EL-MUSTAPHA CHAPTER 4

EL-MUSTAPHA




CHAPTER 4







Ke da mijin ki abin son ki har sai kin nemi alfarma gurin masu baqin cikin auren ki?

Ban kawo kuka na dan ayimin fade ba, indai mutum yaci amanata Allah yana gani.

Jiddah ta juya ta cigaba da abinda take tana murmushi, uwani kuwa cigaba da Jan carbin ta tayi tana mus mus mus da baki.


‘Angon uwani ashe matar taka ta ijiye karatu saboda bautar aure, ko da yake amaryar Ma tace baka shiga dakin ta ballantana tayi tunanin kwanciyarka akan gadonta, jiddah ta fada tana qoqarin sakawa arham riga, el’mustapha na gefen su.

Kallon ta yayi, Uwanin ce ta gaya maki haka?, ta gyada kai tana kallonsa.

Ina guje maka axabar Allah, domin baka adalci a tsakanin mu, ya kamata ko menene a xuciyarka game da uwani kacire sa daga yanxu, kabata haqqinta tunda har ta fara magana akai.

Kin sani baxan iya rabar wata mace a duniyar nan bayan ke ba, bayan wannan ina matuqar jin nauyi da kunyar na kwana da mace a gidannan kina cikin sa jiddah, ballantana bana son uwani ko kadan, I can’t make love with her.

Idan hakane ka sauyamata wani gidan mana, ni dama nagaji da xamanta tare dani.

Xama yanxu kuka fara jiddah tunda kikaji xaki iya, baxan sauya mata wurin kwana ba, amma tunda kin matsa na bata haqqinta xanyi qoqarin cusa soyayyar uwani a xuciyata saboda nayi adalci tsakanin ku.

Idanun jiddah sukayi rau rau, ta dubesa, ka manta a alqawarin mu kace baxaka taba son uwani ba.

Ban manta ba amma ke kike son sakani na karya, maganar karatun uwani babu ruwana aciki adaina sakoni, wait uwani bataga tsakona bane har take mgnr bana shiga dakin ta.

Wane saqo? Jiddah ta tambaya tana kallonsa.

Ina xuwa ya fada a hankali bayan ya diro daga saman gadon, fita yayi aryan yabi bayansa.

Waya take yi lokacin da ya shigo dakin, sakin wayar tayi saboda rudewa kamar ta xura da gudu take ji.

‘Ashe idan naxo na kwanta a dakin ki saman gadonki xaki tafi ki fadawa duniya tunda har xaki iya fadawa matata ban taba kwanciya a dakin ki ba.

Kunya da tsoro suka dabaibaye ta,

Sai a lokacin ta daqo tana kallonsa cikin mamaki,

Ko qarya xan maki, ko kin manta ni dan sanda ne ina da ikon bincike akan komai likitan da kika hada kai dashi shine ya gayamin komai, nayi shiru na kyaleki ban gayawa jiddah ba saboda ina son ta gano kuskuren da ta tabka na yarda dake da baki amanarta harta amince ki auri mijinta, koma menene so nake ta gano da kanta kuma tayi nadamar abinda ta aikatawa kanta.

Shiru uwani ba bakin magana jiki sai rawa yake, iskanci Ma guri gare sa.

Yace inajin takardar dana baki, kin ajiye tane baki duba ba ko?

Tayi xuru tana kallonsa, a ransa yace shegiya mayya sai dai kici kanki, bai qara mgn ba yasa kai ya fice.

Ta soma safa da Marwa a dakin, lallai jiddah ni xata wulaqanta tasa mijinta yaci xarafina, wlhy sai nayi maganin su, kuma baxan karanta takardar ba, bari na kira jamila ita kadai xata warware min yanda xanyi dama itace mai sona.


Story continues below

*

Bayan kwana biyu tunda sassafe sai ga uwani ta fito daure da towel tana gwale qafafuwanta tana yatsina fuska,

Kallonta jiddah tayi a tunanin ko uwani ciwo taji bata sani ba,

Meya same ki haka uwani?

Uwani ta xauna tana yarfe hannuwanta, 
Anti jiddah ba ruwan xafi ne na gasa jikina, ciwo yake min, musamman qasan cinyoyina. 

Me ya sami cinyoyin suke ciwo?

Duk da jiddah taji wani abu a xuciyarta bata nuna ba, murmushi kawai tayi tana fadin, 

Kina so ki nuna min mijin bai dauke ki da daraja ba tunda baxai iya taimakamiki da ruwan xafi har sai kin fito nema, duniya ta shaida anyi sukuwa akanki. 

‘Wannan dai bashine na farko ba na talatin ne karki dauka dama baya barci a dakina. 

Ai naga alama, jiddah ta fada hade da gyara kwanciyarta, kallonta uwani tayi, 

Kada kishi yasa aje a gayawa miji, yaxo yana min muxurai a daki na ko yi maganin mutum a gidannan ehe….. Uwani ta fada cikin jin tsoron kada el’mustapha yaji tunda tasan ko takalminsa bai taba kwana a dakinta ba ballantana shi kansa. 

Jiddah shiru tayi mata, uwani ta raina mata hankali, jiya ta kwana da el’mustapha kuma yanxu taxo mata da xancen dakin ta ya kwana har sunyi wani abin, bata san sanda dariya ta subulce mata ba wanda ya sanya uwani yi mata kallon mamaki. 

Banan ta shigo da sallamarta, dauke da aryan yana kuka, 

Anti jiddah dubi wannan yaron goyonsa yake son nayi, jiddah ta dubeta, 

Saboda me baxaki Goya sa ba, banan 

‘Wannan ai sai ya karyamin baya dama dama arham dai, 

‘Dan Allah ki goyasa kona minti talatin ne, dauko xani daki na kixo, bana son kina masa wulaqanci banan. 

Uwani ta tabe baki Sam ta daina kula yaran, suma sun daina xuwa gurinta tunda take dukansu a boye, ta tashi tayi shigewarta. 

Suna tsaka da goyon sukaji sallamar hajiya, ai kuwa da gudu ya diro yayi kanta har arham, jiddah tayi mamakin ganinta. 

Hajiya ashe kina hanya ko ki sanar dani, banan kawo mata abinci da lemu. 

Hajiya ta xauna tana murmushi, 

Munxo gaisuwa da abbanku ne, shine nace bari na biyo naga yanda kuke xaune da yar uwar taki ince dai lafiya, 

Wlhy lafiya lau hajiya ba wata matsala. 

Ki qara haquri jiddah ki kuma yi haquri tunda ke kikaji kika gani, Allah ya gani banso auren ba kuma bana so har yanxu haka ma abbanku dalilin dayasa yaqi xuwa gidannan kenan saboda kada yaga uwani. 

Jiddah murmushi kawai tayi, tace hajiya kayan menene haka, 

Tsumi ne na kawo maku keda uwani, ki dauki daya ki bata daya, 

Jiddah tace mungode hajiya bari na kira uwani, 

Aa barta inje inganta xamuyi mgn ne dama, jiddah ta koma ta xauna, hajiya kuwa ta nufi dakin uwani. 

Ko maraba batayi da ganin hajiya ba, tea din ta take sha hankalinta a kwance, hajiya ta xauna tana kallonta. 

Uwani baki ganni bane ba gaisuwa. 

‘Na ganki mana bangama mamakin ganin ki gidan aure na bane?

Da kika ganni gidan auren ki ai ba wani abu naxo nema a gurinki ba, ashe laifi ne uwani dan naxo na duba lafiyarki. 

Story continues below

Jikin uwani yayi sanyi, tace kiyi haquri hajiya ni yunwa nake ji shiyasa kika ganni ina shan tea. 

Yunwa kuma, ba abinci a gidanne? Uwani ta tabe baki,

Waccan banxar matar ce ta xuba min abinci kadan, hajiya sai ki rantse ita ke siyen sa ba mijinmu ke nemowa ba. 

Da dai kina da mutunci ko cokali guda ta baki na abinci sai inga kamar tafi qarfin xagi a wajen ki, ai ko buga baici arxikin komai ba yakamata ya ci na igiya bugu da qari kuma ba Karen kane ya nemo ba. 

Wai hajiya tsakanin nida jiddah wa kika Haifa?

Kai tsaye ta amsa mata cikin nuna da gaske take, 

Ke na haifa, amma ita riqonta kawai nayi amma ta daukeni kamar wacce ta kawo ta duniya, tana mutuntani da girmama ni. 

Uwani tace shiyasa ta sami lasisisin rainani saboda an nuna anfi son ta dani. 

An fi sonta din, kuma ana kan son ta bama ni ba har abbanki yafi sonta akan ki, wanda xai iya baki mijinsa ki aura shine xai hana maki abinci, tunda can da kike xaune a gidan bata hana ki abinci ba sai yanxu, maaikatan gidan suka sami wadataccen abinci sai ke matar gida, to uban waye ya hana ki shiga kitchen din ki girka da kanki. 


Ni daman nasan gori kika xo kimin kuma kinyi, tunda na auri mijin jiddah duk nayi motsi sai an goranta min itace mai gaskiya, muje xuwa. 

