DR TAHEER CHAPTER 7 BY UMMU ASHRAF
Www.bankinhausanovels.com.ng
Kai tsaye ummi ta wuce da ita bathroom bayan ta hada mata ruwan wanka da kanta…tace”yi sauri kiyi wankan ki fito..ki tabbata kin wanke ko ina na jikinki”…Layla dai batace Mata komai ba..don gani take wankan ma sai ance ga yanda zatayi…ummi Kuma na fita ta janyo trolley da aka cikashi da some of kayanda zata fara amfani zasu tafi dashi..ta fiddo Mata kayanda zata sa da inner wears snn ta jiyesu kan gado ta sake rufe akwatin…tana nn zaune Nafisa ta shigo da kabbasa a hanunta tace”yawwa ummi gashi”…ummi ta Mika Mata kayanda Layla zata Sanya jikinta tace”amshi kiyi maza ki turarasu Nafee…bansan meya dauke hankalina baayi turaren ba tun dazu wlh..da yanxu yasha iska”…ba musu Nafisa ta mike tareda jona burner dake ajiye kan bedside a socket..ummi ta miko Mata turarenda zaayi amfani dashi ta zuba cikin burner din..in no time qamshin turaren mai sanyin dadi ya fara tashi a dakin…ta dauki kayanda ummi ta bata tareda dorasu kan kabbasa..ta ajiye burner din a karkashin kabbasan…ta lullube ko ina ruf ya zamana bata inda iska zai shiga ciki.. hakan shi zai sa turaren yaita hawa kan kayan…after ike 10 mins ta sake juya kayan snn ta Kara
turaren..nanma ta barshi Yana tayi…Layla kuwa Saida ta kwashi almost 11 mins snn ta fito daga bathroom…idonta ya kada yayi jajir don ba karamin kuka taci a cikin bayin ba…tana fitowa ummi ta mike tareda komawa bathroom din..wani ruwan ta sake hada Mata mai daukeda madarar turare kala kala..snn ta fito ta sake tura Layla kan ta dauraye jikinta dashi…ba musu Layla ta koma bayin tayi kmr yanda ummi tace…ita kanta taji yanda lokaci daya jikinta ya sake dumamewa da kamshi..bayan ta fito again ummi ta sake bata wani Humra nan ma tabi duk loko da saqo na jikinta ta shafeshi tass da Humra din…zuwa yanxu zaka iya jiyo kamshin da jikinta keyi ko baka kusa da ita…bayan Nafisa ta gama turara kayan ta mikama ummi tana fadin”ummi ga kayan an gama”…ummi ta amsa kayan tareda shinshinasu…Saida ta lumshe ido don jin kamshin dake fita jikin kayan…ba bata lokaci ta ba Layla kayan kan ta sa ajikinta…Layla da keta kokarin danne hawayenta ta amsa kayan…Saida ta fara sa pant da bra snn ta saka kayan…atampa ne blue da touches din yellow a jiki..dinkin riga da skirt ne daya zauna a jikinta das kmr a jikin aka dinka..ummi ta zaunar da ita gefen gado kafin a gama turara lafayan da zaa nadeta dashi…kawai saita fada jikin ummin tareda fashewa da matsanancin kuka…ummi ta shiga shafa kanta tana kakalo murmushi…ita kanta duk abunda takeyi dauriya kawai take..Allah ya sani ba karamin missing dinsu zatayi ba idan suka tafi…ta riga ta saba dasu tun suna kanana…tasan idan suka tafi dole kewarsu ya dameta…tabbas ba don aureba da babu abinda zai rabata dasu sai dai ko mutuwa..+
A bangaren ango kuwa tun yamma dama ya gudu daga gidan Yusuf bayan ya sallami some of abokanshi da suka koma…Sam baison wani rakiya da abokai sukema ango wurin amaryarshi..shi Sam hakan baiyi mai ba..haka nn kawai ka kwashi katti suje suyita kallema mata suna mgn da ita…ba dashi zaayi wnn kwadon ba Kam…a masallacin kusa da gidansu yai sallahn magrib snn yaci gaba da zama a ciki har akai Isha..bayan idar da sallahn yayi add’u’o’i sosae kan aurenshi da Layla saida ya idar snn ya nufi gidan don ganin wainar da ake toyawa.
Kai tsaye part dinshi ya wuce bayan ya hadu da some of family members dinsu dake nn compound sunata tsokanarshi…ya bude daki ya shiga snn ya maida kofan ya rufe..ya karasa tareda kwanciya kan three seater dake parlon..sai ya fada duniyar tunani…yana tunanin yanda zamanshi zai kasance da Layla ba tareda wani abu na aure ya shiga tsakaninsu ba..yanaso yai keeping distance dinshi as he promised amma Kuma yana tunanin how…Allah ya gani shi din ba wai ma’asumi bane snn Shiba karfe bane da zai iya rayuwa cikin gida daya da wadda yakema matsanancin So irin haka Kuma ba tareda ya aikata komai a game da ita ba…yana tunanin ta Ya zai iya coping if suna rayuwa da Layla under thesame roof ba tareda yayi messing plan dinshi ba…yasan for sure zai iya kasa jurewa wani lokacin..amma Kuma baiso ya aikata abinda zai zama baiyi fulfilling promise dinshi ba..yanaso ne ya bata kulawanda bata taba tunani ba…yanaso ta tabbatar da ita din yake so bawai wani abu na jikinta ba..but how…a wani bangaren Kuma Yana tunanin rabuwa da ummi…yasan definitely zata shiga damuwa na rashinsu sosae..ta riga tayi sabo dasu na tsawon shekaru..gashi ita ba wasu yaran ke gareta ba..shi kadai Allah ya bata sai Layla…yanxu gashi aure zai nisantasu da juna..wnn shine dalilinda yasa ya dage kan umma ta dawo Abuja gaba daya…yasan idan tana nn ummi zata samu saukin kewansu da zatai…and shima zai riga kokari kullum yazo ya gaishesu as hakan zai rage Mata damuwa sosae..itama Layla sai Yana kawota tana ganinsu time to time…yayi nisa cikin tunani har baiji lokacinda wayarshi tai ringing ba..bai kumaji lokacinda umma ta shigo har ta zauna kusa dashi ba…Saida tasa hannu tadan jijjigashi snn ya mike zaune da sauri Yana rarraba ido…umma na mai kallon mamaki tace”tunanin me kake haka Taheer har nai maka 2 missed calls baka ganiba snn na shigo har na zauna bakayi noticing ba..are you alright”…Saida ya sauke numfashi snn yace”lfy Lou nake umma..kawai Ina tunani ne”…umma tace”ai dama ba bacci kaji nace kanayi ba…so nake inji tunanin me kakeyi haka”…ya saki dan smile snn yace”come on ba wani abu bane fa umma”…Yana rufe baki umma tace”tunanin Yaya kakeyi koh”…a hankali Taheer ya daga Mata Kai alaman eh…ita Kuma ta kamo hanunshi tace”kar ka damu kanka kan wnn.. InshaAllah zanyi iya bakin kokarina inga bata shiga wani hali sbd missing dinku ba..dukda nasan ban isa in hana taji kewan naku ba..but i promise bazan bari damuwa ya rabeta ba..she’s my sister afterall..so Nima tana Sona sosae baku kadai takeso ba”…umma ta karasa mgnr da murmushi a fuskarta..tanaso taga ya saki ranshi shima…saida yai Mata murmushi snn yace”na sani umma..nasan bazaki taba barin ta shiga damuwa ba…Allah ya saka maki da alkhairi umma for making everything here possible …thank you for getting me married to baby…without you this couldn’t have happened..so nagode nagode sosae umma…Allah ya saka maki da aljannah”…umma dake murmushi ta janyoshi jikinta ta shiga shafa bayanshi kawai…ita kanta tasan zatai kewansu.. especially shi da kusan duk problem dinshi itake solving…a hankali Taheer yace”am going to miss all of you umma”…still umma na shafa bayan nashi tace”and we are going to miss you both..Allah ya Baku zaman lfy da zuria dayyiba”… Taheer ya amsa da Ameen…cikin hikima umma ta shiga mai nasiha sosae kan zamantakewar aure…dukda tasan ya sani amma Yana dakyau a Kara tunatar dashi..nasihan nata ko na shiganshi sosae har ba karamin kashe mai jiki yayi ba.
STORY CONTINUES BELOW
A can wurin amarya kuwa..ummi da Nafisa nata Mata nasiha itama..Banda kuka ba abinda takeyi..sun dauki tsowon lokaci kafin su gama..Ummi ta dauki lafaya dinta yellow..wanda aka turara da turare shima snn ta nadeta a ciki…tana kallon Nafisa tace”ki kula da ita Nafee..bari inje in samu in Kira Taheer din..ban taho da wayn nawa ba”…Nafisa ta mike tareda karasawa inda Layla take ta zauna..ita Kuma ummi ta fita…Layla ta fada jikinta tana Kara sakin wani kukan…Nafisa ta rungumeta a jikinta cikin sigan lallashi tace”kukan ya isa haka Layla ko kinaso kanki ya fara ciwo ne..kiyi hakuri kinji duk wata mace da haka ta fara…ki nustu sosae Layla domin aure gareki yanxu…mijinki yana bukatar kulawarki sosae don haka kiyi kokari don Allah kiga kin biya mai duk wata bukatarshi…kiyi kokarin sauke duk hakkinshi dake kanki nasan shima bazai taba tauye maki hakkinki ba…sai ki dena wnn shashashancin don ke zaki kula da kanki snn ki kula da mijinki ma..ki zama jaruma Layla banda raki Banda gudun miji duk abunda yace kiyi kiyi mai Layla..duk abunda yace baiso ki bari kinji… InshaAllah zamuzo har gidan naku kafin mu koma..Allah ya Baku zaman lfy”…Layla najin duk abinda ta fada amma bata dena kukanta ba.
Ummi kuwa na fita ta wuce part dinta..Saida ta dauko wayanta snn ta shiga dialing number din Taheer…lokacin ya fito daga wanka..yana shiryawa Kiran ya shigo..yai picking tareda sallama a hankali…ummi tace”ka sameni part din abbanka yanxun nn”…tun kafin yai mgn ma ta yanke wayar…Yana kallon umma ya fada Mata abunda ummin tace…ita ta fara mikewa tace”kayi sauri ka gama ka fito..nasan an gama shiryatane”..Taheer Kai kawai ya iya daga mata..umma ta fita zuwa part din dad din nashi..shi Kuma ya karasa shiryawa snn ya fita.
Umma bata dade da shiga ba shima ya shigo..kanshi a kasa ya nemi wuri ya zauna…ummi na dubanshi tace”to ga Layla nan dai Taheer…ka dauketa ku tafi…I don’t have to remind you kan duk wasu hakkokinta dake kanka cox kai ba yaro bane…inaso ka riketa tsakaninka da Allah Taheer..karka cuceta Kuma kada ka bari wani ya cutar da ita… remember Amana ce yanxu a hanunka..sai kayi kokari kar Amana ya cika..Allah ya Baku zaman lfy ya kawo zuri’a dayyiba”…Taheer kanshi a kasa ya amsa da ameen a hankali…ummi ta mike tareda kamo Layla da har yanxu ke kuka jikin Nafisa…ta kama hanun Taheer din shima ya mike tsaye…kawai saita rungume su gaba dayansu tana hawaye… tasan tafi kowa farin ciki da wnn hadin nasu..da Layla da Taheer duk nata ne..ta Kuma San irin son da Taheer din ke mata bazai cutar da itaba…kawai she’s going to miss them…ta riga tayi sabo dasu gashi yanxu zasu tafi…a hankali Taheer yaji wasu hawayen tausayin mahaifiyar tashi sun zubo kan face dinshi…yasan su kadai gareta…Layla kuwa dama kukanta yafi na kowa…sundauki kusan 6 mins a haka kafin ummi ta sakesu a hankali snn ta juya tareda shigewa bedroom..Nafisa ta mike tabi bayanta da sauri…ita Kuma umma ta karaso inda suke ta rike hannayensu cikin nata snn suka fita daga part din…har bakin mota umma ta rakasu..bayan ansa akwatin kayan Layla a motan…Saida ya bude mota ta shiga snn shima ya shiga…Yana ganin umma na musu waving har suka fice daga gidan…shi kanshi gaba daya jikinshi a sanyaye yake…tausayin ummin yakeji sosae…yasan dole zataji ba dadi..dama shi kadai ta Haifa kwal..sai Laylan da aka basu…yanxu gashi duk sun tafi sun barta..
