DR TAHEER CHAPTER 6 BY UMMU ASHRAF
Www.bankinhausanovels.com.ng
Yana gama rufe kofan ya juya tareda komawa cikin dakin..ya zauna kusada ita..fuska a tsuke yace”fadamin dalilin da yasa kike guduna baby..ko tsanar da kikamin ne yasa ko ganina baki sonyi”…Layla ta girgiza kai da sauri..har kwalla ya ciko idonta…Taheer ya sake hade rai yace”karki kuskura kimin kuka..kinsan banaso”..aiko ta hadiye kukan nata tareda Kai hanu tana goge hawayen dake kan fuskanta…yasa hanu tareda riko nata..idanunshi a kanta yace”ki fadamin baby..baki son ganina ne in dena zuwa inda kike”…Layla da kuka ke Shirin kufce Mata tace”ba haka nake nufi ba daddy..kawai dai”..kmr zata fada sai Kuma tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya…yasa hannu yai cupping face dinta ya sake cewa”kiyi mgn baby..dare na karayi”…Saida ta lumshe idanuwanta snn tace”ni kunya nakeji daddy..Kuma inajin tsoro”…yai shiru na tsawon secs yana kallonta..sai can Kuma ya nisa yace”meyasa kikejin tsoro na Kuma..kina tunanin zanyi maki wani abun ne”…batace komai ba sai hawaye da takeyi…ya matso da fuskanshi ya hada da nata..hancinshi na gogan nata.. idanunshi shima a lumshe yace”idanma kina tunanin zanyi maki wani abun ne baby to ki dena..bazan taba yi maki abunda bakiso ba..I promise babu abinda zai shiga tsakanina dake sai da amincewarki..am not after that baby..am after your love..so ki dena jin tsorona ki saki jikinki dani don Allah”..Layla da idanunta ke lumshe har yanxu..tace mai”toh daddy”..ya dago fuskanshi yana share Mata hawaye yace”promise me daga yau baki kara guduna”…Layla ta saki murmushi snn tace”I promise”…yasa hanu ya janyota jikinshi sosae..idanunshi kan lips dinta da sukayi ja as a result of kukan da tayi..murya can kasan makoshi yace”saura kunyar..bari in cire maki itama kinga saik…bai karasa mgn ba Layla tai saurin dora hanu kan bakinshi dake gab da hadewa da nata…kirjinta na sama da qasa tace”shima na denaji daddy..bazan karaba”…wani malalacin
murmushi ya saki yana kallonta yace”are you sure baby..da ki bari kawai indan rage maki ita”…ta sake kai hanunta bakinshi tana girgiza kai kmr zatasa kuka tace”Allah na dena daddy..kayi hakuri pls”…Taheer yasa hannu ya sake manne ta da jikinshi yana smiling yace”na hakura my baby..amma daga yau duk kika sake cewa kunyana kikeji sai nayi..kin yadda”..ta daga mai Kai a hankali…ya dagota daga jikinshi yanata kallonta yace”alright na gode sosae baby..I love you”…Layla ta sake fadawa jikinshi tana murmushi..ta bude baki zatace I love you too sai Kuma ta maida bakin ta tsuke da sauri..murya can kasa tace”nayi missing dinka sosae”…ya dagota tareda kama cheeks dinta yace”and I missed you more…yanxu tashi kije ki kwanta tunda mun gama kar ummi ta farka taga bakya nan”…Layla murmushi ta saki data ayyano kawai ace suga ummi a kansu ynxu..ai tasan ba daddy ba ita kanta Allah ne kadai zai rabata da ita.
Taheer ya fara mikewa itama ta mike..ya kama hanunta suka fita daga dakin..ya rakata har kofar dakin ummi tareda yi Mata peck a goshi snn yace daita”sweet dreams”…tana murmushi itama ta gyada kanta tace”Allah ya tashemu lfy…Yana tsaye yana kallonta har ta bude kofar ta shiga..shima ya juya a hankali zuwa part dinshi…har ya fara missing dinta wlh..Allah dai ya dorashi kan ummi ta bashi matarshi su tafi gida abunsu.
+
Washegari ya kasance Monday..a ranar ne kuma Layla zata je school don fara registration dinta…ta gama shiri da wuri..tana zaune parlor itada umma Taheer din ya shigo…bayan sun gaisa da umma yace”baby I hope dai kin gama shiryawa don tafiya zamuyi yanxun nn”…Layla ta mike tsaye tana cewa”na gama tun dazu daddy..Ina kwana”…ya sakar mata smile snn yace”lfy qlou..how was ur night”…tace”Alhamdulillah”…Taheer ya dubi umma yace”ummi bata fito bane”…umma bata kaiga yin mgn ba ummin ta fito daga dakinta sanyeda hijabi..ta karaso parlon tana duban Layla tace”kin gama shiryawa ne”…Layla tace”eh na gama”…ummi ta wuce gaba tana fadin”to sai ku fito mu tafi”…Taheer ya wara idanun sosae yace”ummi unguwa Zakije ne”…ummi ta dakata da tafiyar da takeyi ta juyo tana mai wani kallo tace”ban gane unguwa zanje ba… registration zan rakata tayi Mana..ko da tunaninka zan bari ku tafi daga Kai sai ita ne”…Taheer da mamaki ya cikashi da kyar ya iya bude baki yace”ban gane me kike nufi ba ummi”…Yana rufe baki ummi tace”Ina nufin tare zamuje Taheer..haka kawai in bari ka fita da ‘yar mutane kaje ka aikata abinda bashi knn ba..yanda ka lalace din nn ai bazan iya bari ka kebe da yarinyar nn ba wlh..Kai ba abin yadda bane”…Taheer ya dafa goshi sbb takaici ko mgn ya kasayi..idan yaso karban hakkinshi ne wajen Layla wlh yasan hanyar da zaibi ya karba Kuma ba tareda duk sun ganeba..saidai bayan abun ya faru su fahimta..amma meyasa ummi kemai haka for Goodness sake…ita kanta Laylan wnn karon bataji dadin abinda ummin tayi ba..ai yace mata shi ba abinda zaiyi mata meyasa ummi zatace haka…itama umma tana zaune ta zubama sarautar Allah ido..tana duban ‘yar uwar tata tace”haba Yaya ya zakice haka… don Allah ki kyalesu suje su dawo ni nasan babu abunda zaiyi Mata wlh”…ummi ta saki wani murmushi tace”ai dama bazaki ganiba Aisha tunda bakison laifin danki”…umma ta mike tareda kamo hanun ummi suka zauna snn tace”don girman Allah Yaya kiyi hakuri ki barsu suyi tafiyarsu..ai yaji abinda kika fada Kuma nasan ko Yana da niyyan yin wani abun yanxu ya hakura..kiyi hakuri kar kice zaki bisu don Allah”…ummi tai shiru kawai kmr mai tunani…sai can Kuma tace”to ki gargadesa wlh..kar ya kuskura ya aikata abinda ba shknn ba don ranshi zaiyi mummunan baci”…da sauri umma tace”bazai ma aikata komai ba da izinin Allah”…ta dubi Taheer dake tsaye kmr gunki tace”wuce ku tafi Taheer..Allah ya bada saa”…Taheer kmr abinda yake jira knn ya fice daga parlon…itama Layla ta mike a hankali tabi bayanshi..cikin ranta ko dariya draman ummi ya bata wlh..wai ba abun yadda bane😹
STORY CONTINUES BELOW
Suna fita bank suka fara zuwa..sunyi saa Kuma basu samu layi sosae ba..nanda nn ya biya kudin daga nn Kuma suka wuce school.
Ya taimaka Mata sosae..duk abinda bata ganeba zai Mata bayani snn inda ya kamata suje tare ya rakata inda Kuma ya kamata taje ita kadai sai ya jirata daga waje…basu suka bar cikin Base ba sai around 3…Kai tsaye ya maidata gida shi Kuma ya wuce clinic.
Around 9:30 ya dawo gida..bayan ya kammala duk abunda yakeyi..sai ya dauki chocolates daya siyo Mata tun ranan da ta dawo ya nufi part din nasu…gaba dayansu suna parlor suna kallo..ya nemi wuri ya zauna shima snn ya gaisa da iyayen…Layla dake makale kusada ummi tace”daddy sannu da dawowa”yai Mata murmushi kawai kafin yai mgn yaga an jefo takadda da biro gabanshi..ya kallesu snn ya daga Kai ya kalli daga inda suka fito..ummi ce ta wurgo mai su idanunta a kanshi tace”rubuta sakin yarinyar nn ka bani yanxu..ai dama na ce maka idan bata sonka bazaayi Mata dole ba”…Taheer ya shiga bin ummin da kallo baki bude..he’s totally speechless..kmr daga sama yaji Layla tace”ummi ni nace maki bana son zama dashi ne”…ummi ta juya tana kallon Layla tace”yo ai ba saikin fadaba ‘yar nn..alamomi sun nuna ba sonshi kike yi ba”…tana rufe baki Layla tace”nidai ba cewa nai bana sonshi ba ummi..ni ban taba ce maki bana sonshi ba”..ummi ta shiga salati tana tafa hannaye tace”Ni Zaki bama kunya Layla..Ina kokarin in kwatar maki ‘yancinki shine zaki watsamin qasa a ido”…itadai Layla bata sake cewa komai ba..ta turo baki kawai tareda dauke kanta gefe..umma dake kokarin yin dariya tace”kinga Yaya sai ki dena shiga harkansu yanxu..tunda ta nuna tanasonshi sai ki bashi matarshi suyi tafiyarsu can gidansu..muma mu huta”..ummi na girgiza kai tace”ko zan bashi yarinyar nn sai yayi Mata lefe wlh..duk wani abu da yasan anayi ma mace kafin a aureta sai yayi ya kawo..snn sai ayi biki ya dauki Matarshi su barmin gida”..Taheer daya kame kmr gunki sbd abubuwa biyu da suka sashi farin ciki da Kuma mamaki…na farko shine bai taba tunanin jin mgnr daya fito daga bakin Layla ba..knn hakan na nufin itama tana sonshi..na biyu Kuma dayaji ummk tace zata bashi matarshi..zai iya cewa rabonda yaji farin ciki irin wnn har ya manta…da sauri ya karaso inda ummin ke zaune ya zauna kusada legs dinta tareda Dora kanshi a kan laps dinta..ya lumshe ido yanajin wani extraordinary farin ciki har cikin zuciyarshi..murya can kasa yace”thank you so much ummina..Allah ya saka maki da alkhairi..ummi Allah ya faranta maki kmr yanda kika faranta min..you are the best”..ummi na shafa kanshi itama tana murmushi tace”lallai sannu majnoon”..umma ma na dubansu cikin farin ciki tace”kwarai kuwa Yaya ga Layla ga Majnoon..Allah yai muku albarka gaba dayanku”… Layla da duk kunya ya isheta ta mike zuwa dakinta..gaba daya batasan ya akai ta saki zance haka ba..sai yanzu takejin kunyar mgnr data fada..ga Kuma su umma suma suna Kara sata jin wani kunyan…Taheer ya bita da kallo bayan ta shiga dakin..ya dago kanshi daga cinyan ummi yana dubanta tace”gobe zanyi miki transfer ummi..sai ayi duk abunda ya kamata”..ummi tace to Allah ya kaimu…yace”Ameen”..snn ya mike zuwa inda ledan chocolates daya shigo dashi yake..ya dauka idonshi na kan ummi yana nuna Mata ledan yace”ummi don Allah in Kai Mata”…Ummi tabi ledan da yake nuna Mata da kallo kmr zatace aah sai Kuma tace”Kai Mata Amma karka dade”..wani dadi ya sake kama Taheer ya nufi dakin nata yana”yanzun nn zan fito ummi”…Ummin tabishi da kallo kawai tana murmushi…Saida ya shiga dakin snn ta dawo da kallonta kan umma tace”Ina sane nayi abunda nayi fa Aisha..nasan da zaunar da ita akai akace ta fada tana sonshi ko batasonshi bai zama lallai ta fada ba..yanzu da nayi haka kinga gashi ko tambayan ta baayi ba ta fada”…Umma ma na dariya tace”Kuma wlh kinyi hikima Yaya..da tambayan nata akai zataji nauyin fada..amma yanxu kiga yarinya kai tsaye ta fada abinda ke cikin ranta..Allah ya musu albarka ya basu zamn lfy”…ummi ta amsada ameen snn tace”yanxu sai mgnr biki.. don gsky bazai yiwu ace bikin Layla guda banyi taron biki ba..dagashi sai ita suka ragemin don haka ya zama dole inyi gagarumin biki kafin a bashi ita su tafi”…cikeda gamsuwa umma tace”hakan ma yayi ai Yaya..Allah ya nuna mana lokacin”..umma tace “ameen zanyi mgn da Alh Adam inyaso sai a tsayar da lokacin bikin”….a takaice dai sun dauki tsawon lokaci suna cigaba da tattauna yanda bikin zai kasance.
Layla kuwa na shiga daki ta fada kan gado tanata sakin murmushi..batasan meke sata murmushi haka ba..kawai ta tsinci kanta cikin excitement…a hankali Taheer ya turo kofar dakin ya shigo…tana ganinshi tasa hannayeta ta boye fuskanta dasu..har yanzu Kuma bata bar smiling ba…shima da murmushi a fuskarshi ya karaso inda take ya zauna..Yana kallon yanda ta boye face dinta yace”baby kunyan ya dawo knn”…ta cire hanun nata da sauri tana girgiza kai tace”no daddy ba kunya nakeji ba”…ya sake sakin wani murmushin Yana kallonta..sai ya bude hannayenshi idonshi cikin nata yace”come here baby”…ba musu Layla ta fada jikinshi tamkar dama abunda take jira knn…Taheer yasa hannunshi tareda matseta gam a jikin nashi..yanajin kanshi tamkar wanda yake cikin gajimare can sararin samaniya sbd tsabar farin cikin da yake ciki…daidai saitin kunnenta yace”thank you so much baby..you really save my heart from exploding..da ummi ta dage saina sakeki baby da ban San Ina zansa kainaba..thank you so much love..I love you sosae”…wani irin dadi Layla ta sakeji ya lullubeta..kalamanshi means alot to her..tanajin dadinsu sosae ba kadan ba…yasa hannu tareda dauko ledan dake ajiye gefenshi..yasa cikin hanunta yana cewa”this is yours..idan akwai wani abun da kikeso just name it..zan fita in nemo mikishi ko menene”…Layla ta dago daga jikinshi tareda bude ledan taga tulin chocolates ciki..ta zare ido sosai tana kallonsu..batasan lokacinda ta sake hugging dinshi tace”thank you so very much Daddy”…Taheer na shafa bayanta yace”no thanks baby..yanxu ki fadamin abunda kikeso”…ta sake dago kanta tana murmushi ta girgiza Kai tareda fadin”I want nothing daddyna..wnn din ma is enough..I really appreciate”…yasa hannu ya kamo fuskanta tareda manna mata slight kiss kan both cheeks dinta.. followed by forehead dinta…ya kwantar da ita kan gadon tareda ja Mata duvet ya lullubeta snn yace”ba cewa nai ki sasu a gaba kice Zaki cinye lokaci dayaba..da kadan kadan zakina ci coz banaso ya baki matsala idan period dinki yazo”…haka nn taji kunyar mgnr daya fada..ta lumshe idanunta kawai ba tareda tace komai ba…yana jan dogon hancinta yace”alright zanje in kwanta..sai da safe”…ta bude idon da sauri tace”baka yimin addu’a ba ai”…Taheer ya Kara sakin murmushi.. actually Yana sane dama ba mantawa yai ba..kawai yanason yaji ko zatayi mgnr ne gashi Kuma tayi…a hankali ya karanto adduan tareda shafeta dashi..ya tofa both sides snn ya mike tsaye yace Mata”good night..have a wonderful sleep”…ta daga mishi Kai tana murmushi itama..shi Kuma yasa kai ya fita daga dakin ba don yaso ba…har lokacin Kuma su ummi na parlon sunata discussing mgnr bikinsu..bai sake zama ba yai musu sallama kawai ya tafi part dinshi..he have to pray ya godema Allah da yake daidaita al’amuranshi one by one.. Alhamdulillah Ala kullu Haal.
Kmr yanda ummi ta fada..sunyi mgn da Alh Adam kan bikin da take sonyi..ya kumayi naam da mgnr tata..snn sun tsaida bikin nan da 4 weeks..sbd sunaso su kammala duk abunda ya kamata kafin zuwa lokacin biki..and ita kanta Laylan tana bukatar tutorials kan abubuwa da dama da suka shafi zaman aure..don haka dole sunada bukatan enough lokaci.
Wannan kenan
The following day ya kasance Tuesday..Layla suka sake komawa mkrnta don akwai abubuwanda bata kammala ba…ba yanda batayi da Taheer kan ya tafi aikinshi idan ta gama zata kirashi Amma Sam yaki tafiya..yace Mata zai jirata tunda he’s on evening duty.Ganin time din sallah yayi Layla ta nufi female Majid tayi alwala snn ta shiga ciki don yin sallah..bayan ta idar tana addu’a wata yarinya da ko zata girmeta bai wuce da 2 or 3 yrs ba tazo ta zauna kusa daita..Saida ta shafa adduan snn ta dubi yarinyan dake kallonta da murmushi..ta mikama Layla hannu tace”sunana Hanna Umar Faruk”…Layla ma murmushin tayi snn ta Mika Mata nata hanun sukayi musabiha tace”Maryam Taheer Jakada”…yarinyar na gyada Kai tace”it’s nice meeting you Jakada”…”nice to meet you too”..Layla ta fada itama tana murmushi…Layla ta fara mikewa..itama Hanna ta mike..suka jera a tare suka fita daga masjid din..Hanna tace”na ganki dazu a student affairs office..inata so in maki mgn Kuma sai na nemeki na rasa”…Layla tace”eh na fito inyi sallah ne”…Hanna na daga Kai tace”hakane..amma naga kmr course daya ma zamuyi dake..medicine right?…Layla tace”exactly..ashe course dinmu daya”…tace”yea and I hope zamu zama friends”..still Layla na murmushi tace”InshaAllah”…kafin wani ya sake mgn wayan Hanna dake hanunta ya fara ringing..ta dubi Layla da sauri tace”my Habibi is here to pick me up..kisamin number dinki sai mu na gaisawa kafin a fara lectures”…ba musu Layla ta amsa wayan da take Mika Mata..tasa Mata digits dinta snn sukai sallama ta tafi…itama ta karasa inda ta barshi sukayi gida Kuma.
+
Bayan Sati biyu…
Shirye shirye sosae su ummi suke ba kama kafar yaro…amarya na Shan gyara sosae don takanas aka dauko expert akan harkan gyaran amarya taketa kimtsata ciki da waje..lokaci guda ta Kara haske tayi wani irin kyau..skin dinta sai glowing yake…lokacin da suka fara lectures kullum Taheer ke kaita school..inta gama Kuma ya maidota gida..daga baya ummi ta hanashi kaita wai bata yadda dashi ba..haka kawai yanda yake rawar kan nn gani take ba abunda bazai iya aikatawa ba… dukda Taheer baiso ba amma haka ya hakura..ta wani bangaren shima taimakonshi akai..don duk suka kebe da ita wasu bakin al’amura yakeji na zagayawa cikin systems dinshi..yanda take glowing sai yayi da gaske yake iya controlling kanshi..ko makarantan ma da hijab dinta take zuwa har qasa.
Kmr yanda Taheer yace zaiyi musu transfer hakan yayi..ba bata lokaci Kuma suka fara siyen very unique and expensive kaya da sukasan zaima Layla kyau…duk sukayo siyayya umma zata janyo Taheer dakinta ta nuna mai kayanda suka siyo..haka zaita dubasu Yana comments.
Yauma suna duba kayan da suka siyo sai gashi ya shigo dakin…umma tace”yawwa karaso kaga kayan da Muka siyo”…ba musu ya karasa inda kayan suke a baje..umma ta shiga nuna mai inners din da suka siyo dazu…Taheer ya dinga dagawa yana kallonsu daya bayan daya..Saida ya gama kaf snn yana duban umma yace”wadan nn sun Mata kadan umma”…kafin umma tayi mgn ummi tace”ya zakace sunyi Mata kadan..sai kace wata uwar mata ace wnn breziern suyi ma Layla kadan”…ya sake cewa”Allah ummi sun Mata kadan..Kuma ki kai Mata ta gwada ki gani”…ba musu ummi ta dauki bra din ta fita dashi…ta samu Layla na karatu a dakinta..ta Mika Mata bra din tace”shiga bayi ki gwada yanxun nn inaso inga ko ya miki daidaine”…Layla batace komai ba tasa hanu ta amsa..ta shiga bayi for some secs sai fito..ta mikama ummi bra din tace”ummi yamin kadan wlh..ko shigana ma baiyi ba”…ummi da mamaki ya isheta ta karba kawai snn ta fice daga dakin…cikin ranta tana tunanin anya ko Taheer ba lalube yar mutane yakeyi ba..inba hakaba ta ina yai Mata saninda har ya haddace size dinta haka…tana komawa dakin ta mikama umma bra din tace”baiyi Mata daidan ba kuwa Aisha..yayi kadan”..sai Kuma ta juya ga Taheer tace”ka Fadi tsakaninka da Allah Taheer..anya ba lallabowa kakeyi cikin dare kana lalube ‘yar nn ba kuwa”…Taheer da mgnr ummi ya bashi dariya da Kuma kunya yace”Kai ummi dn Allah..wani irin biyo dare Kuma ana zaune qlou”…a hasale ummi tace”yo biyo dare mana Taheer..ya koni da nake tareda ita ko yaushe ban iya haddace size dinta ba sai Kai da bama tare kuke kwana ba”…shiru kawai Taheer yai yana murmushi…umma ma mgnr ba karamin dariya ya bata ba..ta hade kan breziers din tareda Mika mai tace”gashi nn..zan baka receipt din inda Muka siyo sai ka maida musu ka dauko daidai size din nata..tashi ka tafi”…da sauri ya mike kmr jira yake ya fita daga dakin…umma na duban ummi tace”Kai yaya ai saiki bashi kunya..nasan ba wani lallabowa da yakeyi wlh..kawai dai Sabon da sukayi ne..kuma fa Yaya naga shi da kanshi ma yana siyo Mata inner wears..so ba wani abu bane dan ya haddace size dinta”…ummi dai bata tanka ba amma cikin ranta gani take da kyar idan ba lallabawa yakeyi wurin Layla ba😹
STORY CONTINUES BELOW
Bangaren amarya Layla kuwa zaace ba wani shirye shirye da takeyi Banda wanda ake Mata…kullum tana zuwa school abunta.
Yauma kmr kullum sun gama lectures dinsu gaba daya..suka fito don tafiya gida itada new friend dinta Hanna..sun saba sosae da ita kasancewarta mai surutu da Kuma saurin sabo..sai daga baya Hanna take fadama Layla cewan watanninta uku da aure…Layla tasha mamaki kam don bata taba tunanin Hannan tanada aure ba..snn bata taba nuna mata cewa itama tanada auren ba.
A hankali suke tafiya zuwa parking lots..don tasan maybe driver na can yana jiranta..itama Hanna maybe habibinta yazo yazo…kmr ance ta daga kai sukayi ido hudu dashi..yana jingine jikin motarshi ya rungume hannayenshi a kirji…ta wara ido sosae tana murmushi..snn ta kama hanun Hanna tana fadin”zo muje ki gaisa da daddy na”…yana kallonsu har suka karaso inda yake…tace”daddy sannu da zuwa…sai Kuma ta nuna mai Hanna tana fadin”meet my new friend..sunanta Hanna”…Taheer dake murmushi har yanxu yace”sannunki Hanna”…itama tana fara’a tace”daddy Ina yini”…ya amsa Mata”lfy Lou ya school”..tace”Alhamdulillah daddy”…ta dubi Layla tace”Jakada bari in karasa..ga Habibi can na hangoshi yana jirana”…Layla na daga Kai tace”alright bye..sai munyi waya”..itama tace daita”ba bye”snn ta juya ta tafi..Taheer ya bude Mata mota yana kallon yanda take sheki..Saida ta shiga ya rufe kofar snn ya zagaya shima ya shiga…yai ma motan key suka bar wurin.
Har suka danyi nisa a tafiya bai dena juyowa yana kallonta ba…she looks so takeaway..ji yake kmr daga nn kawai ya wuce da ita gidanshi…kasa hakura yai ya gangara gefen titi yai parking…ya juyo gaba daya Yana kallonta da idanunshi da suka canza launi..ya Mika Mata hanunshi alaman she should grab it..batai musu ba kuwa ta dora hanunta Kan nashi..ya janyota jikinshi sosae tareda dorata kan laps dinshi..ya matseta jikinshi yana sauke ajiyan zuciya a jere a jere…Layla kuwa lumshe idanunta tayi lub..tanajin yanda bubuwa da dama ke Kai kawo a kwakwalwarta..kirjinta sai bugawa yakeyi da sauri da sauri…murya can kasa Taheer yace”baby I love you so much wlh..ni kaina ban San irin sonda nake maki ba..promise you’ll never leave me har karshen rayuwata plss..idan kika barni baby mutuwa zanyi wlh”…Layla taji idanunta har sun ciko da hawayen tausayinshi..ba karamin tausayi yake bata ba yanxu..ta dago daga jikinshi kanta a kasa tace”InshaAllah bazan taba barinka ba daddy”…Taheer ya saki murmushin jin dadi snn ya manna mata peck a forehead dinta…da kanshi ya maidata seat dinta..har yanzu bai dena kallonta yana sakin murmushi ba..saida yaci gaba da driving snn yace”ummi fa bata san na taho daukanki ba..she was saying wai bata yadda dani ba..har ta turo driver umma tace kar yazo ni inzo”..ya kare mgnr still da murmushi..kafin ya sake cewa”umma really is a life saver u know..ba don itaba Allah nasan da yau bazan iya bacci ba..kawai mutum da matarshi duk anbi an hanashi ganinta”…ya karasa mgnr tareda pouting lips dinshi…Layla dake kallonshi ta saki dariya kawai tana girgiza Kai..
Bayan sun isa gida..yana gama parking ta shiga kokarin bude motan zata fita…Taheer yasa lock tareda komawa yai relaxing kan kujeran da yake.. idanunshi na kanta yace”ai ban sallameki ba”…Layla ta dena kokarin bude motan da take tareda komawa ta zauna itama…yadan daure face dinshi yace”baby banason kina zuwa makaranta a haka wlh..banaso”…Layla ta bude idonta sosae tace”hijab dina ya kai har qasa fa daddy”…tana rufe baki yace”to kuma fuskanki da kike yawo dashi a haka kowa na kalla fa..bakisan yanda kika koma ba koh”…Layla ta sauke ajiyar zuciya a hankali kafin tace”shknn..daga gobe zan fara sa niqab idan zan fita”…Taheer ya saki smile yace”good girl..May Allah bless you”..tace”Ameen Ameen..yanzu xn iya tafiya”…Saida ya cire lock din dayasa snn yace”yes ma’am..ki ajiye wayanki kusa..zan Kira”..”toh”tace dashi snn ta bude motar ta fita..shi Kuma ya bita da kallo yanajin kmr ya bita cikin gidan..he can’t get enough of her at all..son da yake mata is different.
Bangaren Hajia Anty Sameera kuwa..tayi bincike kmr yanda tace zatayi..an Kuma tabbatar Mata da Taheer ba kowa ya aura ba face Layla..wnn yarinyar me kama da aljanu..yarinyar da taji ta tsaneta dama from d beginning..ranar taci kuka ta godema Allah..don takaicin wai duk fadin duniya Taheer ya rasa wa zai aura sai wnn ‘yar..wnn abar da ko ita kanta ta kusa haifanta…an tabbatar mata da yarinyan Base University take..snn bata tare gidan Taheer ba har kawo yanxu..wnn dalilin yasa ta kudiri aniyar shiga tsakaninsu nor matter what.
Wannan kenan..
STORY CONTINUES BELOW
Bayan sati guda…
Zuwa yanxu abubuwa kadan ne basu kammala ba na shirye shiryen biki…Nafisa ma zata taho cikin satin nn..su kuma yaran sai gab da biki zasuzo tareda mahaifinsu.
A bangaren ummi ta dage kan lallai saita koyama Layla girki..duk ta dawo daga school da wuri dama zaa turata kitchen ace sai tayi girki..
Yauma tun safe ummi ta turata kitchen wai Mama hawwa ta koya mata yanda zatayi tuwon shinkafa da egusi soup…a karo na uku Layla ta sake fitowa daga kitchen hanunta rikeda ludayin miya tace”ummi don girman Allah kiyi hakuri..wlh karatu nakesonyi”..ummi tai Mata banza tana cigaba da ware cards din biki da aka kawo Mata..Layla har ta juya zata koma kitchen din taji Taheer yayi sallama..sai ta fasa komawan ta tsaya…shi Kuma ya karasa kusada umma ya zauna snn yace”umma gani”…ta miko mai cards din dake gefenta tana cewa”invitation cards ne dama aka kawo daxu..shine nace bari in baka ko zakayi inviting friends dinka..wnn na dinner ne..dayan Kuma na mother’s Eve..kamu na Mata ne kawai so ba sai an baka ba”…Taheer ya rike cards din da take miko mai a hanunshi..idanunshi kan Layla da har yanxu ke tsaye da ludayi a hannu yace”lfy kuwa”..da sauri ummi ta dago tana dubanshi tace”lfy Mana..dambe ka samemu munayi da zata tambayemu ko lfy”…still idanunshi a kan Layla yace”baby me kikeyi a nan wurin”..wnn karon a kufule ummi tace”Kai wai Ina ruwanka da ita ne..girki nasata tayi..ko kana nufin haka zaa dauketa a kaita gidan nata ba tareda ta iya komai ba”…ummi na rufe baki yace”ummi indai don ni zaa koya mata girkin wlh na yafe…idan lokacin da zata koya yayi zata koya ai”…ummi na girgiza Kai tace”kasan wani abu Taheer..yarinyar nn dama da an likama wani ya aureta billahillazhi an cuceshi..yarinyar da bata iya komai ba sai shegen shagwaba kmr jaririya..amma da yake Allah ba azzalumin sarki bane..sai ya manna maka kaje kayita fama da ita..dama ai ba wani ne ya lalata ba daya wuce kai..don haka ba Wanda ya kamata ya kwasheta sai kai din..sai kaje kaji idan dadi ne auran macen da bata iya girki ba”..Taheer da mgnr ummin ya bashi dariya..sai ya saki murmushi kawai yana cewa”eh naji koma menene ummi..ni ba girkinta na auraba..ita na aura”…ummi dai bata sake tanka shi ba..Yana duban Layla yace”jeki ajiye wnn abun a kitchen kije kici gaba da karatunki”…aiko da sauri ta koma kitchen din ta ajiye snn ta sake fitowa ta shige dakinta..umma dake sauraron draman nasu tana dariya tace”wai Kai haka ake rayuwa ne..ace duk wani abu daya kamata bazaka bari yarinyar nn ta koya ba..to idan bata iya girki ba kaine zakana zama kanayi muku girkin ko kuwa”…still Yana murmushi yace”sai in ringa siyowa umma..ko Kuma in dauki mai aiki da zatana yi mana girkin In biyata”…umma ta girgiza Kai tace”wato gak a majnoon koh..to ba gata kake yimata ba wlh..tun wuri ma in zaka canza ka canza”…bai sake cewa umma komai ba ya mike tareda ficewa daga dakin..ummi ta bishi da uwar harara tana dan rainin hankali kawai”😆
Yau Wednesday Layla sun fito daga class..ganin akwai sauran time kafin another lecture..suka nufi cafeteria don cin abinci itada Hanna…table daya suka zauna..Hanna na duban Layla tace”what will you like to have”…Layla ta fada mata abinda zataci snn ta bada order..
Bayan an kawo musu abinci sun faraci..sunadan hiransu jefi jefi..kmr daga sama sukaga mace a gabansu..a tare suka dago kawunansu suna kallonta..Layla ta zare ido sosae tace”Anty Sameera”..Sameera ta saki wani matsiyacin murmushi snn taja empty kujeran dake kusa dasu ta zauna…ta shiga bin Layla da wani kallo tana cewa”so kece kika shiga tsakanina da mijina koh”…da mamaki Layla ke binta da kallo..kafin tayi mgn Sameera ta sake cewa”let me give you this worning..daga yanxu..I mean as from today..ki fita harkan mijina..Taheer mijina ne ba naki ba..so kibar wani jin dadi don an aura masa ke a sadaka..idan Kuma bakiji Mena fada maki ba..wlh wlh kinji rantsuwar musulmi..baki isa ki zauna da doctor lfy ba..yanda kika sa ya fasa aurena sbd ke..kema baki isa ki zauna dashi matsayin miji ba..Taheer mijina ne ni kadai..Kuma babu wadda ta isa inyi sharing dinshi da ita”..da sauri Hanna ta mike tana fadin”Hey.. Hlow..wacece ke..who do you think you are da zakizo ki samemu haka kawai ki fara mana ihu a Kai..have you lost it..anya ko kinada lfy”..a fusace Sameera ta kalli Hanna tace”ba dake nake mgn ba..so stay away”..tana rufe baki itama Hannan tace”ko ba dani kikeba ai da aminiyata kike..yanxu qatotuwarki dake ko kunya bakiji ba..kixo kina fada da yarinya karama a kan namiji..wa yace kiyi sake har ta kwace maki shi din”…Sameer ta daga hannu zata Kai Mata mari kawai taji an rike hannun nata…Layla ta kama hanun Hanna ta shiga janta suka bar wurin…Sameera ta bisu da kallo zuciyarta na tafasa…Saida sukayi nisa da wurin sosae Hanna ta kwace hanunta tace”wai meye hakane Jakada..ya mace zatazo tana faffada maki maganganu Kuma kiyi banza da ita..snn ni da nake rama maki kin wani janyoni kin fito Dani daga wurin..what’s wrong with you”…Layla batace komai ba..Saida ta samu wuri suka zauna snn tana kallon Hanna tareda dafa shoulder dinta tace”calm down mana babe..ni banga abun daukan zafi a nan ba”..Hanna ta ture hanun Layla dake kan kafadanta tana hararanta tace”ai bazaki gani ba dama..kawai mace tazo har inda muke ta raina mana hankali Kuma ki hanani ramawa…that aside..naji kmr tana mgnr kin kwace mata miji fa..Jakada kina nufin wai all this while kinada aure amma baki taba fadamun ba”…shiru Layla tayi na tsawon lokaci..batasan ta ina zata fara fada Mata cewa daddy is her hubby ba…Hanna ta dafa kafadanta tace”hlow..tunanin me kike Kuma”…Saida Layla ta sauke ajiyar zuciya snn ta shiga bata lbrin irin soyayyar da Taheer din ke Mata..alakar dake tsakaninta dashi..da yanda aurensu ya kasance da kuma shirye shiryen bikinsu da akeyi yanxu..da mugun mamaki Hanna ke kallonta tace”Amma gsky Jakada bakida kirki ko kadan..yanxu badon hakaba..da bazaki fadamin zaayi bikinki ba knn koh”..da sauri Layla na girgiza kai tace”wlh inata so in Fadi maki kawai bansan ta Ina zan fara bane”..ta bude bag dinta ta dauko cards da taketa faman yawo dasu ta Mika Mata tana cewa”take these..cards ne na gaba daya events din da zaayi..sun kusa sati cikin jaka na rasa ya zaai in baki..so ni waccan matar ma taimako na tayi”…Hanna tasa hannu ta amsa cards tana fadin”duk da haka baki kyauta min ba..amma kinsan wani abu..kwata kwata banyi mamaki da kikace daddy is your husband ba..don wani special kallo da naga yana jifanki dashi nasan dole Wanda akema tsanstar so akema wnn kallon”..Layla na murmushi ta girgiza kai tace”Hanna you are too much..dama sa mana iso kikeyi knn koh”…Hanna tace”no ba wani sa ido fa..abune da yake a fili..amma kinsan menene babe..ya kamata fa ki dage..ki kula da mijinki sosae..yanda kika samu yana maki irin wnn son..Nanda nn zaki mallake abinki a hannu..kinga ba ta yanda waccan witch din zata nemi shiga tsakaninki dashi”…Layla ta mike tareda kama hanunta tace”naji…yanzu ki mu tafi kar a fara lecture bamu komaba”…Hanna ta mike itama suka nufi hanyar clss dinsu tana cewa”gsky kina bukatn lecture akan yanda ake kula da miji Jakada..dole ma in baki sirrin yanda nake kulawa da Habibi na..shiyasa kikaga kullum Kara Sona yake”…Layla dariya kawai tayi tana girgiza Kai..ai Hanna sai a barta kawai..dama ya lafiyar kura..da can da batasan she’s married bama kullum karatu take mata kan yanda zatai handling saurayi and everything..yanxu kuwa da ta san tanada auren ai sai inda manta ya kare..tasan idan aka fara Mata lectures din kmr yanda ta fada..har sai taji ya isheta ma gaba daya.