Hajiya ta kawar da xancen ta hanyar fadin,  koma dai menene ke kika sani, jiddah ta kirani a waya cewa kin aje boko bautar aure kike ko meyasa. 

Eh ai idan an hana ihu baa hana aha, nace ni baxan yi karatu ba, bautar aure xanyi, duk wanda ya dage sai nayi  to kamar ya dage yin asarar yawun bakin sane, lokacinsa da kuma kudin sa, tunda nike karatun ba wani ba, banda munafurci irin na kishiya har an daga waya an kiraki an gayamaki. 

Saboda tana sonki da karatun ne ya saka ta kira ga wadanda suka isa dake ashe muma bamu isa ba?

Ni nagane dalilin dayasa matar nan ta dage nayi karatu saboda idan na xama wani abu agaba lokacin ta mutu ya’yanta suci moriyata. 

Dukiyar Uban su fa? Ko bakiga a daular da kike xaune ciki bane, kada kiyi karatun kanki xakiyi nadama. 

Ba nadamar da xanyi hajiya kune Ma xakuyi nadamar tursasani karatun saboda kudin ku xaku kashe. 

Allah ya kyauta, ya kuma shirye ki, ki dawo cikin hayyacinki. 

Amin, uwani ta fada tana kumbure kumbure, 

Ga tsumi na kawo maki keda jiddah, amma ta dauki nata wannan naki ne. 

Kallon tsumin tayi kafin ta dubi hajiya baki a bude cikin mamaki, 

Idan ba wani abun ake son hadamin ba saboda me xaa banbance nawa dana jiddah, idan gaskiya ne a hade musha tare mana. 

Yaushe kikaji nace kowa nasa daban, guda biyu ne ta dauki daya ta baki daya shine abin cutarwa, taya xaita cutar da abinda na haifa da kaina uwani. 

Sau nawa akayi hajiya, idan iyaye xasu iya maka baqin ciki a auren ka menene baxasu iyaba, nikam ban yarda da wannan tsumin ba anga na soma jiki nayi fresh na fara jin dadin gidan mijina yana sona sosai yanxu ake son rabani dashi. 

Hajiya bata qara magana ba ta tashi ta fice saboda wasu hawaye da suka xo mata, dakin jiddah ta nufa, kallo daya tayi mata ta gane akwai matsala, 

Hajiya dan Allah kiyi haquri indai akan uwani ne, kada kisa xuciyarki cikin bacin rai, kisa abin a ranki yaxo yana damunki, jiddah ta fada tana qoqarin share mata hawaye. 

Allah shi maki albarka jiddah, dan Allah ki qara haquri akan uwani idan kika ga abin yafi qarfinki kada kiji komai ki saka el’mustapha ya sake ta ta dawo gida. 

Uwani kuwa hajiya na fita ta dauki tsumin ta xuba a pith tayi flushing, 

Kar nake kallonku nasan abinda nake ba wanda xai iya cutar dani acikin ku, xama a gidan mijina daram kuma karatu baxan yi ba bautar aure xanyi. 

*

After 2 days… 

Uwani daukar takardar da el’mustapha ya bata tayi, sai juya ta take amma ta kasa budewa. 

Nikam ko menene aciki matarka xan baiwa ita, sai dai ta bar gidan wlhy, Allah kasa saki uku ne aciki da nayi rawar one corner a gidannan. 

Kafin ya dawo bari na kaimata takardar, tayi ta bar mana gidan, ta fita da sauri. 

‘Anty jiddah hutawa ake haka, 
Ina hutu ga mai iyali, uwani. 

Motsi taji a cikin toilet ta juya tana kallonta, 

Waye a toilet din ki anty jiddah, 

El’mustapha ne, 

‘Ashe ya dawo uwani ta fada tana qoqarin tashi cikin dabara ta ajiye farar takardar. 

Ki xauna mana, 
Aa bari dai na tafi, ta fice da sauri, 

Jiddah ta gyara kwanciyarta sai kuma tayi toxali da farar takardar. 

Takardar mecece wannan? Ta fada tana qoqarin budewa dai dai lokacin da el’mustapha ya fito toilet daure da towel a qugunsa. 


Jin motsin fitowar el’mustapha ya sakata juyawa tana kallonsa, shima kallonta yake, 

‘keda waye naji a dakin nan kuna magana, 

‘amarya ce, ina ji kai take nema bata jima ba ta fita. 

Ya tabe bakinsa, ya qaraso yana kallon takardar dake hannun jiddah, 

‘Wannan takardar mecece?

‘nima yanxu na ganta bansan ko ta mecece ba, ta soma warwarewa, el’mustapha ya karbi takardar da sauri yana fadin. 

Jiddah kira min uwani yanxu.

Me ya faru, 

Just call her. 

Bata qara mgn ba ta fita, bata jima ba sai gata ta dawo tare da uwani a bayanta, wannan karon ma da carbin ta a hannu. 

Yanda uwani ta gansa yayi matuqar bata tsoro, fuskarsa a daure, bama wannan ba ita kam duk iskancinta bata taba ganin namiji haka a gabanta ba, sai ta buya bayan jiddah, 

Fito nan, ya nuna mata gabanshi, 

Wayyo Allah, anty jiddah ki bashi haquri, kice ya saka rigar shi. 

Jiddah ta dan dubeshi cikin marairaice fuska, sai kuma taje ta dauko masa doguwar riga, kamar baxai saka ba ya xura yana kallon uwani. 

Takardar da na baki saboda kin rainani, sai kika kawowa matata ko?

Kayi haquri baxan qara ba, 

A tunaninki menene acikin takardar?

‘Na dauka saki ne aciki, 

Kin dauka saki ne aciki shiyasa kika kawowa jiddah, 

Aa bahaka bane, 
To meyasa kika kawo takardar, saboda kin rainani ko, ba laifin ki bane, fara yimin tsallen kwado anan kafin na hau kanki da duka. 

Da sauri ta fara hade da riqe kunnuwanta, 

Wayyo Allah hajiya, an taru anci amanar aure saboda an ganeni qaramar yarinya. 

El’mustapha bai kula taba xama yayi yana shafawa jikinsa mai, jiddah kuwa jikinta yayi sanyi saboda tausayin uwani, duk ta wani koma kalar tausayi kamar xatayi kuka itama takeji ganin uwani nayi. 


Hajiya… Hajiya…. Kixo karsu kashe maki ni, wayyo ni Allah maqiya sun sakani a gaba xasu ga bayana, saboda baa sona anga bani da kowa. 

Murmushi el’mustapha yayi yana kallon uwani, kuka take idanunta a rumtse take maganar. 

‘Dan Allah el’mustapha ka kyaleta, 

Kallon mamaki yakewa jiddah, lallai har yanxu jiddah bata san kanta ba, yarinyar da ke neman fidda ta a gidan take tausayi yaga alamar Sam bata damu da abinda uwani tayi ba, yana so yasani shin har yanxu jiddah bata san kanta bane ko me? 
Bata san halin da take ciki bane game da uwani, xaiyi magananin ta ya gani ko ina hankalin ta ya tafi. 

Ya dubi uwani, 
Xo nan uwani, 
Da sauri taxo gabansa tana fadin kayi haquri. 
Karbi takarda hannun jiddah taki ce kuma ba saki bane aciki, takardar yarjejeniyar auren muce idan kikayi wasa da ita tamkar kinyi wasa da auren kine kin fahimceni. 

Ta gyada kai gwani tausayi tana kallonsa, tashi ki bace min da gani, 

Ta tashi sai da ta kai bakin qofar ta juyo, Allah ya isa kuma human rights xanje yanxu abimin haqqina… ta fita da gudu, murmushi kawai el’mustapha yayi shi yanxu uwanin Ma ta fara birgesa, abubuwanta akwai nishadi aciki. 

Story continues below

‘Dan Allah el’mustapha ka daina yiwa uwani I…….. Enough ya katse ta, ta hanyar daga mata hannu

Uwani matata ce right, ta gyada kai tana kallonsa, 

Ki samin ido akanta, ba ruwanki, ya juya ya fice.

Ta bisa da idanu har ya fice, menene laifinta saboda ta bashi haquri, sai ta tabe bakinta tayi kwanciyarta. 

Yana fitowa dakin ta yaci karo da uwani ta fito tana kuka, sanye da hijab din ta, yarinyar nan da gaske take yi kenan. 

Da sauri ya nufe ta, hannunta ya riqa ya nufi dakinsa da ita, tun da ya riqa hannun uwani take kallon sa cikin wani shauqi na soyayyarsa, bai taba riqa hannunta ba ballantana tasa ranar da xata shigo dakin sa, koda wasa jiddah bata taba aikota dakin el’mustapha ba, yau gashi da kansa ya kawo ta, xuciyarta fal da farin ciki harta manta damuwar da take ciki, 

Juyowa yayi yana kallonta yaga shi take kallo, ya daure fuska nan da nan tasha jinin jikinta, 

Kika ce Allah ya saka maki ko?

Ni bada kai nake ba, 

Dawa kike yi ai ba jiddah ta saka ki ba, 

Ni wlhy da qafafuna nakeyi, sune suke min ciwo, 

Yace sune xaki kai human rights kenan? ta gyada kai da sauri tana kallonsa. 

Yanxu xamu fara shiri dake saboda wani dalili nawa, amma kada hakan yasa ki rainani ki kuma raina matata ta. 

Shiru tayi tana kallonsa, a xuciyarta tace ni daman nasan sai ka soni dan Ma ban fara yi maka kwalliya ba ina matsewa tunda anti jiddah batayi. 

Jiddah tace kin daina karatu bautar aure kike yi, gayamin abinda kika sani acikin bautar aure?ta washe baki tana kallonsa, 

Bautar aure duk baxai wuce na kula da kaina, na kula da abincin da nake so naci nasha, na nemawa kaina tsari ga mahassadan aure na, na kuma yi maka girki. 

‘Ashe ma komai baki sani ba akan aure uwani, yayi maganar cikin dariya, itama dariya take cikin nishadi gani take kamar tana aljannah ne tare da el’mustapha, 

‘Na raba maku girki daga yau keda jiddah kowacce kwana biyu biyu ne, girkin jiddah xai fara daga yau saboda itace babba, bayan kwana biyu naki ne, tunda sassafe xaki tashi kimin breakfast kin dai san yanda jiddah keyi ko?ta gyada kanta, yace yauwa kuma xaki riqa xuwa kina gyaramin sashe na duka babu mai aiki acikin wannan, idan naga kina bin jiddah sau da qafa xan bude maki dayan sashena ki koma da xama, in kuma naga sabanin haka xaki cigaba da xama a wannan dakin. 

Yanxu kaji kana sona ne?ta tambaya tana kallonsa da murmushi a fuskarta, 

Aa jiddah kadai nake so ai kinsani, bana so nashiga haqqinki ya saka na baki damar yin duk abinda kike so a gidannan tunda akwai auren ki akaina, ki kiyaye. 

Ta bata fuska, dama ina so kabani kudi na fara Sana’a kuma nima ina so abani mota. 

Ya dube ta da mamaki, yanda ta daure take maganar sai kace uwarsa. 

Ki bari xanyi tunani nagani keda jiddah, kowacce ku xan bata jari. 

Har da anty jiddah xaka ba, amma ai ni na tambaya. 

Duk abinda xan bawa jiddah sai na baki, haka itama duk abinda xan baki sai na bata shine adalci. 

Amma ai ita tana da kudin ta kuma tana da mota, 

Yace uwani idan na baki mota sai na canxawa jiddah sabuwa amma fa ba iri daya ba, jiddah dabance a xuciyata, kiso jiddah idan kina so mu xauna dake lafia a gidannan kafin wa’adin auren mu ya cika. 

To nagode ta fada tana qara kallon dakin, yanxu bayan kwana biyu inxo in kwanta anan dakin? 

Baiyi magana ba, ya maida kallonsa ga wayar da yake dannawa, 

Uwani ta juya ta fice farin ciki fal a xuciyarta ji take tafi jiddah yanxu Ma a gidan, 

‘Washe garin ranar iskanci Kala Kala take mawa jiddah harda su habaici ai itama xata karbi miji ta fara kwana a dakin sa, xata fara masa girki, yace yanxu yana sonta, harda yan waqe waqen ta. 

Tun kafin ranar taxo har an fitar dasu Maggi, da sauran kayan da xaa yi amfani dasu an ajiye, arish Ma an diba an ajiye a gefe, kwai ma haka, har plate da cup duk an tana da an kai daki an ajiye. 

Jiddah na kallonta bata tanka mata ba duk wannan habaicin da ake mata. 

Ana gobe xata karbi girki ta sami jiddah a falonta, harda russunawa cikin ladabi. 

‘Anty jiddah naxo abani kudi na fara Sana’a in sami kudin kaina ina debewa kaina takaici indai na gani ga kishiyoyi, mutane suna min kallon na auri mai kudi ina cikin qaton gida ina auren babban dan sanda sai a dauka nima kudin nake da. 

Ni kam banda kudin da xan baki kiyi Sana’a uwani tunda bani ke auren ki ba, 

Tau shikenan, daman nasan baxaa bani ba na bata lokacina da yawuna wurin fallasawa kishiya sirrina, to wallahi xan bawa mutum mamaki, yau xan fara Sana’a kuma ko wacce iri naga dama ita xanyi wacce xata kawomin kasuwa na sami kudi, kuma kar naga mutum yaxo siya, ta fice a fusacce. 

Jiddah kallonta kawai take da mamaki har lokacin da ta fito ta nufi harabar gidan, 

dan aikensu ta kira, kudi ta bashi je ka siyomin buhun masara wadda ake gasawa nima Sana’a xan fara kayi sauri ina jiranka. 

Ta dawo tana cigaba da fada, nace abani jari anqi abani, shi yana min maganar jiddah, ke naxo kina min maganarshi tuni nagane manufar ku baa son bani ne anfiso aganni talauci na qullin kubura dani, to wallahi gasasshiyar masara xan fara saidawa a qofar gidan nan ba ruwana. 

Xumbur jiddah ta miqe tana kallonta, 

Masara kuma uwani, keda kanki?

‘au ashe ma kinji kenan, kudina ne ehe, ni na nemawa kaina jari na tallafi kaina da ya’yana masu xuwa nan da lokaci qanqani dan xan fara kwana da miji gobe, kada suxo yayan kishiya suna masu gorin maman su bata da kudi. 

Kin tambayi el’mustapha ya baki jari ne bai bada ba, kina so ki xubar da mutuncin gidan nan uwani ki bata mana suna, dan Allah kada ki fara wannan Sana’a, shiyasa akace ai ki tsaya kiyi karatu. 

Karatun ne dai baxanyi ba, wasa wasa jiddah ta kasa hanata barin sana’ar amma tasan idan el’mustapha yaxo baxaiji dadi ba. 

Tana ji tana gani uwani ta yasa banan suka fita tare da aka kawo masarar . 

‘Ashe uwani da gaske take cewar banan lokacin da taga uwani ta fara gyaran masara, har garwashin ta ya kama. 

Yan sandan dake qofar gidan suna gadi cike suke da al’ajab, amma sanin halin uwani da kasancewarta matar mai gidan ya saka suka ja bakinsu sukayi shiru, sai Ma suka fara siye suna ci, mutanen unguwa sun fara garxayowa wasu kuma tsegumi ke kawo su suganewa idanunsu. 

Banan kam harda hawayen ta. 

Bayan wani lokaci sai ga motocin el’mustapha sun shigo layin, baiyi mamakin mutanen da yagani qofar gidansa ba dan a tunaninsa yara sukayi fada yan sandar ke sasantasu kamar ko yaushe, 

An bude masu gate, gab da xasu shiga gidan idanunsa na sauka akan uwani dake firfitar gawayi. 

Ya kasa gasgasta abinda idanuwansa na hangowa masa, tun kafin motar ta gama Parking  ya fito da sauri batare da ya jira an bude masa motar ba, 

Wajen gidan ya nufa, yana leqawa kuwa sukayi ido biyu da uwani. 



Ko kadan uwani bata ji tsoron ganin sa ba ko alamar firgita a tare da ita, 

‘Na nawa xaa baka? Shine abinda ya fito bakin uwani lokacin da take kallonsa. 

Murmushi el’mustapha yayi a ganinsa girmansa ya fadi ya tsaya cece kuce da uwani a waje, 

Ya ciro dubu daya yana fadin, bani ta dubu daya ina jiranki yanxu. 

Uwani ta washe baki, Banan bude masara ga costumer na kwarai wanda ba baqin ciki a tare dashi, kinji har ta dubu xai siya…. Uwani ta fada tana bude masarar🌽🌽🌽

El’mustapha juyawa yayi ga wacce yaji an kira da banan, yana jin sunan ta abakin jiddah amma basu taba haduwa ba, idanun su suke sarqe dana juna, yayi saurin dauke kansa da sauri yana kallon uwani, haushinta kamar ya shaqo wuyanta a gurin. 

Banan kuwa tuni jikinta yayi sanyi, yau tayi ido da ido da el’mustapha, ashe haka yake, dole uwani xata kamu da ciwon xuciya dalilinsa, ba kowacce mace xatayi masa kallo daya ba batare da taji wani abu a xuciyarsa ba. 

Uwani dauko wadannan haka sai ki cikamin sauran daga baya ina sauri, 

Banan cigaba da gasawa bari na kai masa acikin gida, 

Tana gaba dauke da masara yana bayanta, suna shiga harabar gidan ya kira wani dan sanda gefe, 

Ka watse min wannan taron, duk abinda ke gaban gidan ka jefar dashi cikin bola duk ka watsar da komai bana son ganin ko tsinke a wajen ko naga an dawo dashi gidannan. 

Suna shiga falon suka tarar da jiddah xaune tana yiwa twins lesson, 

Kafin uwani tayi wani yunquri el’mustapha ya dauke ta da wani wawan Mari a kuncinta, 

Shiru ya biyo baya falon har wace aka Mara saboda rudewa, twins kuma tuni sunyi bayan jiddah saboda tsoro abinda basu taba gani a gurin baban su ba, 

Tsawon second talatin uwani ta dauka kafin ta dawo hayyacinta, sai a lokacin ta fashe da kuka ta dafe kuncinta tana qoqarin barin falon a rude bata ma sani ba, 

Fincikota yayi ya dawo da ita tsakiyar falon ya jefar, qoqarin xare belt din sa yake, tana ganin haka ta rarrafo da sauri ta riqe qafafunsa, duk da haka el’mustapha bai fasa yi mata biyar masu kyau a bayanta ba,

Jiddah ta dauki twins ta fita dasu daga falon itama a tsorace take da el’mustapha, ita kam tunda take tare dashi bai taba sa hannu a jikinta da sunan duka ba abinda tangujewa uwani kenan tun farko. 

Sanda ta dawo ne taji uwani na fadin, 

‘Dan Allah kayi haquri baxan koma ba, anty jiddah ce tace nayi wlhy itace tasa nayi, 

Cak jiddah ta tsaya hade da dora hannunta a qirjinta, ta xare idanu tana kallon el’mustapha cikin girgixa kanta, 

Ni? Wlhy qarya take min sai dana hanata taqi, uwani na kuka tayi caraf tace

Wlhy kece Ma kika bani kudin, ashe sharri ne kika min k….. El’mustapha ya bige mata baki, jiddah na ganin haka ta xura da gudu dakinta, rufewa tayi hade da sanya key cikin tsoron el’mustapha. 

what a disgrace uwani, kamar ki, ki dora sana’ar masara a qofar gidana inama laifin a qofar gidanku ne tunda dama can kinyi kama da masu gashin masara. 

‘Dan Allah kayi haquri sharrin shaidan ne da aljannu, sune suka sani, ka tambayi anti jiddah tasan ina da aljannu kuma suna sani yin abu ban ma sani ba. 

Story continues below

Ai gobe idan suka saki nasan da gudu xakiyi tunda baki san kina yi ba, 

Wallahi ko sun sakani baxan yi ba, dan Allah kayi haquri. 

Juyawa kawai yayi ya barta gurin, anan tsakiyar falon ta kwanta tana kuka bataso ta daga murya sosai yanda yan aikin xasu jita su rainata shiyasa takeyi kadan kadan. 

Har akayi magrib uwani na gurin kwance, jiddah kuwa tunda ta shiga bata fito ba, el’mustapha na fitowa cikin shirin xuwa masallaci ya ganta a gurin. 

‘xaman me kikeyi anan tun daxu?

Ta tashi tana share hawayen fuskarta, 

‘gobe tafiya xanyi, xanje Lagos, idan na dawo na tarar da kin kafa rumfa a qofar gidannan kina siyarda abinci ki xama maman iyabo kinji. 

Ko qala batace ba ta ficewarta, 

Tana gama sallah taji sallamar jamila qawarta, ai kuwa da murna ta tare ta, dauko wannan dauko wancan, ta hada mata kayan maqulashe abinda bata yiwa hajiya ba kenan. 

Wai ke dan ubanki duk da kina auren mai gidan Ma baa canxa maki makwanci ba wannan Ma rainin wayo ne wlhy. 

Cin amanata kawai sukeyi daga ita har shi, anqi a bani Sana’a nayi jari da kaina shine yaxo daxu harda min duka. 

Duka uwani? Kuma kika kyale, amma kekam anyi sakarya daya dake ki yana fita ki daki matar shi mana,  har yaushe xan xauna mace da mijinta su rainani acikin gida, ke dan ubanki sai kace ba qawar jamcy bace ke danme baxaki kirani mu hadu muci u… a gidannan ba. 

Ai kinsan yar uwatace fa kuma tana sona gaskiya, bana so abinda xai cutar da ita. 

Tau shikenan tunda yayar kice ki xauna ta mallake mijin kina kallo sai dai ta haihu ya’yan ta su gadi dukiyar nan ki tashi baki da ko sisi, kina gani maxa biyu ne yanxu a gabanta ke bako da ko daya ki fara neman hanyar da xata barmiki gidan tukunna. 

Yauwa jamcy ta ina xan haihu tunda bamu kwana tare bamu taba yin abinnan ba fa.

Ban gane me kike nufi ba, wlhy yanda nake ji game dake a yanxu kamar na shaqe ki. 

Banda iskanci har sai an nuna maki yanda xaki janyo namiji a jikinki, cabdi, wata nawa da auren yanxu, sai kika xuba idanu ita tana kwanar miki da miji. 

Ki cire duk wannan tsoron da kike masa, mijinki ne babu wani shakku rungumesa ko a gabanta kina shafashi kina kiransa cwty I miss you dis an dat, idan yayi maki Jan ido kema ki bude masa naki alamar haqqin ki kike so, idan kika nuna jin tsoronsa kin fadi kece a baya. 

Kuma kinsan fa xan iya, dama nice da girki gobe. 

‘Yauwa uwani, gobe ki matse a gidannan, da dare kada kiji kunya kisaka nighty wacce xata firgitashi, idan yaqi ina da pills acikin jakata na shaawa yanxu xan baki ki saka masa wlhy da ya ganki xai rude dolensa ya nemi ki, ta ciro taba uwani, ta karba tana kallonta, 

Amma gobe yace wai xaije Lagos fa, saboda cin amana sai ranar girkina xaiyi tafiya. 

Barshi ya tafi sai ki bisa daga baya, kina dolanci haka sai kace a qauye kika tashi. 

Ban taba xuwa Lagos ba fa, 

Acikin yaransa baxaki rasa wanda bai sani ba har masaukinsa kuwa, ki biyasa ya kaiki ni xan baki kudi domin ki kwato yancin ki, 

Aikuwa nagoda xan hada kayana wlhy baxanji tsoron sa ba kin sanni ai, 

Wace Sana’a ce kika fara ya dake ki, 

Masara na fara gasawa, 

Jamila ta kalleta cikin jin haushi, wlhy ko nice ubanki xanci, ki rasa Sana’a sai ta masara, maimakon ki fara business akan abinda xai kawo maki kudi da sauri, shegiya classic Sana’a xakiyi ba irin wannan ba, ai wlhy ko Yusuf ya ganki mutunci ya xube ballantana a gidan AIG na yan sanda.

Story continues below

To nima nagane ai banyi abin kirki ba, shiyasa ma banga laifinsa ba, ni yanxu canxawa xanyi na fidda ainihi uwani dina a gidannan na hana kowa jin dadin sa sai na mallaki gidan, naji dadin shawarar ki shiyasa nake sonki, ni yanxu burina na haifi yan uku duka maxa. 

Allah yasa da kuwa munyi murna wlhy dan kinsan mun haye komai ya dawo gurin mu, suka taba suna dariya. 

Duk jakkancin da kike ki ajiye a gefe, kefa classic ce kina da kyau, haske kawai jiddah ta fiki ki riqa kwalliya kina gogawa da ita, sai ta raina wayonta. 

Anjima may xan je na same sa dole ya bani jari, 

‘Yauwa uwani idan an samu a sammana kinga iPad dita ma nake son canxawa. 

Karki damu dole ne na baki, ai ke mai sona ce kece kawai bakimin baqin ciki komai xan iya maki. 


Da dare bayan tafiyar jamcy, el’mustapha sai kai da kawowa yake dakin jiddah akan ta bude masa dakin taqi duk a tunaninta tunda uwani tace itace itama dukan ta xaiyi. 

Sai da ya marairaice yana rantse rantse kafin ta yarda ta bude qofar, yana shigowa dakin kuwa yayi sama da ita, juyawa ya soma yi da ita a dakin yana yi mata waqar matsoraciya duk dai dan ta saki jiki dashi. 

Qanqameshi tayi tana dariya, ya dire ta a saman gadon, dogon hancinta yaja yana kallonta da murmushi, 

Nayi mamakin matar dan sanda da tsoron duka, 

Ta shagwabe fuska tana turo baki, 

A tunaninki akwai abinda xai saka na dake ki jiddah, babu shi, kada Allah ya nuna min ranar da xan dora hannuna akan jiddah da sunan duka, uwani ma ta kaini bango ne. 

Kayi haquri nima na tsorata ne, dan ma baka ga twins bane inaji yau ko kusa da kai baxa su xo ba. 

Wai da gaske, oh ni el’mustapha na shiga uku yau, kice babu hira yau nida su. 

Nima ai saboda ka rantse ne da baxaka ganni ba, 

Dariya yayi yana cire doguwar jallabiyarsa, 

Jiddah kawo min abincina anan, yau ina so nake muyi soyayya mai tsayawa a xuciya na qara nuna maki qaunarki da matsayinki a xuciyata, 

Murmushi tayi tana kallonsa, 
Ko acikin mafarki nasan el’mustapha mai sona ne da gaskiya ballantana a xahiri, kamar kasan kwanaki hajiya ta kawomin kayan dadi ina ta sha fa, 

Eyyeh shine baa gayamin ba nima na kwashi dadin, yi sauri jiddah na yar albarka, yau babu hirar dare, 

Ta fice tana dariya kicibis sukayi karo da uwani an tsuke cikin riga da jeans sun kame jikin ta sosai, kallonta jiddah keyi tana jin wani abu a xuciyarta, haka uwani xataje gaban el’mustapha ya ganta, na shiga uku ni jiddah wai me uwani ke nufi ne. 

‘Yauwa anty jiddah mijin naki yana ina neman sa nakeyi, ina da magana dashi idan kin bani dama kada na shiga haqqinki dan nima bana so kimin haka gobe. 

Da kyar jiddah ta bata amsa da yana ciki, uwani bata saurare taba ta shige, jiddah ta nufi kitchen a sanyaye. 

Kallon uwani yake sama da qasa sanda tayi sallamar ta shigo, 

Amsa sallamar yayi yana daure fuska, 

Ta russuna irin cikin kissa nan ta soma magana. 

Dama naxo na baka haquri ne naga ban kyauta ba Sam, kuma sana’ar bata dace dani ba, harna bata ma rai, dan Allah honey kayi haquri baxan qara ba, 

Waye honey din? Ya tambaya yana mata wani duban, 

Ina da wani miji ne bayan kai, kasani a duniyar nan ba wanda nake so kamar kai, ni wlhy haka xan riqa kiran ka dashi saboda ka dace da sunan. 

Hmmm kawai yace, 

Sai kuma maganar Sana’a naxo abani jari. 

Sana’ar me xakiyi ne?

Ina so na fara siyar da zinari, xobuna, awarwaro, sarqoqi da dai sauransu. 

Ya xare idanu yana kallonta, 

Banda wannan xarafin uwani, ki canxa wata Sana’a daban. 

Ta bata fuska tana kallonsa, 

Haba honey nasan fa akwai kudinnan, ka daure dan Allah ka bani. 

Sai idan bashi xanje naci na kawo maki kudin, amma banda wannan xarafin nagayamaki tun farko. 

Tau shikenan naji ka kaini gidan hoto xanyi naje amin foster, 

Idan anmiki foster kiyi me da ita, 

Ba el’mustapha ba dake xaune kamar gunki ko jiddah ta tsorata da jin kalaman uwani sanda ta shigo dakin dauke da abinci. 



_wannan shafin naku ne masoyan uwani, amma tace bata yin ku jamcy kawai🤭_




Kallon jiddah el’mustapha yayi, 

Jiddana xo kiji abinda wannan matar ke magana akai, ni na yarda akwai aljannu a tare da ita. 

Jiddah ta ajiye kayan ta dawo gefensa ta xauna tana kallon uwani. 

Uwani da dai kin haqura da siyasar Sam bata dace dake ba, ban da abinki sai kana da masoya da kudi kake siyasa. 

Uwani ta dube ta, da mijina nake magana, kuma ba shawara naxo nema ba ballantana a tsayamin qananun magana, kina cewa banda masoya inji waye ya fada maki hakan? Kina nufin kice hajja da xoxo basa sona kome, ko kuma kina nufin Kdeey da qaumi baxasu xabeni bane? Bar wannan ma ina kika bar nuceey, Sumy, Fido, mom abdul, mom of 12, zahra, usaina, da umm yusuf? In tsaya yi maki lissafinsu Ma xuciyata baqi xatayi saboda bacin rai, 

‘Yauwa nama tuna ko a makaranta ina da mutane tun daga samari har qawaye, lallai Ma anti jiddah kice banda masoya sai kace ke?

Inji waye yace maki jiddah bata da masoya cewar el’mustapha yana kallonta. 

Naki masoyan shirme ne, jiddah tafi ki masoya masu aminci da son ta da gaskiya, 

Koma menene naji abani kudin xanyi siyasa dasu, ni nasan anty jiddah da baqin ciki xatace baxataje rally ba. 

El’mustapha ya dubi jiddah, 

Jiddatulmusty help me with a piece of paper an biro pls, 

Kayi me dashi kuma, 

Ki dai bani, uwani xan bawa sakin ta sai taje gidansu tayi siyasar ba dai a gidana ba, uwani na jin haka tayi caraf ta riqo hannunsa. 

Haba honey, haba my honey daga neman shawara kuma sai abu ya xama dan xani, ni wlhy tun da baka so na haqura, ni sana’ar Ma na fasa bautar aure xanyi, dan Allah kayi haquri kaji honey. 

To sake min hannu ki matsa tukunna, ba musu ta sake sa tana kallon jiddah, 

Ya haqura karki kawo takarda, naga har kin wani ji dadi. 

Uwani tashi ki tafi pls, gobe xan neme ki, ta tashi tana girgixa jikinta ta fice, kallonta kawai el’mustapha yayi ya dafe kansa, yarinyar ta fara bashi ciwon kai, wai siyasa xatayi.

Jiddah ta dubesa, 

Kada kaima ka fara damuwa da halin uwani ne, 

Dole na damu tunda kece kika dora ni akai, before ban san halin uwani ba cos ban taba xama da ita ba bayan gaisuwa dake hada ni da ita, amma yanxu kam….. Allah ya kyauta. 

Kayi haquri nima nagane kuskurena, ina jin haushin kaina el’mustapha ji nake kamar in fitar da uwani a gidannan. 

Tukunna dai, har yanxu baki gano abinda nake so ba. 

Ya xauna qasan carpet hade da tankwashe qafafuwansa, 

Xo ki xuba min, kije kixo min da twins gobe baxan sami damar ganin su ba, mrng flight xan bi. 

*

‘Washe garin ranar dakin uwani ya fara nufa bayan ya shirya, jiddah ta tsaya jiran sa a falo har ya fito xuciyarta ba dadi. 

Uwani na ganin sa taso da gudu ta rungume sa😯, 

Honey tafiya xakayi ka barni dan Allah kaje dani kasan ina sonka baxan jure rashin ka ba, 

Story continues below

El’mustapha ya boye mamakin sa yana kallon uwani, 

‘aiki xan tafi uwani kuma koda tafiyar xanyi da mace jiddah ce tafi cancanta na tafi da ita saboda ban taba xuwa da ita Lagos ba, ko na tafi da mace ba xama nake ba amma idan na dawo xan sami lokaci na fita hutawa dake da jiddah da twins. 

Uwani ta qara lafewa jikinsa, wani dadi take ji tana qara godewa jamcy a xuciyarta da ta bata wannan shawara da yanxu sai dai ta riqa kallonsa fa, qamshin turaren sa qara kashe mata jiki yake ta qara rungumeshi kamar kada ta sake shi. 

Uwani bari na lallaba na tafi kinji, 

Tau sai ka rungumeni nima yanda nayi Ma, kayi min kiss tukunna. 

Mamaki ya kamashi, 
Abinda bakaso ko kayi ba dadin sa kake ji ba, sake min jiki haka. 

Ta qara cukwikuyeshi tana buga qafafunta wasa kamar wacce xatayi kuma, 

Haba honey sai kace ni ba matar ka ba, ina adalcin da kace xaka riqa mana, ni meyasa kake min wulaqanci ne. 

Ba dan ya so ba yasa hannu ya rungumeta, a xuciyarsa kuwa mamakin hali irin nata yake rashin kunyane kome?

Saura kiss honey, yaji uwani na fada ta xubawa fuskarsa idanu, kiss yayi mata a goshi, ta rumtse idonta a xuciyarta fadi take dadi… 

Rigima irin ta uwani ta saka el’mustapha ya fito dakin nata yana murmushi, kallonsa jiddah tayi taji wani abu a xuciyarta. 

El’mustapha ya rungume kafadarta suka fita, yan sanda suka taso suna gaidasa, inda motarsa ya nufa, ya karbi jakar dake hannun jiddah ya wurga cikin motar, ya juya yaga mutanen gurin kowa sha’anin sa yake ba wanda ya damu dasu, 

Jiddah na give me a kiss xan tafi da kewar ki, ta matsa ta sumbaci labbansa, ya qara jawota jikinsa yana kissing. 

Da kyar ta janye jikinta tana murmushi, safe journey and take care pls, I so much love you. 

Love you too jiddah na, kada ki manta kibi driver ku daukoni immediately 10 nayi kuna can. 

Tau shikenan, insha Allah, 

Ya shiga motar driver yaja kafin ta koma cikin gida. 

Uwani kam tuni ta hada kayanta yanda taji jikin el’mustapha yau Allah kadai xai hana mata kwanciya dashi, haba ashe dadi na nesa aka barta baya. 

Jamcy ta kira a waya ta gaya mata duk yanda xatayi kana ta dauki jakarta ta fice batare da sanin jiddah ba. 

Driver ta kira gefe, ka taba xuwa Lagos da mai gidan, ya gyada kai yana kallonta, tayi murmushi, kana nufin harda masaukinsa Ma kasani, nan Ma ya gyada kai. 

Yau samin kayana a cikin mota, muje ka kaini Lagos yanxu sai kadawo dan baxan gaya masa kai bane kuma xan baka 20k kasa a aljihunka ta fada tana washe haqora. 

Hajiya kiyi haquri mai gidan bai bani wannan ixinin ba, 

In baxakayi ba shikenan ni kuma xan maka sharri ya koraka daga gidannan dan xan gayamasa nemana kakeyi a kullum. 

Yayi shiru yana kallonta cikin mamaki, sai taunar cingam take abinta ba damuwa a tare da ita, ba dan ya soba ya amince xai kaita.

Sanda suka isa Lagos tuni el’mustapha ya dade da jimawa acan, yana office, uwani kuwa masaukinsa aka kaita ta xauna xaman jiransa. 

Kamar a mafarki el’mustapha ya tsinkayota xaune gurin, sosai ransa ya baci itama taga haka a tare dashi. 

Sai da kika biyoni kenan, saboda kina da kunnen qashi tukunna Ma waye yaxo dake nan garin har ya nuna maki nan. 

Story continues below

Yanxu dan Allah honey laifine saboda na biyo ka? Ranar girkina ne ka xaka xo ka barni, kasan yanda nake ji a xuciyata game da kai, wlhy ina sonka dan Allah ka soni koda rabin wanda kake Ma jiddah ne. 

Kina sona xan baki umarni ki kasa bi, qarya kike munafuka, tashi maza kisan inda dare ya miki ubanda ya kawo ki sai ya maidaki kuma kika sake min irin wannan nayi tafiya ki biyoni wallahi bakin auren ki and I mean it, banxa kawai. 

Sosai ta tsorata da kalamansa, an gyara goma biyar bata gyaru ba, ta fashe da kuka tana roqonsa tana bashi haquri iya gaskiyarta ganin ransa ya baci matuqa, 

Ya bude gidan ya shiga batare da ya qara waiwayen ta ba, tabi bayansa dauke da jakarta sai faman kuka yake. 

Tun da ya shiga dakinsa ya rufe bai qara waiwayen ta ba, ya barta falo can kamar mujiya yunwar cikinta Ma ta ishe ta, shikam yana can yana waya da jiddah yama manta da wata uwani shiyasa Sam baiyi mata mgnr ba kuma koda ya tuna baisan yanda jiddah xata dauki maganar ba dan xatayi tunanin da gangan yaje da uwani. 

Yana fitowa ya same ta kwance a falon ta koma wata kalar tausayi, tsaki yayi ya fice. 

Sai dare ya dawo dauke da ledar abinci, jefa mata yayi a wulaqance, 

Banda tsoron Allah da kuma haqqi sai dai ki kwanta da yunwa ba damuwa ta bane kuma ki kwana da shirin gobe xaki koma inda kika fito kuma kisani baxamu dai dai ta dake ba tunda bakyajin magana, bana son mace marar tarbiya ko kadan. 

Ita dai sai haquri take bashi, ya fice ya barta gurin. 

Abincin take ci ba cikin dadin rai ba sai dan yunwar dake damunta, tana gamawa ta soma miqa tana hamma, dakin sa ta nufa yana xaune da laptop hannunsa sai dannawa yakeyi da sauri da alama aiki yake yi. 

‘Dan Allah honey ina ne toilet xanyi wanka na kwanta, barci nake ji. 

Yayi mata banxa kamar bai san da ita gurin ba, 

‘Dan Allah honey, kamin magana ko xanji sanyi a raina bana son wannan fushin ko kadan, 

Wani haushinta ya qara lullubeshi, honey da take kiranshi ke qara baqanta xuciyarsa. 

Ta juya tana neman hanyar toilet a dakin, 

Ke…. ta juyo tana kallonsa, 

Dauko min exotic falo a fridge, 

Da sauri uwani ta fita tana jin dadi ya saka ta aiki, tana daukowa taga ai yama fara sha sai ta tuna da pills din da jamcy ta bata, ta nufi jakarta da sauri ta dauko ta xuba masa, 

Ta dauki tsawon mintuna kafin ta koma dakin, 

Kallon ta yayi, 
Tun daxu kina me, sai kin gama sha ne xaki kawo min. 

Aa ban sha ba nadai rude ne da kyar naga fridge din ashe qarami ne, 

Harararta yayi ya cigaba da abinda yakeyi, ta ajiye kana ta nufi toilet din. 

Batare da tunanin komai ba ya fara sha, yana dialing number jiddah bayan ya kauda laptop din gabansa, da alama ya gama abinda yake yi. 

A hankali ya riqa jin jikinsa na canxa mashi sai faman lumshe idanu yake yana sauraren jiddah. 

Duk a tunanin sa saboda yana waya da jiddah ne yake jin feelings a tare dashi, a hankali ya kira sunan ta, 

Jiddah…. Sai kuma yayi shiru. 
Menene naji muryarka ta canxa, 

Nima ban sani ba jiddana, ban taba jin abinda nake ji yanxu ba, I need you, 

Dariya tayi tana gyara kwanciyarta, dai dai lokacin uwani ta fito toilet daure da towel a qirjinta, 

Story continues below

Kallonta el’mustapha yayi gabaki daya sai yaga ta rikide ta koma masa jiddah sak, 

Sai ya fara kiran uwani da jiddah wanda kuma jiddah ke amsa masa a waya a tunaninta ita yake kira, 

Ya tashi da wayar a hannunsa batare da ya kashe ba, ya nufi uwani dake ta faman murmushi ganin ya dosota. 

Ina son ki jiddah ya fada yana shafa jikin uwani, ta bata ranta lallai Ma mutumin nan ita yake kira da jiddah, ta raba ta gefensa ta fice. 

A yanda el’mustapha keji a jikinsa game da shaawar dake damunsa baxai fadu ba shi kansa bai san ya dauki uwani ya nufi gado da ita ba, uwani ta tsorata da lamarinsa wannan karon, ta soma qoqarin kwace jikinta, yasa hannu ya fincike towel din ta rumtse idanuwanta, 

Wayyo yaya kayi haquri dan Allah kabarni wlhy ban taba yi ba, na tuba…. Shine abinda kunnuwa jiddah taji muryar uwani na fada, 

Dif ta kashe wayar hade da wurgata tsakiyar dakin da qarfi har ta tarwatse, saukowa tayi saman gadon ta nufi dakin uwani, wayam babu ta babu alamarta sai tayi tunanin duk yinin yau fa ko motsin uwani bata ji ba a gidan. 

Kenan el’mustapha da uwani ya tafi, shiyasa ta ganshi daxu ya fito dakin yana murmushi ashe sun san abinda suka hada xasu mata, amma yaushe el’mustapha ya soma wulaqantata haka, macen da yake fadin baya so shine xai xabeta akan ta ita da ko Lagos bata taba xuwa ba, shine dan wulaqanci harda kiran ta a waya. 

A daren ranar kuka tayi shi sosai, ta kasa barci ko kadan. 

Uwani kuwa ansha kuka har an gode Allah saboda el’mustapha bai bi da ita sannu ba, da qarfi ya mata yanda yake jin abin a jikinsa. 

Shi kam baiji ya gamsu ba, har lokacin yana jin feelings sosai ya jawo uwani a karo na biyu, ta xare idanunta a karo na biyu sharkaf da hawaye. 

Tace miye haka kuma, dan Allah kayi haquri, wayyo hajiya, yasa hannu ya toshe mata bakin bayan ya qara kwantar da ita. 

Ranar kam uwani an gurxu idanu har sun kumbura saboda kuka, da kyar ta samu barci ya kwashe el’mustapha gurin saboda gajiya. 

Da rarrafe tabar dakin ta nufi falo, wayarta ta dauka ta kira jamcy ai kuwa tana dauka ta fara dura mata ashar kafin ta gayamata komai. 

Dariya jamcy tayi tana fadin, ashe kin sha dadi uwani kin shigo layin manya, to ai shine auren, xafin da kike ji xai bari kuma inaji kinsa masa maganin da yawa ne. 

Biyu nasa masa, gaskiya baxan qara yarda ba ni kin cuceni. 

Keda nace ki saka masa daya, yanxu dai ba matsala kin xama mace abinda jiddah ke taqamar  dashi yanxu kema sai ki fara ki nuna mata kema fa duk daya kuke, sannan abinda el’mustapha yayi maki a yanxu ai kinga ba laifinsa bane naki ne so kada ki nuna masa damuwa ki ta masa shagwaba ki nuna masa babu wani a xuciyarki sai shi, ki daina gudunsa ki daure komai xafi xaki daina ji. 

Anya xan iya kuwa jamcy kinji yanda abin yake kuwa baya tausayina. 

To ai kinga laifinkine, idan kikace xaki riqa hana masa to taya xaki haihu ko kin manta, sannan fa da wannan abin xaki siye xuciyarsa, ki daure qawata. 

Uwani ta sauke ajiyar xuciya kafin tace to shikenan xan qoqarta. 

Yanxu ina el’mustapha din, 

Yana daki yana barci. 

Ki koma ki kwanta dashi, gobe kada ki nuna masa damuwa kuma ki tabbatar kin shiga ruwan xafi sosai kin gasa jikinki. 

Uwani ta ajiye wayar tana tunani.

‘Washe gari da matsinancin ciwon kai el’mustapha ya tashi, ya dafe goshinsa yana kallon gefen da uwani take kwance, 

Gabaki daya komai na dawo masa tiryan tiryan, ya soma tunani meya hau kansa ne har ya kwanta da uwani bai sani ba, shikenan yaci amanar jiddah, da wane ido xai kalli jiddah duk ranar da tasan wannan. 

Allah ya gani bada nufi ya aukawa uwani ba, bai san ya akayi ba sai dai kukan uwani yake ji, sai kuma ya tausayawa uwani, da kyar ya tashi ya nufi toilet. 

Alwallah yayi ya fito a gurguje ganin ya makara sallah yau. 

Har ya gama shirinsa da komai uwani bata tashi ba, ya bar gidan da sauri, koda uwani ta tashi bata damu da rashin ganin saba, ita yanxu Ma ta qarajin tana sonsa sosai. 

Jiddah kuwa xaxxabi ya rufe ta, banan ta damu sosai ganin yanda jiddah ke ta xuba amai gashi sai kuka take har lokacin, 

Itama banan din kuka take tana roqar jiddah suje asibiti, da kyar jiddah ta amince, banan ta kama mata ta shirya suka fito. 

Gwajin farko a asibiti suka tabbatar tana dauke da ciki wata biyu, banan ta rungumeta cikin farin ciki, 

‘Anty jiddah xata haifa mana baby, Allah yasa twins ne mata. 

Duk da halin da jiddah take ciki bai hana mata godewa Allah da kyautar da yayi mata ba, sai kallon banan take da murmushi yanda yarinyar ke nuna damuwarta akanta. 

El’mustapha ya damu sosai na ganin yaqi samun wayar jiddah, da kyar ya kammala abinda ya kawo sa garin amma duk jikinsa ba kuzari, bai koma gidan ba sai dare. 

Inda uwani ma bai kalla ba, yayi shirinsa na barci ya kwanta, uwani bata damu ba ta kwanta bayansa hade da dora hannunta a qirjinsa tana shafa. 

Shiru yayi yana sauraren rashin ido na uwani, ya janye hannunta yasa blanket ya rufe jikinsa hade da lumshe idanuwansa. 

Ranar jiddah taga kulawa gun banan, kayan kwadayi irin na masu ciki banan ke mata, sosai damuwar jiddah ta rage kasancewar banan na qoqari akanta na ganin ta hanata shiga damuwa. 

‘Washe garin ranar da xasu dawo kamar jiddah baxata je tarbar shi ba amma tunawa da tayi shi ya bata umarni akan haka yasa ta shirya suka tafi tare da driver. 

Sun jima suna jiransu kafin jirgin ya sauka, su uwani a jirgi?

Daga can ta hangi fitowar el’mustapha, uwani na bayansa sai kalle kalle take abinka da baa saba ba. 

Babu xato el’mustapha yayi toxali da jiddah tsaye, nan yasha jinin jikinsa, gwiwowinsa suka yi sanyi,  gaban sa ya fadi, ya rasa wace irin fara’a xai mata, dariya ko murmushi? Kamar qasar gurin ta tsage ya shiga yake ji saboda kunyar jiddah. 


Uwani na ganin jiddah ta saki wani malalacin murmushi, 

‘Anty jiddah ashe kece kika xo daukar mu, ya gida. 

Murmushin itama jiddah ta maida mata, 
‘dole nake xuwa daukar amarya da ango, ya amarci. 

‘amarci alhamdulillah mu ma mun xama manyan mata. 

Jiddah bata kula ta ba ta dubi el’mustapha dake tsaye yana kallonta sororo, duk da abinda take ji a xuciyarta game dashi bai hana mata qarasawa gurin sa cikin murmushi ta rungumeshi hade da sumbatar kumatunsa tana kallon idanuwansa. 

‘Barka da xuwa mijina, ya amarci, da kyar ya amsa mata bayan ya qago murmushin yaqe yana kallonta, 

Lafiya lau jiddana, ta dauke dubanta daga garesa, wai jiddansa bayan ya munafurceni yake kirana da jiddansa, sai kace ni kadai ya ajiye, ya dauki uwani sun tafi amarcin su harda kiran ta a waya dan taji idan haushi xai kashe ta sai ai kashe ta ai kuwa baxata nuna masu hakan dan suji dadi ba, ta yarda namiji bashi da ta ido el’mustapha ya raina mata wayo ya bayyana mata zahirin abinda ake kira da Namiji. 

A yanda ta lura el’mustapha ya shiga cikin wani hali na damuwa, ko da suka shiga mota yana gaba da driver bai sake magana ba, ita kuma tana tare da uwani a baya, ko kadan batayi tunanin kallon inda uwani take xaune ba saboda wani haushinta da take ji a xuciyarta. 

Suna isowa gida jiddah ta fara fita daga motar bata tsaya sauraren su ba tayi ciki abinta, Uwani kuwa jakarta ta dauka jikinta ya fara sanyi daga yanayin el’mustapha tun a Lagos bai qara mata magana ba ko yunqurin hada ido da ita, to meke nan?

El’mustapha inda yaransa ya nufa suna gaisawa cikin mutunci da nuna yanda sukayi kewar uban gidan nasu. 

Yana shiga falon twins suka xo da gudu suka rungumeshi, 

Daddy is back, daddy daddy…. 

Ya rungume su yana dariya cikin farin ciki, saboda halin da yake ciki Sam ya manta baiyi masu tsaraba ba abinda bai taba yi ba yayi tafiya bai kawowa yaran komai ba. 

Daddy me ka siyo mana? Abinda yaji Aryan na fadi kenan, ya dubi yaron yana fadin, 

Daddy ya manta bai siyo komai ba aryan, arham ya tunxuro baki. 

Amma daddy kai kace a waya gobe xaka siyo. 

Kubari na huta sai inje in siyo maku anjima. 

Suka soma tsalle, har dakin sa suka bisa suna surutu yana biye masu. 

Ki hadawa el’mustapha abincin sa kafin ya fito, jiddah ta fada tana kallon banan. 

To anti nama kammala maki dan’waken da kika ce ko na xuba maki ne. 

‘Yauwa xubamin naci ko anan kitchen ne ta fada tana qoqarin xama. 

Dariya banan tayi tana kallonta, anty a kitchen xaki ci. 

Yi sauri ki hada masa banan kafin ya fito, kixo kije kasuwa kinsan me xaki siyomin. 

Banan ta girgixa kanta tana qoqarin hada kayan abinci, 

Ko da yake idan na gayamaki yanxu dariya xakimin bari har ki gama tukunna. 

Murmushi kawai banan tayi ta miqa mata plate na dan waken, kallonsa kawai jiddah tayi sai da yawun ta na tsinke yaji kaya sosai. 

Ta dauki abincin el’mustapha ta fita, tana jerawa a dinning ya fito twins na biye da shi har lokacin. 

Har qasa banan ta gaidashi kanta a qasa, ya amsa yana qoqarin xama a dining, suma duk suka xauna. 

Story continues below

Jiddah fa shine abinda ya fito bakinsa yana kallonta, ta juyo tana fadin tana kitchen….. Idanun su suka sarqe a karo na biyu, jikinta ya dauki rawa ta juya da sauri tabar gurin. 

Jiddah fushi take dashi kenan abincin Ma yau baxata yi serving din sa ba, da kansa ya xubawa twins kowane da plate din sa kafin ya xuba nashi. 

Uwani ta fito daga daki tana taunar cingam, tayi mamakin ganin el’mustapha yana cin abinci shi kadai, a tunanin ta xai neme tane suci tare tunda yasan tana jin yunwa ko breakfast bai bata a acan ba. 

Kitchen din ta nufa tana tafe tana girgixa jikinta saboda el’mustapha ya gani, bata sani ba Sam bata gaban sa abinci kawai yake ci amma hankalinsa da nutsuwarsa duk sun tafi gurin tunanin jiddansa. 

Tana shiga kitchen din ta kalli abinda jiddah keci ta yatsina fuska, kafin ta dubi banan. 

Ke me kuka dafa mana ne wai, banan ta dube ta, 

‘Anty uwani baa ce nayi girki dake ba, yaya kawai akace nayi wa girki. 

Uwani ta dubi jiddah sheqeqe kafin ta dubi banan. 

‘au nida gidan mijina sai ayi girki a hanamin, ok sai ance kiyi girki dani xakiyi kenan, to ni me ake so naci ko ni xan shigo kitchen din na dora. 

Banan tace akwai abinci na gida gaba daya acikin gida nasan baxasu rasa cire maki naki ba. 

Uwani ta dura mata ashar, el’mustapha ya dago yana kallon hanyar kitchen din cikin son jin hayaniyar me akeyi. 

Ke har kin isa ki gayamin abincin da xanci, nima ai personally ce a gidannan😂, ina da iko kamar wacce ta ajiyeki, duk abinda xatayi nima xanyi. 

Jiddah ta dubeta bayan ta ajiye plate din dake hannuta, 

Uwani idan kin fahimci maganar banan tana gayamaki ne baa bata ikon ta dafa abinci da kowa a gidan nan bane sai ni da el’mustapha kadai, 

Uwani ta dube ta, ok kece kika daure mata qafa take iskanci Kala Kala a gidannan, haba no wonder yarinyar nan ta rainani yanxu da kike mgnr baa bata ikon ta dafa abinci dani ba hala ni ba matar gidan bace ko kuma ke me kika fini a gidan, nima fa yanxu mace ce kamar kowa fa adaina min kallon yarinya nasan komai yanxu. 

Ai nasan ke macece ba sai kin fito kin fadawa duniya hakan ba, akwai masu aiki a gidan ki saka su dafa maki. 

Ke banan ke xaki dafamin abinci, ina jiranki yanxu kada ki batamin lokaci, ta juya ta fice a fusacce. 

Wlhy baxan mata girki ba sai dai kome xai faru ya faru cewar banan. 

Ba kya tsoron ta maki duka ne banan, jiddah ta fada tana qoqarin wanke hannunta a sink. 

Duka anti, ai na wuce shi a gurinta sai dai ke da kika ajiyeni, yanxu fa na girma candy xanyi na wuce tunanin ta, idan ta dake ni ramawa xanyi. 

Jiddah ta dube ta tana fadin nima watarana haka xakice kin wuce na dake ki banan, sannan ko uwani bataci arxikin komai ba ai taci na el’mustapha ina ke ina dukan matar mai gida, dan haka kiyi haquri ki dora mata ai ba komai bane, duniya yanda ka dauke ta haka take daukar ka, bana so ki xama daya daga cikin mutanen da basajin maganar manyansu. 

Shiru banan tayi amma xuciyarta xafi take, tana ji a ranta watarana sai dai tabar aiki a gidan dan wlhy sai tayiwa uwani dukan tsiya a gidan musamman idan ta cigaba da yiwa jiddah rashin mutunci a gabanta, ko kadan baxata jure ganin ana wulaqanta mata anti jiddah ba.

Jiddah ta fito daga kitchen din riqe da hijab din ta a hannu, 

Kallon twins tayi tana fadin idan kun gama cin abincin kuxo kuyi shirin xuwa islamiya. 

Story continues below

Momy ai daddy yace xamu je yayo mana tsaraba, 

Xakuje da dare bayan kun dawo, be fast aryan dubi yanda kake cin abinci. 

Kallonta kawai el’mustapha keyi har sanda ta fice wannan halin ko inkula da jiddah ke nunawa akansa ba qaramin tada hankalinsa yake ba, shi bai masan yanda xai fuskance da mgnr ba. 

Ya tashi ya nufi dakin uwani, kallonta yayi fuskarsa tamau ba alamar wasa. 

Xan gargade ki akaro na biyu game da jiddah, saboda jiddah kike a matsayin da kike yanxu ba dan haka ba ke kinsan baki isa na tsaya ina hada numfashi dake ba, idan kunnuwana suka qara jiyomin kina mata rashin mutunci irin na yau xan maki abinda xai sa ki tsane ni, gidannan da duk abinda ke cikinsa na jiddah ne ita keda ikon komai nawa, matasayinku ba daya bane matatace ta har abada ke kuma auren shekara daya ne kada ki manta, ina qara jajjada maki ki tsare kanki akan jiddah. 

Kayi haquri honey insha Allah xan kiyaye, 

Mtsewwwww ya fice, ta bisa da kallo lallai anci moriyar ganga dole xaa yarda kore, Kaji dadin abin kaxo kana wani noqewa, ai sau biyu kayi min nasani ban manta ba ko kotu mukaje xan iya bada shaida, bari girkina ya qara xagayowa wani xan qara sakama kuma, kuma gidannan baxan barshi ba sai dai jiddah ta barshi baxaku tabbata har abada ba,  wlhy baka isa ba daga kai har jiddah maganin ku xanyi a gidannan muje xuwa.

Gabaki daya yinin ranar bai sami fuska a gurin jiddah ba, shi kadai ke walagiginsa a gidan sai twins din sa, 

Haka da dare ma bayan sun dawo shi da twins yana kallonta ta saka ya’yanta gaba suka barshi anan falon, kuma jiddah dai tana sane da girkintane tunda kwana biyu yayi acan tare da uwani. 

Sam bata jin haushin uwani kamar yanda take jin na el’mustapha, 

‘Washe garin ranar da kanta ta shirya twins cikin shirin makaranta, bayan sun tafi ta soma kiciniyar hada masa kayan breakfast. 

Ta gama komai tana jerawa a dinning ya fito cikin shirinsa na fita office, 

Kallo daya tayi masa ta kawar da kanta gefe, ya qaraso gabanta idanunsa akan fuskarta. 

Xan jure kowane irin hukunci daga gare ki amma banda wannan fushin jiddah, kiyi min abinda duk xaki min tun daga kan fada, duka koma menene indai xai sanya ki huce daga wannan fushin kidawo da walwalar ki. 

Shiru tayi xuciyarta na qara hauhawa kamar yanda kunnuwanta keyi mata kururuwar muryar uwani a ranar, 

Ta lumshe idanunta ta qara budewa sai ga hawaye sharrr nabin kuncinta, el’mustapha ji yayi kamar shima ya tayata kukan, bai qara magana ba ya juya yabar falon batare da ya waiwayi breakfast din ba yana qara jin tsanar uwani a xuciyarsa domin itace sillar komai. 

Yinin ranar sukuku jiddah tayi, tunanin banan duk jikin ne na jiddah shiyasa komai da jiddah keyi a ranar duk ita tayi, akai akai take xuwa duba jiddah tana tsoron kada xaxxabi ya rufe ta kamar ranar. 

Ta rarrashi xuciyarta dan meyasa xataga laifin el’mustapha tunda itace ta tilasta mashi auren ta kuma dole xai sauke nauyin dake kansa na ganin ya baiwa uwani haqqinta dan baxai xuba ido yana kallon uwani ba ita kanta din an cutar da ita, shikenan uwani ta gama sanin sirrin mijinta shiyasa har take yada mata habaici, meyasa uwani baxata kwantar da hankalinta ta gyara rayuwarta suyi xama na aminci ba kamar sanda suna gaban iyayensu. 

Da xuciya daya ta taimakawa uwani saboda ciwon ta da kuma darajar iyayenta, maqasudin Ma jin uwani na qoqarin yi masu asiri ta rabata da el’mustapha ya qara sanya ta amince da auren ashe bata tsira ba. 

Alamar bude gate din gidan taji wanda babu tantanma tasan el’mustapha ne ya dawo, 

Ta tashi ta nufi toilet ta wanke fuskarta, har ta fito bataji alamar shigowar sa ba, window ta nufa ta daga labulen tana kallon motar. 

El’mustapha na xaune cikin motar, kansa na sitiyarin motar ko me ke damunsa ta fada a bayyane yayin da gabanta ke tsananta bugawa, kada fushinta ya janyowa el’mustapha wata matsalar. 

Ta fita daga dakin ta nufi harabar gidan, har ta isa gurin motar el’mustapha bai san ta iso ba, ta glass din motar ta tura hannu ta jijjigashi hade da fadin baban twins, 

Ya dago firgigit yana kallonta, ganin haka yasa jiddah taja baya tana dariya hade da ware masa hannayenta dan ta kawar dashi daga halin da yake ciki. 

Oyoyo Baby is back….. Nan da nan ya balle murfin motar ya fito, jikinsa na rawa ya rungumeta, ya matseta sosai a jikinsa hakan yasa tagane sosai yaji dadin hakan, taja hannunsa suka shiga cikin gidan. 

Xaunar dashi tayi bakin gado ta dawo gabansa ta tsugunna tana kallonsa, 

‘menene wai duk naga kayi wani iri ka canxa, are you not happy with me, jiddanka fa?

Yatsun hannuwanta ya matse a hankali, kallonta yake murya a sanyaye, kiyi haquri ki yafemin jiddah, kin ganni tare da uwani alhali bakisan tare xamu je ba, wallahi wallahi na miki rantsuwa Allah ne shaidana ganin ta kawai nayi a Lagos banma san yanda akayi taje can ba. 

Murmushi jiddah tayi hade da Jan dogon hancinsa, 

Nasan wacece uwani nasan xata iya, kuma bayan haka uwani matarka ce You have the right kaje da ita duk inda kake so a duniyar nan ba wanda xai hana, ka daina rantse min, fushin da kaga ina yi dakai bacin rai ne amma kayi haquri. 

Yanxu ya xanyi dake jiddah, me xanyi na tsira daga gurinki bana son bacin ranki ko kadan a tare dani. 

Nikam a gurina ka tsira baban twins, bana xargin mugun nufi a xuciyata game da kai ko uwani, dan haka bayanin da kayimin na gamsu, na yarda da kai, na amince Ma 100%, abu daya da xan tunatar da kai adalci kada ka juyamin baya saboda uwani. 

‘Na amince dake kamar yanda kika amince dani jiddah, da yardar Allah baxan juya maki baya ba baxan baki kunya saboda adalci ba uwani bata da matsayin da xan gujeki saboda ita. 

Shiru tayi bata tanka ba tana kallonsa, ya rungumeta sosai a jikinsa yana fadin I love you jiddana, please show me how much you love me. 

Not now, xo muje kaci abinci tukunna haka ka fita baka ci komai ba kuma akwai albishir dana ke son yi mak… tayi shiru sakamakon jin bakinsa da tayi a nata yana kissing din ta a ko ina, tafi tafi yaci galabarta ya nuna mata da qishirwarta a tare dashi. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *