FARHA
CHAPTER 15
Daddy ne ya dauko ruwa a frigde ya bude ya tsiyaya a hanunsa ya fara shafawa King Hafeez a fuskarsa har suka samu ya fara sauke ajiyar zuciya ya bude idonsa qir a kanta itama shi take kallo tabbas tasan fuskarsa ba,a hoto ba a zahiri amma takasa tuna inda tasanshi, miqewa yayi ya zauna tare da sake sanya hannayensa ya ruqo nata ta matsa kusa dashi har numfashinsu na bugun najuna suna qarewa juna kallon, hawayene suka kwace a fuskar King Hafeez ya sake matsarta sosai yace
“Wai da gaske kece a gabana Farhana ke nake gani meyasa akacemin kin mutu bayan kina raye meyasa kika gudu kika barni cikin mawuyacin hali Farha meyesa Farha ina cikina dake jikinki Queen Abdallah shine dana don Allah kicemin shine kada kice bashi bane plz Queen ya akayi hakan ta faru….?” ya qarasa mgnr cikin shaqewar numfashi, kallonsa takeyi har yanzu tanason tunano inda ta sanshi da inda kalamansa suka dosa amma ta kasa kawar da kanta tayi tare da miqewa zatabar gurin yayi saurin sake kamota ta dawo ta fada jikinsa ya matseta a qirjinsa yace “bazanyi sakacin da zaki sake yimin nisa ba Farha” wayarsa ya zaro a aljihunsa ya danna wata number cikin rawar murya yace “ Baffa naga Farhanah a Kaduna” sauke wayar yayi ya sake kiran wata number ya kuma cewa “Hajiya farin cikina ta dawo naga Queen dita a Kaduna” kashe wayar yayi ya fara sunsunar wuyanta kamar wani bunsuru abinda yabawa kowa dake parlourn kunya kenan musamman Sarki da yake kusa dasu yanason gasqata abinda yake faruwa dasu.
Gyaran muryar da Daddy yayi shine ya dawo da King Hafeez cikin hayyacinsa saboda gaba daya ya susuce baimasan me yakeyi ba, zubawa Daddy ido yayi hakanne ya bata damar qwacewa daga ruqon tsaurin da yayi mata ta matsa kusa da Momy ta zauna Maryam ma ta zauna kusa da ita miqewa KING HAFEEZ yayi ya matsa kusa Farhan tashi Maryam tayi ta
bashi guri saboda ta lura kamar baa cikin hayyacinsa yakeba zama ya kumayi kusa da ita ya dora kansa a kafadarta ya sake sakin sabon kuka me narkar da zuciya haka kawai taji
zuciyarta ta karye itama ta saki kukan janyota ya sakeyi jikinsa yana shafa bayanta a
hankali yanason yayi mgn amma ya kasa daqyarya iya hada kalmomi yace. 9
“Sun cutar damu Farha an cutar da rayuwata an rabani da farin cikina da kwanciyar hankali na sama da shekara goma sha biyar kawai akan wani rudun duniya Farha meyasa Amnah tayimin haka me nayi mata data cutar dani haka na rufa mata asiri ita ta tonamin nawa na share Mata hawayenta ita ta zama sanadin zubar nawa hawayen na sanyata farin ciki ita ta sanyani baqin ciki meyasa amma ta zama butulu mai saka khairi da sharri Allah ya isana Amnah kin cutar dani bazan taba yafe miki ba Amnahu.” dago kanta tayi ta kalleshi ido cikin ido tace “ya akayi kasan sunana? Wacece Amnah? Metayi maka? Kaidin waye meye alaqata dakai dana kasa mantawa dakai?”
Zuba mata ido yayi yana mamakin furucinta Daddy ne ya katse shirun da cewa “nima tambayar da nakeson yimaka kenan Mai martaba meye alaqarka da Farhanah?” Kallon Daddy yayi cikin hawaye ya sauka ya zame qasa yace “Matata ce ta sunnah Daddy idan baka manta ba shekaru 16 baya nazo Kaduna gurin Nasir na kawo masa katin gayyatar daurin aurena wanda zanyi a karo na biyu to Farhanah itace matar dana aura munyi zaman lfy so da aminci kafin lkcn da qaddara tasa Farha tayimin nisa lkcn da abin ya faru tana dauke da tsohon cikina a jikinta,..” Nan ya kwashe komai ya fada musu kana ya dora da cewa.
“Nasir yasani na shiga mayuwacin hali wanda har yanzu shine yake dawainiya da rayuwata Daddy lkcn da Farha ta bata iyakar binkice Media da hukumomin tsaro babu irin wanda bamuyi ba amma babu nasara qarshe ma aka tabbatar mani da a ranarda taje tasha motar Jos ta hau kuma motar tayi accident mutanen ciki sun qone babu wanda ya rayu hakanne yasa na fidda tsammani da sake ganin Farha amma zuciyata taqi yarda Farha ta mutu duk inda kasani a qasarnan dama maqotan qasashe babu inda banjeba kozan ganta amma shiru wannan dalilin yasa nima na susuce na zama kamarzararre wlh badan qarfin addu’ar da Hajiya ta da mahaifin Farha suka duqufa yimin ba da tuni na zama mahaukaci na gaske haka shekaru sukayita taflya na zama wani iri niba namiji ba niba mace ba tun lkcn da Queen ta bata muka fara takun saqa da matata Amnah takasa hqr da yanayin da nake ciki ta manta cewa duk duniya burina bai shige Farha da cikin jikinta ba tasha fadamin nida Farha saidai idan ana aure a lahira muyi lkcn
da Farha ta shekara uku da bata lkcn ne Nasir yazomin da mgnr Abdallah tunda ya fara bani lbrn yaron naji ina tsananin qaunarsa qauna irintajini a kuma daidai lkcn ne ya turamin picks din yaron nikuma na nunawa Amnah tana ganinshi tahau bala’i wai wata nayiwa ciki ta haifamin dan shege ita kuma nakasa yimata ciki ai garama da Farha ta bata kumadai duk tsiyata da baqin cikina saidai nayi tunda shege baya gadon sarauta.
Munsha rikici da Amnah duk yanda zan wayar mata dakai taqi ganewa qarshe ta hadani da mahaifiyata Hajiya da taga hoton yaron itama cewa tayi dole akwai abinda yake akwai tsakanina da Abdallah wannan kamar dake tsakanina dashi ba iyakar ta halitta bace kamace ta jini naso mahaifiyata ta fahimceni amma taqi qarshe sai tace tunda abin nawa iskanci ne ba lalura bace to dole tabani wata uku nayima Amnah ciki idan ba haka ba saita fiddani cikin yayanta, lamarin daya tayarmin da hankali harna fara tunanin anya kuwa Hajiya ita kadaice a cikin hayyacinta take kuwa? Banida amsa saboda haka nabada qaimi na dage akan saina yiwa Amnah ciki bisa sonbin umarnin mahaifiyata amma Ina abun ya faskara saboda bani nake bayarwa ba Allah ne harwata uku ta cika komai ya qara lalace min Hajiya tayi fushi me tsanani dani Amnah kuma ta sami damar rainani ban isa nayi mata mgn ba saitace min dalla karka takuramin sullutu kawai a haka gaka kamar namijin gaske amma empty kake baka da ruwan bada haihuwa saina jaraba wannan abu yana yimin ciwo sosai amma babu yanda zanyi.
Muna tsaka da wannan rigimar kuma wata ta bullo na dade dajin lbrn Amnah tana lesbian amma ban tabbatar ba kuma ban yarda ba saboda bantaba gani nasan dai tana yawan baqi mata to a wannan lkcn saboda rainin daya shiga tsakaninmu saita daina shakkata ta fara fito da halinta, ranarwata asabar ban fita ba ina part dina maqale da hoton Farha ina shafa tudun cikinta ina kuka kawai sai naji zuciyata tana rayamin na Kira Amnah banyi tunanin komai ba na kirata amma bata dagaba kira yafi nawa miqewa nayi jikina babu qwari na nuf‘l part dinta ina shiga naga bayin dake sashin sunata yimin kallon tsoro amma basu da damar dakatar dani harna dangana da qofar wlh da nasan abinda zanje na tarar kenan da bazan qarasa ba ina bude qofan na shiga ina kiran sunanta yan mata ne guda biyu a saman Amnah sunata tsotseta gefe ga wani namiji shima yana qwaqular gabanta hankali na ya tashi matuqa nayi wani irin qara ganin wai matata ce a wannan halin bayan qarar ban iyayin komai ba saboda zubewa nayi a gurin nidai farkawa nayi naganni a asibiti yayata Hajjah da qanina Hasheem sunajinyata amma babu matata Amnah a gurin wasu hawayen nadamarsanin Amnah suka zubomin gana kewar rashin matata me tsoron Allah Hajjah ce ta matso ta riqo hanuna itama idonta na zubar da hawaye tace “kayi hqr Hafeez komai yayi farko to tabbas watarana qarshensa zaizo wlh Hajiyanmu baa cikin hayyacinta takeba” shima Hasheem matsowa yayi yace “insha Allah Yaya asirinsu zai tonu koma su waye sukeyi maka wannan mugun abin ni na tabbatar matarka ba mutuwa tayi ba inaji a jikina tana raye Yaya da zakaji shawara ta ka saki Amnah ka huta kaima ka samu sauqi kaji da
matsala daya” “karka soma mukaji an fada daga bayanmu juyawa mukayi dukkanmu da mamakin me mgnr kawai sai mukaga Hajiyan mu ce hanu tasa ta dauke Hasheem da mari tace “la,anannen Allah meson raba sunnar ma’aiki Amnah ba yayarka bace ne Hasheem? Wai ba yayarka bace Amnah? Na dauka yar yayar uwarka ce amma kakeyi mata wannan mugun fatan to bari kaji Amnah bazatayi zawarci ina rayeba wannan dan qaramin kuskuren kawai dan tayi baqi bata sanar dashi ba sai ace ya saketa? To bari kuji Amnah zama daram a gidan Hafeez indai nice na haifeshi kaikuma kake zaremin idanu to wlh da wasa ka kuskura ka saki Amnah saina tsine maka sau dari sallamamme na lura tunda wannan makirar matartaka ta mutu ka susuce saboda ta gama dakai na tabbata da kasan inda kabarinta yake da zuwa zakakeyi kana haqota kana kwanciya da ita tunda babu wacce ta iya sai ita babu mace me dadi da ni’ima sai ita saboda ta kawo maka budurcin qarya ai munsan komai Amnah ta fadamin kaza ka yanka ka cakudajinin da maniyyinka ka zuba a zanin gadon kawai saboda son ace ita ta iya wawa kawai”
Tana fadin haka ta juya ta fice ta barni da kukan zuciya dana fili wlh banajure dukwani rashin mutunci akan Farha saboda itace farin cikina, Daddy inaji ina gani haka naci gaba da zama da amma duk zaman namu barne dadi bane saboda na tsaneta babu wani abu da yake shiga tsakanina da ita qwanqwaminta nakeji sosai na tsani fasiqin mutum a rayuwata, haka mukaci gaba da rayuwa da ita wata rikitacciyar rayuwa mara tagomashin farin ciki kullum da sabon abinda zata bullo dashi gaba daya ban yarda da ita ba gashi hqrna ya qare kullum azumi nakeyi don cirewa kaina damuwa da sha’awa.
Wata rana Ina kwance a dakina nakai azumi harna fara bacci naji an bude qofa an shigo na bude idona na zubashi a kanta ta zauna kusa dani nayi saurinjanyejikina kawai saita samin kuka tana yimin magiyar nayi hqr na yafe mata ta daina duk abinda takeyi ta tuba, Daddy Allah yasamin rauni akan lamarin ya mace musamman wacce take qarqashina ko kadan banason digar hawayen mace da wannan Amnah tayi nasara akaina harwani abu ya shiga tsakanina da ita amma duk da haka saida nayi amfani da comdom don kiyaye lfy ta sati biyu da haka Amnah ta fara rashin lfy likita na kira gda ya dubata gwajin farko aka tabbatar min da Amnah tanada shigarciki wata biyu zabura nayi na miqe ina kallon likitan ina kallon Amnah da taketa murmushi nace Dr wata biyu ko sati biyu? Dagowa yayi zaiyi mgn tayi saurin daga masa hanu tace “wata biyu ne Hafeez nasan dashi abinda yasa ban fada maka ba saboda inason bakashi a matsayi surprise nejeka Dr mun gde”juyawa likitan yayi ya the bayan tayi masa kyauta me tsoka likitan yana fita nayi kukan kura na damqeta
Shigowar Hajiya Sogiji ne ya ankarar dani barnar da nake shirin yi saboda Amnah ta daina numfashi sakinta nayi ta fadi na nufl Sogiji na nunata da yatsa nace “ Wlh Hajiya bazan yarda ba ta nemawa shegen danta uba amma ba cikina bane banida wata alaqa dashi ita ta sani” Ina fadin haka na flce na koma dakina ina shiga na zube a qasa ina dafe da kaina ina kiran sunan Allah tare da maimaita kalmar“ innanillahi wa innah ilaihir raji‘un” na dauki Ike 3 haka batare da nasan me nake tunani baji nayi ana buga qofardakin da qarfi kamar zaa balleta na miqe da sauri na bude ban gama tantance waye ba naji an daukeni da wani gigitaccen mari, baya nayi da sauri tare da dago kaina Hajiyata ce ta shigo dakin tare da daukan duk abinda yazo hanunta tana jlfana dashi tana cewa “ashe kai mahaukaci ne Hafeez bansani ka karbi dan shege wanda kayi cikinsa a titi amma halattace wanda uwarsa take cikin gdan ka matsayin matarka kace bakaso ba naka bane to tunda kace bane fadamin ubansa nace ka fadamin ubansa bayan kai?”