FETTA CHAPTER 25
MURTALA MUHAMMAD INTERNATIONAL AIRPORT.+ Jirgin su yayi landing, Fetta yau ce rana ta farko da ta fara zuwa lagos, Tabi airport d’in da kallo, tsarin sa ya burgeta sosai, Driver Suraj already yana airport, ba b’ata lokaci suna shiga mota, yaja zuwa Victoria Island. Suraj ya kai dubansa ga Fetta yace “Zanje wani wuri, ki shiga ciki, idan kuna buk’atar wani abu ki kirani”, Ta amsa da “Toh”, Ta bud’e murfin motar ta fita, Kamal cikin girmamawa yace “Hajiya sannu da zuwa”, Da sakin fuska ta amsa da “Yawwa”, Yaja lugagge d’insu zuwa ciki, Gidan tsaf dashi, k’aramin falo ne mai d’auke da kujeru sai kayan kallo, D’akuna biyu ne d’aya na kallon d’aya, Na gefen dama ta bud’e ta shiga, Shima a gyare yake, Mimi ta shimfid’e kan gado, Ta cire hijab wanda Suraj ya tursasa mata sakawa, d’akin tabi da kallo tana tunanin ta ina zata fara binciken ta, “Ya Allah give me strength” Ta fad’a tana d’aura hannun ta kan k’irjinta dake buga mata, duk sanda zata tuna furucin Yasmeen, da kalar bugun da zuciyarta ke yi, “This is the right time na karanta littafin kafin ya dawo”, Zuciyarta ta fad’a mata, Akwatin ta jawo, ta d’auko littafin, Ta zauna k’asa tare da jingina cikin gado, Cike da fargaba ta bud’e shafin farko, Ganin rubutun da yaren buzaye, gabanta ya fad’i, Ta fara karantawa…. *GARIN AGADEZ* MASAURATAR AGADEZ Masauratar Agadez babbar masarauta ce a jamhuriyar Nijar musamman saboda yankin azbin, masaurata ce mai cike da d’umbin tarihi, yankin Agadez yafi kowane yanki girma a jihar Nijar, kuma garin ya kasance cibiyar ilimin addini a yankin sahara. Mai martaba Abutalib Shuwairan shine sarkin garin, ya gaji sarautar ne wurin Mahaifin sa bayan Allah ya mishi rasuwa, Sarkin da ya mallaki tarin dukiya wanda duk k’iyasin mutum bai isa ya k’iyasta yawan dukiyar da Allah ya bashi ba, Mutum ne mai halin dattako da k’ok’arin adalchi a tsakanin al’ummar sa, Mutanen garin na kiran sa da Amanukal ma’ana Sarki, Duk da kasancewar sa sarki bai tara iyali da yawa ba, Matan sa biyu Lele da Azagas, Lele itace uwargida mace masifaffiya wacce k’iris take jira tayi fad’a, kowa a masarautar tsoronta yake, ta d’auki karan tsana ta d’aurawa Amarya Azagas da yaranta, Lele yaranta hud’u, uku mata Safah, Laila, Aminita, namiji d’aya Ibrahim, Taso haihuwar namiji a farko saboda ya gaji sarki sai ya zama shine na k’arshe, Tana da yara biyu Sarki ya auro Azagas, ba irin tashin hankalin da Lele bata yi ba lokacin auren, Azagas macece mai sanyin hali, sam bata son hayaniya, magana ma wahala take mata, Hakan ya k’arasa Lele ta raina ta, kowane iskanci yi mata take, bata tanka ta. Duk gidan sarauta ba’a raba shi da hassada, gulma, bak’in ciki, makirci da sharri, hakan take a masauratar agadez, duk da k’ok’arin da Amanukal yake wurin ganin ya daidaita gidan sa. Azagas watan ta tara ta haifu d’anta namiji Elhidir, Farin cikin wurin Mai martaba ba’a magana ganin ya samu magaji, Azagas tasha alkhairai daga masoyan sarki, har ma da mak’iya masu neman gindin zama, masu bata zinari da dirham, da alkyabba na alfarma, kaya masu masifar tsada, haihuwar sa ba k’aramin d’aga hankalin Lele tayi ba, sanin shi zai zama magajin sarki, tun yanxu taga irin alkhairin da Azagas ke samu, A daren suna Lele ta aika a sace shi a kashe, Azagas na kwance d’akinta tare da Elhidir, taji tamkar ana buga k’ofa, masu mata hidima nauyayyen bacci suke, wanda Lele amintacciyar baiwarta tasa ta zuba musu maganin bacci a abinci, “Waye ke buga k’ofa?, ina su Allam su…”, Bata k’arasa ba taji ana fad’in “Gobara gobara”, Cike da tsananin tashin hankali ta d’auki Elhidir tayo waje, sai ji tayi an matse ta da bango, an fisge yaronta, ihun da tayi ya farkar da hadiman ta, “Yarona sun gudu dashi”, Ta fad’a cikin tsananin tashin hankali tana kuka, Kan ace me masauratar ta kicime, aka bazama neman yaron, Labari ya kai sashen Amanukal, yasa dogarai da fadawa su shiga neman sa, STORY CONTINUES BELOW Lele fatan ta Allah yasa bawan da ta aika ya gudu daga masarautar, kada a kama shi. Duk wata hanya da zata fitar da mutum daga masauratar an toshe, Hankalin Bawan ya tashi ganin bashi da wata mafita, wani lungu ya ajiye Elhidir, ya shiga waige waige sai da ya tabbatar babu mai ganin sa, ya fito ya shiga cikin mutanen dake nema, Wani dogaro ne ya hango Elhidir, gudun zargi ya kira sauran mutane ya nuna musu, aka d’auki Elhidir aka nufi wurin Sarki, Amanukal hamdala yayi wa ubangiji da yasa ba’a cutar masa da yaro ba, Ya kuma yiwa Dogarin kyauta babba, Azagas taci kuka har ta fita hayyacin ta, Shigowar Amanukal da yaron yasa ta saki sanyayyar ajiyar zuciya tana ma Allah godiya, ya mik’a mata shi, ta karb’e shi ta manna a k’irjin ta tana jin tsananin k’aunar sa, Mai martaba ya lallasheta tare da ban baki, yasan cikin mak’iyan sa ne ko nata suka saci yaron, Allah bai basu ikon salwantar dashi ba. Lele da baiwarta tazo mata da zancen, ba k’aramin bak’in ciki taji ba, sai faman zirga zirga take a d’akin tana tunanin wata hanya da zata salwantar dashi, in dai tana numfashi a doran k’asa ba zata tab’a bari ya zama magajin Amanukal ba. Tun daga ranar Mai martaba yasa tsaro sosai a b’angaren Azagas, duk iya dabarar Lele ta kasa samun hanyar salwantar da yaron. Amintacciyar baiwar ta ta had’a baki da ita, kan ta kawo mata boka, da nufin bata da lafiya, mai magani ne zai zo duba ta, Lele ta kwanta ciwon k’arya, Ta hana a sanar da Amanukal a cewar ta bata son hankalin sa ya tashi, Baiwar ta jagoranci boka zuwa sashen Lele, Ya buk’aci k’ebewa da ita, duka hadiman suka fita, “Yaron da aka haifawa Sarki nake so ya zama nakassashe, bashi da wani amfani, a saka ma Mai Martaba k’iyayyar sa”, Ta fad’a kai tsaye, “Baki da damuwa Sarauniyar agadez, uwargidan Abutalib, yar’ gaban goshin sa”, Tsubbace tsubbacen sa yayi, ya bata wani bak’in k’ulli yace ta jefa a tsohuwar rijiya, da anyi haka aiki ya gama, Alkhairi mai yawa ta mishi ya tafi. A daren ta aiwatar da yadda yace, Tun daga ranar Amanukal ya daina d’aukar Elhidir, tsakanin sa dashi ido, idan Azagas taje tunkarar sa kwana, daga baya ma cewa yayi ta daina zuwa dashi, abun ya dameta sosai, sanin ba yin kansa bane akwai wata k’ulalliya a k’asa ta fallawa Allah al’muran ta, Ganin haka hankalin Lele ya kwanta, tayi k’ok’arin sake samun ciki, ta haifi da’ namiji, Eldihir na wata bakwai, Azagas ta samu wani ciki, tayi mamakin saurin samun ciki, amma tayi godiya ga Allah da ya bata, bata sanar da kowa ba hatta Mai martaba, gudun yan hassada, tana ta rainon cikinta da dan’ ta. Kwanci tashi babu wuya a wurin Allah, Ranar wata asabar da safe Lele ta haihu ya’ mace, tayi bak’in ciki ba kad’an ba, babu wanda yaga far’arta ranar, Da daddare sai shela suka ji Azagas ta haifi da’ namiji, Tashin hankalin da Lele ta shiga yafi na haihuwar Elhidir, Kusan hauka tayi, duk wani abu dake kusa ta ita sai da ta fasa shi. Amanukal da kansa ya taso har sashen Azagas, yama yaron hud’uba, Yayi farin ciki da samun sa, ya rasa dalilin da yasa baya jin Elhidir a ransa kamar da, amma wannan yana jin sa har k’asan zuciyar sa. Rana d’aya akayi suna yarinyar Lele taci suna Aminita, Yaron Lele Gabdullahi, Wutar k’iyayyar Azagas ta k’ara rurawa a zuciyar Lele. Bayan wasu shekaru Abubuwa da dama sun faru, Lele ta k’ara haihuwar namiji wanda yaci suna Ibrahim, daga shi ta tsaida haihuwa dama da’ namiji take so, Azagas ta k’ara haifar yara uku, mata biyu Tagaishat da Hudijatu, namiji d’aya Ummaru, Elhidir shekarun sa ashirin ya tashi yaro ba lafiyayye ba, K’afarsa d’aya a shanye, kuma baya magana amma yana ji, babu wanda ya kawo sihiri ne, a zaton kowa haka halittar sa take, Gabdullahi ya tashi yaro mai tsananin kyau, yafi kowa kyau a gidan, duk da suma sauran ba daga baya ba, ga hazak’a da hankali, ya shiga ran sarki sosai, ko da yaushe suna tare, Shi ya tsukalewa Lele da yaranta ido, wanda suka tashi da k’iyayyar Azagas da yaranta, Uwar su ta d’arsa musu hakan a zuciyata, Yaran Azagas sun tashi da kyawawan tarbiya da son yan uwan su, suna zaune da zuciya d’aya da kowa, Ibrahim yafi nuna k’iyayyar sa ga Gabdullahi ganin shak’uwar sa da Mai martaba, da kuma yadda kowa ke yabon sa, ana kiran sa Yarima, Sau da yawa yasha neman fad’ansa duk da ya girmesa, ya k’yalesa tamkar mai gane nufin sa ba. Elhidir ya fito b’angaren Azagas, Ibrahim ya hango sa, da sauri yazo ya bige sandar sa, ya fad’i, A idon Gabdullahi, a fusace yayo kan Ibrahim, “Ashe baka da hankali, ba yayanka bane, banda rashin imani taya zaka bige sa”, Wani banzan kallo ya watsa mishi yana dariya yace “Kazo ne ka tare ma nakasasshen dan’uw…,”, Bai k’arasa ba ya d’auke sa da Mari, Dambe ya kacame tsakanin su, Gabdullahi ba k’aramin duka yayi ma Ibrahim ba, Da k’yar aka raba su, kowane aka kai shi sashen Mahaifiyar sa, Azagas fad’a sosai tama Gabdullahi, ta gargad’eshi da kada ya sake, ko ya had’u da fushin ta. Lele ashariya take ta faman dannawa “Na rantse da Allah sai tsinanan yaron can yasan ya tab’a mun da’, wallahi sai masarautar nan ta gagare shi zama”, Ta juya kan Ibrahim da sai huci yake tace “Kai kuma banda kana sakarai ka zauna yana jibgar ka”, Huci yake bai ce komai ba, Hannu tasa a baki ta tauna, ta jijjiga kai. _Wannan shafin sadaukarwa ne ga duk wani masoyin littafin Fetta, masu comments both wattpad da whatsapp kuna matuk’ar bani k’arfin gwiwar typing One luv❤️ wanda suka fi kowa comments In Shaa Allah a k’arshen littafin nan an lissafu sunayen ku_+ Tun daga ranar k’iyayyar Gabdullahi ta k’ara habbak’a a zuciyar Lele da Ibrahim, kullum burin su suga bayan shi, Cikin ikon Allah duk wani makircin su baya kama shi kullum gaba yake. Shekaru sun k’ara ja, Girma da hankali ya k’ara bayyanar wa Gabdullahi, Elhidir babu wani cigaba a ciwon sa, babu wanda ke bi ta kansa a masauratar sai Mahaifiyar sa, da yan’ uwansa da suke d’aki d’aya, ya sha jin yadda ake tsarguwar sa a masauratar, wasu na mishi dariya, babu shi babu sarautar agadez, Ibrahim har so yake hanya ta had’a su ya yab’a mishi magana, “Magajin Sarki mara amfani, kana ji kana gani sarautar agadez zata gagare ka sai HANGEN NESA (LITTAFIN UMMI ZEE KU NEMA KU KARANTA)”, Hakan yake yawan ce mishi ya bushe da dariya, Ba k’aramin ciwo abun ke ma Elhidir ba, amma babu yadda zai yi. Gabdullahi ne zaune a lambun masarautar, gefen sa kofi ne na ataye yana sha, wanda Allah ya d’aura masa son shayin, Amintaccen bawan sa ya gurfana gabansa, “Allah yaja da ran mai jiran kujera, Amanukal na neman ka”, Ya masa alama da kai, Duk da kasancewar Gabdullahi mai sauk’in kai, amma jinin sarauta dole wataran a tab’a kas’aita, Shayin ya k’arasa shanyewa ya nufi b’angaren mai martaba, A can ya tarar da Ibrahim, Cike da ladabi ya gaishe da Amanukal, ya amsa, Yayi gyaran murya yace “Abunda yasa na kira ku, ina so kowanne ya fitar da mata, na baku sati biyu, Umarni ne ba shawara ba, Babu wanda ya isa ya musa akan maganar sa, Cike da girmamawa suka amsa da “Toh”, Ya buk’aci su tafi, Gabdullahi zancen ya masa dad’i dama yana soyayya da yarinyar abokin Amanukal, Yar’ garin Niamey ce, Mahaifinta hamshak’in mai kud’i ne shine mai ba Shugaban k’asar Nijar shawara, dashi ake damawa cikin gwamnatin Nijar. Ibrahim dama yana soyayya da yarinyar waziri, Safah, Lailah da Aminita tuni suka dad’e da aure. Bayan wata d’aya Aka yi bikinsu Gabdullahi, anyi shagali wanda ba’a tab’a yi ba a masauratar, an narki dukiya, duk wanda yazo bikin zai shaida Abutalib Shuwarain ya mallaki arzik’i mai d’umbin yawa, Gabdullahi ya tare da matar sa Zainaba a cikin masarutar amma b’angare daban, wanda sai kayi tafiya mai nisa, haka shima Ibrahim ya tare da matar sa Allam, zaman lafiya dukansu suke, Lele bata fasa makirci ba da shirya tuggu. Zainaba cikin sati na biyu da auren su ta samu juna biyu, Farin ciki wurin Gabdullahi ba’a magana, Azagas da Amanukal ma ba k’aramin farin ciki suka yi zasu samu jika, Ganin haka Lele ta fara takurawa Allam da maganar ciki. Soyayya da shak’uwa ce mai tsanani tsakanin Gabdullahi da Zainaba, yana bata kulawa sosai, Haka tana samun kulawa daga wurin Azagas dasu Tagaishat, da cikin ta ya shiga watan haihuwa, Amanukal da kansa ya umarci ta koma sashen Azagas a can zata fi samun kula, Gabdullahi bai so haka ba, Ranar wata asabar ta haifu yar’ta mace mai tsananin kyau, Kan ace me masarautar ta d’auka, ko’ina shela ake kasancewarta jika ta farko ga Mai Martaba Sarkin Agadez, Kowa fad’in kyawunta yake, ba’a tab’a haihuwar mai kyanta ba a masarautar, A ranar Amanukal ya dinga kyauta, sa biyar da raguna goma aka yanka aka yi sadaka, Jaririyar tazo da sa’a da nasarori ga rayuwar iyayenta, Can Niamey ma iyayen Zainaba ba k’aramin farin ciki suka yi ba, itace jikar su ta farko, A ranar sukayi mota uku zuwa masarautar Agadez, STORY CONTINUES BELOW Masarautar ta cika mak’il kace bikin aure ake, Lele ganin haka hankalinta ya matuk’ar tashi, wuni ranar a d’aki tayi, Gashi har yanzu Allam ko b’atan wata bata tab’a yi ba. Sati ya zagayo yarinya taci suna Fatima Fetta, anyi shagali ba d’an k’arami ba, ranar raguna da shanaye sun sha yanka, Amanukal yaba jaririya kyautar rakuma ashirin da sark’a da yan kunni na zinari, Mahaifin Zainaba shima ya bata kyautar zobe da abun hannu na zinari, Fetta tazo da alkhairai da yawa, Iyayenta suma sun samu alkhairi da yawa, Elhidir duk da baya magana, kallo d’aya zaka masa ka hango tsananin farin ciki a tare dashi, Ya rungume Fetta tsam a jikin sa, yana jin k’aunarta, Tun daga ranar da aka haifeta Allah yasa mishi k’aunarta, Tagaishat da Hudijatu ma wani irin k’auna suke mata, Fetta tayi farin jini sosai a masarautar, Lele ko a ido bata tab’a saka ta ba, wanda ganin ta zai iya sa zuciyarta tayi bindiga tsabar bak’in ciki, Yaranta sunyi k’ok’arin zuwa ta hanyar b’oye bak’in cikin su. Fetta na wata uku a duniya, Allah yayi wa Sarki Abutalib rasuwa, wanda mutuwar sa ta matuk’ar gigita al’aummar adagez, dama sauran garuruwan Nijar, Fad’in tashin hankalin da iyalinsa suka shiga ba zai misaltu ba, Azagas suma tayi, da k’yar aka samu kanta, Gabdullahi yaci kuka har ya fita hayyacin sa, Yaran Amanukal sunji rashi ba kad’an ba, Uba ne nagari. Bayan komai ya natsa, an raba gado, Iyalan Abutalib ba k’aramin dukiya suka samu ba, su kansu sunyi mamakin ganin irin abunda ya mallaka, K’anin Amanukal, Sule yazo da takardar wasiyyar da ya bari, kan a nad’a Gabdullahi matsayin Sarki, Lele ta kasa b’oye bak’in cikinta, kallo d’aya zaka mata, ka hango zallar hassada, Ibrahim zuciyar sa kamar zatayi bindiga, Azagas tayi farin ciki, yayin da wani b’angare na zuciyarta ke cike da tsoro da fargaba, sanin had’arin dake tunkaro rayuwar sa, amma akwai Allah, Gabdullahi ya tsinci kansa da fad’uwar gaba, wani b’angare na zuciyar sa na k’arfafa masa gwiwa, shi ya cancanci mulkin garin, Elhidir murmushin farin ciki kawai yake. Lele na komawa b’angaren ta, ta kira baiwarta ta aike ta wurin boka, taje ta gaya masa tana so ama Gabdullahi kurciya shi da matar sa, su bar k’asar Nijar gaba d’aya, kada su k’ara dawowa, Baiwar ba b’ata lokaci ta tafi, Boka ya shiga aikin sa. Gabdullahi na zaune tare da Zainaba wacce ke goye da Fetta, ya mik’e yace “Ina so mu bar k’asar nan”, Zainaba tace “Nima hakan nake ji”, “D’auko mayafin ki”, Ta saka k’aton mayafi, ta lullub’e fuska, Shima yayi shigar b’at da kama, ya rik’o hannun ta, suka fice daga sashen nasu, kasancewar dare ne, da shigar su, babu wanda ya gane su har suka fice daga masarautar, Suka nufi tasha, mota suka shiga ta zuwa nigeria garin Kano, Mun tsinci kanmu a garin kano, wanda ba zamu ce ga dalilin da yasa muka bar k’asar mu ba, sai dai har k’asan zuciyata bana jin son komawa Nijar gaba d’aya, Haka ma Zainaba, Ranar da muka zo garin Kano, na had’u da Alhaji Adamu bakin tasha ya d’aukeni matsayin mai gadi, ba tare da tunanin matsayina da dukiyata ba, na amince na zamo mai gadin sa, wanda anan muka fara rayuwa da Zainaba, muna rainon yar’ mu Fetta. Fetta kuka take mai tsuma zuciya ta jik’a littafin da hawaye, Kuka ne na farin ciki da tausayin iyayen ta, Wani nauyi take ji k’irjinta ya rage, ciwon da ta dad’e dashi shekaru taji yana barin zuciyarta, ciwon rashin sanin asalin ta, yau tasan asalin ta, yau tasan wacece ita, yau ta tabbatar ta fito cikin ahali mai tsarki, ita ba matsiyaciya bace mara asali yar’ mai gadi kamar yadda lokuta da dama ake kiran ta, ashe tana da gata, saboda mulki farin cikin iyayenta ya ruguje suka rasa komai, tasha jin labarin gidan sarauta, bata san itama hakan ce ta kasance da ita ba, daga irin gidan ta fito, “Alhamdulillah Allah nagode maka da nasan ASALINA(Littafin Zee Yabour)”, “A ina ya samu littafin?” Ta tambayi kanta, Ta dan’ yin jim tana tunani, “Kayana da Addani, da Yasmeen tace ta kai gidan marayu, tabbas acan ya samu littafin”,1 Jin shigowar sa tayi saurin tura littafin k’ark’ashin gado tana share hawaye, tare da tattaro natsuwar ta, ba zata sanar da kowa asalin ta ba hatta Yasmeen, sai ta gano waye Suraj, tayi clearing doubt a kan sa, komai ya daidaita ta sadu da dangin ta. Sallamar sa ya katse mata tunani, ta amsa da sakin fuska, Kallo d’aya ya mata yaga alamar tayi kuka, Zama yayi gefen gado, ya mata alama da hannu ta taso ta zauna kusa dashi, “Any problem?”, Ya tambayeta yana kafeta da ido, “Ina tuna Mahaifina ne”, Ta fad’a tana tsare sa da ido ko zata hango wani abu suspicious a tare dashi, “Ki rik’a masa addu’a ba kuka ba”, Ganin ya fad’a hankali kwance, ba wata alama da ta nuna maganar ta tab’a shi, sai tsantsar tausayin ta data hango a k’wayar idon sa, ya sata sauke ajiyar zuciya, ta d’aga mishi kai, “Muje falo muci abinci”, Ya fad’a yana mik’ewa, tabi bayan sa, tana buk’atar abincin, Agogon dake manne a bangon falon ta kalla, hud’u saura minti biyar, tayi mamakin yadda lokaci yaja, Ko sallar azahar bata yi ba, “Zan duba Mimi naji kamar kukan ta”, Ta fad’a tana nufar d’akin, Mimi na kwance abun ta, tana shan hannu, mamakin rashin rigima irin na Mimi take, Cikin mintuna 20 tayi sallar azahar da laasar wanda k’asaru ne, A falo ta same sa, ya zuba abinci ya fara ci, “Zo muci”, Ya fad’a yana d’aukar wani spoon yasa cikin jollof rice d’in, Bata wani ci da yawa ba, tace “Ta k’oshi”, Bai tursasa mata ci ba. A ranar bata samu ta gudanar da wani bincike ba, farin cikin gane asalinta ya danne komai, yau ta samu bacci, wanda take jin kaso d’ari na cikin damuwar ta, saba’in ya tafi. Hasken ranar da ya dallo d’akin, ya tashi Fetta wacce tayi bacci mai cike da mafarkan dangin ta, wayarta ta danna ta duba lokaci 7:30, Salati tayi ta sanar da ubangiji, mamakin irin baccin da tayi take, baccin da bata yi bane na kwana biyu ta rama.1 Ta kalli Suraj dake baccin sa a natse, “Shima kenan bai tashi ba”, Ta mik’e ta shiga toilet, ta gabatar da Sallah, Bargon da ya lullub’e ta janye, tana kawar da kanta gefe, bata son ya zuba mata mayatattun idon sa, kallonsa na jefata a wani yanayi mai wuyar fassarawa, Idon sa ya bud’e a kanta, yaga tana kallon gefe, Tari yayi wanda yasa tayi saurin juyowa, idon sa cikin nata, ya mata murmushi tare da kashe mata ido d’aya, Zuciyarta taji ta wani harba, tana jin zirr har zuwa tafin k’afan ta, Juyawa tayi ta fice d’akin ba tare da tace masa komai ba, Dariya yayi ya sauko daga kan gadon, ya shiga toilet, Da fuskar yaji yana so ya fara tozali, hakan ya saka shi yin tarin k’arya. Zuciyarta cike da tunanin shi, da mamakin yanayin da take ji a kansa, ta nufi kitchen, dube dube tayi ba komai na girki a ciki, Dole ta koma falo ta zauna, bata kunna kallo ba, ta fad’a duniyar tunani, Tana son daidaita rayuwarta komai ya wuce, she want to live a happy life, tun tasowarta take facing challenges na rayuwa iri iri, duk da cewa kowane dan’ adam da irin k’addarar sa, she is hoping tayi bankwana da bak’in ciki, fatan ta zargin da take akan Suraj kar ya zama gaskiya. Ya fito cikin shirin sa na k’ananun kaya, sun mishi kyau sosai, komai ya saka kyau yake mishi, falon ya game da k’amshin turaren sa. Bata d’aga kai ta kalle shi ba, har ya nufi k’ofar fita, Jin rufewar k’ofa ta d’aga kai ta kalli k’ofar, tana jin takaici na rashin bi ta kanta, bai da breakfast d’inta ba sanin sa ba komai da zata iya ci a gidan, ya fita ba sanarwa, Bud’ewar k’ofar ya katse mata tunani, ta kai duban ta, Suraj ne rik’e da leda mai tambarin restaurant, Sauke ajiyar zuciya tayi tana jin haushin kanta, na saurin judging d’in sa, Kitchen ya shiga ya d’auko plate, ya juye chips da miyar k’odar a ciki, ya ajiye ruwan rubber gefe, Hannun ta taji ya kamo, yana mata alama ta sauko suci abinci, ta zauna ba tare da ta tace komai ba, “Yau bazan samu gaisuwa ba”, Ya fad’a yana jefanta da kallon sa dake kashe mata duk wata gab’a na jikin ta, Sam ta manta ta gaishe sa, Murya k’asan mak’oshi tace “Ina kwana?”, “Ba zan amsa ba tunda sai da na rok’a”, Ya d’auki spoon ya fara cin chips, Ta tsinci kanta da cewa “Kayi hak’uri shafa’a nayi”, “Zan hak’ura amma da sharad’i d’aya, sai kinyi feeding d’ina, baki tab’a ba kullum nike yi”, “Ya Allah mutum kamar mai juji”, Ta fad’a a ranta, Gira ya d’aga mata alamar ya dai, Spoon ta d’auka ta fara feeding d’in sa, ba zata iya da rikicin sa ba, Shima ya shiga bata, Har suka cinye, ya d’auki tissue ya goge bakin sa, ya mik’a mata itama ta goge, “Zan fita, anjima Kamal zai kawo muku abincin rana”, Ya fad’a yana mik’ewa, “Allah ya bada sa’a”, “Amin”, Ya amsa yan ficewa. D’aki ta koma, ta shiga dube dube, duka drawers har k’ark’ashin gado sai da ta duba, bata ga anything suspicious ba, Zama tayi kan gado tare da dafe kai ta furta “Ya Allah ka shige mun gaba, Ya Allah ka nuna mun waye Suraj Sa’id”, Wayarta tayi k’ara, Yasmeen ce mai kiran, Tayi receiving, Bayan sun gaisa, Tace “Ya binciken da kike?”, Cike da karaya tace “Na kasa samun komai a tare dashi, ko a fuska banga wata alama ba”, Yasmeen ta nisa tace “Kada ki karaya Fetta, kibi komai a hankali, In Shaa Allah komai zai warware and keep praying”, “In Shaa Allah”, “Allah ya shige miki gaba”, Ta amsa da “Amin”, Tayi hanging up, Hankalinta ba zai tab’a kwanciya ba sai tasan waye Suraj. “Umma kinji Ya Suraj ya tafi da matsiyaciyar matar shi lagos”, Cewar Bilkisu cike da b’acin rai, “Meye na b’acin rai, wallahi k’iris ya rage tsakanin su, ki daina damun kan ki” Aunty Jummai ta fad’a tana murmushin da ita kad’ai tasan ma’anar shi, Bilkisu tace “Ina fatan hakan”, Aunty Jummai tace “Zaki sha mamaki a wannan karon”, Tayi dariya tana jin hankalinta ya kwanta da furucin mahaifiyar ta. Masu neman auren Feena sunzo, manyan mutane cikin shiga ta kamala, Su Kawo Sule ne suka masu bayar da auren, sun buk’aci a saka bikin nan da sati biyu, basa son wani shagalin biki sai d’aurin aure, sun nuna mahaifin yaron rik’akk’en dan’ izala ne, Sun amince da hakan, bayan sun tuntubi Hajiya, suna tare da Feena, ta nuna itama bata so, burinta ta auri Fahad. Mahaifin Tasleem ya zage yana ta shirye shiryen bikin yar’ sa, Tana kwance d’aki tana chatting, Ya sameta, Ta mik’e zaune tana fad’in “Daddy”, Ya zauna gefen gado yace “My daughter ana hutawa”, Tayi murmushi, “Wane shiri kuke ke da angon na shagulgulan bikin da za’a yi”, “Daddy nifah bai tab’a kirana ba, dama ina so na fad’a maka”, A tsawace yace “What! Bai tab’a kiran ki ba, wane irin sakaran yaro ne, an gaya masa a banza zan bashi ya’ta” Wayar sa ya jawo ya danna kiran Kawu Lamid’o, “Ranka ya dad’e ina wuni?”, Bai amsa gaisawar ba ya rufe sa da masifa, “Me dan’ yake nufi da baya kiran ya’ta ko baya son auren ne”, “Kayi hak’uri Ranka ya dad’e, yana tsoron kiran ne, yasan da farko bai samu karb’uwa ba”, “Ka gaya masa ya gyara, ya’ta ba’a banza take ba, ko wallahi a fasa auren”, “A’ah ba’a yi haka ba, ayi hak’uri”, Ya kashe wayar, Ya kai duban sa ga tilon yar’ sa yace “Kwantar da hankalin ki babu wanda ya isa ya d’auke ki for granted”, A zuciyarta tace “Sai Suraj Sa’id”, A zahiri murmushi tayi. Kawu Lamid’o Alhaji Tambari na kashe waya, ya kira Bello ya dinga zuba masa ruwan bala’i da masifa, “Ni kake so ka kunyata, toh wallahi baka isa ba, gobe gobe ka tattaro kayan ka ka dawo garin nan”, Yana fad’ar haka ya kashe waya, tunda ya fara masifa bai bari Bello yace komai ba, Zufa ke tsattsafo masa yana jin tamkar ya had’iye zuciya ya mutu tsabar bak’in ciki. 2:30am na dare Suraj tun fitar sa da safe bai dawo ba, sai yanzu, Fetta wacce tayi nisa a bacci, motsin sa ya tashe ta, ganin yana shiri wanda da alama daga wanka ya fito, Tayi lamo kamar mai bacci, Jallabiya kad’ai taga yasa, bai fesa turare ba, Wayar sa tayi k’ara, ya d’auka, “Gani nan zuwa, make sure ko shirya komai”, “Me zasu shirya a wannan tsohon daren?, ina za shi?”, Ta jefowa kanta tambayoyin da bata da amsar su, Tana jin fitar sa, ta sauko gado a hankali tabi bayan sa, d’akin dake kallon wanda suke taga ya bud’e ya shiga, Ta koma bayan k’ofa ta lab’e tana jiran fitowar sa, Shigar da ya fito da ita, tasa k’irjinta dokawa da k’arfin gaske, har kanta na sarawa, bak’aken kaya ne a jikin sa, riga da wando, kansa sanye da hula p-cap, hannun sa rik’e da facemask, Ya jawo d’akin ya rufe, tare da ajiye mukullin k’ark’ashin k’ofa, babu wanda zai lura dashi, Hular ya k’ara ja ta kare masa fuska, kafin ya wuce, Fetta jikinta taji na kyarma, tunanin ta ya tsaya cak, k’wak’walwarta ta kasa tunanin komai, zuciyarta ke mummunan bugawa tamkar zata fasa k’irjinta ta fito, Da k’yar bakinta ya iya furta “Ya Allah”, cike da k’arfafa ma kanta gwiwa, ta mik’e ta nufi d’akin da ya fito, mukullin da ya ajiye ta d’auka, tasa a jikin k’ofar, Ta bud’e key d’in, Ta d’aura hannun ta kan handle d’in, taji tamkar an rik’eta ta kasa murd’awa, jikinta ke rawa, tana jin wani tsananin tsoro da fargaba na ratsa zuciya da jikin ta.