DUNIYA CE COMPLETE
DUNIYA CE TAFI BAGARUWA IYA JIMA, Komai Nisan jefa kasa zai dawo, haka kuma komai tsawon dare gare zai waye, ramin karya kurarreni, kana taka Allah Na tasa, hakuri shine ribar zaman duniya, hassada ga mai rabo tak’i, karshen kiyayya soyayya, wanda karaina shi zai taimaki ka gaba, tsartsar addu’a maganin damuwa, sadaka bata sa rashi, Ana zatan wuta a mak’era sai gata masaka! Duk wanda yace tukunyan wani baze tafasa ba nashi ko zafi bazaiyiba, Komai dadewar Asiri watarana zai karye, indai k’ana addu’a nasara tana tare dakai…kubiyone cikin labarin FATIMA…DUNIYA CE… *1-5*
*NA NANA DISO*
Tsawar da mumy tayi shiya rikirketa tunanin ta! “Ke Fatima ina tunanin dake nake magana, ” a
tsorace ta sauka kasa babu inda ta nufa Sai bangarin Yaya Arif sallama tayi ya amsa, da kyar ta’iya
hada ido dashi.
Cikin gadara da isa yaja wane guntun tsaki sannan yace lafiya? ” fatima tace hajiya ce tace k’ak’aine
asubuti!. ” malama fita in nagama abunda nakeyi zan fito.
Tafiya takiyi babu laka ajikin ta “Shamsiya taje tana ke fatima kizo inje Alhaji Kuma kiyi sauri bawai
kina tafiya Sai kace wata mumina ba.
Tana shiga ta tsugunna domin gaida alhaji, ” Bama Sai kin gaida ne ba nagaya miki kifito da miji
nagaje Nabaki Nan da sati daya wallahi in baki fito dashi ba Sai Na hadaki da duk Wanda nayi niyya!
” hawaye ne yafara Bata fusarta da cutar daki damunta zataji ko kuma da matsalar gidanan? ” au
kuka kikeyi kema shirya kuka ba yanzu ba? Suka saka dariya har mumy ai kam kuka ma Sai an
hadata da D’an baba Mai gadi, tashi kibane waje banza sha-sha-sha.
Da sauri ta karasa dakin ta zuciyar na k’una chan kuma Kuka tafarayi oh ni fatima wai indai babu ran
iyayenka babu abunda Baza ayi maka ba, wayyo ne bansan so waye iyaye ba bansan dadin su ba?
Tun shekaran jiya nake fama da ciwon hakuri Amma kullum Sai ace naji gurin Mai chemist, Duniya
kenan!!!
Kiran da taje ya tabbatar mata da Yaya arif ne mayafi ta dakko da wayarta, tana isa Mota yace ” kee
son zuwa asubuti Sai kace mayya ai ne da kinbarne nacire miki da gudu ma, ” kuka takara fashewa
dashi, ” han bareta yayi, ” babu shiri tayi shiru ga azabar hakuri ga azabar duka sun kuyar da kanta
tayi har suka isa.
Dr ammar ne ya kalleta fatima Mai isa ba kizo asubuti da hure ba, ga azabar hakori haba fatima Sai
kace ba y’ar alhaji ba, ” Da taga alamun zaiyi mata fada tace Dr ammar wallahi nafada akawoni
asubutin aka k’i Sai yanzu suka ga dama, ” bakomai fatima komai Mai hucewa ne yanzu ban number
ki zan kiraki ko ciwon kai kikaje kiyimun flashing kinje? ” to ya bata magunguna yariko hanun ta har
bakin kofar mota, ” ya Arif ga ya ammar, ” da kamata tsawa yayi shige mutafi Dan uwarki…..
Urs Nana diso *5-10* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Haba yaya arif menene na zage? ” Nima kike tambaya mari ya
wanka Mata , ” fatima ta rike fuskarta tace lallai mutum bashida tausayi duk wahalar danayi maka
Amma Har da kai atsanata? Mai natsare maka a rayuwa? Ku bakwa tsoron wannan duniyar?? “
Malama yimun shiru cewar arif Sai Dai muje tsoron ubanki ko uwarki, ke bari kije daga yau nadawo
da gyaran part dina in bahaka ba zakiyi bayani, ” banza tayi masa inda ta cigaba da tunani. Suna i’sa
gida ta cewa mumy sun dawo ta huce dak’in ta akwatin ta tagani duk an hargetsa da alamun an taba
Mata kayanta, tasan bazai huce shamsiya ba, gyarawa tayi sannan tasha magani, sakkowa tayi ta
shinfida tabarma ta zauna tana karatu, Kamar daga sama taji an taka mata kafa, shamsiya ce tace
ke Fatima nasaka kayanki tunda ubana ne ya siya miki, ” fatima tayi murmushi ai shamsiya ba yau
kika fara ba Dan kin saka kayana ai Mai sauke ne da baki dauke kin bayarba, ” dallah munafuka
yimun shiru bari ma na tafi gurin mumyna uwata ta kaina,” Hmm Allah muma yajikan namu iyayen, “
shamsiya tace oho dai ba’adasu, ” fatima tayi murmushi ta cigaba da karatun ta. Yau tana karasa
girke d’akin ta ta nufa domin ta gaji, gashi Yau baa kunna inje ba, da taga alamun baza’a k’un na ba
wanka ta fada tana fitowa ta saka wasu kayan baccin ta. Arif Yana chan Yana waya da Ameera gashi
charging wayar sa saura kadan, ” sweetheart rike wayar bari na anso wayan fatima, ” wane irin
lamshashiyar murya tasaki nifa nifa banson kayi nesa dani my arif, ” Haba ameera cool down yanzu
zankiraki fa, ” to to inajeran ka karka dadi masoyi na. D’akin fatima ya buga Amma shiru, tsake yayi
ya budi kofar ko’ina duhu ga wayansa babu charge lalubar wayanta yafarayi akan gado, daga bisane
yaje hannun sa ajikin ta, wane irin shork yaji, fatima ce ta tashi wanene a dakina ko shamsiya ce, “
Sai muryar arif taji yace bani wayar ki, ” bazan bayar ba, ” ko kibane ko nadanneki na amsa, ” Sai
kace Dan iska? ” Yana kokarin riqe hannun ta ta hankada shi waje sauri tayi ta rufe kofar da key tana
huce sai kuma kuka wallahi yaya Arif kusani *DUNIYA CE*…… *ASALIN SU* _urs Nana diso_ *10-15* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Alhaji munzali yana daga cikin manyan ‘yan kasuwa wanda
duniya tasan dasu, yana da mata guda daya hajiya sadiya shekarar su talatin basu taba haihu ba, su
biyu mahaifiyar su ta haifa daga shi Sai hajiya sumayya wacce itace mahaifiyar fatima, ita kadai ce
‘yar ta mace Sai yayan fatima wato mudassir Yana Bangaren baban su Dan achan yake karatu,
mahaifiyar su Allah yayi mata rasuwa kusan shekara goma sha shida bayan mutuwar mijin ta da
shekaru itama tarasu daga baya sanadiyar ciwon zuciya. Alhaji munzali yana son ta sosai sanadiyar
son da yake yi mata, Bayan rasuwarta shine ya dauke Fatima Bayan fatima tana gidansa har yanzu
Allah Bai bashi haihuwa ba ya riketa tun tana yarinya, bayan shekara 4 Allah ya basa haihuwar
shamsiya Allah yabata tsewa ga mugun son ace tana da kyau, aduniya babu wanda ta tsana irin
fatima shiyasa kwata kwata bata sonta takan yi mata abunda takeso ga wulakanci da bori. Fatima
bashir kenan yarinya ce duguwa idanu wanta suna da haske ga manyan hips dukiyar fulani kuwa ba’a
magana, atakaice Dai yarinya ce mai kyau kuma yar lukuta tun tana yarinya Allah yabata kokari ga
hankali Amma kuma bata son hayaniya, ko yaya take Nan da Nan Sai ciwon kai, Tunda tafara
makaranta take samun ta daya, hakan yakan burge baba Amma kuma hajiya sadiya ta matsa mata
kullum sharri, Abun yana batawa fatima rai Amma babu yarda za tayi haka take hakura Wataran idan
hajiya. sadiya tayi mata sharri alhaji yakan harzuk’a ya zane fatima, Amma fatima bata taba jin
haushin sa ko kuma tayi masa Allah ya’isa ba, masu aik’in gida almajirai k’owa son ta yak’eyi saboda
nutsu-war ta da kokarin taga ta taimakawa talaka, hakan yasa tayi kokarin karantar mass com wanda
a yanzu tana level 4 ita kuma shamsiya tana bangaren english, fatima takan zauna tayi ta tunani
wane sa’in tayi tayin murmushi idan ta tuna burinta ya kusan cik’a. Arif D’an abokin alhaji munzali ne
mahaifin sa a canada yake azaune wanda kowa ya sane da alhaji bello cikakken Dan boko ne ga kudi
ga mulki, y’ay’an sa biyu a duniya daga Arif Sai affan, Sai mahaifiyar su hajiya rahama wacce suke
kira da mumy, Arif matashi ne da baifi shekara talatin da biyu ba fari ne Amma siriri ne baida kiba,
ga hanci Sai lip dinsa pink yanada fushi ga fada ga nuna isa baya kula yara a ‘yan matan sa Sai
wacce ta gama uni, kullum cikin naiman aure yake Amma Har yanzu bai samu mata ba, ga son aure
da Allah ya jarrabe shi, yadade da gama karatun sa wanda yanzu haka yanada kamfanoni, abok’anan
sa suna yawon tsokanar sa da “ka kiyaye mai nema! Kullum in k’iyarsa kenan, idan Arif yayi
murmurshi hushiryar sa ta k’an bayyana yan mata sukan muto akansa, affan kuwa likita ne Amma shi
bashida girman kai sai surutu… *Cigaban labari* Tun lokacin da Arif yabar dak’in fatima yake tunani
domin Kasa bacci yayi,yanzu haka yana rungume da Filo tunanin ta kawai yakeyi har yaushe yarinyar
nan ta girma? Mik’ewa yayi ya tafi k’asa domin yin breakfast yana sauka ya tarar duk suna zaune
gaidasu yayi, ” Arif yau ka makara ko sallah baka fito ba lafiya? ” wallahi alhaji ban k’wanta da hure
ba shiyasa, ” shamsiyya ce ta narke murya yaya arif ” kallanta yayi Kamar ya marita yace lapia? “
turo bakinta tayi sannan tace ice cream nakeson sha da daddare zaka Kaine, ” alhaji ne yace in bashi
da abunda zaiyi ai Sai ya kaiku, ” fatima ce ta shigo da dankali ahannun ta ta zubawa Kowa shayi ta
mik’awa ya arif Nashi a hankali tace ina kwana? ” jiyayi jikinsa ya mutu a hankali yace lpya
“shamsiyya da take hararar ta, ” alhaji danAllah zanje gidan goggo ya mudassir yadawo, ” shamsiya
tace dallah malama bakije nace ya arif zai fita dani ba sai dai ko gobe, ” bakomai yau da goben duk
daya ne Allah yakaimu, ” hajiya tace to munafuka uwar mata uwar iya magana, ” ke fatima ya zancen
mijin kin fitar, ” baba danAllah kabari nakarasa makaranta tunda saura wata 2 inshaa Allahu zan fito
dashi kafin lokacin, ” na amince Amma kisane in baki fito dashi ba lokacin da kika saka wallahi da
kaina zan baki wanda nakeso? ” tohm na amince, tashi tayi ta tafi sama. Tana fitowa daga wanka
wane material tasaka na gown ta dakko mayafe ta yafa wayarta ta dauka sai zumudin ganin yayanta
takeyi, sallama tayi hajiya na tafi ” a wacce motar? ” ta haya zan hau, ” Dama ai itace kalarki, tana
fita taga yaya arif da shamsiyya zasu shiga mota ko kallon su batayi ba ta huce, ” fatima arif yafara
kiranta, ” banza tayi mai ” zata fita kenan ya fun ciko ta nan da nan ta wad’a jikinsa…. *Urs Nana
diso* *15-20* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Lok’acin da Fatima ta wa d’a jik’in sa bai an k’ara ba ya
rungume ta sauri tayi ta ture shi tare da fad’in ya arif wai Mai nayi mak’a ne? So na k’eyi naje naga
d’an uwana Amma k’a tare ne, ” shamsiyya da tayi sororo duk jikinta ya mutu ga bak’in cik’in ya arif
bai zage fati, da taga haka kawai Sai tace lallai fatima bak’ida da k’unya ya arif k’ik’e gayawa hak’a
jak’a mahaukaciya, ” hawaye ne yafara wank’e fusk’arta cik’in k’uk’a tace ya arif k’ayi hak’uri in na
bata mak’a duk acik’in zumude ne, ” shamsiyya tace ‘kaji munafuka kai k’ace gaske ne hmm, ” wata
razanan niyar tsawa wacce Sai da ta tsorata, kai ba itaba har ma shamsiyya Sai da ta k’oma cikin
mota, ” har ina k’irank’i k’ina wane takama da i’sa banza kowanne bunsurun ne sai so’ki gwara alhaji
ya bak’i duk wanda yaga dama, ” shamsiyya da murna ta isheta Sai cewa tayi ya Arif katawo mu tafi
tohm sis gani nan. Wane matsanan cin k’uk’a ta fashi da shi daga bisane ta futa, bata dadi da
tsayuwa ba ta tsayar da mota k’uk’a ta k’eyi acikin ta bai ban tausayi, ” Mai motar daya gaji yace
hajiya sai dai kiye hakuri d’an nasan bazai huce rayuwar duniyar nan ba kowa hakuri yakeyi ko kuma
kiyita add’ua komai zai huce, ” tohm nagode, yauwa ai kowa ya cuceki k’arki damu *duniya ce* shiru
tayi masa tana k’ana nan tunanin ta sai da suka k’arasa ta bashi kudin motar. Sallama tayi da murya
mai sanyi goggo ce tayi tsaki sannan tace oh fadimatu ke dai Allah ya wadaran ki sai da kikaje Dan
uwanki yazo sannan kika zo koh? ” shiru fatima tayi nadan wane lokaci, ta matsa kusa da goggo tace
inayini? ” tsaki taja sannan ta kalle mudassir tace ga bak’ar kanwarka nan in banda bin maza babu
abunda takeyi, ” mik’ewa mudassir yayi Sannan ya shige dak’in sa batare da waiwayan goggo ba, “
hakan yasa fatima ta bishe jikinta duk ya mutu da kyar ta’iya sallama ta shigo, ” dariya ya sakar
mata au babu murna nadawo? Rungume shi tayi sannan ta fashi da kuka, ” au Har yanzu baki daina
kukan ba? Haba fatima kinsan bazan taba yadda da zancen su ba, Duniya ce k’i kyale su ta ishe
kowa, nema da Nadawo bata kyale niba Sai da ta cimun mutunci dan haka ki cigaba da hakuri, “
share hawayen ta tayi sannan tace to yaya, tafara bashi zancen auren, ” karki damu Allah Yana tare
daki gobe zaki koma makaranta kinga jarabawar karshe kike dan haka ki dage kinje? Kuma wa kikeso
a samarin nake? ” cikin kunya tace Dr ammar nakeso, ” tohm Allah tabbatar da alheri, ” haka suka
dinga hira Har sai da Arif yazo suka tafi tare. Tunda ta shiga mota takeyin waya da Dr ammar sai
murmushi takeyi, ” Ya arif yace Wai mune ko wa zai k’washek’i ya k’washe asara, ki dinga adduar
barin jiki ya fishe da dariya, ” kallon sa tayi maganar tai mata ciwo Amma tayi masa banza, kiran Dr
tayi tana wane Nan narka murya, batasan sun shigo gida ba, ” Arif yace banza karya Mai bin maza
wayasan ma… *Urs Nana Diso* *20-25* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Arif yace banza karya Mai bin maza wayasan ma.. ” baba Mai
gadi ne yace Arif yaushe ka kuma haka karka manta yarinyar nan marainiya ce, ” Fatima ce tace
haba baba ba sai kayi magana ai Duniya ce! ” tabbas ‘yar nan kinyi magana Allah ya ganar dakai, “
arif wane mugun kallo yayi musu sannan ya kalle Fatima ki kaimun abinci inajeranki ” to tace sannan
ta nufi kofar shiga gida, wanka tayi sannan ta nufi dak’in hajiya a k’an gado ta sameta, sannu da
hutawa mai za’a dafa ne? ” tuwo zakiyi sannan kiyi lemo kishirya anjima zan aiki ki gidan zainab
k’anwata, to hajiya. Kitchen ta shiga tafara girke sai gurin karfe 4 tagama jirasu tayi a dinning, tafara
wanke wanke arif yashigo dak’in ta tana zaune tana ta waya ita da Dr ammar Sai dariya takiyi,
lokacin da arif ya shigo tunda ta kalleshi ta cigaba dayin wayarta. Hakan ya batawa arif rai baisan
lokacin da ya k’wace wayar ba yace wato bakida da tarbiya ko? Natsaya ina yimiki magana kina chan
kina waya da Yan iskan samarin ki, ” haba ya Arif kafi kowa sanin wanene Dr ammar Kuma yanada
cikin wa yanda nakeso a rayuwa ta kuma wanda nake burin kasance wa tare dashi, kuma lokacin da
ka shigo ba kayimun magana ba, ” tsake yayi sannan ya cillar da wayar ta wannan ce wayar da k’ike
waya da Dr ammar na fasa ta inda abunda zakiyi sai kiyi, ” k’walla tafarayi sai tayi gurin wayar tana
kuka dubi yadda ka fasamun waya bakomai duniya ce, ” banza kawai nafasa ko kinada wane gata ne,
” banida kowa sai Allah, ” dallah tawo mutafi. Dak’in hajiya ta huce ta sanar da’ita ta gama aik’in ta
bata sak’on gidan anty zainab, ” ga sak’on nan in kinje sauran k’ike yi mata girke daga nan kubiya
gidan usman matarsa zata bada ank’on ku, ” tohm hajiya. Arif ta tarar a mota ya nata hira shida
amira awaya, abunda k’un nanta yajiye mata shiyasata zama amotar tare da k’allon ya arif, ” amira
kinsan dai ina bukatar mace kullum mumy maganar ta yaushe zanyi aure, kullum azumi da shan
magunguna, ” amira tace karka damu bikin nawa ai baife sati biyu ba kadaina damun kanka, ni ta
kace, ” tohm sweetheart sai nadawo mayi waya, “okay ” fatima ce tace gidan anty zainab zaka kaine,
lokacin da ya dago idon sa yayi jajir, ” sauri tayi ta kau da k’anta, ” fati I can’t drive! Jiki na yayi
sanyi, ” fatima cikin tsoro tace tohm cikin kankanin lokaci suka isa gidan ta, ” arif sai kallon ta
yakeyi, suna isa gidan da saurin ta tafita, dan k’ota yayi tanata fizge hannunta, kokari yakeyi ya
rungumeta ” kuk…… *Urs nana diso* *25-28* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Arif ne yak’e k’ok’arin rungume ta ” k’uka ta sak’a tana
k’ok’arin tureshi sai ga sadik d’an gidan anty zainab ya fito, Arif ne yayi saurin sak’arta, ” itama ta
gyara mayafin ta da ya wado, ” a’a fatima sai yau ak’aga damar zuwa? ” Arif yayi saurin cewa ai ne
na matsa mata ma da bazata zoba, ” gaskiya ka k’yauta yaya arif, ” murmushi tayi ta gaida sadik
suna hira suka shiga cikin gidan, ” Fatima bari naji nadawo ana jirana a office Amma ak’wai maganar
daya k’amata muyi which is very important, ” okay Sai kadawo, arif yana zaune yana jinsu a palour
sai sake sake yakeyi yadda fatima ta kida farin jini, ” tashi tayi ta shiga dak’in anty zainab sai
sallama takeyi Amma shiru a hankali ta bud’e dak’in anty zainab ta gani a zaune tayi ta gumi, zama
fatima tayi ak’usa da’ita ta janye hannun sannan ta kalleta da manyan idanun’ ta “yaushe kikazo
fatima, ” hmm kikuwa anty zainab maik’e damun k’e? ana ganin fuskark’i anga damuwa a cikin ta
duniyar nan dole sai muna hakuri, ” anty zainab ce takalle ta sannan tace fatima rayuwar gidan nan
tafara i’sata kullum Hakuri nakeyi Amma Abu yace tura, baban su sadik ne yak’e neman mata ga
kuma shaye shaye, ” subhanallahi cewar fatima garin yaya anty zainab tuntune baiyiba sai yanzu, “
wallahi fatima nayi hakurin nayi fadan Amma har yanzu na rasa yadda zanyi kullum addu’a na k’eyi
amma shiru.. Haba anty zainab k’i cigaba da hak’uri k’owa da irin kaddarar sa Kuma ki cigaba da
addua komai zaizo karshe, k’i dage da sallar dare da yawan sadaka kinsan tana maganin masifa,
Kuma gaskiya kema ki gyara shi namiji dan lallama ne k’i dage da tsafta kwalliyar nan irin ta zamani,
yawan kunshi da gyara kanki, Kuma ki dinga tararrayar shi karkiga wai kin kwana biyu, wallahi ahaka
karuwai suke kwace muku mazaje gurin kwanciya dai kinsan komai banda abunda zance k’in fine
sani, ” gaskiya fatima Allah miki albarka mijinki yaji dadi nutsuwar ki da hankalin k’i kullum suke k’ara
burgeni Sai naji Dama Sai k’uma tayi shiru..” fita sukayi palour arif yana zaune takaici duk ya i’she
shi, ” anty zainab ce tace au tare da arif kukazo ai baki gayan ba, ” arif cikin fushi yace ina zata gaya
miki ai burinta ya cika tunda kun shanya ni yadda tak’eson, ” ki tashi mu tafi kafin na k’wade ki, “
anty zee bataji dadi ba tace ga dubu uku kyasaka kati, ” angode Sai anjima.. Tunda suk’a dawo gida
hajiya k’e faman yi mata masifa wai ta dad’i, ” hajiya kiyi hakuri danAllah banson rank’i yana baci
domin k’in zamar min kamar tamk’ar uwa, ” hajiya tace ke dai da kinada kishiya ta shiga uku yarinya
karama sai kissa, ” shamsiya tace hajiya gobe zamu fara exam need your prayers, ” karkida mu
shamsiya za k’ice ai ke kuwa Fatima naga ta inda zakice tunda bakida mai yi miki addu’a, ” kuka
fatima tasaka tana fita taga Dr ammar ajikin mota karasawa tayi ta gaidashi, ” fatima kina lpya tun
jiya nakasa bacci saboda banji muryar kiba, ina wayarki? ” kuka ta saka masa, ” ai nasan hakan zai
faru ga wata nasiyo miki, ” wane satin za’a kawo kudi, ina tayi miki addu’a zakice jarabawa kinje, “
dariya tayi wanda yakara k’awata fuskarta ” wane dadi Dr ammar yaji azuciyar sa, ” banda bak’in yi
maka godiya, fatana na kasance tare da k’ai yadda zan nuna maka k’auna, ” wane irin ajiyar zuciya
yayi kice tawa Kuma kinake so, yanzu inada aiki zamuyi waya later Tohm bye yace bye darling….
D’uk an cik’a a palour din hajiya ‘yan gidan su duk sun taro, fatima tana kitchen tana ta girke tana
gamawa ta k’ai musu daga mai harara sai mai habaice, babu wanda ta k’ula, dak’in ta ta huce wanka
tayi sannan tasaka wata gown tayi mata kyau, fitowa tayi a bene ta hadu da arif ” ke ina abinci na? “
Yana kitchen, ” jan hannun ta yayi har tsakiyar palour hajiya wannan ‘yar ta k’e ta raina ne abinci ma
bata kawo mun, ” abdul ne Yace woow perfect match gaskiya kyan ta ace matarka ce, ” arif ne ya
kalleta daga Sama Har kasa, ” Amma abdul ka cuceni Mai zanyi da ‘yar iskar nan? ” ai batada
masoyi, ” hahaha suka saka dariyar kowa yace gaskiya kam, ” Fatima batasan lokacin da tafara k’uka
ba, Allah kadai yasan miji na, Kuma karku manta ne ma mutum ce, ” shamsiya tace kinsan dai ya arif
yafi karfin ki, ” dariyar ta k’aice fatima tayi sannan ta nuna arif, ” haha wannan tuzorun mai zanyi
dashi? ” ai Kowa yanasan ya samu miji nagare amma ya arif na tsane shi ban sonshi, ” wane wawan
mari ya sakar mata….. *Urs nana diso* *28-30* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Wane wawan mari Arif ya sakar mata, ” rike fuskar ta tayi
sannan tace lallai ashi kaje zafin maganar da nagaya maka? Hmm d’uk’an k’an ku da k’uka dage
kuna yimun dariya, ya arif yafi karfina Kuma shi ba sa’a na bani ba, Kudi, dukiya, kyau, ilimi duk
yanada su! Ke da Ke da ke shamsiyya dukanin ku burin ku ku same miji kamarsa ko kuma ku
kasance tare dashi, ” to let me tell you na tsaneshi natsane ya arif babu wane Abu da zanso atattara
da kai, ” duk palour sunyi shiru, ” barin palour din tayi Sai data hau Saman bene taji an hankado ta, “
firgeta tayi tayi saurin rike karfin gurin, ” Arif ne ya kalle ta yadda kika gayan maganar Nan Sai kinyi
nadama, ” tsake tayi tashige dak’inta. Hakan yakara batawa arif rai dak’in sa ya huce, duk lokacin da
ya tuna maganganun da fatima tagaya mai zuciyar sa hassala takeyi, wata muguwar dariya yayi
wacce ta k’awata fuskar shi wanka yayi ya shirya zuwa gidan su amira, Lokacin da ya’isa abban ta
yana waje yana hutawa, Arif ne ya tsugunna har kasa ya gaida shi, ” cikin sakin fuska suka gaisa. sun
dad’i suna hira sannan ya shiga cikin gidan, ” amira tana dak’i tana shiryawa ta saka wane yadi pink
tayi kyau sosai ta shiga dak’in ummi, ummi na kallon ta tace ke yarinya karki raga masa gurin ansar
kudi in da hali ma ki ce masa miliyoyi karki raga masa, domin da Dan kudin zamu karamiki kayan
dak’i, ” tohm ummi karki damu indai arif ne zai bani. Tana shiga palour ya cika da kamshi ita kanta
sai da ta lumshi idanu wanta, ” ayayin da arif ya daga k’ansa ya kalle amira gajeriya ce kuma bata da
kiba, Amma fara ce kal ga hanci sai dai idanun ta kanana ne, shekarar ta 21 tagama makaranta
Amma mahaifinta bayason cigaba da secondary ba yadda batayi akan yabarta ba Amma yace ko da
zata shekaru ahaka sai dai tayi Amma makaranta Sai bayan ransa, hakan yakan batawa itada
mahaifiyarta rai saboda, saboda duk wane plan nata ya warga zamata. Wane kallo tayi wa arif Wanda
ya harge tsa shi, murmushi yayi mata, bashiri ta matso kusa dashi, ” my sweetheart ykke? ” yadda
kike haka nema nake, ” opps Har naji wane dadi kullum son k’a k’ara shiga zuciya ta yakeyi, haka
suka dinga soyayya ya bata katin dinner da na kamu, ” Amma katin yayi kyau, ” yanzu mai kike
bukata na biki gobe zanyi tafiya, ” kamar 2million sun i’sheni, ” hmm Amira komai fa nayi Miki hatta
turare nasiyo zan bada dubu d’are biyu, ” Bata rai tayi haba arif gaskiya sunyi kadan, ” mik’ewa yayi
in bakyaso Sai in mayar, ” tsake tayi sannan ta ansa. Fita yayi straight gida ya huce, kowa Sai shirye
shirye suke, hajiya anatayi mata kunshi, ” shamsiyya tana gwada kayan su, ” arif yace yayi kyau
d’ink’in ko? ” eh ya arif Amma gaskiya banso aka yimana tare da fatima ba, ” anty zee tace ki dai kije
tsoron Allah sannan ta fizge kayan fatima, tana dawo wa ta shiga daki anty zee tagano, a’a saukar
yaushe, ” safe, ya jarabawa Ana final year Allah yabada sa’a, ” lpylou jarabawa babu dadi Allah dai ya
bamu sa’a, ” Arif yace ai dama ita jarabawar bata dak’ik’ai bani ba, ” shamsiyya tace kwarai kuwa, “
ko kallon su batayi ba, ” hajiya ce tace ke bawai kina jarabawa ba ban dora abinci ba, ” anty zee
cikin mamaki tace haba Yaya tun zuwa na yakamata kigayan da tuni nagama, Amma fatima ta gaji,
bari naje na dora, ” aa ba sai kinje ba anty zee kibarshi ne zan dora, ” kitchen din ta huce taji ta
dora. Ke fatima ke fatima dallah malama ba kirank’i nak’eyi ba, ” Wai shamsiyya ya kikeso nayi
karatu fa nakeyi, ” kayan ta k’waso ta watsawa fatima to jaka gashinan na ankon ya Arif ne, ” hmm
wai shamsiyya mai nayi Miki? ” Arif Yana kallon su jira yakeyi yaji mai fatima zatace, ” ubanki kikaye
mun banza jaka kayan bikine ko bakyaso? ” haha ai basai nafada ba Mai zance nayi abikin ya Arif
banda lokacin zuwa cux natsane Naga fuskarshi, ” zuciyar arif ki bugawa ya rasa mai zaiyiwa fatima
gaba daya kwarfota yayi bata ankara ba ta wadi tim… *Urs nana diso* *30-33* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Sa na d’iyar fad’uwar da fatima tayi hak’an yasa bak’in ta ya
fashi sai jini! Nan da nan hankalin arif ya tashi ya matso Yana kokarin rike hannun ta ta fisge, cikin
kuka tace karabu dani, ” bai san lokacin da yaja hannunta sai bandaki ba, cikin k’ink’ina yake magana
sannu fatima kuskure ne, ya wanke mata bakin, ” kallon sa takeyi cikin tsana da kyamar sa, ahankali
ta fizge hannun ta tayi hanyar waje, sannan tace da kasan yadda natsane ka wallahi bak’aso k’allon
fuska ta ba, juyawa tayi hips dinta suka wane kad’a ” arif ne ya rike k’ansa ciki da takaice, fatima
wallahi sai kinso ne ko ki naso ko ba kyaso.. Sama ya hau ya d’akko jak’arsa sallama sukayi da
alhaji, sannan ya shiga part din hajiya tana zaune tana waya katse wayar tayi da taji ya shigo, ” ango
tafiyar ce? ” eh hajiya jibe da huri zan dawo, ” tohm akwai wasu kaya aleda adak’in fatima ka dauka
katafarwa da mumynk’a, ” tohm hajiya ina shamsiyya tazo ta rakani airport, ” kiranta hajiya tayi tace
bari ta shirya, ” shi kuwa arif dak’in fatima ya zarce ko kallon sa batayi ba karatu takeyi, sak’on ya
dauka, ” shamsiyya ta shigo ta dauki mayafin fatima cikin gadara tace ke na dau mayafin ki, ” Fatima
ko kallon ta batayi ba, ” arif ne yayi dariya sannan yace idiot sai girman k’an tsiya ni kuwa zanga mai
aurenki, ” shamsiyya ce tace ai ya arif sai talaka irinta shi zai iya auren ta, kuma ai mai uba shi zaiyi
alfahari, ” arif yaja hannun shamsiyya, ” Fatima cikin kuka tace kafin a dau abun mutum ake
tambayar sa ba bayan an d’auka ba, ” shamsiyya cikin masifa tace ubanki ne yasiya miki, ko kuwa
uwarki? ” fatima tace a a alhajin kine ya siyamun, ” arif ya jata suka tafi, “wane sabon kuka tafashi
dashi ahaka Har bacci ya dauke ta… Lokacin da ta farka karfe hudu, wanka tayi ta saka kayanta ta
sauka kasa, tabarma ta shinfida sannan ta fara karatun ta, kamar daga sama taji muryar maryam,
daga k’an da zatayi taga maryam ba yadda ta saba ganin taba, ” fatima ce ta janyo ta maryam lafiya
mai yafaru? ” kuka ta sakar mata sannan tace fatima danAllah mai nayiwa baffa ya tsaneni? Fatima
kinfi kowa sanin banda samari amma idan a kazo gurina baffa sai yakore su, ya kai ya kawo ko girke
nagama sai anty atine tace na sace nama, ga auwal ya takura mun sona yakeyi? Komai zan taba
agidan nan sai an mun sharri yanzu ma zaneni sukayi wai na sace sabulo, walhi ne zan gudu..”
dak’ata maryam *Duniya ce tafi bagaruwa iya jima* ki godewa Allah wallahi dama ya jarrabi ke,
komai komai mai huce wa ne, kanin mahaufin ki ne kiyi hakuri Dan Allah wataran sai labari, ” ke
fatima nifa dadi na dake bawa mutum hakuri, ” mtsew kinga maryam rashin hakuri baya haifa komai,
koma guduwar da kike anbata an gayamiki abune mai kyau? Wallahi kiyiwa kanki fada kikama
maraicin ki, kuma kidage da addu’a duniyar ce dole sai da hakuri, ” tabbas fatima zan cigaba dayi
nagode, bari na tafi Kar nayi laifi, ” tohm ki gaida gida, ” zaije sai munyi waya… *Urs nana diso* *33-35* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Tana i’sa gida gate din da zata bud’e taji tayi k’aro da ya arif,
wane irin k’allo yayi mata sanadiyar haka ta sun k’uyar da k’anta, Chan k’uma ta tureshi, huce war da
zatayi arif ya rik’o ta, ” menene haka ya arif ka sakeni nagaji Ina bukatar hutawa, ” hutu ai sai d’an
gata kije dak’ina ki gyara mun k’uma akwai kayan da mumy ta bak’i, ” nagode mata, ” what about
me??? ” ai Ana godiya ga Masoyi ne ba mak’iye ba so ka daina shiga rayuwa ta, ” arif ne yagyara
tsayuwar sa common inajinki mai kikace?? Kin tsaneni? ” ohhh how many times zangaya maka? Na
tsaneka, ” Arif baison lokacin da ya matse mata wuya ba, i’don sa duk yayi ja, kika Kara cewa kin
tsane ni sai na karya k’i ya hanka d’ata ta wadi, ” wayyo Allah na wallahi bazan daina gaya maka na
tsaneka ba wane kuka ta saka… Shirye shiryen bikin *Arif* ake tayi, fatima ko ajikin ta, ita jarabawar
ta ce a gaban ta, yau tana skul last paper zasuyi, friends dinsu suna ta amma sai dai tayi murmushi
bata kula kowa Hakan yasa Yan class sai tsiya suke mata, gurin 2 suka gama jarabawa suna fitowa
ta huce k’asuwa siyayya tayi, a hanya ta hadu da hamid abokin ya arif tsayawa yayi, ” kanwar mu
ykke? ” oo ya hamid kana lpya yagida, ” duk lou k’asuwa kikazo ne? ” eh , ” dama gidan naku zani
tawo mu tafi, ” bude gidan baya tayi taga alamun mutum agaba amma bata ga fuskar sa ba, ” fatima
kunata shirye shiryen biki kenan, ” suna dai tayi, ” fati kenan ai nina zata dak’e za’ayi, ” ne walhi
kafara batamun rai mai zanyi da ya arif ne natsane shi ma, ” arif ne yace kema mai zanyi dak’e dan
uwarki? ” ya hamid sauke ni na karasa, ” arif yace kina fita zan karya ke, ” hmm Wai shi mutum baka
damu da shiba amma ya takura maka, ” hamid ne yayi dariya wallahi kuyi a hankali, ” suna i’sa gida
taga Dr ammar murna agurin fatima kamar ta Rungume shi, ” Dr na mai yafaru naga fuskar ka haka?
” wallahi ina sonki Kuma ina kaunar ki, zan tafi ba don son rai na ba, ” hawaye ne ya wanke fuskarta
cikin shash shek’a mai kak’e nufi dr, ” fatima zan tafi karo course a Germany, “tohm Allah ya kiyaye
amma duk abunda kadawo ka tarar karkaga laifi na, ” arif da hamid sun sak’e baki suna kallon su, “
juyawa fatima zatayi Dr ammar ya riko ta, ” cikin k’uka ta rungumesa, ” zan dawo fati kidaina kuka, “
na daina na daina, cikin gida ta ruga aguje, ” motarsa ya koma ya fita daga gidan, ” lallai Arif fatima
tayi ashe Dr takeso, ” kai malam sai fa ta sone ko ta naso ko bataso, ” hahaha lallai kana da aiki..
Sama ta hau kuka takeyi ma cike da tausayi, ka tafi kabarne Dr in sonka ina zan kai sonka, zan jira
ka ko da kuwa za’ayi shekaru, ” Arif ne yasa dariya sannan ya zauna kusa da ita hannun ta ya rik’e, “
malam banson iskance kadaina rike ne Wannan ai, ” ke dakata zanyi maganin ki zaki zama tawa zan
kuma tabaki Sai yadda nayi da k’e, ” in ka i’sa na kasa nafara son ka, ” zakiyi zakiyi fita yayi yabar
dak’in wanka tayi tafara sallolin ta cike da kai k’ukan ta gurin Allah .. K’owa ya k’alli fatima yasan ta
rame, duk ta canza ta koma shiru shiru, aikinta takeyi kafin ma ayi mata zancen, yau ranar jumma’a
gida ya cika da mutane ga wani ciwon ciki da ke damunta, karfe biyar zaa tafi, janan gurin kamu, “
shamsiyya ce ta wanka wa fatima mari k’owa na gurin sai da ya jiyo, ” me nayi miki zaki mari ne? “
ke yar iska tun dazu ina jiran ki bak’i dura abinci ba… ikon Allah yanzu Akan abinci kika mari ne? “
eh akansa Kuma kika kara magana kije saukar wane banza wacce bata iya komai ba, ” ke shamsiyya
dakata ke bansan irinki Ba babu abunda kika iya sai tsanar mutane, babu abunda kika iya tunda nake
agidan Nan bantaba ganin kinyi girke ba, ke bakisan kowanne namiji burin sa macen data iya girke
wacce ta kida ilimi yar kwalliya mai hankali, hmm babu abunda kikasa agaba sai cin mutuncin
mutane, ” wani wawan mari hajiya ta sakar mata yar iska mai bin maza ke maga mai aurar ki, “
fatima murmushi tayi tace *Duniya ce* kuyi mun duk abunda kukeso tayi tafiyar ta, ” nan fa kowa
yafara maganar shamsiyya, ” Arif yana can ya kasa zama burin sa gobe tayi ya kasance tare da
matarsa, wane mugun feeling ki damun sa, Amira ya kira awaya sai kuka tak’eyi masa nan hankalin
sa yakara tashi, ” Amira please aina zamu hadu, ” dariya ta saka kai da gani na sai an daura, ” please
ki taimaka min ” sorry dear ta kashi wayar, ” sallah ya tashi yayi…. *Urs nana diso* *35-38* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Tun k’arfe biyar moto ce suka cik’a a k’ofar gida kowa Sai
shirya shirye yakeyi, shamsiyya ta saka wane material purple anyi mata wasu matsatsun d’in ki, sai
iyaye takeyi hajiya ce ta shigo dak’in ta, ” kai shamsiyya irin wannan kyau haka, ” hajiya ai dole na
dau wanka kinsan aboka nan ya Arif sun hadu, ” gaskiya Kam ne munyi gaba sai kin tawo, ” jabir ta
kirawo awaya cikin yace mata yazo, sakk’owa tayi daga Sama taga su mumy duk sunzo, ” mumy tace
ina yar uwartaki, ” mumy sauri nakeyi bansan inda ta shiga, Sauri tayi tafita a gate ta hadu da
rufaida, ” yayi yar iska kinyi kyau sosai batsalar ba hips ba gaba, ” dallah yimun shiru bakin ciki
kikemun, ta shige mota, ” Allah sawake Miki, cikin gida ta shiga duk an tafi babu kowa dak’in fatima
ta shiga ganin ta tayi akwance, ke Fatima mayi haka mutane kowa yana tambayar ki, mai isa bake
shirya ba? ” ke rufaida kyaleni wayannan mutane ai basu da kirki naji nayi musu me? ” lallai fatima
dole suce bakin ciki kike musu, malama kitashi ki shirya danAllah sai mutafi tare GA uncle chan a
mota yana jira na, ” fatima cikin Sauri ta shiga wanka, tana fitowa turare ta fesa sannan ta dakko
wane less din ta, ” rufaida ce tace woow wannan lesin ya hadu Anya bazaki fi Amaryar kyau ba, “
fatima tace wallahi kika kara damuna zan fasa Kaya ta saka, ” wayyo Rufaida kiba nakeyi, haha
hajiyar hips da..” dallah yimun shiru zokiyi mun kwalliya cikin lokaci kankani fatima tayi kyau sosai
head ta dora orange sai sarka da takalmi, ” wane mayafi ta d’akk’o zata yafa, ” haba fatima danAllah
karki yafa please, ” yaza’ayi na fita haka god’e god’e..” malama kibawa makiya kunya, ” hmm muje
to, wata hadaddiyar mota suka shiga, ” ai bangani kiba nazata amaryarce, ” kai uncle inayini? ” Lou,
Amma kinyi kyau, ” nagode uncle… Arif Da Amira sunyi kyau shigar blue and white su k’ayi, amarya
sai iyaye take tayi masa, a mota sun kusa karasawa tace ” Arif baka bani kudin leki ba, ” kallon ta
yayi jiya ba nabaki kudin leki ba? ” na rabawa kawaye na, ” hamid ne yace to ga 20k kiyi lek’in, ” ko
godiya batayi ba ta ansa suna isa kofar janan event aka bude musu gate, ” masu hotona sai faman yi
sukeyi, ” Kowa ya kalle Arif sai yakara saboda k’yan da yayi, ” Amira sai shishige masa Takeyi, kowa
sai hotona akeyi musu suna shiga hall suka zauna a kujera, masu kida sai yi sukeyi, ” su shamsiyya
kuwa sun dadi a filin rawa gani take tafi kowa kyau, hajiya kuwa murna ta isheta ‘yarta tayi kyau,
sunaye aka fara ambata wanda zasu zauna a dinning…. Kowa sai kiran sunan ta akeyi da saurayin ta,
ankira sunan fatima shiru cikin mintuna fatima suka fito daga mota, gaba ta danyi, ” uncle yayi saurin
jawo rufaida tace naam wallahi ina son fatima tana da wanda takeso, ” to zan gwada sa’a ta ” tohm,
” sai da zata shiga Hall taga basu karaso ba, baya tayi uncle katawo mutafi, ” tohm kanwata, ajeri
suka shiga, kowa kallonta, karasawa tayi gurin momy ta gaida ta, ” ai Har raina ya bace, ” gaba daya
hankalin Arif Yana kanta, ” hakan yasa Amira tace waccan wacece yace tawace, ” cikin gyatse nan
fuska tace oh itace wacce ka tsane ta ashe, ” yayi dariya, ” masu kida suka fara yawon fatima yar
masu kyau ‘yar asalin kyau uwa ilimi ga wajen zamanki, sai ku tawo tare da mijinki, ” uncle ne ya
rike hannunta suka tafi gurin zamansu sai leke yake mata, ” taji dadin hakan da yayi mata sai kallon
sa takeyi, rada mata yayi a kunne nayi kuskure but ayimun afuwa, ” kashe masa ido tayi bakomai, “
cikin mintuna kuma fuskarta ta canja, Bakowa take tuna waba daya huce Dr ammar, ” momy ce ta
katse Mata tunanin ta….. Fatima kitawo muje kiyi rawa, bikin d’ana guda, ” ne ne momy ki kyaleni
bazan iya ta shiba, ” oh fatima nah sokike aji kanmu? ” uncle ne yace tashi mana kitafi, ” to tace
suna shiga filin, ” shamsiyya da hajiyar ta kamar su mutu dan bakin ciki, bama e kayan jikin fatima
yadda take daukar hankalin mutane, ” l’eke taketa yiwa amarya, Masu kida Sai washe ta sukeyi, ” Arif
ne yajata gefe kamar zai Bata kudi, ” Wai maye haka ya arif, ” idiot ina mayafin ki ahaka kikazo kowa
sai kallon ki yakeyi, ” tsake tayi tashiga filin tafara rawa, ” Arif hankalin sa yakara tashi..” fatima ce
tafito domin tagaji da rawa, ” Arif yayiwa ameera karya ya biyo fatima hannun ta yaja ya jefa ta a
mota, wane irin gudu yakeyi Har Sai da ya’isa gida dakin ta yakaita wasu mari ya sakar mata, kuka
tafara yi, ” iskancin nake Har yakai kidinga shigar nan kalle ki? Wallahi kika kara fita haka saina
ballaki idiot Mara kamun kai wawiya, ” wayyoo Dr ammar Wallahi ina sonka, ” Arif cikin fushi yace za
kuma kirabu dashi ba, ” Mota ya koma baa tashi daga dinner ba sai 10, ” fatima tunda tayi wanka
tafada gado sai bacci….. Yau lahadi aka daura auren *Arif bello*da *juwaira (amira)* Akan sadaki
dubu dari, ” Kowa murna yakeyi aka zarce gidan amarya akasha hotona, ” su shamsiyya bakin ciki ya
i’sheta kullum gaba fatima takeyi amma ita tana baya, ” affan sun shigo tare da ango Sai hotona
sukeyi ” shamsiyya ina fatima, ” tana daki, aguje ya shiga kanwata kina ina? ” akujera ya sameta da
wata gown Jan hannunta kawai yayi ya affan bari nadau mayafi, ” cikin zumudi ya kaita cikin Yan
hoto, ” jiyowar da Arif yayi yaganta take ya daka mata tsawa, ” affan yace mayi haka Arif, ” tabar
gurin nan, ” fatima cikin bakin ciki tabar tsakar gida kuka takeyi mai tsanane ahaka ya muddassir ya
kirawo ta mayafi tasaka ta sakko, ” gaisawa sukayi suka sha hira da Dan uwanta…….. Karfe bakwai
aka kai amarya gida yayi kyau haka akayi siyan baki aka barta ita kadai, ” Amira murna agurin ta
ba’a cewa komai gida 3 part ga motoce, wanka tayi sannan ta saka kayan bacci ta kwanta, ” Arif ne
yashigo yace tatashi suyi sallah, sukayi yayi addu’a suka kwanta, ” han da nan hankalin Arif ya tashi
shafata yakeyi ko ta’ina kayanta yafar…….. *Urs nana diso*
*38-40* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Nan da Nan hankalin arif ya tashi, shafata yakeyi a hankali,
cikin mintuna kalilan ya furgeci Sai da ya rabata da kayan jikinta, ” amira Har tausayi arif yake Bata
yadda yake da mugun feelns, Amma Kuma wane yariga shi! Kuma mum tace bazai gani ba, Wane irin
kukan shagwaba takeyi masa hakan yasa yafara aikata sunnah, ” ina ranshi ya bace da yaji ta abude
atake yasake ta, ” kuka Takeyi mara sauti, ” arif kuwa rigarsa yasaka yabar dakin cike da bakin ciki
da nadama. Acikin daren amira takira mumynta awaya tayi saa kuwa ta dauka, ” Amira lapia da
tsakar daren nan? ” momy Arif yagani wallahi yagane! ” oho yanzu dai kisame shi kibashi labarin
komai, ” tohm momy dak’in sa ta nufa Amma yasaka key, ” arif wallahi ina sonka please ka bude kaji
wayoo arif, ” Arif da yayi wanka zuciyarsa Sai faman tafarfasa takeyi, ” mai isa amira tayi mun haka
tasan ina bukatar ta Yana saki sak’in bacci ya kwashi shi… Da asuba yafito zai tafi masallaci yaganta
akofar dakin tana bacci haushi da kyamarta yayi banza da’ita yayi tafiyarsa masallaci, tana farkawa
taga bayanan wanka tayi sannan tayi sallah wasu kaya ta saka sannan ta hau kan gadon sa, ” Arif
Yana dawowa sanadiyar fitilon akashe suke gadonsa ya hau, “Yana hawa ta rungume shi tana kuka
wallahi kayarda kaddara ce Arif, ” kaddarar bin maza, ” a a arif karkace haka lokacin da ina ss3 a
Kwai wane yaro da muke soyayya, anyi anyi arabamu dashi Amma dayake ina sonsa duk wanda yace
na rabu dashi haushin sa nakeji, watarana yajani zuwa gidansu muna shiga baba mai gadi yace
yarinya kituba kirabu da yaron nan, nan nace masa kaga tsoho shiga hurumin ka, ” bakomai yarinya
DUNIYA CE!!! ” ahaka ya yaudari ne Har ya rabani da budurci na, ” wallahi tun alokacin na tuba, ina
sonka Arif, ” rungumeta yayi ahaka har suka gabatar da sunnar su….. Fatima ke fati dan ubanki ba
daki nake magana ba? ” hajiya banjiba ina wanke toilet ne, ” to arif ne yakira yace adafa musu
abinci? ” abinci fa hajiya kin manta dangin Mata kiye, ” ke kek’i yayi ne, to anan zaa dafa musu kuma
ke zaki dafa, ” hajiya danallah shamsiyya ta dafa, kinga ko gama gyaran dakuna banyiba ga gogar
Alhaji, ” muryar shamsiyya taji tana wallahi bazan ba, ” Amma karfe hudu graduation din mu, ” ke yar
iska sharhin mene haka? Sai kin dafa, ” cikin hawaye to, ahaka takarasa aikin ta, ” ta dora girke
sannan ta shiga wanka, bai fi awa daya ba tagama komai ta saka riga da wando, Fatima tayi kyau
sosai, ” Dakin hajiya ta huce hajiya zan tafi , ” ita kanta hajiya taga kyan fatima amma saboda bakin
ciki takasa nunawa, ” ke mai kike nufi ne? Ko ne zan kai musu abincin ? Dallah malama shige ki tafe
ki kai musu daga nan kya huce skull din, ” cikin murmushi tace to hajiya, ” takai kofa kenan hajiya
tace karta dauke kowacce moto Sai civic, ” tohm hajiya…. Driven takeyi cikin nutsuwa, al’qurani ne
yake tashi acikin motar a hankali ta’isa gidan Arif lallai gida yayi kyau sosai, horn tayi aka bude
fitowa tayi tarike basket din abincin, sallama tayi taje shiru, ” Amira ce tafito daga daki, ” cikin
yatseni tace oh yama sunanki, ” am sorry bashi nazo fada ba, ” Arif ne yashigo kin kawo kenan” tace
kaduba kagane, ” har zata fita yace ga wanken toilet dina, ” ficewarta tayi tare da Jan tsake, ” amira
ce ta shiga daki cike da tunanin kyan da Fatima take da, ” Arif ne ya bita mota, ” excuse me please
zan tafi, ” ja motar tare zamuje batayi wane magana ba taja mota sai jami’a kowa yasa kayan grad
abin sha’awa tana fita taga ya mudassir murna duk ta’isheta haka akadinga gabatar da kyaututtuka
murna gurin Fatima ba’acewa komai hotona sai yinsu akeyi, ” shamsiyya Kamar ta mutu duk
yawancin kyautukan Fatima ce tasamu, a haka a kabawa kowa certificate ya tafi gida, tare da ya
muddassir suka tawo, agida ta sauke shi Arif kuwa gida ya huce…. Tana shiga baba mai gadi yace
yar jarida Allah miki albarka tace amen alhaji kuwa sai haushin ta yakeji yadda tafi ‘yarsa kokari, “
wanka taje tayi ta zauna ta nata tunanin rayuwa, ” hajiya ce ta shigo tafara dukan Fatima da waya
dan uwarki ina kudina jiya alhaji yabani har kin sace du k’anta takeyi ko ta’ina ahaka Arif ya shigo
hajiya kibarta haka mana, ” nezan biya kudin tohm tohm walhi da saina karya ta, rungumeta yayi yana
Bata hakuri, malam ka kyaleni *Duniya ce* komai sukayi mun Allah zai sakamun, kallonta kawai
yakeyi cike da burgeshi da kuma kwadayin ya so ta, ” hajiya tashiga Dakin shamsiyya ta tarar tana
wanka, tana bude jakar shamsiyya tana kudinta shiru tayi takasa magana, ” Arif ne yace….. *Urs
nana diso*
*40-42* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Arif ne yace dama ai gashi nan wanda baka tunani shi yakeyin
abunda yaso, kun lalata shamsiyya bata ganin kowa da mutunci, Wai kuma ahaka take fatan samun
miji nagare ai duk mace ballagaza, shasha sha wacce bata kame kanta da mutuncinta ai ba abar so
baci ba, ” hajiya ce tayi tsake kai arif ai kasan shamsiyya k’in kowa k’in wanda yarasa ce! kuma kudi
nasan Fatima ce tasace..” kafin takarasa maganar ta Sai ga shamsiyya tafito daga bandaki,cikinta ne
ya kada kafin bisane tace dama dama hajiya, ” arif ne yace yimun shiru munafuka, ” Wai Dan na
dauke dan wannan kudin shine kuke mun ihu? ” kafin takarasa maganar taji mari, ” shiru tayi takama
kumatun ta, ” hajiya tace arif harda mari? ” kadan ma tagani wallahi tunda iskance tasaka agaba,
kuma kidafa abinci akaimun nawa office akaiwa amira nata, ” wallahi bazan dafa ba Sai dai kayimun
duk abunda zakayi, ” Dallah yimun shiru mai kika iya dama inbanda rashin mutunci, ” dai dai bandaki
ta tsaya eh naji tunda matarka ma haka take ai wallahi bakayi sa’ar mata ba,” kada kai yayi yafita, “
shamsiyya kuwa Sai masifa takeyi wa hajiya Amma hajiya hakuri ta k’e bata… Arif Yana fitowa
yagano Fatima atsaye kusa da baba maigadi da alama wane abun take tambayar sa, ” karasowa yayi
ke ke ke…” banza tayi dashi, ” baba mai gadi ne yace uwata daki yak’e, ” baba ai naji ance ke kuma
Naga fatima aka samun ko dabba mutum baya kirata da ke ba, ” ke malama kidafamun abinci anjima,
” abinci? ina matarka, bazan iya ba inada guga ta alhaji, ” nadai gayamiki ya shiga mota yabar gidan,
” baba mai Gadi yace duniya ce duk abunda kayi wanga shi za’ayi maka kuma duk wannan wahalar
da suke baki gani sukeyi wahalar dake sukeyi? To wallahi uwata agurinki Gata ne dan haka karki
damu, ” murmushi tayi to baba Bari na shiga kar na makara a aikin, ” to Allah miki albarka… Lokacin
da arif ya i’sa office tunanin Fatimah kawai yakeyi ta’ina zai fara nuna mata soyayya? In baiyi wasa
ba wallahi Sai ta subuce masa amma kuma matar mutum kabarin sa, ” aikinsa ya karasa ya huce
gida, amira ya tarar tana kallo, ” ko kallon sa batayi ba kawai saije yayi tace nifa yunwa nakeji, “
shiru yayi mata sannan ya huce dak’in sa, dakin tabishi Wai arif ba dakai nake ba, ” bargo ya shiga
tazo ta ja bargon, banza yayi mata ga takaici daga auren, ” masifa ta dinga yi masa… Hajiya da
shamsiyya suna palour sai hira sukeyi, fatima kuwa Sai gyaran gida takeyi dan fulani ya shigo hajiya
Wai fatima tazo, ” shamsiyya tayi saurin cewa inji wa, ” banganin sa Amma wane a mota katuwa
kukanku baku da’ita, ” hajiya tace sauri kije ko zaiganki yace yafasa da waccar jakar, ” yanzu ma
kuwa hajiya dan ko mayafi bazan sa ba, ” yauwa tafi, ” tunda ta’isa hankalin ta ya tashi yadda taga
hadadden saurayi ga ilimi, suka gaisa ” ta wane kada ido naji ance kana naima na, ” uncle ne yace
ko dan aikin Bai jine bani Amma ne fatima nace, ” shamsiyya tace Wai dame fatiman tafine, ” yace
bakomai amma please kituromin Fatimah, ” to tace tana tafi tana yanga, Har ta shiga ciki ” hajiya
tace yaya hmm hajiya Bari nakira mai fatiman, ” ke banza ga yan iskan ki Chan a waje, ” hajiya tace
tafi haka, ” fatima ta kalle jikinta duk ruwa Amma sai tace to, tana fita tace uncle ina yini? ‘lpy, ” fati
babu wata dugowar nagana wallahi fati haduwar mu dake yasani son kasancewa daki ina sonki Kuma
ina son nazama uban ‘ya’yanki, ” uncle sai Dai kayi hakuri domin inada Wanda nakeso, ” fati kenan
zan jarraba nawa sa’ar, wasu ledoji yabata take ansa dakyar ta ansa tana zuwa hajiya ta k’wace
komai tare da shamsiyya zaki raba dan ubanki….. Yau yinin nabeela hajiya sai masifa takeyi wa
fatima tagama aikin ta wayan ta taji Yana kara dubawar dazatayi Wata number tagani kwatakwata
bata ganita ba, ” hello salamu alaikum, ” waalaikis salam gimbiyata, ” cikin mamaki taji muryar Dr
ammar kuka tafashi masa dashi, dama baka sona tun tafiyarka baka kirane ba, ammar How can I
stop myself from loving you!!! Bayan baka damu dani ba I try na cire ka from my heart but you know I
will never? ” cool down dear karki yimun mugun fassara walhi aiki ya rike kine, but soyayyar mu tana
nan saboda am truly, madly, deeply in love with you, ” wane dadi taji azuciyar ta, ” kafin ta bude
bakinta wane zage taji hajiya ta sakar mata, ” sauri tayi ta kashe wayar, ” muna can muna jiranki ke
kuma k’ina nan kina waya shige dan ubanki kishirya, ” jiki babu kwari ta shige…. Tunda sukaji gidan
bikin kowa sai mamakin girman fatima yakeyi, ” sai murmushi takeyi dak’in amaryar ta shiga
kawayan amarya ancika kan bed, nusaiba tatashi ta rungume fatima, ” wallahi nayi fushi ko kamu
baki zoba, ” ayimun afuwa haka ta gaisa da kowa, “suna zaune Ana hira amarya tasa ihu shikenan
yazo na banu, ” kowa yace menene? ” period d’ina kawayen ta sai cewa sukeyi tasha magani gwara
kisha magani, ” fatima K’uwa ta bisu da kallo, ” nusaiba ta lura da hakan, fatima yaya kikaye quit
please say something, ” ai basai tayi magana ba gaskiya ce baro baro kisha magani, ” bamco kiyimun
shiru fati please kiyi magana haba yar jaridar mu, ” dariya tayi to gaskiya kar kisha wane magani? “
duk sunyi saroro suna jinta… Karki sake kisha maganin dauke jini saboda wai first night, kibar jininki
yayi addadin kwanakin sa, karki yadda kisha magani, Kinga nusaiba period baya hana komai sai
saduwa dan haka wallahi karki sha magani, magungu nan wasu suna da illa wasu Kuma sai su riketa
Miki al adark’i, ” tabbas hakane fatima, ” idan kin chanja pad din kisamu turare mai dadin kanshi,
kifesa ako ina ajikinki har cinyarki, Na farko dai kisiya pad ishash shiya kitafi daita, dazarar ankaiki
kafin ango yazo kichanja karki yar a inda zaigani ballanta na yafara kenyaminki, Kuma karki saki kibar pad tayi awa biyu, dazarar kinji dumi kije kichanja, dazarar kin janja pad to
kifesa turare, Kuma karkiyi tunanin wai aikina period babu harka hahaha anan kuwa za’afara harka
walhi dazarar zaku kwanta karki sake kiyi nisa dashi ki rungumeshi, tukunna Sai ku rufa abargo,
alokacin kidinga yimai kiss nabazata, wanda zai narkar da jikinsa, kikuma yi adduar kwanciya idan
za’ayi bacci, kitufa ahannunki, kishafi duka jikin’ku kuma dazarar kin kwanta to muryarki ta koma
kasa kasa kiyimasa romance yadda zai gigice, karkisaki a kwana biyu, ki saba masa tunda aka kaiki,
babuma aci kissing karki sakace dashi idan kuntashi da asuba ki tsugunna kigaida shi, sannan Sai
kishiga wanka ki wanki ko ina ki chanja pad, kina fitowa kisamu atamphar ki wanda sukayi kyau
wanda Kuma suka kamaki, ki sakasu kifesa jikin ki da turare, kiji cikin shagawaba kice kin hada mai
ruwan zafi yana shiga, kigyara dakinki, da gadonki kisiya wannan gawayin Dan naira dare kitafi dashi,
in kuma kinada abun turare to ki kunna saiki turara turaren, ki dakko masa kayansa Wanda kikaga
sunfi sauki, kibasa kice yasaka, ” tohm fatima, ” kawayen amarya ihu suka saka lailai zama da mai
ilimi yayi…” hmm fatima tace… Narantse miki da Allah gurin farantawa miji babu kunya, babu kunyar
data huce ki kama kanki awaje yanzu Kuma kin shigo gidan miji duk wane motsi nake Allah zai baki
lada, danhaka kisaka Allah aranki to Shima zai faranta miki.. Karki yarda bakinki yayi doyi haryaji
kina wari, kinajin bakinki yafara wari to yimaza ki dauke brush da maclin kiwanke, karkizauna babu
kamshi, Kuma kizauna ki karance halayyansa tsaf… Yawaita sallah dare ko da sau biyu ne a sati kiyi
addua Allah yabaku zaman lpya ke da mijinki yadauwamar muku da kauna tahar abada yakademuku
sharrin mutum da aljan.. Ki kuma tsai da sallah danallah karkiyi wasa da sallah duk mai tsayar
dasallah daban yake agurun Allah.. Wallahi in har kina karatun alqurani toh haske zai dawwama
agarike…. Hakane nagode, ” kinje yar air mun dai gode ahaka akasha yini da daddare aka kai
amarya… Amira ce take kwance Akan gado wai batada lpya, arif ne yake wane lallabata yazata cike
ne, ” kawai sai cewa tayi nefa banson haihu…. *Urs nana diso* *42-45* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Amira ce k’wance Ak’an gado, bata da lafia, arif ne yake
lallabata ya zata ciki ne, ” budar bakin Amira Sai cewa tayi nefa banason ciki, wannan cuta tawa
masu ciki Naga sunayi, ” Arif ne yayi dariya haba amarya ai inshaa Allah ciki ne, ” kaga Arif tsaya
nifa ingayama wallahi bazanyi dak’on ciki yanzu ba Dan ban shirya haihuwa ba, ” haba Amira kinsan
yadda nakeson yara kidaina irin wannan wasan, ” oh kana ganin Kamar wasa nakeyi? So let me tell
you banson na tsufa yanzu..” Amira kidaina magana Sai kace wata jahila, ” budar bakin ta ke da wuya
Sai amai..Arif ne ya tashi da gudu ya biyo ta, kamar zata amayar da kayan hajjinta dan amai, sannu
amira ” malam dallah ka kyale ne wallahi in ciki ne sai na zubar afusace tabar dak’in, Arif kuwa
hankalin sa ya tashi kar taji ta zubar Yanzu ta’ina zai fara lallabata….. Shamsiyya tana zaune a
palour tana k’allon American film, ” fatima tayi sallama Amma ko kallon ta batayi ba, sharar palour
tafarayi tana gama wa tahau yin guga, fatima tanata gogar table aikuwa wane ashar taje Wanda sai
da ta tsorata, ” ke fatima bazafa kizo gidan ubana ba kuma kidinga yimun iskanci, ina kallo Amma kin
dage sai kaikawo kikeyi ki bare in nagama kyayi, koda yake ko marayu bakuda mutunci, mtseww
tsake taja, ” Fatima da take aik’in ta ko kallon ta batayi ba, ” alhaji ne ya shigo a’a ‘yar lele kallo
kikeyi ne? ” eh, ” fatima tace sannu da zuwa baba, ” yauwa ke Wai bance ki fito da miji ba? Nagaya
Miki wallahi zan badak’e, ” shamsiyya tace gwara Dai kabayar da ita dan batada mai son ta, ” nagaji
da ganin ki cikin gidana tun kina yarinya fa haba, ” alhaji inshaa Allah zan fitar kayi hakuri, ” banza
yayi Mata ya cigaba da hira da shamsiya, ” fatima data gama aikinta fita tayi tabar musu palour,
girke ta karasa sannan ta huce zuwa dak’in ta domin tayi wanka…. Sai da ta shirya cikin abaya tayi
kyau dak’in hajiya ta huce, ” sallama tayi sannan tace hajiya zanji gidan goggo, ” ko kallon ta batayi
ba tace kidawo da wuri, ” tohm tace sannan ta tafi, ” Mota ta hau cikin mintina ta’isa unguwar, “
goggo ta tarar sai aiki takeyi tana karasawa ta ansa, ” oh ne yau kin tuna da talakawan kenan, “
fatima tayi murmushi haba goggo ai ne daku nake alfahari, ” wannan kuma ke kaka sani, ” fatima ce
ta samu kujera ta zauna, ina yini goggo, ” lpya ke fatima karki maidani Sha sha sha mana wato kinje
an kusan auren ki shine kika wanke kafa kikazo ko? ” to Abu na farko kisane kudin gad’on ku baya
hanuna ko ficika ban dauka ba, ke kisane babu abunda zanyi miki inzaki shiga duniya ke naima yafi
yayi miki! ” fatima cikin wane yanayi tace haba goggo mai ya ‘kawo wannan zancen ne wallahi nazo
na gaidake ne, ” dallah yimun shiru ne zaki mayar karamar yarinya? Eh tashi kitafi dan bazanyi girke
dake ba, ” haba goggo..” ki tafi nace ubanki na haifa bake ba, ” hawaye ne ya wanke fuskar fatima
wato kowa baya son su! ahaka tafita daga soron sukayi karo da ya mudassir, ” mai yafaru fatima kike
kuk’a? ” murmushin kuka tayi masa sannan tace bakomai, ” Haba fati ki dinga Hakuri kinfi kowa sanin
DUNIYA CE! !! Abunda kayi shi zaka girba, Yanzu yaya danAllah ina zan samu miji, shi aure lokaci ne
Amma sunk’i su gane, ” kai bakomai kiyita addua, ” tohm yanzu muje na kaike tohm tace sannan
suka tafi… *Urs nana diso*
*45-47* DUNIYA CE *NA NANA DISO* In kai Dan iska ne to ne ba’i taba ce, kazo har dakina kana
kokarin rungume ne, kamanta da haramcin dake aikata hakan, can kuma Fatima tafashi da kuka,
danAllah Idan laifi nayi muku kuyi hakuri, saboda wannan kiyayya da kukeyi mun tayi yawa..” dakata
fatima son ki nakeyi kuma nace miki komai nayi miki kiyi hakuri Amma kin dauke tsana kin duramin??
Why fati wallahi am in love with you, ” Dr ammar nakeso kuma shine mijin da nake fatan nakasan ce
dashi, Dan haka kadaina cewa kana sona, bayan kasan na tsaneka!!! “Murmushin takaice da bak’in
ciki yayi sannan yabar dak’in..kasuwa yazarce yaraba kayansa sannan ya wuce gida….. Shamsiya da
take faman bacci hajiya tazo ta tashita, ” haba hajiya yaya zaki ta shine tun yanzu, ke malama
kishirya yanzu za’a tafi danbermu garin su babank’i, ” tsake taja sannan ta tashi ta wada bandaki, “
hajiya ce ta huce dak’in fatima tana shiga ta ganta kan dadduma, ko sallama batayi ba tace kishirya
zakuje kauye, tohm hajiya bari nataso na kara gyara gidan karmu tafi mu barki da aiki..” ke malama
kishirya nace ba haka nace kinuna min kinada d’a ba babu abunda zan dauka ko nayi agidan nan har
sai kin dawo..” murmushi fatima tayi tafara shiryawa…. Arif dak’e faman surutai ak’an gado bai san
lokacin da yak’e furta maganar afili ba, fatima nasan nayi miki kuskure amma ki sone Koda
kadanne..” muryar Amira yaji tace to karamun dan iska Mara mutunci, ” baisan lokacin da yatsunsa
biyar suka sauka afuskarta ba..” nika Mara dama anci namiji ba dan goyo baniba kwata kwata bakuda
tabbas amma wallahi zakasan nika mara?” Kina kara magana zanci maki mutunce, kafin kishigo
gidana kin nuna min babu mai hankali irinki ashe baki da tarbiyya? kin nuna min kin iya girke ashe
baki kikeyi ba? Uwa da uba ma soyayyar da k’ika yaudari ne da’ita, ” eh nayi din in kagaji dani
kasake ne!!! Duk wannan cin mutuncin akan na zubar da ciki ne? ” arif yace dama haka duniya take
wasu nada hankali wasu mahaukata ne! Yanzu in banda jahilce yana damunki mutane dubu nawa kiso
su samu haihuwa amma Allah baibasu ba, dubu nawa kida cikin amma baya zama, ke Allah yabaki
kinje anzubar dashi danme dan karki tsufa acewar jahilcin ki, bakisan matsala ta ba bakisan damuwa
ta ba, na tashi da safe bakisan yadda natashi ba cina shana duk bakisani ba, ina da bukatarki banda
bukata wannan ba matsalar ki baciba, kusan sati daya kinaso ki bugamun kwakwalwata kibarni naji
dadi dake amma kinke, ko so k’ike nafara zina yadda duniya zata tu humeni ko kuma nafara shaye
shaye yadda duniya zatayi mun tofin Allah tsine wallahi ki tuba kisan menene aure ki kuma koma
makaranta….” tsake tayi tabar dak’in… Lokacin da fatima ta shirya hajiya ta sanar, ” hajiya tace mata
shamsiyya zataji unguwa sai ta dawo tukunna zasu tafi, ” to tace kafin ta koma daki uncle yace mata
yazo, kujera ta dak’ko masa da lemo sannan ta tawo, ” ina yini uncle yasu rufaida, ” ai ne nayi fushi
ace ko flashing kwata kwata bakya yimun, shiyasa nace Bari nazo naji ko lafiya? ” dariya fatima tayi
lafiya lou uncle nayi laifi amma ayimun afuwa, ” hahaha ai masoyi ya bata laifi fatima, bansan mai
isa baki kwadayin soyyaya ta ba? Ki tausaya mun ko dan halin da nake ciki, nayi ‘Yan mata dayawa
amma kowacce saboda kudina take sona, wato wane zamani muke ciki iyaye ma sunfi son mai kudi a
‘ya’yansu dalilin Hakan yajawo min bakin jini acikin yan uwana, fatima nayaba da hankalin ki shiyasa
nace ina kaunarki, ” uncle kenan bakomai in ne matarka ce zan aure ka addua Dai zamuyi tayi, “
shiyasa nakeson ki..” ta saka dariya..” a lokacin arif ya shigo ya lura yadda ta sake jikinta suke hira,
cikin gida ya shiga da masifar sa hajiya tace lafiya?? ” ya za’ayi abar fati tana zance a waje haba
hajiya Ya za’ayi adinga barinta, ” kaga arif gwara ta samu mijin ta bar mana gida, ” hajiya Kenan
shamsiyya zakiyi fatan tasamu miji tunda ita ce ta addabi ke, amma fatima dake faman wahalta
mana…” shiru hajiya tayi tace yaushe zaka tafi canadan yace yanzu zan tafi, sukayi sallama yafita… Lokacin da Arif ya’isa canada farouk ne Yazo ya dauke shi, suna isa gida hutawa yayi sannan ya fito
palour, suka gaisa da su momy dady yace kabarmu anan ka koma wane Gari na daban, ” hahaha ai
dady chan yafi dadi, ” wallahi ina fama da matsalar shiyasa nace bari nazo, ” suka hada baki mai
kuma yafaru..” Arif yace aure nakeso nakara, ” mumy tafara fada har yaushe kayi auren? To tsaya
wama kakeso ka aura? “yace fatima..”mumy tace zancen banza kenan ai wahalar da kanka kakeyi, “
wallahi ina sonta dady kayi magana mana, ” arif zamu tayaka da addua Idan da alheri Allah yasa ka
aure ta, ” su kace ameen….. Mota suka shiga zasu tafi k’auyen hajiya tace to sai kun dawo, “
shamsiyya ta wane bata rai wai hajiya bikin wa akeyi ne? ” bikin bintu ne..” hmm ne kyankyamin su
nakeji wallhi dan kwana daya zamuyi..” hajiya tace tohm Allah ya kiyaye agaida su, ” fatima ce tace
zasuji, ” tunda suka kama hanyar kauye basu tsaya ba sai da suka i’sa kofar gidan, suna shiga dak’in
baffa fatima ta shiga shamsiyya tabita, ” zama tayi kusa dashi ta gaida sa, ” yar albarka saukar
yaushe? “Fatima tace yanzu baffa ashi biki yazo Allah yasanya alheri, ” yace amin..” baffa ya cewa
shamsiyya ke jaera bazaki zauna ba ne? ” shamsiyya ta wane ya mutse fuska ai dak’in ne banga
gurin zama ba, wane kayansa ta gano kana gani kasan sababbe ne ta dauka zata zauna, ” haba
Shamsiya bari naciro miki dan k’walina? ” fatima zata shinfida mata kusa da baffa sai kuwa
shamsiyya cewa tayi ke malama bazan shake warin bak’i ba bani nan? ” baffa yace ubanki ma da
haka yake mara mutunci gaki ga duniyar zakigani, ” haba baffa danAllah kayi hakuri kaji, ” shiga cikin
gida sukayi bintu tana cikin kawayen ta, ta matso kusa da shamsiyya maganar da zatayi wane warin
baki yadoki ta, ” shamsiyya tace dallah malama matsa ne wannan wari baki haka, ” inna tace dama
aike bakida mutunci, ” fatima taja bintu dak’in ta domin kar ayi fada, amarya bakya lefi, ” haha fatima
kenan uwar dabara, hmm nidai naji suka gaisa da inna shamsiyya kuwa k’an gado ta d’ane sai
bacci….. Bintu da kawayen ta suna dak’in baffa azaune fatima ta shigo, ” budar bakin bintu sai cewa
tayi fatima ki daure kiyimun bayani ak’an tsafta kinga anjima da dare za’a kaine, ” tohm ya bintu
gaskiya tsafta tana nufin kawar da dauda ko datti da kuma mummunan wari ko kawar da duk wni
abinda baya da kyawun gani, Don haka tsafta ta shafi abubuwa dayawa, ” tohm fatima wallahi ina
kokar tawa, ” nasani ya bintu kiyi kokarin gurin kin tsaftace bandaki, dakin girke, tsakar gida, kayan
sawa, dakin kwana..” tohm fatima nagode, ” Haba ai babu godiya tsakanin mu, kinga tsaftar Jiki ana
nufin wanke gangar jiki da ruwa da sabulu ko abinda zai tsaya a matsayinsu su wanda zai taimaka
wajen kawar da dauda da wari, yawan shafa turare idan kingama girke kiyi wanka, in zaki kwanta ma
domin gujewa mijinki Jin warin jikin ki, ” tohm..” tsaftar baki kuwa i tace karshe idan mutum baya
gyara bak’in sa to fa akwai matsala,aqalla a wanke bak’i da maganin wanke baki ko aswaki sau biyu
ko uku a kullum, kuma dadi akan haka ya kamata mace ta riqa amfani da alawa mai dadi mai bada
daddadan qamshi, idan babu zata iya cilla kanin fari abakin nata a duk lokacin da zata kusanci
mijinta, ” kai amma mungode…” ki yawaita yin aski wurin da suke tara gashi, kamar hammata, mara
da sauransu, wanda dama yana cikin fitra guda biyar da Manzon Allah S.A.W ya fada, aqalla mace ta
tabbatar tana yin wannan aski duk bayan kwana arba’in, idan Kin aske dan gudun wari sai kishafa
alumun, yawan yin kitso kunshi da sauransu…” fatima Allah yabiyake cewar kawayen ta, da daddare
aka kai amarya gidan ta mai kyau…. Da safe akazo daukar su suka kama hanyar birni lokacin da
suka isa gidan kaca kaca gaba daya ya bace nan fatima tahau aiki, lokacin da ta tsaya a bak’in bene
da ruwan guga ahannun ta shamsiyya na zuwa ta cillo ta, fatima batasan lokacin da ta fara
gangarowa ba, Shigowar arif kida waya ta saka wata irin k’ara, aguje ya sureta sai asubuti…. *Urs
nana diso* *47-50* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Aguje Arif ya sureta Sai asubuti, gudu yakeyi a cikin bai dira a
ko’ina ba Sai filin asubutin Nan da Nan likitoci sukayo kan fatima Sai emergency, ” Arif dak’e zagayi
agurin yarasa Mai kiyi masa dadi, ayayin da zuciyar sa ke faman tafarfasa,ga zancen zuci daya keyi
shamsiyya in har fati takaryi wallhi saina karya ke, ” Yana cikin sunbato Dr fahil ya dafa k’a fadarsa, “
afirgice arif yajiyo ya kalle dr, Mai Yafaru da’ita? Ka gayamun?? ” Arif cool down your mind cikin i’kon
Allah nothing happen to her jikinta Dai yayi tsame sai kuma zazzabi, k’anta yaso ya bugu but Allah
yakiyaye babu abunda yayi, ” wata irin hamdala Arif yayi, ” yanzu zata iya farfadowa Nan da 3hours
munyi mata allurai ga magungunan da zaka siyo, ” takardar ya amsa, acikin hanya yake sanar da
alhaji abunda yafaru amma Sai alhaji yace bashida lokaci yakatse wayar wanda hakan yayi mutukar
batawa arif rai, ahaka ya siyo maganin ya koma asubutin….. Ameera ki zaune a palour momynta ce
tayi sallama tashi tayi ta rungumeta, ” oh amira dubi yadda kikaye kyau ba’acewa komai, ” hmm
kikuwa momy auren arif wasa ne komai ya tanadar mani banda wane problem sai kwana biyun nan
da mukayi fada akan cikin Dana zubar, ” mumy tace kyale wawa sai kin tara abun duniya tukunna sai
ki dau cikin, kinga amira kidaina barin yana yawan ma kusantar ki, ” haba momy kin manta nine,
amma fa da matsala? Dan kuwa kishiya zaiyi, ” momy ta dafe kirjinta ki..me aikuwa wallahi bai isa ba
dole muba zama gurin bok’a…” dama zancen sa nakeso kiyimun yanzu yaushe zamuje?..” momy tace
jibe kishirya da safe kinsan garin nada nisa Dai? ” eh zan shirya yanzu ga dubu goma anjima zan
aiko miki da nama da kuma kayan abinci…” tohm sai anjima…. Baba Mai gadi ne yaketa cigiyar
fatima aikuwa yaji mummunan labari hakan yasa ya koma gida domin ya sanar da matansa cewa
fatima ba lafiya, ” amma yana shiga gidan yaga Ana fada da lubabatu uwar gidansa da hadi k’anin sa,
” yana shiga yasan ankai lubabatu bango shiyasa, ” hadi ne ke zunduma ashar ita kuwa lubabatu sai
Dai takalle shi, ” baba yace Mai yafaru luba kike kuka?” Malam bantaba gaya maka ba amma kullum
kasaka kafa ka fita kullum da cin mutuncin da hadi Zaiyi mun, rannan kashi yayimun akasa, rannan
kuma jefana yasa anayi har cikin dak’ina, haka yazauna jiya yanata yimun addu”oin jafa’i da masifa,
malam wallahi bansan Mai nayiwa k’anin kaba?? Mijina bai takura min ba sai kanin Miji na? ” hadi
yace munafuka karya kikeyi zaki hadani da dan uwana, ” baba Kuwa yace yimun shiru munafike, to
daga yau ko akofar gidana naganka wallahi saina hadaka da hukuma, kaji chan duniya ce!!!….
Lokacin da fatima tafarka idunta a hankali ya bude, ya mudassir tafara gani sauri yayi yace sannu
fatima, komai mai huce wa ne! ” murnushi tayi tace bakomai yaya Allah ya riga ya kaddara ne,
wanene yakawo ne asubiti? ” Arif ne, ” kau da kanta tayi adaidai Lokacin arif ya shigo, ” washe
bak’insa yayi fati sannu kinje, ya jikin da sauki duk ya gigice, ” hakan yasa ya mudassir yagane
amma kuma sai yayi shiru..” sai gurin magariba aka sallame su gurin karfe shida Suka isa gida
lokacin da suka shiga dukkanin su suna palour, sallama yayi fatima tana bayan shi… Shamsiyya ce
taja wane tsake shikuwa alhaji dakyar ya’iya amsa salamar hajiya kallon ta ta cigaba da kallon, “
fatima ce tace hajiya nadawo, ” au baki karye ba?? ” shamsiyya tace shigeya ba, ” arif ne ya wanka
mata mari yakara wanka mata mari har sai da ta koma kujera ta zaune, wai ke mara mutunci bakisan
kemar mutane ba Dan uwarki fatima ai itace rayuwarki naga lokacin da kika cillota daga binnen ai
gugar daki zatayi, sha sha sha, wallahi da Ace wane abun ya sameta saina karya ke, ” alhaji nakiraka
awaya kace bakada lokaci ina tunanin da shamsiyya ce take asubuti ko da kudi zaka karbo sai
k’afasa, wannan yarinya amana take agurinku, ” hajiya kinfe kowa sanin rabonki da shara da wanke
wanke ballanta na girke, na tabbata da abinci za’ayi babu nama saik’in ji kinsiyo, amma fatima rai
ahannun Allah kunyi mata banza, ” duk jikin su yayi sanyi, ” shamsiyya tace ai gidan ubana ne, ” Arif
yace inje wa?? ” fatima ce ta matso kusa dashi tace danAllah ya arif kayi shiru, ” rike hannunta yayi
sannan yace fatima kice kina sona danAllah Dan annabi?? ” lokaci daya tayi wane diris kukan dake
idanun ta suk’a k’afe na tsaneka ya Arif Na tsaneka, alokacin tabar Dak’in…” jikinsa ne duk ya
mutu…. *Urs nana diso*
*50-52* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Fatima ce tace danAllah ya arif kayi shiru?? ” rike hannun ta
yayi sannan yace fatima kice kina sona danAllah Dan annabi…” lokaci daya tayi wane diris k’ukan
dake idanun ta suk’a k’afe, Na tsaneka ya Arif! Na tsaneka!! a lokacin tabar dak’in… ” jikinsa ne duk
ya mutu sannan yace zaki sone nayi miki nema dole kiyimun ” shamsiyya ce tayi wane tsake tare da
wata dariyar mugunta lallai ne bure yayi kama da mutum! ” Hajiya tace shiyasa yake wane Nan nan
da ita, ga shamsiyya anan amma kafak’e da fatima mahaukaciyar yarinya, yar iska Mai bin maza! “
wane kallo yayiwa Hajiya wanda Hakan yasa tayi shiru, ” arif ya kalle alhaji, ne zan tafi afara shirye
shirye, ” da sauri alhaji yace to…. Fatima tana shiga dak’in ta sai kuk’a, tana ta sinbatu..arif bak’a
sona na tabbatar cutata ka keson yi, tana cikin kukan taji sallamar maryam shiru tayi sannan ta dago
k’anta, ” fatima Mai ya sameki kike kuka haba Fatima kidaina saka damuwa aranki, ” maryam kenan
kinfi kowa sanin halina, wannan matsalar daban take! ” wacce matsala kuma?? ” Wai ya arif ke
sona!!! ” subhnalhi arif kuma?? ” shi dai maryam tafashi da k’uka..” Fatima ba k’uka zakiyi ba komai
na rayuwa hakuri ya gada kuma kinsan wane hanin ga Allah baiwa ne, k’i daina damun k’ank’i kitashi
ki nemi zabin Allah tare dayin sallah raka’a biyu kiyi addu’ar da annabi ya koyar damu wato istikhara,
inshaa Allah komai zai daidaita, ” tohm maryam amma kinsan ya arif ba sona yakeyi ba, ” haba
fatima in ma ya aure ki Dan ya wulakanta ke, *DUNIYA CE*…” nagode da shawarwarin k’i… Alhaji nifa
bangani maka ba? Ina k’adosa ne? ” to ya zanyi hajiya tunda yaron Nan yariga ya furta da bak’in sa
ban i’sa na hanashi ba, ” shiyasa tun farko naso na aura Mata Wanda nakeso, amma baiyu huba..
naso ace shamsiyya ya aura a matsayen ta biyu amma rashin kunyar ta da Rashin tarbiya yasa ba’a
son ta, ” a a Alhaji karkai Mata wannan muguwar shaidar yanzu dai wannan yarinya in an tashi kasa
Mata katifa da kujerar roba da murhu.., ” hahaha gaskiya kam…. Yau laraba ankawo kudin auren
Fatima da arif dubu dare, an saka biki nan da wata daya, ” fatima da hankalin ta yatashi ga wane
mugun zazzabi daya rufeta, ” shamsiyya kuwa tsabar bakin ciki ba’a cewa komai..” fatima tana cikin
bargo jikinta duk yadau zafi ga wane hawaye dayake wanke fuskarta? Jitayi an bude dak’in ta
sallama yayi ya tsaya Yana kallon ta, fatima kenan banyi mamaki ba da naganki kina k’uka, matsowa
yayi ahankali yazauna kusa da’ita Yana kokarin yayi bargon yaji jikinta zafi? Fati Mai ki damunki
kisanar dani komai, kuma kitashi mutafi asubuti? ” malam baruwanka dani babu inda zane taja
tsake…” Murmushin takaice arif yayi ba shiri ya huce zuwa office Dan anata jiransa…. Mumyn Amira
tana gida sai faman jiranta takeyi, wayarta ta dauka sannan ta bude dakin arif da mukullen ta ta dau
dubu dare, cikin kananan mintuna ta’isa gidan su..” ke Amira k’in barne atsaye inata jiranki wannan
Garin Mai nisa..” oh momy sorry tashi mu tafi nan suk’a hau mota momy tana Shiga mota tafara
driven, suna tafi akan hanya suna kara ahada makirci k’ala k’ala, ” momy kenan ai ke dai kibare
Amma banson boka ya yiwa arif Imani yagama mun dashi..” hahaha shiyasa nake son k’i domin
halina k’i kaye..” lokacin da suka Isa mutum daya suka tarar sai da ta fito sannan suk’a shiga..”
shige uban shigu ya haukatar yayi iskanci da yadda yakeso kafin wuta tace ubanka…” hahaha wata
irin dariya yakeyi wacce babu imani a tattare da’ita, ” keh!!! ” Tayi saurin tsorata maganar kishiyar ki
hahaha yarinya ce Mai addini asiri zaiyi wuyar kamata amma mijinki zan baki magani sai an kai
amarya zaki zuba a ruwan Shan sa..” hahaha zakuyo mamakin yadda zaki gama dashi, ” godiya
mukeyi boka…” ku ajiye kudin ku achan…” suk’a huce zuwa gida…. Amira na shiga palour arif ya
wanka mata mari, daga ina kike?? ” bansani ba..” kinfara Sata kenan Har da bude dak’ina, ” haba arif
kudin ka ai kudina ne! ” dariya yayi yace au haba da gaske?? Masu miji manya, ” eh man domin kuwa
wanda zasu shigo sune baiwa domin na riga nagama da mijina..” dallah yimun shiru a wannan
kazantar ko kuma arashin dafan abinci ” ai gashinan zaka auro Mai dafa mana… Tunda yaje gida
suke hira da alhaji, ” sai aiki Fatimah take tayi, ta dauke botiki zata zubar da ruwan gogarta sai ga
arif ya rik’e mata hannu wai k’e bak’ya gajiya da aik’i ne? ” dagowa tayi cik’e da tsana kadaina rik’e
ne? ” gaba dayan k’i zaki zama tawa ba wai hannun k’i ba, ” tsake tayi sannan ta bar gurin.. “
tsayawa yayi yanata kallon ta….. *Urs nana diso* *52-54* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Arif ne ya tsaya yana kallon ta yadda hips dinta yake moving
shi yakara tayar masa da hankali Bai bar gurin ba Sai da ya tabbatar ta shiga ciki, wane irin hamdala
yayi da Allah yasa fatima zata zama matarsa bazai iya jurar ganin ta da wane ba, shiga cikin gidan
yayi sunata hira da hajiya Akan business din da zata fara, ” hajiya nifa yunwa nakeji..” hmm kasan
halin fatima batasan hakk’in mutane ba kaji ka tsawa tar Mata tay’i sauri ta gama..” Hajia kenan
danAllah k’i dinga gyara k’a lamank’i! ” oho Maka Dai ba yunwar kak’eji ba, ” a a wallahi bari naje,
shigar sa cikin kitchen din ya tarar da ita tana waya ga wani kuka shagwaba da takeyi, hankalin sa
bai tashi ba Sai da yaji tace” Dr ammar k’aine ruhina, banida kamarka, kuma wallahi soyayyar ka
tanan azuciyata..” kafin takarasa maganar afusace arif ya wanka mata mari sannan ya fizge wayar
yafasata, ” from today nakara ganin ki kina waya da wani wallhi Sai ranki ya bace idiot kawai.. yafita
aguje yabar dakin motarsa yaja Ya bar gidan, ” fatima daki faman kuka a kitchen, hajiya ce ta shigo
yarinya kenan ai bala’i da masifa yanzu suka fara bibiyark’i, ta dun guri mata kai sannan ta huce…
Goggo ce take Faman mita..” haba goggo tun ina bandaki nakejin maganarki lafiya? ” kadai mudassir
kyaleni naji da takaicin rashin mahaifin ku yanzu gashi za’ayi auran fadima bani da ko sisi, ” mamaki
ne ya cika mudassir duk uban kudin da goggo kida Amma saboda bakin ciki da takaici yasa tace
batada ko sisi lallai duniya abar tsoro ce…” karki damu goggo ni zanyi mata kayan kitchen ko labeli
kya saka mata, ” Kai mudassir banda hali ko da nasamu gudun mawa addu’a zansa ayi mata..” Allah
yasawake ne natafi kasuwa, ” yana fita goggo tayi tsake banzayin ‘ya’ya ficikata bazan kashi ba…..
Arif ya akeyi kwana biyu na ganka cikin murna? Ko dai ansamu karuwa ne? ” haha ai kasan nakusa
angon ce wa jira kawai nakeyi najine tari da fatima, every beat of my heart ita nakeji..kai nagaya ma
bakajin yadda nakeji? ” hmm gaskiya da aiki agabanka domin kasan soyayyar su da Dr ammar? “
fahad kenan bazaka fahimta yadda nake sonta ba, Bata sona but ahankali zan koya mata yadda zata
so ne, ” okay arif Allah yabada zaman lpya…” Ameen fahad… Wai Fatima bazaki Yadda da kaddara
ba? Kullum cikin tunani, ki gode Allah dayasa arif mutumin kirke ne to gashi jiya nema ankawo
kudina wai abdul za’a aura min! ” da sauri fatima tajiyo abdul ince ya daina shayi shayin, ” inafa jiya
ma Sai daya zani ne dubi jikina akan nace bana sonsa, k’awu yace wane satin za’a fara bikin..”
innalillahi Allah yabaku zaman lpya maryam amma wallahi k’awu Bai kyauta ba..” to fatima babu
yadda zanyi nayi hakuri kema kiyi hakuri muyita addua kawai! ” hakane maryam..” fatima ga wannan
zaitun ne da dilka da lemon tsami k’i hadi su guri daya ki shafe jikin ki zakiga Yadda zaki murji, da
safe in kin tashi kishafa Zuma ajikin ki gaba daya…” hmm maryam nifa bason sa nake ba so babu
abunda zanyi..” tsaki maryam tayi malama ke da k’ike da kishiya wallahi ki gyara kanki, ” shiru
fatima tayi tana zare ido, ” hahaha zaki zare ido da kyau kuwa ga wannan Zuma ce da zogale sai
madara ki hada kiyita Sha…” hahaha su maryam anraja’a nagode..” malama nema sai kidan ban
wane sirrin please! ” to nidai abunda zance miki a matsayina na aminiyarki shine Kinga al’azkar
dinnan na safe da yamma ki dinga yi karkiyi sakace,domin tsarene daga sharrin abubuwa da dama,
“Abinci karki sake kiyimasa abunci batare da kinyimasa Dan drinks ba,”maryam addu’ar da akeyi
ayayin da zaku sadu da juna koda mijinki baiyiba, ke kiyi ﺑِﺴْﻢِ ﺍﻟﻠَّﻪِّ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺟَﻨِّﺒْﻨَﺎ ﺍﻟﺸَّﻴْﻄَﺎﻥَ ﻭَﺟَﻨِّﺐِ
ﺍﻟﺸَّﻴْﻄَﺎﻥَ ﻣَﺎ ﺭَﺯَﻗْﺘَﻨَﺎ domin indai harciki yashiga wannan saduwar, to shaidan bazaiyi tarayya dashiba,
Kankana, abarba, Zuma, zogale su kasance abincinki domin suna kawo ni’ima sosai, ” Na gode yanzu
kasuwa zantafi sai nadawo… Yau arif ya tafi canada, lokacin da yaji yayi murna dayaga yadda dady
ya hada lefe akwati goma kaya sunyi kyau, mumy ce taketa yi masa fada arif Naga kanada saurin
hannu ga kuma fushi katuna duk abunda zakayi Allah Yana ganinka Kuma babu abunda yake narkar
da zuciyar mace irin kulawar d’a namiji Dan haka kaji tsoron Allah ka kasance mai adalci tsakanin
matanka, ” Tom mumy I will try my best..” yauwa son Allah yayi maka albarka Ameen, ” suka dauke
hanyar gida…. Amira hankalin ta yatashi yadda taga part din fatima hakan yasa duk ta gigice wanka
taje tayi tasaka wasu kayan bacci sun kamata zuwa tayi ta kwanta, ” lokacin da arif yadawo yayi
mamakin Har ta kwanta dak’in sa ya huce yayi wanka Har ya kwanta a gadon sa Sai Kuma ya huce
zuwa dak’in ta kwanciya yayi yafara shafata nan da nan hankalinsa yafara fita daga nan suka
gabatar da sunnar su…. Yau jumma’a ankawo lefen fatima akwati goma ansaka sati daya, ” su hajiya
harda kuka ita da shamsiyya tsabar bak’in ciki, mutane duk sun gani, ” fatima ce ki zaune a Kan
kujera tayi tagumi tunanin duniyar kawai takeyi jitayi an janyi mata hannu, ” dago fuskar ta taga arif
ne wane irin kallo yayi mata itama ta kada idon tace lpya? ” dariya yayi sannan yace haba fatina
kinga ankusa bikin nan 1wk kawai yarage kigayamun abunda kike bukata, ” wane guntun tsake tayi
sannan tace bana bukatar komai sai dai danAllah karabu dani, bakinsa yayi kokarin Kai nata sauri tayi
taja baya mayi haka? ” wallahi kikara yimun rashin kunya sai kingane kurank’i..” tashi tayi zata bar
gurin ya riko hannun ta……. *Urs nana diso* *54-56* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Tashi tayi zata bar gurin Arif ya rik’o hannun ta Wai k’e mai
k’ik’a mai dani? So k’ik’e na hauk’ace k’o k’uma me? several time ina nuna mik’i yadda nak’e son k’i
but Sai k’i dinga share ni? Why fati? Wallahi Wallahi ina sonki K’uma I can’t explain how I feel!!! “
hannun ta ta fizge Malam cik’a ne wannan ai iskanci ne ai ban zama matar kaba da zak’a dinga taba
ni, ” hahaha in dai k’ece k’i fadamun duk abunda k’i k’ayi niya, Amma banda abunki saura kwana
nawa?? ” wannan agurin ka kak’e ganin Kamar ba zunubi baniba, Dan haka Sai kashirya domin
zuciyata ta Dr ammar ce! Amma gangar jikina zak’a aura, ” wane mugun k’allo yayi Mata Wanda
alokacin yaji wata muguwar sha’awar ta, ” tsake fatima tayi sannan tabar gurin…… Motar sa ya shiga
daga Nan ya huce gida Yana shiga ya tarar da amira ak’an gado da alamun bacci ne ya kwashi ta,
Bai tsaya komai ba Sai jawo ta tayi a hankali yafara shafata, ” i don ta ta bude Arif manene haka? “
ina cikin wane Hali amira please kibarne nayi, ” kai ka isa? Dallah malam kyaleni ai bari ingayama ka
riga kasiyar wa kanka rashin mutunci, “haba amira nifa mijin ki ne? Please k’i taimakan..” zancen
k’ak’eso kaji Chan kajira amaryar ka, ” bazan iya ba janta yayi tana ihu…… Ke fatima Dan ubanki
menene haka? Mai kike nufi ko ne zan dafa abincin wallahi uban ki zance mara mutunci, ga kayanan
kije ki goge mun, wallahi hajiya ciwon ciki ki damuna, ” lallai kin girma bari yanzu nayi maganin ki
janta tayi ta dinga duk’an ta ” hajiya danAllah kiyi hakuri zan dura, ” shamsiya ta shigo ki miki
damunki? Yau baki gyaran dakina ba, ” duniya ce kuyi mun abunda k’uka ga dama wannan ai zalince
ne wallahi k’uje tsoron ranar da Allah zai k’ama k’u, ” dallah jak’a yimun shiru agidan ubana k’ik’e
k’uma baki isa kice bazamu mure ki ba, ” eh naji arzukin alhaji naki ce, Amma wallahi ko me za’ayi
mun bazan komai agidan nan ba ai sai da lafiya ake yin komai dan haka ke kije kiyi…” hajiya tace
yar iska mara mutunci dadinta na haifa bari ita taje tayimun taja shamsiyya suka fita, ” fatima tasaka
kuka ita kanta tausayin kanta takeji bashiri dataga kukan baida anfani tayi alwala tazo ta tayar da
sallah…. Arif ne ya kira mudassir awaya sai da suka gaisa yace yazo yaga gidan fatima..” cikin
Rabin awa ya’isa gida tunda ya shiga hawaye ya zubo masa yanzu wazai cik’a mata wannan dak’una
hudu ga sama ga katon palour, “Arif ne ya shigo Yaya mudassir naga k’ayi shiru ko akwai abunda
baiyi ba? ” ina ai sai dai mugode Allah Amma gida yayi kyau, ” to mungode b’enen na wane anjima
ma odar kayana zasu zo, ” to mashaa Allah zuwa yamma inshaa Allah za’a fara jeran nata, ” okay to
ga muk’ullin, ” tohm mudassir yana fita motarsa ya fada Yana cikin driving ya tsayar da motor yanzu
ya zaiyi kawai na cike mata daki biyu yanzu bari naji kanfanin daman nasayi kayan dak’i, sai
labulaye, Jan motarsa yayi ya dinga zirga zirga karfe 4 akafara saka gado ka godanta yayi kyau sai
kujera duk anshaka mata purple and milk akasaka mata, “kayan kitchen duk masu gyaran suka saka,
yanzu frige da tv ya rage sai agogo chan yahuce duk ya siyo lokacin da yake saka wa sai yafara
kuka.. “najif yace muddasir maye na kuka? ” yanzu da bananan akayi bikin fatima ya zatayi? Kasan
babu mai yimata komai, ” mudassir kenan ai Allah yana tare da kowa, yasan zuciyar kowa, D’an hak’a
k’awai k’a godewa Allah daya baka yadda zakayi domin lamarin Allah yafi karfen wasa, ” hakane
wallahi nagode abokina…. Yau asabar k’arfe uku za’a fara k’amun fatima, shara tagamayi sannan ta
dafa abinci daga nan ta huce dak’in ta, zama tayi ak’an gado yanzu ko wacce rayuwa zatayi a gidan
arif? Ya ubangiji kowacce kaddara idan zata huce mun kabani ikon hakuri da juriya, ” anty zainab ce
ta turo kofar dak’in sauri tayi ta goge hawayen ta, ” amarya bakya lefe.. “murmushi fatima tayi nifa
babu abunda zanyi anty zee yau ma atamfa ta zan saka, ” haba Fatima ai haka bazai yihuba
gashinan wannan material ne na dinka miki wannan shadda da less kisaka ranar dauren aure, ” anty
zainab banda bakin yi miki godiya nagode nagode sosai, ” haba fati ai ke yarinyar daya kamata ayi
wace, anjima mai kwalliyar zatazo “tohm nagode, tashi tayi ta gwada kayan sunyi masifaffin kyau
cirewa tayi taji tayi wanka…. K’arfe hudu aka cik’a agidan.. ” shamsiyya taci kwalliya sai iyaye takeyi
sai gayawa kawayen ta takeyi zakuga amarya Kamar mahaukaciya don ko kayan sawa bamu bare
alhaji yayi mata ba, ” a a kice zamu sha dariya, ” farida ce tayi wane tsalle kinga yadda kikaye kyau
yarinya mai hips da boobs gaskiya arif ya dace, ” danAllah k’i daina k’arki sane kuka, ” tohm zauna
na nad’a miki head din.. “tohm,Ana gama wa rike hannun tayi suka fita kowa k’allon su yakeyi sunyi
kyau Bama aci fatima, ” shamsiyya kasa tsaya tayi sai burin kunya takeyi..”haka aka dinga hotuna..”
k’arfe shida su arif su kazo shida abokanan sa yayi kyau shima rike hannun ta yayi zo mu dauke hoto
Jan hannunta tayi “dallah ka kyale ne… “rungumota yayi mai hoto ya dinga daukarsu kudi ya d’akko a
hannunsa ya mika mata k’allon sa tayi ta hau bene, ” farida kun gani ko ” hahaha bita Dakin nata,” a
a kyale ta gobe zamu hadu ina bukatar hutawa…. Yau lahadi an daura auren ARIF DA FATIMA ak’an
sadak’i dubu Dari Sai rabon goro da alawa akeyi..” su Fatima ne suka shirya cikin shadda tayi kyau
sosai tana zaune Sai kuka takeyi arif ne yayi sallama ta shigo, bai lura da kukanta ba rungumeta yayi
sannan ya zira hannun sa acikin rigarta afurgice fatima ta…. *Urs nana diso* *56-58* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Arif ne ya rungumeta, sannan ya zira hannun sa a cikin rigarta
Afurgice fatima ta tashi, menene hak’a?? ” ya zak’azo har dak’ina ka dinga yimun wannan abun k’ai
Wai bak’ajin kunya ma, a hankali ta zauna a kasa ta sun kuyar da kanta sai k’uka! ” ina da right da
zanyi yadda nak’eso dake dan haka karki k’ara ihu akaina, ya sak’ko kasa mai isa kike kuka fatina ko
Dan na tabaki? Kinsan shekara ta nawa ina jeran jikin ki kuwa? kinsan irin hakurin danayi, please ki
daina kuka kinje, ” d’ago fuskar ta tayi cikin yatsena fuska tace ai dole inyi kuka tunda gidan ka
za’akai ne..” nafa zama mijinki fati kidaina gayamun irin kalaman nan, ina sonki ina Kuma kaunar ki, “
ni kuma har yanzu na tsaneka ban son ka kuma Bana kaunar ka, ” fita yayi cikin k’unar rai….. Alhaji
ne ya shigo dak’in fatima tana zaune ko sallama baiyi ba ya zauna a k’an gado, ” jiyowa fatima tayi
ta gaida sa, ” niba ansar gaisuwa yakawo ne ba zuwa nayi domin nayi miki kashid’e tunda aure zakiyi
inason kisane kin bar gidana har abada idan kika k’aso auren k’i karki dawo mun gida, Kuma kisane
karki kawo mun k’ara, kayan daki ma sai za’a kaik’i za atafi dasu dan haka nasan kin fara kwasar
k’uncin rayuwa kenan, ” kowa yasan asiri kikayewa arif dan ya aure k’i, ” alhaji duk abunda kayimun
tun ina karama har zuwa girma na nagode Allah ya biyaku da aljanna duk abunda nayi muku danAllah
kuyafe mun, ” Kuma naji magan ganunka inshaa Allah zan kiyaye..” munafuka yarage naki wannan
tashi yayi yabar dak’in anty zee ce tashigo dak’in yabaki shiga wanka ba? ” hawayen fuskarta ta goge
bari na shiga tana fitowa tasaka lesi sannan ta yafa mayafi anty zainab da inna suka riko hannun ta
aka shiga dakin hajiya da’ita to ga ‘yar taki zamu tafi da’ita ” hajiya ce tayi wane tsaki acikin jama’a
to ku tafi da’ita man na hanaku, ” inna tace *Duniya ce tafi bagaruwa iya jima* motar da aka kawo ta
daukar amarya suka shiga kowa sai shiga yakiye daga nan aka huce gidan fatima..” hajiya da
shamsiyya sai dariya sukeyi hahaha hajiya bari na tafi naga yadda zaa saka mata kujerun roba..”
kafin shamsiyya ta karasa maganarta sai ga sadiq babbar yaya ga kayan ku can mundawo dasu..”
hajiya tace me kake nufi sadik? ” wato kallo yabarku kunga kayan dakin fatima kuwa, gaba daya
gidan Kamar a waje yak’e, ” anya yarinyar nan bata bin bokaye, ” kin jike hajiya ai nutsuwar ta,
hakurin ta, biyayya, shi yak’e bibiyarta, ” wannan yar iskar shamsiyyar zaki gyara wallahi in bahaka
yanzo kuka fara ganin takaice da bakin ciki…. Lok’acin da suk’a i’sa k’ofar gidan magan ganun
maryam ne Suk’a wad’o mata ” yauwa fatima K’uma ga adduar da zak’i k’aranta i’dan zak’i shiga
gidan k’i tundaga waje har zuwa, shigarki ciki,tun agida in zak’iyi wanka k’i daura alwalar k’i,
Qulhuwallahu Ahad, da Falaqi da Nasi, da Ayatul kursiyyu, da Amanarrasulu don k’ari k’anki daga
sharrin shaidanu da mutane idan anzo k’ofar gidan k’i to k’i shiga gidan da qafar dama tare da
(isti’aza da basmalah don neman tsari) sannan k’iyi sallama in zak’i shiga gidan koda kuwa ba k’owa
Hak’a k’uma ki shiga da dakin nak’i da sallama, “ahaka ta karanta addu’oin sannan inna ta shiga,
gaba daya amira ta kulle part din ta K’arma ace za’a ci za’a kawo amarya, bagaren fatima suka huce
gidan ta yayi kyau kowa Sai addu’ar zaman lafiya ake yi musu, masu nasiha sunayi masu addu’a
suma sunaye ahaka akatafi aka barta ita kad’ai ango da abokanan sa suka shigo dak’in sukayi musu
addu’a sannan suk’a tafi daga shi Sai amaryar sa wayar sa ce tayi ringing ya dauka amira ce ta kira
tashi yayi ya fita…. Part din amira ya shiga lafiya k’ik’e k’irana? “Lafiya ga kaza nan dazu farouk ya
shigo part Dina shine yace na baka, ” oh Amma ya kyauta dama na bar kazar da nasiya a motarsa,
Amma ke da bakwa shiri da farouk taya ya shigo, ” oho masa…” to sai da safe..” Yana fita amira ta
dak’a tsalle yanzu aikin boka zai fara ce…” sallama yayiwa fatima a zuciya ta amsa, ” fatina tashi
muyi sallah, ” bude fuskarta tayi idon ta yayi jajir sallar me? ” ki tashi muyi..” bazanyi ba..” kallon ta
yayi yadda ta k’wanta to sak’ko muce kaza da frsh mlk, ” banaci please ki sak’ko, ” banza tayi masa
tayi kwanciyar ta..” bude kazar yayi ya dinga ci har sai da yaji ya koshi, ” yana gamawa yayi wanka
bargon fatima ya shiga ” tana jin ya tabata tayi saurin tashi, kuka tafara yi, ” danAllah fatina kibarne
wallahi ina bukatar k’i, ” kasa ta dawo ta zauna biyota yayi tureshi tafarayi yana kokarin rungumeta
yaji wane Abu kamar ya fasa masa kai cik’ata, ” can taje yace banza mai ya kawone gurin k’i tunda
inada amira mai zanyi dak’i kafarsa yake kokarin maka mata tabar dakin aguje..” saina lahan ta ki yar
iska, ” wane sabon kuka tafarayi….. *Urs nana diso* *58-60* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Wane sabon k’ukan fatima tafara, data ga k’ukan bashida wane
amfani ak’anta tashi tayi, ta shiga bandaki alwala tayi sannan tafito, sallah raka’a biyu ta gabatar,
cikin murya mai dadi tafara karanta al’qur’ani cikin suratul bakara bata tsaya ba Sai da ta tabbatar ta
i’ddata, sannan tayi addua Allah yabasu Zaman lapia ita da mijin ta da kishiyarta daga nan barci ya
kwashi ta….. Arif kuwa tunda yace kazarnan kansa yake faman yin ciwo daya shiga bandaki domin
gabatar da sallah sai ya k’asa ga zuciyar sa yadda take hassala, a haka bacci ya kwashe shi, ” ita
kuwa amira tana chan murna ta’ishe ta, chan kuma dataji karatun da fatima takeyi shi yakara tayar
mata da hankali, gani takeyi Kamar tasan abunda ta k’ulla… Da asuba fatima tayi sallah sannan ta
shiga tayi wanka atampha ta dakko ta saka d’ink’in yabi jik’in ta, sannan tafito palour gyarawa
tafarayi duk d’ak’unan ta ta gyara ta kunna turaren wuta, ” cikin dakin ta ta shiga cik’in mamaki taga
Arif ak’an gado a hankali ta matso kusa dashi ya Arif katashi kayi sallah, afirgece ya tashi ko addua
bai yiba jatayi da baya, can kuma ya rike k’ansa, wannan wata irin tarbiya akayi miki? Shine zaki ta
shine ina bacci, ” cikin saurin murya fatima tace Naga bak’a tashi kayi sallah ba shiyasa, ” Amma
yarinyar nan jaka ce ke wato ke kadai kikasan Allah nakasa alwalar dan haka bazanyi ba, ya tashi
yabar dak’in, ” innalillahi fatima take Kira chan Kuma ta fara sharar dak’in ragowar kazar ta gani
gaba daya tasha magani lallai ansa wane abu acikin kazar nan, Amma sai ta tattara ta k’aita shara
haka tagyara gidan daga nan ta huce kitchen shayi ta dafa, ta duba taga babu bread ballantana ta
hada dashi dining takai masa ta samu guri tanata lazuminta har ya sak’ko ko kallon dining din baiyiba
ya samu guri ya zauna ko kallon ta baiyi ba….. Suna zaune su k’aji sallama Amira ce ta saka wata
gown, fatima ma sai dataga k’yanta ballanta na kuma Arif, kafin takaraso Arif yaji ya kamota matata
kinyi kyau, ta wane langwabe kai, ga breakfast nakawo maka dan ban sonka da yunwa, ” fatima data
sake baki, sai kuwa cewa tayi uwargida ina kwana? ” cikin isa tace lpya, ” Arif yace shiyasa nake son
k’i saboda k’in son ci na da shana, ” haba sweetie na kasan bazan barka da yunwa ba ai, dan nasan
ba lallai a k’ula mun da Kai ba, ” fatima taga abun nasu gaba yakeyi tashi tayi zata bar gurin Arif ya
dak’a mata tsawa ke karki kara tashi idan ina guri, ” yauwa fatima kije ki gyara mun gurina, ” tsaki
fatima tayi zata shiga dak’in ta a fusace Arif ya mik’i, ” Amira ta riqesa haba mijina kadaina ta yar
da hankalin ka, ” wannan yarinyar batada hankali agida ba kikeyin komai ba? Kije kigyara mata, “
fatima cikin takaice tace zanje basai ka Bata ranka ba, ” a hankali cikin nutsuwa ta shiga part din
daga idon ta dazatayi tayi kirjinta sai da ya buga yadda taga gurin ya kazance ahankali ta dinga
gyarawa….. Da ma ba haushe yaci ba k’asanin Amfanin k’ayan k’a sai bak’a dashi! Yau hajiya ta
tashi taga gidan duk yayi kacha kacha tsintseya ta dauka tafara shara tanayi tana hutawa da kyar
ta’iya karasawa tana zama sai hak’i, alhaji ne ya sak’ko da Alama da yunwar sa ya tashi, hajiya
lafiya, “kadai bari alhaji dan wannan aik’in da nayi sai hak’i nak’eyi, shamsiyya ce tafito daga dak’in
ta kallon dining tayi taga bakomai, hajiya ina break fast? “sha sha sha kidai bansan wacce irin ‘ya
bace to ke muke jira kidora mana, ” ne? Kunsan Dai ban iya komai ba, ” alhaji ne yace yanzu sai
asamo mai aiki ai, ke kuma shamsiyya kiyewa kanki fada wallahi in bahaka ba k’ina cikin wane hali, “
tsake tayiwa iyayen sannan tabar dak’in, gurin karfe hudu tabar gidan motar ta taja sai gidan fatima
tana zuwa bangaren Amira ta shiga uwargida ran gida, ” aa shamsiyya yau kece agidan namu hahaha
nice mana, ince Dai k’ina gasa mana amaryar, dan banson kiyi mata imani, dan mallaki miji ta hanyar
biyayya agurinta baida wuya dan haka sai ki dage ” karki damu ai nagama da mijin! ” fatima fa
tanada ibada sosai da sosai, ” nagani da ido na ai, ” kinga yunwa nakeji kin Gama abinci? ” ai ne
bana abinci sai abunda fatima ta girka nakeci, ” muje to ko ta gama? ” suna shiga palour dinta su
kagan ta a zaune tana karatun al qur’ani ko sallama basuyi ba, ” shamsiyya kuwa data raja’a gurin
kallon gida, ” Amira ce tace kin gama abinci ne? ” fatima tace yace kar na girka, ” aikuwa baki isa ba
sai kin dafa mana, ” fatima ta kalle ta why not kekije kidafa I think yau girken ki ne kuma kema mace
ce dan haka bazan girka ba tunda bayai bani umarni ba, ” shamsiyya da tak’e ta kallon fatima yadda
tayi kyau…. Karar motar da taje yasa tafita ya mudassir ne Yana bak’in mota, ” aa Yaya ka shigo
mana, “a’a bazan shigo ba nan ma ya’isa, haka kika dawo yar lukata, ” hahaha k’aji ka yaya yasu
goggo ince lafiyar su kalou, ” lafiya lou fatima kije tsoron Allah ki zauna da mijinki lafiya kiye masa
biyayya kinje, kiyi hakuri aduk halin dak’ike watarana sai labari, ” tohm yaya Amma Yaya yaushe
zakayi aure? ” fatima kenan kina akwai wane abun ne? ” Yaya dan Allah ka aure shamsiyya, ” haba
fatima shamsiyya fa kikace? ” eh yaya please..” tohm zanyi tunani akai..” yauwa Yaya nagode suna
cikin magana Suk’a fito, ” shamsiyya tana ganin mudassir ta karaso gurin yaya mudassir inayini? “
lafiya kalou, ” kasan me yaya? ” sai kin fada…” duk girman gidan nan babu wacce tayi abinci, “
dariya mudassir yayi kar dai kice mun abinci ne ya k’awoki? ” haba yaya huce nan wallahi, ” to ai sai
ki dafa musu, ” hmm kyalesu kawai..” kin manta yau alhamis fatima ai tana azumi, ” lah naman ta fa,
” Amira datake tsayi jikinta yakara mutuwa, ” haka sukayi sallama Suk’a tafi shida shamsiyya…. Yau
da sassafe ta tashi ta gyara gidan sannan taje na amira shima ta gyara, wanka tayi ta saka duguwar
riga sannan ta samu guri ta zauna Yana fitowa yaganta kau da k’ansa yayi, sannan yace ki dafaman
dankali da nama da daddare toh tace masa.. Tunda ya shega Mota yaje jikinsa da dadi bakamar
kullum ba domin jiya zam zam din daya sha yaji dadin sa, Karatun alkur’ani ya kunna tunda yafara ji
jikinsa yaje kamar Ana gasa masa shi, ahankali yaje yayi dadai fatima ce kita wado masa ahaka ya
karasa office…. Tana zaune tana duba littafin tafsir dinta wato (safwatul tafaseer) taji anyi sallama daga kanta da
zatayi taga Maryam ce da sauri ta mike ta rungume ta, sannu da zuwa zauna na kawo miki ruwa da
lemo, ” a’a fatima irin wannan kyau haka? ” kuka fatima ta saka Maryam bakisan cikin halin da nake
ba tunda nazo gidan nan kullum cikin walaha, wallahi nagaji ga zagina da sukeyi, nasha wahala a
chan gida yau ma gashi ina fama arif baya sona bakuma ya kaunata, so nakeyi ya sawwake mun
wallahi, ” fatima Anya kuwa? Haba Fatima halin da kike cike kawai kika sane ki tuna mutanen da
suke da kudi Amma basu da ‘ya’ya? Ki tuna marayu marasa uwa da uba basuda komai, ” ki tuna
miskinai da gajiyayyu, ke kuwa duk wahalar dakika sha akwai ci da sha kuma kinasa kaya, wasu
nema sukeyi amma Har yanzu basu samu ba? ” Allah yabaki lafiya, Amma wasu tsabagen wahala
suna gadon asubuti, ” kuma Allah Yana tare dasu, wacce wahala kike sha fatima? Wallahi ki gode
Allah domin wasu matan ma mazajen su dukan su sukeyi wasu neman Mata wasu shaye shaye ke wa
suma basa basu komai daga ci har sha, ke mijin ki yana yimike daya daga cike? ” a’a baya yimun, “
Amma kike kiran wahala kullum? Ko kin feso Allah yabarki haka babu wata jarrabawa? Kinfeso yau
kiyi dariya gobe kiyi? Haba fatima duniyar har nawa take ki tuna duk abunda ya samu mutum alheri
ne? Kuma arif shine mijinki ba Dr ammar ba, Dr kunyi soyayya ne amma kuma arif ne mijin k’i kije ki
tambayi mudassir yagaya miki yadda arif yake sonk’i, kuma matar mutum kabarin sa dan haka ki
nutsu kiyewa mijinki biyayya ku zauna lafiya, ki manta da Dr! ” inshaa Allah zanyi abunda kikace wato
in banda kin tunatar dani inason saka kaina acikin masu nadama, ” fatima kenan dama ita kishiya
idan Allah Bai hadaki da tagare ba to fa zaki hadu da Mai shirka ko kuma mara mutunci, Dan haka
kowacce ce kishiyarki nidai shawarar da zan baki ki zauna da ita lafiya kuma karki cutar da ita, “
wato lokacin da aka kaine gidana Abdul yayi shaye shaye yazanine ahaka kuma ya kusance ne,
amma dana zauna nayi tunanin yariga ya zama mijina banida wata mafita sama na dage da yi masa
addu’a gashinan yanzu idan ya tuna abunda yayi da har kuka yakeyi, Dan haka kema ki kama mijinki,
wallahi fatima kin ban haushi fa kida mijinki yasaba da abincin ki da kuma kingaya mun arif babu
abunda yakeso sama da yasamu kulawar mace, ” hakane maryam indai zaki kula da arif kin gama
dashi kuma..” ai fatima k’owanne miji yana son kulawa, gake da kayan aiki amma kin zauna, ” bani
da bakin yi mike godiya wallahi kin tunasar dani nagode da shaidan yayi mun busha amma yanzu ya
gudu, ” yauwa kawas ko kefa, ga wannan aya ce ki markad’a ki tace Sai ki zuba zuma 4 spoon, “
wannan kuma kwa-kwace da madara ki markada ki shanye kiyi kwadan zogale da kantu kicinye hmm
bayane ma bata bakine sai kin bane labari dai, ” sakallahu khair godiya Mara adadi Allah yabarmu
tsare……. Maryam tashi mu shiga kitchen mijina yace yana son dafaffen dankali da nama, ” hahaha
masu miji manya..” duk’a fatima takai mata, dankalin ta ibo suka ferayi fatima ta wanke ta dura
gishiri tasaka Dan k’adan, sannan ta dak’ko nama ta yi fadi dashi ta yayyanka a tsaye sannan tasaka
mai a kasko ta juye naman ahankali ta dinga juyawa albasar da ta yanka ta juye, sai attaruhu da
tafarnuwa sai tumatur Dan kadan ta markada shima ta juye ahaka suka dan soyu ta zuba ruwan
naman da curry sai maggi kanshi ne kawai yake tashi.., ” fatima irin wannan girke, ” Maryam sai
abdul yama ci tukunna, yanzu mik’omin kankana da abarba sai ki mikon mangoro, ta hada tayi
blending dinsu sugar kadan ta saka sai flavour, ” a haka suka Gama abdul yazo daukar maryam sai
da sukayi sallama ta tafi… Gyara gidan tayi sannan tayi wanka, yau tafara period so bata sallah
turaren wuta ta saka a Dak’in ko’ina gwanin sha’awa, tana zaune tana jiran shigowar arif sai baba
Mai gadi ya shigo aguje hajiya alhaji yayi accident, ” da sauri ta dak…… *Urs nana diso* *60-62* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Gyaran gida tayi sannan tayi wanka, yau tafara period so bata
sallah turaren wuta ta saka a Dak’in ko’ina gwanin sha’awa, tana zaune tana jiran shigowar arif! Baba
Mai gadi ya shigo Aguje hajiya hajiya alhaji yayi accident, ” Da sauri fatima ta dauke wane Dan
mayafin ta fita waje, tana fitowa taga babu key din mota tayi saurin tawa dak’insa domin dak’ko key
tana dauka ta sauka, Har zata shiga mota sai Kuma ta jiyo baba Mai gadi ina fatan Amira tatafi tun
dazu? ” ina ai bata tafi ba dazu ma dana gaya mata ahaka tace nabar mata dak’i nazo nagaya miki
kice baiwarsa, ” wane yanayi fatima taji tashiga kawai sai ta rufe motar tayi hanyar cikin gida, ” baba
mai gadi da mamaki ya kamasa yarasa mai zaiyi sai cewa yayi fatima ina zakije, ” jiyo wa tayi ta
danyi shiru na lokuta sai cewa tayi matarsa wacce yakeso yake kauna bataji asubutin ba saine da ko
ganinsa banason yi, ” baba yace ai bantaba tunanin ke yarinya bace ba sai yanzu mijin nake? Ko kin
manta aljannar ki tana tafin kafarsa? ” baba bazaka gane yadda natsane Arif ba banason sa kwata
kwata, ta fashi da kuka, ” kiyi hakuri kije ki duba sa danAllah, ” tohm baba…. Mota tashi takama
driving cikin mintina ta’isa asubutin babu kowa agurin sa sai hajiya, sallama tayi, ” hajiya tace yar
iska sai yanzu kika damar zuwa ki duba sa, ” waya sani ma ko wanne abun kikaye masa yaji ya buga
motar? ” Fatima da mamaki ya’isheta kallon ta tayi tace hajiya ina yini? ” tsake tayi waje sai ki kula
da mijinki ne ga tafiya ta, ” hawaye duk ya cika i’don fatima, Dr ne yashigo tayi saurin gogewa, “
karin ruwa yasawa Arif sai Kuma magungunan da yakawo, ” madam ga shinan in ya farka yaci abinci
sai a bashi maganin sa, ki kuma kula domin jininsa ya hau, Amma babu wata matsala sai ‘yar
buguwa itama a hannun sa, ” kad’a Kai tayi sannan Ta koma gida ta dak’ko abinci, tana isa asubutin
ta tarar dashi ya tashi, tunda ta bude kofa yake kallon ta, sai kau da kanta takeyi, ” zama tayi Sannan
tace sannu Allah yakara sauke, ” A hankali yace amin, ” Arif zuciyar sa sai tafarfasa takeyi jin sa
yakeyi Kamar ya rungume matarsa su tafi Amma ina yasan bamai yuhuwa bani ba, ” a hankali taji
sautin maganar sa zan shiga bandaki, ” ko kallon sa batayi ba tace ko fita zanyi ne in kafito nashigo?
“Ki taimaka min bazan iya mikewa ba, ” okay Bari nakira Dr Sai ya kaika, ” zata bude kofa Arif yace
indai ne mijin ki ne to ki taimaka min na tashi, ” sai da ta tsaya na Dan lokaci sai Kuma tazo ta tsaya
ya riqeta takaishe toilet tukunna ta jiyo, ” kafin ya fito ta gyara gurin ta zuba masa abinci da lemon ta
koma ta zauna, ” da kyar yafito daga bandak’in, ” kollon ta yayi yace ina Amira, ” tana gida, ” tasan
ina asubuti kuwa, ” eh mana ta sani tunda Wanda ya gayamin ya sanar da’ita, ” k’ad’a kansa yayi
sannan ya dauki abincin da hannun haqu, hannun daman sa kuwa ko motsa shi baya iya yi saboda
zafi, sai kallon abincin yakeyi ga yunwa gashi babu ta inda zaice, ” Dr ne ya shigo Arif yagani sai
kaĺlon abinci yakeyi, sai ya bashi tausayi, ” Dr yace madam mayi amfaninki I’dan bazaki taimaka
masa ba? ” damai Kuma zan taimaka? ” ai nagaya miki hannun sa a kunbure yake bazai aiki ba, “
tashi tayi batare da wata magana ba ta dau abincin tafara bashi abaki, ” Arif Dadi Kamar ya kashi
she, can sai cewa yayi kince abinci? ” eh, ” yawane girgiza kai anya kuwa? Bari nashafa cikin ki naji,
Har zaisa hannunsa ” tace karka soma malam….. Ke mansura Har yanzu baki gama aikin bani ba,
yunwa nakeji Dallah malama kiyi sauri kigama kije ki wanke mun bandaki, to shamsiyya ai saurin
nakeyi, ” mtsw wannan kuma matsalar kice ” wallahi hajiya wannan Mai aikin ta k’i jakace lokacin da
fatima take gidannan karfe shabiyu angama girk’i Amma yanzu karfe biyu ko gyaran gida bata gama
ba, ” hajiya tace yar bura’uba ce ke mansurah..” Naam hajiya gani, ” wai ke wacce iri ce nace tun
dazu nace kiyi sauri, ” shamsiyya tace ai kinsan jahilace shiyasa, ” haba hajiya tun safe kina ganin
aiki nakeyi ban zauna ba, tunda shamsiyya da girman ta ta dinga tayane wane aiki, kinga itama
macece, ” ai biyanki kudi mukeyi dan haka kikara hada ‘yarta dake Sai kince ubanki, ” Allah Baki
hakuri hajiya, Amma gaskiya bazan iya aiki agidan da basu san darajar mutane ba, karki manta
shamsiyya mace ce gidan wane zataji, a hankali mansurah ta dauke kayanta ta bar gidan, “
shamsiyya ai gashi nan kowa Sai ya gudu saboda halinki wallahi kichanja halin ki, ” suyeta tafiya
mana bakina da kudi ba sai k’i kara kawo wasu, ” kitashi kishiga kitchen ne yunwa nakeji….. Fatima
ce tayi sallah tana zaune akasa tayi tagumi, ” Arif kuwa so yakeyi yayi sallah Amma bazai iya tafiya
ba sai an rik’e shi..” sallamar su mumy sukaji da dady sai farouk, ” mumy tace sannu Arif garin yaya
haka yafaru…” fatima tace ina yinin ku..” mumy ta amsa da lafiya, ” farouk ne yace yaya ya jikinka?
naji sauki anjima zaa sallame ni, dan taimaka min nayi alwala, ” arif tun dazu bakayi ba saboda me? “
dady babu komai..” fatima dataga hirar su sukeyi sai tabar Dak’in tunda tafita tunanin Dr ammar
kawai takeyi..” Arif kaga abunda nake jiye maka gashinan fatima bata sonka mukan mu fita tayi
tabarmu, ” mumy Kenan ne ina sonta Kuma ina kaunarta, please karku bata mata rai, ” haba Arif ya
naga kuka mayi haka? ” dady ina sonta, ” farouk cikin tausayin dan uwansa yace yaya itama tana
sonka..” mumy kuwa zama tayi cike da tausayin dan nata….. Shamsiyya daman nazo akan maganar
najanyi auren mu dake, ” innalillahi saboda me abubakar, ” a gaskiya shamsiyya kinada matsaloli
dayawa kwa-kwata baki iya komai ba common gyara gida baki iyaba ballantana girke, kuma
azamanin nan babu mai auren mace ahaka dan haka kiyi hakuri, ” wayyo Allah na shiga uku tafara
rusa kuka, tana shiga gida hajiya tace lpya? ” ya janyi wayoo ya janyi baya sona… Tunda aka sallame
su, suka tawo gida tare da su mumy suna isa amira ta fito oyoyo sweetheart, ” mumy ce tasha kunu,
me yasa bakije asubutin ba? ” lah fatima bata gaya muku ba ai haka tace min na zauna zataji, “
Fatima ta kalle ta cike da mamaki amira karkiyi mun karya akan mijinki indai Arif ne na barmiki shi
tunda kike sonsa…. *Urs nana diso *62-64* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Fatima ta k’alli Amira cik’e da mamak’i, Amira k’ark’iyi mun
karya Akan mijink’i indai Arif ne na barmiki shi tunda naga alamar k’e kina sonsa, ni kuwa…” mumy
ce tace ya’isa haka ke fatima ko a mafarki naga kina wannan rashin kunyar nayi sadaka amma a
gabana kike fad’in haka, anya kinsan tahirin rayuwarki kuwa? Kiji k’i tuntuba k’ije wanene arif? ” jikin
Fatima duk yayi sanyi kayansa ta dauk’a mota ta huce bangarin ta dasu, ” Amira kuwa da take jiran
kadan tace ai mumy bakiga komai ba amma zaki gani da idonki, ” Arif daya kasa cikakkiyar magana
ahankali Amira ta rike shi suka tafi bangaren sa, su mumy suk’a bita abaya…. Farouk ya tafi part din
fatima Yana shiga yaga tana k’unna turaren wuta Matar yaya yunwa nakeji, ” yanzu na d’ura abincin
amma ka jira yanzu zan gama, ” tohm, matar yaya ” Naam..” Na tambayi ke mana? ” ina jinka, “
akwai abunda yafi soyayya? ” farouk kenan babu abunda yafita soyayya tana da dadi tana kuma da
d’ace a rayuwa! Rabuwa da masoyi bashida dadi kwata kwata, ” tabbas haka yake amma ita kuma
k’iyayya fa? ” bakaje sunan ba babu dadi, I’dan mutum ya tsaneka a rayuwa, Sai kaji dama k’a bar
duniyar! ” ta yaya k’ik’asan haka ? ” saboda mutanen Dana tashi dasu sun tsaneni, ” ashe mutum ya
soka abune Mai mutukar kyau? ” Tabbas abune Mai kyau, ” Mai i’sa kika tsane ya Arif bayan kinsan
yana sonki? ” maganar da fatima Bata taba tunanin Zata fito daga bak’in Farouk ba, farouk kenan
bantsane yayank’a ba illa son sa da nakeyi, ” yaudarar ran so? Ko kuma me, ” jikinta duk ya mutu
inada aiki yanzu, maganganun da yagaya mata su suk’a dinga yawo a k’anta, ” farouk mik’ewa yayi
ya tafi masallaci, ” Arif tunda yayi wanka yayi sallah ya kwanta ak’an Gado Dan ya huta, Amira ce ta
shigo sannu arif dama inason magana dak’ai, ” ina jink’i hope lafiya? ” eh lafiya dama account dina
yayi low siyasa nace zangaya maka, ” me zakiyi dasu? ” kaya nakeson siya kuma inason yin abubuwa
K’ala K’ala…” okay kamar nawa kikeso? ” dubu dari biyu, ” dubu dari zan baku ke da fatima kuraba, “
haba Arif yayi kadan, ” eh nabawa mukhtar ya siyo muku kaya da lesuna, ” tohm sai ka turon ta
account dina kokuma kabani check okay zanturo miki kawai…… Hajiya na rasa yadda zan zuba rice
din, ” sau Nawa fatima takeyi agabanki, ” tohm Hajiya bari na dafa, ” yauwa ko kefa..” ruwa
shamsiyya ta dura sannan tasaka waken da shinkafa, Sai da takara ruwan kusan ciken tukunya
shinkafar da bata fi 1cup ba, tunda ta tafi dake Sai datayi k’usan one hour ta koma kitchen din, tana
bude tukunyar gaba daya shinkafar ta chabe ta juyo haka, ” alhaji yace ko kefa munada budurwa
Amma bata iya girke ba, ” ai yau zakaci, kowa na zubawa ya tashi, ” alhaji mai yafaru? Kizauna ke
kici, ” gaskiya shamsiyya kinada matsala kin cuce kanki, ” turo baki tayi oho oho nidai…. Mudassir ne
yake kwance juyi kawai yakeyi, maganganun fatima yake tunawa lokacin da take cewa ya so
shamsiyya, wata zuciyar tace ya sota wata kuma tace mai zakayi da ita, alwala ya tashi yayi sannan
yafara neman zabin Allah…… Fatima tana gama abinci ta zuba, Har zata saka kayanta ta tuna suna
jin yunwa ta bar vest da dogon wandon ta, mayafi ta rufa ta dau abincin, ta huce part din Amira tana
shiga palour ta gansu azaune gaba dayan su, zama tayi tace sannunku da hutawa momy, ” yauwa, ki
shiga kikera arif din cewar amira,” tana tashi ta shiga dak’in a kofar dak’in ta tsaya kafito kace
abinci, ” Yana dariya yace yunwa nakeji Amma bazan iya ta shiba, ” matsowa tayi ya riketa cham ya
tashi Yana dariya, ” fatima tace ashe k’aji sauke, tayi gaba ya janyi mayafin ya wadi, kallonta yayi
gaba daya ta riketa shi, breast dinta sunyi tunbul tunbul matsawar datayi Zata dau mayafin ta hips
dinta suka kada, Nan da nan Arif hankalin sa suka tashi, tana yafa mayafinta ya riko ta, ta fizge
hannun ta ta tafi palour, ” biyota yayi abaya Yana dariya, su mumy har sun kusa gaba cin abincin, “
farouk yace Matar Yaya dad’ina dake iya girke, ” Amira ta bata rai bari na zuba maka abincin, “
tohm..” yauwa fatina tace ” Naam ga kudinan ko zakiyi amfani dashi, ” a a da kudi na, basu kare ba,
” aa..” inada kudi bari naji inada aiki… Tana fita tafara hira da salusu mai wanke, ” Arif Yana fitowa
ya ga Sai dariya takeyi ga jikinta sai kadawa yakeyi..” wane tsawa Arif yadaka mata… *Urs nana
diso* *64-67* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Fatima tana fita tafara Hira da salisu mai wanke, ” Arif yana fitowa yaga sai dariya takeyi ga jikinta sai kadawa yakeyi..” wane tsawa Arif yadaka mata batasab lokacin data shiga parta dinta ba, ” Arif ne ya karaso gurin salisu, yace ina fatan kanason aikinka agidan nan? ” kwarai kuwa oga inaso dama tambayata tayi shine na bata amsa..,” from today komai ta tambaya karka bata amsa kabar gurin if not zan sallame ka, ” a’a oga zan kiyaye ayi hakuri danAllah, ” a hankali arif yahuce part din fatima yana shiga yaga bata palour daki ya bita ya tarar tana saka riga, tsayawa yayi yana kallonta, ” jitayi kamar alamar an shigo, tana jiyowa ta saka ihu, da sauri Arif ya motso yasa bakinsa anata nan da nan ya k’idemi, tureshi tayi tafito palour tana masifa, nifa banason nace please karabu dani mana, ” fitowa yayi idonsa har sun chanja, kallon sa tayi sai da kirjinta ya buga, ” fatina kinkasa fahimtar halin danake ciki, ina bukatar ki akusa dani karkisa hankali ya gushi ko kuma nafara naiman mata please kitaimaki ne wallahi ina sonki, ” kallonsa tayi ta k’ada idonta, ya Arif please karabu dani nema nahuta mana, kullum aikinka k’ana sona, to wallahi da sauranka tunda sona kakeyi ba kaunata kake ba, Kaji gurin matarka amira but ne har yanzu dr ne araina, dak’in ta ta shiga ta kulle……… Arif da yak’e tsayi jiyaye zai fadi ahankali ya zauna, daga bisane kuma ya tashi k’ansa ki juyawa, ahankali ya shiga motarsa yafara tuk’e, ” yana isa office kowa sai ya jike yake yimasa, ” yana cike wasu files, mubarak ya shigo yanata sallama bai amsaba, sai daya buge tebur sannan yadan firgeta, ” haba arif mai ke damun ka? Tun dazu fa nazo amma kana duniyar tunani,” mubarak wallahi nayi kuskure, ” name fa? ” son maso wane nakeyi, fatima bata sona ko kallona batason tayi kwata kwata, she hated me dont kno why!!! ” hahaha daman ai nagaya maka kaji tsoron ranar da sonta zai shigeta gashi nan, ” malam ne kabani shawara kaji? ” na farko dai kasan mace babu abunda tafiso irin kulawar d’a namiji dan haka kalura da wannan, sannan duk abunda takeso kayi kokarin ganin ta samu, ” yau karkaci abinci in dare yayi karike cikin ka kace ciwo yakeyi nan ma hankalin ta zai chanja, ” wayar da ka hanata yanzu kasiyar mata irin text dinnan kamar I trust you with anything, you know everything about me, we have been through so much, you are closer to me than anyone else, I love you! Please don’t hate me, ka dinga turamata cool kuma ka dinga shamtarta kamar kissing dinta daukar ta irin dai suprise haka, ” Kai muktar kana wuta fa, amma nagode sosai… Baba mai gadi mota ta tayi datti ka wanke min kamin na shirya, ” tohm shamsiyya, ” hajiya tana kallo adaki gidan sai k’arne yakeyi, “anty zainab tayi sallama, babbar yaya yanaga gidan nake haka? ” ina shamsiyyar? ” hmm ne bamasan ma me zanci miki ba, a kalla tafiyar fatima ankawo yan aiki sun kai 7 kowacce tace bazata zauna ba saboda halin shamsiyya, ” ai hajiya ke kikaye sak’ace Tun farko, shamsiyya ko shara bata iyaba sai rashin kunya, kidube gidanki haba haba sai kace bakida ‘ya, ” to yazanyi tafi karfi na, ” tabbijan da aiki agabanki, ” shamsiyya tace kinga anty zee idan Zaki dafa mana abinci kidafa mana banson surutan da kikeyi! ” ai ne nagama da iyayena lapia sai kiyi fatan kema kigama dasu lpya waweya kawai tayi ficewarta….. Farouk farouk, ” Naam matar yaya ya’akayi Please kakiramun ya Arif kace zanje asubuti zanga likita kaji, ” okay no matsala sai k’in dawo, ” to motarsa ta shiga taja sai asubutin tana isa tatarar babu mutane sosai, aka bata number ta 7 anata shiga Ana fitowa, ” wane mutum ne ya shigo da matar sa da cikinta alamun nakuda takeyi sai zubar jini takeyi, ” fatima da ke zaune hankalin ta ya tashi yadda taga matar, mijin nata sai magiya yakeyi wa likitocin amma babu wanda ya kula ta, ” hakan yasa fatima ta mike tatafi gurin likita ta gaya masa, ” kinga inada marasa lafiya please kifita, idan number su tazo sai su shigo, ” please doctor ka taimaka musu wallahi zata iya rasa ranta, ” kifita nace idan…” cikin fushi tabar office din nurse ta dinga bi tana musu magana amma babu wanda ya kulata, Ana kiranta, tace bayin Allah nan su shiga, da kuka yafito ya rike matarsa, ” fatima ta taso aguje me yasa kake kuka? ” yace tunda banda kudi na k’aita gida takarasa, ranta abaci tace doctor’s kowa ya fito, nu nasu tayi da hannun ta tana magana k’ai kuwa Dr fahad wanne irin imani ne dakai? Anya kuwa kanada tausayi? DanAllah ka dube yadda take zubar da jini amma baka tausaya mata ba Dan basu da abun duniya, yanzu idan mahaifiyar kuce bakwaso ayi mata haka ba, ku tina itama uwace tana da ‘ya’ya k’uma uwace ta haife ku, kuma mace zaku haifa kuma wataran sai kun aurar da mace, haba yan uwa mayasa muke manta mutuwa? Wallahi *Duniya ce..* A duba ta zanbayar da kudin, ” Dr fahad yace a’a ne zan bayar kuyi hakuri, ” fatima ta matsa kusa da Mai cikin ga wannan Allah yaraba lafiya, ” nagogode…dakyar take magana mijinta kuwa addua kawai yakeyiwa fatima, ” haka fatima ta koma mota ko likitan bata gani ba ta jiyo gida… Tunda fatima ta koma gida girke ta dora takaiwa kowa nasa sannan ta shiga wanka, tana fitowa ta saka duguwar riga ta kamata sosai , tayi kyau hula tasaka ta kunna turaren wuta ta zauna tana duba wane novel , ” sallama taji tana amsawa taga ummi ce, ” Amarya yanzu Haka akeyin rayuwa biki ko gayyata? ” hmm ummi naji gidanku lokacin akace mun kina nijar, ” eh naji gidan kawu kinga yadda kikaye kyau lallai Arif ya’iya k’ewo ko ma ciki ne dake, ” hahaha uwar zolaya katin k’ika kawo, ” eh shi ne bikina wane satin, ” kai Amma naji dadi Allah sanya alheri ” ameen please kiban wane sirrin mana, ” hmm ne mai zan gayamiki? ” haba teema please!…. Ummi kisane shi aure hakuri ne, ” fatima nasan wannan duk anyimun wannan kibane na mallakar sa cikin ilimi da fahimta, ” tohm ummi idan an kwana biyu da daddare gurin 6 kisaka da zarar zaku kwanta saiki saka fitinannun kayan bacci, ” yauwa hajiyata wannan karatun nakeso, ” hahaha Allah ya shirye ki, ummi idan ankaiki dole ne yanzu zakifara domin ki mallaki abunki dawuri, daman jiran da kikeyi kishiga kuma kin shiga, kuma kidinga saka masu fito da bbs, ” tohm, ” Ki kasanci mai girmama iyayen mijinki, ‘yan’uwanshi, da dangin shi gaba daya, domin biyayya da ladabi zai qara miki mutunci a idan mijianki da ‘yan’uwanshi baki daya, ” Ki Kasance mai gyara gida, jikin ki, abin cin ki, da komai na ki,ummi Ki kasance ma’abociyar kwalliya da zata qayatar da mai gidanki, don nisantar dashi shiga halaka…”inshaa Allah zanyi yadda kikace nagode sosai Allah bar zumunci ne zan tafi ki gaida Arif, ” zaije.. Sai karfe 8 arif ya shigo, yana dawowa wanka yayi ya sak’ko kasa ya kwanta, akan kujera yunwa kawai yakeji, ” fatima tafito takalli dinning baici abincin ba, ” ya arif ga abinci Akan dining nan, ” ko kallon ta baiyi ba yace na koshi, ” haba ya arif please kaci kar..” ke na koshi nace miki, ” daki tashiga, gurin karfe tara ya kwallara wata k’ara, aguje fatima tafito lafiya ya arif tana jijjiga shi, nace maka kaci abinci gashinan ruwa ta zuba masa ahankali ya bude idonsa abinci ta zuba masa tafara bashi Sai da ta gama bacci ya kwashe shi, ” kallon sa kawai takeyi, kasa daga shi tayi Sai kallon sa takeyi….. *Urs nana diso* *67-69* DUNIYA CE *NA NANA DISO* A haka Arif ya kwana ajikin fatima, ” da asuba yatashi ya ganta ajikin kujera ta jingina, Nan Arif yayi hamdala ya kuma godewa Allah domin gani yakeyi Fatima tafara son sa, a hankali yafara shafata, ” arazani ta tashi tana k’allon sa, ” bari naje masallaci nadawo, ” dak’i ta shiga tayi Alwala tayi sallah gidan ta gyara, ta dora breakfast, tafere dankali ta gama ta dura akan dinning, wanka tayi sannan ta zauna tunanin ta inda zata samu waya takeyi, ” Arif Yana dawo wa daga masallaci ya rungumo fatima tabaya, ” a tsorace tace wayyo, ” oh tsorona ma kikeyi, ” please ka aramun wayarka, ” me Zakiyi daita? ” uhm uhm zankira Maryam ne, ” tana fada yagani karya takeyi kawai ya mik’o mata, ” washe baki tayi cike da murna, ba wanka zakayi ba? Gwara kaji kayi sai ka sakko kayi breakfast, ” ko dariya baiyi ba ya hau sama, ” fatima tayi wane tsalle harda juye tatafi dak’i, ” Arif a hankali ya sak’ko, ya bita dak’in abakin kofa ya tsaya, ” wasu numbers ta danna sannan takara a k’unne, hello Dr, ” fatima ykke ygd, ” ba lafiya ba, haba Dr kamanta soyayyar da tak’e tsakanin mu wallahi nakasa cire sonk’a a raina, ” fatima dole mu yadda da kaddara ina sonki amma Allah yasa ne ba mijinki baniba, actually ya kamata ki zauna da mijinki lafiya, nema dady ya hadani da ‘yar kanwarsa bikin mu saura 2weeks, ” Amma kabani mamaki.., k’amin takarasa magabarta Arif ya wanka mata mari, ya kara wanka mata..Yana huce Ne zaki mayar dan iska Ne zaki yaudara, ko k’in manta neni mijinki, to wallahi Sai nayi maganin ki waweya, ke kike cewa wasu duniya ce to wallahi kiyi hankali Akan hakkin mijin ki kada duniya ta tambayi ke, samansa ya hau, Sai kaiwa yakeyi Yana komowa, fatima why Ina sonki but sai azabtar dani kikeyi kansa ya rike yanata surutai, ” k’an gado tafada Sai k’uka takeyi Mai ci k’e da Nadama…… Hajiya please kisanar da alhaji yakaine umrah, ” lallai bakida kunya mekike mana agidan? Babu faranta mana dakikeyi shine zakice abiya miki umrah, ” hajiya please kitaimaka walhi bazaki gani ba, ” hmm zancen kikeso tashe kibane wuri, ” hajiya kitaimaka? Ne bari Natashi nabaki gurin Mara kunya kawai, ” sallamar habiba shamsiyya taji, ” higeyar gari sai yau kika ga damar zuwa, ” kidai bari shamsiyya wallhi dad Ne ya matsa min akan maganar aure shiyasa, anjima ma za’a kawo kudina, ” dagaske? Oh ne shamsiyya sai tafiya kukeyi Ne har yanzu babu tsayayye, ” Allah sarki kawata kidaina damun kank’i aure nufi ne na Allah, Kuma gaskiya ki gyara halayenki walhi, iyayenki kidinga taimaka musu, kusan 23 Amma kink’e kiyi hankali, dubi gidan ku? ” hmm habiba bar zancen zomuje nasiyo ice cream ” hmm dadina dak’e gudun gaskiya…. Wanka Arif yayi ya shirya cikin shaddar sa blue yana fitowa palour yaga fatima batanan ga yunwa da yakeji amma haka ya kalle abincin yafita, part din Amira ya huce yana shiga tafara masifa sai yanzu zakazo baka damu daniba kwata kwata, ” haba sweetie kina raina nafison idan nashirya sai na shigo, ya rike hannun ta kiye hakuri idan nabata miki, ” bakomai bari nafesa Maka turare naga kamar amaryar taka bata fesa, ta dak’ko ta fesa masa kaga yadda kayi kyau, ” really yau ki dafamun tuwo shinake sha’awa, ” tohm sai kadawo… Yana fita gidan su ya huce suka gaisa dasu dady, ” mumy ce ta kalle sa tace Arif karka manta fatima yarinya ce duk abunda zatayi Maka kuruciya ce, ” tohm mumy, ” kasuwa ya shiga kayansa sunzo ya rarrabawa mutane, yasa mubarak ya fitar masa da k’ala bakwai bakwai na matan sa… Fatima tana zaune tayi tagume, maganganun Dr su suketa yawo a kwaryar k’anta, ” Arif zankula dakai kuma zan zauna dakai komai rintse komai wahala, ” bene ta hau ta bude dak’in Arif gyarashi tafayi sai da ta tabbatar ko’ina ya gyaru sannan tak’unna turaren wuta ta sak’ko, kasancewa bata sallah zuwa tayi ta chanja pad sannan ta feshi jikinta da turare, ” dariya tayi sannan ta huce kitchen tuwo ta dora, tafara gyara danyar kubewa, cikin awa daya ta gama tuwan ta da miyar kubewa danya tasha kifi suk’un biya, Amira ta zubawa nata sannan baba Mai gadi da sunusi, takai nasu dinning table… Baba ga abincin ku uwar dak’ina tun yanzu sannunki da kokari Allah yakawo ‘ya’ya nagari, ” dariya tayi sannan ta huce part Din Amira, ” amira tana zaune tana tunanin inda zata samo tuwo ko bayarwa zatayi asiyo mata? ” fatima tayi sallama, ” da kyar ta amsa, ” uwargida inayini ga abincin ki, ” lpya yaza’ayi kiyimana abinci tun yanzu? ” karfe 6 ne tun yanzu? ” eh mana salan ya sandari? ” fatima tace idan ya sandari sai ki dumama, ” akagaya miki kowa ne yak’e cin dumame, ” haha ai sai kidafa wane, ” sai anjima, ” excuse me fatima inason kike kowa? Please ki daina barin mijina ba kulawa, tunda naga bakisan darajar miji ba, ” k’allon ta fatima tayi tabar dak’in, wane kuka tasaka tana shiga part dinta, Allah kasamin son mijina da kaunar sa….. Amira tana bude wa taga tuwo ne wane murna ya’ishe ta, flsk ta dak’ko ta zubawa Arif duk da tasan ba girkin ta baniba, amma ta haka zata gama dashi, dariyar mugunta tayi sannan ta huce dak’i, ” fatima kuwa lemo tayi masa sannan ta k’ara gyara jikinta tunda tayi sallar isha’i take jiran shigowar sa, ” Arif Kuwa yadade da shigowa yana part din Amira yana cin abinci, Kai rabona dana ci tuwo Mai dadin wannan Har na manta, ” amira tayi dariya nema naga ya kamata nafara yiwa mijina abinci that’s why, ” shiyasa nake sonk’i wallhi, ” Amira takara murna yadda taga yana haba haba da’ita, ” sai gurin karfe 11 ya shiga part dinsa .. fatima tana zaune a palour tayi ta gume, ” sannu da zuwa, ” kallon ta yayi yace sannu, ” Ina ka tsaya inata jiranka, ” me zakiyimun? ” idon ta ya ciko da kwallah tace ga abincin ka, ” Na koshi, “me kace? Sama ya hau ya kyaleta, “dak’i ta shiga, ne Najawo wa kaina…. Da safe ta hada breakfast, ” Arif ya sak’ko..” ina kwana? ” lafiya lou, ” ga breakfast Nan karka tafi da yunwa, ” wane dadi yaje a cikin ransa sannan yace na koshi, ” please kace kaji, ” dariya yayi sannan ya tafi, ” yaya please zanje gidan Maryam, ” 2hours kawai Zakiyi, ” tohm nagode..” shiryawa tayi sannan ta tafi tana zuwa maryam ta rungumeta, zauna wa su kayi, ” irin wannan zuwan bazatan? ” haha wallhi, ” muryar Abdul su kaji, sweetie nakasa saka rigar, ” ina zuwa Fatima bari nagama da mijina, ” tohm sunfi awa daya, ” fatima Har tagaje..” taji sun fito, Sai kadawo, ” haba amaryata baki hugging Dina ba, ta rungume shi much love dear..” tayi dariya, fatima ce tatashi na tafi mijina 2hours yabani….. *Urs nana diso* *70-72* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Ke Fatima har yaushe k’ikazo? ” maryam zan biya gidan farida shiyasa kuma yace 2hours zanyi, Amma nayi miki alkawari zandawo, ” tohm shikenan ga zogale Nan kitafi dashi..” yauwa daman kamar kisan inaso, ” hahaha anfada soyayyar Arif, ” kinga sai anjima, ” k’i gaida gida.. Tunda ta fara driving mai ta tsaya tasha sai tayi gaba, dakyar tagani gidan farida tana shiga taganta a tsaye tasaka wasu english wear, ” lallai ne amarya irin wannan shiga haka? ” yanzu mijina ya fita Kuma shigar yakeso, ” ya gida kina lpya, ” lpy lou bari na kawo miki ruwa, ” nagode azumi nakeyi, ” gaskiya abunda kikeyi fatima Bai kamata ba Arif yazo gidan nan yafi a kirga…, ” Fatima tayi saurin katse ta hmm farida Arif din da ko abinci na yanzu baya ci, ” hahaha kenan ke kikace yarabu dak’e, ” nasan nayi kuskure but bansan ta ina zanfara ba, ” ke kuwa k’ek’asan ta inda zaki fara Dan haka k’i zauna da mijinki lpya k’i kuma gama dashi ta hanyar kisisina, ” in bahaka ba sai kishiyar ki tagama dashi, ” farida inason Arif Ina kuma kaunar sa, idon ta ya cika da k’wallah banson inason sa ba sai this day’s, ” haha gaskiya naji dadi ga wane sirri na gyaran jiki k’i jik’a lalle idan ya kwana sai k’i hada lemon tsami da turare k’i wanke jikin ki dashi for good 3 days zakiga yadda fatarki zatayi, ” nagode bari na tafi, tohm sai nazo….. Tana koma wa gida wanka tayi tasaka duguwar riga duk tabi jikin ta, girke ta dura Cikin awanne tagama ta hada mai lemon abarba da kwakwa tajera komai a dining, baba mai gadi ta kaiwa nasu, ita k’uwa amira sai bayan sallar magariba nakai mata, qurani ta dak’ko tafara karatun ta, duk ta damu Arif ba halinsa baniba Amma yanzu yana dadi wa, dankwalin ta ta daura ita kanta sai dataji kunya yadda kayan suka bita, abincin ta dauka ta tafi kaiwa amira sallamar da zatayi taga arif sai soyayyar su sukeyi shida Amira, ” kallon ta yayi shi kansa yaji babu dadi, sai kuma yace sweetie kiyimun tausa, ” Amira ta wane kad’a ido, tohm ina zuwa…” fatima kuwa ajiye abincin tayi ta ruga aguje, kuka ta saka sai da tayi mai isar ta sannan tabar palour…” yana shigowa yaga batanan lemon ya dauka yasha, da asuba fatima ta tsugunna har kasa ina kwana yaya? ” lpylou..” please kayi hakuri in nayima lefe..” bakomai, ” zanje gida yau.., ” a’a baza kije ba, ” kusan wata hudu fa kenan Amma banjiba, ” zakije Amma ba yanzu ba, ” Zama tayi akujera tana satar k’allon sa wane kyau yakara mata , ” yau dai zaki fita daga girke ko? ” eh yaune..” yauwa…. Shamsiyya tana kan gado sai juye takeyi, wayarta ta dak’ko waya ta kai waya amma babu mai kirana, ga yunwa nakeji, ” palour tafito taga hajiya tana waya, abinci tagane akan table dauk’a tayi ta cinye..” abincin k’i ne? Da zaki dauka, ” wallahi yunwa nakeji hajiya Amma kiyi hakuri, ” wayar shamsiyya ce tafara kara dauka tayi muryar muddassir taji ” aa yaya mudassir yau k’aine ka kirane? ” eh..” haka suka gaisa tana kashe wayar.. hajiya tace kinsan dai yafi karfin muddassir? ” haba hajiya ki dinga fadar alheri mana dama inasonsa… Mudassir dakai fa nake magana, ” goggo ya akaye? ” dama kauye zanji shine nakeson kabani dubu dari, ” me zakiye da dubu dari, ” Dan ubanka ne kake tambaya Kai kasan tun lokacin danake rainon ka, to tunda bazaka bani ba ka biyane kudin rainon ka, ” goggo ba wai bazan baki baniba, ” yimun shiru kaji ka dakko min, ” tohm in naje kasuwa zan bayar Akawo miki, ” kayi wa kanka arzuki da yau kagane k’uran ka, ” dak’in sa ya shiga ya sawake wannan duniya…. Mansura banaci kidinga hakuri ba? ” haba mai gida wannan Abu da akeyi mun agida wallhi na gaji cin mutuncin yau daban na gobe daban, ” anyi miki din k’o shi mai gidan Bai isa ya tanka ba, ” *Duniya ce* dai… Amira ki zaune ita da mumy, ga giyar nan nakawo miki amma kizuba masa kadan fa Kar agane, ” tohm mumy daman kinsan yarinyar nan naga Kamar tafara gamawa dashi, amma idan na zuba giyar nan kinga yaje mata ahaka zata kara tsanar sa , ” hakane Amira ai Sai mun fitar da’ita kota halin yaya ne, ” gaskiya ne mumy yanzu k’i tafi yanzu zai dawo, tohm sai anjima..” gurin karfe shida Arif ya shigo wanka yayi sannan ya fito palour, ” amira ce ta rungume shi duk kagaji ko eh wallhi, bari nakawo maka lemo, tana kawo masa bashi tayi, ” Arif yace wannan wane irin lemo ne mara dadi? ” amira tayi dariya, ” bacci nakeji Bari na tafi, dakyar ya karasa part din fatima Yana layi dak’in sa ya shiga, ” da sauri ta bisa tana kuka, ” ya Arif mai kasha ya Arif, ” ahankali yake magana ba kince bakya sona ba, ” rungume sa tayi ina sonka Allah…. http://nanadisoo.blogspot.com *72-75* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Ya Arif Mai kasha, wane kuka fatima takeyi mai cike da tausayi, Ya arif kagayan abunda kasha? ” A hankali Arif yake magana ba kince bakya sona ba?? ” Fatima ce ta rungume shi, cikin kuka harda shash shek’a tace ina sonka Allah inasonka, tanata surutin ta bacci ya dauke sa, ” rungumesa tayi tana ta surutai abunda nayi maka ban kyauta ba, arif nayi kuskure kanuna min soyayya amma na banzatar da’ita, nayi kuskure Amma ina sonka ina kuma kaunar ka, ahaka ta gogi hawayen fuskar ta, ” sallama taji a palour sauke Arif tayi tafita, ” mumy tagani azaune ita da amira, ” mumy ina wuni? ” Lpya tun dazu mukazo munata sallama Amma kinyi mana banza? ” uhm uhm Daman Bana Jin dadine ban kuma jiku ba, ” to shi ina Arif din cewar amira, ” Fatima Tarasa me zata ce Sai can Kuma tace bacci yakeyi, ” Amira tace kinje ko mumy Daman nacemiki giya take bashi Amma…” kafin ta karasa mumy tace dakata amira Arif d’ana ne, Kuma a duniyar Nan duk tsanar da Fatima zatayi masa bazata bashi giya ba domin tasan illar datake tattare da’ita, ” Amira tayi tsake Daman ai nasan za aruna! Ta fita…” Fatima duk tsorace tace mumy bani nabashi giya ba, ” nasani Fatima Amma ina neman wata alfarma agurinki please! ” Mumy ki fada ina jinki, ” Fatima please kiso Arif koda kadanne acikin zuciyarki, ” Fatima tace to mumy, azuciyar ta kuwa tace ai nadadi da son abuna, ” to ne natafi gida Idan ya farka kice yaje gida ina neman sa, mumy ki gaida gida…… Taliya Fatima ta dura Sannan ta gyara dakin Arif tana tsaye agurin dinning taje an rungumeta, ” juyawa tayi tana kallon sa harka tashi? ” kallon ta kawai yakeyi yakasa magana, ” iskar bakin ta ta hura masa? Yaya dakai fa nake, ” ohh ai naje maganar ne kamar amira kigayamun ba fatima ba, ” gashi kuma wacce baka tunani itace tagaya maka, zanfi jindadi kaje kayi sallar ka sai kazo kace abinci, ” kai har anyi isha’i? ” lah yanzu fa karfe goma,” subnlhi ne Kuwa wane irin bacci nakeyi? ” yawan magana banaka baniba kaje kayi sallah….. Shamsiyya tana kwance acikin bargo wane zazzabi takeyi dakyar take magana,” alhaji ne ya shigo dak’in sannu shamsiyya, ” hawaye takeyi…”ki daure kisha maganin ko kyaje kwarin jikin ki, ” hajiya tace abunda naketa fama kenan amma tak’i, iyayena nasan kunyi mun gata kunkuma nunamin so, Wanda Hakan ya jawomin girman kai, da rashin bin nagaba Dani, ” lallai na yarda *DUNIYA CE…* abunda kayi shi zaka gani nasaba muku Amma danAllah ku yafemun? ” alhaji yace na yafemiki, ” hajiya da hawaye ya ciko a i’Don ta tace nema haka amma kidaina zance kamar wacce zata mutu, ” hajiya nema zanso aci nagyara mugayen halina…….. A a mudassir yau k’aine agida na lah alhaji Kenan barka da asuba, barka k’adai, ” ya jikin shamsiyya? ” jiki dai babu dadi, ” Daman alhaji maganar shamsiyya cr ina sonta Kuma inason bikin Kar ya huce wata biyu, ” kai alhamdlhi amma naji dadi, bakomai ka kwantar da hankalin ka na baka shamsiyya halak malak, ” tohm anjima za’a kawo kudi, ” to madallah ” Bari na shiga gidan, hajiya ya samu a palour suka gaisa ya shiga cikin dak’in, sallama yayi sannan ya shigo, ” ahankali tace ina yini? ” sannu kinje lpy lou ya jikin, ” naji sauki, ” haka Dai kikace shamsiyya zaki aure ne? ” eh, ” murmushi yayi yace Bari natafi ana jirana a kanti, ” tohm kadawo lpya I love you…. Amira da take faman zirga zirga a palourn ta hankalin ta ytashi Kar agani ita tazu bawa arif giya, dumin duk wane sharri dazata yiwa fatima babu hanya saboda kowa yashaide halinta, tsake ta buga, daga bisane kuma ta tsinkaye muryar nusaiba, ” mutuniyar yana ganki atsaye? ” ai dole kiganne nusaiba, kishiya tafi karfe na, ” hmm wato ke bazaki nutsu ba kenan kullum ana gaya miki gaskiya amma kinke k’ije, wallahi kisane aduniya babu abunda yafe kwanciyar hankali dadi, Idan zaki zauna da kishiyar ki lapia to kinye wa kanki arzuki Idan kuwa kika tsaya rashin hankali da hauka to fa kullum kizake wulakanta domin kuwa *DUNIYA CE TAFI BAGARUWA IYA JIMA* Dan haka kisane kika rasa arif kinye babbar rashi domin samun kamarsa azamanin Nan Sai Allah tunda kinsan matsalarki ke ba tsafta ba ke ko girke bakya yimasa mazan zamanin Nan kuwa bazasu yarya da wannan ba, ” Amira jikinta duk yayi sanyi…. Fatina, ” Naam yaya, kisaka hijjabin ki zamuje gida, ” Yaya please kabari sai da gobe, ” shamsiyya ce babu lpya kishirya yanzu amera ta fito, ” kai Allah sarki hijjabin tasaka sannan ta fita tsayawa tayi tana jiran Arif, yana karaso wa, ya bude motar amira tace ke fatima kishiga baya domin wacce akafi so ce zata shiga gaba, ko kallon ta fatima batayi ba Arif kuwa Daria yayi..lokacin da suka isa gida fatima murna duk ta i’sheta hajiya sai maraba takeyi fatima ce ta gaidasu duk kanin su suka amsa cikin fara’a hakan yabata mamaki, ” dakin shamsiyyar ta shiga duk su kayi mata ya jiki shamsiyya ta kalle fatima tarike hannunta yar uwata cewar shamsiyya ” jikin fatima duk yayi sanyi.., ” Nasan nayi miki abubuwa kalakala arayuwa dan haka nake rokonki danAllah kiyafe mini, kuma danAllah idan naji sauki zanzo koyar abubuwa kinje? ” lah babu komai shamsiyya wallhi na yafemiki allah ya kara sauki suki..” ameen, ” duk suna palour suna ta hira fatima taje ta gaida baba mai gadi, tana tsaye jabir ya shigo, ” mutuniya ta, lah ya jabir, ” ai nayi fushi kullum wayarki a kashe, ” kai dai bari wallahi nayi missing naka, ” dubi yadda kikara girma, ferce ferce…” fatima ta saka dariya Au baka manta sunan nawa ba? ” haba ne ya za’ayi Na manta sunan tsokana ta, ” Arif da Amira suna kallon ta, ” to muje ka gaida Ya arif, rai abace arif yabare suka gaisa, ” tun amota yake zan bada Mata masifa wannan ai iskanci ne? Kin manta ke matar au ce, ” ita dai fatima shiru tayi har suka isa gida ko kallon su baiyiba, ” Amira kuwa murna ba’a cewa komai, ” saman sa ya hau yayi wanka ya kwanta, ” fatima tunda tayi wanka ta saka wasu sleeping drss but Riga da wando tafesa turare sannan ta hau sama tana shiga taga har ya kwanta ta Bayan sa ta rungume sa wane turare mai kanshi ya doki hancinsa, ” jiyowa yayi yana kallonta tana kallonsa har zai fara fada fatina bansan..” kafin ya karasa tafara kissing dinsa……… *Urs nana diso* *75-80* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Fatima tunda tayi wanka ta saka wasu sleeping drss but riga da wando ne, turare ta fesa, sannan ta hau Sama tana shiga ta ga arif Har ya kwanta, a hankali ta kwanta a bayan sa ta rungume sa, ” kamshin turaren ta ne ya dok’i hancin sa, a hankali yajiyo Yana kallon ta, Bude bakin da zaiyi yafara yi mata fada…” kafin ya karasa tafara kissing din sa, Nan da nan hankalin arif ya tashi, fatima kuma a hankali ta zare bak’in ta daga nashi, ” lokacin da arif ya bude idanu wansa sun chanja gaba daya, ” hakan yasa fatima ta Dan tsorata, tashi yayi chak ya fita yabar dak’in, ” hakan yasa fatima tashiga rudu ko daman arif ba sonta yakeyi ba yaudarar ta yakeyi, hakan yasa ta fashi da kuka har bacci ya dauke ta..” Arif kuwa yadda yaje hankalin sa yatashi alwala yayi yazo yafara gabatar da sallah, addua yakeyi Allah yasa fatima ta kauna ce shi fiye da dr…… Shamsiyya tana zaune a palour tana shan magungunan ta, cikin sanyin murya da girmama shamsiyya tace hajiya zanji gidan ya arif, ” yaushe zakije? ” tunani na gobe amma gwara na bare jikina yakara sauki, ” da hakan Dai zaifi, ” zanje gidan anty zee.., ” ki gaida ta, ” tana fita suka hadu da baba mai gadi ta gaida sa, ” cikin mamaki ya amsa, naji bakice a wanke motar ba, ” eh yanzu zan kaita wanke anjima, ” tohm Allah yakiyaye hanya, tana Isa gidan anty zee ta gaida ita ” anty zee tace yau kuma kice agida na ko abincin kikazo ci? ” anty zee ankawo kudina gobe za’a kawo lefe, ” hmm..” anty zee na chanja halina yanzu duk abunda kikasan inayi nadaina, kema abunda nayi miki kiyafe mun kinje? ” Amma naji dadi Allah yayi miki albarka… Karfe 8 Arif ya sak’ko, yau sauri yakeyi suna da meeting a offices” ita kuma fatima tana kitchen yau ta makara Sai sauri takeyi tagama breakfast gashi yanzu ta dura tea, bandaki tayi saurin fadawa cikin mintuna ta fito red din atampha ta saka sun kamata duk yawancin breast dinta awaje suke, kitchen din ta koma ta juye tea din, ” lokacin Arif ya lek’o, ” fatima tace yaya yanaga Har kashirya? ” eh bakigama breakfast din ba kenan Bari na tafi naci gurin Amira, Har ya fita tayi saurin shan gaban sa ne wallahi yaya banason abunda kakemun tanayi tana wane shagwaba ko kana tunanin tafi ne sonka? ” Kinga kibarne naji Chan kidaina batamin lokaci, ” idonta duk ya ciko da kwallah daman bakasona, dama tace kafi sonta, tafara tafiya, ” jiyaye takara masa gajiya, lallai idan Yana tare da fatima zai iya rasa hankalin sa, ” hannun ta ya rike ina zakije? Kinfi kowa sanin yadda nakeson ki domin soyayyarki ta daban ce, ” wane kallo tayi masa to muje kaci banson mijina ya zauna cikin yunwa, ” a’a da sharadi idan kinaso naci, Sai kinbani abaki kinje, ” wane k’ayataccen murmushi tace tohm muje, hada masa tayi tafara bashi gaba daya hankalin shi Yana Kan kirjinta, taga hannu yayi zai taba, ” tayi saurin cewa yaya maryam ta haihu jiya namiji, ” shiru yayi nadan lokaci yace Allah yaraya, ” yanaji kayi sanyi, ” Arif yayi murmushi jinayi daman ne aka haifarwa, ” fatima tace hmm..” fatima please k’ibani hakkina kinje? K’ar k’isa na shiga halak’a? ” when zak’i gama period? ” tausayin mijin ta taje a hank’ali tace gobe, ” key dinsa ya dauka yace sai na dawo, ” mik’ewa tayi a hank’ali ta sunbace sa, ” dariya yayi ya tafi, ” part din amira ya huce tana zaune tace sannun ka sai yanzu Kinga inada meeting Sai na dawo…. Yau sunan maryam fatima da wuri ta tafi, Dan gurin 12 ta isa gidan ko’ina ya cika da mutane haka suka dinga gaisawa, har sai data shiga cikin dak’i da sauri ta dauke d’an mashaa Allah kamarsu daya da baban sa, ” maryam tace ga mahmud nan mai kama dak’e, ” fatima tayi dariya ai yafi ne kyau aka saka dariya, ” kawayen maryam su kace saura ke maijego Allah yaraba lpya, ” fatima tace ko nifa banda komai kodaina jiran ma kayan suna, ” suka saka dariya, ” maryam ce ta kalle hauwa alamun tana cikin matsala, hauwa me yake damunki ne? Tun dazu bakya cewa komai, ” maryam matsalata karamace amma tana da hatsari mijina Yana sona, tunda mukaye aure yau wata 5 amma nak’i na yarda ya kusance ne? ” fatima jikinta duk ya mutu ji takeyi kamar daita ake, amma sai tayi shiru, ” nabeela tace gaskiya bakida hankali hauwa, ke wato bakisan illar hakan ba yanzu da yafara neman mata fa yaya zakiyi? Wallahi ki nutsu inba haka ba *DUNIYA CE*” yanzu yayi fushi dani baya kulani, ” maryam tace dama bai sakeki ba, da farko dai kidinga saka kaya masu kwashe hankali, kuma ki dinga kwanciya kusa dashi…” maryam ta tabo fatima yimata bayani..” fatima tace ai kin riga kinyi ta dai gyara halinta…. Maryam tace amma nabeela kin bani mamaki kin fasan yana daga cikin haqqin miji shine idan yayi miki umarni dole kiyi biyayya in dai bai sabawa Allah ba wannan dole ne wajibi ne, shiyasa iyayen mu tsofaffi idan zasu kaimu gidan miji suna cewa ‘to yi nayi bari nabari’ saboda hakkin daya ke kanki.. Bilkisu tace ku gaku da ilimin amma bakwa aiki dashi ko kin manta hadisin annabi (saw) da yake cewa ‘jin dadin duniya dan kadan ne amma wanda zai fi kowa jin dadin duniya shine wanda yasamu mace tagari ! sai sahabbai su kace ya mace tagari take? Sai annabi yace wacca iddan mijinta ya kalleta zaiyi farin ciki…” naji duka shawarar ku kuma nagode nasan nayi kuskure tun kafin nayi dana sani zan gyara kuma zan nime yafiyar sa, haka suka dinga hira fatima ta shirya sukayi sallama ta tawo… Tunda ta tawo a hanya taga Wane yaro Yana Bara kudi ta dauka ta bashi, ” yaron yace nagode Allah yasaka da alheri, ” fatima tace “ALLAH yana Taimakar Bawa, Matuqar Bawa yana Taimakon Dan Uwansa, ” yaron yayi dariya….. Tunda ta isa gida wanka tayi ta saka wane wando gajere sai vest sun kamata sosai, ta dura abunci, tana zaune a palour taga amira ta shigo ke fatima har yanzu baki gama abincin bani ba? Kinbe ki asirin ce min miji banza mai bin bokaye, ” kana ganin fuskar fatima babu alamun dariya Amira kike ko? Yanzu ne lokacin cin abincin ne? Kuma maganar bokaye da kikeyi Ubangiji madaukakin sarki yace: hakika Allah ba ya yafewa a tara wani da shi, shirka, amma yana yafe abinda ke koma bayan haka, ga Wanda yaso,” ( suratun Nisa’i ), yanzu idan nasan wannan shine zan dinga bin mushiru kai? Kuma Allah madaukakin yace: hakika Wanda ya tara wani da Allah, wajen bauta ubangiji ya haramta Aljanna gare shi, makomarsa ita wuta, Azzalumai basu da wasu mataimaka ( A ranar kiyama ) Suratul ma’ida, malama fitar mun daga dak’i, ” Amira tace munafuka zanyi maganin ki banza kawai… Arif yana dawowa ya zobe Akan kujera, fatima kuwa Bata lura dashi ba sai Kai kawo takeyi, kallonta kawai yakeyi ta saka wasu kaya masu rikirkitar dashi tun yana jurewa, tazo zata huce ya riko hannun ta ahankali ta dawo kusa dashi ta zauna, sannu da zuwa yaya, ” wannan wane irin kayane? ” ta turo baki nefa zafi nakeji, ” fatima look karki haukata ne please tunda kinke kibane hakki na dan Allah kidaina saka irin kayan nan kada na haukaci, ” uffan batace ba ta tashi tsayi rek’ota ya karayi, tana sani ta wada kansa, ahankali taji bak’in sa a hanata ga hannun sa da yake kokarin tab….. *Urs nana diso* http://nanadisoo.blogspot.com
*80-90* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Fatima ta zauna a k’usa dashi tace sannu da zuwa yaya, ” shigar da tayi duk tasa tunanin sa na kokarin guduwa, a hankali yace wane irin kayane kikasaka haka? ” turo bak’i tayi cikin shagwaba tace ne fa zafi nakeji! ” Fatima look karki haukata ne please! Tunda kinke ki bani hakkina please kidaina saka irin kayan nan kada kisa nazare, dubi lokaci guda na rikeci, ” uffan fatima batace ba ta tashi tsayi, rek’ota Arif yakarayi cikin sanyayyar murya yace ina zakije, ” fatims ta wada kansa, hakan yabashi damar jin kanshin turaren ta ga breast kamar ya wado,” bak’in sa taji a nata ga hannun sa Yana kokarin taba vest dinta, ” sauri tayi taja baya, ” fatina help me please karna zauce, ” haba yaya yau fa girken amira ne banson a shiga hakk’in ta, ” lallai na yarda bakyaso na amma ya sun kuyar da Kansa, ” Fatima tayi saurin chanja kayan jikinta ta tafi kitchen, Har tsawon lokacin Yana sunkuya da kansa, ” Bata kulasa ba Har ta gama ak’inta, tana shiga daki ya fita…. Lokacin da ta arif ya shiga bangarin amira, dak’i ya zarce amira tana zaune abak’in Gado yadda taga arif kwakwata ba halinsa bani ba, idon sa kuwa ya chanja kala gaba daya alwala taga yayi tace sannu da zuwa, ” kwanciya yayi ak’an gado sannan yace yauwa, ” Arif me ki damunka? ” kamar tasan bazai amsa mata ba, kaya ta chanja ta kwanta akusa dashi,” taji dadi sosai yadsa taga yana rububin ta, ahaka suka jidadin su…. Arif kuwa kawai Har yanzu k’ansa bai daina ciwo ba, ” yayi alwashin Bazai kara yiwa fatima magana ba har sai tafara son sa da k’anta, lokacin da ya shirya Amira ta miko masa tea yana gama sha suka tafi ya ajiye ta a gida ya huce office Amma tunanin fatima ya hanashi suk’une, lokacin da amira tatafi gida tatarar da dad agurin gate zai fita, dad ina yini? ” lpya dama inason ganinki duk da sauri nakeyi wallahi Amira kije tsoron Allah kiso mijinki da kishiyarki in bahaka ba kina tare da nadama, ” tohm dad nagode, tana shiga cikin gida ta tarar da mumy Sai kuka takeyi, ” lpya mumy kike kuka? ” amira wato nayi asara da na kasance ba uwa tagare ba nasa kina aikata abubuwa kala-kala nayi nadama na tuba babu abunda yafi tsoron Allah da gaskiya kisamu kishiyarki kinemi yafiyar ta, ” tohm mumy inshaa Allah…. Fatima har karfe 3 taji arif bai shigo ba, Hakan ya mutukar bata mamaki dan haka ta wayar daya bata ta k’unna kusan ta kirasa gurin sau uku Amma bai dauka ba! a na hudu ma rejecting din Kiran yayi, ” hakan yayi mugun bata mata rai, ” arif kuwa danna zuciyar sa kawai yakeyi dan bazai iya jurar ganin fatima tana kiransa ba kuma bai dauka ba, kashi wayar yayi, ” fatima ta fito part din Amira taje ta gani akulle hakan yasa tayi tunanin ko jikin arif ne yatashi, bakin gate taje ta samu baba Mai fadi, lafiya uwar dak’i na, ” uhm arif yafita ne baba? ” ai tun karfe 8 suka fita shida uwargida, dan lokacin ma sunata dariya, ” wane iri taje tayi hanyar ban garinta tana zuwa ta zauna Akan Kujera wane kuka tasake Mai cike da tausayi da kauna, wayar tace tafara ringing sallama tayi sannan ta dauka, ” shamsiyya ce tace sister wallahi baki kyauta ba ace biki saura sati daya amma baki zo kinga lefe ma? Haba fatima, ” kidai bari shamsiyya nasan nayi kuskure sosai amma kiyi hakuri gobe zanzo, yauwa munajiran ki ” tohm…. Tana idar da sallah taje sallamar goggo, da sauri ta tashi tana sannu da zuwa goggo, yauwa suka zauna, inayini goggo? ” lpylou fadima kinga yarinya kin fashe kin koma kamar mahaifiyar ki, ” hahha kiba nayi ko goggo? ” mashaa Allah Dai ga k’inan shar, ” Daman Abu biyu yasane zuwa nafarko na baki hakuri abisa son zuciyar da na nunamiki, ” haba goggo ai babu komai ya zama tahiri kidaina damun kanki, ” fadima bazaki gani baniba wato hakk’in maraya abune Mai nauyi sosai Dan haka nake kara baki hakuri, ” bari na kawo miki ruwa da lemo, ta zuba mata takawo mata sannu ko dai ciki ne daki? ” aa banida komai, ” fadima wata shida fa? ” shiru tayi ba takara magana ba, ” to fadima dan fadan da zanyi miki nasan anyimiki sai dai nakara Dan kad’an wato Asma’u bnt Kharijatul Furaziy take cewa ‘yarta ranar budar kanta cewa: “Yanzu fa kinfita daga sheqar da aka qyanqyashe ki zuwa shimfidar da baki santa ba, da abokin rayuwar da baki san shiba, ki zamar masa qasa sai yazamar miki sama, kizamar masa shimfida zai zama miki turaku, ki zamar masa baiwa, zai zama miki bawa… kar ki nace wajen neman abubuwa domin karya gujeki, kar kiyi nisa dashi domin karya manta dake, idan ya matso, ki kusance shi, Ki zama mai riko da addini a gidan mijinki kada ki zama mai kauracewa shimfidar mijinki, Ki zama mai hakuri da halayyar mijinki..” tohm goggo inshaa Allahu zanyi amfani da abunda kikace Kuma nagode Allah kara girma, ” Ameen ne bara natafi yauwa kisa Arif din yasiyo miki hanta Sai ki dafa da zogale Shima wane shirri ne na daban, ” rufe fuskarta tayi….. Shamsiyya tana zaune ita da mudassir sai hirar soyayyar su sukeyi, ” yauwa inaso in tambayi ke ko kinason dinner, ” opps gaskiya banaso yadda akeyi na sister haka za’ayi nawa, ” yanzu mai kuke bukata kudi da kaya? ” gobe fatima zatazo duk yadda mukayi da ita zamu fada maka, ” tohm shikenan bye bye…. Amira ce taketa zunduma sallama a palourn fatima, sai daga baya taji tafito, kiyi hakuri ina dak’i ne banji ba, ” bakomai..” yadda tayi maganar yabawa fatima mamaki, yanzu nake kokarin dora abincin, ” Amira tace yauwa Gara da baki fara ba, gwara mu dinga yi tare kinga nema na’iya, ” fatima tace ba matsala muje, ” haka suka fara girken Amira tana ganin yadda akeyi, gurin 1 hour suka gama shinkafa da miya, ” Amira tace please fatima ki koyamun pancake wallahi ina sonsa sosai, ” tohm da farko Dai zaki samu Fulawa gw2, sugar, madara gw1, kwai4, fulebo, mai bakar hoda bc1, gishiri kadan, Zaki hada fulawa da madara da kwai da sukari kisa Dan gishiri kadan kisa bakar foda da ruwa kiyi kwabin kamar ta wainar fulawa amma yafi na wainar fulawa kauri sai ki dura frying pan a kan wuta ki zuba kadan kuna soyawa, nagode…. Arif yana dawowa ya tarar da amira a palourn fatima suna ta hira yana shigowa wane murna yayi acikin ransa, ” sannan yayi sallama yana zama amira tace sannu da zuwa yauwa, ” fatima tace sannu da zuwa a hankali ya furta, ” suka tafi dinning duk sunata cin abinci fatima tana loma biyu tace yauwa please Yaya gobe zanje gida kaga biki ya kusa, ” amira tace to ai nema zanje, ” Arif baici musu komai ba, ” fatima ta tashi tace sai da safe ku….. Da safe arif ya kai su gida achan suka yini suna ta hirar biki Har yamma, ” shamsiyya ce tace please fatima yakike yin cake dinki, ” kinga mijina yazo daukata kibare in kinzo jibe mayi, ” okay…. Suna gama cin amince Amira tayi musu sallama arif kuwa sama ya hau wanka yayi ya hau son da yakeyi wa fatima yana furgeta shi, tunani kawai yakeyi, ” fatima kuwa tayi wanka ta shafa misk a pant dinta turare ya runtsata wasu kaya tasa shara shara baifi gwewarta, sama ta hau tana shiga tayi sallama, ” Arif yace lafiya? ” zama tayi kusa dashi, ya arif nasan nayi maka laifi amma k’asan cewa ina sonka kuma na mallaka maka ne, ” azabure arif ya tashi da gaske? ” rungumeta yayi yasa suka gabatar da sallah raka’a biyu, ” surar ta yayi sai kan gado gaba daya hankalin sa ya gushe tunda suka shiga bargo fatima take ta kukan shagwaba, ” gaba daya jikinsa rawa yakeyi yadda yafara sunbatar ta, ihu yadda yake sarrafata yakara sa cikin ta ya k’ada lokacin da zai gabatar da sunnar ihu tayi takara rikeshi, Nan ma arif yakara gigicewa tare da cigaba, suna kashe fitila nayi saurin guduwa don ne banason duhu, da asuba naga fatima ko magana batayi Arif kuwa daya ti sata agaba wanka yayi mata sannan ya bata magani, ” rungumeta yayi fatina, ” dakyar tace naam, ” yace nakar….. *Urs nana diso* http://nanadisoo.blogspot.com *90-95* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Fatima? Dakyar tace naam, ” sannan ya kalleta ciki da kauna da soyayya nakara ko sau biyu ne? Kafin ya Karasa maganar idon ta ya ciko da kuka, ” girgiza kansa yayi karki damu na hakura, kiyi baccin ki ki huta, ” Sai da ya tabbatar tayi bacci sannan yaji ya shirya ya tafi office, tun a office suke ta hira shida abdur kadir, abunda yake gaya masa yabasa tsoro, ” arif kana ganin magana ta tamkar karyace ko? Wallahi duniyar nan abunda akeyi kwata-kwata mutane basa kyauta wa rayuwa ta zama abunda ta zama gaba daya Son zuciya ke damun mutane, ka dube alhaji auwalu duk kudinsa Amma ka duba kaga yadda alhaji jameelu yake shan wahala bai damu da dan uwan sa ba rannan matar jameelu ta mutu dalilin babu kudin yimata aiki, Amma ne kullum ina gaya masa yayi hankali da rayuwar Dan *DUNIYA CE TAFI BAGARUWA IYA JIMA*” tabbas hakane abdur kadir yanzu ga kudi nan ka Kai masa ko zaiyi bukata, ” tohm arif nagode Allah yakara bude ne na tafi….. Lokacin da fatima ta tashi wanka takarayi jikin nata babu kwari sosai ahankali ta gyara gidan tana kokarin shiga kitchen Amira tace mata tatafi gidan cousin dinta, ” itama fatima taji kamar tatafi gida, sukayi sallama, tana gama girken ta, sallamar shamsiyya taje, tashi tayi ta tarota, Kai amaryar yaya kinga yadda kikaye kyau ga wata kiba da kikeyi, ” fatima tayi murmushi kinje ki ta tsokana to mashaa Allah, ” haha kinga dink’una na nak’arbo, ” kai amma sunyi kyau, ” ga nake Suma ya gama, ” fatima harda dankaramin tsallen ta kai amma sunyi kyau wanna cif cif zaimun ajikina, ” alhaji ne ya dinka mana, takalmi Kuma hajiya ce, ” amma mungode Allah yakara arzuki, ” sister kinsan yau me nagani, ” Sai kin fada? ” hmm wallahi wata mata nagani a asubuti tanata kuka mijinta ya gudu tun tana da ciki, ” Allah sarki ai hakuri zatayi, ” nema haka nace mata wallahi, rayuwar Nan in ka dogara da wane zakaga kwama chala, ” shamsiyya kenan mijinta ne abunda yayi Bai kyauta ba, yanzu wazai bata kayan jariri da sauran abubuwan, ” hakane, Allah ya karama na soyayya mu da mazajen mu, ” to amen, kinga anjima Mai kunshin zatazo ga abunci kizuba kice ne Bari nayi wanka, ” tohm, sai karfi 3 mai kunshin tazo shamsiyya tafara yiwa daga karshe akayiwa fatima, dakyar kunshin ta ya bushi tanata tsoron kada Arif yadawo bata dora girke ba, ” Mai kunshi tace ko masu mazajen ma, ” fatima tayi dariya Kuma Allah zai baku, shamsiyya Ana gama miki kiyi sallah, ” kai anty fatima shamsiyya za kicewa tayi sallah, *Duniya ce* fa dai dai take da kowa, wallahi babu abunda yakai ibada dadi babu ma ace tsayar da sallah, kunsan Allah da kullum cikin cuta nake amma tunda nafara azkar din safiya da yamma ga kuma idan zan kwanta, yanzu jikina Alhmdlhi, ” hakane, a daren shamsiyya ta tafi gida…… Amira bata dawo ba sai bayan magariba, hmm kinganne yanzu ko? Hira muka tsaya yi, ” fatima tace ai ga abinci nan ki zauna kici, ” tohm amma fatima wanene yake yimike dinki? Dubi yadda ki Kaye kyau, Kuma kikabar mai kunshin tatafi? ” mansur keyimin, gobe zatazo tayi miki fa, ” yauwa Bari naje nayi wanka kafin mijin namu yadawo, ” tohm sai kin dawo, bayan fitar amira, fatima tana ta danna waya taje sallamar arif da sauri tatashi sannu da zuwa yaya, kallon ta yayi wai menene sirrin kyau dakikeyi? Murmushi tayi Tace kaine sirrin ai, ta riko hannun sa, kayansa tafara cire masa taga duk yasake jiki,da wayo ta zame, Bari naji nadawo, ” a Kwai inda zakije da yahuce gurina mahimmaci? Zama tayi agefen gadon tace babu shi, rungumesa tayi a hankali tace yaya Arif ina sonka ina kuma kaunarka! ” Har cikin ransa sai da yaje magabar ta dagota yayi sannan ya sumbace bak’in ta, ” murmushi tayi sannan ta jashi ta kaishi toilet, tayi saurin fitowa a palour taga amira tana zaune, duk da taga amira ta dan bata rai amma ahaka ta kyale ta ta zauna, ” Arif ne yadawo ina ciki shiyasa banji motsenki ba, ” amira tace yayi kyau haka shiyasa kika barne a zaune “fatima tayi dariya to kinje inda akace in miji yadawo akula dashi? ” amira tadan dara tace wato ki biyayya? ” amira kenan Biyayya ga miji ba mai iyawa sai mace ta tagari, kuma ina fata muna ciki, da yawa mata suna so ace sune wadanda Annabi (S.A.W) ya sifanta dinnan da (Nagari) sai dai biyayyar itace tayi qaranci, ko za ayi saidai a gabansa, idan ya matsa an watsar, Wallahi na taso naji ada iyayenmu mata magabata suna kwatantawa, kuma nema zanyi kokarin kwatan tawa, ” hakan yayi kyau bari naje na kwanta sai gobe ki tambayar mana shi kwana, ” tohm…. Da safe suna karya wa, fatima tace yaya ” yes sweetie na ya akayi? ” dan Allah kabarmu mu kwana ran lahadi sai mudawo please, ” ban amince ku kwana ba, ” haba yaya bikin shamsiyya fa? To ita amira ta dawo ne sai na kwana, ” umarni na baki ba shawara nace kibane ba, kuma sai hudu zaku shirya na kaiku, ” gefe fatima tayi tace to shikenan, ” Amira ma dataje abunda Arif yace bataji dadi ba, karfe hudu ta saka les dinta yayi mata kyau sosai, jakar ta ta dak’ko da wane mayafin ta mai shara shara, ” tana fita palour taga arif kallon ta yayi tunda Sama Har kasa nan jikinsa yaje Yana yar, yar, ” yaya mun shirya fa ” ina zakije? “Bikin mana ko har kamanta, ” ai nazata kayan jikinki ni kadai ya halatta kisawa, ” kyau sukaye maka ne? ” ga dukkan namiji zaiso yaga matarsa da shigar nan dan haka kichanja su yanzun nan, ” na chanja fa kace? Chan kuma ta chanja abisa bataso ba, duk da hakan tayi kyau amira tayi kyau suna zuwa kowa yacika amarya sai hotona takeyi, shiga sukayi suka gaida hajiya, hajiya tace sannu da zuwa mai ciki, ” dariya fatima tayi tace dan Allah hajiya kisa yabarne na kwana, ” nagaya masa yake, ” ran fatima duk abace tarasa yadda zatayi…. Gurin 8 ango yazo sukayi hotuna, ” Amira tun bakwai ta koma dan arif yayi mata kashide, gurin 10 Anata hira wayar ta ta dinga ringim sai ta kashi, ” kawayen amarya sai hira akeyi, fa fatima hartasa doguwar rigar bacci hajiya ta shigo tace taje inji alhaji, ” hijjabin shamsiyya ta saka tatafi tana shiga ya rufeta da fada mijin nake Bai barki ba kika tawo to gashinan ba shida lpya kije ki kula dashi ga usman Chan yakaike, ” jiki duk babu kware ahaka ta shiga Mota, ” tana shiga part dinta Sama ta hau arif tagane kwance hijjabin ta tacire ta kwanta a kirjen sa lpya yaya? ” a hankali ya bude idanun sa da suka k’ada yace yaushe zaki sone? Kinsan ina bugatarki sosai, kafin takarasa magana taje hannunsa a rigarta nan ya fita hayyacin sa, addua yafarayi daganan ya fara rabata da rigarta,” duk sunbatun da Arif yakeyi fatima taji wane dadi kamar zata sume…. http://nanadisoo.blogspot.com *95-97* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Duk sun batun da Arif yakeyi fatima taji wane dadi kamar zata sume, Nan hankalin su duk ya gushe..da asuba kowanne su yayi wanka sukayi sallah, ” Fatima tanayin littafin ta na azkar Arif yajiyo ya kalle ta, cikin murya Mai sanyi yace fatina kice farin cika my heart long for respect and adoration to flow to you as I gently catch ur glimpse, with all the love of my tender heart, ” murmushi fatima tayi ta cigaba da addu’ar ta, Arif gado ya koma ya cigaba da bacci fatima datake sauri gurin gyaran gida, tahada breakfast wanka ta shiga tana fitowa ta saka shaddar ta tayi mata kyau sosai sai 7 arif yafarka yana tashi wanka yayi yashirya don karfe 9 zaa daura auren, ” fatima tana kan kujera azaune Akan kujera tana danna waya, kamshin turaren arif taje, dagowa tayi tace Har ka tashi yaya, ” yeah natashi Kar na makara ne, tohm katashi muje kayi breakfast, ” okay ta zuba mai, yana gama ce yace to ne zan fita, wannan shaddar tayi miki kyau sosai, ” nagode yaya mutafi yanzu please sunata jira na, ” kallonta yayi cike da isa, ina zakije ? ” dariya tayi tace kataso mutafi mana, ” Amira ce tayi sallama ta shigo inata jiranku Baku fito ba, ” arif yace fatima babu inda zakije kije kigyara mun kayana, anjima zan aiko da nama sai ke dafa mana, ” batasan lokacin da tafara kuka ba, yanzu ya arif bazanje gida ba bikin fa dan’uwa na akeyi wanda babu kamarsa, ” ransa abace yace ban aminci kije bani amira taje abak’acin ki, ” kuka takara fashe wa dashi tare da fadin dama nasan zaayi haka, daman baka sona, ” rike hannun Amira yayi suka fita, ” fatima tace *DUNIYA CE…* kayimun duk abunda kaga dama ” Amira tace amma yaya gaskiya..” kafin takarasa maganar yace kema zaki zauna fa, ” hakuri tabashi suka tafi….. Fatima takasa sukune mayafin ta ta dauka da jaka Har tafita ta tuna tsinewar da mala’iku zasu yi mata, saboda tafita bada izinin mijinta ba, koma wa tayi ta zauna tarasa me yakeyi mata dadi, wayanta ta dauka takira shamsiya tayi saa bugu daya ta dauka, ” fatima kidaina kuka tun jiya yariga ya gaya kowa bazaki zoba, kiyi hakuri please karkiyi fushi dashi? ” amma kinsan Bai kyauta ba ya za’ayi..” ki daiyi hakuri kinje, ” tohm takashe wayar da kuka.. Gidan biki ancika sai sha’ani akeyi kowa yana ta murna babu kamar hajiya, shamsiyya kowa duk ta kideme tana mamakin Wai yau ita zatayi aure, Allah mai iko, dariya tayi sannan ta shiga wanka…. sai da tayi sallar la’asar sannan ta hau sama ta gyara masa kayan sa da aka kawo daga guga, nama tagyara taje ta dafa tagama abincin wanka tayi sannan ta zauna tana lazimi sai karfe goma suka shigo suna ta dariya..” ko kallon su batayi ba, sunacin abinci amira tace amarya mun dawo fa, ” wane irin kallo tayi sannan tace sannun ku, tana jinsu suna hira bata kulasu ba, ” Arif ne ya matso kusa da kunnen ta ne Baza ayimun sannu da zuwa ba ko? ” kallon sa tayi ta tashi tabar dak’in Har zai bita Amira tace girke nane fa, ” ribos yayi ya bita…. Karfe 11 ango ya shigo shida abokanan sa, murna gurin mudassir bata misiltuwa, abokan sa sukayi addu’a suka tafi, ” yana dawowa yace su tashi suyi sallah ahaka sukayi sallama ya dora hannun sa akanta yayi addua daga nan Kuma aka fara angwance wa wa, da asuba yayi mata wanka su kayi sallah.. Arif bai shigo dak’in fatima ba Sai sha biyu na rana, tana zaune tana kallo ya shigo, ” ahankali ta gaida shi, ” ya amsa mata yana dariyar mugunta, kinga ban fito ba sai yanzu ko ina can Ana nunamin soyayya, ” uffan batace masa ba, ” yauwa kishirya kije gidan mukhtar matarsa ba lpya, ” ai bansan unguwar ba? ” dakko hijjabin ki zan kaiki, ” fita su kayi yanata janta da hira tayi masa shiru gashinan kishiga anjima zanzo na dauke ki, ” Bana jin dadi idan bakazo da hure ba zan koma da kaina, ” yace to, zata fita ya rike hannun ta au haka zaki tafi ba kiss ba hug, ” hanunta ta fizga tayi ficewarta tana shiga tayi sallama nan ta Tarar da ita apalour haka suka gaisa tayi mata yajiki sannan tafito….. A hankali take tafiya wane jire jire takeji ta rasa yadda zatayi, gashi babu abin Hawa , mota ta gani ta tsaya lekowa akayi fatima taji muryar uncle taje dagowa tayi aa uncle inayini ? Lpylou amarya ya angon nake naganki kina tafiya ke daya lpya? ” walhi gida zani Kuma babu mota, ” okay tawo muje na kaiki tohm, ” arif ya shigo da mota kenan ya ganta ta zata shiga, wane tsake yaja yabisu abaya yana ajiyeta tayi masa godiya, ta shiga gida tana zuwa part dinta tashiga tazauna Akan kujera sai hak’e takeyi Arif ya shigo Wai mai kika mai dani ne? Motar wanne dan iskar kika shiga? kwata kwata bakisan hakkin aure ba, ko Dan kinga inasonki, ” daga idunta tayi da yayi jajir wallahi yaya.. ” kafin yakarasa yace dakata bason Jin komai a bakin ki, kuka tafarayi ya fita yabar dakin…… Da safe fatima ta dinga jiran arif ya shigo Amma bai shigo tagama abinci sai ga Amira ta shigo haka suka dinga hira Amira aka kira tana dauka taje bilki ce, bari naje nadawo fatima, ” tohm.. Wai kina ina Amira tun dazu inata jiranki Wai kina bangaren kishiyar ki..” eh ina chan mu shiga to yagida? ” lpylou, ” gaskiya baki da hankali kishiyar kika mayar yar uwa wallahi kina cikin wahala, ” haba bilki zancen me kikeyi? ” to ki zauna miji yafe son ta kawo kunnen ki kije ” tohm ahaka suka karasa hirar su tayi sallama tatafi…. Arif yana dawowa Amira tasha kuka ta rungumeshi sweetie yau kaga cin mutuncin da fatima tayimana ko abinci hanamu tayi baba mai gadi ma yana ta meta, ” fatima ci tayi miki haka? ” eh ” part dinta ya huce yana shiga yaganta atsayi wanka mata mari yayi ne zaki matar mara mutunci wato abincin ma bazaki bawa su Amira ba ke kika kawo, ” wallahi yaya karyane nagama abinci tun tazu, iyimun shiru wannan shine na karshe, ” tohm Allah yana tare dani kuma *DUNIYA CE…* Tun daga ranar fatima bata da lpya zazzabe ga jire, ga tashin zuciya jiya da arif ya shigo baiganta ba, yau dakinta ya shiga yaganta akwance fatina what wrong yana taba jikinta yaji zafi, ” haba fatina mai isa baki kirane ba, kiyi hakuri raina ne ya baci” hucin kuka yaje ya rungumeta yayi daga nan ya dauketa sai…. http://nanadisoo.blogspot.com *97-98* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Daga nan Arif ya dauketa Sai asubuti, suna zuwa suka ga likita yace sai anyi mata test dawa su aune aune, ” Arif yace babu matsala bari naje nadawo kafin nan angama, fatina me kikeso nasiyo Miki? ” murmushin takaice tayi sannan tace babu komai ” Arif tunda ya fita hankalin sa yake kwanciya wane sabon son Fatima ne ke kamasa Amma duk abunda yakeyi mata yanaso ya nuna mata darajar shi, ” likita da ya kalli Fatima madam sannu Abunda nake zargi shiya tabbata, ” Fatima ta zaro ido da alamun tsoro! ” cool down am hppy for you, cuz abunda mijinki ke bukata a yanzu, kina da ciki, ” murmushi tayi sannan tace please doctor kayimun promise bazaka gayawa Arif ba, ” why?? Ai idan bangaya masa ba nace amanar sa saboda babu abunda yakeso sai ‘ya’ya, ” actually doctor ba wai ina nufin aboye masa ba, i mean ni zanyi masa albishir, ” ohh I understand stand! That’s good ai here zan rubuta miki magunguna sai asiya ki dinga sha, Kuma ki yawaita shan fruit sosai da su hanta and co..” Arif ya shigo doctor I hope my wife is wll, ” yeah she’s okay, ” Arif ya rike hannun ta suka tafi a hanya suka siya magani, suna koma wa gida tayi wanka ta ci abinci sannan ta tasha magani, ” Arif yazo Kan kujerar ta ya rungume ta Fatina ina sonki, ” tana jinsa Amma tayi luf ajikinsa..” hannun sa yafara turawa cikin rigarta..” aguje ta tashi tatafi toilet, ” Arif kuwa daya bita abaya ransa Har ya bace yazata ko bataso ya tabata, tarar da’ita tare k’i ciki tanata Amai riketa yayi tagama ya wanke mata baki rigarta duk ta jike zai cire mata kuma sai ya fasa saboda yanzu hankalin sa zai tashi gashi kuma jikin ta kamar wuta, ” gado ta wada ” Arif yace mai kikeso nasiyo miki, ” a hankali tace k’antu, ” da mamaki Arif yace kantu sai kace wata mai ciki, ” Amma bari na cewa ummi tatawo miki dashi….. Amira da ta rasa me yake mata dadi sai zirga zirga takeyi a tsakar daki, ” tunda taga arif ya fita da Fatima hankalin ta ya tashi atake ta kira bilkisu awaya ke dafa matsala wallahi, ” me Kuma yafaru? ” arif Naga Ya dauke Fatima,..” dallah banza yimun shiru daman Bana gaya miki ba to kina zaune sai kije ciki ne da’ita, ” la kuma hakane fa innalillahi, ” karki damu ta kintsa mata abubuwa sannan sukayi sallama, Amira ta chanja kaya ta saka riga da siket, ” Arif ne ya shigo lafiya amira ga Fatima can ba lafiya shiyasa tun safe ban zauna ba, ” uhm nima dama inason ingaya maka ciki ne dani, ” arif cikin murna ya dauke ta, sweetie are you serious? ” yes mana daukan ta yayi cak cikin daki kissing dinta yakeyi ko ta’ina nan fa suka siga shafin soyayya, ” amira taje dadin hakan sosai cuz tasan Fatima zataje haushe sosai, tunda girkin ta ne…… Lokacin da hajiya ta tazo amira tagane ita kadai ce a zaune tana kokarin tashi ” hajiya tace zauna na karaso yar albarka, ” tohm, ” sannu kinje Allah yasawake ina Arif din yake? ” yana part din amira in banda sha shanci banda ya zauna ya kula dake, ” ai bai dadi da fita ba, ” ga zogale nan bare na dafa miki kyaje kwarin jikin ki, tohm cikin a wanne tagyara dak’in ta zuba mata, fatima Dai taje dadin zogale Dan tas ta cinye shi, Sai bayan isha’i Arif ya shigo amira tana ganinsa duk idon sa yayi ja, ” hajiya tace anya arif matar taka batada lafiya tun dazu kana gurin Amira, ” hajiya ai dole amira ciki ne da’ita fa, dan haka dole na kula da’ita ko ran girken wanene, ” fatima dai batace komai ba, in banda kirjenta ” hajiya tace muje karaka ne, fatima Sai munyi waya, ” tohm nagode…… Arif yana dawowa yatarar fatima tasaka kayan bacci rungume take ya rungume ta ya kaimata sun bata abaki, ” am very happy dear nema na kusa samun baby ina ta yaka murna yaya, bacci ne ya kwashe ta, Arif kuwa wayarsa ya dakko yakira amira suka dinga waya…. Shamsiyya tana zuwa ta rungume fatima sister ya jikinki? ” naji sauke, to mashaa Allah ga hantar nan nadafo miki, ” yauwa sannun ki, ” gakiya fatima ina bukatar kiyimun lecture please, ” hmm to abubuwan dazan gayamiki baifi one to three ba… Yauwa sister inajin ki kinsan mijina yana son kulawa ” Ai matakan tsaro ya kamata ki sawa mijinki idan ki k’a lura safiya tayi sai ki saka kayan daukar hankali yadda ko yarinyar tazo bazata sak’i ba, ballanta na tayi tunanin bakya kula da mijinki, ” hakane sister ” lokacin zafi ki dinga saka gajiran wando da Vest, da dai kayan daukar hankali in ba haka ba kuna zaune za kuga yafara waya, Dan in sun fita Sai sunga masu saka riketaccen kaya, ” hakane Kam batima dan yanzu din k’unan sai ahankali, ” ashi kin gane, in bahaka ba yadawo gida yatarar daki da atamba dinkin buhu ta yaya bazai yi ma’amala da mataba Kuma in yayi kuji haushi kunji matsalar ko,In zafi yazo kije a wanki miki kanki arangada miki kitson ki Kiyi Jan kunshi da baki In baki da kudin siyar y’an kanana kaya jike gwanjo kisiyo dazarar yana gida saka kidinga barar da galan din da Allah yabaki, ” hahaha amaryar yaya arif kina bala’i fa, ” aa bala’in lafiya ai gaskiya ce…. Ai wallahi shamsiyya ki dinga aske karkice zakiyi dabi’arki ta gida dan k’o ni alokacin na matso naji wari wallahi naji babu dadi, ” ai fatima da kenan, ” to dai ki dinga Saka turare in ba haka ba Kina gani zai fita wata ta gifta turaren ta ya rikir ki tashi… Kuma kisane Rashin aske gashin gaba shi ke jawo dattin pant yana jawo infection da sauran su, ko agurin yar uwarki mace bakyaso taje zanin ki taji wari ballanta na mijinki, kina matsowa yazata mosheni, ” hahaha aikuwa zan kiyaye,” yauwa in bahaka ba kishiya tana haya in baki gyara ba miji ya bude Mata tashigo aguje, ” hahaha Gaskiya ne sister dan ban manta malamar mu ba lokacin da take cewa *DA KAZAMAR MACE GWANDA KWA-NA DA YUNWA!* *WATA KO ZANI BATA IYA DAURA-WABA,BALLAN TA NA KWALLIYA*…. Kuma shamsiyya mace ta gama al’ada, tana gama wa ta sami auduga tasa turaren miski tasa a al’aurarta zuwa wani dan lokaci ta cire tayi wanka.. Rashin yin wanka da wuri yana haddasa wa mace rashin gamsar da Maigidanta Dole ne mace ta kula da tsaftar tufafinta da na ‘ya’yanta da na Maigidanta, ki sani cewa yawan kayan sawa wata baiwa ce daga Allah, amma tsafta da wanki da guga da fesa turare idan ana gida shi ake nufi da tsafta, da wannan ne mace zata amsa sunanta na mace… Apple matsayinta a jikin ki zai kara miki ni’ima a jiki har ka sauki kuma jikinki ya ringa laushi yana kyau ba kamar wasu matan ba inka taba jikinsu ka ji tauri..” hakane sister ” ” kuma Ana so mace ta kula da gabanta domin Allah ya sa namiji ya kwallafa ransa gare shi, Barinsa ya lalace kamar zubar da kimarki ne a wajen sa kada ki bar shi ya yi wari, kada ki bar shi ya yi fadi..” godiya nakeyi yar uwa Allah ya bar zumunci muje na tayaki girke kafin yazo, haka suka shiga kitchen suna ta girke har ya mudassir yazo suka gaisa suka dan taba hira sannan suka tafi…. Fatima ta kasa zama yau Arif bai shigo dakin ta ba kuma tasan girke tane, yana shigo wa ta tareshi yaya Arif me nayi maka please kwata kwata baka bani kulawa, ” hmm haba fatina kinsan me ciki sai da kula wa dan haka kidaina damun kanki, ” murmushin ta kaice tayi… Kusan watan ne 5 kenan cikin fatima sai girma yakeyi Amma Arif rabon shi da’ita tun lokacin da amira tace zata bugar mata ciki, ” a lokacin ya dauke Amira suka je abuja, yau Friday suna kan hanyar su ta dawowa Amira tana ta kuka wai cikin ta kwantacce ne, ” sai lallaba ta yakeyi direct asubuti suka isa, ” baban unborn kaddai matar ce ba lafiya but jiya tazo awo, ” no doctor amira ce cikin ta baya girma fa? ” which amira wannan madam kake nufi? ” amira duk ta gigece, ” ai wannan matar taka mahaifarta a daure take, since last 2year tasaka doctor john, ” what?? Amira dama yaudara ta kikeyi, ” cool down Arif mana Fatima ta kusa haihuwa baifi 4 mouth ba, ” tsake yayi ya fita, ” Amira ta bishi, wata tsawa yadaka mata sannan yace kije na saki ke sak’i daya, ” wayoo Allah na Arif please katsaya wallhi sharrin shaidan ne….. Motarsa yaja ya nufi gida baba mai gadi shikansa yayi mamaki, Yana shiga yaga gidan babu kowa ko’ina a kulle yake, ” da sauri ya fito ya tambayi baba mai gadi ina fatima, baba yace ai watanne 4 kenan tana gidan ummi, ” motar sa yaja Sai gidansu yana zuwa yatarar da ummi da dady azaune, dur kusa wa yayi yagaida su, ” ummi please kuyafe mun wallhi duk acikin son ‘ya’ya ne, kuma da makircin amira, ” oh haba?? Cewar mumy, ” fatima ce tafito zata bawa mumy waya tasaka riga da siket cikinta yafito gwanin sha’awa, ” rike hannun ta, ” fizgewa tayi ta nufi Sama, ” zai bita dady yace karkasaki ka……. Urs nna http://nanadisoo.blogspot.com
*98-100* DUNIYA CE *NA NANA DISO* Rik’e hannun ta arif yayi ..” fizgewa tayi ta nufi sama zuciyar ta cik’e da bak’in ciki da k’una..” Arif ne yak’e k’okarin binta..” dady ransa a bace yace karkasaki ka hau mun sama, “Arif yadawo da baya please dady kuyi hakuri matata tana bukatar kulawa daga gareni, ” dady yace ai naga kai har yanzu bakayi hankali ba kuma lokacin da k’uk’a gudu kai da daya matar taka, kai kak’e kula da Fatima?? Banson zancen banza dana wofi fa, baza ka mai damu sha sha sha ba, ” dady please kayi hakuri wallahi sharrin macce ne Dan Allah please dady wallahi zan iya rasa raina in kuka hanani fatima, ” ummi tace kaga wannan ‘yar marainiya ce ba uwa ba uba amma kwata kwata bakaji tausayin ta ba to kaji *DUNIYA CE TAFI BAGARUWA IYA JIMA* ” haba ummi karki hadani da duniya danAllah kuyafemun, ” tashi kabar min gida stupid wanda baisan mutuncin mu ba… Fatima tunda tahau Sama dak’i tafada tanata kuka, tana son mijinta Amma abunda yayi mata bazata iya yafewa ba itama mace ce Kuma sai ta nunamai kuskuren sa, cikinta ta shafa tana kuka baby cikina baban ku yana sonku… Arif Yana fita awaje ya zauna yayi tagumi ..” farouk ne ya janyi hannun broz lafiya naganka anan, ” farouk su dady sunk’e su yadda dani wallahi inason fatima, ” haba Arif kaima dai kasan kayi kuskure yaza’ayi kayafe kabarta bako sallama kuma kasan tana da ciki? ” wallahi bansan tana da komai ba! Boye mun tayi Amma ne bansaniba, Kuma su dady sunfi kowa sanin yadda nakeson haihuwa dan haka Amira dashi ta yaudari ne, ” ita ina amiran? ” Na sake ta..” haba Arif sake fa? ” shi yafe chan chanta da’ita, ” to yanzu katafi gida zanje nasamu ummi Sai tabawa dady hakuri, ” yauwa to nagode…. Assalamu alaikum! ” wa’alaiku mus salam, ” ummi barka da hutawa, ” barka lafiya dai naga yanayin ka wane iri, ” ummi dole na damu kun hana dan uwa na matarsa, wallahi ummi yana sonta sharrin mace ne, ” farouk Kenan ni kaina nasan da hakan Amma Sai yagane k’uran sa tukunna, ” ummi kinsan bashida lafiya fa, ” wannan da muwarsa….. Mara mutunci ke a mata ma banga da k’ikeya irin ki ba kwata kwata baki da hankali, yanzu kin kaso aure kinje dadi, ” mumy sharrin shaidan ne? ” dallah yimun shiru karyar kina da ciki ko to kibare babanki yadawo yau zakiyi bayani, ” Dan Allah mumy kiyi hakuri ….. Darling…” yes so nake na biya muku aikin hajji ke da fatima, ” anya yaya Arif zai yarda, ” hmm ai kinga tana gidan ummi bata gidan ta, ” kasan ummi da son jikoki bata son taga Fatima ita kadai shiyasa, ” mudassir Sai yaje dadi ya rungume shamsiyya kema kinkusa ki haifa mana ko? ” cikin kirjen sa ta shiga ciki da kunya Nan kuma salo ya chanja…. To tunda kin kashe auren ki to sai kifara wank’au agidan nan Ana biyan ki kina siyan abincin dazaki ce, ” dady kayiwa Allah kayi hakuri? ” bana magana biyu dayar nan itace karbabbe ya…” mumy please kisa baki, ” tsake tayi tabar dak’in.. Fatima tana zaune a palour tana k’allo ” Arif kuwa ya dadi da shigowa kallon ta kawai yakeyi a hankali yakaraso kusa da’ita tana ganin sa tafara kokarin mikewa, ” Sai data tashi hankalin sa ya koma kan kayanta yadda suk’a kamata, Fatima, ” ko kallon sa batayi ba tace amira zakace ba fatima ba tunda itace matarka, ta hau sama..” Sai daya bari ta dadi da hawa sannan ya bita, dakin ya bude tana kwance tana hawaye Fatima yazakiyi mun haka kinsan inasonki ya zanyi da sonki to? ” cikin kuka tace yadda ka yaudari ne na fara sonka haka zaka cire sona da kaunata, ” rike hannun ta yayi bazan iya ba, ” kaga malam fitar mun adaki, ” Babu inda zane, ” mikewa tafarayi yayi saurin rungume ta ya saka bakinsa anata tanata kokarin kwace wa amma ina yafi karfin ta, yadda taga ya sa k’ank’anci ta tureshi tayi saurin bude kofa, ” kasa tashi yayi gaba daya wata narkakkeyar kasala tabi jikinsa, Chan Kuma ya mike yace dole abani mata ta, Yana sauka yaga dady azaune tsugun na wa yayi yace ina yini dady, ” karka kara shigo min gida fita, ” kayi hakuri dady, ” fita a hankali ya fita….. Amira da take ta wanke, duk tayi baki ta rame..” mumy ce tafito, in kinga ma ki dura abince mumy ku taimakan kuyafe mun nayi nadama dan Allah, ” daman nagaya miki idan bakiyi a hankali ba *Duniya ce..* maganin ki zatayi sosai wallahi, ” kuka ta saka mai cik’e da tausayi….. Yau satin Arif daya baya shiga gidan su, idanun sa sunyi luhu luhu saboda kuka, ga zazzabi, ga zuciya datake suka, ” yana koma wa gida, ya zauna Akan dadduma baba mai gadi sai tausayin sa yakeyi, mintuna baifi 10 ba sai yafara tare nan da nan jini yafara fita, baba mai gadi aguje ya tafi gidan ummi, ” lafiya cewar farouk ga Arif chan yanata taren jini, ” what aguje suka fita ummi batasan lokacin data ja hijja binta ba suk’a tafi gidan sa, kafin suje yana kwance duk jini ya bata sa, ” Mota suka saka shi, gudu farouk yakeyi sai da suka i’sa asubutin emergency aka shiga dashi, ” nan ummi takira waya ta gayawa dady yace kundai kaishe asubuti gani nan, ” farouk yace kunga irinta ko? ” innalillahi cewar ummi ai ne nazata abun Bai kai haka ba, ” doctor John ya fito, ” ya mutu ko cewar ummi? ” no Bai mutu ba amma d’anku yana cikin mugun hali zamuyi masa aiki zuwa anjima akwai inda zuciyar sa jini yataru sai mun kwashe, so you need to be careful, ” tohm doctor Allah yasawake bari naje gida…. Tunda ummi taje gida takasa zama, dady yana zuwa yace ki kwantar da hankalin ki anyi aikin, sai dai mujira zuwa gobe muga yadda jikin nasa zaiyi, ” fatima dataje kuka tasaka dan tasan itace sanadi, ” ummi da taketa sallah kasa bacci tayi, ” fatima na sai addua takeyi… Arif tunda ya farfado sunan fatima kawai yake fada..” farouk yace ka kwantar da hankalin ka zatazo, “ummi tana zuwa tace Arif kadaina saka tunani please Kar murasaka, ” ummi fatima, ” jikin ummi yayi sororo saboda dady yace Kar fatima tazo, tun daga lokacin ya koma bacci… Ummi da farouk sun dawo gida, ” tace dady zanje awo, tohm shikenan sai kin dawo, tunda fatima ta hau titi bata tsaya a ko’ina ba sai asubuti, tana tambayar dak’in Sa ta wada kuka tafarayi a halin da ta ganshi rungume sa tayi yaya katashi please bakin ta tasaka anasa a hankali ya bude idonsa, fatima a hankali ya fada, dagowa yayi tana kallon sa, kinsan cewa Kece madubi abar duba wata duk safiya, kin zamo min tamkar fetur a mota, rayuwat ba ke lami ce ya rabin raina, Amma Mai isa bakya nunamin kulawa? Kunne ya kurmance saboda rashin jin kallamen quanar ki kullum, baki ya daina magana dai dai saboda rashin begen zumar rayuwata kullum, ” mijina ina Sonka ina kuma kaunar ka, zan kuma zauna dakai, kayarda da hakan mijina, ” na yarda, ” to bari naji na dafa maka abinci, ” fatima ki zauna ki kula dani please, ” tohm bari naji nadawo motarta taja ciki da farin ciki da son kasancewa da mijinta….. Amira da safe ta yanke shawarar taje tabasu hakuri, ” tace mumy natafi kai wanke tohm sai kin dawo, tunda tahau mota ba a ajiye ta a ko’ina ba sai kofar gidan ummi sallama sukayi fatima da dady da ummi duk suna zaune, ” har kasa tagaida su ummi tace lpylou, ” daman nazo neman yafiyar ku abisa abunda nayi danAllah fatima kiye hakuri, ” hmm ai ne dama ban kullace ki ba, amma dai inaso kisane Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma Allah Yana shaida lallaimunafukan hakika, makaryata ne” (k: 63: 1) da kuma fadinSa “A cikin zukatansu akwai wata cuta; sai Allah Ya kara musu wata cuta, kuma suna da azaba mai radadi saboda abin da suka kasance suna yi na karya (k: 2:10) Kuma karki manta fadin Abdullahi bn Amir (RA) ya ruwaito cewa mahaifiyarsa ta kira shi tana cewa zo ka karba,sai Manzon Allah (SAW) ya ji ta, ya ce mata: “Me za ki ba shi? Sai ta ce “Zan ba shi dabino ne.” Sai Annabi (SAW) ya ce, “Da ba ki ba shi komai ba, da an rubuta miki zunubin karya” Abu Dawud da Baihaki suka ruwaito…. Nagode fatima Amma dady kayafewa Arif danAllah,tayi sallama tatafi, dady ya kalle fatima kina son Arif tayi murmushi tabar gurin, ” yayi dariya yace ja’ira tashirya gobe takoma gidan ta, ” ummi tace yauwa alhaji…. Tunda aka sallamo Arif suka tawo hanya, yaga farouk ya kaishe gida, ” malam kakaine gurin mata ta, “farouk yayi dariya kamanta dady yace Kar akara barinka ka shiga, ” oh hakane fa namanta anjima zanji na bashi hakuri, Yana shiga yaga gidan a Bude wa zai gani in banda fatima karasowa tayi ta rungumesa, ” dadin dayakeji baya misal tuwa Nan ta huce dashi daki yayi wanka daga nan salo ya chanja suka wada sunnah… Yau fatima tashi tayi da wane azababbin ciwon ciki zamzam ta dinga sha, ” Arif Yana zuwa akace yah dauketa Sai asubuti, ta shiga labour sai addua takeyi wane salati da tayi sai ga baby ya fito Yana inya inya inya, ” nurse tafito aguje tace congrats matarka ta haihu namiji, Har zai shiga akace ya dan tsaya a gyara shi… Ya kira waya ya dinga sanar da mutane Nan da nan dangi aka cika asubutin anan yayiwa dan Kiran sallah ya kuma yi masa hudu ba… Ana sallamar su suka tafi gida, da daddare jariri ya hana bacci, nan ya dinga raino, abun Har dariya yake bawa fatima, ” a kwana atashi Yau sunan fatima amsa wa d’a (Aliyu) kowa ya cika sai suna akeyi yaro yasha kayan barka….. Fatima tana kwance kusa da Arif tace Yaya please kadawo da Amira, ” ya kalle ta yaga zatayi kuka yace tohm shikenan, washe gari ta dawo zuka zauna lpya cike da soyayya, Arif yasa dariya dama nagaya miki *DUNIYA CE TAFI BAGARUWA IYA JIMA* *Gudu nakeyi domin naga ko nagama littafin ashe nakai karshen bango, wallahi mutane muje tsoron Allah mu aikata aiki Mai kyau domin DUNIYA CE Dai Dai take da kowa komai ka Aikata sai kagani kuma kome kayiwa wasu sai fa anyi maka,Kai mutane musa tsoron Allah aran mu, mu guje kuntatawa bayin Allah* *ALAMOMIN TSORON ALLAH GUDA BIYAR NE: FADIN GASKIYA DA CIKA ALKAWARI DA RIKON AMANA DA JIN TAUSAYI D KYAUTATA MA MUTANE. YA ALLAH KA SA MU CIKIN MASU TSORONKA* *A wuri biyu ne ake gane kirkinkaYin Hakuri idan ka rasa,dabayarwa idan ka samu* Throughout life people will make you mad,disrespect you and treat you bad Let God deal with the things they do,cause hate in your heart will consume you too… Always Do Your Best. Your best is going to change from moment to moment; it will be different when you are healthy as opposed to sick.Under any circumstance, simply do your best, and you will avoid self-judgment, self-abuse and regret. ALHAMDULILLAH