FARHA
CHAPTER 9
Kafe likitan yayi da dara daran idanunsa yanajin mgnr kamar mafarkin daya sabayi kullum so yake likitan ya tabbatar masa da abinda ya fada saboda haka ya kamoshi da qarfi ya abinda zai tabbatar min Queen tanada cikina pls” yana mgnr muryarsa na rawa hawaye na zuba a idonsa , cire hanunsa likitan yayi daga kan kafadarsa ya dafashi yace “tabbas wannan karon ba mafarki bane KING HAFEEZ matarka tana dauke da babynka na kwanaki talatin da hudu sati biyar da kwana daya kenan…” wani ihu yayi ya rungume Dr David yana gdy ga Allah zubewa yayi qasa yayi sujjud shukur dan nuna gdyrsa ga buwayi gagara misali kafin ya dago wani kuka me qarfl ya kwace masa amma na farin ciki yana ayyana abubuwa da yawa a ransa ji yake kamarya tashi ya dauki Farha ya hadiye lallai Allah da hikima yake shekara shidda suna yawon neman haihuwa daga qasa zuwa qasa ashe shi haukansa yakeyi uwar yayansa tananan a kusa dashi gashi cikin hikima ta ubangiji saduwar farko sai ciki, dagowa yayi lkcn da yaji motsin farkawarta ya qarasa kanta da sauri ta bude idonta akan fuskarsa da har yanzu ya kasa tsayar da hawayensa, ruqo hanunta yayi ya hau gadon ya zauna yana murza hanun nata a hankali tare da dagota ya rungumeta ya sake sakin sabon kuka wannan karon harda shassheqa janyejikinta tayi a hankali ta sanya hanunta tana share masa hawayen cikin muryar mara karsashi wadda dagaji kasan babu kuzarin lfy a cikinta tace.
“Ka daina pls kuka ba yayiwa mutum mai daraja irinka kyau kaji?” Ajiyar zuciya yayi ya sake hadeta da jikinsa jiyake kamar ya raba jikinsa ya shigar da ita yace “Queen kukanma kansa yakeyi ina cikin farin cikin da babu abinda ya kamaceshi sai kukan baby bushara akayimin yau ni Hafeez nima na kusa zama uba ta dalilin ki zanyi sanadin zuwan wani duniya Farha am very happy Queen na kusa zama uba nima kin kusa haifamin baby Farha cikina ke gareki ya zanyi na nunawa Allah gdy ta idan banyi kuka ba” qanqameshi tayi ta saki kukan itama tanajin qaunar mijin nata na huda jininta tana shiga Sarki Hafeez dabanne a cikin maza ya iya kula da mace da nuna mata qauna, a hankali ta zame jikinta daga nasa ta koma ta kwanta tana shassheqar kuka sake matsawa yayi ya riqo hanunta yace “why you crying Queen?” Lumshe idonta tayi ya rinqa zagaye idon nata da hanunsa har yakai bakinta yasa hanunsa cikin bakinta ta rinqa tsotsa a hankali yanajin wani dadi, sake tambayar ta yayi dalilin kukanta a kasalance ta kalleshi tace “kawai naji nima ya kamata nayi kukane saboda kasancewata wadda Allah ya zaba na zama uwa ga yayan Sarkinmu Hafeez a lkcn da duniya bata taba zataba amma ya akayi haka Mai martaba nifah bantayin haila ba kuma malamanmu sunce sai mace tana haila sannan take haihuwa” murmushi yayi yana kallonta har tayi shiru sannan yace “sa’ata ce a haka cikin watan da zaki fara period na sanki kwan dan mutu ya fita a matsayin jinin haila saiya koma a matsayin da kinsan alfarmar da nake nema a gurinki?” Kada masa kai tayi alamar aa yayi murmushi yace “ki kulamin da kanki da dana dakejikinki kinji?” Daga masa kai tayi alamar eh yayi murmushi yace “I love you so much” dariya tayi ta rufe idonta shima yayi dariyar yace zakiyi bayani ne yarinya” miqewa yayi ya dagota yace tunda babyna ya hanamu yin dinner mu tashi mu tafi gdanmu mu huta” yafa mata mayafinta yayi ya rungumo tajikinsa saboda ya lura bata da qarfi a jikinta kamar ma jiri takeyi suka flto nan fah mutane suka rinqa tasowa sunayi masa
Congress yanata washe baki yana amsawa cike da murna har suka isa gurin motarsu suka . . . . . . shiga driven yaja suka tafi gda.
Suna zuwa ta kwanta saboda hajijiyar da takeji shima shigowa yayi ya kwanta kusa da ita
ya janyota jikinsa yana shafa cikinta yanajin wani farin ciki a ransa wayarsa ya dauka ya kira Hajiya bugu biyu ta daga suka gaisa yake fada mata samuwar cikin qwarai tayi murna
tayiwa Allah gdy sannan ta bashi shawarwari sosai na yanda zai kula da ita yaji dadi yayi
gdy suna shirin aje wayar Asiya ta fusge tace “Yaya kace da Aunty Farha ta haifa mana kyakkyawan yaro me kama da ita don Allah yaushe ma zaku dawo wlh part dinku zan dawo muyi rainon babynmu tare” murmushi yayi ya kashe wayarsa saboda shirmen Asiya yayi yawa lkcn daya gama wayar har tayi bacci baiyi qoqarin tashinta ba ya shiga bathroom yayi wanka ya rage qarfin A.C dakin ya kwanta tare daja musu blanket bayan yayi musu addu’a. u
Saida suka qara wata uku a birnin London suna rainon cikinsu baya barinta ko wanka tayi da kanta komai shine yakeyi mata hatta abinci bai yarda taci da kanta ba lkcn da cikin ya shiga wata na hudu ne ya fara fitowa aka fara ganinsa masifarji yakeyi da cikin ko bacci zaiyi hanunsa yanakan cikinta shi kadai zai zauna yayita mgn da abinda ke cikinta itadai saidai tayi dariya kawai, abinda yafl burgeshi da Farha yanda ta saki jiki dashi take nuna masa kulawarta da bashi duk abinda yakeso lamarin daya qara ninka girman matsayinta a
gurinsa. Watan cikin Farha biyar suka fara shirin komawa qasarsu Farha tayi wani fitinannan kyau haske da qiba sannan ta qara wani kwarjini na musamman ta cika sosai, ranar da suka dira a 9ja motocin gdan sarauta sukazo tarbarsu harda mataimakin governor a tawagar suka rinqa gaisawa da mutane kafin su shiga mota aka jasu zuwa gdan sarautar qofar fada ta kacame da kide kide da bushe bushe Mai martaba ya dawo suna tafe yana dagawa mutane hanu cike da farin ciki suna shiga akayi parking tare da shimfida musu abin takawa suka rinqa tafiya a hankali kamar bazasu takaba ana watsa masu fure tare dayi musu kirari itadai dole take
irin wannan taflyar isar don tayi bala’in gajiya yaso wuccewa ya huta amma babu dama dole saida suka shiga part din su Hajiya fulani da part din Hajiya Sogiji suka fara suna zaune itada Amnah da Umaima sai bayin da suka kewayesu anata zuba mulki suka shigo tunda suka shigo idon mutane ukun yake kanta musamman Amnah da take qara zaro idonta waje tanason gasqata abinda take gani, miqewa tayi da sauri ta zata nufi inda suke Hajiya Sogiji ta ruqota da qarfi ta koma ta zauna itama Hajiyan idonta nakan cikin Farha daya fara turawa duk da yabi jikinta amma hakan bai hanashi dan dagowa ba daga cikin alqabbar dake iikinta.
Kujera ya samu ya zauna Ita kuma ta tsuguna a qasa saman carpet duk da baiso hakan ba saboda bayason tana abinda zata takura amma bai hanata ba ta qwace hanunta tace“sannu da gda Hajiya mun sameku lfy” wani yawu ta hadiya me daci tare da daga mata hanu tace “lfy” daga haka bata qara cewa komai taci gaba da taunar apple dinta juyawa tayi suka hada ido da Amnah da takeyi mata kallon qurullah miqewa yayi yajuya zai fita yace “ki taso muje” miqewa tayi tabi bayansa suka nufi bangaren Hajiya Kilishi tayi murna sosai da ganin Farha ta rungume ta tanata yimata sannu tana tambayarta jiki.
A bangaren Hajiya Sogiji kuwa suna flta ta dubi Amnah ta qudduma uwar ashariya tace “ciki? ciki fah nagani a jikin wannan makirar yarinyar Amnah bantan ubancan billahil azeem bata isaba dole ko sunaso ko basaso kece uwar Yariman masarautar nan ” kuka ta sake saki me gunji tana cewa gsky da sake Hajiya cin mutuncin yayi yawa yana sane ashe yaqi yimin ciki saboda ni ya tsaneni to wlh bazai yuwu ba dole ma asan yanda zaayi Hajiya tun farko kece kika ja mini wannan masifar tun lkcn da aka kawota gdannan nace mu dauki mataki amma kikace mu kyalesu kinada tabbacin bazai taba haihuwa ba yanzu ga irinta nan…” Ta qarashe mgnr cikin kuka kamota Hajiya Sogiji tayi tace “ki kwantar da hankalinki wlh nayi miki alqawarin bazan barki ki koka ba kamar yanda Hafeez yasaki kuka to shi saiya mutu yana kokawa kawo kunnenki kiji wani abu” miqa mata kunnen tayi sai kuma suka kwashe da dariya tare da tafawa.
Saida suka zauna sukayi dinner a bangaran Hajiya Kilishi sannan sukayi mata sallama suka part dinsu an gyara mata komai tsaf tana zuwa kwanciya wanka tayi ta canza kayanta zuwa na bacci tayi sallah tayi azkar sannan ta koma ta haye gadonta ta lafe bayan ta kulle qofarta baccinta me dadi ya dauketa, shima bayan yayi wanka ya kwanta harya fara bacci yaji ana danna qararrawar dakin remote din ya danna qofarta bude saboda yariga yasan wacece me bugawar shigowa tayi ta zauna a gefen gadon jan blanket yayi ya rufejikinsa, dubansa tayi tace “mgn nazo muyi dakai” sake shigewa yayi cikin bargon yace “ki adanata mayi da safe yanzu bacci nakeji idan kin gama ki rufemin qofar na gaji da yawa bacci nakeji” haushi ne ya kamata tayi kamar ta miqe ta fita amma babu hali saboda tana buqatar kasancewa dashi sosai, shigewa tayi cikin bargon ta kwanta tare da tura masa qirjinta tasa masa kuka tace “tunda kayi aure ka watsar dani ka daina kulani rabonka da kusanta ta tun kafln ka fara neman auran munafukar yarinyar na…” daga mata hanu yayi yace “idan abun daya kawoki kenan to ki tashi ki ficemin dagani kullum saina fada miki ki rinqa iya bakinki akan Farha amma baki fahimta matata dana aureta saboda inasonta kuma matsayin ta ya dada daukaka don itadin uwaryayana ce”
Shiru tayi masa saboda bazata iyajure wannan cin fuskar tashi ba itadai burinta ya biya mata buqata shigewa ta kumayi jikinsa yasan inda ta dosa saboda haka ya biye mata badon yanaso ba saidon sauke haqqinta dake kansa babban abinda yake damun Hafeez da Amnah bata damu da biyan buqatar sa ba indai tata ta biya shikenan ga rashin kula da ni’imarjikinta a cikin wata biyar dinnan da basa tare ya kamata ace tayi abinda zai manta kansa idan ya shigeta Farha ce kawai take yawo a zuciyarsa tunda ya aureta ranaku daidai ne baya kusantarta amma kullum ya shigeta sabuwa yake jinta gata da saurin daukan move daya dorata ta hau ta zauna harma ta fisa zaqewa sometimes idan yana tare da ita mantawa yake da yanada wata macen bayanta yau dukjinsa ji yake kamar wani mara lfy, wayarsa ya dauka ya rubuta mata dan gajeran saqo me cike da kalmomi masu kwantar da
hankali lkcn itama ta farka juyi kawai take da tunanin mijin nata taji qarar saqon dubawa tayi ga mamakinta sai taga ashe shine murmushi tayi bayan ta karanta saqon itama ta rubuta masa amsa a gajarce ta tura masa k0 minti daya baayi ba kiransa ya shigo wayarta ta daga da sauri tace “hello” ajiyar zuciya ya sauke yace “meye ya hanaki bacci My Queen?” Asanyaye tace “ kewarka Mai martaba yau jina nake cikin wani sabon yanayi na saba kwanciya tare dakai dukjuyi da zanyi a jikinka nakeyinsa amma yau saini sai pillow na kasa bacci wlh King Hafeez nakasa jurewa rashinka bansan jikina da zuciyata sunyi irin wannan mugun sabon dakai ba sai yau…” ta qarasa maganar cikin kuka
Hankalinsa ne ya tashi ya miqe da sauri yace “ya Salam ki daina kuka don Allah ganinan bari nazo nasaki bacci yanzu” bai jira cewarta ba ya miqe ya dauki boxes dinsa yasa ya leqa fuskar Amnah yaga kamar bacci takeyi baisan bakam tayi masa ba tanajinshi yayi murmushi tare da ja mata bargon ya bude qofar a hankali ya fita yana zuwa ya dannan qararrawar dakin tana zaune saman sallaya ta miqe ta bude masa shigowa yayi ya mayar da qofar ya janyota jikinsa ya hadata da qirjinsa suka sauke ajiyar zuciya lkc guda ya dagata cak ya dorata a gadon ya kwanta shima ya matseta a qirjinsa yana hura mata iska a kunnenta yana fuzgo numfashi daqyar ya dauki hannunta ya dora a kansa ta tura hanunta cikin sumarsa ruwa taji cikin sumarsa ta zare hannunta ta fara qoqarin zarejikinta qara matseta yayi yace “bacci nakeso kiyi Queen baby ya gaji yana buqatar hutu” ajiyar zuciya tayi tace“ruwa naji a kanka” shafo fuskarta yayi yace “yayarki ce ta sani wanka maza yi baccinki don Allah ina tausayinki da babyna” bata kumayi masa mgn ba ta kwanta luf a jikinsa zuciyarta na tafarfasa “ashe da gaske dama haka akeyi kamar yanda yake kwanciya da ita suyi wanka itama Amnah haka ya kwanta da ita?” wasu hawaye ne suka zubo mata masu zafi tayi saurin gogewa saboda bataso ya fahimta jitayi ya dagota ya juyar da ita ya hau samanta yasa harshensa yana lashe hawayen nata yace “kishi k0 Farha kema kinada irin wannan kishin ashe Farha mene abin damuwar kinsani kece nakeso kece rayuwata kece farin cikina don Allah kada kema ki dauki wannan halin ku hanamin kwanciyar
Hmm