FETTA CHAPTER 27
Cikin Mintuna kad’an ya iso gidan, ba k’aramin gudu yayi ba, tuk’i yake kamar zai tashi sama, daga yanayin shigowar sa da parking d’in sa ya tabbatar wa ma’aikatan gidan ba lafiya ba, kowane ya shiga zancen zuci,+ Part d’in sa ya nufa kai tsaye cike da fatan Allah yasa yaga Fetta, ya mayar da auren sa, bai san me ya shiga kansa ya rubuta sakin ba, “Zuciya da b’acin rai”, Zuciyar sa ta bashi amsa, Tsaki yayi yana k’arasawa ciki, Ganin bata falo ya shiga d’aki bata nan, ya lek’a toilet da kitchen babu alamar ta, Sashen Hajiya ya nufa cike da fargaba, nan ne lost hope d’in sa, babu natsuwa ya shigo falon ba tare da yayi sallama ba, Cirko cirko ya tarar dasu, Aliya da Mallam suma sun zo, hankalin su ya kasa kwanciya a gida, suka nufo nan ko zasu ji wani labari da zai kwantar musu da hankali, Kowa ka kalla fuska d’auke da damuwa, Mallam na ta faman jan charbi, Hajiya ta fara ganin sa, “Suraj kai ne, ina kuka shiga tun jiya, kun jefamu a damuwa, Ina Fetta?” Ta fad’a tana mik’ewa tare da yin hamdala ga ubangiji, Aliya, Mallam da Yasmeen a tare suka kai dubansu ga Suraj, suna jere hamdala, Tambayar k’arshe da Hajiya ta masa yasa yawun bakin sa tsinkewa, bai san wacce amsa zai bata ba, sabon tashin hankali yaji ya lullub’e sa, “Ina Fetta ko tana b’angaren ku?”, Hajiya ta jefo masa tambayar da ta k’ara dagula lissafin sa, Ganin sa yanayin sa, ya tabbatar ma kowa ba lafiya ba, Aliya a rud’e tace “Wani abu ya sameta? Dan Allah ka sanar damu ina Fetta take?”, Yau duk wata kunyar sa ta fice, lafiyar Fetta kad’ai take son ji, Suraj ya kasa furta komai, sai zufa da ta shiga karyo masa, sanin Fetta bata da kowa sai su Aliya, idan suma basu san ina take ba, toh ina ta nufa, Hajiya ta k’araso gabansa tana rik’o hannun sa tace “Ka sanar damu ina Fetta? Me ya sameta?”, Bashi da wani option da ya wuce ya sanar dasu gaskiya, besides ita ta buk’aci saki a wurin sa, “idan ka fad’a kana da hujjar kare kanka, na dalilin da yasa ta nemi sakin?” zuciyar sa ta fad’a, wani b’angare na zuciyar sa yace “Hanya d’aya ce ka b’oye abunda ya faru tsakanin ku”, “Kayi ma girman Allah ka sanar damu ina Fetta take ko hankalin mu zai kwanta” Mallam ya fad’a cike da damuwa, “Nima bansan inda take ba, ban sani ba” Ya fad’a yana jin yadda zuciyar sa ke bugawa, Hankalin kowa ya matuk’ar tashi da jin furucin sa, Aliya a wurin ta fad’i tana fashewa da matsanancin kuka, Malam jikinsa gaba d’aya yayi sanyi yana ambaton sunan Allah, Yasmeen zuciyar ta na tabbatar mata akwai wani abu a k’asa da Suraj ya b’oye, “Tabbas ta gano yana d’aya daga cikin yan fashin dasu kashe su Daddy” Cewar zuciyar ta, “But meyasa ta tafi ba tare da ta neme ni ba?” Ta jefawa kanta tambayar da bata da amsa, “Ka fad’a mana abunda ka sani game da b’acewar Fetta, me ka mata?, Fetta ba zata tafi haka kawai ba tare da wani dalili ba”, Hajiya ta fad’a cikin d’aga murya, Suraj wanda zuciyar sa ke tafasa, yana jin tamkar ya d’aura hannu a kai yayi ta tsunduma ihu ko zai samu sassaucin abunda yake ji, da k’yar iya furta “Ban sani ba Mama, ban sani ba”, Ya nufi hanyar fita, dishi dishi yake gani har ya kawo bakin motar sa, Ya bud’e ya shiga, yaja motar yana ficewa daga gidan, gefen titi yayi parking, ya d’aura kansa kan sitiyari, bai san ina zai nufa ba, bai san a ina zai ga Fetta da gudan jinin sa ba, “Ya Allah” ya furta yana dafe zuciyar sa dake barazanar tarwatse wa. Matashin saurayi wanda ba zai wuce shekaru goma sha takwas ba, ta hango ya fito daga wani b’angare na masarautar, yasha nad’i irin na buzaye, kallo d’aya zaka mishi kasan ya had’a jini da masarautar, ga kamanin sa da Addani, Ya nufo wurin da take, “Sannu” Ta fad’a da yaren buzaye, “Yawwa” ya amsa yana bin ta da kallo, ganin tayi kama dasu, gashi tana yaren buzaye, tun tasowar sa, bai tab’a ganin ta a masarautar ba, Tunanin sa ta katse da fad’in “Dan Allah ina ne b’angaren Azagas?”, B’angaren da ya fito taga ya nuna mata, “Nagode” ta fad’a tana nufar b’angaren, yabi bayanta da kallo yana mamaki. Girman b’angaren yasa ta rasa wacce hanya zata sadata da Azagas, Wata baiwa ta tambaya, ganin kamanin ta yasa babu musu ta mata jagora har turakar Azagas, Falo ne na alfarma, wanda an narka dukiya a ciki, yasha ado da tsarin gidan sarauta, sanyin Ac ta ko’ina yana bugawa, ga k’amshi mai dad’i na tashi, “Aljannar duniya” Fetta ta furta a ranta, tana zama d’aya daga cikin lumtsattsan kujerun dake falon, “Kin zo a sa’a, yanzu ne lokacin fitowar ta, ki jira a anan”, Cewar Baiwar, Ta gyad’a kai tana mata godiya, Minti biyar da zaman ta, Dattijuwar mace ta fito, wacce kallo d’aya zaka mata kasan hutu ya zauna mata, zaka rantse bata yi shekaru sittin a duniya ba, saboda yadda fatar ta ke shek’i, Kayan alfarma ne a jikin ta wanda sai hamshak’an masu kud’i a cikin sarakuna ke sawa, sam bata lura da Fetta ba wacce tun fitowar ta, ta zuba mata ido tana jin k’aunar ta da farin ciki na ratsa ta na tozali da kakar ta, mahaifiyar Addani, Manyan manyan tuntun na alfarma da aka zagaye wani b’angare na falon dasu, anan Azagas ta zauna, tana kishingid’a, d’ago kanta da zata yi suka had’a ido da Fetta, Gabanta ya fad’i tayi saurin tashi zaune, Kafin tayi magana, Fetta ta fad’a jikinta tana fashewa da kuka mai tsuma zuciya wanda na farin ciki ne, Azagas tsintar kanta tayi da rungume Fetta, tana d’aura hannun ta kan Mimi dake goye a bayan ta, Sai da ta tsagaita da kukan, Azagas tace “Ko baki fad’a ba nasan Fetta ce yarinyar Gabdullahi”, Kanta ta shiga d’agawa tana hawaye, ina ma tare suka zo asalinta da Addani, da farin cikin yafi haka, ba zata tab’a gafartawa Suraj ba da ya zama silar kashe mahaifin ta, wani sabon kuka ya taho mata, “Kiyi shiru Fetta, ba kuka zaki yi ba, Ina Gabdullahi da Zainaba”, Cikin sark’ewar murya tace “Sun rasu” Azagas gabanta yayi mummunan fad’uwa ta shiga jere “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un”, Hawaye na wanke fuskar ta, A kullum da burin sake saka Gabdullahi take a idonta, kullum addu’arta Allah ya dawo dashi gare ta, “Ashe ba zan sake ganin Gabdullahi ba, rabuwar k’arshe muka yi ba” Ta fad’a tana fashewa da kuka. Tun fitar Suraj falon, babu wanda ya samu k’arfin gwiwar sake cewa komai, Malam ganin kukan Aliya ba mai k’arewa ba ne, Yace “Ya isa kukan Aliya, tashi mu tafi”, Ta mik’e tana zubar hawaye, ba tare da sun cewa Hajiya komai ba, suka fice, Yasmeen itama ta mik’e tabi bayan su, Hajiya tagumi tayi ta rasa yadda zata b’ullowa al’amarin, zuciyar ta na tabbatar mata akwai abunda Suraj ke b’oyewa. Kusan minti ashirin kansa na kan sitiyarin ba tare da ya d’ago ba, “Meyasa zaka damu da tafiyar ta bayan ita ta buk’aci sakin, bata son ka, bata son zama da kai” Wani huci yaji zuciyar sa na yi, “I will let her be tunda ita ta buk’aci hakan, bata son jin komai daga gare ni, zan k’yaleta, Mimi jini na ce dole watarana zata dawo gare ni”, Ya fad’a yana k’arfafa ma kansa gwiwa tare da k’ok’arin yakice tunanin Fetta, yaja kan motar sa zuwa guest house, yana son kad’aicewa, baya son duk wani abu da zai kawo masa tunanin ta. Azagas tayi k’ok’arin tsayar da kukan ta, ta shiga lallashin Fetta, k’aunar Azagas taji na ratsa ta wanda ya haddasa tsayuwar kukan nata, Azagas ta kalleta tayi murmushi, itama ta mayar mata, Hannu ta mik’a mata alamar ta bata Mimi, Ta d’auketa tana jin k’aunar yarinyar, “Ina baban ta, ba tare kuka zo ba?”, Fetta murmushin yak’e tayi tace “Ya rasu”, “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un Allah ya jik’an sa, kin ga jarabawa mutuwar uwa, uba, miji Sannu” Ta fad’a tana kamu hannun ta, “Ki bani labarin ki da kika sani bayan tafiyar su Gabdullahi”, Ta sauke nauyayyen ajiyar zuciya ta shiga bata labari, rabuwar su da Suraj ta canza kanun labari cewar accident yayi ya rasu, a lokacin taga littafin Addani, ta gane asalin ta, ta yanke hukuncin zuwa gare su, Azagas har da hawayen ta na tausayin Fetta jin ta taso cikin rayuwar maraici da rashin gata, Yaron ta Gabdullahi dan’ sarauta a matsayin mai gadi, tsanar wanda suka kashe mata shi taji a ranta, ina ma zata gansu, tasa a yanke musu hukunci daidai da abunda suka aikata, “In Shaa Allahu daga yau kinyi bankwana da maraici, zaki samu gatan da baki tab’a mafarkin samu ba, kin shigo shiga dangin ki Fetta inda zaki samu k’auna mara nn misaltuwa, tabon da kika dad’e dashi a zuciya na rashin asalin ki, a yau zai goge, ina miki alk’awari da d’umbin kulawa da gata” Fetta sanyi da farin ciki taji na ratsa ta, tana fatan hakan, tana fatan bankwana da dukkan bak’in ciki, ta manta rayuwarta ta baya, tana son fara sabuwar rayuwa. _Kusa kanwar Mamana a addu’a plss🤲🏻 Allah ya mata rasuwa_ Sautin k’ararrawar da Azagas ta danna, ya fargar da ita tunanin da take, Masu mata hadima ne suka shigo su hud’u, suna gurfanawa gabanta tare da kai mata gaisuwa, Fetta ta kalla tace “Taso muje”, Ta mik’e tabi bayan ta, hadiman na take musu baya, har sashen Amanukal na yanzu, Fetta sakin baki tayi tana kallon had’uwa da tsaruwar shi, an narka dukiya ba kad’an ba, sai taga na Azagas ba komai ba ne, Kai tsaye suka shiga ciki ba tare da neman iso ba,+ Ganin Azagas hadiman sa suka fice, Mai martaba da yasha ado cikin kayan sarakunan buzaye, yasha nad’i wanda baka ganin fuskar sa sai idon su, Ya gaishe da Azagas, ta amsa, Fetta ta zuba masa idanu tana so tasan waye ya zama sarki bayan tafiyar mahaifin ta, Ibrahim yazo mata a rai, but ganin yadda ya gaishe da Azagas cike da girmamawa yasa zuciyar ta shakku, ko ya canza daga halayyar sa na shekarun baya, “Fetta ce yarinyar dan’ uwan ka Gabdullahi”, Cewar Azagas, “Tun shigowar ku naji a jikina Fetta ce, tsawon shekaru ba zai sa na kasa gane ta ba, k’aunar da nake mata mai girma ce”, Azagas ta jinjin kai, ta juya kan Fetta tace “Elhidir ne yayan Mahaifin ki”, Idanu ta zaro tana mamaki sanin bashi da lafiya, yaushe ya warke har ya zama sarki, Azagas ta katse mata tunani “Kina mamaki ko?”, Ta gyad’a kanta, Azagas ta numfasa tace “Bayan tafiyar Gabdullahi mun shiga tashin hankali ba kad’an ba, na dad’e kwance ina ciwo, mutanen gari ma sun girgiza da jin b’acewar sa, wanda da yawa suna zargin k’urciya aka masa, hakan yasa aka jinkirta da nad’in sarauta zuwa wata biyu ko Allah zai sa ya bayyana, Lele ta kasa hak’uri ta shiga ruwan bala’i kan a nad’a Ibrahim ba za’a jira dawowar sa ba, Kowa yace sam bara ayi haka ba, ganin an rinjayeta ta shiga cewa ni na had’a makirci, ciwon da nake na k’arya ne, ina bak’in cikin nad’a d’an ta Sarki, ban bi ta kanta ba, ciwon dake damuna da rashin Gabdullahi yafi komai ci mun zuciya, Ganin ciwon nawa kullum gaba yake, Sule k’anin marigayi ya d’auka mun malami, A lokacin Elhidir na tare dani, kallo d’aya ya masa yace an masa sihiri shiyasa yake haka, Sule ba tare da wani ja ba, ya yarda kuma ya bashi damar ya karya sihirin, Nan take ya shiga aikin, kullum ana masa ruqiya da basu magunguna masu d’auke da ayoyin Allah, Cikin ikon Allah sati d’aya Elhidir ya warke ya dawo cikakken mutum, farin cikin hakan yasa na warke, kowa a masarautar yayi mamaki da al’ajabin warkewar sa, Lele ta shiga tashin hankali mara misaltuwa, Aka yanke shawarar nad’a sa Sarkin Agadez, dama shine magaji, Ranar da aka nad’a yayi kukan farin ciki da mamakin hikima ta ubangiji, babu wanda ya tab’a zata Elhidir zai gaji sarautar Agadez, Lele kusan haukacewa tayi, Ibrahim har da kwanciya ciwo, ko a mafarki basu tab’a zato ba, Zakaran da Allah ya nufa da cara….. Sati biyu da nad’in sa, Ya auri yarinyar Sule mai suna Kabidat, yaran su hud’u tare yanzu, biyu maza Abutalib wanda yaci sunan marigayi, Gabdullahi sunan mahaifin ki, biyu mata Safa da Sana, Fetta mamaki da al’ajabi had’e da farin ciki yasa ta kasa furta komai sai jinjina kai take, Da hannu ya mata alama ta taso tazo kusa dashi, Rungumeta yayi yace “Maraba da dawowa ahalin ki, nayi matuk’ar farin cikin sake ganin ki”, Fetta k’aunar sa taji na ratsa ta tana jin sa tamkar Addani d’in ta, Ya sake ta yana fad’in “Ina dan’uwana da matar sa?”, “Sun rasu” Cewar Azagas, “Innalillahi wa inna ilahir raji’un” Ya shiga maimaitawa yana jin hawaye masu d’umi na wanke fuskar sa, wanda tunda ya hau sarauta bai tab’a zubar dasu ba, Labarin da Fetta ta bata, ta sanar dashi, Yaji tausayin ta ya kama shi sosai, Ya kuma d’auki alwashi bata kula da gata wanda bata tab’a mafarkin samu ba. STORY CONTINUES BELOW Suraj duk k’ok’arin sa na yakice tunanin Fetta ya kasa, idan ya runtse idon sa ita yake gani, idan ya bud’e tunanin ta yake, sai faman juyi yake kan gado, yaja tsaki a karo na ba adadi, “Damn it” Ya fad’a yana dukan goshin sa da tafin hannun sa, “Why? Why? Meyasa zan rik’a tunanin ta?”, Wayar sa ta shiga k’ara, yana ganin kiran Hajiya ya kasa d’agawa, bai san me zai ce mata ba, baya son ta k’ara masa damuwa, Kira uku ta masa bai d’auka ba, Ta turo masa text message, kamar ba zai duba ba, wata zuciyar ta buk’aci ya duba, “Ka gaggauta dawowa gida kafin ka had’u da mummunan b’acin rai na” Karon farko a rayuwar sa da Hajiya ta masa furuci irin haka, Yasan tabbas ya b’ata mata rai matuk’a, Hankalin sa yaji ya tashi, baya son fushin ta ko kad’an, Jiki a sanyaye ya mik’e, ya d’auki mukullin motar sa, ya fita yana jin komai na duniyar baya masa dad’i, bai tab’a tunani riskar kansa a rana irin ta yau ba. “Ni fah hankalina sam bai kwanta da Suraj ba, jikina na bani yana da masaniya, Fetta ba zata tab’a tafiya ta bar mu ba, duba da shekarun da muka d’auka tare da ita, bata tab’a yunk’urin tafiya wani wuri ba”, Cewar Aliya tana sharar k’walla, Malam ya nisa yace “Nima ina zargin hakan, amma addu’a zamu dage da ita”, Aliya ta jinjina kai, tana jin tamkar taje ta shak’ure Suraj sai ya fad’a mata inda Fetta take, da tana da k’arfin iko wallahi ba zata bar sa ba sai ya fad’i gaskiya, amma talaka irin ta ba zata iya karawa dashi ba. “Suraj” Hajiya ta kira sunan sa, Suraj dake durk’ushe gabanta ya amsa da “Na’am”, “Ka fad’a mun gaskiya Ina Fetta take?”, “Ban sani ba Mama”, “Wallahi tallahi kaji na rantse ko na gane kana da sa hannu a b’acewar ta sai ranka yayi mummunan b’aci”, Ya razana da jin furucin ta, but ba zai iya sanar da ita komai ba, ba zai jure ganin halin da zata shiga ba, “Tashi ka tafi”, Ya mik’e kansa na juya masa, Da k’yar ya kai b’angaren sa, K’amshin turaren ta da ya kama gidan ya ziyarci hancin sa, a rud’e ya k’arasa cikin d’akin, zuciyar sa na tabbatar masa ta dawo, dama yasan zata dawo gare sa, bata da wurin zuwa, bata da kowa dole zata dawo, Ganin bata d’aki ya shiga kiran sunan ta, shiru ba’a amsa ba, Jikin sa ya matuk’ar sanyi, Ya zauna gefen gado yana dafe kansa, k’amshin turaren ta na ziyartar k’ofofin hancin sa, yasa hannu yana toshewa. An sanar da kowa na masarautar dawowar Fetta, da rasuwar Gabdullahi da matar sa, Da yawa sun ji rasuwar, Lele bata damu da dawowar Fetta ba, haka bata buk’aci ganin ta, yanzu tayi sanyi sosai, bata da wani power a masarautar babu bai bi ta kanta, duk da Elhidir na k’ok’arin kyautata mata, Tauraruwar Azagas ke haskawa, kullum bak’in ciki kamar ya kashe ta, Ibrahim bashi da aiki sai shaye shaye da bin mata, da yawa bayin masarautar shi ke lalata su, matar sa ta gaji da halin sa tayi yaji. Fetta taga gata da tarairaiya, abinci kala kala irin na buzaye aka dababaiye ta dashi, taci har ta ture, Tamtsamemen d’aki mai d’auke da kayan alatu aka ware mata, da bayi masu mata hidima, Kallon d’akin take tana godiya ga Allah, ko a mafarki bata tab’a d’auka haka dangin ta ke da arzik’i ba, Baiwa d’aya ta shiga ta had’a mata ruwan wanka, Ta gurfana gabanta da fad’in “Ranki ya dad’e na had’a ruwan wanka”, Fetta tayi murmushi tare da gyad’a mata kai, Minti ashirin ta kammala wanka, ta shirya cikin kaya irin na buzaye, kaya ne na sarauta da alfarma, sun matuk’ar yi mata kyau, ta sanya sark’a da yan kunni na zinari, k’aramin kit Azagas ta bata mai cike da sark’ok’in zinari, da kaya masu yawa na alfarma da tsada, Fetta mamaki ya hana ta furta komai, Ganin bata zo da kaya ko kala d’aya ba, Ta tambayeta dalili, tace babu wanda yasan da tafiyar nata, idan suka sani zasu hana ta, Azagas tayi dariya ba tace komai ba, Mimi na wurin Sanah yarinyar Mai martaba. Kwanciya tayi kan tantsamemen gadon, tana kallon bangon d’akin, Tunanin waye Suraj ya fad’o mata, Da sauri ta mik’e ta nufi hanyar fita daga d’akin, bata son tuna duk wani abu da ya dangancen shi. D’akin Azagas ta nufa wanda sashe d’aya ne da d’akin ta, Elhidir yaso ta zauna b’angaren sa, Azagas tak’i yarda, tana son Fetta a kusa da ita, STORY CONTINUES BELOW Zaune ta tarar da ita tare da saurayin da ya mata kwatance, Azagas da murmushi d’auke a fuskar ta tace “Kinyi kyau sosai, kin fito sak buzuwar Nijar”, Dariya tayi tana zama kusa da ita, “Itace Fetta” Cewar Saurayin, Azagas ta gyad’a masa kai, “Abu talib ne yaron Elhidir”, Fetta ta jinjina kai, “Barka da dawowa” Ya fad’a yana murmushi, Ta amsa da “Yawwa”, Hira suka shiga yi mai cike da nishad’i. Su’ad cikin bacci taji tamkar ana gurnani, bud’ewar idon da zata yi, taga Adnan haihuwar uwar sa, yana video call sai gurnani yake yana fad’in “Am eager gobe tayi mu had’u ki mun abunda kike mun yanzu a waya”, Jikinta na kyarma ta kunna ta kai hannun ta kan switch ta kunna, Maimakon taga tashin hankali a fuskar sa, wani banzan kallo ya watsa mata yace “Dalla kashe fitila”, Da kallo tabi sa tace “Ni zaka ci amana Adnan, kaji tsoron Allah”, “Baby ina zuwa” Ya fad’a yana kashe wayar, Dariya ya bushe da ita yace “Tsoron Allah kike fad’i, ke ina tsoron Allah ne, kin manta yadda kike kware mun jikin ki nayi yadda nake so, yanzu baki isa ki hana ni kula babe d’ita ba”, Ya sake kiran budurwar sa, yana cigaba da video call suna zuba fitsara, Su’ad kuka ta shiga yi jikinta na kyarma, ba zata iya jure gani ba, ta tashi ta koma d’ayan d’akin ta, tana kuka kamar ranta zai fita, tare da nadamar sakin mishi jikin ta. Feena b’acewar Fetta sam bata dameta ba, harkokin gabanta take, da zumud’in auren ta. Suraj duk inda ya saka hancin sa k’amshin turaren ta yake ji, Yaja bargo ya lullub’e k’amshin ta yake, Tsaki yaja ya mik’e ya fito d’akin, Ya nufi wanda kayan Mimi ke ciki, Kewar yarinyar yaji ta lullub’e sa, Hoton ta na ranar suna dake cikin dan’ k’aramin frame ya d’auka, yana kallo “I miss you My angel, i miss you so much” Ya fad’a zuciya a raunane, Maimakon ya tsaya a tunanin yar’ sa, ya fad’a na Fetta, duban sa ya kai kan hoton ta tana d’auke da Mimi, ba k’aramin kyau tayi ba, ya kasa d’auke idon sa daga kallon ta, Hannun sa ya kai zai d’auki hoton, yayi saurin tsayar da hannun yana tambayar kan sa “Are you ok?”, Sha biyu na dare ta dawo d’akin ta rungume da Mimi wacce tayi bacci, ta shimfid’e ta, ta kwanta tare da jan bargo ta lullub’e su, Cikin ikon Allah bacci ya d’auke ta ba tare da wani tunani ba. Suraj a daren bai runtsa ba, damuwa da tunani sun hana zuciyar sa sakat, Alla alla yake safiya ta waye, ya nufi gidan gonar sa, yayi engaging kansa abubuwan da zasu d’auke masa tunani. Aliya da Malam kwana suka yi k’ilamul laili, suna addu’ar Allah ya tsare Fetta a duk inda take, ya kuma bayyana musu ita. Yasmeen sai faman juyi take kan gado, da tunani birjik a ranta, ga tarin tambayoyi a zuciyarta da Fetta kad’ai zata bata amsar su, tana fatan ta nema ta kamar yadda ta fad’a. Ta b’angaren Hajiya da k’yar bacci b’arawo ya sace ta. Kiran sallar asuba daga masallacin masarautar ya tashi Fetta, ta mik’e da sunan Allah a baki, ta gabatar da sallah, ta dade zaune tana karatun Qur’ani da addu’o’i kafin ta mik’e ta koma kan gado, Ta so komawa bacci, tunanin su Aliya yazo mata, tasan babu shakka suna can cikin damuwa na rashin sanin halin da take ciki, ya zama dole ta kira su ko hankalin su zai kwanta, duk yadda zuciyarta taso mata tunanin Suraj tak’i bari. 10:00am na safe Tayi wanka ta shirya tsaf, k’amshi mai masifar dad’i na fita a jikin ta, Hadiman ta sun so yi ma Mimi wanka ta hana, Kallon kanta take a madubi tana ganin yadda ta fito sak buzuwa jinin sarauta, sanyi taji ya ratsa zuciyar ta, “Allah ya jik’an ku iyayena”, Sanah dake shigowa ta amsa da “Amin”, Murmushi ta mata, itama ta mayar mata, “Nazo d’aukar ya’ta”, Ta fad’a tana d’aukar Mimi, Fetta tayi dariya, Baiwar ta wacce aka amincewa shigowa d’akin, Tayi sallama ta shigo ta sanar da ita Agazas na nemanta, Mayafin ta ta yafa kan gashin kanta da yasha gyara, ta fito. A falo ta sameta, da duk’a har k’asa ta gaishe ta, ta amsa da sakin fuska, “Karin kumallo zamu yi”, Abinci ne kala kala birjiki, shayin ataye tasha, shi kad’ai take jin zata iya saka mata cikin ta, Azagas ta kalle ta da murmushi tace “Kinyi gadon shan ataye, Gabdullahi na son shi sosai”, “A can nigeria yana mana, a wurin shi na koyi shi”, Ta jinjina kai da murmushi, Bayan sun kammala ta buk’aci aron wayar ta, Ta mik’a mata tace “Anjima zata aika a siyo mata tata wayar”, Zata yi godiya, ta hana ta. D’akin ta ta koma, ta saka number Aliya da ta haddace a kai, Aliya tana shan ruwan shayi wanda sha take ba dan tana jin dad’in shi ba, wayarta ta soma k’ara, ganin wata kalar number tak’i d’auka, sai kira na biyu ta kanga a kunne cike da fargaba, “Assalamu Alaikum”, Jin muryar Fetta, ta zabura tace “Fetta kece, ina kika shiga?”, “Umma ku kwantar da hankalin ku ina nan lafiya”, “Toh Alhamdulillah, me yasa kika tafi?, ina kika je?”, Tana saukar ajiyar zuciya tace “Zan sanar daku komai amma ba yanzu ba, na kira ne dan ku kwantar da hankalin ku, ki gaishe da Mallam dasu Hajar”, Bata jira amsar ta ba, ta dak’ile kiran, tare da saka number a reject list, “Hello Hello Fetta”, Jin shiru, tabi bayar da kallo jiki a sanyaye, “Alhamdulillah tunda tana lafiya”, Ta nufi d’aki tana sanar da Malam, hamdala ya shiga yi ma ubangiji. “Kuyi hak’uri Umma bazan iya sanar daku komai ba, ina son daidaita rayuwata da na ya’ta”, Ta fad’a, hawayen dake shirin zubo mata tayi saurin tare su _Zainab Lawal, Ayshafareeda, Sa’adatu M Ya’u, Maryam M Ya’u, Shoter, Sophy, Murjanatu Sabi’u, Sarah, Reimxe ina jin dadin comment dinku😍😍_+ Ba wanda take buk’atar magana dashi a yanzu sai Yasmeen, numberta ta saka, tayi dialing, Yasmeen dake kwance wayarta ta soma ruri, ganin number nijar, Tace “Wa ke kirana da number nijar”, Sam tunanin ta bai kawo mata Fetta bace, Ta d’auka tana kangawa a kunne, “Assalamu Alaikum” Jin muryar Fetta tayi saurin tashi zaune da fad’in “Fetta ina kika shiga? Me ya kai ki nijar kika jefamu a damuwa”, Ta sauke ajiyar tace “Wurin dangina na tafi”, “Dangin ki?”, “Eh zan sanar dake komai amma sai kin mun alk’awari ba zaki fad’awa kowa ba har su Umma”, “Na miki alk’awari babu wanda zai ji”, Ta numfasa ta sanar da ita ba tare da ta b’oye mata komai ba, Yasmeen ta girgiza da ji at the same time ta taya Fetta murnar gane dangin ta, “Na taya ki farin cikin gane dangin ki, but meyasa kika tafi tsaya mun d’auki hukunci haka ba?, Me yasa kika tafi ba tare da cikar burin ki ba, bayan a ko da yaushe fatan ki a gano wanda suka kashe Addani ki mik’a su kotun addinin musulunci” “Da wane baki kike so na furtawa Hajiya yaro mafi soyuwa a gare ta dan’ fashi ne?, Da wane ido kike so na kalle ta idan na mik’a yaron ta kotu bayan halaccin ta gareni, ba tare da ta duba matsayina ba da rashin asalina ta had’a ni aure da gudan jinin ta, Taya kike so na fallasa sirrin mutumin da ya zama uban ya’ta, ko nak’i ko naso Suraj shine mahaifin Mimi, bana so a goran ta mata watarana, rabuwa dashi ita kad’ai ce mafita gare ni”, Ta k’arasa da fashewa da kuka, Magangunta sun tsuma zuciyar Yasmeen, samun kamar Fetta a wannan zamani yana da matuk’ar wahala, despite shine silar kashe mahaifin ta har ta samu sauran rangwame a zuciyar ta, “Kina ganin barin sa haka ya cigaba da ta’asa a doran k’asa taimakon sa kika yi?”, “Komai nisan jifa k’asa zai dawo, a juri zuwa rafi watarana tulu zai fashe, yadda na gano dan’ fashi ne haka watarana asirin sa zai tonu, idan kuma Allah yayi nufin sa da shiriya sai ya shiryu, Ina rok’on ki da Allah Yasmeen kada ki zama silar rugujewar farin cikin Hajiya”, “In Shaa Allah Fetta babu wanda zai ji, Suraj na bar sa da Allah tado case d’in a yanzu zai zama babban rikici”, “Nagode da kika fahimce ni”, Suka yi sallama ta kashe wayar, Hawaye masu zafi suka cigaba da ambaliya kan kumatun ta, Magana da Yasmeen ya taso mata tabon da take k’ok’arin binnewa, “Why Suraj? Meyasa ka zab’i wannan mummunar d’abi’a ta zama hanyar ka ta ci da sutura?, Meyasa ka zama d’aya daga cikin masu kisan kai?”, Turnik’in zafi zuciyarta ke yi, tana bugawa da tsananin k’arfi, ta dafe ta tana ambaton sunan Allah, Mik’ewa tayi kanta na tsananin sara mata, ta shiga toilet, ta d’aura alwala, ta fara gabatar da nafilfil tana rok’on Allah ya mantar da ita komai, ya saka mata natsuwa da kwanciyar hankali a zuciyar ta. Suraj yadda yaga dare haka yaga rana, bacci ko da wasa bai d’auke sa ba, Tunda sassafe ya nufi gidan gonar sa, da hannu ya amsa gaisuwar ma’aikatan sa, Files ya dauko yana dubawa yana lissafi ko zai d’auke masa hankali, but sam damuwa ta kasa barin sa, Knocking k’ofar da ake ya tabbatar masa Rabi’u ne, ya umarce sa ya shigo, Cike da ladabi ya gaishe sa, Ya amsa, File ya ajiye a gabansa yace “Na samu dukkan bayanai akan Alhaji Barau, yau zamu iya zuwa gidan sa”, “Ok ka shirya komai k’arfe uku na dare za…..”, Kasa k’arasawa yayi sakamakon kalaman Fetta take masa yawo a kai “Taya kake tsammanin na cigaba da zama dan’ fashi, wanda cin sa, tufafin sa, muhallin sa duka daga haramun ne, har nima ya ciyar dani ta wannan hanyar…kana tsammanin zan bari ya’ta ta taso cikin k’azamar haramtacciyar rayuwar ka, har abada ba zan bari tasan waye mahaifin ta ba, dan bara ta tab’a alfahari da kai ba……” STORY CONTINUES BELOW Tsintar kansa yayi da cewa “Operation cancel”, Da kallon rashin fahimta Rabi’u yabi sa yace “Amma ranka ya dad’e Alhaji Barau fah, gidan sa da muka dad’e muna hari”, “Nace an fasa ko, get out”, Ya fad’a cikin d’aga murya, Rabi’u tuni ya fice, “Haramun nake ci, shin rayuwata k’azama ce? Ya’ta ba zata yi alfahari dani ba?” Ya jefowa kansa tambayoyin zuciyar sa na bugawa da tsananin k’arfi, File da Rabi’u ya ajiye masa, ya cilar gefe, ya buga teburin dake gaban sa, ya dafe kansa dake masifar sara masa, Bilkisu ta fad’o d’akin Aunty jummai babu sallama har tana tuntub’e, “Lafiyar ki dai?”, “Fetta ta bar gidan Suraj ba’a san inda take ba”, Zabura Aunty Jummai tayi tace “Da gaske?”, “Wallahi Allah yanzu nake ji wurin mai aikin gidan”, Wani juyi tayi tace “Aikin boka yaci, dama yace zasu rabu”, “Gaskiya Umma na yarda da aikin sa”, “Bana fad’a miki ba ai aikin sa tamkar yankan wuk’a”, Suka rungume juna cike da tsantsar farin ciki, Bilkisu har ta hango ta gidan Suraj. Shigowar Safah yasa ta tsaya da karatun Qur’anin da take, “Tanti (Haka suke kiran Azagas, yana nufin Aunty haka suka taso suka ji yan masarautar na kiran ta) tace wai kizo”, Tace “Toh”, Tana mik’ewa da nad’e sallayar, ta ajiye, tabi bayan Safah, Sashen Amanukal taga sun nufa, A falon sa da iyalin sa kad’ai ke shiga, suka tarar da Amanukal, Matar sa Kabidat da Azagas, Ta gaishe su cikin girmamawa, Suka amsa da sakin fuska, Elhidir na mata kallo mai cike da k’auna haka yake jin ta tamkar yar’ sa ta cikin sa, Kusa dashi ya mata alama ta zauna, Azagas ta numfasa tace “Mahaifin ki Gabdullahi ya bar dukiya mai d’umbin yawa, gadon sa da Marigayi ya bar masa, bai tab’a ba ko kad’an, ya kuma mallaki kadarori da yawa, haka Mahaifiyar ki tabar zinari mai d’umbin yawa ciki har da wanda Mahaifinta ya baki ranar da aka haife ki, Rakuman ki da Mai martaba ya baki suna nan, a k’aida idan mamaci ya rasu ana raba masa gado, duk wani makusancin Gabdullahi dake da hakk’in na gadon sa ya yafe, Haka dangin mahaifiyar ki sunce sun yafe gadon ta, Dan haka zamu tattara duka mu mik’a miki”, Fetta mamakin al’amarin ubangiji take yadda ya azurta ta lokaci d’aya, lallai al’amarin ubangiji bashi da shamaki, wannan d’umbin dukiya ta kai ta ina, Ta numfasa tace “Ku cigaba da ajiyewa a hannun ku, har lokacin da zan buk’ata, yanzu bana buk’atar komai, hidimar da kuke mun ta wadatar”, Sosai suka yaba da hankalin ta, Elhidir yace “Kina da hankali Fetta, Allah ya miki albarka”, Suka amsa da “Amin” Azagas tace “Dangin Mahaifiyar ki sun buk’aci ganin ki, tun jiya suka so zuwa su tafi dake, amma nace su bari gobe daga nan zaki tafi, Sanah zata raka ki”, Fetta tayi nodding kai cike da farin cikin zata sadu da dangin Mahaifiyar ta. “Gaba d’aya kaina ya d’aure tunanin ina Fetta taje ya hana ni sakat, gashi number da ta kirani ko na kira bata shiga”, Cewar Aliya, Malam dake kishingid’e gefen ta yace “Ni kaina nayi iya tunani na kasa hasashen ina ta tafi, da kuma dalilin tafiyar, amma kwanciyar hankalin shine sanin tana lafiya”, “Shi kad’ai nake tunawa naji natsuwa wallahi”, “Nima hakan, kin sanar da Hajiya kuwa”, “A’ah”, “Ya kamata ki sanar da ita ko hankalinta ya kwanta”, “Zan kira ta a waya na sanar da ita”, “Yawwa” Wunin ranar Suraj yayi sa a gidan gonar sa bai tsinana komai ba, sai tunanin Fetta da kalaman ta, Salloli duka a office d’in yayi, bai fita yayi jam’i da ma’aikatan sa kamar yadda ya saba ba. Hajiya tunda Aliya ta kira ta sanar da ita wayar da suka yi da Fetta, take jimamin ina ta tafi, da kuma dalilin tafiyar, but hankalin ta ya kwanta na jin tana lafiya, Shigowar Feena ya katse mata tunani, “Mama dama Fahad yace wai bayan la’asar yake so a kaini”, Da kallo mai cike da takaici da mamaki tabi ta “Ke wai meyasa baki da kunya, baki da hankali, tun tafiyar Fetta ko da wasa baki mun maganar ba, balle ki nuna damuwar ki, tsabar rashin kunya kin zo kina sanar dani lokacin da za’a kai ki, da asuba za’a kai ki ba la’asar ba, wuce ki bani wuri”, Ta fita tana tunzura baki, a k’ofa tayi kaura da Suraj, tayi saurin ja da baya cike da tsoro, Ganin ko ta kanta bai bi ya wuce ciki, ta saki baki da mamaki, “Tabbas rashin Fetta ya tab’a Ya Suraj, da yanzu ya sharara mun mari ai”, Ta fad’a tana wucewa. “Ina wuni?” Ya gaishe da Hajiya yana duk’awa har k’asa, “Lafiya lau” Ta amsa ba yabo ba fallasa, “Ga abinci can na ajiye maka”, Ta fad’a har lokacin fuskar ta ba sake ba, Ya amsa da “Toh” Yana mik’ewa ya fita, tabi bayansa da kallo tana ayyana abubuwa da dama a ran ta. Sai faman juya cokali yake, ya kasa kai ko da loma d’aya bakin sa, Jin motsin fitowar Hajiya, yayi saurin kai loma d’aya bakin sa, abincin yaji kwata kwata babu dad’i, girkin Fetta ya masa illa sosai wacce baya jin dad’in abincin kowa idan ba nata ba, tun tafiyar ta bai saka abinci a cikin sa ba, sai ruwa da yoghurt yake faman sha, Hajiya ta shiga kitchen ba tare da tabi ta kansa ba, Haka ya gama cakalkala abincin ya ajiye. “Tumuqqartin(Yana nufin Yayata) baki gama shiryawa ba” Cewar Safah, Turaren da take fesawa ta ajiye ta juyo tana cewa “Na gama mu tafi”, Safah sakin baki tayi tana kallon ta tace “Kin matuk’ar yi kyau wallahi, kamar a sace ki a gudu”, Dariya tayi har fararan hak’oran ta na fitowa, Manyan motoci jeep prado guda biyu, da bayi da yan sanda, Amanukal yasa a kai su Fetta Niamey, Murfin mota ma bud’e mata aka yi ta shiga, Baya suka zauna tare da Sanah tana rungume da Mimi, Tafiya suke cikin natsuwa, ga sanyin Ac da sautin wak’ar Nijar na tashi a motar, tana bin hanya da k’auyuka da kallo, tsarin k’asar Nijar ya mata. Tafiyar awanni ta kawo su garin Niamey, tasha bacci a motar, babban gari ne mai tsarin birni, Tana bin garin da kallo har suka kawo gidan su Mahaifiyar ta, Makeken gida ne tun daga wajen sa zai tabbatar maka gida ne na masu hannu da shuni, wanda suka murzu da naira, “Ban da k’addara yaushe mahaifiyar ta zata yi rayuwa a gidan Alhaji Adamu matsayin matar mai gadi”, Securities na ganin motocin da number masarautar Agadez, suka wangale gate, Fetta sakin baki tayi tana kallon girman gidan, tafkeken gida ne wanda titi ne shimfid’e a cikin sa. Mamaki bai k’ara cika ta ba, sai da suka shiga ciki, a iya tsawon rayuwar ta bata tab’a ganin gida mai kyau, had’uwa da tsaruwar sa ba, ginin zamani mai tsarin turawa, Dattijuwar mace wacce ba zata iya sa’ar Azagas ba ta fito, da yan mata biyu a bayan ta, Kallo d’aya zaka musu daga yanayin shigar su da fatar su zai tabbatar maka suna cikin daula, Da gudu suka k’araso suka rungume Fetta, “Ku bita a hankali mana sai kun k’arya ta” Cewar Dattijuwar, Dariya suka yi suna fad’in “Kai Mummy” Duk da kasancewar su buzaye, sun d’auki wasu d’abi’u na turawa, suna yawan tafiye tafiye k’asashe, Ta k’araso tana rungume Fetta jikin ta tace “Barka da zuwa”, K’aunar mata taji a ranta da murmushi tace “Yawwa”, Mimi dake hannun Sanah, yan matan ke rigimar karb’a, “Wai ku bakwa girma ne, kullum cikin rigima, Ke Amra ki barwa yayar ki ta d’auka”, Amra ta b’ata rai ta matsa gefe, Fetta tana bin su da kallo tana jin k’aunar su, ko ba’a fad’a k’annen Mahaifiyar ta ne, kamannin su da Mummy sak, A ranar Fetta taga gata wurin damgin mahaifiyar ta, Kowa tarairayar ta yake, Daddy (yadda suke kiran Mahaifin maman ta) tamkar zai mayar da ita ciki, Abubuwan ciye ciye har sai da ture, Mimi kuwa wannan ya d’auka wannan ya d’auka. “Ashe abunda ya faru kenan, uhmm wallahi da naji sai da kaina ya sara” Cewar Aunty Jummai ta marairaice fuska, zaka rantse da Allah har cikin ranta damuwar, Hajiya tace “Abun ai ba dad’i ba”, “Baku sa cigiya ba”, “Addu’a ita muke cigiyar bata da wani amfani, ban da ayi ta yad’awa” Hakanan taji bata son sanar da ita Fetta tana lafiya, “Hakane kuma Allah yasa tana hannu nagari”, Hajiya ta amsa da “Amin”, Aunty Jummai a zuciyarta addu’a take Allah yasa kar ta tab’a dawowa. Satin su d’aya garin Niamey, satin tayi shi ne cikin jin dad’i da kulawa, ta zagaya gidajen dangin mahaifiyar ta, tarba sosai take samu daga gare su, a kwanakin shak’uwa ta shiga tsakanin ta dasu, Wani lokaci har mamakin k’aunar su gareta take, ina ma shekarun baya tare dasu tayi, da ko shakka babu ba ruwanta da damuwa balle tashin hankali, ko zata yi b’acin rai k’alilan ne, dukkan dan’ adam ba’a raba sa da b’acin rai watarana.