Har suka isa gidanshi dake Maitama..Layla bata dena kuka ba…gaba daya kukan nata ya dameshi…daurewa kawai yake…bayan ya shiga ciki yana gama parking ya bude motan ya fita…side din da take ya zagaya tareda bude kofan…bai tsaya yi Mata mgn ba kawai ya dauketa cak snn ya rufe kofan da bayanshi…Layla ta shiga wutsil wutsil tana fadin”daddy drop me..I can walk by myself”…Taheer baibi takanta ba ya nufi entrance din gidan…Saida yai unlocking kofan da key din dake hanunshi snn ya tura ya shiga ciki…Layla nata kuka tana ya ajiyeta amma yai Mata banza…Saida ya haura sama direcit to his bedroom snn ya direta kan gado…ta kwanta kan gadon tana Kara sautin kukan nata..Taheer ya dafe goshi tareda fadin”na shiga uku”..ganin da gske fa ba dena kukan zatai ba ya nufi inda take da sauri…ya dagota yana share Mata hawayen yace”so baby bakya tausayina koh..baki damuba duk halinda zan shiga right”…da sauri ta shiga girgiza mai Kai tace”daddy ummi…banaso mu barta daddy don Allah mu koma gidanmu”… yana girgiza kan shima yace”nan ne gidanmu baby..ummi Kuma i promise you ba abinda zai sameta..umma na tareda ita and na tabbata she’ll look after her..so stop crying..you know my heart aches for you…it aches whenever I see you in pain..so don Allah stop it”…ta gyada Kai a hankali…Taheer ya janyota jikinshi yanajin yanda jikin nata ke fitar da wani ni’imtaccen kamshi…sai ya janyeta da sauri yana fadin”now let me get you something to eat kafin mu kwanta koh”…Yana rufe baki tace”banajin yunwa”…yace”kinci abinci ne kafin mu taho”…da sauri ta daga mai Kai tana tuna uban kazan da ummi tasa Mata a gaba Saida ta cinye…bai sake cewa komai ba ya mike Yana cewa”alright muje kiyi changing I want to sleep”…ba musu ta mike tabi bayanshi..Saida ya fita ya dauko trolley din nata dake mota snn ya dawo tareda kulle ko ina..ya Kuma kashe bulbs din gidan snn ya haura sama…har yanxu Kuma Layla na biye dashi a baya kmr bindi…wata kofa taga sun shiga dake nn cikin parlon… corridor ne mai daukeda dakuna biyu…na farkon taga ya bude ya shiga…itama ta mara mishi baya…ya ajiye trolley din kan gado snn ya bude don nema mata sleeping dress…wata riga ya dauko ash color..jikinta cotton ne sosae…hanunta bai da wani girma can likewise tsawonta bazai wuce iya gwuiwa ba…ya ajiye gefe snn ya dauko daya daga cikin hulunanta na bacci shima ya ajiye gefe…ya juyo ya sameta tsaye tana binshi da kallo…Dan murmushi ya saki snn ya taka a hankali zuwa inda take…yasa hannunshi ya janyota jikinta…kafin ya shiga warware lafayan dake jikinta…itadai idanunta rufe ruf tanajin yanda yake warware lafayan…Saida ya gama wareta gaba daya snn ya shiga bin jikin nata da kallo…tayi mai kyau as always…a hankali ya dauko kayan dake ajiye kan bed din ya Mika Mata…idonshi a kanta”kinyi wanka kafin mu taho?..”…ta daga mai Kai alaman tayi…yace”ok ki cire kayan kisa wnn…nima zanje inyi changing”…yana rufe baki tace”ai tsoro nakeji daddy..nidai ka jirani pls”…bai sake cewa komai ba ya zauna gefen gado…har ta daga riganta zata cire a nn sai kuma ta fasa ta nufi bathroom…bayn mintina kadan ta fito sanyeda rigan da ya bata…ya sauke boyayyen a jiyar zuciya cikn ranshi yace”she always cute”…Layla ta karaso inda yake tace”na gama”…sai ya kama hanunta suka fita daga sakin zuwa nashi…ya zaunar da ita kan gado snn ya nufi closet tareda dauko pyjamas dinshi ya shiga bathroom…after like 6 mins ya fito…ya karasa inda Layla ke zaune har yanxu…kmr jira take ya zauna din ta matso tareda kwanciya a jikinshi…Taheer murmushi ya saki snn ya jata ya kwantar a kan gadon…ya rufa Mata duvet snn ya kwanta kusa da ita…Saida yayi addu’a ya shafa mata snn ya shafa ma kanshi…ya sauke wani nannauyan numfashi…this is what he has been praying for for…ya dade ya fatan Allah ya kawo ranan da idan yayi Mata addu’a zai kwanta kusa da ita kmr haka..ko bazaiyi komai da itaba he’s ok…ya lumshe idanu tareda fadin”Alhamdulillah”.
(Asuba ta gari amarya da ango😇)
Washegari…
They slept peacefully that har suka kusa makara sallahn asubah…lokacin da Taheer ya tashi har an fara sallah a masjid..ya mike zuwa bathroom ya dauro alwala da sauri snn ya fito..ya tasheta itama taje tayi alwalan ta fito…shi ya jasu jam’i sukai sallahn..don ko yace zai fita masallaci ba lallai ne ya samu sallhn ba..Saida suka fara raka’atainil fajr snn sukai subhi…bayan sun idar Layla ta mike tareda komawa kan gado ta kwanta…shi Kuma nan yaci gaba da zama yana add’u’o’inshi…Saida gari yai haske sosae snn ya koma shima ya kwanta.
10:45am
Daidai wnn lokacin Taheer ya fito wanka…ya tsaya gaban mirror yana tsane ruwan jikinshi da towel…su Layla ajebo kuwa har yanxu baa tashi daga bacci ba…bayan ya gama tsane jikinshi sai ya zauna kan stool yana shafa mai…Saida ya gama tsaf snn ya nufi closet ya dauko kayan da zaisa…ya shiga bathroom ya sa Kayan snn ya fito…yana combing gashinshi a gaban mirror wayanshi ya fara ringing…yai saurin maidata silent gudun kar karan ya tashi Layla…yai picking tareda kaiwa kunnenshi…muryan umma yaji tace”Ina ka shigane na Kira baka daukaba”… yace”ina wanka ne umma…Ina kwana”…umma ta amsa da”lfy lou..ya gidan”…yace”gida lfy umma..Ina ummi”…umma tace”gata nn bari in bata ku gaisa”…umma na gama mgn ta mikama ummi dake zaune kusa da ita wayan…ta amsa tareda yin sallama…Taheer ya amsa sallaman shima snn ya gaisheta…tace”duk muna lfy..ya gidan..hope dai ba wani matsala”…yace”ba komai ummi”…ummi tace”to Alhamdulillah..Ina Layla”…Taheer ya danyi shiru kmr bazai ce komai ba..sai Kuma yace”tana bacci”…ummi ta saki salati tana fadin”dama abinda nake gudu knn wlh..inba iskanci ba Taheer ya zaka bari tayita bacci har karfe 11…wane zaiyi Mata gyaran gidan toh”…Taheer na shafa Kai yace”calm down ummi..ai yanxu ta kwanta baccin…gidan Kuma ba abunda ya sameshi…ko Ina tsaf yake”…wani salatin ummi ta sakeyi tace”ka tasheta a baccin nn ko sai naci ubanka…wane irin gida a gyare yake bayan jiya duk anyi dabdala a cikinsa…yanxu abunda zaka koya Mata knn”…murya can kasa Taheer yace”to bari in tasheta”…yana rufe baki ummi taci gaba da fadin”ka tasheta yanxu yanxun nn…tun sassafe Aisha ta damemu wai a kawo muku breakfast…Ni nace bazaa kawoba don nasan Kuna can Kuna baccin asara…gashi kuwa mgn na tabbata..Allah ya sawake muku wlh”…shidai bai sake cewa komai ba ya kashe wayar…ya ajiyeta nan kan mirror snn ya juya zuwa kan gadon…ya zauna a hankali yana kallon yanda take baccinta hankali kwance…harga Allah shidai ba son tashinta yakeyi ba…