DR TAHEER CHAPTER 9 BY UMMU ASHRAF

DR TAHEER CHAPTER 9 BY UMMU ASHRAF

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Wani kallo mai cikeda ma’anoni daban daban yake jifanta dashi..wai meyasa ya siyo kaza…cikin ranshi yace”me kike ci na baka na zuba”…a fili Kuma sai yace”just eat baby..bana son surutu”…bata sake mgn ba ta fara cin kazan…shima yanaci idanunshi a kanta…yau kallon da yake jifan ta dashi ma na daban ne…tana lura dashi amma batace komai ba har suka gama…ya dauke ragowan da suka rage tareda tattara duk abubuwan da suka bata yayi kasa dasu…ita Kuma Layla sai ta koma dakinta..haka nn ta ji gabanta na wani irin faduwa…kan gadonta ta hau ta kwanta…sai Kuma ta shiga tunanin abubuwan da suka faru tsakaninta dashi…tanaso ta tambayi meya sauko dashi daga fushin nashi amma tanajin tsoro…+

Shikam Taheer bayan ya ajiye komai a kitchen ya sake komawa saman…dakinshi ya wuce direct don yasan itama tana can…amma sai yaga ba kowa.. ya duba bayi bai ganta ba..sai ya fita zuwa dakin nata…tayi nisa cikin tunani ko noticing shigowanshi batayi ba…ta daiji ya dagata cak snn ya dorata kan laps dinshi…ta lumshe idonta da sauri don ya bata tsoro sosae…shi Kam binta kawai yakeyi da kallo kmr zai cinyeta…ya dago fuskanta dab da nashi..yana kallon lips dinta data tsukesu sosae..ta bude idanun a hankali..murya a shagwabe tace mai”daddy ni ka bani tsoro wlh”…tana turo baki ta karasa mgn…shiko Taheer bai maji me take cewa ba don ya shagala sosae yana kallon bakin nata…ta dago idanun nata tana dubanshi…taa dan jijjigashi ta sake cewa”daddy mgn fa nak”…bata Kai ga karasa mgnr nata ba ya hade bakinshi da nata…Layla ta zaro idanu waje tana mutsu mutsun kwace kanta amma daddy ba rikon banza yayi Mata ba yau…tasa hannunta ta shiga bubbuga bayanshi tana girgiza mai kai amma inaa..daddy bai ma san tanayi ba kwata kwata… ringing din da wayanshi ya fara ne ya dawo dashi hayyacinshi…ya saketa da sauri tareda dafe Kai da hannu bibbiyu yana salati…ita kuwa data samu ya saketa sai ta matsa daga jikinshi da sauri…a hankali Taheer ya mika hanu tareda dauko wayan nashi daya sake daukan ruri for the second time…umma yaga ke Kira..yayi silencing wayan tareda ajiyeshi nn kusa dashi don ko ya dauka ba iya mgn zaiyi ba…ya dauki almost 5 mins a haka kafin ya tattara dan sauran energy daya rage mai ya mike tsaye..ya dauki wayan nashi yasa a aljihu snn ya dago week and tired eyes dinshi ya dorasu kanta…tana zaune tsakiyar gadon kanta kasa…yanaso yace mata zaije masallaci yayi sallah ya dawo amma yasan bazai taba iya yin mgn a wnn halin da yake ciki ba..bazai taba iyawa ba…ya karasa inda take tareda kamo hanunta yana kallonta…ta dago da sauri tana dubanshi da idonta da har  ya cicciko da hawaye…ya girgiza mata Kai snn ya share Mata hawayen ya fita…ita Kuma ta bishi da kallo ganin yanda lokaci daya yanayinshi ya sauya..idanunshi har tsoro suka bata tsaban Jan da taga sunyi…gashi kuma ya fice baiyi mgn ba..ko me yake damunshi oho…a hankali ta koma tareda kwanciya kan gadon tana shafa bakinta da takeji kmr Yana bakinshi ne har yanxu.

Taheer na fita ya wuce dakinshi direct ya shiga bathroom ya sake alwala snn ya fita zuwa masjid da sauri don har ankai raka’an farko…har yanxu mood dinshi bai dawo yanda yakeba.

Yana dawowa yasa duk wayoyinshi a silent snn ya nufi dakinta don yasan har yanxu tana can…tana nn kan gadon har yanxu…ya karasa ciki ba tareda ya zauna va yace mata”kinyi sallah”…ta daga kai ba tareda ta dago idanunta ba…Taheer ya kama kugu yana kallon yanda taketa wani sunkuyan da kai kmr mara gaskia… murmushi ya saki yana girgiza kai kafin ya karasa inda take…ya janyota ya rungume a jikinshi..murya can kasa yace”fadamin meya faru kike sunkuyan da Kai”…Kai ta sake girgiza mai alaman ba komai… Taheer yace”come on baby talk Mana..kina azumin mgn ne”…a hankali tace”babu komai fa daddy..kawai ni bacci nake so inyi”…tana rufe baki ya dauketa cak yana cewa”yanzu kuwa zakiyi bacci babyna..muje in kwantar dake”…ya shiga wutsil wutsil da kafanta tace”dan Allah daddy put me down…a dakina fa zanyi bacci baa dakinka ba”…bai ce Mata komai ba..Kuma bai sauketan ba Saida ya shiga dakinshi…ya direta kan gado yana cewa”karkije ko Ina..am coming”…yana gama fadan haka ya juya ya shiga bathroom…alwala ya sakeyi don already wancan ya karye snn ya fito…ya mikar da ita tsaye yana cewa”we are going to pray”…ta dan dubeshi a kaikaice snn ta turo baki tace”ni na riga nayi sallah na”…bakin nata ya kama yana smiling yace”wnn bakin anjima kadan zaiyi min bayani…sai naji dalilinda yasa yakeso kullum ya ringa tsole min ido”…ta maida bakin nata normal snn tace”Allah da gske da nayi sallah na daddy”…ya dauko dadduma ya shimfida musu..snn ya dauko Mata hijab da dogon riga ya bata kafin yace”ai Nima bance baki yi sallahnki ba baby…kawai nafila ne nakeso muyi”…bata sake mgn ba ta nufi inda yasa dadduman ta tsaya…shima ya karasa ya hau Kai snn ya tada sallahn.

STORY CONTINUES BELOW

Raka’a biyu sukayi snn sukai sallama…bayan ya gama add’u’o’inshi sai ya dafa kanta ya shiga yin wani addu’an…Layla ta lumshe idanunta tana fatan Allah yasa ba abinda take tunani bane…Saida ya gama addu’an snn ya mike yana ninke sallayan…itama mikewan tayi ta ninke nata snn ta ajiyesu inda suke…tana ajiyewa kuwa hadda gudunta ta fada kan gado tareda lumshe ido…Taheer dake kallonta yai murmushi kawai…cikin ranshi yana cewa”komai wayon amarya dai sai ansha manta”.

Saida ya bari ta gama guje gujenta snn ya haura kan gadon shima ya kwanta…snn ya matso jikinta sosae…Layla da gabanta keta faman lugude ta sake yin luf da idonta wai a dole ita bacci take…a hankali Taheer yasa hanunshi tareda janyota jikinshi gaba daya…sai ta matsa da sauri har yanxu Kuma bata bude idon nata ba…ya sake janyota a karo na biyu tareda matseta gam gam yanda ko motsin kirki bazata iya ba…ita Kuma ta sake yin lub wai ita nn bacci take…fuskanta ya dago daidai da nashi snn ya lumshe idanunshi tareda manna lips dinshi kan nata…sai ta bude idanun da sauri tana rarrabasu kmr munafuka😹

Lokaci daya Kuma ta fara kuka don dama kukan na kusa ne tun dazu…ta shiga mutsu mutsu tana son kwace kanta a hanunshi amma ta kasa…kuka take sosae Wanda da bakin nata is free ba karamin ihu zata mai ba…ta shiga Shure Shure da kafanta duk a kokarinta na kwatan Kai amma ko alaman saketa baiyi ba…wnn karon Taheer ya riga yayi nisanda ko mutuwa zatayi a yanxu dai bazai iya ganewa ba…ya manta da komai ya Kuma manta da kowa sai abun da yasa a gaba kawai…Layla tayi kuka..tayi cizo…tayi yakushi all to no avail don Taheer bai ma san tanayi ba kwata kwata…yau ya tsinci kanshi cikin duniyar da tunda yake bai taba tunanin tana existing a doron kasa ba…it’s like the sweetest thing he’ve ever come across iya tsawon rayuwarshi….Layla Kam zuwa yanxu kukan ma ta kasa don idan kaji ana kuka azaba bata Kai azaba bane…tayi tsuru da idanu kawai tana jin zafi da radadin da tunda uwarta ta kawota duniya bata taba jin makamancin wnn azaban ba….in takaice muku dai yau Taheer sai daya zazzage duk soyayyan nan daya dade yanayi Mata kaff tun tana ‘yar mitsitsiyarta har kawo yanxu…abubuwn sai suka hadu suka zame mai guda biyu…ga azabtacciyar soyayya daya jima yana dako na tsahon shekaru…ga tuzuranci shima da ya dade yana fama dashi na tsahon wasu shekarun…gsky dole abubuwan su yima Layla yawa…

A hankali na kwashi sayyada ta nima tareda ficewa daga dakin don in basu sarari…na koma parlor na zauna Ina jira idan suka gama sai in koma in cigaba da dauko muku rahoto.

Lokacin dana koma na sameshi rungume da ita sai jijjigata yakeyi amma kmr bata numfashi…Taheer ya kidime sosae har ya manta cewa shi wai likita ne…jijjigata kawai yakeyi cikin voice dinshi da bai fita sosae yake fadin”baby dont do this to me dn Allah…wake up kinji…I promise bazan kara disturbing dinki ba baby dn Allah ki tashi”…duk wnn surutan da yakeyi Layla batama san yanayi ba don she’s unconscious…sbd tsananin azaba bata san time din da ta sume mashi ba…da sauri ya kwantar da ita tareda sauka daga kan gadon kmr Wanda ya tuna da wani abu…ruwa ya dauko da sauri snn yazo ya shafa mata a jiki da kuma face dinta amma a banza…sai ya ajiye ruwan ya kamo hanunta..ya shiga murza tafin hanunshi cikin nata tafin hanun amma ko gezau…sai ya rungumeta gam a jikinshi lokaci daya hawaye suka wanke mai fuska…cikeda rauni yace”baby wake up dn Allah..am sorry plss..it’s not my intention to hurt you dn Allah ki tashi kinji…I promise bazan sake yi maki abinda baki so ba…kar ki tafi ki barni plss…I will be nothing without you plss”…har yanxu dai Layla ba alaman zata tashi…a hankali ya sa hannu ya sake dauko goran ruwan daya ajiye a gefe..ya bude Goran snn ta zuba ruwan da dan yawa a hanunshi ya watsa Mata a fuska…ta sauke ajiyan zuciya mai karfi sai Kuma ta sake komawa tayi lakwas kmr ba ita tayi ba…Taheer ya sake watsa Mata ruwan a karo na biyu sai ta bude ido a gigice tana kuka tana fadin”daddy am sorry plss…dn Allah kayi hakuri ka kyaleni daddy mutuwa zanyi…wayyo Mami na shiga uku…wayyo ummi wayyo daddy…wayyo Allah naaaa”…da sauri ya maidata jikinshi yana toshe Mata baki da hanunshi…lokaci daya regret din abunda ya aikata ya dira a zuciyarshi…baiyi handling dinta yanda ya dace ba…Allah ya sani yayi iya bakin kokarinshi to be gentle amma it’s like abun yafi karfinshi…shi kanshi bai san duk yaushe ya aikata abubuwan nn ba.. gaba daya yayi loosing mind dinshi that bai tuna komai bai Kuma ganin komai sai abunda yakeyi…yasan dama dole zata wahala a hanunshi tunda she’s too small compared to him…yayi mata girma nesa ba kusa ba..amma ya zaiyi…shima bazai iya jurewa bane da ko kusa ba abunda zaisa yayi hurting nata to this extent…a hankali ya Kai bakinshi saitin kunnenta yace”baby am so sorry plss…kiyi hakuri ba intention dina bane nayi hurting dinki…I just can’t help it ne baby…i couldn’t control myself”…banza Layla tayi tana cigaba da kukanta…for the very first time taji ko ganinshi bata sonyi talkless of sauraron maganganun shi…a hankali ya kwantar da ita nn kan gadon tareda mikewa da kyar ya shiga bathroom…ruwa ya hada mai dan zafi sosae snn ya dawo ya dauketa ha shiga bathroom din da ita…ya sata cikin ruwan zafin a hankali yana runtse idanu…wani uban ihu data fasa bai San lokacinda ya toshe mata bakin da hannunshi ba…cikin lallami yace”baby dn Allah kiyi hakuri ki zauna nn ciki..zakiji dadin jikinki”…Layla banda kuka ba abinda takeyi..sai tuttureshi takeyi tana dukan chest dinshi amma bai saketa ba saida ya tabbata ruwan yayi sanyi snn ya canxa wani ruwan ya sake sata ciki…

Kuka dai yau Layla ta Shashi kmr ba gobe…shima Kuma yasha duka da yakushi ta ko Ina amma bai saurara Mata ba Saida ya tabbatar ta gasu tukunna…yana kokarin yi mata wanka cikin hargagi tace”ni zanyi abuna da kaina ka kyaleni”…sum sum mutuminku ya fice daga bathroom din kmr munafuki…a yanda take din nn yasan idan ya matsa tsaff zata iya tara mai mutane..maganin kar ayi kar a fara…yana fita yai changing bedsheet din da yayi staining snn ya kai shi dayan dakinshi yasa cikin washing machine…a gurguje ya koma dakin wai don karta gama bai nn..

Bayan kmr minti 6 yaga bata fito ba sai yaje bakin kofan bathroom din ya Kara kunne…sai ya jiyo sheshshekan kukanta a hankali…a rikice yace”baby dn Allah what is it”…tace”ni ka kyaleni”…ya kwantar da murya yace”baby kiyi hakuri pls..ko in shigo ciki?..da sauri tace”nidai aah..ni karka shigomin wlh”…Taheer ya dafa kai yanajin yanda take sake dagula mai lissafi…bai sake cewa komai ba kawai ya shiga bathroom din…tana ganinshi ta mike tsaye da niyyan guduwa sai kuma ta zube nn kasa da sauri tareda sakin wani razanannen ihu sbd zafin da taji ya ratsata…da sauri ya karasa inda take ya dauketa snn ya fita da ita daga bathroom…tana dukan kirjinshi tace”ni ka saukeni..ba ruwanka dani wlh ka rabu dani”…Taheer ya direta kan gado yana cewa”I can’t baby…wlh bazan iya rabuwa dakeba kin sani…kiyi hakuri ki dena wnn kukan kinji”…bata sake cemai komai ba taci gaba da kukanta don a yanzu gane takeyi ba wani sonta da yakeyi…da yana sonta kmr yanda yake fada bazai taba azabtar da ita haka ba…a hankali Taheer ya mike zuwa inda first aid box dinshi yake…ya dauko analgesic da ruwa snn ya karasa inda take…ya dagota a hankali…kmr zaiyi kuka yace”baby to ki daure Kisha magani sai ki kwanta..am sorry kinji”…bata ce mai kala ba..ta dai sha drug din daya bata…ya lullubeta da bargo snn ya fita zuwa dakinta…ya dauko mata dan riga mara nauyi snn ya koma dakin…har yanzu bata dena kuka ba dukda muryanta ba fita yakeyi sosae ba…ya karasa inda take tun kafin ma yayi mgn yaji tace”dan Allah ka kyaleni plsss”…a sanyaye ya ajiye rigan nn gefe snn ya shiga bathroom don yin wanka shima…

Yana shiga ya tsaya gaban mirror yana karema kanshi kallo…jinshi yake kmr bashi ba…bai taba tunanin haka abun yake ba…ya lumshe ido yana murmushi daya tuna dadin da ya kwasa…wato da yasan haka auren yake wlh da bai tsaya bata lokaci kafin yayi ba…da tuntuni yasan haka take so sweet da bai daga mata kafa kmr yanda yayi a baya ba…yanxu da yasan dadinta baijin zai iya kwana guda ba tareda ya karayi ba don ba karamin zuma gareta ba…murya can kasa yace”my sweetest baby…Allah ya maki Albarka..Allah ya faranta maki fiyeda yanda kika faranta min..I love you sosae”..

Saida ya gama surutanshi shi kadai snn yayi wanka ya fito…a hankali ya karasa inda take..ya sauke ajiyar zuciya ganin tayi bacci…dama yana sane ya hada da maganinda yasan zai Sata bacci…Allah ya sani tsoron rigimarta yakeyi…dama yasan zai sha rigima da shagwaba a wurinta tunda duk halin tane…ga kuma raki…ya saki kyakyakyawan smile daya tuna yanda take cewa ya rabu da ita…ai bazai taba iyawa ba wlh…not after what happened….

Ya dade nan tsaye kafin ya sa pyjamas dinshi shima ya kwanta tareda janyota jikinshi sosae…rigan daya dauko dazu ya Sanya Mata a hankali snn ya rungumeta…wani irin extraordinary farin ciki yaji yana sake lullubeshi…wato babu abinda yakai samun nutsuwa daga macen da kake so sa farin ciki…jin kanshi yake kmr yana cikin gajimare…Saida ya gama blowing mata kisses all over snn ya sake manneta da jikinshi tsam…shima wani ni’imtaccen bacci mai cikeda tarin ni’imomi da mafarkanta ya saceshi.

(Asuba ta gari Layla da Majnoon😻)Da sauba saura kadan ya makara sallah sbd baccin ba karamin dadi yayi mai ba…rabon da ya samu bacci mai dadi irin haka har ya mance..yana tashi a gurguje ya fada bathroom yayi alwala snn ya tafi masjid.+

Yana dawowa ya zauna a hankali kusa da ita yana kallon yanda har yanxu bata dena sauke ajiyan zuciya ba…ya kai hannu zai tasheta yaji jikin nata ya dauki wani irin zafi alaman da akwai zazzabi a jikin…a hankali ya kama hanunta guda ya rike cikin nashi..sai kuma ya sunkuya dab da fuskata yasa dayan hanunshi yana gyara mata gashinta daya rufe mata fuska…bakinshi daidai kunnenta yake dan hura mata iska a kunne da nufin ya tasheta tayi sallah…cikin bacci Layla taji wani iska mai sanyi na ratsa har cikin dodon kunnenta..ta shiga bude idon a hankali har ta saukesu kanshi…Taheer ya taimaka mata ta mike zaune ganin zata tashi da kanta…har yanxu hanunshi na rikeda nata yace”baby kiyi sallah sai ki koma ki cigaba da baccinki”…dauke Kai Layla tayi daga kallonshi…lokaci daya Kuma hawaye ya wanke mata fuska data tuno azabar daya bata jiya…ko kusa bata taba tunanin daddy can be that dangerous ba sai jiyan…ta riga ta gama ganin true colors dinshi so ba wani sweet mouth da zaiyi mata daga baya…cikeda damuwa Taheer ya matsa kusa da ita sosae…ya janyo kanta tareda dorawa a kirjinshi…yana shafa bayanta yace”don Allah baby kar kimin kuka kinji..akwai fever jikinki idan kikace zakiyi kuka fevern zai sake karuwa ne..am so sorry kinsan i Iove you..and bazan taba hurting naki purposely ba”…a takaice tace mai”baka Sona”…ya shiga girgiza kai yana cewa”baby how could you say bana sonki…Billahi i love you..Kuma you are the only woman da zan cigaba da so har karshen rayuwa ta..yanxu kiyi hakuri in taimaka maki kiyi sallah kinji…I promise bazan wuce limit dina ba”…shiru tayi mai bata sake cewa komai ba…shi Kuma ya mike a hankali snn ya sunkuceta ya Kai bathroom…ba yanda baiyi kan ta sake shiga ruwan zafi ba amma tace bataso…haka nn ya kyaleta ba don yaso ba…ya taimaka mata tayi alwala..snn ya sake daukanta ya fito da ita..ya shimfida Mata sallaya ya Sanya Mata dogon riga da hijab da kanshi snn ta tayar da sallah…shi Kuma yana zaune gefe yana aikin kallonta…yanajin yanda wasu sabbin kaunarta ke sake ratsa ko wace kafa ta heart dinshi…jinta yake tafi gold and diamond tsada a wurinshi…yana jinta can cikin zuciya da gangar jikinshi…

Tana idarwa ta mike da kyar..Taheer ya isa inda take da sauri ya kamata zuwa kan gado…ya kwantar da ita..a hankali yace”kina son wanin abun ne”…idanunta lumshe ta girgiza mai kai alaman babu…bai sake mgn ba shima sai ya haura kan gadon ya kwanta kusa da ita…ya janyota ya sanya jikinshi yana sauke numfashi yace”Allah ya saka maki da mafificin alkhairi baby..Allah yayi maki Albarka..thank you so much for yesterday..I really appreciate”…ya Karasa mgnr tareda manna Mata kiss a forehead dinta da both cheeks dinta…a haka bacci ya sake yin gaba dasu.

11:45am

Daidai wnn lokacin Layla ta fara bude idanuwa zata tashi daga nannauyan baccin da takeyi tun asubah…Taheer da tun dazu ya tashi har yayi wanka ya shirya..yaje ya siyo musu breakfast yanata zaman jiran tashin nata..ya karasa inda take da sauri ganin ta fara kokarin mikewa zaune…ya kama hanunta zai taimaka mata sai ta fizge hanun tana cigaba da yunkurawa zata tashi da kanta…kawai ta fashe da kuka tana jujjuya Kai from side to side tana cewa”wayyo Allah na..wayyo kafana..wayyo bayana..wayyo ko Ina na jikina..wayyo Allah na Shiga uku”…da sauri Taheer ya sake kamata ya dorata kan cinyanshi…ya rufe Mata baki da hanunshi yana girgiza Kai yace”baby dn Allah am sorry..ki dena wnn kukan ko kinaso fever ya sake kamaki ne”…tace”daddy ko Ina na jikina fa ciwo yakeyi..wayyo Allah nidai ka kaini gida wlh”…Saida ya matseta jikinshi snn yace”naji zan kaiki..amma ki bari in fara yi maki wanka..idan kikaci abinci kikasha magani sai in kaiki”…a hankali ta daga mai Kai tana cigaba da hawayenta…shi kuma ya kwantar da ita snn ya wuce zuwa bathroom…ruwa mai zafi ya hada snn ya dawo ya dauketa yai bathroom din da ita kawai sai jinta tayi cikim ruwan zafi…aiko ta fasa wani wahalallen kara tana ita bataso..ita ya Dena mata mugunta…Amma Taheer bai sarara mataba Saida ya gasata tsaf snn yayi Mata wanka ya fito da ita…har ynxu bata dena hawaye ba…da kanshi ya shiryata…ya sa mata gown mara nauyi snn ya kawo mata breakfast din daya siyo ya shiga bata da kanshi…tana hawaye tanaci har suka gama…ya tattara komai ya fita dashi..Allah sarki shi ko ta kanshi ma baiyi don yama manta baiyi breakfast din ba shima…so yake kawai ya gama shiryata snn ya tabbatar yayi mata duk abinda ya kamata.

STORY CONTINUES BELOW

Kusa da ita ya sake komawa ya zauna…a hankali tace”daddy to baza muje gidan ba”…yace”baby bakida lfy…ki bari idan kika warke zamuje..ba jiya ma muka je gidan ba”…yana rufe baki tace”Allah daddy nidai yau nake son zuwa…nidai kawai ka kaini”…yace”meyasa”…tace”ni bazan sake kwana a gidan nn ba daddy..baka Sona”… murmushi sosae Taheer ya saki don mgnr nata ya bashi dariya…Yana shafa kanta yace”baby wai why kike cewa ban sonki…ya kamata ace kinfi kowa sanin irin sonda nake maki…Ina sonki more than any other thing a doron kasa”…ya karasa mgnr yana Jan dogon hancinta still yana murmushi…saida ta dago fuskanta tana kallonshi snn tace”idan kana sona to meyasa ka kusa kasheni jiya…Allah daddy saura kadan in mutu sbd azaba”…Taheer da har yanxu ke smiling yace”come on baby ta ya zaayi in kasheki… believe me ba laifi na bane…I wasn’t on my right senses na aikata duk abunda na aikata…ke dince baby baa mgn… saura kadan ki zautar dani wlh…you are the sweetest…I love you sosae”…lumshe idanunta tayi tana boye face dinta a kirjinshi tace”to abar mgnr daddy..ni kunya nakeji”…yasa hannu yana sake matseta a jikin nashi before saying”an bari my baby..your wish is my command”…

A bangaren AY Gambo kuwa he’s totally depressed…Allah ya sani ba karamin so yakema Layla ba…sai daya riga ya gama sa rai snn ya fahimci matar wani ce…a ranan ko bacci kasawa yayi…yanda yaga rana haka yaga dare..onthe other side Kuma yana tunanin hanyar da zaiyi dealing da Sameera da Class Rep dinsu Layla..Wanda shine sanadin duk halinda ya samu kanshi ciki.

Washegari yana shiga school ya tura a Kira mai class rep din…ba bata lokaci kuwa sai gashi yazo…AY ya daure fuska kwarai snn yace”inaso ka fadamin wacece wnn yarinyar da ka kawo kace sis din Jakada ce”…da sauri class rep din yace”Sister dinta ce sir”…tun bai rufe baki ba AY ya daga mai hannu alaman ya isa…ya jingina jikin kujeran da yake zaune a kai snn yace”I want you to tell me the truth..na rantse da Allah idan ka sake ka Kara yimin karya ranka sai yayi mummunan baci..zakasha mamaki na wlh”…calss rep da mamaki ya kamashi don bai San meke faruwa ba…shi dai a iya saninshi Sameera tace mai Layla sister dinta ce…lokaci daya jikinshi yayi sanyi kafin yace”Allah sir gaskiyana nake fada maka..ita ta sanar dani cewa ita yayar tace”… AY shiru yai yana kallonshi for some secs snn yace”ok naji…yanxu fadamin a ina ka Santa..snn menene dalilinda yasa kace zaka hadani da ita sbd ta shawomin kan Jakada..but mind you karka kuskura kamin karya..I want nothing but the truth idan kayi karya ma zan ganoka”…a hankali class rep din yace”wlh sir duk abinda na fada maka gsky ne…tazo school din nn ne tana tambayan class dinmu…sai nace mata zan rakata don nima a class din nake…muna tafiya ne take cemin akwai sister dinta a class din namu sunanta Maryam Taheer Jakada..wai wurinta tazo…sai nace mata bata shigo school ba yau tun jiya wani lecturer dinmu ya tura in kirata bata zoba…sai tace bata fara zuwa gida ba wai tayi tunanin tana school shine ta biyota..shine ta tambayeni wai meke tsakaninka da ita..nace mata ban saniba..tace idanma sonta kake ita kadai ne zata ita shawo maka kanta…amma tanaso in hadaka da ita tanaso tayi mgn dakai…shine na fada maka snn na rakota office dinka…wlh sir iya gaskiya na fada maka..ni abunda tacemin knn”….tunda class rep din ya fara mgn AY yayi shiru yana maimaita Innalillahi cikin zuciyarshi…mamakin makircin Sameera kawai yakeyi…duk don tana son Taheer take hada munafurci haka kawai sbd bai aureta ba ya auri wata…wato shima class rep din tayi using dinshi ne sbd ta cimma burinta…Saida ya dade yana sake sake cikin ranshi kafin yace”shknn zaka iya tafiya..amma inaso ka tabbatar da abinda ka fada min gsky ne.. idan nayi bincike na gano kaima kayimin karya bazakaji dadi ba wlh”…da sauri class rep din yace”na yadda sir”…daga nn bai sake mgn ba ya fita daga office din yana tunanin abunda ke faruwa..

A bangaren love birds kuwa yau Layla yini tayi tana zuba shagwaba son ranta…dama ya lafiyar kura…ba dalilin komai ma shagwaban takeyi balle Kuma yanxu da takeda kwakwkwaran dalili…Taheer duk yau a gida ya yini..sallah kadai ke fitar dashi kuma yana idarwa zai dawo…da tace Abu kaza takeso zaiyi Mata da rawar jiki…daga Safiya zuwa ynxu yayi lallashi kusan sau 20…motsi kadan zata fara kuka wai ita ko ina na jikinta ciwo yake…sai yau Taheer ya tabbatar da shagwaba da rakin Layla da ummi keta fada…Ashe da duk wanda takemai ba komai bane…yanxu ne yake ganin ainihin ta6ara da shegen rakin tsiya..

STORY CONTINUES BELOW

Yanxu ma tana kwance kan gado sai massaging kafafuwanta yake..tun dazu take mai mita wai ita komai na jikinta na mata ciwo…yanayi yana sakin murmushi time to time…duk ya tuno ihun da ta ringa mai dazu sai abun ya bashi dariya..duk wahalan daya bata jiya Saida ta fanshe kayarta don ko abinci saidai ya bata a baki…ko toilet zata shiga haka zatace ita bazata iya takawa ba saidai ya dauketa..haka yaita jigila da ita from one place to another…

Cikin lumshe ido alaman bacci na son daukanta tace”daddy”…ya amsa Mata”naam my baby”…Saida ta turo baki snn tace”promise me bazaka kara yin wnn abun ba dn Allah…wlh idan kace zaka yi mutuwa zanyi daddy”…yana cigaba da yi Mata massage din yace”stop saying Zaki mutu babu inda zakije ki barni..I can’t do without it…bazan iya hakuri ba but i promise I will be gentle..bazaki sake jin zafi ba”…yana rufe baki ta shiga bubbuga kafanta da yake massaging tana kuka tace”Allah daddy bazan yadda ba…nidai ka maidani gida…in ba haka ba in fadama ummi”…dariya ya saki sosae snn ya dagota ya dorata jikinshi…ya lumshe ido yanajin yanda yanayinshi ke sauyawa…a yanxu ma da zata amince he’ll do it again and again amma yasan bazata taba yadda ba…wnn shagwaban nata na daya daga cikin abubuwanda sukesa yake Kara sonta kullum…bai taba gajiya da kasancewa tareda ita…yayi mata irin rainon da yakeso…ta Kuma kasance irin matar da yakeso…a hankali yace Mata”to naji baby ban karawa..stop crying”…”daddy kayi alkawari”…ta fada don ta tabbatar da ba wasa yake Mata ba…ya matseta jikinshi yana cewa”nace maki ban karawa..kiyi bacci dn Allah”…ta makale kafada tace”sai kayi alkawarin bazaka sake ba snn zanyi baccin”…tana rufe baki yace”to bari mu sakeyi ynxu kinga daga nn sai inyi maki alkawarin”…tun bai gama mgn ba ta daka tsalle tareda sauka daga jikinshi…Taheer yasa dariya sosae yana kallon yanda ta mike tsaf kmr ba ita ke cewa bazata iya takawa ba…yana girgiza kai yace”dn Allah baby ki yadda mu sakeyi ko sau dayane..gashi nn kafan naki ya warke gaba daya”…yana rufe baki ta kama kugu da duk hannayenta tareda sunkuyawa kmr mai yin ruku’u…ta zuba mai idanunta dake shining as a result of hawayen daya taru ciki tace”Allah daddy bai dena ba..bakaji yanda bayana kemin ciwo ba kmr zai 6alle”…yace”naji..zo ki kwanta idan ba hakaba kuma am going to change my mind”…yana rufe baki ta shiga takawa a durkushe kmr mai labour har ta isa kan gadon ta kwanta…shima ya matsa kusa da ita tareda lullubeta…yanata faman kallonta yana smiling har bacci yayi awon gaba da ita…yayi mata kiss a forehead dinta kafin yace”have a wonderful sleep my juciest baby..I love you so much”..

Washegari dai ta tashi da sauki sosae..amma har yanxu bata dena complain din ko ina na jikinta na mata ciwo ba…tare suka shiga kitchen suka hada breakfast dinsu..don cewa tai bata yadda yaje siyan abinci ba…bayan sun gama kowa yaje yai wanka ya shirya snn suka sauka don yin breakfast din…bayan sun zauna dinning tana kokarin yin serving dinshi ya hanata..shi yayi serving nata snn yayi ma kanshi…suna cin abincin yana kallonta..har yanxu ya kasa mance how sweet she was in bed…he can’t wait to have her for d second time..he’s just eager…ita kuwa Layla cin abincinta take hankali kwance…suna gamawa Kuma kowa ya dauki abunda zai bukata suka fita..ita zataje school..shi ma zaije clinic…

A kan hanya ne yake tambayanta why bata tambayeshi yanda sukai da AY Gambo ba…a hankali tace mai”inajin tsoro ne daddy…I don’t want you to get upset with me again”…nan ya bata labarin duk yanda sukayi da AY din…da mamaki sosae Layla ke kallonshi tace”yanxu daddy you mean duk abubuwan da suka faru plan dinta ne knn”…yana daga kai yace”wlh..ni kaina ta bani mamaki”…”ikon Allah..dama she’s this heartless bamu saniba daddy”…Taheer yace”ki bari kawai…I will definitely find a way to deal with her..shima Lecturer din naku yace bazai barta ba”…Layla da har yanxu mamaki bai saketa ba tace”amma daddy kasan me”…yace”no sai kin fada”…Saida ta kamo free hand dinshi ta rike snn tace”duk ta aikata wnn abubuwan ne because she loves you…tana sonka sosae daddy..har yanxu bata dena sonka ba”…ta karasa mgnr jikinta a sanyaye sosai..harga Allah tsoro take kar taci gaba da bibiyan Taheer har ya zama watarana zaiji ya fara sonta shima…hanunta dake rikeda nashi ya sake rikewa snn yace”bata Sona baby..da tana sona zata tayani son abinda nake so…ni ke nakeso ba itaba..you are the only woman I love”…wani murmushi ya subuce mata jin kalamanshi…ba karamin faranta mata rai sukayi ba…at leats dai ta yadda da irin kaunar da yake Mata…a haka har suka isa school dinsu…ya dauko wayanta daya fito mata dashi ya bata..yana kallon cikin idanunta yace”I don’t want him to see you baby”…tadan wara idanu kafin tace”who are you talking about”…”your lecturer..baby da gaske yake sonki wlh ba da wasa ba..that’s why am jealous banaso ya ringa ganinki yana sakejin yana sonki”…Layla ta karyar da kai tana cewa”come on daddy..wnn ba abun damuwa bane fa..da bakinka kace yace muyi hakuri bai san inada aure bane..yanzu Kuma da yasan inada auren am sure ba abinda zai sake shiga tsakanina dashi..so ka dena damun kanka pls”…a hankali Taheer ya daga Mata Kai yana murmushi…ita Kuma ta bude motan ta fita tana daga mai hannu…yana ganin tafiyanta shima ya tafi.

Yana isa clinic tun kafin ya bude office dinshi ma wata nurse tazo tana sanar dashi yayi bakuwa tun dazu..ya dan dubeta da mamaki yace”bakuwa Kuma..ba patient bace?..”nurse din tace”tace she’s not your patient..wai tanason ganinka ne”…bai sake cewa komai ba yace a kirata…ya bude office din ya shiga…ko zama baiyi ba ta turo kofan office din ta shigo…ya daga Kai da mamaki sosae ya shiga binta da matsiyacin kallo…tun kafin yai mgn tace”don Allah listen to me doctor..I need to talk to you plss”…tana rufe baki ya dauki wasu files dake kan table dinshi ya jefeta dasu..fuskanshi na nuna tsananin bacin ran da yake ciki yace”so you have the audacity to come into my office bayan duk abubuwan da kika aikata…kinada guts”…Sameera da har ta fara hawaye tace”ka tsaya ka saurareni doctor..wlh duk abubuwan dana aikata na aikatasu out of love.. son da nake maka yasa bazan iya jure ganin kana tareda wata ba..ka yafemin plss”….tana rufe baki ya sake jefo mata stepler dake kan table din nashi yace”Sameera ki bar min office dina nace…I don’t want to see you..nor do i have the patience to listen to you..leave my office right now”.. bata sake yunkurin mgn ba ta fita..don ta fuskanci ranshi bace yake da ita sosae…wnn wulakancin da yake mata shi yake kara tunzurata tana aikata abubuwan da ba daidai ba…

Shiko Taheer komawa yai kan kujera ya zauna dabas yana sauke numfashi…he can’t believe tana can tana kokarin rabashi da matarshi Kuma wai har takeda nerves din da zatazo office dinshi tace he should listen to her…listen to what..duk abubuwan data aikata basu isheta ba sai tazo office dinshi ta sake lalata mai zuciya…tsaki yaja mai karfi tareda zaro phone dinshi daga pocket dinshi…maybe sbd taga sunyi shiru dagashi har AY din shiyasa take ganin taci bulus…Kai tsaye number din AY da har yanxu baiyi deleting a wayanshi ba ya lalabo… without waste of time ya shiga dialing number din nashi..Ringing biyu a na uku AY Gambo da zuwanshi school din knn yayi picking call din…bayan sun gaisa yake bama Taheer lbrin yanda sukayi da class rep dinsu Layla…wani mamakin ya sake kama Taheer wato Sameera ta wuce duk tunaninsu..knn shima kanshi class rep din tayi using dinshi ne ba tareda ya sani ba…shima Taheer lbrin yanda sukayi da ita yanxu a office dinshi ya bashi snn ya dora da fadin”yanxu hukuncin dana yanke zanje har gidansu in samu mahaifinta inyi masa bayani..inaso ya shiga tsakanina da ita don nan gaba idan ta sake yunkurin rabani da matata kotu ce zata rabamu da ita..yanxu ma sbd Ina ganin girman mahafinta ne kuma batayi succeeding ba amma wlh da kotu zan makata..so idan kanaga zamuje gidan nasu tare sai muje..idan kuma kana ga akwai hukuncin da zaka dauka shknn”…Taheer na gama mgn AY yace”ba damuwa sai muje gidan nasu tare..da Ina tunanin in hadata da hukuma amma kuma naga kmr bai kamata in kaita kara ba tunda she’s a woman..ko ba komai Ina respecting Mata sosae..so taci albarkacin wnn respect da nake dashi a kan Mata..and InshaAllah zamuje tare wurin mahaifin nata..kaga koda next time ta sake wani abun muna da right da zamu kaita koma inane tunda mun hadata da iyayenta bata bari ba”…Taheer yace”shknn..yanxu yaushe kake free sai muje?..”AY yace”gaba daya yau am free..class daya gareni kuma 10 to 12″…”alright zan tura maka address din gidan zuwa anjima sai mu hadu a can”…Taheer ya fada mai…shima yace”ba damuwa Allah ya kaimu..na gode sosae”..nn sukayi sallama..Taheer ya tura mai address din gidansu Sameera kmr yanda yace..

+

A can school kuwa bayan sun gama lectures Layla ke bama Hanna lbrin duk abinda ya faru..Hanna tayi mamaki sosae tace”shiyasa nayita kiran wayanki bai shiga..gsky wnn matar ba karamar muguwa bace..ynxu kinga amfanin rashin boyema miji irin wnn issues din koh”…Layla tace”na gani wlh..na kumayi dana sani sosae..inata so in kiraki to bai bani wayana bafa sai yau”…Hanna na gyada kai tace”Allah ya kiyaye gaba..ynxu sai ki gyara next time…nima  na kwana biyu ban zuwa sch din sbd banjin dadi”…Layla ta Dan zaro idanu hadda gyara zama tace”Hanna kawai ki fadamin ciki ne dake..ni banga abin boyewa ba”…itama Hanna murmushi tayi kafin tace”two months”…Layla hadda fasa ihu tace”I can’t wait wlh..kice mun kusa muyi ‘da ko ‘ya very soon”.. Hanna na dan hararanta tace”bazaki gane bane babe..laulayi wahala wlh..ko abincin kirki ban iya ci ga fever kullum dashi nake kwana..ga shegen bacci kmr as’habul Kahfi..ga Kuma exams zamu fara very soon..ni ban San ya zanyi da karatu ba”…Layla tace”ba wani wahala kin fiya raki ne kawai..haka Zaki cigaba da hakuri har ki fita daga first trimester”…cikeda tsokana Hanna tace”babe fadamin..ya kikaji fisrt night din..akwai dadi koh”…wani zaro ido Layla tayi tana girgiza kai tace”ke Ina wani dadi..saura kadan in mutu wlh”…dariya sosai Hanna ta kwashe dashi tana fadin”yarinya taji maza..ni dama nasan duk kika shiga hanun mutumin nn sai kinci kaniyarki wlh..wnn soyayya da ake maki ai bazai tafi a banza ba..sai ya fanshe kayarshi tasss”…tsaki kawai Layla ta saki tana cigaba da hararanta…Hanna bata da kirki wlh..wato dariya ma take mata…

Taheer da AY kuwa sunje gidansu Sameera kmr yanda suka tsara..sun yima mahaifinta bayanin komai..sun Kuma ce mai ya tsawatar mata don idan ta sake aikata wani abu makamancin haka a nn gaba to hukuma ce zata rabasu da ita…da yake mahaifin nata is responsible and reasonable man…ya kirata yayi Mata fada sosae a gabansu kmr zai sa mata duka…ya Kuma ce lallai lalla ta nemi yafiyarsu…haka duk ta basu hakuri tana kuka….su Kuma sukayi sallama da dad dinta suka tafi.. the next time ta sake aikata wani abun dama kawai saidai tajita a hannun hukuma…wnn din ma don Taheer na respecting mahaifin nata ne shiyasa ya sanar dashi…tun lokacinda yazo ya sanar dashi ya fasa aurenta yasan cewa mahaifinta babban mutum ne.

Wannan kenan

Kwanaki nata tafiya yayinda Layla is becoming very occupied with her studies…kusan kullum sai sunyi test as exams dinsu is approaching…ta dage karatu sosae…duk abinda bata ganeba Taheer na koya Mata…har yanxu Kuma ba abinda ya sake shiga tsakaninshi da ita…duk yanda yakai ga so tana fara kuka yake hakura ya kyaleta…gaba daya a tsorace take da al’amarin don ba karamin wahala tasha a hannunshi ba last time…fannin girki kuwa zaace an samu improvement sosae…don tana iya girkinta ynxu ita kadai without watching any video…dukda bawai ta kware sosae ba amma she is really trying…taste din abincin ma na yanxu yafi na baya…Taheer na alfahari da ita ta wnn fannin Kam..Sam bata barinshi yace zaije siyan abinci yanxu..don bataso a kwace Mata shi..musamman yanda taji ana maza basuda tabbas..so bazata bashi single chance da zaisa  ya hadu da wata macen har su fara soyayya ba…

His only problem is yanda tun first night dinsu taki bari wani abu ya sake shiga tsakaninshi da ita…hakurinshi na gab da karewa don yanxu bazai iya hakurin da yayi a baya ba sbd ynxu yasan dadinta so bazai iya taking so much time without having her for the second time ba.

STORY CONTINUES BELOW

Yau ma kmr kullum suna zaune bedroom dinshi..shi yanata faman aiki a laptop ita Kuma ta baje handouts dinta kan gado tana karatu don gobe tanada test karfe 9…wayan Taheer dake gefenshi ya fara ringing…yasa hannu ya dauko wayan tareda picking call din..yasa a speaker snn ya ajiyeta kan laps dinshi Yana cigaba da aikinshi yace”Ummi barka da dare”…a daya bangaren ummi tace”barka dai Taheer ya gidan”…yace”gida lfy Lou Ummi”…ummi tace”to madallah…kana jina”…”inaji ummi”…ya fada idonshi kan laptop dinshi…ummi tace”dama bikin Asma’u ne dana fada maka..to wnn satin ne..gobe Nafee zata biyo jirgin yamma ta sauka a nn..idan Allah ya kaimu jibi Alhamis zamu tafi Dutsen gabaki daya”…Taheer ya Dan dakatar da aikin da yakeyi yace”ummi wace Asma’u kike mgn wai”…ummi tace”Asma’u mana ‘yar gidan yayan Awwal dake Dutse..bana fada maka zancen bikin bane?..yace”ummi kin fada min amma wlh na manta..Allah ya kaimu lokacin.. Saturday ne daurin auren koh”…ummi tace”eh asabar ne…sbd haka ka dauko Layla ka taho da ita gida gobe..inaso ta kwana a nn don jibi sammako zamuyi InshaAllah tunda ba jirgi zamu bi ba”…Taheer buda ido yayi sosae yana cewa”in kawota gida Kuma ummi…ba tare zamu taho da

Ita ba…ai yayi wuri ta tafi biki tun yanxu”…a fusace ummi tace”bikin ‘yar wan uban nata kake cewa yayi wuri ta tafi yanxu..wane irin mutun ne Kai wai..ka maidani abokiyar wasanka koh”…yayi kasa da murya yace”wlh ba haka bane ummi..kawai dai gani nayi ta tafi biki tun yanxu kusan sati guda fa knn zakuyi a can..kuma kinga tana zuwa makaranta fa exam ma zasu fara”…Saida ya gama mgnrshi a takaice ummi tace”bani Laylan muyi mgn”…ba musu ya Mika Mata wayan…tana amsa tace”ummi Ina yini”…ummi ko amsa gaisuwan batayi ba tace”ba kince min Kun kusa fara exams ba Layla..ko Kuna wani abun sosae ne a makarantan?..”Layla ta dauke kanta daga kallon Taheer daketa girgiza mata kai wai tace eh suna lectures…snn tace”ba abunda mukeyi ummi…duk revision ne sai tutorials..test ma idan nayi na gobe saura guda daya mu gama Kuma ba cikin week din nn zamuyi ba”…ummi tace”to Alhamdulillah..yanxu ki hada kayanki kaff..gobe zai kawoki nn..jibi Kuma in Allah ya yadda zamu tafi Dutsen”…Layla na murmushin farin ciki tace”toh ummi”…sai ta mikama Taheer daketa kallonta da wani expression kan fuskanshi wayan…ya amsa ya Kara a kunne…ummi tace”to tace ba abinda zatayi a makarantan..don haka gobe lallai lallai ka kawota gidan nn..idan ba hakaba kuma zan bata maka rai wlh”…tana gama mgnrta ta kashe wayan…Taheer ya ajiye wayanshi yana duban Layla daketa faman murna zataje biki yace”so baby kin matsu kije ki barni koh…baki tausayina…baki tunanin halinda zaki tafi ki barni a ciki right?..”Layla ta dan rausayar da kai tace”ba haka bane daddy..kawai dai inason zuwa bikin..kuma da gaske ba abinda zanyi missing a school”…idonshi na kanta yace”baki amsamin tambayana ba ai”…ta dan turo baki gaba tana cewa”Ina tausayinka mana daddy..ai ba dadewa zamuyi ba Kuma kaima ba zakazo daurin aure ba”…shiru kawai Taheer yayi yana kallonta.. sai can Kuma yace”tunda haka kika zaba shknn…ynxu bari in karbi na satin d zakije kiyi a can..kinga shknn nima bazan damuba”…Layla ta gwalo idanuwa waje tace”don Allah don Annabi daddy kayi hakuri..wlh na fasa zuwa bikin..zancema ummi na fasa zuwa Allah”…ya ajiye system dinshi kan bedside snn ya shiga matsawa kusa ita yana fadin”ai kin riga kin gama mgn yarinya.. tunda kikace mata ba abunda zakiyi..ynxu ko kin Kira kince ba haka bane ba yadda zatayi ba..cewa  zatayi ni nace ki fada haka tunda banso kiyi tafiyan..so it’s better ki bani hakkina yanxun nn tunda daga gobe ba Kara ganinki zanyi ba..na dena tausaya miki nima tunda ba tausayina kike ba”…yana gama mgn ya kamota tareda hadata da jikinshi sosae…Layla ta shiga kokarin kwatan kanta amma ta kasa…ya riketa gam gam yanda ko kwakwkwaran motsi ta kasayi…Saida ya fara rabata da kayan jikinta snn ya shiga yin abunda ya dade yana bege duk tsawon kwanakin nn…lokaci daya ya fita a hayyacinshi fitt…ya manta da mgnr daya fada mata cewa he is going to be gentle…gaba daya ya susuce burinshi kawai ya Kai inda yake son zuwa…Layla banda kuka ba abinda takeyi…amma Taheer bai ma san tanayi ba…ya riga yayi alkawarin bazai iya bari ta tafi har na tsawon sati ba tareda ta bashi hakkinshi ba..bazai iya jurewa bane…yayi nisa sosae cikin abinda yakeyi..yayinda duk wani ihu da kukanta ya dena jinsu yanxu…he’s having the fun of his life..yaudai Taheer ya toshe kunnuwanshi tass…bai saurara Mata ba Saida yaje inda yakeso…ya Kuma tabbatar da he’s satisfied snn ya saurara Mata…ba don yana tausaya Mata ba da babu abinda zai hanashi going for another round amma sai ya hakura….Layla tayi ‘dai’dai kan gado kmr matacciya tanata kuka tana Kiran sunan duk Wanda yazo bakinta…shi kuwa cikin kasalan s

daya lullubeshi ya sanyata a jikinshi tareda matseta gam…yanajin yanda yake jinta har cikin jini da tsokarshi…Saida suka dauki tsawon lokaci a haka kafin ya ajiyeta a hankali snn ya mike zuwa bathroom…ruwan zafi ya hada snn ya sake fitowa ya dauketa yai cikin bathroom din da ita.

Yauma Saida ya gasata sosae snn yayi Mata wanka da kanshi ya nadota a towel ya fito da ita..har yanxu mutuniyarku bata dena kuka bafa…Taheer yasa mata kayan baccinta..snn ya bata pain releive tasha ya kwantar da ita tareda blowing Mata kisses ta ko ina..kafin ya koma bathroom don yin wanka shima…wnn karon ma kmr wancan…ya sameta  fiye ma da yanda yake tunani …gani yake babu namijin da ya kaishi dacewa da mace mai tarin ni’ima kmr shi…baby is just different..komai nata is perfect shiyasa kullum sonta karuwa yakeyi cikin zuciyarshi…Saida ya gama wankan snn ya fito…a hankali ya haura kan gadon kusa da ita bayan ya gama shirin kwanciya..ya kwanta kusada ita tareda janyota jikinshi…sai Kuma ya shiga tunanin tafiyar da zasuyi gobe…Allah ya sani dn dai ba yadda zaiyi da ummi ne amma da ba inda zaa Kai mai matarshi…gaba daya baison yin nesa da ita yanzu…not for a second…haka nn kawai zaa dauke mai ita suje suyi kusan sati a wani gari…shi baice bazata je biki ba amma da a bari Saturday in zaije daurin saure sai su tafi tare..idan suka kwana daya ranar Sunday sai su dawo…amma ummi ta dage sai sun tafi tare..Allah ya sani shidai bakaramin shiga hakkinshi akai ba..yasan zaiyi missing matarshi sosae ba kadan ba…da wnn tunanin shima bacci yayi awon gaba dashi.

Washegari ma da kanshi ya taimaka Mata tayi wanka snn ya sake sawa ta shiga ruwan zafi..shi yayi mata komai har Shirin tafiya school…ita kuma har yanxu bata dena kumbure kumbure tana fadin jikinta na mata ciwo ba..Taheer saidai yayi dariya kawai hadi da girgiza kai…rigimar baby sai ita wlh.

Tun dazu yake zaune cikin mota yana jiranta..daga taje ta dauko hijab su tafi shine har yanxu bata fito ba kusan minti biyar yana jiranta…ya duba agogon hanunshi yana sauke numfashi..bai son yai lattin zuwa clinic don yanada abubuwan yi sosae…can sai gata ta fito bakin nn a tsuke..Taheer ya bita da kallo mayafi ta yafa orange Wanda ya shiga da riga da skirt na atampa dake jikinta maimakon hijab da yace mata…Saida ta karaso inda motar ta bude ta shiga snn yace”baby wnn ne hijab din Kuma”..tana sake turo dan bakinta tace”daddy ni jikina namin ciwo..idan nasa hijab nauyi zaimin wlh..so plss let me”…Taheer ya jinginar da kanshi kan kujera yana binta da kallo..dukda ba make up tayi applying sai yaga tayi mai wani shahararren kyau kmr tayi heavy make up..uwa uba daurin dankwalinta daya zauna das a kan nata sai kace ba hannu ne yayi shi ba…bai sake ce Mata komai ba ya kunna motar suka tafi…har ga Allah ba da son ranshi zataje makaranta a haka ba..yasan ba kowane namiji ne zai iya dauke ido a kanta ba..amma bazai iya da rigimarta ba..yasan duk tanayi ne sbd taji haushin wahalan daya bata jiya…haka yaita Satan kallonta yana danne dariya dakeson kufce mai..ita wai bata yadda ba ta daure fuska😅

12 saura ta kirashi a waya tace mai ta gama abinda zatayi yazo ya kaita gida…yace Mata gashi nn zuwa…ba bata lokaci kuwa sai gashi yazo…maimakon su nufi gidan ummi kmr yanda tayi tunani sai taga sun dauki wani hanyan.. tana dubanshi tace”daddy Ina Kuma zamuje..ummi fa tace ka kaini gida”…yana cigaba da tukinshi yace”zan kaiki mana baby amma ba yanxu ba..so nake sai dare idan mukayi picking su Nafeesa daga airport sai mu wuce gidan gaba daya”…ta marairaice mai tace”nidai dn Allah daddy ka kaini ynxu”.. ya juyo ya dan kalleta snn yace”baby kin gaji da ganina koh..Ina takura maki abi?..”tace”Ni ba haka nake nufi ba..kawai dai inaso inje gidan ne”..Taheer shiru yayi mata..kmr bazai sake mgn ba sai can Kuma yace”to ynxu muje wani wurin muci abinci..muna gamawa sai mu koma gida ki hada kayan naki sai in kaiki can”.. Kai kawai ta daga mai tareda kwanciya kan seat din da take..har yanzu bata bar jin jikinta kmr anyi mata dukam tsiya ba..ba karamin wahala tashaba jiyan nn..dukda bai kai na first encounter dinsu ba still tanajin jikinta a gajiye..ga bayanta da cinyanta har yanx basu dena yi mata ciwo ba..ta lura gaba daya daddy ficewa hayyacinshi yakeyi duk yake mu’amala da ita… murmushi ta saki data tuna mgnr da suka tabayi da Hanna…wai idan mijinki bai takura maki baki cika a kiraki da mace ba…haka tayita sake sakenta har suka isa wani restaurant mai kyau..bayan ya samu wuri yayi parking sai ya bude mota ya fita…ta bude ta fita itama snn suka shiga ciki.

Karfe 8 daidai yayi musu a airport don daukan su Nafee… jirginsu bai sauka ba sai 8:15..suna nn zaune cikin mota mutanen dake cikin jirgin suka fara fitowa…Taheer ne ya fara bude motan ya fita snn ya bude mata itama ta fito…yaran ne suka fara hangosu…aiko sukayo wajen da suke da gudu..gaba daya kan Taheer sukayi suna rungumeshi kowa yana fadin”daddy..daddy”…shima rungumesu yayi sosae yanabinsu da kiss a goshinsu daya bayan daya..Nafeesa ma ta karaso inda suke face dinta da murmushi tace”angon baby”.. Taheer ya dan kalleta ta gefen idonshi yana dan kauda Kai…wai ita batasan yanajin nauyinta bane..shi kanshi bai taba tunanin akwai rananda zatazo yaji yanajin kunyar Nafeesa ba..yarinyar da suka taso tare tun suna kanana..ya tuna irin fadan da sukeyi tun da can…ya saki wani murmushi yana shafa kanshi..bai taba tunanin Nafeesa ce zata haifi macen da zaiyi ma matsanancin so irin haka ba..ko da yake Allah ba yanda baya al’amuranshi…Layla ce ta karasa tareda daukan hibba dake kusada Maman nata tana fadin”Mami sannunku da zuwa”… Nafeesa na gyada kai tace”yawwa”..shi Kuma Taheer ya bude ma yaran mota suka shiga..itama Nafeesan ta shiga..Layla da shi duk suka shiga snn yaja motar suka bar wurin.

Suna isa gida yaran suka bude mota suka shiga ciki a guje..Taheer ya fito tareda zagayawa ya budema Layla itama ta fito…Nafeesa dake kallon abinda yakeyi tai murmushi kawai tana girgiza Kai..wai yarinya karama yakema wnn abun sai kace wata babba.. ta bude itama ta fito..tare suka nufi entrance din gidan..+
Su ummi na zaune parlor da alama dama suna jiran zuwan nasu ne…yaran ne suka fara shiga snn suma suka shigo..Kai tsaye Nafeesa ta karasa inda ummi take ta bata kyakykyawar runguma tana fadin”fatan mun sameku lfy ummina”…itama ummi ta rungumeta tana cewa”lfy Lou muke Nafee”..sai Kuma ta saketa ta shiga dube dube tace”ina wnn mara mutuncin take”… Al’ameen ne yace”gata can a bayan daddy”…ummi tasa hanu ta janyo Hibba dake boye bayan Taheer tace”zo nan don gidanku..ke baki iya gaida mutane bane..duk yayyenki sun gaisheni kece mara kunya koh”…gaba daya suka sa dariya…bayan sun zauna gaba daya suka shiga gaisawa dasu ummin…Taheer ya mike ya fita tareda su Al’ameen suka shigo musu da kayansu ciki…daga nn Kuma suka nufi dinning sukayi dinner tare..sunayi suna dan taba hira..shikam Taheer kacokam hankalinshi na kan babynshi…kawai tunanin yanda yau zai kwana ba tareda itaba yakeyi…Anya kuwa zai iya..tunda akai bikinsu zuwa yanxu in ka cire case dinsu da AY bai taba kwana ba tareda itaba..ko a wancan karon ma yaji jiki balle yanxu da suka riga suka zama daya..duk sai yaji abincin ma ya fita a ranshi..Sam bai wani ci sosae ba ya mike tareda komawa parlor..
Bayan sun gama suma duk parlon suka koma..nan Kuma aka sake dasa sabon hira kmr irin sun shekara basu hadu ba…umma ce ta lurada yanda Taheer duk baida walwala sai tace”kai lafiyanka kuwa”..maimakon yayi mgn sai ya karyar mata da kai kmr karamin yaro.. exactly yanda yake mata idan yanaso ta tausaya mishi… murmushi kawai ummi tayi don tasan da kyar idan ba kan tafiyansu da Layla yake wnn abun ba…sai ta mike tareda kama hanunshi shima ya mike..tace”muje ka fadamin menene matsalanka”…haka Taheer ya shiga binta a baya kmr bindi…ummi da Nafee suka bisu da kallo..ummi na tabe baki tace”ai ko me zakayi saidai kayi wlh..baka isa ka hana yarinyar nn zuwa bikin ‘yar uwarta ba”…Nafee tace”ummi hanata zuwa yayi”… still bakin ummi a tabe tace”yo meye banbancin abinda yake shirinyi da hanata zuwa din..wani wai bazamu tafi da itaba saidai in zaizo daurin aure ran asabar ya tafi da ita..ranan lahadi kuma ya sake dauko kafa ya dawo da ita..sbd ance mai na farajin tsoronshi”…Nafeesa dariya ta danyi kafin tace”Ummi da kin barshi Mana..matarshi ce fa”…itama harara ta samu daga wurin ummi tareda fadin”bai isaba wlh..ko zai mutu sai mun tafi da ita gobe”
Suna shiga daki umma ta zaunar dashi itama ta zauna snn tace mai”to inajinka..menene matsalan”…Saida ya narkar da murya kafin yace”umma dan Allah kicema ummi ba sai kun tafida baby ba..tsakani da Allah umma har tsawon kwana nawa akeso inyi ba tareda itaba..ni bazan iyaba wlh.. dn Allah kuje ku kadai abinku.. inyaso mu sai mu taho ranan Friday”…dariya umma ta saki dama tatsuniyar gizo ai baya wuce koki…ta kama kunnenshi da kyau snn tace”wato ko kunyana bakaji koh”…Taheer ya kama hanunta dake rikeda kunnen nashi yace”auchh umma akwai zafi”…”zafin nakeso kaji dama ai”umma ta fada tana sakin kunnen nashi…shiko yana shafa kunnen ya sake cewa”Allah umma da gaske nakeyi..yanxu gobe Wednesday ni kuma bazan zo bafa sai ranan Saturday.. seriously bazan iya spending 3 whole days without seeing her ba..do something plss”…da mamaki sosae umma ke dubanshi tace”ban san yaushe ka zama mara kunya haka ba wlh..ynxu kwana ukun kakema wnn abun sai kace shekara uku”…cikin zuciyarshi yace”umma bazaki gane bane”..a fili Kuma yace”nidai umma do something plss..ki taimaka kima ummi bayani”…umma ba tace komai ba Saida ta mike..tana kokarin fita daga dakin tace”to tashi muje ka fada Mata da bakinka”…Taheer ya zaro idanu waje yace”kema kinsan rufeni da fada zatayi”…umma tace”to shawaran da zan baka shine kawai kayi hakuri..tun jiya nace mata ta bari ku taho tareda ita amma taki yadda..Kuma kasan halin Yaya da kafiya..so gara ma ka sama ranka dangana tun yanxu”…tana gama mgn bata jira me zai ce ba ta fita daga dakin…Taheer ya shiga hargitsa gashin kanshi yayinda ya bita da ido har ta fita….da kyar ya mike shima ya fita daga dakin…Yana isa parlor ummi tace”Kai wai sai yaushe zaka tafi gida ne..dare na karayi fa”…tana rufe baki yace”a nan zan kwana ummi”…tana binshi da kallon mamaki yace”a nan zaka kwana Kuma”…Taheer ya daga mata Kai..ummi kmr zata sake mgn sai kuma ta fasa ta cigaba da hiran da sukeyi itada Nafeesa…shiko Taheer idonshi na kan Layla dake nunama su Al’ameen abu a wayanta ya fita daga parlon…Kai tsaye part dinshi ya nufa don da gaske bazai iya komawa yaje ya kwana gidanshi while ita Kuma tana nn gidan ba…da zaa mai adalci sai a turo mai ita ace suje su kwana tare amma yasan ba Wanda zaiyi hakan..Saida yaje part din nashi ya tuna bai amso key a wurin umma ba…dan tsaki yaja snn ya sake juyawa ya nufi part dinsu…wnn karon Al’ameen da Ramadhan kadai ya samu a parlor… yana dubansu yace”Ina baby take”…Ramadhan yace”ynxu ta shiga dakinta”…tun kafin Ramadhan ya rufe baki ya kama hanyar dakin nata da sauri…Yana budewa kuwa ya ganta a ciki ita kadai..tana kokarin cire kayan jikinta…”am one lucky man”ya fada yayinda yake karasawa kusa da ita…Layla na ganinshi ta zo inda yake tareda juya bayanta tace”daddy budemin zip dina plss”…baiyi mgn ba yasa hannu ya bude mata zip din..ta juya zata koma inda kayan nata suke kawai taji ya kamo waist dinta da both hands dinshi…ta juyo tana kallonshi a marairaice tace”daddy plss..kayana fa nakeso in cire”…still baice komai ba yasa hannu ya shiga cire mata rigan nata a hankali..ya zare both hands dinta daga ciki snn ya cire rigan gaba daya daga jikin nata..ya zama daga ita sai bra..sai Kuma skirt dinta…ya sake sunkuyawa a hankali ya bude zip din skirt din shima ya shiga janyeshi daga jikinta a nutse..saida ya saukeshi har kasa snn yasa hannu ya dagata sama cak..skirt din ya fita daga kafafunta snn ya ajiyeta gefe..ya risina tareda dauko skirt din sai ya karasa gefen gado dasu a hannunshi..ya zauna snn ya fara ninke Mata kayan..yana gamawa ya ajiyesu nn gefe snn ya maido da idanunshi kanta…tana nn tsaye kmr gunki daga ita sai pant da bra a jikinta tana binshi da idanu kawai..ita kanta tunanin yanda zata debi tsawon kwanaki haka ba tareda Shiba takeyi..ya riga ya sabar mata da kwanciya a jikinshi always…ta saba da yanda yake kulawa da ita kmr baby..ta saba tayita mai shagwaba yana biye mata..tasan definitely ba karamin missing dinshi zatayi ba…tana tsaka da tunanin kawai taji yayi sama da ita..Saida ya koma gefen gadon ya zauna snn ya dorata kan laps dinshi tareda rungumeta tsam a kirjinshi… idanuwanshi lumshe yana shaqan daddadan kamshin da gashinta ke fitarwa muryanshi a shake yace”baby plss..kar ki tafi ki barni don Allah..i can’t live without you..kiyi wani abu plss”…muryanta very low itama tace”nima ban San me zanyiba daddy..am going to miss you too”…Taheer ya dago idanunshi da suka kada sukai jajir sbd wata wutar fitina dake cinshi…ya kamo fuskanta ya hada da tashi…still muryanshi can kasa ya sake cewa”kawai cewa zakiyi bazaki bisu ba shknn..kina fadan haka nasan ummi zata kyaleki..ko kinaso kije ki barni ni kadai ne”…ta girgiza mai kai a hankali…yace”then do something..kiyi wani abu indai ba so kike inyi sabuwar budurwa ba idan kin tafi”…da sauri ta bude idanunta tana kallonshi..ta tsuke baki kmr zata sa kuka tace”Allah ban yadda ba..kuma wlh kanayin budurwa na dena kulaka infact kwaso kayana ma zanyi in dawo nn gidan”…ta karasa mgnr tareda murguda dan bakinta da tun dazu Taheer yai kurii yana kallonshi..ya lumshe ido tareda dora lips dinshi kan nata..itama lumshe idanun nata tayi luf as tanajin dadin yanda yake sarrafa bakin nata..har ga Allah bata isa tace daddy is not romantic ba..he is extra romantic.. kawai dai tanajin zafin abinda yakeyi Mata kuma ga tsoro shiyasa bata cika sakin jiki har da zataji dadin abin da yakeyi din ba…sun dauki almost 10-12mins suna abu daya…da kyar Taheer ya raba bakinshi da nata gudun kar yakai limit dinda bazai iya controlling kanshi ba Kuma..yasan wani na iya shigowa dakin at any time so yayi stopping kanshi ba don yaso ba…rungumeta ya sakeyi a jikinshi yana sauke numfashi da sauri da sauri…idanuwanshi rufe yanajin tamkar ya zubar da hawaye yace”bazan iya spending almost a week ba tareda keba baby..I just can’t..do something dn Allah”…Layla ta zame jikinta daga nashi..tana goge tears dake fitowa idonta tace”badai cewa kayi zaka sake budurwa ba..dena kulaka zanyi wlh”…ta karasa mgnr tana kokarin mikewa daga jikin nashi ya dawo da ita da sauri..ya sake matseta sosae..dukda he’s emotional hakan bai hanashi dariya ba..duk tace ta dena kulashin nn dariya take bashi wlh..but he’s happy she’s jealous..at least yanxu yasan bashi kadai yake kishinta ba..itama tana kishinshi and he’s happy to know that…Layla ta shiga mutsu mutsu tanason barin jikinshi..tana kuka tace”let go of me daddy..ka sakeni inyi tafiyana ni”… maimakon ya saketa sai ya sake Rungumeta gam…still yana smiling yace”ohk ohk naji..am sorry da wasa nake maki..kema dai kinsan bazan taba kallon wata mace da sunan so ba baby..not after inada kamarki..so stop crying kinji”…bata sake yin mgn ba..ta dai dena kukan da takeyi..a hankali tace”to ka sakeni insa Kaya kar wani yazo ya sameni a haka”…baiyi musu ba ya saketa snn ya mike zuwa inda kayanta suke…cotton dogon riga ya dauko mata armless mara nauyi..ya dawo inda take tareda kamota ya shiga sa mata rigan da kanshi..tayi shiru tana binshi da kallo har ya gama sa Mata..ya kamota tareda manna Mata kiss a forehead dinta yana fadin”you look gorgeous my baby..I love you”…Layla ta saki kasaitaccen murmushi itama tace”I love you more..yanxu kazo ka tafi daddy kaga ummi zata iya shigowa”…ya kama hanunta suka fita dakin yana cewa”baby muje ki tayani bacci dn Allah kinji”…ta zaro idanu tana dariya tace”Tabb..kanaso ummi tayi min kaca kaca knn”…shima dan dariyan ya saki jin abinda ta fada..wai kaca kaca…suna zuwa parlon suka samu duk sun dawo..su Al’ameen ne dai duka tafi daki suka kwanta…hanunta cikin nashi suka karasa ciki…ummi tabi hannayensu dake sarke da kallo kafin tace”ikon Allah..kai Kuma daga Ina..ba munyi sallama dakai ka tafi ka kwanta ba..me Kuma ya dawo dakai nn”…Taheer ya shafa goshi jin tambayoyin da ummi ke jero mai..sai kace ba ita ta rike mai matarshi ba…a zuciya yace”ki bani matata mana kiga bazaki sake ganin keyana ba sai garin Allah ya waye”..a zahiri Kuma ya nuna Layla da hanunshi cewa yai”Kaya na bata ta canza ummi..zamuje mu kwanta”…ummi ta zaro ido tace”la’ilaha illallahu muhammadu rasulillahi sallallahu alaihi wasallam..kai wai meke damunka ne..meya shiga kanka haka..yanxu Taheer ko kunya babu kake duban tsabar idonmu kana wani cewa zakuje ku kwanta..to ka saketa snn ka wuce ka bar min parlor tun ban gaggala maka mari ba wlh..fitsararre kawai”…a hankali Taheer ya saki hannun Layla dake cikin nashi snn ya fita daga dakin..ko key din ma bai karba ba aka koroshi…saiya Kira umma a waya yace ta bada key din a kawo mai.
Bayan fitanshi Nafeesa da taji kunyan abinda ummi tayi mai…tana duban ummi tace”ummi da baki mai haka ba wlh..ni tausayi yake bani..kuma meye amfanin ajiyeta a nn tunda gashi yana gidan”…ummi tace”ni rashin kunya ne banso..dubi fa ya ketare mu yabi yarinyar nn har daki sbd bashida ta ido”…sai ta maida kallonta ga Layla dakejin kmr tasa kuka sbd abinda ummin tayi mai..tace”kema kuma kika biye mai sbd ba kunyan ne ya isheki ba koh”…batace komai ba sai ma mikewa da tayi ta koma daki abunta… ummi ta rakata da harara tana tabe baki tace”ba laifinki bane wlh..duk shi ya lalata ki da dabi’unshi..duk halayen Taheer ba wanda ta mance bata dauka ba..Allah ya shiryeku”…Nafeesa shiru kawai tayi hadda su tagumi tana kallon ummi da karfin hali…ita kuwa umma mikewa tayi tana dariya kasa kasa..ta tafi daki don dauko mai key din.
Washegari suna idar da sallahn asuba suka fara Shirin tafiya..Taheer ma tunda ya dawo daga masjid bai koma part dinshi ba..yanata kallonsu sunata shiryawa..saidai tunda ya zauna baiga Layla ba…su Al’ameen suka fita da kayayyakinsu suka Sanya a mota snn suka dawo..daidai lokacin Kuma ummi da Nafee suka fito cikin Shirin su..can saiga umma ma ta fito daga dakinta…yanata baza ido ya hangota ta fito daga dakinta..tana kokarin gyarama Hibba hulan dake kanta so bata kula dashi ba…Taheer yai shiru yana kallonta..tayi mai kyau sosae as always…lace ne a jikinta riga da skirt..ta yafa mayafinta golden yellow daya shiga da lace din nata…lokaci daya ya lumshe idonshi ya bude..yanajin kmr ya dauketa su gudu inda ba mai takura musu..sam bai son kowa ya kalleta a yanda tayi kyau din nn..wani kishi yaji ya tokareshi daya tuna gidan biki zataje..and Allah kadai yasan adadin mutanen da zasu kalleta…at this point sai yaji kmr ya sa kuka…a hankali ya juya ya fice daga dakin ba tareda sunyi notcing dinshi ba.
Yana nn zaune cikin motanshi ya rasa inda zaisa kanshi sbd bacin Rai suka fito…bai yi yunkurin tashi ba yaci gaba da zamanshi nn ciki…su Kuma suka karasa gaban motan da zasu tafi dashi..suka fara shiga..da yake family car ne so ta daukesu gaba daya…ummi..umma da Nafee suna baya..tsakiya Kuma Layla ce da Hibba sai Ramla da zasu tsaya gidanta su dauketa.. Al’ameen da Ramadhan kuma suna gaba…Layla sai wara idanu take tanason ganin ta inda zai bullo amma bashi ba alamarshi…gaba daya ta damu so take kawai ta sashi a idonta kafin su wuce…shiko yana cikin motanshi yana kallonsu..duk zuciyarshi a jagule yake..yaji kowa da komai ma na bashi haushi…a hankali ya fito daga motan tareda nufowa inda suke…
A cikin motan kuwa umma sai tambayanshi take amma ba Wanda ya ganshi..Saida ya karaso inda suke snn ya shiga gaida su umman fuska ba walwala.. Nafeesa taji tausayinshi ya sake kamata kwarai..wnn wane irin punishment ne ummi take mai haka…a hankali ya matsa inda Layla ke zaune itada Hibba…tunda yazo wurin take satan kallonshi tana mamakin meya bata mishi rai haka…shiko Taheer kallonta yake yanaso ya dan kakalo murmushi ko na karya ne amma kmr fuskan ne yake daurewa da kanshi..tsabar kishi duk ya rufeshi ita kanta yaji yana jin haushinta kan wnn dressing da tayi..gashi bai isa yayi mgn ba ummi ta haushi da fada…a hankali Layla tace”daddy ina kwana”…daga kanshi kawai yayi da kyar yace”lfy”..sai Kuma ya juya ga su ummi yace”Allah ya saukeku lfy”…bai jira jin me zasu fada ba ya bar wurin da sauri…Layla ta bishi da kallo tanajin yanda hawaye yake kokarin zubowa a face dinta…wnn fushin nashi definitely tasan akwai abinda ya faru..haka nn bazai dauki fushi ba tareda reason ba..to ko sbd ummi ta dage sai sunje da ita ne..Ummi ce tacema driver yaja mota su tafi…maigadi na bude musu gate suka fita daga gidan..
Haka Layla tayita sake sake har suka isa gidan Ramla suka dauketa snn suka kama hanya…har yanxu bata bar tunanin sudden change din nn nashi ba..why is he upset..duk sai taji tafiyan ma ya fita kanta gaba daya..Allah ya sani tanajin tsoro yayi sabuwar budurwa kmr yanda ya fada Mata.
Taheer na ganin tafiyansu ya tada motanshi shima snn ya bar gidan…Kai tsaye gidanshi ya koma…yayi wanka ya shirya snn ya tafi clinic…har yanxu Kuma bai denajin zuciyarshi a dagule ba..aikin kirki ma kasawa yayi a clinci din tsabar bacin ran da yake ciki.
+
Su Ummi kuwa tafiyan almost 6 hours ne ya kaisu Kano..umma tace ko zasu tsaya a kanon su kwana zuwa gobe Thursday su kama hanyan Dutse amma ummi tace gara su hada tafiyansu lokaci guda…haka suka dauki hanyar Dutse duk ba Wanda bai gajiba a cikinsu…sallah kadai suke tsayawa suyi..abinci kuwa dama da kayansu suka taho..duk wanda yace yanajin yunwa zaa zuba a bashi yaci…Layla Kam ko abincin ma bata iya ci sosae ba..ta damu sosae akan bacin ran data gani shimfide kan fuskan Taheer..bata San meyasa ba amma ko kadan bata so taga yayi fushi da ita…gaba daya neman sukuninta takeyi ta rasa duk yake irin wnn fushin da ita.
Sai waje karfe 4 suka shiga garin Dutse sbd yanayin hanya da bata da kyau sosae…suna isa family house din su Awwal aka tarbesu sosae..aka kaisu masaukin da aka tanadar musu su kadai…cikin lokaci kankani Kuma aka cika gabansu da kayan ci da sha iri iri..gaba dayansu a gajiye suke sbd zama wuri daya..don haka kowa saida ya dan watsa ruwa snn suka zauna cin abincin dukda ba wai suna tareda yunwa bane tunda sunci abinci a mota…Saida suka gama snn suka shiga gidan aka fara gaisawa da mutane..duk inda suka shiga sai an nuna Layla ana cewa itace marigayi Usman zai aura Kuma sai Allah baiyi ba…gaba daya Layla sai suka tuno mata da Ya Usman dinta..ta tuna yanda yake sonta sosae…dukda baza tace yakai Taheer sonta ba amma shima tanada tabbacin son da yake mata mai girma ne…lokaci daya jikinta ya Kara yin sanyi.. memories dinta da Usman din suka shiga dawo Mata..ga Kuma Taheer da taketa expecting kiranshi tun dazu amma bai kiraba…abun sai ya hadu ya Mata yawa..don haka ta samu ta sulale daga cikin mutane tareda komawa masaukinsu ta kwanta ita kadai..kawai sai ta fara hawayen da bata San takamaiman dalilinsu ba…meyasa daddy zaiyi mata haka ne..?
Abuja…
Yinin yau gaba daya Taheer yayishi ne cikin damuwa da rashin walwala…ko abincin kirki ya kasa sama cikinshi har yanxu…haka yayita zama a clinic har dare snn ya tafi gida.. Yana so ya kira yaji sun sauka lfy snn yanaso itama yaji muryanta amma he’s upset with her…don me zata dauko wnn kayan ta sa hadda su mayafi snn ta kama hanya ta tafi inda yasan dole maza zasu kalleta…
Ya gama duk Shirin da yakeyi before kwanciya snn ya hau kan gadon ya kwanta..sai ya rungumi pillow yana sakejin takaicin rabashi da matarshi da akayi kawai sbd biki…the more yana tunani the more zuciyarshi ke Kara lalacewa…a karshe dai gani yai bazai iya jurewa  ba sai ya dauko wayanshi ya shiga dialing number dinta..ko su ummin bazai kiraba don suma sun bata mishi rai…
Layla dake kwance daki tun dazu taji wayanta ya fara vibrating…ta daukota da sauri don tana expecting kiran nashi…tana ganin shine me Kiran kuwa tayi picking don karma ya katse bata daga ba…Taheer da yaji tayi picking call din sai ya sake tamke fuska kmr tana gabanshi ya Kuma ki yin mgn…a hankali cikin voice dinta dake nuna alamun tasha kuka tace”daddy are you upset”…Taheer banza yayi mata don yana ganin tambayan nata akwai rainin hankali a ciki…ta sake cewa”am sorry idan nayi maka wani abun”…tun bata karasa mgnr ba yace mata”don’t sorry me okay..karki kuskura ki bani hakuri”…Layla ta dafa goshi tanajin yanda yakeso ya caja mata kai tace”daddy laifin me nayi Kuma”…a fusace yace”oh tambayana ma kike..bakisan laifinda kikai ba right..wa ya baki izinin yafa mayafi ki kama hanya kije har Dutse dashi”…shiru Layla tayi a zuciyarta tana yanxu wnn fushin duk na mayafi ne..a fili Kuma tace mai”to am sorry..bazan karaba”…Taheer yai shiru kmr bazai sake mgn ba..sai Kuma yace”Ina su ummi”…tace”suna cikin gidan”…yace”ke kina Ina”…”Ni Ina daki tun dazu..na gaji ne shine nazo na kwanta”…a takaice yace Mata”to sai da safe”.. ta amsa mai da toh snn sukai hanging call din…Layla ta ajiye wayan tana mamakin wnn fushin nashi duk don tasa mayafi ne..
STORY CONTINUES BELOW
Washegari…
Yauma dai kmr jiya haka Taheer ya tashi kmr mara lfy..gaba daya baida wani energy a jikinshi don ba wani abincin kirki yaci ba..baima da appetite din da zaici abincin kwata kwata..haka ya gama shirinshi sukuku snn ya tafi clinic…zuwa yanxu ji yake bazai iya bari har sai jibi snn ya tafi Dutse ba..ya zama dole yayi wani abun don baijin zai iya tashi lfy gobe idan bai sanyata a idonshi ba..sai ya kira wani yace a bincika mai in da akwai available flight da zaije kano yanaso…luckily Kuma an samu da akwai amma sai gobe Friday zai tashi karfe 8 na dare…dukda Taheer baiso haka ba..amma haka ya siya ticket din don a yanda yake din nn baijin zai iya driving daga Abuja har zuwa Dutse..yau ma Kuma ko kadan bai kirasu ba..Kuma bawai don bayason Kiran bane..ah ah kawai sbd duk yana fushi dasu ne..
Dutse…
Yau sun tashi da shirin yin kauyawa party da zaayi a cikin gidan…kowa sabgan gabanshi yake amma Layla ta kasa samun sukuni at all..yau tunda garin Allah ya waye take zuba idon ganin Kiran daddy amma ko flashing dinshi bata ganiba..gabaki daya she’s disturbed..da yasan yanda fushin nn nashi ke affecting dinta da ya dena yinshi komai girman laifin da zata aikata kuwa…haka suka gama shiri gaba dayansu snn suka fita wurin da zaayi kauyawa din…
Ba laifi ta dan sake daga baya..bayan ta shiga cikin family..taga mutane da dama..wasu ma ta kwashi shekaru bata gansu ba tunda ba kowane yaje bikinta da Taheer ba…amma dukda haka tunaninshi bai bar cikin zuciyarta ba har aka tashi a taron…
Suna komawa masaukinsu dama daki ta shige ta fara rage kayan jikinta snn tayi wanka..tayi sallah snn ta kwanta abunta kmr yanda tayi jiya…tana nn zaune tanata tunane tunane Nafeesa ta shigo dakin…gefen gadon ta zauna snn tace daita”mike Layla mgn nake sonyi dake”…ba musu ta tashi zaune tana fuskantarta… Nafee na kallon yanda jikinta ke a sanyaye tace”inaso ki fadamin mene matsarki..na lura duk a sanyaye kike..bakida lfy ne?..”Layla taji hawaye ya fara zubo mata..a hankali ta girgiza Kai alaman aah… Nafeesa ta sake cewa”to me yake damunki..ko wani abu ya jadaku da dadyn naki ne?..”a hankali Layla ta matso jikinta sosae tareda dora kanta a kafadanta..hawaye na zuba a idonta tace”Mami fushi yakeyi dani tun jiya..ni bansan laifin da nayi ba..duk yau ko kirana baiyi ba”…Nafeesa dan murmushi ta saki..a ranta tace”oh wnn soyayya”…a zahiri Kuma cewa tayi”ke me ya hana ki kirashi tinda kikaga bai kiraba”…Layla tace”Ni banaso in kirashi inji yana hahhade min rai”…wnn karon dariya ta saki sosae kafin ta dago Layla daga jikinta tana share Mata hawaye tace”baa yima namiji haka Layla..da kikaga bai Kira ba ke sai ki dauki waya ki kirashi..idan yace ga laifin da kikayi sai ki bashi hakuri..ba wai kizo ki yita faman kunci kina damun kanki ba..Kuma kema da ummi tace zamu taho dake don me baki ce mata Zaki taho tareda shi ba..nasan hadda wnn dalilin ma yasa yakejin haushin naki tunda baiso ki biyomu ba..dena biyema ummi zakiyi ki tsaya ki kulada mijinki da kyau..tunda kinsan bazata taba dora bukatarshi akan taki ba..bazata taba goyon bayanshi ba koda ace shine mai gsky kuwa..Kuma hakan bawai yana nufin bata son ‘danta bane..no tana sonshi..kawai soyayyan da takemin da Kuma Kara irin nata shiyasa bata taba koyon bayan abinda yakeso..don haka sai ki kiyaye..yanxu ki dauko wayanki ki kirashi..Kuma ki tabbatar kin bashi hakuri kinji na fada maki”…ba musu Layla ta dauko wayanta snn ta fara dialing number dinshi.. ita Kuma Nafee mikewa tayi ta fita…Saida Kiran ya kusa tsinkewa snn yayi picking…maimakon tayi mgn kawai sai ta fashe mai da kuka…Taheer yayi shiru yanajin yanda kukan nata ke ratsawa har cikin heart dinshi…how he wish tana kusa dashi take kukan nn..daya lallasheta yanda ya kamata…ita kuwa kukanta takeyi bilhaqqi don tasan it’s the only thing da zai sauko dashi daga wnn fushin da yakeyi…Taheer ya runtse idanunshi don baison jin sautin kukan nn ko kadan…ganin da gaske ba Dena kukan zatayi ba yace”baby mana..kawai sai ki kirani kisamin kuka sbd kinsan banaso koh”…batace mai kala ba sai kukanta da take cigaba dayi…yasa hannu tareda haigitsa suman kanshi yace”ohk ohk am sorry toh..yanxu ki dena kukan”…nan ma batace komai ba..Kuma bata bar kukan ba…a raunane Taheer yace”baby plss nace am sorry koh..kece fa kikaimin laifi and you are making me apologize.. sbd kinsan banason kukan koh..baki damu daniba koh”…Saida ta share hawayenta snn tace”nidai kayi hakuri toh..bazan Kara ba..kawai ka dena yin fushi”…ya dan lumshe ido hadda sauke ajiyan zuciya kafin yace”alright na dena baby..nima duk a takure nake sbd fushin da nakeyi dake din..amma na dena”..tana murmushi tace”na gode daddyna”… yace”Nima na gode babyna..ynxu fadamin kinyi missing dina ko bakiyi ba”…yana rufe baki tace”I missed you like crazy..jiya ko bacci banyi sosae ba”…Taheer dake jin dadin hiran nasu sosae..ya shafa gemunshi snn ya kwanta tareda dora pillow kan chest dinshi yace”idan akwai abun da yafi missing dinki baby wlh nayi..am about going crazy..ko abinci ban iya ci..haka kawai kin tafi kin barni da rungumar pillow”.. murmushi mai sauti ta saki kafin tace”nima ai pillown nake runguma daddy.. afterall ba dadewa zamuyi ba”…a hankali taji yace”baby”…itama a hankalin tace”yes daddy”…Taheer ya sake narka murya yana sakin wasu nufarfashi yace”I love you”…itama ta maimaita”I love you”…ya sake cewa”I want you”…ba tareda tasan me take cewa ba itama tai kasa da murya snn tace”I want you”…Taheer ya saki wani dariya snn yace”don’t worry my baby..Ina zuwa zan fanshe maki duk na kwanakin da kikayi missing”…Layla ta zaro idanuwa waje jin abunda yake fada..harga Allah batasan meta fada ba sai daga baya…bakinta ta tura gaba tace”Ni ba abunda nake nufi knn ba”…yace”ai kin riga kin gama mgn..don  haka ki shirya dama Ina zuwa  hotel zamu tafi”…kukan shagwaba ta fara mai tana bubbuga kafanta kan gadon tace”nidai aah wlh..ni Allah bazan yadda ba”…yana smiling yace”Hey relax..wasa nake maki”…haka dai suka cigaba da hira har basu san dare ya tsala ba sbd dadin hira…Saida yaji ta fara bacci snn sukai sallama ba don yaso ba..in don tashi ne baiki su kwana suna hiran ba coz ba karamin dadi take mishi ba..
STORY CONTINUES BELOW
The following day ya kama Friday..ranan ne Kuma zasuyi dinner..
Around 6 na yamma duk sun kusan gama shirin tafiya dinner din…wnn karon lace suka dinga gaba dayansu iri daya..ummi..umma..Nafee..Ramla..Layla da Kuma Hibba..
Ummi ta mikama Layla Nasreen dake hanunta tace”je ki nemo Ramla duk inda take ki Kai mata ‘yarta..don iskanci shine tasa kafa ta tafi ta bar mana ‘yar duk ta cika mana kunne da ihu”…ba musu Layla ta amsa Nasreen din snn ta fita daga part din nasu..Kai tsaye main hause din ta nufa tana tunanin ta Ina zata fara neman Ramla…a parlor taci karo da wata aunt dinta sai ta tambayeta ko taga Ramla..ta nuna Mata wani daki tana fadin”suna ciki itada amarya tun dazu..kwalliya ake musu”…ba bata lokaci Layla ta nufi dakin da aka nuna Mata…ta tura kofan ta shiga…suna ciki an gama ma amarya make up ana Shirin fara yima Ramlan sai gata ta shigo..Layla ta Mika Mata Nasreen dake ta tsala ihu tace”tun dazu take kuka anty Ramla”..Saida Ramla ta amsheta snn ta juya wurin da amarya Asma’u take…tana murmushi tace”Ya Ma’u bakiga kyan da kikai ba wlh”… Asma’u na dariya tace”thank you. .sai kizo ki zauna ayi maki tunda Allah ya kawoki”…Layla ta zare ido hadi da girgiza Kai tace”Aah Ya Ma’u nagode”… Asma’u tace”wlh baki isaba yarinya”…Layla ta sake bude idanu tace”Ya Ma’u kiyi hakuri dn Allah..daddy baya son make up nasan idan yaga nayi bazaiji dadi ba”…Ramla dake gefe tana feeding Nasreen tace”come on kije ayi maki da Allah..daddyn naki ai ba gani zaiyi ba tunda sai gobe zaizo”…tana rufe baki Asma’u tace”yes kizo kawai ayi maki kafin Ramla ta gama itama sai ayi Mata”…Layla ba don taso ba suka tilasta ta zauna aka fara Mata make up din…basu wani dauki tsawon lokaci sunayi ba tunda very light make up akayi Mata…ita kanta bayan an gama data kalli kanta a mirror sai da ta furta MashaAllah sbd kyan da taga tayi…dinkin jikinta straight gown ne dayabi ya lafe a jikin nata..ya kuma fito da ainihin surarta…mayafinta blue black Wanda yai matching da lace din nata..kasancewarta fara sosae sai colour din ya sake haskata…Daurin kanta Zara Buhari daya matukar yi Mata kyau…an zubo jelan gashinta zuwa tsakanin wuya da kafadanta…she looks so breathtaking…ita kanta mai make up din kallonta kawai takeyi kmr zata hadiyeta…ana gama mata ta sake amsan Nasreen ta rike snn aka yima Ramla.
8 daidai yayi musu a hall din da zaayi dinner…da yake ba tare dasu ummi suka taho ba..su kansu da suka ganta ba Wanda bai yaba kyawun da tayi ba…Nafeesa na dan hararanta tace”wa ya baki daman zuwa kiyi wnn make up din Layla..kinfi kowa sanin idan Taheer ya gani bazaiji dadi ba”…tana rufe baki umma tace”nima abinda nake son tambayanta knn tun dazu..ko da bikinsu ma cemin yayi da yasan haka make up din zaiyi mata kyau da bai bari anyi mata shiba..shine yanxu kikaje aka sake yi maki sbd baki jin mgn koh”…Layla na kokarin mgn ummi tace”yanxu Aisha meye laifi idan tayi kwalliya da bikin ‘yar uwarta..inace ba Haram bane yin kwalliyan..yarinya da kuruciyanta da komai sai a hanata gayu kawai sbd wani Taheer..kemafa kinsan rigiman Taheer idan zaa biye mai to yarinyar nn ba karamin takurata zaiyi ba..don Allah da annabi ku kyaleta tayi abunta”…sai ta juya tana fuskantan Layla tace”yi tafiyarki kinji..kinyi kyau sosae wlh..banda kaddara ma ai kinfi karfin Taheer wlh..mutumin da ya girmi uwarki sbd tsabar son kai aka shiga aka fita Saida aka bashi aurenki”…da sauri Layla ta bar wurin dama Allah Allah takeyi ace ta tafi don bata San me zata ce musu ba…umma na duban ‘yar uwar tata tace”ya zakice haka Yaya..ita ba itace ma tayi dacen miji ba..wlh Layla ko bata auri Taheer ba nasan zai iya samun Wanda ma tafita komai ya aura..amma ita har ta mutu bazata sake samun wanda zaiyi mata irin son da Taheer din ke mataba”…ummi na tabe baki tace”ai bazaki taba ganin fault din danki ba dama”…Nafeesa dake sauraron draman nasu dariya kawai takeyi kasa kasa..
8:45 daidai Taheer ya shigo cikin gidan bikin..bayan sun gaisa da Alhaji ya tambayi su ummi akace mai duk gidan sun tafi wurin dinner da akeyi…alhaji ya hadashi da wani daga cikin jikokinshi yace su tafi tareda Taheer din…Taheer ya mai sallama snn yabi guy din suka tafi…Allah Allah yake kawai ya ganshi a wurin…yasan zasuyi mamakin ganinshi don ba Wanda ya fadama he is coming…
Saida sukayi tafiyan almost 20 mins snn suka isa hall din…bayan guy din ya gama parking suka fito daga motan snn suka doshi cikin hall din…tun daga waje ana jiyo sautin kida dake tashi a ciki…
Suna shiga idanun Taheer suka sauka kan Layla dake gaban amarya da ango a tsakiyar fili tanayi musu liki…ba ita kadaice a wurin ba hadda Ramla da sauran family dinsu amma idanunshi ita kadai suka hango mai taci kwalliya kmr itace amarya snn tana lika kudin tana dariya tana Kuma dan taka rawa a hankali…wani abu yaji ya taso tun daga cikin cikinshi ya tokare mai a makogaro…ya lumshe ido snn da kyar ya hadiye wani yawu mai daci da yaji ya cika mai baki all of a sudden..idanunshi ba abinda zaka gani sai zallar kishi…kishin yanda ta caba uban kwalliya haka..ta shiga cikin Arrijaal suna kallonta..suna kallon dariyarta snn suna kallon jikinta da yake juyawa as a result of rawan da takeyi… “innalillahi wainna ilaihi rajiun”kawai yake furtawa..gaba daya ya sandare a wurin ya kasa gaba ya kasa baya sai kace gunki..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *