FARHA CHAPTER 3

FARHA






CHAPTER 3




Tajima a qasa a zaune tanaci gaba da kukanta tana matsa hanunta da yakeya yimata zugi shigowar malamin da zaiyi musu darasi ne yasa Rahmah leqawa tace “sai ki fito in kinga dama malam ya shigo” daqyar ta fito ta zauna har yanzu idanunta hawaye yake fitarwa, aiki ya samu mata ranar ko break bata fitaba kasancewar azumi takeyi amma bawai azumin ne ya hanata fita ba wai hanunta ne ya karye’ badan hakaba dako tsokana saita fita tayi sai qarfe biyu suke tashi lkcn da suka tashi suka fito suna tafe anata hira amma banda ita kowa mamaki yake yanda akayi jikin ta qaura yayi la’asar da wuri haka. 
Binta ce da tasan komai ta dubeta tace “amma mutumin nan mugune kinga yanda hanunki yayi ja kuwa anya ba gdan madora zamu wucce ba” matse qwallar idonta tayi tace “qyaleshi macuci aini dayasan muguntarda zaiyimin kenan dama bari yayi wadannan wahalallun dogarawan nasa suka kasheni kuma wlh bazan yafeba bashi yaci Allah saina rama saina tsige masa gashin hammatarsa da daidai” dariya ce takecin Binta amma babu halin yi tasan yanzu zata sauke kwandon jarabarta akanta haka suka rabu kowacce ta shiga gdansu saida ta tsaya a soro ta qara qaqalo kuka sannan ta shiga gdan tana shiga ta cire Jakarta ta ajiye ta fada gado taci gaba da kukanta tanata zabga Allah ya isanta, Babu wanda ta samuya kulata saboda sunsan halinta rarrashin ma baji takeba idan tanajin iskancinta da haka bacci ya kwasheta. 
Bata farka ba sai qarfe uku da rabi tana tashi ta shiga wanka ta fito ta zura uniform din islamiyyar ta dauka ta dauki qur’aninta da sauran littatafanta zata fita taji Baffa ya kirata daga dakinsajuyawa tayi ta shiga murmushi tayi tace “Lahh Baffa ai bansan kananan ba na dauka kana kasuwa” fuskarsa babu yabo babu fallasa yace mata “aa ina gda daga Giyyade na dawo yanzu akan mgnr auranki wakilan Mai martaba sunje sun sami su Baffanku Jafaru da Balaji sunyi mgn har sun bayarda dukiyar auranki shanu hamsin da sadaki dubu hamsin kamar yanda Baffanki Jafaru ya yanke musu” dagowa tayi da idonta daya ciko da qwallah tace “wai dama da gaske kukeyi Baffa aure zakuyimin Baffa kaifa kake cewa ni yarinya ce kuma ma duk a qawaye na Salman gdan Hadi me raqumi kawai akayiwa aure gsky ni aa Baffa bazan yarda ba mugu ne fah dazu karyamin hanu yayi a makaranta danma nidin qashi dayane dani danayi bacci ya hade” harta gama shirmenta kallonta yakeyi saida yaji tayi shiru sannan yayi gyaran murya yace “koma dai menene haka zakiyi hqr dashi tunda shine zabin da Allah yayi miki kuma ya kafa maki dokoki yace daga yau bayason qara ganinki a waje saboda akwai barazana a cikin fitar zaa iya daukeki idan akasan kedin zai aura yace yaje makarantar bokonku yau sunyi mgn da principal dinku zaa zana miki jarabawa a cikin wadanda zasuyi jarabawa wannan shekarar in yaso idan kina raayin cigaba da karatun sai kici gaba a gdansa saboda haka kije ki cire uniform dinki yace anjima zai turo a daukeki za,a kaiki gun tailar da zasuyi dunkunanki su ganki” Dagowa tayi zatayi mgn ya katseta ta hanyar daga mata hanu yace “umarni aka bani nima umarni nake baki tashi maza kije ki shirya” miqewa tayi a salube ta fita daga dakin tsayawa tayi a jikin dakin tana share hawaye tana cewa “Allah dai ya sakawa wanda aka zalumta 
kawai azzalumai masu ci da rawani shi ko kunya bayaji yanda yake kaya gudannan yace 
waini zai aura maji dai ma gani ai nasan yanda zanyi dakai” 
Shigewa tayi dakin ta kwanta tare da Kiran almajirin da yakeyi musu aike tace yaje yace da Binta bazataje makarantar ba makiri algungumi yasa Baffanta ya hanata zuwa ko ina. 
Da yammaci wajan misalin 05:37pm Baffanta ya kirata yace taje ana jiranta a waje, saida ta gama yauqinta sannan ta fita tsayawa tayi a qofar gdan nasu tana qarewa motar dake parking kalloh qirar Hunday baqa wulik har sheqi takeyi kamar an shafa mata mai jitayi an danna mata horn tayi firgigit ta dawo daga duniyar tunanin ta fara takawa a yangance har ta qarasa jikin motar ta tsaya, bude mata akayi kamar bazata shigaba sai kuma ta tuna da kashedin da Baffa yayi mata, kama murfln tayi ta qarasa budeshi ta shiga ta zauna tare da rufowa tace “bismillahi Allah ka rabamu da yan gangan da gangancin qarya”juyowa tayi ta kalleshi tare da dafe qirjinta tace “na shiga uku dama kaine naga cewa kayi da Baffa na turowa zakayi a daukeni a kaini” lumshe idonsa yayi tare da dawo da kallonsa kanta ya zare glass din idonsa ya ajiye yanda ta zuba mishi ido tana qissima irin mutumin da zata 
kwatantashi dashi ajerin yan film din India ne yabashi damarzuba idanunsa cikin nata. 
Da sauri ta dauke idonta tayi qasa da kanta cikin rawarjiki da muryar tsoro tace“ni ka daina kallona da idonka gsky ni banason sa ido” ya jima yana kallonta cike da mamaki wato shine ma yasa mata idon kenan, lasar lips dinsa yayi tare da yima motar key yayi ribas suka bar unguwar suna tafe tana addu’a saboda gaba daya a tsorace take gaban wata Plaza yayi parking ya dauki wayarsa ya kira wata number “Yeah” kawai taji yace ya ajiye wayar ya kwantar da kansa a saman kujera inda ita kuma take satar kallonsa ganinta take wata yar tsakuwa a kusa dashi, qwanqwasa qofar motar akayi batare daya dago kansa ba ya bude mata qofar yace “kije ki dawo” yanda yayi mgnr ne yasata saurin kallonsa “wato ita kanta mgnr ma dole yakeyinta” hanunsa ya daga tare da nuna mata waje ta zura qafafunta qasa ta fita suka jera da wata mata da alamun itace tazo Tafiya da ita suka shiga cikin Plazar 
rarraba ido takeyi ta kalli nan ta kalli can ji tayi an dafata ance. 
“Ranki ya dade ana mgn” juyawa tayi ta nufl inda ake kiran nata kasancewar gurin duk mata ne yasa ta saki jikinta aka gwadata sosai sannan matar data shigo da ita ta kuma kama hanunta suka nufi wani bangaren daban nan kuma bangaren gyaran gashine da wankin qafa da gyaran farce mamakine ya cikata ta tsaya tana kallon ikon Allah ji tayi matar tace “Ranki ya dade idan ba damuwa ki zauna a tsefe miki kanki” zaro ido tayi waje tace “kam bala’i tabdi yasin aa damuwa ma qatotuwa toni bari kiji tunda nake kosu Rahama basu taba tsefemin kaina ba Ummah ce take tsefemin balle naba wasu da bansan 
su waye ba su tabamin kaina” 
Murmushi tayi tace “kiyi hqr umarnin Mai martaba ne wannan saboda haka dole ki bari ayi miki” zatayi mgn tace “aa ranki ya dade hakan fah zaayi” haushine yasata cizge dankwalin 
kanta tace “nifa kaina a tsefe yake ma dan kuji” dukkansu saida sukayi dariya wacce taji an 
Kira da Manah tace “gaki da gashi ranki ya dade nicema zan wanke miki kan muje ai yanzu zaa gama miki” babu yanda zatayi saboda taga sun fara kawo mata rainin hankali shiyasa tabita suka nufi wani guri na musamman gefe kuma wani qasan gurin glass ne ruwa da wasu qananun kifaye tarwada suna yawo a ciki rintse idonta tayi tana salati murmushi Manah tayi tace ga guri zauna mu jefi tsuntsu biyu da hoge daya tsugunawa tayi ta cire wasu yan robobi a jikin glass din daidai qafar Farha wata a gurin ta taso ta dauko wani Mai zata shafa mata a qafarta tayi saurin janyewa tace “to ita kuma qafar me zaayi mata?” Kallonta Manah tayi tace “zaa shafa miki wannan manne sai ki zurata cikin ruwannan 
maana wanketa zaayi sai ayi miki lalle” 
Qurawa ruwan ido tayi tana ganin kifayen da suketa wutsil2 ta kalli Manah tace “kuma a cikin ruwannan?” Daga mata kai tayi numfashi Farha ta sauke tace “kuma da wadannan kifayen a ciki?” sake daga mata kai tayi, murmushi tayi tace “aa wlh banaso ku barshi idan naje gda zan wanke da soson gogewa ni qafata ma bata faso bata kaushi wannan ma ai salonjawa kai jafa’i ne to kuma yanzu idan suka gutsire min qafa sai nace me?” dariya sosai sukeyi mata daya cikin ma’aikatan gurin ta sanya qafarta a ciki taga yanda kifayen suka taso suka yanyame qafar tata suna lasa sai kuwa ta zunduma ihu tanaja da baya, daqyar suka shawo kanta ta bari akayi mata wani wankin qafar daban amma fur taqi yarda da 
wannan na kifayen. 
Amma fur taqi yarda da lallen shima tace ita bataso dole suka qyaleta Manah ce ta sake rakata ta bude mata motar ta shiga yaja suka juya suka fita daga Plazar ba gida sukayi ba wani guri ya kuma nufa wannan karonma bai fita ba wayarya kuma kira wani mutum ya fito ya russuna ya kwashi gaisuwa sannan ya bude bayan motar ya ajiye ledar dake hanunsa ya juya ya tafi yaja motar Suma suka tafi, cike ta mamakin lamarinsa shi bakinsa ko tsami bayayi tunda suka taho bataji yayi mgn ba saida Eh ko Aa tabe baki tayi tace “Allah dai ya kyauta bama dole mutum yayita hawaba mgn ma bazaayi ba saikace kurma nifa natsani mutum mai girman kai wlh yo akwai wani sarki ne a duniya bayan Allah sarautar ma…”damqar da yayiwa hanunta ne yasata hadiye mgnr tana fadin “wayyoh Allah zai qarasa kasheni aini dama nasan badan Allah ka daukoni daga gdanmu ba wayyoh kayi hqr jijiyarda qashin duka sun karye” bai saki hanun nata ba kuma baiyi mata mgn ba haryayi parking daidai qofar gdan yanayin parking takai hannunta zata bude yayi saurin danna mata key tare da funciko ta ta fada jikinsa ya damqin gashinta da daya hanunsa yaja da zubarwa bai saketa ba saida yaga tajigata tukunna ya sakar mata kan nata tare da bude mata qofar ta fita da sauri har tana faduwa zagayawa tayi daidai inda yake zaune fuskarta sharkaf da hawaye tace “Allah ya sakamin mugu kawa…” motsawa yayi kamar zai bude murfln motar aikuwa ta kwasa da gudu ta shige cikin gdan murmushi yayi tare da Kiran wani yaro 
ya bashi ledar da suka karbo yace yakai mata ciki. 
Tana shiga ta fada dakinsu ta fada saman katifa tasa kuka tana fadin “wlh duk abinda 
kayimin bashine akwai ranar dazan rama don bazan taba yafe maka ba kaci banza mugu kawai” shigowar yaronne dakin yasata dagowa ta haushi da masifa tace “munafiki ubanme kazo yimin anan” cikin tsoro yaron ya miqa mata ledar yace “wani ne a waje yace na kawo miki” fuzgar ledartayi tace “mugu kawai ai wlh bazan mayar masa ba yaci banza” tana mgnr tana zazzage ledar tarkacen turaruka ne sai kwalin biscuits da chocolate sai wata qaramar ledar aciki ta daukota itama ta bude kwali ta gani a ciki ta zaro kwalin tana dubawa Rahmah ce ta shigo ta kalleta tace “ina kikaje ne” turo baki gaba tayi tana bude kwalin tace “yawo naje munafukai masu zuwa lahira da qoqon dambu to mijina ne yazo mukaje yakaini wai aka gwadani harda wankemin kai akayi kuma aka wankemin qafa kingani ma” ta fada tana daga mata qafar hanu tasa ta shafa tace “lahhh kinji yanda qafarki 
tayi laushi Farha wannan kuma menene a wannan kwalin?” 
Miqa mata tayi tace “nima bansaniba mugu kawai haryanzu kaina zafi yakeyi…” maganar ce ta maqale ganin abinda Rahmah ta zaro a cikin kwalin da sauri ta miqa hanu  ta fusga tana qare mata kallo waya ce sabuwa dal qirar I phone 7+ tsalle tayi ta rungume Rahmah tana dariya tace “yehh nima na zama babbar yarinya na faso gari wlh zan tsula tsiyata son raina nima sai na rama rashin mutuncin da Zainab Shattl’ma tayimin kwanaki akan wayarta” dariya Rahmah tayi tace kedai a ramuwa zaki qare Farha ki tashi kije ki dauko abincin ki a kitchen” yatsina fuska tayi tace “tabdi ai na daina cin abu me nauyi ni yanzu kinsan ance matan manya basacin abu me nauyi daga cake sai ice cream sandwiches da bugger and sweet cheeks chocolate something like that dai kindai gane ai” dariya sosai Rahmah takeyi harda riqe ciki wato ita gaba daya ma bata fahimci abunda ake 
nufi da auran ba saida ta gama dariyarta sannan tace 
“Waike Farhanah idanma anyi miki auran me zakije kirinqayi a gdan mijin naki?” Dariya tayi harda tafa hanu tace “lallai ma kin rainani to bari kiji na lissafo miki zanke girkiwanke wanke shara kula da dakuna na da wanke bandakuna sannan zanke gyara shimfidar mijina kamar yanda malam Nuhu yace mana nifah baki sani ba cewa zanyi da Baffa kada ya siyamin gado iya katifa ta isheni saboda qatoto ne mijinnawa sannan katifa biyu zaa siyamin tawa da tasa yawwa kuma yace zanci gaba da karatuna a gdansa” murmushi Rahmah tayi tace “kinsan wani abu idan fah akayi maki aure yarinya mijinki zai iya taba ko ina ajikinki kuma 
zai iyayin komai dake yarinya” 
Juya mata baya tayi ta kwanta tace “keni fah koma me akeyi zan iya indai ba dambe bane keko damben ne da cizo da yaqushi zan qwaci kaina” dariya Rahmah tayi tace “aa babu batun dambe a wannan harka soyayya ce za,a sha madararta bare ke da kike da abun badawa” dariya sukayi dukkansu sukaci gaba da hirarsu har bacci ya daukesu, da safe tana gani suka shirya suka tafi makarantar amma banda ita tanaji tana gani saidai ta kwanta tayita bacci tama manta da wata waya tunda ta mayar da ita kwalin ta ajiye bata kuma bi ta kanta ba, tun saura kwana hudu aka fara shirye shirye a gdan nasu yan qauyensu duk sunzo 
gdan ya cika sosai. 
A gdan sarautar ma haka abin yake shagali akeyi sosai qofar fada ta kacame kilisa aketayi a tsakanin gdan sarki da filin sukuwa baqi sun cika garin sosai inda aka qawata lungu da saqo na gdan sarautar daga gdan sarautar aka tura mai gyaran jikin amarya take gyara 
Farha biki fah yayi biki gari yadau harami ranar alhamis ne yakama zaayi kamu qaton Hall ne na gani a fada aka ware musamman saboda kamun sai qarfe bakwai na dare motoci sukazo suka dauki amaren zuwa gurin da zaayi kamun saida aka takura mata sannan ta yarda suka tafi goma da rabi suka gama bidi’o’insu injita da fada aka kuma dawo dasu gida suna zuwa ta cire rigarta tayi jifa da ita ta daura zani tace “haba dan masifa a qaqabawa mutun riga sai cizona takeyi yasin bazan qara sanyata ba ranar juma’a sukayi traditional day shima ba qarya an kashe daloli wajan shirya komai sudai bangaren amarya saidai ace musu zaaje guri kaza zaayi kaza saboda abun na masu garinne asabar ce ta kama ranar da zaa daura auren tun safe data fahimci da gaske dai auran zaayi mata take kuka har qarfe biyu aka daura auran a masallacin fada daurin auren da ya kafa tarihi me tarin yawa a garin Bauchi saboda k0 auran Sarki Hafeez na farko bai nuna farin cikinsa kamar wannan ba da wanda ya isa da wanda bai isaba a wannan rana miqa masa hanu yake su gaisa lamarin dayake baiwa kowa mamaki da yawan mutane abinda suke ayyanawa a ransu lallai so gamonjinine shikuma duk girman kansa da izzar mulkinsa Farhanah ce tayi masa duk cikar garin Bauchi, ga wadanda sukasanta kenan wadanda basusanta ba kuma suna cewa ita kuwa wacece wannan me saa data saqalo rayuwar 
lsasshen Sarkin da baya ragawa kowa. 


Hmm muje zuwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *