FETTA
CHAPTER 2
K’arfe sha biyu da minti biyar daidai ya farka da sunan Allah a baki, Mik’ewa yayi ya shiga toilet, Wanka ya fara yi, Yayi brush, Ya fito, Cikin minti 15 ya shirya cikin wata arniyar shadda light blue, Ta matuk’ar amshi jikin sa, kuma ta mishi kyau. +
Dining area ya nufa, Yayi serving kansa potato chips da egg sauce ya fara ci, Wayar sa tayi ringing, Murmushi yayi ganin farin cikin sa ce, Ya danna receive, tare da saka handsfree, “Mamana ina kwana?”, ” Lafiya lau Yaron albarka, ka tashi lafiya?”, “Lafiya lau”, ” Naji ka shiru ne, na kira naji lafiya”, “Am fyn Mamana, gani nan zuwa da na gama breakfast”, ” Toh sai kazo”
Yayi hanging up, Yana murmushi, Bai had’a mahaifiyar sa da kowa ba, Yana tsananin k’aunar ta.
Ya gama ci, yasa tissue ya goge baki, Ya fito zuwa sashen Hajiya Tumba.
Anty Jummai kamar zata kifa k’asa wurin gaishe sa, “Ina kwana Alhaji Surajo”, Rai a b’ace ya kalle ta yace ” Bana son irin gaisuwar nan da kike mun, matsayin mahaifiyata kike fah”, Sam baya son irin gaisuwar nan da take masa, wanda yasan duk akan abun hannun shi ne take haka.
“In banda abun ka ai durk’usawa wada ba gajiya bane”, Ta fad’a tana dariya, ” Ni dai na rok’e ki da Allah ki daina”, “Toh na daina, Allah yayi albarka”, Ya amsa da “Amin”
Gaban mahaifiyar sa ya duk’a ya gaisheta, Ta amsa tare da shafa kansa kamar kullum, Zama yayi k’asan carpet, Hajiya Tumba ta nisa tace “Dama batun taimakon da aka saba kai was gidan marayu duk wata, lokaci yayi”, ” Ohh na manta gaba d’aya” Ya fad’a yana d’an dafe kai, “Akwai ka da mantuwa kamar wani tsoho”, Yayi murmushi yace ” Gobe In Shaa Allah za’a kai”, “Allah ya kaimu, Ya k’ara arzik’i”, ” Amin”
Anty Jummai dake gefe tace “Akwai wasu marayu kusa damu, suna buk’atar taimako wallahi”, Suraj yasan ba wasu marayu, ita ke so a bata kud’i ta cinye, Hannu ya saka a aljihu ya zaro bandir na 500, Ya ajiye gabanta yace ” Gashi ki basu”, Ta shiga zuba godiya, “Allah ya biya ka dan’ albarka, Allah ya jik’an mahaifin ka”, ” Amin”, “An gode an gode”
“Mamana zan fita cikin gari, ina so na duba shaguna naga ya suke tafiya”, ” Allah ya bada nasara”, “Amin”
*Asalin su Suraj*
Marigayi Sa’idu Mai kasuwa shine miji a wurin Hajiya Tumba, Haifaffan garin kano ne, bafullatani d’an garin shanono, Mutum ne shi mai tsananin hak’uri da halin dattako, Sana’ar trader yake, Yana da k’aramin shago da yake siyar da kayan provision, Da sana’ar yayi aure har ya haifi yara hud’u, Suraj ne babba sai Su’ad, Safeena da Sameera autar su, Suna zaune cikin rufin asiri da matar sa Tumba,
Marigayi Sa’idu gidansu su 7 ne kuma cikin su shine bashi da k’arfi sosai, Dan haka suka k’aurace mishi komai basa shawara dashi, basa ma zuwa gidan sa sai dai shi yaje nasu, Bai tab’a nuna musu wani abu ba, Suraj tun yana k’arami abun na matuk’ar k’una masa rai yadda ake ware su cikin dangi.
Yana shekara 17 Allah yayi wa mahaifin su rasu, bayan yayi yar gajeruwar rashin lafiya, Daga lokacin suka fara d’and’ana wahalar rayuwa, da ganin tsantsar k’yamata wurin dangin mahaifin su, Sa’idu ya rasu bai bar musu komai na gado ba, Itama Tumba danginta ba masu k’arfi bane, Iyayenta sun dad’e da rasuwa,
Suraj ya fara fita kasuwa yin aikin k’arfi, shine d’aukar kaya, tuk’a barrow da sauran su, Yan’ kud’in da ya samu dashi suke siyan abinci suci, Allah yayi shi yaro mai son neman nasa sam baya son raini, shiyasa baya shiga mutane, magana ma wahala take masa, Mutane da yawa kance ya cika fad’in rai,
Watarana suna zaune tsakar gida, Su’ad da Safeena suka shigo suna kuka an koro su daga makaranta basu biya ba, Cike da damuwa Tumba tace “Kuyi hak’uri ku daina kuka”, Suraj ne ya daka musu tsawa ” Dalla ku rufewa mutane, kukan me zai k’ara ko ya rage”, Suka yi saurin yin shiru, sun san halin sa yanzu jikin su zai gaya musu.
D’aki Tumba ta tashi ta shiga, Ta saka hijabi ta fito, Suraj ya kalleta yace “Mama ina zaki je?” “Zan je gidan Sule na rok’e shi rancan kud’i na fara sana’a, idan na samu riba sai na biyasa, na cigaba da juya saura”, ” A’ah Mama kada kije, kinsan halin su kada su wulak’anta ki”, “Rance zan karb’a, ba kyauta ba”, Ya mik’e yace ” Muje na raka ki”
Bayan ta gama fad’a masa buk’atar ta, Ya tura hula gaban goshi yace “Naji buk’atar ki, sai dai maganar gaskiya ba zan iya baki ba, dan bani da tabbas na zaki biya, kuma lalurori sun mun yawa”, ” Haba Yaya Sule yanzu dubu goma ai na dauka ko kyauta zaka iya bani”, “Toh ba zan bayar ba, nace ba zan bayar ba, wani ya tayani neman kud’in”, A fusace Suraj ya rik’e hannun mahaifiyar sa yace ” Tashi mu tafi”, “Eh ku tashi ku fad’i, shegen yaro mai mugun fad’in rai, dama talaka da fad’in rai, kayi zuciya mana kayi kud’i ka taimaki uwar ka, Dan’ jakar uba”
Ransa ya kai matuk’a wurin b’aci banda kasancewar sa Yayan mahaifin sa ba abunda zai hana ya mayar masa magana,
Haka suka dawo gida rai ba dad’i, Tumba nata hawaye, Ya shiga share mata, “Ki daina kuka Mamana, In Shaa Allah sai na d’aga darajar ki, zan kula dake da k’annena ta yadda kowa zai dinga sha’awar ku da sun rab’ar ku, Dangin Abba sai sunzo suna neman taimako wurin ki”, Murmushi kawai tayi, ba dan ta kama zancen sa ba, tana ganin abu ne da ba zai tab’a yiyuwa ba, A ina zai samu wannan arzik’i, A duniyar da ta zama kowa nashi ya sani, ramin kura daga ke sai yaran ki.
Suraj ya k’uduri a ransa zai nemi kud’i, Yayi arzik’i sosai da zai d’aga darajar mahaifiyar sa, Sati biyu ya jera yana aikin k’arfi sosai, Har ya tara kud’in motar zuwa Lagos, Da ya sanarwa mahaifiyar shi k’udurin shi na tafiya, Taso hana shi, Yayi k’ok’arin lurar da ita, har ta amince.
Ranar da zai wuce har tasha ta rakasa tana masa addu’o’i da fatan alkhairi, Ya tafi cike da kewar gida, Suma ya barsu da kewa.
Suraj ya shiga lagos da k’afar dama, zuwan sa kenan ya had’u da wani Alhaji hamshak’in mai kud’i, Ya jawo sa a jiki, Ya yaba da hankalin Suraj haka yasa, ya jefa shi cikin sana’ar sa ta kasuwanci na siyar da motoci, Lokaci d’aya Suraj ya kud’ance, Ya gina makeken gida, ya d’auke mahaifiyar sa da k’annen sa suka koma can, A lokacin ne dangin mahaifin su suka fara rab’ar su, Ba k’aramin kulawa yake ba mahaifiyar sa da k’annen sa ba, duk abunda suke buk’ata yana musu.
Yaba k’annen shi kyawawan tarbiya, Mutum ne shi mai zafin rai, miskilanci, Shekararsa 27 amma sam mace bata gaban sa, bai tab’a soyayya ba, dan bata cikin tsarin sa. Duk da matan dake nuna zalama a kansa, Wanda yasan ba dan Allah suke son shi ba, Sai dan kyawon sa da abun hannu.
Shagunan sa yake zagayawa yana ganin yadda suke gudanar da kasuwanci (Na sana’ar siyar da wayoyi da electronics).
“Suraj ne wallahi”, Wata matashiyar budurwa ta fad’a tana nuna shi, ” Wane Suraj?”, “Mai gidan marayu fah, wanda yake taimakawa gajiyayyu da zawarawa wanda ake nunawa a TV”, ” Ohh” ta fad’a tana kallon saitin da ta nuna mata, “Wallahi shine kuwa, muje mu masa magana”, ” A’ah nikam bana son ya wulak’anta ni ance yana da girman kai”, Tsaki taja tace “Duk fad’in mutane ne, mai girman kai ne zai dinga taimakawa al’umma”, Taja hannun ta suna nufar wurin shi,
D’auke kai yayi tamkar bai gansu ba, ” Ina wuni?”, D’ayar su ta fad’a, “Lafiya”, Ya amsa ba tare da juyo ba, Ya kalli d’aya daga cikin masu tsaron shagon yace ” Attend to them, customers ne”, Yana fad’ar haka ya fice abun sa,
Ya barsu tsaye cike da zafin rai “Kinga abunda kika ja mana ko, ya yarfa mu, mune yaran commissioner amma mun zubar da class d’in mu”, Kasa cewa komai tayi, Suka yi hanyar fita, ” Yan mata kun fasa siyayyar ne”, Harara ta juyo ta watsa masa, Ya fashe da dariya a ransa yace “Shine daidai da irin ku mata masu rawar kai”Gidan marayun sa ya nufa, ya kai taimako kamar yadda ya saba, Ya duba lafiyar yaran tare da tambayar matsalolin su, Yara da manya a gidan marayun suna matuk’ar son sa, Har su suke yazo, Dan sun san duk ranar da yazo zasu samu sababbin kaya kuma suci dad’i, Kaji yake kawowa masu yawa yace a soya musu suci. +
Ma’aikatan wurin har bakin motocin sa suka raka sa, Suna amsa addu’a da fatan alkhairi.
Gida ya umarce su da suna nufa, Motocin sa na shiga, Motar Yaya Sule ta biyo baya, Fitowa yayi cikin takun sa da kamar baya son taka k’asa, Yaga Sule yayi kamar bai gan sa ba,
“Ahh Suraj ne, sannu da dawowa”, Juyowa yayi yace ” Ina wuni?” Ba tare da ya duk’a ba, “Lafiya lau, ya ayyuka?”, Ya fad’a yana washe baki, ” Alhamdulillah”, Ya amsa ya shige sashen shi, Bai nufi cikin gida ba yasan can Kawo sule za shi, baya son wata doguwar magana ta had’a su.
Babu kowa a falon ya zauna kan kujera, Yana raba idona “Arzik’i kashi, Allah ya bamu mu tattaka, dole na had’a auren Aysha da Suraj ko ma samu rabon mu”, Yayi maganar a fili, Safeena ce ta shigo falon, dawowarta daga makaranta kenan, Ta gaishe sa, Ya amsa tare da cewa ” Ki fad’awa Hajiya nazo”, Ta amsa da “Toh”, A zuciyar ta tace ” Wasu dai basu san kunya ba, ko kunyar zuwa gidan nan baya ji, bayan irin rashin mutunci da ya rik’a shuka mana”, Taja tsaki ba tare da yaji ta ba.
“Mama ga wancan mutumin nan yazo”, Cewar Su’ad tana yatsina baki, ” Wa kenan?”, “Kawo Sule mana”, ” Shi kike cewa wancan mutumin, meyasa baki da kunya ne Su’ad, k’anin mahaifin ki ne fah”, “Toh ai ba….”, ” Kar na sake naji bakin ki a wurin nan, fita ki bani wuri”, Ta fita ta gunguni, da mamakin sanyin halin mahaifiyar su, banda tana hana su wallahi ko ruwan gidan nan, kawo Sule da yaran shi bara su sha ba, kai duk ma wani dangin mahaifin su, Hajiya Tumba duk abunda suka aikata gare ta bata k’ullace su ba, kuma ba zata tab’a zumuncin dake tsakanin su da yaran ta ya lalace ba, ko dan Mahaifin su har ya rasu yana son yan’ uwan sa, bai tab’a k’ullatar su ba.
Hajiya Tumba gyalenta ta yafa ta sauko falon k’asa, Da sakin fuska tace “Sannu da zuwa Yaya Sule”, ” Hajiya ina wuni?, Ya hidimomi?”, “Alhamdulillah”
Masu aiki ta unarta suka kawo mishi ruwa da lemo, bayan yasha ya natsa, Yace “Uhmm dama maganar yaran nan”, ” Wane yara kenan?”, “Suraj yanzu shekarar shi 27 ya kamata ace ya fara tunanin ajiye iyali, ya mallaki komai aure kad’ai ya rage masa”, Hajiya tayi smiling tace ” Nima na fara tunanin haka, kuma ina da niyyar yi mishi magana”, “Toh Mashaa Allahu, dan aure shine cikar kamalar mutum”, ” Hakane amma a yadda na lura dashi, babu soyayya tsarin sa, ban tab’a ji ya kawo mun zancen wata ba”
Yar dariya yayi yace “Banda abun ki Hajiya, ga yan mata a gida ai sai a zab’i d’aya a bashi”, ” Suwa kenan?”, “Kamar dai ba bahaushiya ba, ko Aysha aka had’a shi da ita, ai an k’ara k’arfin zumunci”, Tasan za’a rina tunda yazo mata da zancen auren Suraj,
” Yaya Sule yaran yanzu, ba’a musu dole, tunda bashi ya gani yana so ba, ko ita ta gani tace tana so”, “Babu maganar dole, yan’uwa ne, jini d’aya suke ba yadda za’a yi suk’i juna, ki kira Suraj ki sanar dashi, ni da kaina zan fad’awa Aysha, sai su fara ganin juna”, ” Shikenan, Allah ya zab’a mana mafi alkhairi”, “Auren nasu shine alkhairi ma”, Tayi murmushin takaici na sanin ba dan Allah da zumunci yake so ayi auren nan ba, sai dai abun duniya, Nuna rashin amincewar ga auren nan, zai iya haifar da matsala babba, ya zama dole ta nuna goyon baya, Fatan ta idan ba alkhairi bane Allah kada ya had’a kansu.
Cike da farin ciki Kawo Sule ya koma gida, ya sanar da matar sa, bakin ta kasa rufowa yayi dan itama lashe money ce, Ya kira Aysha yace ta dawo gida, Rai bai so ba ta koma, Tana da masifar son rayuwar k’arya, sam bata son zaman gidan su, can ba wani dad’i suke ci ba, gidan Hajiya Tumba kuwa sai abunda suka zab’a, Ta d’auke su tamkar yaran ta komai yi musu take.
Zancen da mahaifin ta ya mata, ya wanke zuciyar ta, Ta dinga tsalle a d’akin ta, zata auri Suraj, Ta shiga cikin sahun manya, ta kece raini, ta gurza naira yadda take so, Zama mata a wurin SURAJ SA’IDU SS ba k’aramin abu bane.
Labarun NTA suke kallo, Fetta ta lullub’e cikin hijabi sanyi take ji, Garin yayi sanyi sakamakon ruwan sama da akayi,
Suraj aka hasko yana mik’a taimako ga gajiyayyu a wurin wani taro da akayi na taimaka mara sa k’arfi, “Kamar mutumin kirki, yana nunawa duniya shi na kirki ne amma mugu ne”, Malam da Aliya suka maido kallon su gare ta, Aliya tace ” Fetta kinsan shine?”, “Shine ya mare ni”, Malam yace ” Kai Fetta, wallahi na d’auka wani mugun abun yake”, “Suraj ne d’an gidan Hajiya Tumba, akwai sa da zafin rai amma yana da tausayi da taimako”,
Tab’e baki tayi, a ranta sam bata yarda yana da tausayi ba, mai tausayi ba zai mata marin da ya mata ba.
Sai da ya tabbatar Kawo Sule ya bar gidan, Ya shigo wurin Mahaifiyar sa, Bayan sun gaisa.
Cikin tattausan lafazi tace ” Suraj girma kake, kana k’ara manyan ta ya kamata ace ka fara tunanin ajiye iyali”, Far’ar dake kan fuskar sa ta d’auke, “Mama Dan Allah ki daina zancen aure yanzu”, ” Idan ban maka yanzu ba, yaushe zan ma Suraj, cikar kamalar da’ namiji aure”, “Kiyi hak’uri Mama, amma babu yarinyar da nake so”, ” Ga yan’ mata da yawa na son ka, ka duba d’aya daga cikin su “, ” Ban yarda da tarbiyar su, da son da suke mun, nasan akan dukiyata ne, ina son na samu yarinyar da zata soni tsakani da Allah”, “Kana da gaskiya, amma me zai hana ka gwada Aysha yar’ gidan Yaya Sule”
A razane ya d’ago yace “Mama da kanki, Aysha fah Yar’ gidan Kawo Sule”, Ta d’aga mishi kai tace ” Eh”, Zufa ce ta fara karyo masa, ya kasa yarda ace mahaifiyar sa ce ke cewa ya auri Yar’ kawo Sule, bayan tafi Iowa sanin halin su, Ta rik’e hannun shi tace “Ka fahimce ni My son, Kawo Sule yazo mun da buk’atar, idan na nuna rashin yarda ta hakan zai iya jawo matsala, ina so ka nuna yardar ka daga baya sai mu san abun yi”, ” Na yarda dake Mamana nasan ba zaki tab’a cuta ta ba”, “Allah ya maka albarka”, Ya amsa da ” Amin”
Yana jin b’acin ran na barin sa, babu aure a tsarin rayuwar sa, balle auren Yar’ kawo Sule abunda ba zai tab’a yiyuwa bane.Malam ya nemarwa Fetta wata makaranta a kusa dasu ta fara zuwa, Tafi makarantar data baro, Duk da cewa itama wannan bambamcin ta data gwamnati kad’an ne, Dubu biyar ake biya a wata. +
Da sanyin safiya tayi shirin ta na makaranta tana saka safa, Aliya ta lek’o tace “Fetta ki fito kiyi karin kumallo”, ” Toh Umma”,
Kunu da k’osai ne Malam ya siyo musu, A babbar tabarma da Aliya ta shimfid’a tsakar gida ta zauna, Tana ci, K’wara uku kad’ai taci ta tashi, “Dawo ki zauna ki k’ara ci, yarinya bata son cin abinci shiyasa bakya k’iba”, ” Allah Umma na k’oshi'” Ta fad’a da shagwab’a, “Toh ai shikenan”, Bata son takura mata, tana tausayinta saboda maraicin ta.
Jakar makaranta ta d’auka wacce yanzu bata buhu bace, dubu d’aya da d’ari biyar Mallam ya siyo mata a kasuwa, Ta fito ta sami Aliya a tsakar gida tace ” Umma na tafi”, Hab’ar zani ta kwance ta zaro naira hamsin tace “Ungo kud’in break”, Tasa hannu biyu tayi godiya, ” Allah ya bada sa’ar karatu”, “Amin”
Ta fice, tana jin k’aunar su Aliya a ranta, sun zame mata tamkar iyayen da suka haife ta, a duniya yanzu bata da kamar su.
Tun daga bakin gate na makaranta, Duk wanda ya ganta sai ya mata magana, Allah ya zuba mata farin jini, Kyawon ta ke k’ara jawo hankalin su gare ta, “Yaya kinga yarinyar da nake fad’a miki”, Taji wata na fad’a tana nuna ta, K’arasuwa suka yi kusa da ita,
” Mashaa Allah, Allah ya mata kyau daga gani kam buzuwa ce ko balarabiya, Ya sunan ki?”, Ta fad’a tana rik’o hannun ta, “Fetta”, ” Daga yau ki d’aukeni yayar ki kinji, kome kike so kizo wurina”, Tace “Toh”, Ta wuce ajin su,
Yan makarantar da suka sha ce mata haka suna da yawa, sai dai tace toh, bata k’ara waiwayar su, Allah bai yi ta mai shige shige ba.
Kawo Sule ya kira Hajiya Tumba a waya yace Ta turo Suraj yazo yaga Aysha, Ta amsa da toh dan a zauna lafiya, amma Aysha kamar wata bak’uwar ganin sa, Yarinyar da kullum tana gidan.
Suraj ya manta sam da zancen Aysha da suka yi da Hajiya, Harkokin sa yake, Yana kwance gadon d’akin sa yana hutawa, Mum ta kira shi, tana son ganin shi.
” Mama kina nufin naje wurin Aysha zance”, Ya fad’a cike da takaici,
“Ya zamu yi Suraj, da mun nuna wata hanya da zasu gane bama so matsala ce”, ” Meyasa kike tsoron su, ki barni dasu, zan fad’awa kawo Sulen ba aure a tsarina yanzu”, “A’ah hakan zai iya zama sanadiyyar lalacewar zumuncin mu dasu”, ” Ya lalace mana, dama ba na Allah da Annabi ba ne”, “Ba dan su ba, dan mahaifin ku”, Yayi shiru yana cije lips,
” Ka shirya anjima kaje”, Kansa kawai ya iya d’agawa, bak’in ciki ne ya mamaye zuciyar sa, Yaje zance wurin Aysha, yace mata me?, Taya zai fara tunkarar ta, bai tab’a cewa yana son wata ba, balle ya san ya ake,
Wayarsa ya d’auko k’irar IPhone 11pro, Yayi dialing Number abokin sa Munir, “SS(haka abokan sa ke kiran shi) yau Kaine ka kira ni”, Dariya yayi yace ” Taimakon ka nake nema”, “Dama nasan ruwa baya tsami k’asa banza”, ” Ni dai kazo gida ka sameni”, “Bani awa d’aya”, ” Ina jiran ka”, Yayi hanging up, tare da fusgar da iska.
Gidan Kawo Sule shirye-shiryen tarbon Suraj ake, Kai kace wani bak’o ne da basu tab’a gani ba zai zo, “Ungo je ki saka turaren wuta a falo, kizo kiyi wankan ruwan turare”, Cewar Aunty Yelwa(Matar Kawo Sule), “Umma ki ba Binta ta saka”, Dak’uwa ta mata tace ” Kinsan manufa ta na baki kije ki saka, ai nasan da bintar na baki “, Tana turo baki ta karba, ” Zan buge bakin wacce bata san ciwon kanta ba, na saka maganin mallaka da ya shak’i k’amshin shikenan auren ku anyi an gama”, Baki ta washe tace “Ina sonki Ummana”, ” Mara kunya, da kin tsaya shashanci, irin su Suraj ai sai mun kama su a hannu, dan mata basa rabuwa dasu kowacce burin ta ya aure ta”,
“Hakane Umma, dan ko Aunty Jummai naga tana so ta had’a shi da Bilkisu, ranar naji suna magana”, ” Ai nasan take taken su, zanyi maganin dukan su, yi sauri kije ki turara”, Ta fice, “Sai ya auri yaran naku mu gani”, Ta fad’a tare da yin kwafa.
Suraj har ya fara bacci, Zuwan Munir ya tashi, Ya fito falo ya same shi, Sukayi musabbaha, Ya zauna kujerar kusa dashi, Ya zayyane masa abunda ke faruwa, Ya jinjina kai yace ” Babbar magana, tun muna yara nasan irin zaman da kuke da Kawo Sule, auren yar’ sa ba abu mai yiwuwa bane”, “Ni bama wannan ba, taya zanje zancen wurin ta”, ” Baka da wani option da ya wuce haka, ko dan ka kare mahaifiyar ka daga zargi”, Tsaki yaja yace “Muje ka rakani”
“A haka zaka”, Jallabiya ce a jikin shi, Kai babu hula, But yayi kyau, Komai ya saka kyau yake mishi, Banza ya mishi yana yin gaba, A motar Munir suka tafi, Suna dosar gate na gidan yaji gaban sa na fad’uwa.
” Munir bana son mutanen nan, ba zan iya shiga ba mu juya”, Ya dafa kafad’ar shi yace “Kayi hak’uri, ka daure, ka duba kwanciyar hankalin Mahaifiyar ka”, A kan ta zai iya komai, Bud’e k’ofa yayi ya fita,
Aysha ce ta fito tasha ado mai d’aukar hankali, tana zuba k’amshi,
” Sannun ku da zuwa”, Ta fad’a tana far’a, Munir kad’ai ya amsa ta, Uban gayyar d’auke kai yayi, ya had’e rai, Iso ta musu zuwa falo, Yana shiga ya zauna yaji kansa ya sara, Yayi saurin dafe gefe, tare da karanta addu’o’i, A hankali yaji shi Normal.
Cike da yanga ta shigo ta ajiye tray na abinci gaban su, ta koma ta d’auko drinks da snacks, Ta duk’a zata fara serving d’in su, Ya dakatar da ita “Kada ki saka ba dad’ewa zamu yi ba”, Ta koma gefe ta zauna rai ba dad’i,
Ya mik’e da niyyar tafiya, Tace ” Har zaku wuce”, Munir ne ya amsata “Eh, ana jiran shi ne”, ” Bara na kira Umma ku gaisa”, Kamar ya hanata sai kuma ya fasa,
A tsaye ya gaishe ta, Munir ne kawai ya duk’a, Ranta ya b’aci da irin gaisuwar da ya mata, tana matsayin surukar sa, but ta nuna kamar ba komai ba, Bandir na dubu d’aya ya ajiye musu, Ta shiga zuba godiya,
Suka fito gidan yana jin kansa unusual, duk maganar da Munir ke yi bai amsa shi ba, har ya gaji yayi shiru, Yasan halin abokin nashi, not all the time yake son magana.
Hajiya Tumba ta kasa natsuwa ga gabanta dake fad’uwa, Tana tsoron kada yayi abunda zai janyo musu matsala.
Sallamar sa da taji, Ta amsa da murmushi, Tace “My Son ka dawo”, Ya d’aga mata kai, yana zama k’asan carpet na d’akin ta, Ya jingina da gado, ” Yaya had’uwar ka dasu?”, “Lafiya lau babu wata matsala”, ” Mashaa Allah, Allah ya shige mana gaba”, “Amin”
Ali ke ta kuka, Fetta tayi lallashin yak’i shiru, Ta rasa meke damun sa, Mallam baya nan, Hajar dama bata cika zama a gidan ba, Gidan kakannin ta a can take makaranta, weekend take zuwan musu, Aliya na gidan aiki.
A rud’e ta d’auko hijabin Aliya ta zura, ya mata yawa, har k’asa ya kai mata, Wuyan ma ya mata yawa, gashinta duk ya fito, Ta rufe gida, Ta nufi gidan Hajiya Tumba, Ali nata kuka.
Security sun gane ta, tana zuwa suka bud’e mata k’ofa, Kamar zata kifa saboda sauri, ba zata iya gudu dashi ba da tayi, Kaura taji tayi da abu, Tayi saurin ja baya,
Suraj ne tsaye a gabanta, Fuskarsa a d’inke, Cikinta ne ya d’uri ruwa, Ta k’ara saurin ja da baya, Idon sa na kan bak’in dogon gashin ta, Yana mamakin tsawo na gashin ta, a rayuwar sa yana son gashi, A zuciyar sa yana mamakin me tazo yi, Allah yasa iyayenta ba rok’o suka aiko ta ba, suce yaron nan mai kuka shine ba lafiya, idan hakane yau zai mammake ta, ya kora ta gida,
A tsawace yace “Ke me kika zo yi?”, Jiki na rawa tace ” Kuka yake zan kai shi wurin Maman shi, anan gidan take aiki”, Rab’awa yayi gefenta ya wuce, bai ce komai ba, “Kullum she is looking untidy”, Ya fad’a
Cikin gidan ta k’arasa a kitchen ta tarar da Aliya ta bata shi, Tana bashi nono, Ya karb’a yayi shiru, ” Ohh Ali dama yunwa kake ji, ka rud’ani”, Fetta ta fad’a, “Ai kin ganshi akwai rigima idan yaso”,
Tsawar da ya mata ke mata yawo a kai, Ta rasa me ta tarewa wannan bawan Allah, tun had’uwar su ta farko, yake nuna mata k’yamata da k’iyayya, Ko dan kasancewar ta Talaka, ” Da Addani nada rai, ni ko gani na ma ba zai yi balle ya mareni yamun tsawa”, Ta fad’a, hawaye na zarya kan kumatun ta,
“Subhanallah, Kuka Fetta, meya sameki?”, ” Cikina ke ciwo”, Tayi k’arya, “Sannu bari na tambayi masu aikin nan dake kwana idan akwai mai maganin ciwon ciki, ki daina kuka”, Ta d’aga kai, tana share hawaye.