kanta har ta hakura tayi lakwas a jikinshi tanajin yanda yayi dominating dinta that ko motsi bata iyawa..gaba daya ya kashe Mata jiki da wnn kiss din nashi..it’s like he’s doing it on purpose…saida ya gaji don kanshi snn yayi pulling out..sai Kuma ya sake rungumeta gam a jikinshi yana sauke numfashi…murya can kasa yace” baby you know I love you right?..and I will continue loving you till my last breath..so kiyi hakuri muje ki karasa breakfast dinki plss”…a hankali ta janye jikinta daga nashi..shima ya dago weak eyes dinshi yana kallonta..saita dauke nata da sauri don bazata iya cigaba da kallonsu ba..a hankali ta mike tsaye shima ya mike da sauri yana dubanta yace”yawwa my baby..muje”…ba musu tayi gaba tana cewa”kuma muna gamawa zan tafi daddy..I don’t want to be late for school”..yace mata”yes muna gamawa zanyi dropping dinki..you don’t have to drive yourself today..I will be your driver”…banza tayi dashi tana ficewa daga dakin shima ya mara Mata baya…suna sauka downstairs Layla ta fara tsayawa cak tana kallon dinning da yake wayam ba Nawal ba kuma abincin da suka tashi suka bari..shima ya karaso tareda tsayawa kusa da ita yana duban dinning din..to Ina Nawal zataje da abinci Kuma…ya ayyana cikin ranshi…motsin da sukaji a kitchen yasa suka nufi kitchen din da sauri…tana kitchen din ta juye duk abincin nasu a wormer da Layla ta ajiye dinning..sai ta sa wormern cikin sink tareda kunna tap ruwa nata zuba a ciki snn ta dauko serving spoon ta shiga juyawa bayan ta taka stool ta mike tsaye a kanshi don tsayinta bai kai sink din ba…a tsawace Layla tace”Nawal”…aiko ta juyo a firgice har stool din da take Kai ya goce..ta fasa wani uban Kara jin zata Fadi kasa…Taheer ya karasa da sauri ya tarota ta Fadi jikinshi…sai ta kankameshi gam tana sake rushewa da kuka..jikinta har shivering yakeyi sbd tsoratan da tayi…Taheer ya shiga jijjigata yana shafa Mata Kai yace”shshshs stop crying sweetheart am here kinji..am right here and ba abinda zai sameki”… itadai kukanta takeyi don har yanxu bata dawo normal ba…Taheer ya maida idonshi kan Layla data sandare a inda take tana kallonsu..ya rausayar da kanshi kafin yace”baby you shouldn’t have shouted at her like this..she is just a child..and bazata iya differentiating right from wrong ba”…yana rufe baki rai a bace Layla tace”shiyasa nake son nuna Mata abinda takeyi din ba daidai bane”..sai ta matso inda yake tana hararan Nawal din tace”come on kin rufe ma mutane baki ko saina fasa bakin..sbd tsabar iskanci ki dauko mana abinci kizo ki tara kan tap sbd bakida hankali koh”…da sauri Taheer yace”haba baby..ba nace ki bari zanyi mata fada da kaina ba”…shima ta maka mai wani harara before tace”dama abinda kake fada knn kullum..da tayi laifi zakace a bari zaka yi mata fada da kanka bayan Kuma ba yin fadan kakeyi ba..shiyasa gashi nn kullum fitinanta karuwa yake Kai Kuma bazaka bari ayi maganinta ba..duk kabi ka lalata ta Kuma wlh nidai ba ruwana da ummi zan hadaka”…tana gama mgn ta juya da sauri ta fice daga kitchen din…Taheer ya ajiye Nawal shima yabi bayanta da sauri…tana kokarin fita daga parlor ya cimmata..ya janyota ciki yana girgiza Mata Kai yace”baby come on..menene abun daukan zafi Kuma”…a fusace tace mishi”ni ba zafi na dauka ba sbd haka ka sakeni in wuce school”…yace”bakiyi breakfast bafa”.. tace”ai baka damu inyi breakfast din ba now let go of my hand”…ya sake riko hannun nata yana kallon cikin idonta yace”Allah baby ni banga abun daukan zafi ba anan..duk kinbi kin koyi fada kema sai kace ummi wlh..duk irin fadan ta kin dauka kema kinayi”…ta dago idanunta ta saukesu kanshi snn tace”is that all you could say?..now let go of my hand plss”…ya makale Mata kafada yace”I won’t..inaso ne kice kin hakura plss..da gaske in kina fadan nn sai naga kmr ummi ce take min fada..kinsan that’s exactly yanda takemin tun kina ‘yar karama… idan kikayi laifi nace kar ayi maki fada zatace ai dama nine ke lalataki”..a hankali Layla ta sake cewa”amma daddy kasan baka kyautawa koh..what if wnn son da kake nuna Mata yayi affecting tarbiyyanta..ko kanaso ta lalace ne”…ya rufe mata baki yana girgiza kanshi yace”ba abinda zai sameta Bi’iznillah baby..bazata lalace ba..if you remember kema ai haka nakeyi maki tun kina karama..Kuma gashi nn ba abinda ya sameki..so itama zata dena InshaAllah..it’s just a matter of time”…muryan Nawal suka jiyo daga kitchen tana kwala mai Kira..da sauri ya kama hannun Layla yaje yasata cikin motarshi yayi locking dinta a ciki wai don karta tafi snn ya koma ciki…ya dauko Nawal da har ta fara kuka a kitchen..ya dauki school bag dinta da lunch box snn ya fita daga gidan…baya ya isa inda motarshi yake ya fara ajiye school bag da lunch box din nata a back seat snn ya shiga driver seat Kuma har yanxu tana rungume a jikinshi…Layla dai ido ta zuba musu tanaso taga da ita zaiyi driving din ko Kuma Yaya..ganin ya kulle mota Yana kokarin kunnata Layla tace mishi”daddy are you for real..bazaka ajiyeta snn kayi driving din ba”…Taheer na kallon Nawal da tayi lakwas a jikinshi yace”sweetheart ki koma wurin maama ki zauna kinji”…ta makale kafada a hankali tace”Papa am scared”…ya dagota yana kallo snn yace”don’t be scared sweetie ba gani kusa dake ba”..sai Kuma ya daga kanshi Yana kallon Layla da tayi relaxing tana kallon ikon Allah…a hankali yace mata”baby kin ganiko..gashi nan yanxu kinda tanajin tsoronki”..yana rufe baki Layla tadan saki fuska tana kallon Nawal din tace”come here sweetie”..aiko da sauri kmr jira takeyi ta fada jikinta tana dariya…Taheer ma kallonsu yake yana dariyan..Nawal tayi kissing forehead din Layla tace”I love you maama”..itama Layla tayi kissing nata back tace”I love you too baby”…Taheer ya dan bata rai yana kallonsu snn yace”sweetie nifa”…da sauri ta matso jikinshi shima tayi mishi kiss din snn tace”I love you so very very much my Papa”…shima yayi Mata thesame snn yace”and i love you more than any other thing sweetheart..I love you”…ya karasa mgnr yana kallon Layla snn ya kashe Mata ido..ita Kuma ta kauda kanta gefe tana girgiza Kai..idan da sabo ai yaci ace ta saba da wnn son kan nasu…har mamakin wnn soyayya takeyi..sai takega kmr idan ta haihfi wasu yaran bazai so su kmr yanda yakeson Nawal din ba…a haka Taheer ya tada motan suka tafi..saidaya fara tsayawa yayi musu takeaway na abinci snn ya fara sauke Layla a school snn ya bata abincinta ya Kuma ta tabbata taci sbd babaynshi…daga nn Kuma ya sauke Nawal itama a nata school din snn ya wuce Clinic…

STORY CONTINUES BELOW

Bayan Wasu Shekaru…

A takaice dai rayuwar auren Layla da Taheer rayuwa ce da suka ginata kan soyayya da Kuma kulawa da juna..rayuwace sukeyinta na tsakani da Allah babu munafurci Kuma babu ha’inci a cikinta…suna matukar so da Kuma kulawa da junansu sosae…Layla ta kammala karatunta inda tayi specialising bangaren gynecology…yanxu hake she’s a medical doctor and sunyi aiki tare da Taheer a Clinic dinshi…kafin daga baya ya bude Mata Clinic nata na kanta itama take running dinshi da sauran employees dinta…rayuwarsu na tafiya cikin farin ciki da kwanciyan hankali…

Yanxu Layla ta zama big madam don yara hudu gareta..bayan Nawal Saida tayi maza biyu snn ta kara mace guda daya…akwai mai sunan dad din Taheer ana ce mishi khaleel…sai Abdallah sai Kuma auta mai sunan Nafeesa ana kiranta Neehal…gaba daya yaran Kuma da babansu suke kama haske ne kawai suke dauko na Layla..banda Khaleel dake kamada Taheer sak..hatta skin colour dinshi irin na babanshi ne…wani lokacin Layla saita zauna tayita kallonshi don har acting dinshi irin na Taheer ne..ita Kuma Neehal ce ta dauko rigimanta…halinsu iri daya itama da Layla shiyasa wani lokacin Taheer ke kiranta da His little baby…su Nawal Kuma yanxu an girma don mostly ma bata cika zaman gidan ba…idan umma ta Kira tace a kawo Mata namesake dinta haka Taheer zai sauketa ya kaita ba don yanaso ba..shi Sam baison rabuwa da ‘ya’yanshi..

Yau Friday Layla ta tashi daga aiki 12 sbd tanaso taje gidan ummi ta dubata da jiki don tayita fama fever kwana biyu…Saida ta tsaya tayi picking yaranta a school snn suka nufi gidan..shima Taheer zaizo after Jumu’at prayer…tunda suka isa gidan yaran suka shiga da gudunsu suna rungumar su umma dake parlor suna musu kiss suna fadin”we missed you grannies”…Nawal kam tana makale jikin umma da take kirada Namesake…ita Kuma ummi tana zaune sai tabe baki take tana cewa”Yaran Taheer Kuma dama idan basuyi haka ba wane zaiyi ni Maryam…idan basu iya runguma da kissing goshin mutane bama ai Allah saiya tambayesu tunda ba abinda ubansu ya iya sama da wnn..banajin duk duniya akwai Wanda ya kaishi iya kissing da hugging din mutane”…umma na dariya tace”Kai Yaya..shi hugging da kissing din ai sign of love ne..so banga laifi a ciki ba..besides itama Layla tanayi ai..ba Taheer din ne kadai ya iya ba”…ummi dai tabe baki tace”ai dama baki son gaky Aisha..Sam bakison kiji an Fadi laifin Taheer..Kuma dai Shiba waliyyi ba dole Yana yin ba daidai ba”…Layla dai na gefe tana ta musu dariya..sauran yaran suma suna tayata..

Karfe biyu daidai Taheer ya shigo gidan..da gudu yaranshi suka fita sunajin dirin motanshi…Layla ta bisu da kallo with so much love..sun riga sun saba ko a gida dama Yana dawowa har rige rigen tafiya mishi oyoyo akeyi..ita kanta daurewa kawai tayi taci gaba da zama amma da a gida suke Kam itama binsu zatayi…

Taheer bayan yayi parking ya fito sai ya shiga daukan yaran daya bayan daya hugging da kissing dinsu..suma suk suna maida mishi da martani…Saida suka gama rungume rungumensu snn ya jasu suka shiga cikin gidan…Yana shiga ya saki hannun yaran tareda karasawa inda umma take yayi hugging dinta yana gaisheta…ummi tace”kaidai Allah ya shiryeka wlh..duk kabi ka lalata yaran nn da rungume rungume..basuki su rungume kowa ba wadann yaran”…Taheer na murmushi ya karasa kusa daita..itama kawai sai ji tayi yayi hugging dinta…sai tayi shiru kawai tana girgiza Kai..a fili ta furta”Allah ya shiryeka Taheer”..shi kuma yace”Ameen Ameen Ummi”…Saida ta saketa snn ya dauki Neehal daketa faman miko mishi hannu tana dariya..ya dagata sama yana juyi da ita cikin parlon..duk suka zuba mishi ido Saida ya gama snn ya zauna kusada Layla ya dora Neehal din kan cinyanshi yana Jan kumatunta yace”Nafee ‘yar lukuta”…ummi ta galla mishi harara tace”wato bazaka dene kiranta Nafee ba koh..sai kace sirikarka ba kake wnn iskancin”…Taheer na dariya yace”ummi ko sirika tace ai she’s still my younger sister…so ni a kanwar na dauketa ba sirika ba”…ummi tace”dole kace haka mana tunda ta Haifa maka ‘ya ka aura”…umma dake gefe tace”to Yaya abun gori ne Kuma”…ummi tace”dole in mishi gori ai tunda har yanzu daukanta yake matsayin kanwarshi”…Taheer kuwa hannun Layla ya kamo cikin nashi snn ya faki idonsu ummi yayi kissing hannun nata before saying”I love you so much babyna..bazan taba iya rayuwa babu ke ba”…itama idon nasu ta faka snn tayi kasa da murya tace”I love you too hubby..I love you so much”…Taheer ya lumshe ido tareda kissing forehead dinta..

Alhamdulillah! Alhamdulillah!!

Alhamdulillah!!!

A nan na kawo karshen Littafina mai suna Dr.TAHEER..Allah ya bamu ikon yin amfani da darussan dake ciki…Kura kurai dake ciki kuwa Allah ka yafe Mana🙏🏻

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *