FARAR WUTA CHAPTER 2 BY AISHA MAHMOOD

FARAR WUTA CHAPTER 2 BY AISHA MAHMOOD

Www.bankinhausanovels.com.ng 

A wannan daren…+

NO. 38 Ramie Street, Nassarawa GRA, Kano.

A cikin ƙawataccen ɗakin, wata yarinya ta buɗe ƙofar ta shigo, ba zata fi shekaru uku da kaɗan ba, tana sanye da irin kayan yara kamarta, wani ɗan gajeran skirt kalar lemon greeen, (lemon tsami) sai farar rigar da itama akayi mata da ado da irin kalar, gashinta da ba wani yawa ne dashi haka zalika tsawo ba an tufke shi cikin kalba guda biyu da ribbon masu kalar kayan.

Ta karaso cikin ɗakin daya gauraye da sanyin A.cn da aka kai maƙurarta, akwai wani tebur irin na ado dake gaban hadadden gadon dakin, ta kansa ta taka ta isa kan gadon, ta hau tana bi ta kan ƙafafun wadda ke kwance har ta isa daidai fuskarta da ta rufe da bargon data lulliba gaba ɗaya.

“Mammy Mammy Mammy….”

Ta kira ta na bubbuga daidai kanta da ƴan hannayen nata, a lokaci guda mahaifiyar tata ta yaye bargon daga fuskarta ta buɗe idanunta da kyar tana kallonta.

“Menene Hameeda? Me ya kawo ki?”

Ta tambaya ranta a ɓace.

“Mammy I’m hungry. (Yunwa nake ji.)”

Taja tsaki a hankali.

“Ina Nannynki?”

Sai kawai ta miko mata takardar hannunta, kamar ba zata karba ba sai kuma ta yatsunta  biyu ta sakala ta cikinsu sannan ta buɗe ta.

‘Ajiya I’m sorry Oo, dey don call me now say my mother dey hospital. I’ll return tomorrow by God grace.’

Ta sake jan wani tsakin mai tsayi, bata san sau nawa take gayawa Mary cewar ta daina yi mata pidgin a gida ba, amma don rashin mutunci shine har rubuto mata take yi a takarda.

Ta juya ta sake kallon yarinyar data tsura mata idanu, dogwayen gashin idanunta sun kusa haɗewa da juna, yadda take lumshe su ya tuna mata da fuskarsa a lokaci guda.

…idanunka kake gani ko Ma’aruf? Irin naka ne sak!

Muryar Mami ta haska a cikin kanta ranar farko na zuwan Hameedan duniya, ta tuno fuskarsa, yadda ya kalmashe ta cikin hannunsa, lumsassun idanunsa na haskawa da tarin ƙaunar da kamar wani abu ba zai taɓa giftawa a cikinta ba.

Ruƙayya ta sake yin wani tsakin da ya riga ya shiga cikin dabi’arta kafin ta ture bargon gadon ta miƙe, wata lallausar doguwar rigar bacci ce a jikinta da idan ka kalle ta zaka ga kamar tana zamewa ne tsabar santsi da kuma kyallin da take yi.

Ta kalli agogo wajen karfe bakwai na dare.

“Baki ci abinci bane da rana?”
Ta tambaya tana daure gashin kanta da za’a kwana a yini ana musu da wani akan cewar nata ne, don human hair ne (gashin mutum) da aka dinka mata shi cikin nata ya saje tsaf!

“Mami tun da na sha tea, Mary bata bani komai ba. Waya take ta yi.”

Gwarancin yarinyar mai daɗi ya fito tana kallonta. Wani tsakin ta sake ja kafin ta dauki wayarta sannan tace.

“Oya, taho muje to.”

Da sauri yarinyar kuwa ta sauko tabi bayanta, suka fita daga ɗakin zuwa wani dogon korido daya hada fuskokin ɗakuna, suka isa wani rantsatstsen falon da komai na cikinsa kalar ruwan gwal ne da kuma makuba, a gefensa akwai matattakalar bene, suka sauka har kasa zuwani falon da yafi wannan girma, ta jikin dining area suka shiga wata kofar da take ta kitchen ce, wani katon kitchen da yake a gyare tas.

Babu ko tukunya guda daya akan gas don haka ta san babu wanda ya dawo a cikin kannen nata uku maza, suma can yawonsu waye ma zai gansu yanzu da magaribar nan? Dama Ashraf mai bi mata ne idan ya dawo daga aiki sau da yawa zai shigo ya dafa abincinsa tun bayan da suka rasa Josh (mai yi musu girki)  yanzu kuma yayi aure sati uku da suka wuce don haka babu mai shigowa kitchen din.

STORY CONTINUES BELOW
Hameeda ta ɗane kan ɗaya daga cikin kujerun da suka zagaye worktable din kitchen din sannan ta zuba mata idanun tana jiran taga me zata yi, Allah ya sani ita bata son wani girki yanzu, da safen nan fa dawowarta kenan Nigeria daga ƙasar Paris inda suka tafi ita da mahaifiyarta, shi yasa ta kwanta take ta sharɓar baccin ta kuma yanzu ta tashi ta kama girki?… sai kawai ta dago da wayarta ta shiga nemo nambar Mariya, babbar ma’aikaciyar gidan.

“Hajiya barkanmu da safiya. Ina kwana.” Muryar dattijuwar ta cika kunnenta, bata ko amsa ba tace.

“Mariya, abinci zaki kawowa Hameeda yanzu, a dafa mata duk abinda zata iya ci kawai.”

Daga cikin wayar Mariyan tace.

“Hajiya ai bana gidan, yau kwana na uku a madobi, mahaifina ne ya rasu wallahi, amma su Jamila da Aisha suna nan.”

Ta ɓata rai a lokaci guda don ta manta lokacin da suna can taji mahaifiyarta ta na fada, sai kawai tace.

“Allah ya jiƙansa.” sannan ta kashe wayar.

Ba zata yarda ƴarta taci abincin waɗannan kazaman yaran ba su tsaya a iya gyaran gidan da suke yi kawai, don ko Mama Mariyan ma da suka saba da ita tun yarintarsu ba kowanne girkinta suke ci ba, tunda Josh ya mutu shikenan kowa ya ta’allaƙa akan siyan abinci a waje tunda dama gidan ƴan maza ne ita kadai ce mace.

“Hameeda me zaki ci?”

“Mammy banda indomie.” Ta fadi hakan alamun da gaske ta gaji da cin indomien, haka yasa ta gane cewar Indomie kawai Maryn ke ɗura mata da basa nan don haka ta gyaɗa kai kawai.

Ta ajiye wayar akan table din sannan ta juya ta shiga store, ta fito da kwai guda uku a hannunta, ta kunna ruwa a kettle sannan ta fasa kwan ta soya shi cikin ƴan mintuna, ta haɗa mata tea da ruwan zafin da yayi sannan ta ɗauko biredi a fridge ta saka mata kwan a tsakiyar, ta zauna a kusa da ita tana kallon murnar dake kan fuskarta sanda ta fara cin ƙwan, har yanzu bata kai shekara hudu ba amma tsaf ta iya cin abinci da kanta, sai kawai tayi murmushi sannan ta janyo wayarta.

Ta shiga whatapp tana fara ganin yadda messages ke tururuwa har da sababbin nambobi, sai da suka gama tsaf sannan ta danna kan sako guda ɗaya mai sunan Jawad da mintuna biyu kawai akayi da turo shi.

“Baby kin dawo ko? I’m badly missing u here… Zanzo anjima kinji.” (Ina mutukar kewar ki anan.)

“Mammy nayi missing dinki.”

Muryar Hameeda ta katse ta daga amsar da take shirin rubutawa. Ta juyo ta kalle ta, tana ta cin biredin da sauri alamar da gaske yunwa take ji. Itama tayi kewarta da gaske shi yasa ma ta kasa jiran Maamah ta taho. Bayan bikin Ashraf ne suka tafi Paris ɗin ita da mahaifiyarta don medical check-up kasancewar hidimar bikin ta wajiga su da yawa, kuma satinsu ɗaya acan ta gaji ta taho don ranar da suka tafi ma Hameedan na bacci a hannun Mary ko sallama basu yi ba.

Allah ya sani ta fara gajiya da wannan rayuwar,  ba haka take hango ta ba sam, ba haka ta dinga hango abubuwa ba lokacin da mahaifiyarta dama kawayenta suka bata goyon bayan kashe aurenta ba, Maamah cewa tayi…

“Idan baki fito daga gidan nan ba kin kusa kashe kanki ki tsufa a banza Ruƙayya, ta yaya zaki zauna babu wani isasshen hutu sannan kuma ki
fara tara ƴaƴa bi da bi? Yanzu kika fara rayuwar ki fa, kina da dama mai yawa a gabanki Rukayya.”

Haka take gaya mata kullum, shi yasa ta rufe idanunta a wancan lokacin ta danne zuciyarta tayi abinda ya fito da ita ɗin, kuma har bayan aurenta da Alhaji Ahmad, tafiya take akan wadannan kalaman na mahaifiyar tata, takunsu take bi har ya kai ga mutuwar aurenta da Alhaji Ahmad ɗin shima, kuma ko a yanzu ma bata fasa gaya mata cewar komai kaddara ce ta cigaba da cin ganiyarta ba, amma ita ta sani cewar bayan wannan ƙaddarar har da ƙaddarar zuciyarta akansa shi ma.

STORY CONTINUES BELOW
Ta san duk irin halayen da zuciyarta ta shiga a gidan Alhaji Ahmad, ta san duk irin wahalhalun data fuskanta a kowanne lokaci na zamanta a gidan yadda ta dinga kwatanta abubuwa a gidanta na farko da kuma nasa tana ganin bambanci su a baiyane har suka kai ga matakin ƙarshe na mutuwar auren, don Maamah bata taɓa sani bane, amma MA’ARUF shine sanadiyar mutuwar aurenta da Alhaji Ahmad.

Kuma ko a yanzu da kowa ke kwaɗaita mata auren Jawad, ita ta sani cewar abinda ya faru shi zai sake faruwa, babu wanda zai taɓa iya cike gurbin Ma’aruf a ranta, ta so shi tun bata ma san kanta a duniya ba balle ta san menene son, ta so shi da dukkan kowanne bangare na ruhinta, don rayuwarta ma gabadaya tare dashi ta gina ta.

Iyayensu maza abokan juna ne tun da dadewa, saboda haka ba zata taba iya cewa ga ranar data san Ma’aruf ba, tayi wayo ne kawai a duniya tana iya lissafo shi a cikin abubuwan da ta sani na rayuwa, don haka kowa ya sani cewar tsananin kulawar da take yi masa shi ya janyo hankalinsa akanta shima har ya kai ga soyayyar su.

Sai dai a lokacin da ta aure shi, ta auri wani Ma’aruf din ne daban saɓanin wanda ta sani, ta san hakan don yasha gaya mata cewa Ma’aruf din data sani ya mutu babu ko da digonsa a cikin zuciyarsa, amma ta rufe idonta daga komai tace taji ta gani har aurensu ya tabbata.

Auren da tun a darenta na farko a gidan abubuwa suka yi juyin waina daga yadda take hasko su. Ta rufe idanunta a hankali tana tuna dukkan abubuwan da suka faru a waɗannan shekarun, irin wahala da barazanar da rayuwarta ta fuskanta, sai dai ashe bata san gwara su sau dubu akan abinda zata je ta tarar a gaba ba, don a yanzu ta gane abinda taso ta manta a baya, cewar duk duniya Ma’aruf ne kadai namijin daya tattara duk wasu halayen da take so a wajen namiji. Shi yasa bata son sake maimaita kuskure na uku a yanzu, bayan guda biyun da tayi a baya na fitowa daga gidansa har kuma da auren Alhaji Ahmad.

Ta riga yankewa kanta shawarar cewa ba zata sake biyewa kowa ba, ra’ayin zuciyarta kawai zata bi, zata samo yadda zata koma cikin rayuwar Ma’aruf kotawacce hanya kuwa, kuma bata ma tunanin cewa hakan zaiyi mata wuya tunda tana da abinda daga shi har iyayensa zai kassara su. Hameeda…

Tayi murmushi tana sake kallon yarinyar, lokaci yayi da a yanzu zata san waye mahaifinta!

***

A wannan daren….

Na baki amanar rai na, daiman
Yau zaki ceton raina, abadan
Kin ƙulle mini kwaɗon raina, da’iman
Ki taho, raina yana sururi numfashina kece abadan dai’man!

“Maryam dan Allah ki kashe waƙar nan, dan Allah.”

Amina ta faɗa tana hararar rediyon da Maryam din ta kunna, ta jingina ta da langa-langar langar kitchen ɗinsu yayin da ita take ciki tana girki.

“Haba mana Yaya, kin san yadda nake son irin waƙoƙin nan fa, kuma yanzu zasu cire ma don wani shirin zasu fara.”

Maryam ɗin ta faɗa daga cikin kitchen ɗin, kuma jin tayi shiru yasa ta kara da…

“Idan ana yi wallahi ji nake kamar in tashi sama don dadi, da wayarki android ce ai da har sai kin gaji da jin su ma.”

Amina ta girgiza kanta daga kan tabarmar da take zaune Hafsa a kwance akan cinyar ta tana tsefe mata kalbar da ta baɗe ta tsaf da wani sabon yashi da aka zube a layin nasu inda yara kamarta ke tururuwar wasa.

“Ni basu dame ni ba sam, kawai a yanzu ne ban ga amfanin jin waƙar ba tunda kin san abinda yake faruwa.”

Jin haka yasa Maryam ɗin tayi shiru tana cigaba da yanka cabbage ɗin dake hannunta, kuma a daidai lokacin ma suka cire waƙar, muryar wani ma’aikaci daga gidan rediyon ta fara gabatar da shiri na gaba a jerin shirye-shiryen su, amma tuno abinda ke faruwar kamar yadda Amina tace, yasa Maryam ta ajiye wuƙar hannunta ta taso ta kashe rediyon gabaɗaya.

STORY CONTINUES BELOW
A jiya da Baba ya fita zuwa kiran Hajiya Kilishin da yace, bai dawo ba sai wajen sha ɗaya saura na dare har su Hafsa da Adam sunyi bacci a sannan, wanda hakan wani abu ne sabo a wajensu, wani abu daban, saboda ba don sun kira shi a waya har ya ɗauka ba ma, Amina ta san tsaf Amma zata iya saka hijabinta a daren  ita da Aminu su fara tafiya nemansa.

Shi ba mutum ne mai dadewa a waje ba musamman idan dare yayi, abubuwa da yawa komai muhimmancin su in har dare ya raba to zai ajiye su ne sai zuwa gobe, ko hirar maza irin ta daren nan Baba baya taɓa zaman yinta, tun suna yara sun taso da sanin cewa lokacinsa da daddare nasu ne, a cikin iyalansa zai zauna ayi wasa da dariyar da a cikinta zai fahimci dukkan matsalolinsu.

Don haka a jiyan da ya kai goma sha ɗayan dare dole zuciyoyinsu suka kasa nutsuwa sai lokacin da suka ji ƙarar shigowarsa da kuma rufe kofar gidan da yayi, babu wuta a lokacin, sannan Aminu ya fara tararwa jingine da bango yana danna wayarsa.

Kuma ta cikin ɗan hasken fitilar tsakar gidan da batiranta suka gama yin sanyi, Amina ta hangi fuskarsa tattare da dukkan wani nau’i na damuwar dake fitowa har a cikin sautin muryarsa sanda yake amsa gaisuwarsu, gaisuwar da daga ita bai sake cewa komai ba, ya nufi hanyar ɗakin sa kawai ya shige.

Amma ta ɗebi kwanukan abincinsa ta bishi dasu yayin da suma kowa ya kama hanyar makwancinsa, Aminu yayi hanyar soro inda ƙofar ɗakinsu shi da Adam take, su kuma suka dauki Hafsa suka shige nasu dakin, kuma ba sai ta tambaya ba, Amina ta sani daga ita har Maryam da Aminun babu wanda yayi baccin kirki a ranar. Kuma babban abinda ya ƙara tsurar dasu shine na yadda har a yau basu ji komai ba, ko daga bakin Amman kuwa.

Baban bai ko je aiki ba a yau, tun safe ya fita zuwa gidan wansa da suke kira da Kawu mallam kuma bai dawo ba har yanzu, Amman ma kusan a daki ta yini tun bayan fitarsa, ita kadai tayi ta kai kawo a gidan bayan sun tafi makaranta, tace mata wai gyaran durowarta take yi, amma tsaf Amina ta sani cewa kayan nata data barbaza akan katifar ɗakinta ba don ninki ta fito da su ba saboda yanayin dake fuskarta kusan iri daya ne da wanda ke kan fuskar Baba tun a jiya da daddare, kuma wajen la’asar sai ga kiran Baba a wayar Aminan cewa Amman taje ta same shi a gidan Kawu mallam ɗin, wanda hakan shine abinda ya ƙara ɗaga hankalinta, da ƙyar Aminu ya shawo kanta bayan sun dawo daga makaranta kafin ya tafi wajen aikinsa shima.

Sai dai kafin ta bawa Maryam amsa, Adam yayi sallama yana shigowa.

“Salamu alaikum, wallahi Yaya yarinyar nan ƙarya take, babu wanda ya ture ta, wasan banzan su kawai suke yi, ga sauran ƙawayen nata can ma har yanzu a  kusa da yashin.”

Ya zayyano dukkan wannan bayanin daga tsaye kasancewar shi yaje ya zaƙulo ta tsakiyar masu wasan yashin. Da jin haka kuwa Hafsa tayi narai-narai da muryarta ta shiga rantsuwa tana faɗin da gaske ture ta akayi ta faɗa kan yashin, wanda kowa ya san ƙarya ne wasanta tayi daga yadda baƙin gashin kan nata ya burɗine tsaf da ƙasa.

“Ko baki ɓata kanki ba meye amfanin zuwa wajen yashi da magriba Hafsa?”

Amina ta faɗa a hankali tana kama wata jelar, don ita ko kaɗan ba ta fadan nasu take yi ba, jikinta ne kawai zaune a gidan amma hankalinta ruhinta zarya kawai suke a hanyar gidan Kawu mallam kamar tururuwa, shi yasa ko girkin daren ma tace Maryam tayi.

Allah ya sani abu na ƙarshe da zata so a yanzu shine wata matsala ta
sake gifta musu, rayuwarsu ta haska da kaloli mabanbanta a shekarun baya, sun fuskanci abubuwan da ko a labari basa son tunawa, kuma har yanzu ƙoƙarin tashi suke, ƙoƙari Baba yake don ganin rayuwarsu ta daidaita ko da ba kamar a baya ba, don haka ta yaya zasu taɓa son ace sai sun sako daga farko idan wani abu ya sake gifta musu ya a yanzu…

Har sai da ta gama wankewa Hafsa gashin nata da karkashi sannan Amma ta dawo, Baba kuma bai shigo ba sai bayan sallar isha, wanda kafin ayi hakan har Aminu ya riga su dawowa, a tsakar gidan ya tarar dasu tana sake yiwa Hafsa wata kalbar bayan ta wanke matta kan, yayi wanka yazo ya zauna a cikinsu shima yana ta mita da tsokana akan girkin da Maryam ɗin tayi, jollof din shinkafa da taliya ce da ko a ido tayi kyau, amma tunda ya zauna yake sukar abincin yana kuma kai loma.

STORY CONTINUES BELOW
“Wallahi akayi miki aure kika je kina irin wannan abincin sati daya zaki yi ya koro ki, ace jollof amma ba mai sa faman kora ruwa nake kamar dambu nake ci.”

An kawo wuta a lokacin don haka tsakar gidan yayi tar da wasu sababbin ƙwan fitilar da ya haɗa da kansa ya saka musu. Maryam da a lokacin take wanke uniform dinta daga can bakin famfo tace.

“A haka babu man kake ƙoƙarin tayar da plate din ai.”

“To idan ina jin yunwa ya zanyi? rufa miki asiri kawai nake ma wallahi, don yanzu ina tafiya wajen Isah (mai shayin layinsu) kowa sai ya gane cewar a gidanmu ba’a iya girki ba kenan, kinga masu kokarin zuwa nan gaba ma sai su fasa. Kuma Amina ita ta riga ta samu kece a ruwa.”

Maryam ta juya bayanta amma yana ganin adadin yadda gefen fuskarta ke juyawa wajen murguɗa baki tana faɗar wasu abubuwa da ba jin su yake ba. Yayi murmushi yana sake faɗin.

“Hotonki zan nemo a wayata in maida shi fari da baki in rubuta ga matar da akan girkinta aka ƙirƙiri sunan abincin ‘Ci kar ka mutu, 1987.'”

Bai saurari abinda take cewa ba ya juya ya kalli Amina da bata sanya baki a hirarsu har yanzu ba, ganin damuwar dake kan fuskarta har a lokacin ya dawo da hankalinsa kanta sosai.

“Wai har yanzu damuwa kike? Nace miki fa ki kwantar da hankalinki tun dazu. Ni alamar ma da na gani kamar wasu maƙudan kuɗi Baba ya samo shine aka tafi gidan Kawu mallam ɗin ake ta faman lissafi.”

Ba shiri dole Amina tayi murmushi tana kallonsa.

“Aminu Allah ya shirye ka, komai sai ka maida shi wasa wallahi.”

“To me yasa zaki yi ta damun kanki akan abinda bai ƙaraso ba tukunna.”

Ya faɗi hakan sanda ya juyo, idonsa ya kai kan hannun Maryam dake ta cuɗa kayan wankinta.

“Ke, idan kinyi ƙunshin nan ma haka zaki cigaba da irin wannan wankin? Kwana biyu ya goge? Kuɗina zaki taso ki dauko min Allah indai haka ne.”

“Kudin ka ai sun riga sun shigo kenan wallahi baza su dawo ba, sai dai idan nayi ƙunshin ka kankare shi.”

Amina ta kalli yadda yake murmushi yana kallon Maryam din, ta san shima ya damu, watakila damuwar ma har tafi tata, amma haka Aminu yake a kodayaushe, shi mutum ne da zai sa kaji kamar baka da wata matsala koda kuwa kana nutsewa a cikinta ne tsamo-tsamo. Lokacin da Baba ya shiga tashin hankalin karayar arziƙinsa, Amma tace Aminu shi ya ɗauki kaso mai yawa bayan addu’a wajen dawo dashi daidai.

A daidai lokacin Amman tayi sallama ta shigo, kuma kallonta kawai Amina tayi taji gabanta ya faɗi duk duk da cewar yanayin damuwar fuskar tata ya ragu akan da safe.

“Haba Amma kun barmu sai kace marayu a gidan nan, ko shirin yaƙin duniya kuka tafi yi yaci ace kun gama.”

Duk da yanayin Amman sai da tayi wani guntun murmushi tana girgiza kai sanda suka shiga yi mata sannu da zuwa, don ta saba a irin lokutan wasansa, Aminu ya riga ya mayar da ita kamar kakarsa.

A lokaci guda sai komai ya dawo daidai a gidan, da duk yawansu ji suke kamar a cikin wani fanko suke, Adam ya dawo daga siyan wainar fulawar da Maryam ta aika shi, Aminu ya kafa ya tsare cewar sai yaci rabi don wai ya san da kudinsa ta siyo, duk dauriyar Maryam sai da ta rufe idaninta ta fito da duk masifar dake cikinta wanda dama abinda yake jira kenan don haka shi da Adam suka dinga kyalkyala mata dariya.
Sannan a ƙarshe bayan sun shiga falo, wani film din indiyan da ake yi a tashar Bollywood ya ɗan daukewa Amina hankali daga wannan damuwar ganin cewar Amman ma har ta sake tana kokarin sakawa Hafsa maballi a wuyan rigar makarantar ta, tana yi tana mitar yadda Hafsan ke yawan yar da maɓallan rigar.

STORY CONTINUES BELOW
Falon ya ɗauka da sautin wakar film ɗin da ake yi lokacin da take ke kallon fuskar kowa tana murmushi, yadda Hafsa ta zuba manyan idanunta tana saurarar kashedin da Ammar keyi mata akan maballin, da yadda Aminu da Adam ke cigaba da dariya tsokanar Maryam da bata ganewa ta daina biye musu, har ma da idanun Maryam ɗin da suka cika da haushi fal! Haka take so… Haka take so rayuwa ta kasance musu a kodayaushe.

Sai dai rayuwar bata taɓa biyewa muradan zuciya, ita da zuciyar ma sunyi hannun riga, ƙaddara take kallo a kodayaushe tana bin takunta, don a lokacin da Baba ya dawo bayan sallar isha a lokacin komai ya ruguje, zuciyar Amina ta sake ruftawa cikin ramin da yafi wanda ta fito daga cikinsa zurfi. Su Hafsa suna makarantar dare a lokacin, Aminu kuma ya fita wajen abokansa sannan Maryam da wata ƙawarta sun tafi bakin titi wajen mai yin zayyanar allo kasancewar suna dab da yin sauka a islamiyya, gidan ya rage sai ita kaɗai, kamar dama ƙaddarar ta zaɓi wannan lokacin ne don ita kadai ɗin.

Amma ta kira ta zuwa ɗakin Baba lokacin da take kokarin haɗa kan kitchen ɗinsu, kiran daya tabbatar mata da cewar abinda take jira ne zai kasance kuma a hanyar zuwan tunanin ta ya ɗan ɗaure don a zaton ta ita da Aminu ya kamata su zayyane wa komai.

Ta shiga ciki lokacin da Baba ya rufe flask din nasa abincin da ya gama ci, ta zauna a daidai saitin Amma da har a lokacin ta kasa tantance yanayin fuskarta.

“Amina jiya da naje gidan Hajiya Kilishi aurenki na bayar ga ɗansu.”

Maganar ta fito daga bakin Baban kai tsaye ba wane shamaki balle kewaye kewaye, kuma ta tafi kai tsayen har zuwa cikin ƙwaƙwalwar ta, sai dai bata nutse ba, zagaye kawai ta dinga yi a zaman kan nata kamar mai jiran a buɗe mata ƙofar shiga.

Shiru ya ratsa ɗaukacin dakin, shirun da a cikinsa Amina ta kasa ko zuƙar numfashi, kuma bata damu da tsayinsa ba don har a lokacin bata gane maganar da Baban ya faɗa ba, shiru kawai tayi kamar bata ji shi da farko ba a yanzu take jira yace wani abu, sai da shi da kansa yaga bata da alamar magana sannan ya sake kiran sunanta.

“Amina..”

Ta kuwa ɗago ta kalle shi, da idanunta dake haskawa a cikin hasken fitilar ɗakin, sai ya cigaba shima kamar bai fadi maganar farko ba.

“Jiya da naje gidan Hajiya Kilishi da mijinta nayi magana ba da ita ba, kiran nasa ne ba nata ba, don da na isa gidan mota kawai tasa aka ɗauke ni aka kaini har ofishin mijin nata.

Acan na tarar dashi tare da ƙaninsa, mutane ne manya-manya Amina masu mutunci da kuma kwarjini, kuma kai tsaye suka shaida min cewar aurenki suke nemawa ɗansu, yace min Hajiya Kilishin ita da kanta ta roƙe shi alfarmar hakan saboda yarda da hankali da kuma tarbiyar da muka baki. Al’amarin ya girgiza ni kamar yadda kika ji shi a yanzu kema, amma wallahi a wannan lokacin ba zan iya kallon idanun wadannan mutanen ince musu ‘A’a’ ba don bani da wata hujja ko dalilin da zai sa in faɗi hakan…”

Ba fahimtar abinda yake faɗa Amina take ba har a lokacin, kallonsa kawai take tana jin yadda muryarsa ke karyewa da kowacce kalma daya fada, mahaifinta mutum ne da ta sani jajirtacce, ko a lokacin da yake cikin tashin hankalin karayar arziƙinsa, baya taba fasa binsu da alkawuran cewa zai inganta rayuwarsu don kar su karaya da komai. Amma a yau kiri-ƙiri take jin duk wata amon karaya a muryar tasa, amon da tak
e ji yana bin jijiyoyin ta yana tayar da tsigar jikinta bi da bi ta kowanne ɓangare.

“Na san karatu ne a ranki Amina, kuma na san ba sau daya ba sau biyu ba na sha yi miki alƙawarin cika miki wannan burin amma a kullum abinda muke tsarawa daban, wadda ƙaddara ta tanadar mana daban, kuma na san ba sai nayi miki bayanin wannan ba don a ƙananun shekarunki kin gan kalolin ƙaddarar mabanbanta, shi yasa nake son ki kalli wannan ɓangaren ƙaddarar ma, ki kalle ta idanun rahma Amina, Allah ya sani a zuciyata na yarda cewa ban miƙa ki inda zaki wahala ba, don komai halin da zan shiga a duniya ba zan yarda da duk abinda zai cutar daku ya matso kusa ba balle har in kai ku da hannu na.

STORY CONTINUES BELOW
Kin san Hajiya Kilishi kin san kirkinta, kin san yanayin gidanta, ina ga kinje kusan sau biyu ke da mahaifiyarki, saboda haka Amina wallahi zuciyata bata bani cewa zaki wahala a wannan wajen, damuwata kawai shine yunƙurin rushe miki burin ki da nayi da kuma cewar na yanke hukunci a lokaci guda.”

Yayi shiru a lokacin, Amina ta haɗiye wani abu a makogwaron ta da bata san sunansa ba, maganganun Baba a gefe suke daga cikin kanta, har a yanzu damuwar dake cikin muryarsa itace a gabanta, ita take lissafawa tana son kirga adadinta. A hankali ta juyar da idanunta kan Amman dake zaune a saitinta, kuma a hankalin idanunta suka fahimci abinda ta kasa ganewa a fuskar tata ɗazu, damuwa ce fal ke yawo a cikin nata idanun!
Wani abu da ya ƙara rikita tunaninta a lokaci guda… Don bata taba tunanin cewa irin wannan maganar ce zata saka Amma cikin damuwa itama ba, idan har zata iya tunawa tun farko dama ita tafi son zancen aurenta akan karatun da take naci, kawai ganin cewar daga ita har Baban akan son karatun suka tsaya yasa ta sallama itama, amma duk da haka tasha gaya mata cewar ba ba lallai sai ta gama karatun zata yi aure ba, to me yasa wannan maganar zata dame ta?

Sai ta sunkuyar da kanta ƙasa sannan ta gyara zamanta a hankali, tana jin nauyin idanun iyayen nata biyu dake kallonta, so take tace musu in har wannan ne abinda ya tashi hankulansu a gidan tun jiya to su kwantar dashi, don a cikin aure da zancen rashin karatun tana jin ba wanda na zata iya daurewa ba don farin cikinsu.

“Baka ƙarasa zancen naka ba ai Mallam, baka gaya mata abinda yafi komai muhimmanci ba.”

Kamar saukar ruwan sama a lokaci guda muryar Amman ta faɗa, kuma a lokaci gudan Amina taji gabanta ya faɗi, abu muhimmanci tace, kenan wani abu ne daban, wani abu da yafi girman abinda ya faɗa, wani abu da wataƙila shine dalilin damuwar dake kan fuskar Amman da ma zuwansu gidan Kawu mallam a yau.

Taji Baba ya sake gyara zamansa sannan ya kira sunanta.

“Amina…”

Ya kira kamar tayi nesa dashi, kuma ta san me hakan ke nufi saboda haka da sauri ta ɗago idanunta daga kan ƴan yatsunta ta kalle shi, ƙaguwar ya furta abinda zai faɗa na haskawa tar a cikin idanunta.

“Kiyi hakuri Amina, amma sun shaida min cewa yaron yana da matsalar taɓin hankali!”

A daidai sanda ya rufe bakinsa, a daidai lokacin aka haska wata walƙiya har da tsawa a cikin ɗakin!

***

A wannan daren….

Wajen ƙarfe tara saura a lokacin da wata mota ƙirar kamfanin ‘Elantra’ ta shigo cikin layin, ƴan yara maza dake wasa akan hanya suka dinga darewa da gudu cikin wasansu suna bawa motar hanya kasancewar faɗin layin ba zai yiwu ta wuce kuma suna wajen ba. Ko’ina yayi tar da wutar nepar da aka kawo don gaka ƙyallin sabubtar motar haskawa kawai yake yi a idanun mutane kamar an shafe ta da maiƙo.

A cikin motar saurayin dake zaune a kujerar gefe mai suna Jamilu ya nuna ƙofar wani guda inda hasken jan kwai ke ci a samansa.

“Wancan ne gidan yallaɓai, in dai gidan Alhaji Sulaiman ɗin daka kwatanta min ne to shine gidan.”

Ma’aruf dake rike da sitiyarin motar a gefen sa ya gyada kai a hankali yana kallon ƙofar gidan shima.

“Nagode sosai kaji.”

Saurayin ya washe baki.

“Ah haba yallabai ai ba wani abu wallahi. A sauka lafiya.”

Ya faɗi hakan da tsantsar murna yana ƙara rike sababbin kudin da Ma’aruf ɗin ya danka masa tun lokacin da ya shigo motar, a can farkon layin ya dauko shi, cikin dandazon wasu samari a inda ake sayar da rake. Kuma duk yadda ya kai ga kwatanta musu gidan Alhaji Sulaiman ɗin da yake nema, saurayin ne kaɗai ya gane don haka ya roƙe shi yazo ya ƙarasa dashi.

STORY CONTINUES BELOW
Saurayin ya rufe ƙofar motar daidai lokacin da kira ya sake shigowa a wayarsa, tun dauko shi dama ake kiran wayar kuma daga nambobi biyu kawai Ishaq da Mami, yana kallon yadda saurayin ma ke ta kallon wayar tun da ya shigo idanunsa na haskawa da mamakin cewa me yasa ba zai ɗauki kiran ba.

Ya ƙyale wayar yayi gaba a hankali zuwa daidai kofar gidan da yake kallo ya tsayar da motar daga gefe sannan ya janyo ta.

“Ma’aruf kana ina? Ina ka tafi?” Muryar ishaq ta fito a lokaci guda da ya amsa, sai ya koma da baya ya jingina kansa da kujerar motar sannan yayi murmushi.

“Kana magana kamar kana neman wani yaro ɗan karami, sau dubu nawa a rayuwata na ɗauki mota na fita da daddare Ishaq?”

Yaji yadda Ishaq din ya fitar da numfashi cike da takaici.

“Wai ka haukace ne gabadaya Ma’aruf? Yanzun nan fa muka dawo ƙasar nan, minti biyar kawai kayi a gida kayi wanka ka fito! Yanzu ƙarfe nawa? Tara fa ta wuce, ta yaya zaka ɗauki mota ka fita a halin da kake ciki?”

Ya sanya ɗaya hannunsa ya cusa yatsuntsa cikin gashinsa yana tuno abinda ya faru bayan barinsu Office ɗin Daddyn, tsaf ya zayyanewa Ishaq abinda Daddyn ya shaida masa tun a hanya kafin su ƙarasa gida, kuma zai iya rantsewa kamar yadda maganar ta tsorata shi haka ta daki Ishaq ɗin shima, amma duk da haka ya boye ta hanyar gaya masa cewa ya kwantar da hankalinsa kawai insha Allah zasu daidaita komai a hankali, wasu maganganu da jinsu kawai yayi a lokacin da yake furtawar.

Don suna shiga gida wanka kawai yayi ya shirya cikin wasu riga da wando duka kalar baki sannan ya dauki wata rigar mai hula (hood) da dogon hannu ita kalar ruwan toka ya dora akai, ya rufe kansa da hular amma duk da haka ana ganin sumar kansa data taru itama baƙa wuluk da ita kamar kayan.

Lokacin da ya fito falo Ishaq ya shiga wanka shima, don haka wayarsa kawai ya dauka da muƙullin motar Ishaq ɗin yayi waje, don shi tasa motar tana can gida ba’a dawo da ita ba tun ranar da al’amarin ya faru (lokacin da ya ɗauko mutumin da yayi wa duka daga Office ya kaishi wajen Daddyn.)

Ya tabbata Ishaq yaji lokacin da maigadi ya buɗe masa gate ya fita, don bai ko bar kan layinsu ba kiransa na farko ya shigo, amma bai dauka ba, sai da ya katse sannan ya lalubo nambar Sameera a cikin wayarsa ya kira. Sameera itace kusan komai na gidan nasu don itake kula da kusan harkar komai a gidan, shi yasa duk wanda zaiyi wani abu sai ya neme ta, saboda haka ya sani duk wani information in dai ya taɓa ratsawa da gidan ba lallai ne taƙi samunsa ba.
Daddy ya gaya masa cewa mahaifin yarinyar da suke zancen zata shigo rayuwarsa ɗan’uwan Mami ne kuma sunansa Alhaji Sulaiman.

Don haka kai tsaye bayan Sameeran ta gama murnar dawowarsa da kuma shaida masa cewar ai direban Hajiya Madinan da yayi clear dashi kafin ya fito titi zai kawo musu abinci yanzu, sai ya tambaye ta.

“Waye Alhaji Sulaiman a ƴanuwan Mami?”

Shirunta ya nuna alamun tambayar ta bata mamaki amma duk da haka mamakin nata baiyi tsawo ba tace.

“Ko wanda yazo jiya? Ɗan’uwansu Hajiyar Mami ne, yana ɗan zuwa dai ba sosai ba.”

Ya cije gefen lebbensa kafin ya sake tambayarta.

“Da yazo jiyan me yayi?”

“Bai wani daɗe ba Yaya, Mallam Sani ma aka saka ya tafi dashi office ɗin Daddy wai zasu yi magana.”

Da jin haka ya tabbata shine wanda ya
ke nema don haka kai tsaye ya sake tambayarta.

“Kin san gidansa?”

“A’a, amma Mami tace a Gadon ƙaya yake wai wajen layin transformer.”

Ya gyada kansa.

“Kin san sunan ƴaƴan sa?”

“Eh, Babbar dai kawai na sani sunanta Amina.”

Ya riga ya gama samun abinda yake so don haka ya gyada kansa kawai yana gode mata sannan ya kashe wayar, kwatancen daya kawo shi har kofar gidan kenan a yanzu.

“Ina Gadon ƙaya.”

Ya bawa Ishaq amsa ta cikin wayar.

“Gadon ƙaya? Wajen wa? Me zaka yi?”

“Ni da kai mun sani cewa abinda Daddy ke shirin ba ƙaramin hadari bane Ishaq, don haka zuwa nayi na warware komai tun kafin lokaci yaja da abinda ba zai taba faruwa ba.”

“What?” Ƙarara mamaki da kuma fargaba suka fito daga muryar Ishaq ɗin, kuma Ma’aruf zai rantse ya shiga girgiza kansa lokacin da yake faɗin.

“Kar kayi haka Ma’aruf dan Allah, ka juyo ka dawo. Zuwa wajen mutumin nan ba shine zai kwance komai ba…”

“Ba wajensa nazo ba don dashi da Daddy duk abu ɗaya ne. Ita nazo gani Ishaq, saboda a yanzu maganar ta koma ni da ita kawai.”

“Inalillahi wa’inna ilaihir raji’un… Ma’aruf me zaka yi?”

Salatin ya saka shi sake yin murmushi yana cije lebbensa.

“Nuna mata zanyi irin ramin da ake shirin jefa ta, nuna mata zanyi da gaske bani da hankali.”

“B, tsaya kaji…”

Dib. Ya katse kiran ya ma kashe wayar gabaɗaya. Idonsa ya sake kallon ƙofar gidan yayin da zuciyarsa ke zana masa dukkan hotunan abinda zai faru kafin ya kashe motar ya fito.

Ya sake janyo hular rigar yana ƙara rufe fuskarsa daidai lokacin da wasu yara biyu mace da namiji suka zo shiga gidan idanunsu akan shi da kuma motarsa. Da sauri ya yafito namijin alamun yazo.

Ya kuwa taho yayin da macen ta tsaya tana kallon su hannunta rike da wani abu da take ta lasa.

“Bigboy ya sunanka?” Amon muryarsa mai zurfi da taushi ya tambaya sanda yaron ya ƙaraso.

“Adam.”

Ya gyada kansa yana murmushi lokacin da ya zaro wata sabuwar ɗari biyar daga aljihunsa yana miƙo nasa.

“Idan ka shiga gidan nan Adam kace wai Amina tazo.”

“Toh.”

Ya amsa da nasa murmushin shima sannan ya juya, idanunsa ko kaɗan bama su ga kuɗin da yake bashi ba.

Da murmushin da bai san dalilinsa ba Ma’aruf ya maida kudinsa cikin aljihu yana kallon tafiyarsu zuwa ciki, ƴar yarinyar har sai da sake juyowa ta kalle shi lokacin da Adam ɗin yaja hannunta zuwa ciki.

A hankali ya dawo da fuskarsa kan katangar gidan, idanunsa na hasko masa dukkan abinda zai faru nan da mintunan dake shirin tahowa!

***

Me zai faru??

Me zai faru??
.”Kiyi hakuri Amina, amma sun shaida min cewa yaron yana da matsalar taɓin hankali!”+

A daidai sanda ya rufe bakinsa, a daidai lokacin aka haska wata walƙiya har da tsawa a cikin ɗakin! Kuma bayan walƙiyar ta ɗauke a idanun Amina, Baba ya cigaba da maganarsa.

“Wannan maganar ita ta sanya a safiyar yau dana shaidawa Kawu mallam dukkan abinda ya faru ya tara meeting din da ya sanya yinin mu a gidan, don har su Kawu Ibrahim da Kawu Hamza sun zo a yau…”

Ba shiri tasirin sunayen ya sanya Amina ta sake ɗago da idanunta ta kalli mahaifin nata, yayyen Baba hudu ne kuma shine ƙaraminsu, Daga Kawu mallam sai Kawu Abubakar da suke kira da ‘Baban kurna’ sai kuma Kawu Ibrahim da Kawu Hamzan da dukkansu biyun suke zaune a garin Abuja tare da iyalansu, don haka bata san adadin mamakin da zata iya kiyastawa ba na cewar saboda maganarta Kawu mallam ya taso su a yau tun daga can suka zo, ganin yadda Babn ke kallonta yana son fassara yanayinta yasa ta maida idanunta ƙasa a hankali yayin da hannunta na dama ya kamo karshen skirt dinta da ƙarfi.

“Amina a jiya babu irin boren da mahaifiyarki bata yi min ba akan maganar nan, dukkan ku shaida ne cewa Halima mace ce mai biyayya gare ni, don tun daga ƙuruciyarku har yanzu babu ranar da ɗayanku zai ce kunji kanmu ni da ita game da wani al’amari a gidan nan, duk abinda na fada ko nayi daidai ne a wajenta, amma a karo na farko jiya mahaifiyarki ta bijire min akan wannan hukuncin, tace bata yarda ba, tace ba ni kadai na haife ki ba itama tana da nata haƙƙin akanki don haka ba zan siyar dake ga wasu mutane ba kamar yadda ta fassara al’amarin.

Kuma bayan zuwan su Kawu Ibrahim a yau sai suma duk suka goyi bayanta, da ni da Kawu mallam da Baban kurna Amina mune kadai muka hango wannan al’amarin ta fuskar alkhairi da kuma cigaban ki wanda su basa gani. Don haka na san a shekarunki da kuma hankalin yabzu zaki iya banbance daidai da akasinta, don haka muka yanke cewar matsayar tana gare ki yanzu, duk ɓangaren da kika zaɓa shi zai fi rinjaye kuma maganar ta zauna kenan har abada, kar ki ga cewar na amsa musu acan, ki faɗi ra’ayinki Amina babu wanda zai taɓa ganin laifinki don rayuwar ki ce, mu duk ƴan kallo ne kawai.

Don haka kije kiyi tunani daga yau zuwa gobe, saboda idan har ɓangaren mahaifiyarki kika ɗauka, ina so ne muje mu sami mutanen tare da su Kawu Ibrahim kafin su koma kuma kafin wani abu ma daga ɓangarensu yayi nisa. Kije kiyi tunani Amina.”

Shikenan! Shikenan sai duk bayanin ya ƙare da wannan jimlar, lokaci kuma ya fara bugawa da adadin awannin da zasu tadda goben, goben da Baba ta furta kamar tsawonta na shekara guda ne.

Taji lokacin da ya miƙe ya zo ya wuce ta, taji shi ya zura takalmansa daga waje sannan taji ƙarar takunsa na nufar hanyar soro, sai kawai ta rufe idanunta gabaɗaya tana hadiye wani abu da bata sanshi ba a maƙogwaron ta.

“Duk abinda mahaifinki ya fada haka ne ya faru Amina, kuma ba komai yasa nayi hakan ba sai don nemar miki ƴancinki…”

Da wani sassanyan amo muryar Amma ta maye gurbin ta Baban tun kafin ta bude idanunta

“… Ƴancinki nake nemar miki Amina, don ni na hango abinda mahaifinki ya kasa ganowa, mutanen nan masu kudi ne da gaske, kuma duk tsananin kirkin mai kuɗi a zaune yake cewar baya taba son mu’amalar rayuwarsa da talaka kamar mu, zasu taimaka, zasu yi zumunci kamar yadda ita wannan Hajiya Kilishin ke yi amma aure Amina, aure babban abu ne da shine linzamin rayuwarka ta duniya har zuwa lahira, don haka kowa ya sani cewa hakan ba ƙaramin abu bane ga rayuwar mutum da zai haɗa shi da kowa.

Da ke muka je auren wani ɗansu a shekarun baya da suka wuce, kinga matar daya aura ai, kinga irin tarin dukiyar ubanta da danginsu, don ba a banza bahaushe ke cewa ‘ƙwarya tabu ƙwarya ba… Kowa daidai dashi yake nema. Saboda haka Amina ko makaho yaji wannan zancen ya sani cewa mu ba daidai da mutanen nan muke ba, sun nemi aurenki ne kawai don son zuciyarsu…”

STORY CONTINUES BELOW

Sai tayi shiru kamar tana kokarin haɗewa wani abu da ya taso mata ƙirji yayi sanadiyar canjawar muryarta.

“Amina, ciwon yaron nan na ‘Hauka’ ne na tabbata suka yi masa ado da matsalar ƙwaƙwalwa kawai, kuma kin san wannan ba ƙaramar magana bace, kowa ya sani, su ma sun sani shi yasa basu tunkari kowa da wannan zancen ba sai mu, mu talakawa da aka mayar kamar ba mutane ba, mahaifinki dasu Kawu mallam suna ta danganta al’amari da ƙaddara, alhalin basu ƙara binciken komai akan yaron nan ba, amma ni nace idan har ƙaddarar ce me yasa basu kai ta ga irin ƴaƴan masu kudin da ɗaya ɗan nasu ya aura ba? me yasa sai a yanzu ne irinmu zasu yi musu amfani… Na sha gaya miki masu kuɗi basa kallon kowa sai kansu, suna ganin tala
ka kamar shi ya zaɓawa kansa rayuwar sa, kamar dama Allah ya halitto shi ne kawai don ya kawar musu da matsalolinsu.

Rayuwarki zaki sadaukar musu idan har kika zaɓi tafiya Amina, don aure ba karamar gwagwarmaya bace ko da mutum mai hankali kuma wanda kake so balle babu duk biyun a naki, rayuwarki zaki sadaukar musu a banza, dukkan wani mafarki da burinki sai ya mutu wajen yi musu bautar da baza su san kina yi ba, don wannan sigar auren a wajensu, bata da banbanci da cewar siyen ki suka yi…”

Ta sake yin shiru sakamakon yadda Aminar ta runtse ido da tasirin maganar, amma duk da haka sai ta cigaba.

“…Annabi yayi gaskiya da yace kudi sune masifar ƙarshen duniya, a karo na ba adadi wallahi na sake yarda da hakan, don ban taɓa tunanin cewa mutum kamar mahaifinki zai iya faɗawa cikin tarkonsu ba…”

Wannan karon kalaman suka daki zuciyar Amina da tasirin da yasa a lokaci guda ta ɗago ta kalle mahaifiyar tata tana girgiza kai. Ta sani dukkan abinda ta faɗa gaskiya ne, amma ba ta yarda da wannan hasashen nata na ƙarshe ba, ba zata taɓa yarda cewa kuɗi zasu rufewa Baba ido har ya mika ta ga inda zata cutu ba, haba mana! ta manta ne? Ta manta duk wannan tarin ƙaunar tasu dake tare dashi? Ta mata tarin sadaukarwar da yayi a rayuwarsa saboda su kawai?

Sai dai kallon da Amman ke mata yasa ta sake sunkuyar da kanta a hakali tana rufe idanunta da ƙwalla ta taru a cikinsu, dukkan maganganun da Amma ta fada gaskiya ne ta sani amma har a lokacin ta kasa gasgata zancenta na karshe don ta sani cewa ko da numfashinta na ƙarshe a duniya ne zata yarda cewa ba zai taɓa mika ɗayansu ga inda zasu cutu ba… A kullum shi mai son gyara rayuwarsu ne.

Ta kai hannu tana share idanunta lokacin da Amman itama tace.

“Kije kiyi tunani zuwa goben Amina, ki auna kowanne ɓangare ki ga wanda yafi rinjaye, ni dai a matsayina na mahaifiyarki kuma mace kamar ki na gaya miki abinda nake ganin shine daidai”

Ta rufe bakinta daidai lokacin sallamar su Adam daga makarantar dare ta kwararo a tsakar gidan. Shi da Hafsa ne suka karaso har cikin dakin bayan sun duba falon da babu kowa, da sauri Amina ta saka bayan hannunta ta share hawayenta kafin su ƙaraso da hayaniyarsu.

“Amma kaina ciwo yake yi.” Muryar Hafsan ta ambata tun kafin ta shigo ɗakin da kalar ƙorafinta na kullum yayin da Adam shima ya shiga ƙaryata ta.

“Amma wallahi makaranta ce bata son zuwa gobe ƙarya take yi, yanzun nan fa har kusan faɗa fa suka yi ita da wasu a wajen ƴar tsohuwa, ba don nazo da wuri ba da ko kafi-kazan data siya ma baza ta samu ba.”

Babu wanda ya lura da yanayin dakin a cikinsu sai bayan da suka ga Amman bata basu amsa ba, tayi shiru kawai tana kallonsu, wanda hakan yasa Adam yasha jinin jikinsa, ya sake kallon fuskar Amman da kuma ta Amina ya tabbatarwa kansa cewa basu yi daidai da lokacin da ya kamata ba, don haka ya nufi kofa, sai dai har yasa ƙafarsa ɗaya a waje ya tuna da saƙon da aka bashi.

“Au na manta wallahi, Yaya in kin fito ana kiranki a waje.”

Da haka ya juya yayi hanyar Kitchen ayana fadin zai sake zuwa yaci abinci. Amina ta ƙara share hawayen idanunta, Abdallah ne ta sani, don dama tun jiya take tsammanin zuwansa dama don ta sani lokacin komawarsa makaranta yayi, sai dai yazo a lokacin da take jin bata son ganin fuskar kowa, maganganun Baba da Amma sun riga sun cike duniyarta ta yadda bata tunanin a cikin zuciyarta ma akwai wani waje komai kankantarsa da zai sake ɗaukan wani abu a daren yau.

STORY CONTINUES BELOW

“Ki tashi kije, ganinsa zai sa ki sake yankewa kanki hukuncin da ya dace Amina, daga daren yau zuwa gobe kawai kike dashi…”

Muryar Amman ta sake faɗa, taji kamar tayi ihu lokacin data ɗago ta kalle ta, Hafsa na tsaye har yanzu sai kallonsu take alamun rashin fahimta akan fuskarta, kuma daga yanayin Amman ta san ko ihun tayi ba zata canja maganarta ba don haka ta sake goge hawayen da bayan hannunta sannan ta miƙe a hankali tana jin yadda kowa ce kalma da iyayen nata duka furta tayi mata tsaye a zuciya bayan nauyinsu da take ji a kafaɗunta.

Akan igiyar tsakar gida ta tarar da hijabin da Maryam ta goge ɗazu don gobe za’ayi musu hotunan photo album ɗin sauka a islamiyyar su, na sallar idinsu ne, dogo har ƙasa kalar ruwan ƙasa, ta jawo shi kamar zata saka amma sai ta fasa, ta nufi ƙofar soron ta tsaya, ziciyarta na ƙoƙarin ƙulla ta yadda zata yiwa Abdallahn bayanin komai, komai ɗin da itama bata gama sani ba, taji ɓangare da yawa a cikin ƙwaƙwalwar ta na gaya mata cewa fitar ta a wannan lokacin ba alkhairi bace, don haka sai kawai ta dawo ta kira Adam dake karo da kwanuka a kitchen.

“Adam zo.”

Ya juyo riƙe da plate yana kallonta kafin ya ajiye shi ya biyo bayanta, suka koma har hanyar soron.

“Adam dan Allah kaje kace masa bani da lafiya sosai, ya dawo gobe ba zan iya fitowa yanzu ba.”

Kamar ya tambaye ta dama ta sanshi ne tunda bai taba ganinsa a gidan nasu ba, sai kuma kawai ya fasa ganin yadda idanunta suka yi ja ya san ba lallai taso tambaya a lokacin ba, ya juya ya fita, ita kuma ta tsugunna a wajen tana ƙara share hawayenta ba tare da ta fahimci kuskuskuren da tayi ba.

Lokacin da Adam ya fita, Ma’aruf na tsaye har a lokacin kuma ganin tahowarsa yasa ya ɗago da hannayensa duka biyu a hankali yayi baya da hular (hood) dake kansa, fuskarsa ta fito cikin hasken ƙwan fitilar barandar gidan,

“Yaya tace wai dan Allah kayi haƙuri bata da lafiya ba zata iya fitowa ba ka dawo gobe.”

Ba shiri wani murmushin ya subuce a fuskar Ma’aruf, For real? Shine ma zai dawo goben? Bata san me ta tsallake bane, sai kawai ya gyada kansa tare da faɗin.

“Okay.”

Har Adam zai juya yayi saurin tsayar dashi.

“Kana ji ko, ɗan tsaya ka bata wannan.”

Adam ɗin kuwa ya tsaya, shi kuma ya buɗe ƙofar motar ya buɗe aljihun dake jikin dashboard ya zaro wata jotter da biro daya san Ishaq baya taba rabo dasu motarsa a matsayinsa na lawyer, ya yago takarda guda ɗaya ya ɗora daga saman yayi wani rubutu layi biyu da rabi kawai sannan ya rubuta sunansa daga ƙasa. Ya kalli abinda ya rubuta din yayi wani guntun murmushi kafin ya juyo ya mikowa Adam ɗin

“Nagode sosai kaji.”

Ya faɗa yana sake yi masa wani murmushin, da fara’a shima Adam ɗin ya amsa yana masa a sauka lafiya kafin ya juya, shi kuma ya jefa kansa baya jikin motar yana cusa hannunsa na hagu cikin gashin kansa.

Ba haka yaso ba, amma hakan ma yayi… Ya riga ya gama da yarinyar nan ya sani, don abinda su Baffa ke tunani ba zai taɓa yiwuwa ba.

Aka ɗauke wuta a daidai lokacin, unguwar tayi wani irin duhu dinɗim kamar yadda yake jin zuciyarsa! Don haka ba shiri ya kunna motarsa ya shiga ya bar wajen.

“Gashi yace in baki.”

Adam ya faɗa a cikin duhun soron bayan ya koma, Amina tayi saurin sake goge hawayenta kafin ta karbi takardar ba tare da tunanin komai ba don ta san ba wani abu bane Abdallahn ya iya rubuto mata fatan samun sauƙi dama, ta damƙe ta a hannunta sannan ta miƙe ta bi bayansa. A kitchen suka tadda Amma na kokarin kunna kyandir guda
biyu Hafsa kuma na sake zuba abinci itama, kuma bayan ta amsa sallamarsu sai ta miƙowa Amina guda ɗayan yayin da Adam ya shiga fadan cewar Hafsan ta dauki farantinsa.

STORY CONTINUES BELOW

Ta wuce ɗakinsu kai tsaye, ta ajiyewa Maryam Hijabin akan katifarta sannan ta manna kyandir din akan wata kwalbar magani, a gabansa ta tsugunna hannunta rike da takardar, daga jikinta har zuciyarta daban take jinsu, wucewar awa guda kawai ta tafi da Aminar da take a baya, a yau da safe ma… tana jin zata rubuta dukkan abinda ya faru a daren yau a wajaje da yawa ta yadda ba labarinsa ba zai taɓa gogewa ba.

Ta sake goge wani hawayen sannan ta buɗe takardar a hankali, zuciyarta cike da fatan ta karanta wani abu mai rangwame daga Abdallan ko yaya ne wataƙila ya iya zaftare wani ɓangare na damuwarta, sai dai kuma rubutun da idanunta suka gani a jiki shine abu mafi tashin hankali fiye da duk maganganun da rayuwarta taci karo dasu a wannan daren.

Kar ki yarda da auren nan, da gaske ne abinda suka faɗa miki, I’m a psycho, zan kashe ki idan har kika shigo rayuwata. Ma’aruf B.

*****

11:15Am.

“Mai gaskiya kaci abincin kasha magunguna naka?”

Muryar Hajiya Kilishi ta tambaya cikin wayar dake kare a kunnenta, kuma a cikin wayar aka bata amsar data sa ta gyaɗa kanta kafin ta sake cewa.

“Zan kira Ishaq, zamu yi maganar komai dashi, idan zaka shigo kawai ka taho da magungunan duka.”

Har tayi shiru sai kuma tace.

“Dan Allah Ma’aruf kafin ka shigo kaje ka aske gashin nan dan Allah, ko ɗazu da na shiga wajen Inna Danejo abinda ta fara tambayata kenan.”

Amsar da Ma’aruf ɗin ya bayar mai tsawo ce, don ta dade tana saurarensa kafin tace,

“Shikenan idan ka shigo kayi mata wannan bayanin da kanka, akwai faten dankali a ɗaya daga cikin kwanukan abincin nan ka ganshi?”

Ya fadi abinda ya saka ta yin dariya kafin ta sake cewa.

“To aci lafiya, sannan idan ka wuce 1 baka shigo ba, zaka ganmu gabadaya gidan mun taho.”

Ya fadi wani abun da ya kara saka ta dariyar da tafi ta farko tana fadin.

“Ai da ƴanmata zamu zo sai suyi muku sharar.”

Da haka suka yi sallama, tana sauke wayar daga kunnenta.

“Wallahi na dade ina gaya miki Hajiya, da irin mahaukatan secret agent din nan na turawa ya kamata ki samu aiki, ko banza dukkanku zaku amfana da juna, ke da kudinsu su kuma da kissa irin taki.”

Cewar Hajiya Salamatu, wata hamshaƙiyar ƴar gayu dake zaune daga gefen Hajiya kilishin.

Wajen ƙarfe goma sha ɗaya ne na safe a lokacin, kuma kasancewar ranar ta asabar ce kowa yana nan, gidan cike yake da hayaniya da kuma hada-hadar masu aiki da suka gama abincin safe suke kokarin ɗora na rana.

A cikin ɗakin da suke zaune an ɗage labulayen tagogin dakin guda biyu iska da hasken rana na shigowa yayin da a lokaci guda kuma filutulun ɗakin suke a kunne haɗe da fankar da aka ware har ƙarshenta. Hajiya Kilishi dake zaune itama cikin nata adon daidai misali ta ajiye wayarta a gefe sannan ta kai hannu ga robar ketchup ɗin dake kan katon farantin da aka zubo musu kayan breakfast akai, ta sake zubawa a farantin dankalin turawan dake hannunta ta sannan tace.

“Idan har zaki samo min me zai sa in ƙi sanya hannu Hajiya, kin san ai waje in dai da raɓa da kuma sirri ba na ƙinsa.”

Hajiya Salamatu ta sake kai kofin shayinta baki tana girgiza kai.

“Ai kullum ina gaya miki al’amarinki abun mamaki ne Kilishi, wallahi duk yawona a doron duniya ban taɓa ganin mace irinki ba, yadda ba boka ba malam, kike juya komai da ɗan yatsa guda kuma hankalinki a kwance.”

STORY CONTINUES BELOW

Hajiya Kilishin tayi wata guntuwar dariya alamun ta saba da jin hakan daga bakin ƙawar tata.

“Mu bar wannan zancen yanzu Salamatu, mu tafi ga abinda yasa na kira ki.”

Sai da Hajiya Salamatun gyara zamanta a hankali tana ajiye kofin daga durowar gefen gadon, idanunta kaɗai zaka kalla ka san cewar da gasken ta tattara dukkan hakalinta ga abinda Hajiya Kilishin ke ƙoƙarin ɗorawa akan tsohon shirin da suka saba.

“Auwalu yana riƙe da ma’aikata har yanzu, sannan wannan auren kamar ya tabbata ne mu ajiye shi a gefe, me kika cigaba da shiryawa daga ƙarshen ƙullin da muka yi wa zaren, me kika tsara?”

“Tsari na da yawa Salamatu, farko dole ne in fara sakin manufata tun yanzu akan ita yarinyar, dole ne ta ɓoyayyiyar hanya in ƙara bincike akan zuciyarta ta yadda zan fara ƙawata tunaninta da miƙakkiyar hanyar da zata ƙulle ta a gaba.

Na biyu, dole ne a yanzu inyi taku mai nisa daga mahaifin yarinyar da kuma maigidana, zan ƙara zame hannuwa daga al’amarin na in zama ƴar kallo ta yadda ko ƙura ba zata hau kan farina ba, balle wani ɗigo na baƙi, amma zan kusanci mahaifiyar yarinyar dole, don haka ne ingantacciyar hanyar da kowa zai kalla a yanzu.

Sannan na san Ishaq zai shaida min dukkan sabon tsarin magungunan Ma’aruf, don haka wannan ma babu matsala, komai zai cigaba ne daga inda ya tsaya. Game da auren su Salma kuma wannan komai tsaftatacce ne don kin san bana taɓa haɗa ƙasa da gari waje guda. Daga Auwalu kuma, mun sake bude wani sabon account zai loda kudaden wancan watan…”

Ta faɗi hakan sannan tayi shiru a hankali, ramin bakinta na wasa da wani murmushi mai armashi.

“A yadda lissafin komai yake Salamatu, shekara guda tayi yawa kafin komai ya ɓare!”

Hajiya Salamatun tayi nata murmushin itama yayin da take kallon fuskarta.

“Na fahimta Kilishi nima na lissafa wannan adadin tun a wancan karon. Sai dai kin san a kullum nice mai hasko miki ƙalubalen da ke bakya ƙirgawa dasu. Ƙalubalen da duk zare ɗaya ne ya ƙulle su suke reto a jikinsa, ƙalubalen kuma da shine raunin ki Kilishi, shi kadai ne raunin da na san ubangijin ya halitta a ƙirjinki, Ma’aruf!”

Murmushin da kullum ke sauka a fuskarta duk sanda Hajiya Salamatun ta furta mata magana makamanciyar wannan shi tayi a yanzun ma, tayi shi tana ajiye farantin hannunta, ta jawo tissue a gefe ta goge maiƙon hannunta sannan ta miƙe, ta isa ga makekiyar wardrobe ɗin dake ɗakin ta buɗe waje na biyu, a ciki kayan Ma’aruf ne wanda ya cire daga jikinsa ranar da aka tafi dashi tafi London ba’a hayyacinsa ba.

A gaban kayan akwai dukkan tarkacen dake cikin aljihunsa a wannan ranar, muƙullin mota, chewing gum, chapet, biruka da kuma wallet ɗinsa, wallet ɗin ta dauko sannan ta rufe wardrobe ɗin ta dawo gaban Hajiya Salamatu ta miƙo mata ita.

Sanin halinta sarai yasa Hajiya Salamatun ta karɓa ba tare da ta tambaya ba, ta ware cikinta, kuma bayan tudun kuɗin da taji a ciki da kuma jerin credit cards, wani hoto da aka maƙala a jiki shi ya ɗauki hankalinta, samari biyu ne a jikin hoton wanda kallo ɗaya kawai zai shaida maka cewar wa da ƙani ne, don bayan girman da ɗaya yafi ɗaya, akwai kammani sosai a fuskarsu. Suna dariya mai cike da nishaɗi yayin da babban ke miƙo hannunsa kamar zai naushi
ƙaramin.

Ƙaramin Ma’aruf ne Hajiya Salamatu ta sani, babban kuma…

“Jamal…” Sassanyar muryar Hajiya Kilishi ta furta tare da tunanin Hajiya Salamatun.

“Jamal shine ƙalubale na kuma shine rauni na Salamatu, shi yasa na rufe idanuna nayi abinda ya kamata akansa, don haka kamar kullum zan gaya miki cewa ki yarda bani da wata matsala a duniyar nan yanzu idan ba kuma ƙaddarar ubangiji ba. “1

Ta fadi hakan yayin da take tsaye akanta, Hajiya Salamatun ta ɗago ta kalle ta, wannan murmushin na baya ya tafi, idanunta sun canja ta yadda ko ɗigon raha babu a cikinsu.

STORY CONTINUES BELOW

“Kar ki ƙara lissafa Ma’aruf a cikin ƙalubale na Salamatu, don kinfi kowa sanin matsayinsa a waje na.”

Kuma a cikin idanuwan nata, Hajiya Salamatun ta shiga hango abubuwan da suka faru wasu tarin shekaru da suka wuce!

******

11:20 Am

“Inalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Wai baka da imani ne Ishaq? Tun da na tashi kake ta masifa a gidan nan kana mita, nace maka wallahi ko ganin yarinyar banyi ba balle inyi mata wani abu, do I have to bury myself before you believe?” (haƙa kabari zanyi in shiga kafin ka yarda dani?)

Ma’aruf ya fada a lokacin da yake zaune kan dining table din falon gidansu, inda ya samu ya ture wasu litattafai da kuma kayan wankin Ishaq ya dora plate ɗin abincin da yake ci.

Ishaq na tsaye daga cikin falon shima rike da nasa kofin shayin da kuma remote ɗin da yake kokarin chanja channel daga ta labaran da Ma’aruf ya kai.

“Ka gayawa wani ba ni ba, na san halinka sarai B, hankalinka ba zai taba kwanciya haka ba idan har ba kayi abinda kake so ba. I’m just advising you (shawara nake baka) komai zai iya faruwa idan har maganar nan ta lalace kuma Baffa ya san da saka hannunka.”

Ma’aruf yayi murmushi a hankali sanda yake jin zafin faten dankalin dake sauka cikin maƙogwaronsa wanda motsawar Adam’s apple ɗinsa kadai zai shaida maka hakan.

“Wai ina zaka je ne ma? Yau asabar fa?”

Ya canja akalar zancen nasu ba tare da ya kalle Ishaq ɗin ba, don tun da farko kayan jikinsa sun riga sun nuna masa cewa Office zai je. Babu adadi na lokutan da zuciyar Ma’aruf ke motsawa a duk lokacin da yaga Ishaq na yin wani abu da ya danganci aikinsa, aikin da yake so kuma abinda shine mafarkinsa ya fito dashi zahiri kuma yake yi ɗin. Shi nasa burin da kuma mafarkin sun dade da kaɗewa shekaru goma da suka wuce. Abinda yake yi a yanzu, ba rayuwarsa bace ko kaɗan, wata rayuwa ce da ta zama dole ya ƙarasawa mai ita.

“Thanks to you, nayi missing tarin ayyukan da dole inje in san halin da ake ciki kafin Monday, Idan ciwon ka ya sake tashi Ma’aruf wallahi ka nemi mai raka ka asibiti.”

Murmushi Ma’aruf keyi har a lokacin yana cigaba da cin abincinsa yayin da ƙamshin curry da kuma naman dake cikin abincin ke gauraye ɗakin, ya kai hannu yana cusa yatsunsa cikin gashin kansa, wani abu da ya riga ya zama ɗabi’arsa kafin yace.

“Ka san me Mami take ce min yanzu? Wai inyi aski kafin in shiga gida, don Inna Danejo na tashi da safen nan abinda ta tambaye ta kenan.”

Ba shiri Ishaq shima yayi nasa murmushin kafin ya gyaɗa kai don har ya hango irin rigimar da za’ayi da Ma’aruf din da ba zaiyi askin ba da kuma Inna Danejon da ba zata haƙura, don kafin tafiyarsu London ta kawo dalilai sun fi ashirin na cewar rashin lafiyar Ma’aruf tana maƙale da gashin kansa ne, Baffa ne kawai bai bada goyon baya ba da tuni sai dai Ma’aruf ɗin ya tashi yaga kansa ɗal!

“Hular sanyi kawai zaka dauka, in zaka shiga wajenta ka saka kace anyi askin ba’a bude kan ne.”

Ya faɗi hakan lokacin da ya gama neman abinda yake so a jikin Tvn don haka ya ajiye remote din ya juyo ya kalle shi.

“Za’a kawo maka motar ka ne?”

“Eh, na kira direban Office tun dazu nace yaje ya ɗauka ya kaita Carwash, I’m sure kafin 12 zai dawo da ita.”

Ishaq ya gyaɗa kansa.

“Shikenan mu haɗu a gidan, nima can na nufa idan na tashi insha Allah.”

Ya faɗi hakan yana juyawa hanyar ƙofa, idanun Ma’aruf suka bishi da kallo yana tunanin wani abu, kuma sai da ya isa ƙofar da zata fitar dashi waje har ya buɗe ta sannan yayi saurin kiran sunansa.

Ya kuwa juyo a take kamar shima dama jiran kiran yake yi. Ma’aruf ya girgiza kansa yana kallonsa.

“Wallahi ban ga yarinyar ba Ishaq, kawai dai na bata wani saƙo ne da na san dole ba zata taba yarda ba.”

****

11:30Am.

“Na yarda!”

Kalaman guda biyu suka fito daga bakin Amina lokacin da take tsugunne a gaban iyayenta guda biyu da dukkan fuskokinsu ke haskawa da tsananin mamaki.

Tata fuskar fayau take, ba abinda zaka iya tsinta a jiki.

Ta gyara zamanta sannan ta sake maimaitawa kamar wani ya sata.

“Na yarda zan aure shi Baba.”

Maimaitawar ta fiyo tare da faɗowar flask ɗin ruwan zafin da Amma ta ɗauko don juyewa Baba ruwan wanka, ya subuce a hannunta ya faɗi har ƙasa, kwalbar ciki ta tarwatse yayin da ruwan zafin ya fallatsa akan dukkaninsu.

*

Me kuke tunani yasa Amina ta yarda da auren Ma’aruf?1

Wacece ainihin Hajiya Kilishi?

Me ya faru da Jamaal?4

Shekarun cikin labarin sun wuce da wasu abubuwa da zamu fara kwance su daga Babi na gaba insha Allah…☺️

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *