FETTA CHAPTER 1

FETTA




CHAPTER 1






*GARIN KANO* +

Hadari ne ya gauraye sararin samaniya, Garin yayi duhu, Ruwa zai iya sauka a kowane lokaci, Tsaye take jikin k’ofa tana jiran saukar ruwan, Yarinya ce yar’ kimanin shekara 12, Fara ce tass, kamar ka tab’a jini ya fito, Gashin ta a fake, ya zuba har gadon baya, Kallo d’aya zaka mata kasan buzuwa ce, Daga kayan jikin ta zai tabbatar maka iyayen ta ba masu k’arfi bane.

Saukar ruwa sama, ta buga tsalle ta fad’a ciki, Ruwa na sauka kanta, Tana wak’a da juyi, hakan na cikin hobby d’inta, Ba k’aramin nishad’i take tsintar kanta ba a duk lokacin da ake Ruwan sama take wasa ciki.

“FETTA! FETTA!”(Na nufin Fatima da yaren buzaye), Taji muryar mahaifin ta na kira, ” Ba zaki fito cikin ruwa ba sai mura ta kama ki”, Ya fad’a da hausar sa da bata kama baki ba,

Wasanta ta cigaba da yi kamar bata ji sa ba, Sai da ruwan ya tsagaita, Ta nufo k’aramin d’akin su, wanda ko ba’a fad’a maka ba, na masu gadi ne.

Rawar sanyi take, ruwa na d’iga daga jikin ta, Mahaifin ta ya kalleta yace “Son wasan ruwa kamar yar’ ruwa”, Tayi dariya tana tub’e kayanta, Ta shanya su a jikin k’ofa, Ta d’auko wata tsohuwar rigar atamfa, wacce yaran masu gidan ne suka bata, Ta saka, Ta kwanta kan yar’ yoluluwar katifar ta, Taja bargo da duk ya tashi tsabar tsufa ta lullub’e.

Garwashi ya had’a, Ya d’auko k’aramar butar su ta had’a shayin ataye, Ya zuba garin, Ya tafasa, Ya sauke, Ya tache, Ya zuba a k’aramin k’ofi guda uku, ” FETTA tashi ki mik’awa Hajiya, shayin Alhaji ki dawo ki sha naki”, “Toh Addani”(Yana nufin Baba), Ta fad’a tana mik’ewa,

Ta karb’a ta nufi cikin gida, a bakin k’ofar kitchen taci karo da Yasmin yarinyar masu gidan, ” FETTA ya aka yi?”, Ta fad’a da sakin fuska, “Shayin Baba ne na kawo”, Ta mik’a mata ta karb’a, Ta koma d’akin su.

  Shayin ta zauna tana sha, sai da tasha kofi uku, tana tsananin son ataye, ” Addani waya koya maka had’a shayin nan?”, “Al’adar garin mu ce”, ” Sai yaushe zamu je?”, “Ba yanzu ba”, ” To yaushe zaka bani tarihin mu?”, “Sai kin k’ara wayo”, Yana fad’ar haka ya mik’e ya fita, Baya son yawan tambayoyin da take mishi.

  FETTA tun da tashi bata san kowa ba sai mahaifin ta, tun tana shekara biyu Allah yayi ma mahaifiyar ta rasuwa, Maciji ya sare ta, A gidan nan ta tashi taga suna rayuwa, mahaifinta matsayin mai gadi, Yana tsananin son ta, Baya son b’acin ran ta ko kad’an, Duka rayuwar shi ya sadaukar a kanta, Ko albashi aka bashi, Ita yake kashewa kud’i, Idan bata da lafiya, tsananin rud’ewa yake, Ya shiga tashin hankali.

    Bata had’a mahaifin ta da kowa ba, Tana tsananin k’aunar sa, Makarantar gwamnati take zuwa nan kusa dasu, Tana da tsananin son karatu, Makarantar ba’a wani koyar dasu abun arzik’i, Wataran har suje su dawo ba malamin da ya shiga aji (Hmm Yayan talaka na ganin rayuwa)

    D’umamen tuwo suke ci, wanda aka aiko musu daga cikin gida, A kwano d’aya suke ci, ” Kiyi sauri FETTA, lokaci na k’urewa”, “Ko naje da wuri sai kaga har k’arfe 10 malami bai shigo ba, watarana ma haka zamu je mu dawo ba’a koya mana komai ba”, ” Gwamnatin ce sai dai muce Allah ya sawwak’a amma komai k’ara lalace yake”, “Addani, idan na girma nayi kud’i, Zan gina mana k’aton gida mu tashi daga wannan, na siyan maka mota irin ta Alhaji”, Yayi dariya yace ” Allah ya yarda ya’ta”, Kullum maganarta kenan, Tayi kud’i ta kula da mahaifin ta.
       
  K’arfe 8 ta fito, Sanye da Uniform da silifas, da jakarta ta buhu, Tana gani yaran gidan suka fito sanye da uniform d’in su masu kyau, da socks da sandal, kowanne ya rataya school bag, Suka shiga mota, Direba yaja su.

    Ta kalle su cike da burgewa, Ta gyara hijabin ta, Ta fita gate ba tare da ta damu ba, Tana ta yan wak’e wak’en ta na k’asar nijar, wanda mahaifin ta ne ke yawan kunnawa, har ta isa makaranta.

   Yau anci sa’a malamai har biyu sun shigo ajin su, Ana buga k’arrarawar tashi, Ta sab’i jakarta ta taho gida, bata da k’awaye, ita kad’ai ke yawon ta, Duk da cewa da yawa yan makarantar na son k’awance da ita, saboda kyanta.

    Bakin gate ta tarar da Mahaifin ta zaune, Yana sauraren radio, Ta gaishe shi, Ya amsa, Yace “An dawo?”, ” Eh Addani”, “Toh ki shiga ciki, abincin ki na nan”

    Jakarta ta ajiye, ko uniform bata cire ba, ta bud’e kwanon abincin, Ta kwaso yunwa, Ba’a tab’a abincin ba, Wanda haka ke nuna bai ci ba, Baya tab’a cin abinci, sai taci ta rage ko su ci tare, ko rabi bata ci ba, Ta k’oshi, Ta rufe saura, Ta d’ibi ruwa a randa dake bakin d’akin su ta sha.

  Sam bata shigewa yaran gidan, Kullum tana d’akin su, sai idan mahaifin ta aike ta yayi, Waje ta fita wurin shi, Tana bashi labarin abunda ya faru makaranta yau.

      Dare ne ya tsala, gari yayi duhu, Hasken fitilun gidan ne Suka haska gidan baka jin motsin kowa, sai haushin karnuka can ba’a rasa ba.

   Garadan maza ne ke dirkowa ta saman fence na gidan, Dukkan su fuska rufe, Ogan su wanda matashin saurayi ne ta k’ofa ya shigo, wanda wani k’arfe yayi amfani dashi, Ya tsaga k’ofa, Ya shigo.

   D’aya daga cikin su ya buga k’ofar mai gadi sai da ta b’alle, A razane ya tashi da salati a baki, FETTA a tsorace ta tashi tana b’oyewa a bayan shi.

    “Muje kayi mana jagora zuwa wurin Alhaji” D’aya daga cikin su ya fad’a, K’in tashi yayi , “Zaka tashi ko sai na fasa kanka”, Ya fad’a yana saita mishi bindiga, A cikin ranshi baya jin zai yarda a cuci Alhaji dashi, duk halaccin da ya mishi, ” Taurin kai zaka mana”, “Ba zan tab’a nuna muku wane sashe Alhaji yake ba”, ” Dama buzaye akwai ku taurin kai, yau zaka gane kuren ka”

   Ogan su ya mishi alama da hannu, Bindigar da ya saita a kanshi, ya harba, bullet ya shiga cikin kan shi, Ya fad’i a wurin matacce, K’ara FETTA ta saki a gigice, Ogan su yasa hannu ya toshe mata baki, Ya mata alama da bindiga, Ta sake ihu zai fasa kanta, Dole ta gimtse baki, Tana hawaye, Tare da jin tsananin tsanar wad’annan mutane.

   Cikin gidan suka shiga, Tana jin k’arar harbe-harbe, A gigice ta fito d’akin su, Ta fita a guje, ta tsorata kada itama su fito su kashe ta, Gudu take cikin dare ga duhu, bata san ina take jefa k’afar ta ba.Ta galabaita sosai, jiri ya d’ibeta ta fad’i k’asa, Tana haki, Kuka take sosai tana tuna mahaifin ta, “Allah ya saka maka Addani, Allah ya jik’an ka”, Shine abunda take fad’a. +

    Tana kwance a wurin har aka fara kiraye kirayen Sallar asuba, Mutane suka fara fitowa sallah.

    Karon da yaji yayi da abu, yasa shi haska fitila saitin wurin, Ja yayi baya a tsorace, ganin mutum kwance, Hannu tasa tana kare hasken fitila da ya dalle mata ido, ” Ke yarinya daga ina?”, Kukan ta ne ya tsananta, Tausayin ta ya kama shi, Ya duk’a, Ya d’ago ta, “Tashi ki fad’a mun ina ne gidan ku”, Cikin shesshek’ar kuka ta sanar dashi abunda ya faru a daren.

   Ya jinjina al’amarin, a ran shi yace ” Wasu mutane basu da imani”, Ya rik’o hannun ta yace “Tashi muje gidana”, Ba musu ta mik’e tabi bayan shi,

    K’ofa ce babu gate, gida ne madaidaici mai d’akuna biyu, da falo d’aya, Daga gani ba mai kudi bane, Matar shi dake tsakar gida tana alwala, Tace ” Malam ina ka samo yarinya”, Ya zayyane mata abunda Yarinyar ta sanar dashi, Tausayin ta taji a ranta, Ta rik’o ta tace “Zo yarinya ya sunanki?”, ” Fetta”, “Allah Sarki Fetta, Allah ya jik’an mahaifin ki, ya tona asirin wanda suka kashe shi”

    Ta amsa da “Amin”, Tana sharar k’walla, ” Ki d’auke mu tamkar iyayen ki kinji”, Ta d’aga kai sama, Ya koma masallaci, Ya bar matar shi taja ta ciki.

   Gidan Alhaji Adamu(wanda anan mahaifin Fetta ke gadi), Ya cika da mutane, Ana ta fito da gawarwaki ciki hadda ta Mahaifin ta, Mutum hud’u suka kashe a gidan, (Alhaji, matar sa, babban d’an shi), Sauran yaran gida da yan’uwa nata kuka, duk sun fita hayyacin su, Yan sanda sunzo sunyi binciken su, Sun tafi.

     Fetta tagumi tayi tana tuna irin rayuwar da suka yi da mahaifin ta, ba zata tab’a yafewa wad’annan mutane da suka yi sanadiyyar raba ta da farin cikin ta, Shi kad’ai take dashi a duniya, Sark’ar da ya saka mata shekaru biyar da suka wuce, Ta jawo ta sumbata, Matar ce ta shigo, Tace “Ki daina kuka kinji, idan bakya so a mishi azaba, addu’a zaki mishi”, Tana jin an ambaci azaba, tayi saurin share hawayen ta.

     Malam bala shine mutumin da ya tsinci Fetta, Nama yake siyarwa, Matar sa d’aya Aliya, gidan wasu masu kud’i nan kusa dasu take aiki, ana biyan ta duk wata, kuma tana d’inki, da haka suka rufawa juna asiri, Yaransu biyu Hajar da Aliyu, yaran k’anana ne.

        *Bayan kwana biyu*

   Fetta ta saki jiki dasu, But duk dare tazo kwanciya sai tayi kuka na rashin mahaifin ta, Malam Bala da Aliya sun d’auke ta tamkar yar’ su, Har atamfofi roba ya siyo Aliya ta d’inka mata.

    Tana tsananin son yaran, Tana taya Aliya rainon Aliyu, yaron d’an wata bakwai.

      Kwance take d’aki shiru, tana tsananin kewar mahaifin ta, watarana sai taga kamar a mafarki bai rasu ba, Aliya ta lek’o tace ” Fetta tashi ki rakani gidan Hajiya Tumba, yau akwai aiki sosai, ki rik’e mun Alee, bana son ya hana ni aiki”, Tace “Toh” tana mik’ewa.

   D’an kwalin kayanta, Ta yafa ta d’auki Ali, Aliya na gaba tana bin ta a baya har suka isa gidan.

   Makeken gida ne, tun daga gate abun kallo ne, Yan’ sanda dake tsaye bakin gate, Aliya ta gaisa dasu, Fetta ma ta gaishe su suka amsa, D’aya ya bud’e musu k’ofa suka shiga.

     Fetta sakin baki tayi tana kallon girma da had’uwar harabar gidan, tsaf zaka b’ace a cikin gidan, Saboda girman shi,  Ga motoci had’add’u guda biyar a fake, Sai faman raba ido take har Aliya tayi gaba ta bar ta, Da sauri tabi bayan ta.

      Ta k’ofar baya suka shiga wanda zai sada ka da k’aramin falo, wanda anan Hajiya Tumba ke ganawa da masu aiki, Duk safiya kowacce mai aiki nan take zuwa ta gaishe ta, “Aljannar duniya”, Cewar Fetti, dan falon ba k’aramin tsaruwa yayi ba,Sai kalle-kalle take.

    A k’asan carpet suka zauna, kamar yadda sauran masu aiki suka zauna, Suna jiran fitowar ta, ta basu umarnin abincin da zasu girka.

    Da sallama ta shigo falon, Mace ce wacce kallo d’aya zaka mata kasan hutu ya zauna a jikin ta, Sanye take da wani tsadadden material, wanda ko ba’a fad’a maka kud’in sa ba, Kasan mai tsada ne, Tasha sark’a da yan’ kunni na gwal, da zobuna, Ta zauna a kujera.

Duka masu aikin suka shiga gaishe ta, Tana amsawa da sakin fuska, Mace ce mai sanyin hali, Cikin ladabi Fetta ta gaishe ta, Ta amsa tare da tambayar ” Wacece?”, “Ya’ta ce”, Aliya ta fad’a, Bata gamsu yar’ta bace, dan ta tab’a gaya mata yaran ta biyu, kuma bata ga suna kama, Yarinyar da an ganta an ga buzuwa, Taji kawai ta kwanta mata a rai.

    Ta kawar da tunanin ta hanyar cewa ” Yau Suraj zai zo, ina so ku girka duk abincin da kuka san yana so, Kuyi mishi snacks, Kuyi drinks kamar kala biyar”, Suka amsa da “toh”, Duk ranar da Suraj zai zo to fa, basu da sukuni, Aiki ne sai sun sha shi, Yana iya zuwa yace abincin ma, Bai mishi ba.

    Fetta a ranta tace ” Dan’ gata ne”, Gefe ta koma tana yiwa Ali wasa, Su Aliya nata faman aiki.

     Wuraren azahar suka gama komai, Suka jere a dining table na babban falon gidan, Hajiya Tumba tasa suka k’ara gyara gidan, aka saka turaren wuta.

     “Wash na gaji wallahi, bayana har ya rik’e”, Cewar Asabe(d’aya daga cikin masu aikin), Rashida tace ” Ke kika gaji ko ni, shiyasa bana son zuwan sa, idan zai zo mutum ba zai huta ba, baka k’ara samun wani hutu sai ya koma”, “Hmm ke dai bari, ga shegen jin kai kamar dan’ Sarki”, ” Ni zan iya k’irga sau nawa na gan shi”, “Ai gara kar mutum ya gansa, dan kallon wulak’anci da k’ask’anci yake wa mutane, laifi kad’an zaka yi yaci mutuncin ka”, ” Yana tak’ama da kud’i, wannan da dan’ Sarki ne da mun shiga uku”

    “Ku dai bakwa gajiya da maganar Suraj”, Aliya ta fad’a, ” Maman Ali Bawan Allah nan akwai murd’add’an hali”, Dariya tayi ta girgiza kai.

  Aliya ta gama ayyukan ta, Tace Fetta ta tashi su tafi, Ta karb’i Ali ta goya shi, Tana gaba tana biye da ita a baya, Aliya Allah ya mata saurin tafiya, Fetta cikin natsuwa take tafiya kamar bata son taka k’asa, wanda idan ka ganta zaka d’auka yanga ce.

      Motoci uku ne suka shigo cikin layin a jere, masu azabar kyau, sun fi na cikin gidan had’uwa, Fetta ta shagala wurin kallon su, Har dan’ kwalin ta na fad’i, Yabi iska, Ta juyo baya zata kamo, Motocin suka zo gab da ita, na gaban na mata horn, Rikicewa tayi, tama rasa ina zata yi, Wani wawan burki yaja, Motar bayan shi ta bege shi.

     Jingine yake jikin kujerar mota, Ya lumshe ido, Gaba yaji yayi, Yayi kaura da kujera, A fusace ya d’ago, Ransa ya matuk’ar b’aci, A tsawace yace “What d hell?”, Driver a rud’e yace ” Ranka ya dad’e ba laifi na ba ne, Modi ne yaja burki”

   Bud’e murfin motar yayi, Ya fito cikin takun sa na k’asaita, Farar shadda ce tsadadda a jikin sa, babu hula a kansa gashin sa bak’i wulik yana shek’i kamar na mace, Fari ne tass, Jikin sa zai nuna maka Dan’ Hutu ne kuma naira ta zauna, Namiji ne da ya amsa sunan sa namiji, Mai kyawun fuska da na halitta.

    Modi na ganin sa yayi saurin kai k’asa yasan halin Maigidan nasu da zafin rai, Yace “Ranka ya dad’e tuba nake, ba laifi na ba ne, wannan yarinyar ce tazo ta gifta”, Ya nuna Fetta daga rakub’e gefe a tsorace, Hannu ya d’aga ya zuba mata lafiyayyan mari, Kunci ta rik’e ta tsala ihu, “Shegun yara mara sa tarbiya, kuzo kuna tsallaka hanya bayan kun ga mota, salon ku ja ma mutane masifa, dama yaran buzaye so kawai suke mai kud’i ya d’an buge su, su mak’ale mishi ya biya su, saboda tsabar kwad’ayi ku salwantar da rayuwar ku”, Yana fad’ar haka ya juya ya koma mota, Motocin shi suka d’aga, tare da bad’a mata k’ura.

   Duk da kasancewar ta mai k’ananun shekaru, maganganun sa sun matuk’ar k’una mata rai, Tun da tazo duniya ba’a tab’a wulak’anta ta irin yau ba, babu mahalukin da ya tab’a marin ta, Shine farko, tsanar shi taji sosai a ran ta,

” Wayyo Allah Addani, meyasa ka tafi ka barni, ka dawo kaine kad’ai gatana”Aliya da har ta kusa kaiwa gida ta waiga bata ga Fetta ba, “Ina yarinyar nan ta tsaya?”,  Ta koma tabi hanya tana sallallami, +

  Can ta hango ta durk’ushe gefe tana kuka, ta rik’e kunci, Da sauri ta k’araso tana fad’in ” Lafiya me ya same ki?, Fad’uwa kika yi?”, Kukan ta cigaba bata tanka ba, Hannun ta ta janye, yatsun hannun sa biyar sun fito akan fuskarta rad’au sunyi jajir abun ku da farin mutum, Salati tayi ta sanar da ubangiji, “Waya mare ki?”, ” Wani ne a mota, dan kawai sun kusa buge ni”, Ta d’ago ta, ta rungume a jikinta, Tana shafa bayanta tace

   “Kiyi hak’uri, Allah zai saka miki, shi talaka a k’asar nan sam bashi da galihu, yana ganin ya mare ki ya mari banza, to akwai Allah”, Taja hannun ta tana cigaba da masifa har suka kawo gida.

    Ta shimfid’e Ali da yayi bacci, Ta zuba ruwan d’umi a roba, Ta d’auko towel, ta fito tsakar gida, Ta zaunar da Fetta, tana gasa mata wurin marin, Sai kukan azaba take, Tana mata sannu.

    Malam ya shigo yana tambayar meke faruwa, Aliya ta sanar dashi, Ledar da ya shigo da ita ya ajiye, Ya zauna gefen tabarma yace ” Talaka na ganin rayuwa, banda tsabar zalunci, ka tashi buge mutum, maimakon ka bashi hak’uri, sai mari”, “Hmm Allah ya kyauta dai Mallam”, ” Toh Amin, Sannu kinji Fetta”, Ta d’aga kai tana share hawaye.

     Cikin takun sa na k’asaita ya shigo falon da aka narkawa dukiya, (Masu kud’i na sha’anin su, wannan falo kamar ba’a 9ja ba)

    Yan’matan ne su kusan 6 kowacce rik’e da waya tana dannawa, wasu a kwance wasu a zaune, babu mai shigar hausawa, Duka english wears ne a jikin su,

Jin sallamar sa, kowacce ta tashi tana gyara zaman ta, Suna matuk’ar tsoron sa saboda baya musu da wasa.

    “Sannu da zuwa Yaya”, Kowaccen su ta shiga fad’a, Da hannu yake amsa musu, A ransa yana mamakin hali na mutanen duniya, Gidan su ko da yaushe cike yake da yaran yan’uwa sab’anin shekarun baya da babu mai rab’ar su kasancewar basu da abun duniya, rayuwar nan idan kana dashi ana yi da kai, idan baka dashi hatta yan uwan ka zasu guje ka, tamkar dan’ adam ke bawa kansa arzik’i, Har ya k’arasu kujerar da mahaifiyar sa ke zaune, Ya rissina ya gaishe ta, Cikin tsananin farin ciki na ganin dan’ ta, Ta amsa tace ” Sannu da zuwa My son”

    “Yawwa Mamana”, Ya fad’a da guntun murmushi, ita kad’ai ke ganin murmushin nan nasa, ” Ga abincin ka can”, “Zan fara wanka”, Ya fad’a yana mik’ewa.

    Tun shigowar sa duka yan’ matan suka watse, suka nufi d’akunan su.

    Sashen shi ya nufa, Mai d’auke da d’akuna biyu, Sai babban falo d’aya da kitchen, da yar’ veranda, Tsayawa fad’a muku had’uwa da tsaruwar part d’in k’auyanci ne, Duk yadda ginin zamani ya kai ga had’uwa, Sashen Suraj ya kai,

    Kayan sa ya tub’e ya jefa cikin laundry basket, Ya shiga cikin jacuzzi, Yana wanka yana lumshe ido, Kusan 10 ya d’auka, Ya fito, ya zauna kan dressing mirror dake shak’e da turaruka da kayan shafa, Haka yabi jikin shi yana kyalk’yalewa, da fesa turaruka sak’o-sak’o na jikin shi, tamkar mace.

  Wardrobe ya bud’e ta k’ananun kaya, Shak’e take da kaya, gefen riguna long sleeve daban, na short sleeve daban, na wandona daban, Ya jawo riga short sleeve, da dogon wando, Ya saka, Sun matuk’ar yi mishi kyau, Gaskiya Suraj ba k’aramin handsome guy bane, Ya fito skin d’in shi na glowing, K’amshin mai dad’i na fita daga jikin sa.

     Hajiya Tumba ita tayi serving d’in sa abinci, Abinci kala biyu yaci kad’an, yasha drinks, Ya tashi, Tasan halin dan’ nata da rashin son abinci, Tana sa a mishi abinci kala-kala ne dan ta faranta mishi rai, Mutum ne shi mai son harkar girma.

 A tsakar gida suna cin tuwon masara suna hira, Fetta ke ba Hajar a baki, Aliya tace “Ke kike biye mata kina bata a baki, da kin bar ta taci da kanta”, ” A’ah Umma, idan na bata tafi ci”, “Toh shikenan”, Suna gama ci, taja Hajar, Suka nufi d’aki suka kwanta, Fetta sam bata hirar dare, Ta saba da tayi sallar isha’i take bacci, Kiran sallar asuba a kunnen ta ake yi, (Duk mai son ya rik’a samun sallar asuba to ya rik’a kwanciya da wuri).

    “Yarinyar nan tana matuk’ar bani tausayi, ace ta rasa iyayenta, bata san kowa nata ba, a k’ananun shekarun ta”, Cewar Malam, ” Nima wlh Malam, ina tausaya mata, shiyasa nake k’aunar ta”, “Ba abunda yafi sai muyi k’ok’arin kyautata mata, mu sa ta manta maraicin ta, duk da cewa ba kud’i ne damu ba”, ” Ai farin ciki da kwanciyar hankali ba kud’i ke kawo su ba, soyayya, kulawa da zaman lafiya yafi kud’i, dan da yawa zaka ga  kud’i amma ba kwanciyar hankali”, “Hakane, ina tunanin nemar mata makaranta nan kusa damu sai ta rik’a zuwa”

   “Da ka kyauta kuwa Mallam”, ” In Shaa Allah zan k’ok’arta”, “Allah ya bada iko”, “Amin”

    Washegari Aliya kad’ai taje aiki, ta bar Fetta, ta mata wasu ayyuka a gida, Breakfast kala uku suka had’a masa aka kai sashen shi aka jera kan dining table, Sai k’arfe 11 ake masa, Dan baya tashi da wuri.

   Idan ya dawo gida, bacci yake sosai, Baya fitowa sai k’arfe 1, Wani sa’in sai Hajiya taje da kanta ta tado shi.

     Tana zaune kan dining table tana breakfast, D’ayan daga cikin yan matan ta sauko daga stairs, Cikin shigarta ta atamfa da d’an k’aramin gyale, ta rataya handbag, da mukullin mota a hannu, “Mama zan tafi school”, ” Toh Su’ad Allah ya bada sa’a”, “Ameen”, ” Amma da gyalen nan zaki fita, kinsan fah yayan ki na gari”, Ta kama baki “Oops wlh na manta”,  Tayi saurin komawa ta sako babban gyale, ta fice, Hajiya tabi bayanta da kallo tana dariya, Yadda suke tsoron Suraj ko ita basa tsoro.

  Doorbell yayi k’ara, Samy dake game a Apple tab d’in ta, Ta tashi ta bud’e, Ta gaishe da Anty Jummai(K’anwar mahaifin su), Ta amsa da sakin fuska.

    ” Sannu da zuwa Jummai”, Cewar Hajiya, “Yawwa Hajiya”, Ta fad’a tana zama kan d’aya daga cikin kujerun, ” Wash na gaji wallahi, ku kam kuna jin dad’in ku, ba ruwan ku da zafi, baku san ma ana yi ba, 24hrs kuna cikin AC”

   Hajiya tayi dariya tace “Ga breakfast”, ” Kamar kinsan yunwa nake ji”, Ta fad’a tana mik’ewa.

    Zama tayi kan dining table, ta cika plate, ta fara ci, Tana jan Hajiya da hira.

    Yan’matan ne ke saukowa daga stairs, kowacce tasha ado, Suka gaishe da Hajiya Tumba, sannan suka gaishe da Anty Jummai, D’aya daga cikin su tana tsananin kama da Aunty Jummai ko ba’a fad’a ba ta kama zaka san yar’ta ce.

    “Ki bud’e kunne da kyau ki saurare ni Bilkisu”, Cewar Anty Jummai, Ta k’ara matsowa kusa da ita, Su biyu ne kawai a d’akin,

   Ta cigaba ” Kada ki kuskura ki bari zaman ki gidan nan ya zama na banza, kiyi amfani da hikimar ki na ya’ mace ki jawo hankalin Suraj, kada ki bari wata ta riga ki, naga yaran su Sule a gidan nan, nasan manufar su, yar’su ta auri Suraj, ki duba kiga duka dukiyar nan da Hajiya Tumba ke fantamawa a ciki mallakin shi ne, idan kika zama matar sa, ai mun warke”, “Kar ki damu Mama, ni zan zama mata a wurin Suraj”, ” Shiyasa nake sonki ya’ta, In Shaa Allah ta sanadin ki zamu yi hannun riga da talauci”, Shigowar Aysha yar’ gidan Sule, yasa suka canza zance.

   Madubin dake jikin bangon d’akin Fetta ta kalla, Shatin marin ya fara bajewa, Ta shafa wurin tare da furta “Allah ya saka mun mugun mutum kawai”, Ta murgad’a baki kamar yana ganin ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *