FETTA CHAPTER 17

FETTA 




CHAPTER 17



Kusan minti uku yana haka, zuciyar sa na harbawa da k’arfi, Shafah na gefe duk ta had’a gumi, +

    “Fatima”, Ya kira sunan ta cikin d’aga murya, Fetta wacce ta idar da sallar magrib kenan, Daga yanayin kiran tasan ba lafiya ba, Addu’ar neman tsari ta karanta ta fito,

   Kallon da yake jefan ta dashi yasa jikinta yin sanyi, yau kuma wani sharrin aka k’ulla mata,

” Meye ribar ki na son mallake ni?, ana so dole?”, Taji kalaman sa kamar daga sama, Kallon rashin fahimta tabi a dashi, “Am asking you”, Ya fad’a a tsawace, Cikin dakewa tace ” Ban fahimci inda kalaman ka suka dosa ba”, “Kada ki raina mun hankali”, Ya juya kan Shafah ” Me na kama ki kina yi?”, Cikin rawar murya tace “Ina sa magani a abinci”, Fetta ta zaro ido, ” Waya saka ki?”, Ta nuna Fetta,

    Kusan mutuwar tsaye tayi, tamkar a mafarki haka take gani, Shafah da ta d’auka da zuciya d’aya, lallai dan’ adam ba abun yarda ba ne, Bakin ta taji ya d’aure ta kasa furta komai,

    “A ina ta samu maganin?”, ” K’awarta ta kawo mata”, Ta kafe Shafah da ido cike da tsananin mamaki, “Kina mamaki asirin ku ya tonu ko?”, Ko gezau bata yi ba, sai ma k’ara matsawa kusa da Shafah da tayi,

    ” Me zaki mata?, dukan ta zaki yi dan ta tona miki asiri?, Allah ne ya kama ki, ashe zaki iya shirka”,

Zuciyar ta ke tafarfasa, bara ta iya jure munanan kalaman sa akan ta, Hannu ta d’aga mishi cikin d’aga murya tace “Enough”

   Mamaki ya kama shi, ya hana shi furta komai ba, “Na gaji! Na gaji! Ni kad’ai ce mutum a duniya da kowa ya tashi sharrin shi Fetta, me na tare ma mutane, meya sa baka kyautata zato a kaina, you always think negative of me, Zaman mu ya kamata ace kasan wacece Fatima?”, Hawaye da suka yi biyo kuncin ta, ta share ta juya kan Shafah, ” Kiji tsoron Allah, kiji tsoron had’uwar ki da ubangiji a filin alk’iyama, ki zab’a kunyar duniya ko ta lahira, na d’auke ki da amana, ashe cuta ta kike, me na tare miki a duniya, Suraj kike so, idan shi kike so gaki gashi, ba sai kin mun sharri ba”,

   Suraj zuciyar sa yaji ta karaya, tausayin ta ya kama shi, “What if she is forming an act”, Wata zuciyar tayi saurin kwab’ar shi ” No iya gaskiyar ta ce”, Ta katse mishi tunani “Idan mallakar ka nake son yi, why on earth zan saka Shafah, da kaina zan yi, for how long muke zaune tare da kai kafin zuwan ta, idan har zan iya sawa da kaina a lokacin meyasa yanzu bazan sa ba, Manzo SAW yace mu kyautata zato, why a ko da yaushe baka bincike kafin ka yanke hukunci, am not as bad as you think, rashin imani na bai kai can ba, i can’t take this anymore, zuciyata bara ta iya d’auka ba, Na gaji SURAJ”, Ta fad’a tare da zubewa k’asan carpet, ta fashe da kuka mai cin rai, 1

   Jikinsa ya sake yin sanyi, bai san lokacin da ya kai k’asa ba, Ya rungumota jikin shi, yana bubbuga bayan ta,

  Shafah tausayin Fetta taji na shigar ta, Tabbas ta d’auki hakk’in ta, idan kuma ta cigaba da yi ma Tasleem aiki, zata k’ara d’aukarwa kanta hakk’i, Da taji kunyar lahira gara taji ta duniya, akan kud’i da yanzu Allah zai iya d’aukar rayuwar ta, Tsoron Allah taji na shigar ta,
    
    ” Ku gafarce ni”, Cewar Shafah tana matsar k’walla, Fetta ta janye jikin ta daga jikin sa, “Wallahi ba Aunty ce ta sakani ba”,  A fusace Suraj ya taso, ya shak’aro wuyan ta, ” Maganin meye?, kuma Uban wa ya saki?, akan me zaki ce matata?”,

   Shafah ta shiga kakari ta kasa magana, ya sake ta ta bugu da bango, Ta dafe kanta cike da azaba, Ya take yatsun k’afarta, tare da murza su da k’afa, Tayi ihun azaba, ya bige bakin ta da k’arfi, Tuni ya shiga jini,

STORY CONTINUES BELOW

   “Zaki yi magana ko sai na binne ki da rai”, ” Bansan na meye ba, Wata mata ce wallahi ta bani tace na saka, ban san sunan ta ba, tasa hijab da niqab”, “Baki santa ba, kuma kika karb’a”, ” Kud’i ta bani”, Ta fad’a murya na rawa,

    “Kud’i ko, kud’i yasa zaki cutar da bayin Allah, ki k’ulla ma Matata sharri”, ” Dan girman Allah kuyi hak’uri, ku yafe mun”,

   Charger laptop ya zaro, ya shiga zuba mata tana ihu, da rok’on sa but kamar cewa take ya k’are, Fetta d’aki ta shige cike da takaicin sa na yarda da yayi,

    Sai da ya mata ligiss, Yasa security suka fitar da ita, Tana kuka ta kira Tasleem ta sanar da ita,

    “Kin taimaki kanki da baki fad’i ni na saki ba, da wallahi na lahira sao yafi ki jin dad’i, Daga yau kin gama mun aiki, kada ki k’ara kirana, ko a hanya kika ganni, kar ki kuskura ki nuna kin sanni”, Ta kashe wayar, Da mamaki tabi wayar da kallo, a tunanin ta idan ta rufa mata asiri zata taimake ta, tace ta dawo gidan su da zama,

   ” Dan’ Adam butulu, wallahi baki isa kici moriya ta a banza, ina zaman zamana gidan aikina, kiyi sanadin a koreni kuma ki zauna lafiya”, Banda tasan security bara su barta ta koma ciki ba, da tsoron Suraj yak’i sauraren ta, ya mata duka, da ta koma ta fayyace komai,  but ko a yanzu bata ci bulus ba, Ta tari napep ya kaita gidan k’anwar Maman ta dake cikin gari.

   Suraj is feeling guilty, Yasan bai kyauta ba, D’akin ya shiga, Fetta tayi tamkar bata gansa ba, Tana cigaba da folding kayan baccin ta da ta wanke, bata sawa a wanki, Yana son mata magana bai san me zai ce ba,

    “Kin ga wasu takardu da na ajiye a dressing mirror?”, ” A’ah”, Ta bashi amsa ba tare da ta kalli saitin da yake ba, “Anan na ajiye fah”, ” Sai kazo ka duba”, Ta fad’a tare da ficewa daga d’akin, Yabi bayan ta da kallo cike da mamakin ta, “Wannan karon ba k’aramin b’ata mata raina nayi ba”, Yacewa kansa, ” Dole zata ji haushi sharri ba dad’i ba”, “To ai bani nace tayi ba”, ” But kayi believing”, Yana ta maganganun sa shi kad’ai, Takardun a bedside drawer ya saka, yana son mata magana ne kawai.

   Fetta zaman ta tayi a falo, ta kunna kallo, This time around she must make sure he realize his mistake, Ta gaji da cin kashin da yake mata,

   Almost 2hours da fitar ta, bai ga ta shigo ba, Ya lek’a yaga kallo take hankali kwance, Ya fito ya nufi kitchen, ya had’a tea, Ya dawo falo ya zauna, yana sha da bread, ko kad’an bata yi wata alama da ta nuna, tasan da zaman sa falon,

“Kin ba babyna abinci?”, Ya jefo mata tambayar, Kai kawai ta d’aga mishi ba tare da ta juyo ba, Jikin sa yayi sanyi yasan bata tab’a mishi irin haka ba, (Nace ka guji fushin mai hak’uri) 1

    Kusan minti goma, ba mai cewa kowa komai, Ta mik’e ta shiga d’aki, Tayi shirin bacci tare da kwanciya k’arshen gado, taja bargo ta lullub’e,

    Suraj kamar kar yasha tea yaji wata irin sha’awa ta motsa mishi, Yayi mamakin me ya kawo mishi lokaci d’aya, da wani ya had’a mishi tea toh tabbas zai ce ya saka mishi wani abu,

    D’aki ya shiga, Da k’yar ya canza kaya zuwa na bacci, Yabi lafiyar gado,

   Duk yadda yaso controlling kansa ya kasa, Ya mirgina ya jawo Fetta jikin sa, Kamar a mafarki taji ana shafa ta, Ta bud’e ido ta sauke su kan Suraj da idon sa ke lumshe, Ta ture sa, tana k’ok’arin mik’ewa ya sake jawo ta, cikin wani irin yanayi, Ta fisge da k’arfi, ” Bazan sake bawa namijin da bai san darajata, bai yarda dani ba jikina”, Ta sauka daga kan gado, ta koma falo, tana dariya, bayan fitowar ta d’aki, ta jefa k’waya mai sa sha’awa cikin flask na ruwan zafi, wacce Yasmeen ta dad’e da bata akan ta rik’a sawa Suraj, Tasan tunda abinci ansa magani, dole zai buk’aci tea,

   Suraj da idon sa suka yi jajir yake cikin matsananciyar buk’ata, ya biyo ta falo, Ta d’aure fuska tace “Kada ka sake ka tab’ani, garar da kasha ta isa tunda har ajiya kayi”,

   Suraj wanda ke jin idan yau bai samu yadda yake so ba, zai iya mutuwa ya rik’o hannun ta, Ta fisge, ” Kada ki hukunta ni ta wannan hanyar please Fetta, bakya tsoron mala’ikun rahma su tsine miki”, “Kana tunanin hakk’ina dake kanka a lokacin da kake aikata mun son ranka”, Suraj ya sake langab’ewa a hankali ya furta ” Am sorry”

   Kalmar da take son jin kenan daga gare sa, Ta maze tace “Ban ga alamar you are sorry ba”, Suraj wanda a buk’ace yake yace ” I mean it, wallahi am sorry”, Ya fad’a tare da rungumota jikin shi, bata yi aune ba taji ya had’a bakin su wuri d’aya, Ta kasa hana shi, Suka lula duniyar ma’aurata.

     “Yanzu sam kin daina damuwa dani ta Hajiya Rabi kawai kike”, Zulaihat ta fad’a cike da kishi, Bilkisu ta jawo ta jikinta tace ” Ba haka bane sweetyna, kud’in ta nake so”, “Ba wani”, ” Allah kuwa”, “Toh naji, zanyi missing d’inki idan kun tafi”, ” Nima zan yi naki”, “Ki mun abunda zan rik’a tunawa nake”, Ta had’e bakin su, suka shiga duniyar masha’ar su.

    Da daddare jirgin su ya d’aga zuwa Dubai, Zulaihat ta mata rakiya airport, Aunty Jummai hadda list na abubuwan da zata siyo mata (Allah ya rabamu da iyaye masu kwad’ayi)

  Karima tayi istibra’i, ta buk’aci Bello ya bata sati d’aya kafin a d’aura aure, Ya amince, ta shiga gyaran jiki.Suraj yana tsaye bakin dressing mirror, yana saka cufflinks, Cikin shigar sa ta shadda light blue sai d’aukar ido take, Ya d’auki turare ya fesa, Ya gyara zaman hular sa, +

   Ya juya kan Fetta dake gyara gado, “Zan tafi d’aurin aure”, ” A dawo lafiya”,

   Har ya kai bakin k’ofa ya juyo “Kar ki sake kiyi shara”, Tayi shiru tamkar bata ji sa ba, ” Are you deaf ?”, Ta sake mishi shiru, Takowa yayi cikin izza ya dawo cikin d’akin, Yazo daf da ita ta yadda tana jiyo numfashin sa,

    “Daraja d’aya kike ci”, Ya fad’a tare da hura mata iskar bakin sa ya fice, K’amshin mouth fresh mai dad’i ne ya ziyarci hancin ta, ya saka ta lumshe ido, ” Ya Allah”, ta furta, Ta sauke ajiyar zuciya tare da mik’ewa ta fara goge dressing mirror.

    Sashen Hajiya ya nufa, ya umarci Inna mai aiki tazo sashen shi ta gyara,

    Sallamar ta ta jiyo daga d’aki ta amsa ta fito, “Mai gida ne yace nazo nayi gyara”, ” Ki bar shi kawai Inna”, “A’ah ba’a yi haka ba, kina buk’atar hutu”,

     Ta bud’e baki zata bata amsa mararta ta murd’a, Ta duk’a tare da ambaton sunan Allah, Inna ta rik’e ta tace ” Subhanallah, sannu ki koma d’aki ki kwanta”, “Yawwa”, Ta amsa da k’yar, Tana dafa bango ta shiga d’aki, ta d’auki zam zam tasha, ta shafa, Tabi lafiyar gado cikin minti uku bacci ya d’auke ta.

    ” Sister please tayani na saka rigar nan”, Su’ad ta fad’a tana k’ok’arin saka riga tak’i shiga, “Mutum yayi ta sa ana mishi matsattsun kaya”, Cewar Feena tana taya ta jan rigar, ” Adnan ne yafi so ya ganni da irin kayan”, “Ah lallai ai sa kiyi ta wahalar sawa da cirewa”, ” Idan munyi aure shi zai rik’a tayani”, Feena ta bud’e baki tace “Ahh ko kunya”, ” Kunyar ki zan ji”, Sukayi dariya.

    K’aramin gyale ta yafa, ta fice tana rambad’a k’amshi, Ta cikin mota ya zuba mata ido, yana jin wani feelings a tare da ita, Ta bud’e murfin gaba ta shiga, k’amshin turaren ta ya game motar, wanda ya sake jefa shi a wani yanayi(Mata a kula, a daina cika turare idan za’a waje saurayi)

   Rungumota yayi jikin shi, Yace “Kinyi kyau My baby”, Ta sake kwantar da kai jikin shi tace ” Thank you”, Ya manna mata kiss tare da cusa hannun shi cikin rigar ta, bata hana shi ba, sai ma k’ara bashi goyon baya da tayi, suka shiga romancing juna, a kasalance ya d’ago yace “Baby please muje hotel”, ” Am scared”, “Ba wani tsoro ni zaki aura fah, kina so na shiga wani hali”, Ta girgiza kai, ” Please ki amince muje”, Tayi nodding kai, “Wow I love you”, Ya fad’a tare da manna mata kiss.

   Bilkisu sun isa Dubai, Hajiya Rabi ta kama musu makeken hotel wanda sai masu kud’i ke sauka a can, suna ta masha’ar su, a tare suke kwana tamkar mata da miji.

    Karima ta shiga gyaran jiki, duk wani kayan gyaran jiki da maganin mata, ta siya tana amfani dashi.

    ” Shiru kake ji Malam yaci shirwa” Aunty Jummai tacewa Aminiyar ta, “Hmm nifah lamarin nan ya soma bani tsoro, ba irin asirin da bamu yi ba amma ace cikin yak’i zubewa”, Cewar Aminiyar ta, ” Hmm mu zuba ido dai muga aikin Boka”, “Toh ya zancen komawar Bilkisu”, ” Sai Yar iskar baroroji tayi gaba”, “Yawwa haka ya dace ta wuce ajin kishi da baroroji yar’ mai gadi”,

    Fetta wuni tayi bacci, bata farka ba sai ana kiran la’asar, Ta tashi da sunan Allah, Toilet ta shiga, ganin mutum kwance cikin jacuzzi, tayi hanyar fita a tsorace, Taji an jawota, Ihu ta saki, bakinta taji  an toahe, juyowar da zata yi idonta ya sark’e da na Suraj, ” Yaushe ya dawo?”, Ta tambayi kanta,

    Soso ya saka mata a hannu, tare da nuna mata baya, Mamaki ya hanata ce masa komai, Gira ya d’aga mata alamar ya dai, Hannun sa ta jawo, ta saka mishi soson ta juya ta fice, Yabi bayanta da kallo cike da mamaki, “She  is taking advantage na babyn jikinta tana raina mun hankali dole na gyara mata zama”, Ya fad’awa kansa, Ya cilar da soson gefe ya watsa ruwa ya fito,

    Fetta  baya wurin kitchen taje tayi alwala, Ta shigo d’akin ta d’auki sallaya ta shimfid’a ta saka hijab, Ta kabbara sallah ba tare da tabi ta kansa ba, wanda hakan ya k’ara k’ular dashi,

    Shirin sa yayi cikin kaya mara sa nauyi, Ya zauna gefen gado yana jiran ta idar,

   Minti biyar ya d’auke ta, ta idar tayi addu’o’i, Ta nad’e sallaya da hijab ta ajiye, zata fita d’akin, Yace ” Zo nan”, Cikin isa,

    Gaban sa taje, “Kin tsaya mun a kai tamkar soja”, Ya fad’a cike da fad’a, Kujerar dake gefe ta zauna, Ya taso ya tsaya daf da ita, ” Dan kina d’auke da babyna bashi zai baki privilege na mun rashin kunya da rainin hankali ba”, Kallon bata fahimce inda kalaman sa suka dosa ba tabi shi dashi, “Wallahi ya zama na k’arshe da zan saka ki abu ki k’i yi, Suraj baya bada umarni a tsalleka”, Ya fad’a tare da had’a yatsun sa ya basu d’ass,

   Murmushin gefen baki tayi tace ” Shikenan, zan iya tafiya?”, Bakin sa ne ya sark’e tsananin mamaki ya hana sa furta komai, Jin yayi shiru ta mik’e ta fice,

    “Yarinyar nan ta raina ni fah, kai ta raina mun hankali”, Zuciyar sa ta fad’a mishi, Ya mik’e a fusace, ” Idan kamata wani abu ya shafi babyn ka fah”, Wata zuciyar tace mishi, “Zanyi maganin ta daga ranar da babyna yazo duniya”, Yayi assuring kansa.

    ” Haba My baby ki daina kukan mana, so kike kije gida a fuskanci wani abu”, Cewar Adnan cikin sigar lallashi, Su’ad dake lullub’e cikin bargo taja majina tace “K’asana ke zafi sosai”, ” Muje na saki a ruwan zafi”, Ya fad’a yana janye bargon, Ya d’auke ta zuwa toilet, ya tara ruwa a bathtub, ya saka ta, Tana ihun azaba,

    Tayi wankan tsarki, Ta shirya ya mayar da ita gida, bayan ya biya ,ya mata shopping mai yawa, Tana komawa gida sai baccin wahala, dan Adnan bai mata da wasa ba.

     Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah, Cikin Fetta ya shiga wata bakwai, yau ciwo gobe lafiya, ga ciwon mara da take yawan fama dashi, Suraj na bata kulawa sosai, Hajiya, Aliya da Yasmeen suma ba’a bar su a baya ba, wajen bata kulawa, Malam na aiko mata addu’o’i akai akai, Ganin ciwon ba sauk’i, Yayi deciding su tafi Umrah, su rok’i ubangiji daga can su wuce London, baya so ta haihu a 9ja.

    Fetta ta fito da shirin ta cikin jallabiya da gyale, sun matuk’ar yi mata kyau, cikinta da yayi tsini ya fito d’ass, Da kallo yabi ta,

   “Koma ki saka hijab”, Ba tare da tace  komai ba, ta koma tasa, still ya mata kyau,

   A mota ba mai cewa kowa komai ba, har suka kawo immigration office, Yace ” Ta fito”, Ta biyowa bayansa,

     Sun tarar da layi sosai, Amma abun ku da naira da kuma hanya, ba b’ata lokaci ta shiga aka mata passport.Ya ajiye ta gida, Ya wuce ya kai international passport nashi da nata a musu visa. +

    Karima anyi auren su da Bello, ya d’auke ta sun koma Abuja da sunan ya samu aiki a can, Ta shiryu, ta koma ga Allah, kullum cikin istigfari,

   Su’ad da Adnan abun su yayi gaba, almost all the time suna tare, ya d’auke ta suje hotel suyi sharholiyar su, ta saba wani lokaci ita ke requesting.

    “Please bana so yayi taking time”, Cewar Suraj, ” Kada ka damu ranka ya dad’e in two days time komai zai kammala”, “OK”, Ya fad’a tare da ficewa.

     ” Komai baya tafiya daidai, yanzu ya kamata ace tuni na dad’e da mallake Suraj”, Tasleem ta fad’a tana zagaye d’akin, Sophy dake zaune bakin gado tace “Nasha gaya miki ki hak’ura da Suraj, samun irin shi nada matuk’ar wahala”, A fusace ta juyo tace ” Ni kuma nasha gaya miki bazan tab’a hak’ura dashi ba”, “OK then”, Ta fad’a tare da d’age kafad’a, Ta shiga danna wayar ta,

   Tasleem ta kasa zama, tunanin ta ya zata shawo kan Suraj, duk hanyar da ta bi is not working, Ya zama dole ta k’ara zage damtse, babban takaicin ta Fetta da zata haihu, ” Ki sace babyn ki kashe shi”, Zuciyarta ta fad’a mata, Tayi murmushin mugunta.

   Aunty Yelwa ce zaune tsakar gida, Wayarta a hannu tana kira ana ce mata number busy, “Ko da uwar wa yake waya yasan ina jiran sa”, Ta fad’a tare da yin k’wafa, Kiran sa ne ya shigo wayar, Ta danna receive,

    ” Dawa kake ta waya ne?”, “Ai ke nake ta kira ana cemun busy”, ” Oh toh, ya ake ciki ka same shi?”, “Eh yanzu haka muna tare”, ” Good aikin ka yayi kyau, gani nan zuwa”, “Sai kin zo”, Ta kashe wayar tare da fad’in ” Lokacin ramuwa yazo Jummai, kin d’auka kinci bulus”, Tayi murmushi mai cike da ma’anoni.

    Aunty Jummai tana zaune d’aki ta rafsa tagumi, Bilkisu ta shigo da sallama, sam bata ji ba tayi nisa a tunani, Ta janye hannun ta tace “Umma tunanin me kike?”

   Ta sauke ajiyar zuciya tace “Hmm cikin Fetta da yak’i zubewa, gashi har ya girma”, Bilkisu tace ” Nima abun na matuk’ar damuna, dan wallahi ina so na koma gidan Suraj kuma bana son kishi da ita”, “Ina tunanin mu kashe jaririn kar yazo duniya ko ranar da aka haife shi”, ” Nima nayi tunanin hakan”, Cewar Bilkisu, “Wannan itace mafita”, ” Umma zan fita”, “A dawo lafiya, kina da yan’ chanji”, Ta bud’e jaka ta zaro dubu biyu ta bata, Ta karb’a tana washe baki, Bilkisu a ranta tace ” Umma ba dai son kud’i ba”, Ta fice zata je wurin wata yar’ lesbian da suka had’u a Dubai.

  
     “Zancen tafiyar ka da Fetta, hankalina bai kwanta ka tafi da ita haihuwa wata k’asa, ba wani nata a can” Cewar Hajiya, “Mama tafiyar nata shine mafita, duba da yawan rashin lafiya da take, wanda mak’iya ne gara ta bar 9ja ta haihu a can lafiya”, Hajiya ta nisa tace ” Hakane but ya kamata ku tafi da wani babba da zai kula da ita”, “Kada ki damu Mum, a can zan samu masu kula da ita”, ” OK Allah yayi jagora, Allah ya sauke ta lafiya”, Ya amsa da “Amin”

     Fetta na kwance a kujerar falo tana kallon Sunna TV, Ya shigo da sallama, Ta amsa ba tare da ta d’aga kai ta kalle shi ba, Kusa da ita ya zauna tare da d’aura hannun shi saman cikin ta, Ta d’ago kai ta kalle shi, Kallon da ya jefa mata yasa ta sunkuyar da kai jiki a sanyaye, Suraj ya nak’alci kallo iri-iri,

   Cikin yake shafawa cikin wani salo wanda ya saukar mata da kasala, Rigar ya d’aga ya sumbaci cikin, “Safe delivery”, Ya fad’a tare da mik’ewa ya nufi d’aki.

STORY CONTINUES BELOW

    Aunty Yelwa ta fito cikin napep, ta sallame shi, ta shiga wani k’aramin gida wanda shi kad’ai ne a layin, unguwar tsit ba gidaje da yawa, Ta duba gabas da yamma, Ganin ba kowa ya shiga, Ta wuce tsakar gida zuwa falo,

     ” Sannu da zuwa Ranki ya dad’e”, Cewar Matashin saurayi kallo d’aya zaka mishi kasan dan’ daba ne, Ta amsa da “Yawwa, Ina Sahabin?”, Da hannu ya nuna mata shi, Yana zaune ya d’aura k’afa d’aya kan d’aya, Yana zuk’ar sigari,

    ” Kai ne Sahabi?”, Ya d’aga kai tare da hura iskar sigari, Ta kawar da kai gefe tana toshe hanci, “Kai ke yiwa Jummai aiki”, ” K’warai”, “Ina so ka mun aiki a kanta”, ” Wane irin aiki?”, K’asa tayi da murya ta sanar dashi, Wanda ko Dan’ Bala dake gefe bai ji me tace ba, “An gama in dai zanji dumus”, Tayi murmushi tace ” Kar ka samu damuwa”, Ta bud’e jaka ta zaro dubu goma tace “Ka fara da wannan”, Ya karb’a ya saka a aljihu, ” Zan koma ina sauri”, Dan’ Bala yace “Toh ni me zan samu?”, Ta zaro dubu biyu ta bashi, Ya mata rakiya bakin gate ta wuce.

      Suraj throughout yana office, aiki ya mishi yawa kasancewar gobe zasu wuce, yana so yayi handing over wasu ayyukan shi ga yaran shi.

     Fetta nata faman had’a kayanta da taimakon Yasmeen, yace kar ta d’auki kaya da yawa, ” Zanyi missing d’inki sosai Maman Unborn”, “Nima zanyi naki”, ” Da ina da kud’i da na bi ki”, “Da nafi kowa farin ciki”, ” Uhmm ba ma zan bi ki ba, na hana ku shan love, dan nasan hadda honeymoon za’a je”

   Rigar dake hannunta ta wurga mata,  Dariya tayi tace “Daga fad’ar gaskiya”, ” Ke ko?”, “Eh mana”, ” Ni dai muyi sauri, ina so naje nayi sallama dasu Umma”, Suna gyaran kayan tana tsokanar Fetta akan Suraj.

     “Kina ji Ya Suraj zai tafi da baroroji London ta haihu a can”, Cewar Feena, Su’ad tace ” What!”, “Wallahi”, “Lallai, yarinyar nan da shirin ta fah”, ” Hmm ni bak’in cikina ma zamu had’a iri da bararoji dangin matsiyata”, “Ni har bana son tunawa”, ” Dama yaron ya mutu wurin haihuwa”, “Allah yasa”, ” Amin”

     Fetta tare da Yasmeen suka je gidansu Aliya, Sunyi farin ciki sosai jin ba’a anan zata haihu ba, Sun san kariya ce zata samu daga mak’iya, duo da zasu yi kewar ta sosai, Aliya ta had’a mata dukkan abun buk’ata na haihuwa na gargajiya, Mallam ya mata wasu addu’o’i a zamzam,

   Bayan sallar magrib suna zaune tsakar gida, suna hira suna cin dan’ wake, Wayarta ta d’auki ruri, Tana gefen Yasmeen ta kalli screen tace “Habibi na kira, mu tashi mu tafi”, Ta harare ta, ta d’auki wayar,

   ” Ki dawo gida”, Shine abunda ya fad’a ya kashe wayar, “Mutum sai isa da izza”, Ta fad’a a ranta, ” Umma zamu tafi”, “Toh Fetta, Allah ya kai ku lafiya, Allah ya tsare ki ya sauke ki lafiya”, Ta amsa da ” Ameen”, “Idan Malam ya dawo ki fad’a masa mun wuce”, ” Toh”

    Ta musu rakiya har mota, Yasmeen a harabar gidan ta tsaya, Tace “Bazan shiga ba, gida zan wuce”, Fetta tayi fuskar tausayi tace ” Haba Dan Allah”, “Rufa mun asiri, bana son harka da mijin ki, Allah ya kai ku lafiya, sai munyi waya”, Ta b’ata rai ta shige ciki ba tare da ta sake ce mata komai ba.

    D’aki ta tarar dashi, Ya fito da takardu ya barbaza akan gado, Yana rubutu akai, wasu yana d’auka hoto,

   ” Kullum fama da takardu kamar dan’ jarida”, Ta fad’a a ranta, Toilet ta nufa ta d’auro alwala ta fito, Idon shi akan ta, “Ba ki iya gaisuwa”, ” Naga hankalin ka ya d’auko ne, kar nayi distracting d’in ka”, “Oh really?” Ya fad’a yana d’aga gira, “Sorry Ina wuni?”, Bata shirya ma tsiyar shi ba, “Sam baya so a zauna lafiya”, Ta fad’a ranta,

    ” Rik’e gaisuwar ki, bana so “, ” Huu”, Ta fad’a a ranta tare da sauke ajiyar zuciya, Bata sake ce mishi komai ba, Ta nufi Sallah.

      *10:00am*
Fetta da Suraj suka fito cikin shirin su, zuwa airport, Sashen Hajiya suka shiga su mata sallama, Tana zaune kan dining table tana breakfast,

    A tare suka gaisheta ta amsa, “Tafiya ta tashi?”, Suraj yace ” Eh”, “Allah ya tsare ya kai ku lafiya”, Suka amsa da ” Amin”, “Sai mun zo ganin baby”, Kunya ta kama Fetta, ta saukar da kai k’asa.

   Bakin mota ta musu rakiya tare da addu’o’i.

      Dukkan su bayan mota suka shiga, Driver yaja su zuwa airport, Suna zuwa ba b’ata lokaci, sukayi boarding, suka shiga jirgi, ya d’aga sararin samaniya, Fetta sai zare ido take abun ku da sabon shiga, Suraj ya shiga yi mata dariya, Ta kalle shi cike da takaici, Bai fasa ba, sai ma k’arawa da yayi, Tsayawa tayi kallon sa, dariyar ba k’aramin kyau ta mishi ba, wannan ne karon farko da ta ganshi yana dariya, Ta nemi haushin nasa ta rasa, sai ma shagala da tayi da kallon sa,

    Ganin tana kallon sa, Ya maze ya d’aure fuska ” Ya dai kika zuba mun ido kamar zaki cinye ni”, Kafe idonta tayi tamkar bashi take kallo ba, irin hankalin ta na wani gun, Hannu yasa yana waving, Still bata motsa ba, Yayi clapping hannun, 1

    Ta motsa idon ta, tace “Ya dai?”, Kawar da kansa yayi gefe, itama ta kawar da nata gefe, Tana kallon sararin samaniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *