FETTA CHAPTER 9

FETTA






CHAPTER 9






Zaune take a falo, bayan wasu mintuna tana duba agogo, Ana sallar isha’i ya fita, gashi sha d’aya da rabi bai dawo ba, ba rashin dawowar sa ya dame ta ba, baccin da ya dami idon ta, kar ya dawo yana knocking tayi bacci. +

Duk k’ok’arin ta kar tayi bacci sai da yaci k’arfin ta.

12:15am na dare

Ya shigo gida, ransa a matuk’ar b’ace, kallo d’aya zaka masa kasan a gajiye yake, Masu gadi ma sai da ya balbale su basu bud’e gate da wuri ba, Hak’uri suka shiga bashi,

Knocking k’ofar yake, Fetta sam bata ji ba, tayi nisa a duniyar bacci, Wani duka ya kaiwa k’ofar kamar zata b’alle da ta katako ce ba abunda zai hana ta b’allewa, A firgice ta mik’e, lek’awa tayi ta jikin k’ofa, Shi ta hango ya had’e rai kamar hadarin gabas,

Ta bud’e, Tamkar zai bi ta kanta ya shigo falon, Kallo d’aya ya mata, yaga alamar daga bacci ta tashi, “Kasa”, Ya fad’a yana jan tsaki, ” Bacci ma lafiya ne”, Har ya wuce, Ya dawo,

Gab da ita ya tsaya k’irjinta ya shiga bugawa bata d’auka yaji ba, Kanshi ya had’a da nata ya gwara da k’arfi, Tayi baya ta fad’a kan kujera cike da azaba, komai na falon double take ganin sa, “Suraj ba sa’an wasan yarinya ba ne, wallahi kika k’ara mun rashin kunya sai na bambamce miki tsakuwa da aya”, Ya wuce ciki yana huci.

Hannu tasa ta dafe goshinta dake zugin azaba ” Allah ya isa na mugu”, Ta fad’a tana hawaye,

    “Tukur you must pay for this, Wallahi bashi ka d’auka, babu wanda ya isa ya shiga trap d’in SURAJ SA’ID ya kwana lafiya”, Ya fad’a yana cukwikwiya rigar da ya cire, ya jefar da ita cikin basket, tare da fusgar da iska.

    Toilet ya shiga, ya watsa ruwa, Cikin minti 5 ya shirya, Singlet da boxer ne a jikin shi, Ya fito hankali kwance, Ganin sa tayi saurin sunkuyar da kai, ” Mara kunya”, Ta fad’a a ranta,

    ” Taso kiyi aikin ki”, Ya fad’a da umarni, Ita sam ta manta da zancen wani tausa, Kamar ta fasa ihu ta mik’e tabi bayan sa, goshin still yana azaba.

     Kan gado ya kwanta ya mik’e k’afa, Yasa hannu ya tallabo kansa saman pillow, Fetta tunanin yadda zata d’aura hannun ta kan jikin sa take,  k’ato a gabanta sanye da boxer da singlet, taga tausa ana yi ko sanye da kaya, jikinta bai tab’a had’uwa da na da’ namiji ba,

     “Oya start”, Ya daka mata tsawa, A hankali ta d’aura hannun ta kan k’afar sa tana runtse ido, Laushi da taushi da yaji ya saka shi jin zirr, bai tab’a tunanin zai ji hannunta haka ba, yasan masu aikin wahala hannun su tauri yake, Bata fara ba, kuma bata d’auke hannunta ba, A tsawace yace  ” Zaki fara ko sai nayi ball dake”,

    A hankali ta fara masa tausa, Cinyar sa ya nuna mata alamun har nan zata yi, Ta runtse ido tana cije baki, ta shiga yi,

   Lumshe ido yayi sakamakon sak’on da tausar ke aikawa gangar jikin sa, Ba zai iya misalta yanayin da yake jin sa ba, Gajiyar da ya tattaro a hankali take barin jikin sa,  wani k’arfi na sauko masa.

    Fetta har ta fara gajiya bai ce ta daina ba, sai ma k’ara lumshe ido da yake, Tsayawa tayi ta huta, Ya bud’e idon sa ya zube kanta, Sai da ta tsargu da irin kallon da yake mata, ba shiri ta cigaba, Da hannu ya mata alama, ta daina taje ta kwanta,

STORY CONTINUES BELOW


   Hamdala tayi a ranta, Ta nufi k’ofar fita, “Dawo ki kwanta nan”, Ya fad’a yana jefo mata bargo,

      Cike da mamaki ta d’auka ta shimfid’a ta kwanta, A yadda ta lura dashi yana matuk’ar son a girmama shi, baya son raini, Ta kawar da tunanin, ta gyara kwanciyar ta, bacci ya d’auke ta.

     Suraj tuni ya manta duk wani b’acin rai, bacci ya d’auke sa.

            9:30am

   Fetta tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa, Tayi kyau sosai, k’amshi mai dad’i na fita daga jikin ta, Ta had’a breakfast yam balls da sauce, sai kunun gyad’a, Ta gyaran gidan, ta saka turaren wuta, Ta dawo falo ta zauna tana game da wayarta, Har lokacin Suraj bai tashi ba.

      Ya farka da sunan Allah a baki, Sosai yaji dad’in baccin jiya, Cikin minti 20 yayi wanka ya shirya, Kamar ko da yaushe k’amshin turaren sa ya sanar mata da fitowar sa, Da kallo yabi falon, komai tsaf yana k’amshi, ” Akwai tsafta”, Yacewa kansa, sab’anin Bilkisu da yake zaton tunda tazo gidan bata tab’a d’aukar tsintsiya ta share ba, Duk lokacin da zai dawo kaca kaca yake tarar da gidan, har ya tafi ba zata gyara ba, sai wani lokaci idan ya umarci masu aiki su gyara, hakan ya k’ara mishi k’yamatar ta, Shi mutum ne mai tsananin son tsafta (Mata a gyara a dinga tsafta da kula da gida, tsafta na d’aya daga cikin abunda ke jawo hankalin da’ namiji)

” Ina kwana?”, Ta gaishe sa ba tare da ta kalle shi ba, “Lafiya”, Ya amsa tare da kafe ta da ido, Yana nazarinta, Ya kawar da kai, Ya nufi dining area,

   Yana bud’e warmer k’amshi ya daki hancin sa, ko shakka babu ita ta girka, ba haka na masu aikin gidan yake ba, Yaci yamball da sauce d’in da yawa, ya masa dad’i sosai, but zaka rantse bai masa ba, bai nuna wata alama na yayi dad’i ba, Bata damu da yabon sa ba, in dai ba zai fad’a mata bak’a ba.

        Ya gama ci ba tare da yabi ta kanta ba, Ya ficewar sa, A ranta tace ” A gayas”, Idan yana gidan sam bata samun sukuni,

     Zaman shiru yau ya ishe ta, TV ta kunna ta kamo tashar arewa24, ana Kwana casa’in ta maida dukkan hankalin ta kan kallon.

    Suraj gudun kar Hajiya ta zargi wani abu yasa ya kai lokacin nan, ba tare da ya koma Lagos ba, Yana son nisanta kanshi da Fetta, Zuciyarsa sau da yawa ta kan ce masa “Ba ajin ka bace, baka dace da ita ba, Mata duk halin su d’aya”, Wannan tunanin ke k’ara sa baya son ta a kusa dashi.

    ” Ni fah Mama wallahi ba zan iya zuwa naga wata a matsayin matar Suraj ba, zan iya shak’eta”, Bilkisu ta fad’a tana cika da batsewa, Aunty Jummai tace  “Ke dalla ba cewa kika yi zaki iya zama da kishiya ba”, ” Na fad’a ne cikin giyar so”, “Hmm haka zaki daure mu tafi idan kina so komai ya tafi daidai”, Hijab ta zura tana tunzura baki.

     Bayan sun gaisa da Hajiya tace zata je su gaisa da Fetta, Ba sallama ta shigo kamar an jefo ta, Da kallon rashin sani ta bita,

   Tana zagaye falon tace ” Abun aro baya tab’a zama naka, komai dad’ewa mai shi zai karb’a”, “Baiwar Allah ban gane ki ba”, Shu’umin murmushi tayi tace ” Yar’uwa, masoyiya kuma mata a wurin Suraj “, Fetta tayi murmushi tace ” Sannu da zuwa, zauna a kawo miki ruwa”, “Ba zama ya kawoni ba, nazo na fad’a miki, ki fara shirya barin ki gidan nan, wa’adin ki ya kusa”, ” A sauka lafiya”, Fetta ta fad’a tana gyara zaman ta kan kujera, ta d’auki remote tana k’ara sautin murya.

     Bilkisu rai a k’ufule ta fita tana fad’in “Zanyi maganin ki a lokacin da kika tsinci kanki waje”, Fetta sam maganganun Bilkisu basu dame ta, ” Da tasan yadda bata ra’ayin Suraj, da bata wahalar da yawun bakin ta, ita kanta zaman jiran ranar rabuwar su take, tasan tana zuwa.

Aunty Jummai labarin k’arya da gaskiya take fad’awa Hajiya Tumba, wanda rabi akan Bilkisu ne, hadda cewa itace Amirah a islamiyyar su, Hajiya sauraren ta take, but tuni ta harbo jirgin ta.

STORY CONTINUES BELOW


     Suraj ne zaune gaban Hajiya, yana matsa yatsun k’afar ta, Tun yana k’arami yake haka, Cikin kwantar da murya yace;

” Mama gobe nake son komawa Lagos, na bar ayyuka da yawa”, “Allah ya kaimu, ya shige maka gaba”, ” Amin”, “Wani hanzari ba gudu ba, da Fetta zaka tafi”, ” A’ah anan zan barta, kafin na kimtsa na samar mana babban gida”, Ya zuba k’arya kar Hajiya ta tilasta mishi tafiya da ita, “Toh Shikenan Allah ya tsare ka ya bada nasara”, ” Amin Mamana”,Ya amsa cike da farin cikin gobe zai harba, yayi nisa da Fetta, nisan da zata gaji da jiran sa ta koma gidan su.

     Tana toilet tana wanke inners d’in sa da ya cire yau, sai b’ata rai take, “K’ato dashi sai an wanke masa”, A hanger dake bayin ta shanya, Ta fito, zaune ta tarar dashi kan gado, Yana cire safa, ” Sannu da zuwa”, Bai amsa ta ba, ya cigaba da abunda yake, “Miskilanci da jin kai kamar dan’ Sarki”, Ta fad’a tana murgud’a baki,

     Kwanciya tayi kujerar falo, ta runtse ido tamkar mai bacci gaske, Ya gama shirin sa ya fito, Kallo d’aya ya mata yasan ba baccin gaske take ba, Dariya ta bashi yadda ta wani matse ido, unfornately suna rawa,

” Ke tashi”, “Uhmm Uhmm”, Ta fad’a tana wani gyara kwanciya, “Zaki tashi ko sai na zabga miki mari, ni zaki rainawa hankali”, Da sauri ta bud’e ido, har abada ba zata manta marin da ya mata ba, bata so ko a mafarki ya sake, Yayi gaba, tabi bayan sa, Tana had’e rai,

Yau da wani salo yazo har bayan sa ya juya, yace ta mishi tausa, ” Kamar wata baiwar sa”, Maganar ta fito fili, “Baki da bambamci da baiwa ta, a banza zan zauna ina ciyar dake, kici ki kasar kiyi bacci, ba tare da wani aiki ba kinsha k’arya, kin k’ara wa kanki, kwana zaki yi kina yi”

    Idon ta ya rine kamar zata yi kuka, Cike da mugunta ta shiga danna cinyar shi, Hannun sa ya d’aura saman nata, Wani yarr taji, tana k’ok’arin janyewa, ya matse shi cikin nashi, Sai da tayi k’arar azaba, Yasa d’ayan hannun ya bige bakin, “Jikina an fad’a miki na wahala ne, na miki kalar mai son wahala”, Tayi shiru, hannun ta ya k’ara matsewa cike da mugunta,

    Ta shiga girgiza kai, Ya sake ta ” Oya cigaba”, Hannu ta shiga yarfawa ta tsala ihu “Wayyoo hannu na ya karye”, Zaka rantse da gaske take, nan kuwa so take ya barta ta kwanta,

    Ta bashi tausayi yadda take ihun azaba, da hannu ya mata alamar ta masa shiru, Yasan ba karyewa tayi ba, but ya d’auka targad’e ne,

    Rob ya d’auko jikin madubi, Ya kama hannun ya shafa, yana ja, sai ihu take kamar da gaske, Ta cika masa kai sam baya son hayaniya, Dan’kwalin dake kanta ya fisge, gashi ya zuba gadon bayan ta, ” Turbarkallah”, Ya fad’a a ransa, bai tab’a ganin mai tsawon gashinta ba, sai a k’asashen turai.

     Kamota yayi ya manna jikinsa, k’amshin turaren ta ke dukar mishi hanci yana saka shi a wani yanayi, Dan’ kwalin yasa ya d’aure bakin ta, ya raba jikin sa da nata, Ya cigaba da jan hannun sai da yayi k’ara, ya kwance bakin ta, ya mata alama da hannu taje ta kwanta.

      Ya kashe wutar d’akin ya kwanta yana jan tsaki, ihun ta ya saka mishi ciwon kai, Ya k’osa gari ya waye, ya tafi ya huta.

    Suraj ya had’a abubuwan sa na amfani, dan zai jima bai dawo ba, Tana zaune falo ya fito janye da trolley, Suit ne a jikin sa da suka matuk’ar yi mishi kyau, Kallo d’aya ya mata ya kawar da kai, A ransa yana jin kallo na k’arshe ne ya mata.

     Ganin sa da trolley ya tabbatar mata tafiya zai yi, Dad’i da farin cikin ne ya ziyarci zuciya da ruhin ta, Yaron sa ya shigo ya d’auki trolley, Shima yabi bayan sa.

      Sashen Hajiya ya nufa. ya mata sallama, bayan ya ajiye mata mak’udan kud’i, Ta k’ara jadadda masa ya dawo ya d’auki Fetta, ya amsa da toh.

     Shigar sa jirgi yaji tamkar an sauke masa dutse dala, Ya kwantar da kansa jikin kujera yana jin annashuwa.

    Ta b’angaren Fetta, sashen Hajiya ta nufa, Su’ad da k’awar su Tasleem ne a falon sai harare harare suke da yada habaici, bata bi ta kansu ba, ta shige ciki, Hajiya bata mata iyaka da ko’ina a gidan ba, Tace a duk lokacin da tazo bata sameta babban falo ba, Ta k’arasa ciki,

    A falon sama ta tarar da ita, Cike da far’a tace “Ya’ta”, Da ladabi ta gaishe ta, T amsa, Bowl na apple ta mik’a mata ” Gashi kici”, Ta girgiza kai, “Bansan sai yaushe zaki saki jiki dani ba, ki d’aukeni tamkar mahaifiyar ki”, ” Allah na k’oshi ne”, “Ko har kin fara kewar mijin naki”, Cike da kunya ta sunkuyar da kai, “Allah sarki Hajiya, if only kinsan irin zaman da muke”, Tacewa kanta, “Allah ya had’a kanku, ya bada zuri’a ta gari”, Addu’o’in  Hajiya sam bata jin dad’in su.

     ” Ina kai ina auren Karima, Yarinyar da take tamkar karya akan bin maza”, Mahaifiyar sa ta fad’a, “Gwaggo ki fa….”, ” Yimun shiru, ni fah bana son had’a zuri’a da Yelwa, ba mutuniyar arzik’i bace, Shima Sulen ba’a bar sa a baya ba, ka cire auren Karima a ranka”, “Gwaggo ko dan zumunci”, ” Idan zumunci ne ga yaran Hajiya Tumba, kaje ka zab’i d’aya a cikinsu, bana son harkar tsiya da tambad’ewa”, Shiru yayi cike da takaicin halin uwar sa, Ya tabbata da iyayen Karima nada arzik’i tuni zata amince da zancen auren, ba tare da ta duba halin ta da na iyayenta ba, Gwaggo ta dad’e tana ma Bello sha’awar auren Su’ad ko Safeena dan suma su d’and’ani arzik’i.

  Ta jima sashen Hajiya, tana bata shawarwarin zaman duniya da zaman aure, kafin ta koma sashen Suraj,

    Bandak’i ta nufa tayi alwala ta gabatar da sallar azahar, Ta mik’e tana folding sallaya, idon ta ya kai kan kud’i masu yawa saman gado, ta zaro ido, bata tab’a ganin yawan su ba, Takarda ta gani a saman su, Ta d’auka ta karanta;

  _Aslm, Nasan kinsan bana son auren ki, zaman mu a inuwa d’aya ni dake ba zai tab’a yiyu ba, Bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane, kamar yadda babu had’in kifi da kaska, Zuciyata ta kasa amsar ki matsayin matata, bana jin sonki ko k’adan a zuciyata, zan nisanta kaina dake, nasan kina sona ina baki shawara ki cire ni a ranki, idan kika gaji da jirana ki koma gidan ku, kafin na aiko miki da takardar ki, ga kud’i nan nasan zasu ishe ki kafin lokacin da hakk’in ki zai sauka kaina_

     “Nasan kina sona”, Ya tsaya mata rai ya bak’anta zuciyar ta, A fili ta furta,

   ” Ni Fatima Muhammad sai na nuna maka bana son ka, bana k’aunar ka, bana son kasancewa tare da kai, “,_Murtala Muhammad International Airport_ +

   Jirgin su na landing, Driver sa na garin ya iso, ba b’ata lokaci ya karb’i luggage d’insa ya saka a mota, Shima ya shiga, Driver yaja zuwa Victoria Island (Unguwar da Suraj yake).

     Rigar sama ya cire, ya zauna yana huce gajiya kamar wanda yayi tafiyar mota, Cikinsa yayi kuka alamar yunwa, hanzari bai barsa yayi breakfast ba, Yaron sa ya kira yace yayi masa order chips da egg sauce.

   In less than 30mins ya kawo, A plate ya zuba, Ya fara ci, sam bai masa dad’i ba, Wayarsa ya d’auka ya kira Kamal(Yaron sa)

      “Ina ka siyo chips d’in nan?”, ” Wurin da aka saba siyowa”, “K’arya kake, it taste different”, ” Wallahi Sir a can na siyo”, Ya kashe wayar yana cewa sun b’ata abincin su, Haka ya cusa ba dan yaji dad’in shi ba sai dan yunwa, (Girkin Fetta ya fara tasiri, Mata a zage wurin iya girki, yana da matuk’ar muhimmanci a zamantakewa ta aure, yana k’ara miki k’ima a wurin miji, da hana miji cin abincin waje, yaji idan ba girkin ki ba, ba zai iya cin na kowa ba sai dole)  

Fetta tattara kud’in tayi da takardar ta bud’e drawer ta saka, A ciki taga wani d’an k’aramin littafi, Hakanan taji tana son ganin rubutun dake ciki, “Idan sirrin sa ne da baya so kowa ya gani fah”, Zuciyarta tace mata, Ta mayar ta ajiye, ta rufe drawer, Ta nufi falo ta kunna kallo.

    “Aikin Malam yaci, Ya Suraj ya tafi lagos ya bar Fetta”, Bilkisu ta fad’a cike da farin ciki, Aunty Jummai ta washe baki tace “Dama Aminiya tace aikin sa tamkar yankan wuk’a yake”, ” Na yarda”,  “Yanzu Hajiya zamu yi k’ok’arin cusa ma k’iyayyar ta”, ” Taya?”, “Kawo kunnen ki”, Aunty Jummai ta rad’a mata, Sukayi dariya suka tab’e kamar k’awaye.

     Hajiya tace Su’ad taje ta taya Fetta kwana, Rai bai so ba ta shigo sashen.

    Fetta bacci take ji but tsoro ya hana, ba zata iya kwana ita kad’ai, Ganin Su’ad taji dad’i, bata tanka ta ba, Ta wuce cikin d’aki, Ta hau gado ta fara waya, tana kashe murya, daga ji da saurayinta take.

     Fetta bata bi ta kanta ba, Tayi shimfid’a a k’asa, cikin minti biyar bacci ya d’auke ta.

      Da asuba da tashi, ta tashi Su’ad, tsaki ta mata ta k’ara gyara kwanciya, Sallah tayi ta zauna tana karatun Qur’ani har gari ya waye, Tayi wanka ta shirya, ta gyara gidan ta saka turaren wuta,

    Tea da bread tasha, dama ita ba gwanar cin bacci ba, saboda Suraj take girki, har lokacin Su’ad bata tashi ba.

     ” Itama bacci ne da ita, kamar yayanta”, Fetta ta fad’a, Wata zuciyar tace mata “Me yafi ransu basu da wata damuwa”,

     Kiran Yasmeen ya katse mata tunani, Tayi receiving, Da sallama, ta amsa tana fad’in ” Nayi fushi, kin nuna dai bakya son zumuncin dani”, “Ba haka bane”, ” Hakane mana, kiyi aure ba sanarwa, haba Fetta”, “Aure ne yazo a bazata”, ” Na miki uzuri, Allah ya bada zaman lafiya da zuri’a d’ayyiba”, “Toh yaushe zaki zo?” Ta fad’a ba tare da tace Amin ba, “Gobe In Shaa Allah, ki turo mun address”, ” OK”, Sukayi sallama ta kashe.

     Suraj duk abincin da yaci baya jin dad’in sa, Ya rasa dalili, Yaronsa restaurant kusan 4 yaje yayi masa order abinci, but duka yace babu dad’i, Sai faman masifa yake mishi, Mota ya shiga da kanshi, yaje best restaurant na garin, in dai abincin ne babu wanda ya kaisu iyawa, Manyan mutum garin da bak’i a wurin su suke ci,

     Yayi order fried rice da chicken, Spoon d’aya yaci, yaji ba dad’i, Tashi yayi ya bar abincin cike da takaici, Yoghurt ya siya yasha, Ya nufi company sa na siyar da motoci, Cike da tunanin Why kowane abinci baya jin dad’in sa, which is unusual, ko asibiti zai je a duba sa, Maybe daga laifin bakin sa ne.

    Su’ad ta taso yana mik’a, Dining area ta nufa, taga wayam babu breakfast,

    “Ina breakfast?”, Ta tambaya tana bin Fetta da wani shegen kallo, ” Kin bani ajiya ne, ki shiga kitchen ki dafa”, “Baki isa kizo gidanmu ki raina mana hankali ba”, ” Yadda kike da iko da gidan, haka nake dashi, gidan Mijina ne”, “Wallahi bada jimawa ba zaki bar gidan nan”, Ta fad’a a k’ufule ta fice.

    Fad’awa tayi jikin Hajiya ta fashe da kuka, Ta d’ago ta tana tambaya lafiya, ” Matar Ya Suraj ce, ta hana ni breakfast, na shiga kitchen zan girka wai na fita, naje nayi aure ba yawon banza ba”, Hajiya tasan k’arya Su’ad take, ta yarda da hankalin Fetta, bara ta tab’a yin haka ba,

   “Ke Su’ad kiji tsoron Allah”, ” Wallahi Ma…..”, “Rufe mun baki, tashi ki bani wuri”, Ta mik’e rai a b’ace, taso ta had’a mata gwarama, ta rasa me tama Hajiya bata ganin laifinta,

     Fetta wunin ranar ruwan tea ne a cikin ta, sai wainar fulawa da tayi taci, Da yamma Su’ad da k’awayenta suka cika falon, Fetta d’aki ta shige ta saka key, Ba irin knocking da basu yi ba, zasu yi fitsari tak’i bud’ewa, idan fitsarin gaske ne suje sashen su,

    ” Kun sakar ma matar nan da yawa fah”, Cewar d’aya daga cikin k’awayen su, “Zamuyi maganin ta kafin Ya Suraj  ya dawo”, Suka yi rashin mutuncin su, da yada habaici, Suka fice,

     Fetta na d’aki bata fito ba, balle ta nuna tasan da ita suke.

     Suraj ya dawo gida a gajiye, yunwar cikin sa ta ishe shi, ba abunda yaji yana buk’ata kamar tausa, Kamal ya kira yace ya nemo masa masu tausa home service, Ya amsa da toh cike da ladabi,

     Maza biyu ya d’auko masu tausa, Shago ne dasu mai so yaje a masa ko suzo har gida su ma, ka biya.

     Suraj ya mik’e k’afa, Emmanuel na d’aura hannu, yaji kamar katako, Da sauri ya bud’e ido yace ” Don’t tell me da wannan hannun kake wa mutane tausa”, Emmanuel yace “Sir ai duk garin nan, ba wanda ya kaimu iya massage”, ” You are not serious, you zo kayi”, Ya fad’a yana nuna d’ayan,

    Cike da nuna k’warewa ya d’aura hannun sa ya fara, Suraj ji yayi tamkar ana matsa mishi da dutse, ” Karya ni zaka yi” Ya fad’a a tsawace, Da sauri ya janye hannun shi yace “Sorry Sir”, ” Kamal fitar mun dasu, hannun su kamar katako, jikina bai saba da wahala ba” 1

    Emmanuel da Jacob sun nunawa Kamal b’acin ransu, Sunce ya kira su ne dan a wulak’anta su, Lagos kowa yasan sun k’ware wurin massage, but dan wulak’anci yace hand d’insu kamar katako, Kamal hak’uri ya basu, Suka tafi rai a b’ace,

    “Kaje ka d’auko mun wanda hannun su duk kanta, Allah yasa basu ji mun ciwo ba”, Ya fad’a yana dudduba jikinsa, ” Zo kamun”, Ya umarci Kamal, Shima dai cewa yayi hannun nasa ya cika tauri,

   Kamal ya fita rai ba dad’i, Dawowar nan ya kasa gane kan ogan nasa, Ga dukkan alamu akwai abunda ke damun sa.

      Fetta zaman ita kad’ai ya ishe ta, Ta lek’a sashen Hajiya, A falon k’asa ta tarar da ita, tana waya,

    “Ka ganta yar’ halak ana maganar ta”, Cewar Hajiya, zancen ya dawo ya d’auki Fetta take mishi,

    ” K’araso ga mijin ki”, Ji yayi kamar ya kashe wayar, sam baya son jin muryarta, Da yasan Hajiya zata mishi maganarta da bai kira ba, “Meyasa na shigo?”, Fetta ta tambayi kanta, tana dana sanin shigowa da jin kamar ta koma,

    Hajiya ta mik’a mata wayar, Ta kanga a kunne tare da yin sallama, Ya amsa, ” Ya Ayyuka?”, “Kina kewata ko, kinji dad’i kinji sweet voice d’ina”, Mamaki ya hana mata magana, banda tana gaban Hajiya ta da fad’a masa maganar da zata dad’e tana ci masa rai, ” Duk jin muryar tawa ce ya kashe miki jiki”, Mik’awa Hajiya wayar tayi, idan tana cigaba da jin talks d’insa, zata iya yab’a masa maganar ba tare da ta sani ba.

     Sallama suka yi da Hajiya, Ya kashe wayar, Ya kwanta kan kujera, Yana lumshe ido, “Sorry Mama, zan fara karya umarnin ki, ba zan tab’a dawowa kano ba, sai bararojin da kika aura mun ta fita rayuwata”,Gaishe da Hajiya tayi, ta koma sashen ta, Suraj ya dagula mata lissafi, Tsaki taja a karo na ba adadi tace “Nice ma nayi kewar sa ya raina ni”, Ta fad’a tare da yin k’wafa. +

     TV ta kunna, ta kamo tashar arewa24 bata missing kwana casa’in.

     Sallamar da taji ana yi, ta tashi ta bud’e k’ofa, Yasmeen ce, ” Ashe kina hanya”, “Eh surprise na miki”, “Sannu da zuwa”, “Yawwa”, Ta fad’a tana zama kan kujera,

     ” Amarya har  fresh kinyi”, Tayi smiling tace “Ba wani fresh”, ” Wallahi kuwa, ina angon?”, “Yayi tafiya”, ” Dama irinsu basa zama, Fetta wallahi kin dace miji, Suraj yana cikin masu kud’in garin nan”, Tayi smiling a ranta tace “Ku kud’i ya dama, Mutumin da yasan darajata nake so”, A fili tace ” Bari na kawo miki ruwa”, “A’ah barshi wlh, ba dad’ewa zanyi ba, ana jirana”, ” Ba wuni kika zo mun ba”, “Zan dawo , ai zan rik’a zuwa”, ” Allah ya yarda”, “Amin”

   Sun d’an tab’a hira, ta mata rakiya ta tafi.

   Suraj ya daina jin dad’in abinci, sai dai yaci dan yunwa, Yau ma kaza ya siyo ya kura da lemo,

    “Ranka ya dad’e kayi bak’uwa”, Kamal ya fad’a cike da ladabi, ” Who?”, “Chioma”, A tsawace yace ” Sau nawa zan fad’a ma ka daina barin mata na shigowa”, “Am sorry Sir”, ” Get out”, Jikina na rawa ya fice.

    Yaja tsaki yana gyara kwanciya kan kujera, He is feeling too weak, Dawowar nan shi kansa ya kasa gane kansa, komai baya jin dad’in sa, Ga jikin sa dake ciwo, Yaje asibiti Dr ya tabbatar masa lafiyar sa lau, tsaki yaja a karo na ba adadi.

     “Amarya ta fara fita, shine bata kawo mana ziyara ba”, Aunty Jummai ta fad’a, ” Wacce Amarya?” Hajiya ta tambaya, “Fetta mana, jiya na ganta ta fito super market tare da wani, wanda nake tunanin direba ne”, Hajiya tace ” Kinga mai kama da ita dai, Fetta bata fita”, “Hajiya kenan, ai ko cikin duhu na ganta zan ganeta, k’ila dai baki san ta fita ba”,

   Hajiya tayi shiru tana nazari, yaushe Fetta ta fita bata sani ba, bata ji fitar mota ba, waye daga cikin drivers ya kaita.

     Su’ad ta shigo sanye da earpiece tana wak’e-wak’e, Kwanciya tayi kan kujera ta mik’e k’afa,

     ” Ai shi talaka, burin sa ya auri mai kud’i ko danginsa su d’and’ani arzik’i” Su’ad ta fad’a a cikin wak’arta, Fetta bata tanka ta ba, ta cigaba da sharar ta,

      “Na barta cikin kokwanto, haka zan cigaba da saka mata zargi akan Fetta, kinga d’ayan plan d’inmu zata yarda, Tasa Suraj ya kora ta, ke kuma ki shiga”, Cewar Aunty Jummai, Bilkisu tayi dariya tace ” Ina Sonki Mamana”, “In dai ina raye babu ke babu kuka”, Ta rungume ta.

   Fetta fatan ta Allah yasa ya aiko mata da takardar ta kamar yadda ya fad’a, Bazata koma gida da igiyar auren sa a kanta.

    K’arar wayar sa, ya tashe shi daga bacci, Tsaki yayi ya jawo wayar da niyyar kashewa, Ganin mai kiran ya danna receive.

    ” Ranka ya dad’e ina kwana?”, “Lafiya”, ” Na samu information kamar yadda kake buk’ata”, “OK send it through my email”, ” Amma Ranka ya dad’e ana buk’atar shigowar ka Kano”, D’an jim yayi an tab’o masa abunda baya so, but ya zama dole yaje Kano dan cikar burin sa, “I will make it In Shaa Allah”, Ya fad’a yana kashe wayar, Ya fusgar da iska, tare da cusa yatsun hannu cikin gashin shi, Yayi murmushi mai ma’anoni daban daban.

STORY CONTINUES BELOW


    “Aliya me zai hana ki samu mana taimako wurin mijin Fetta, ko jari ne ya bamu mu fara sana’a”, Cewar Ya Hafsa, ” A’ah Ya Hafsa ina jin kunyar sa, kuma bana son abunda zai ja mata raini, kinsan masu kud’in nan”, Ta rik’e hab’a tace “Yau ina ganin bak’in ciki, yayarki uwa d’aya uba d’aya kina mata bak’in ciki, to ni da kaina zanje, ban rasa k’afa da baki ba”, Aliya shiru tayi rai ba dad’i, sam bata son wannan hali nasu.
   
    Ta sab’a gyale ta fice a fusace, Napep ta shiga, ta mishi kwatancen gidan Hajiya Tumba, Fetta na zaune k’asan carpet, ta tashi da kewar Mahaifinta, da zata ga wanda suka kashe shi kotu zata raba su, duk da kasancewarta mara gata, zata mik’a su kotun musulunci, idan ta gagara Kotun Allah filin Alk’iyama zata musu hisabi.

     Sallamar Ya Hafsa ya katse mata tunani, Ta gaishe ta da ladabi, Ta amsa, ” Ina Mai gidan?”, Ta tambaya tamkar wata mahaifiyar sa, “Yayi tafiya”, ” Yaushe zai dawo?”, “Wallahi ban sani ba”, ” Kina matar sa baki san yaushe zai dawo ba”, “Bai sa ranar dawowa”, Ta fad’a, bata son kowa ya fuskanci irin zaman da suke, ” Ohh toh, baki yi girki bane, yunwa nake ji”, “Sai dai a girka miki”, ” Ba zan iya jira ba, bani na tafi dashi na girka”, Mamaki ne ya kama ta but ya ta iya, ta hana ya zama laifi, “Ki tashi ki d’ebo mun ko na shiga da kaina ne”, Kafin ta mik’e ta fad’a kitchen, Shinkafa ta d’iba dasu maggi, Ta fito dasu cike da leda.

      A k’ofa taci karo da Su’ad da Feena, Tamkar zasu bangajeta, Suka bita da harara, Ya Hafsa bata damu ba, tunda buk’atar ta ta biya,

     ” Ba zamu d’auki ana kwashe abincin Yayanmu ana ba dangi ba”, Su’ad ta fad’a tana harare harare, Feena tace “Yar’uwa ta auri mai kud’i, ana zuwa d’ibar abinci, dama shi yasa akayi auren ko aci yar’ gwamnati a murmure”, Fetta ranta ya kai k’oluluwa wurin b’aci, bata da abun cewa, Ya Hafsa taja mata tunda sun ganta da ledar abinci, D’aki ta shiga ta barsu suna yada habaici.

   Hajiya suka tarar a falo tare da Aunty Yelwa da Karima, sama sama suka gaisheta shima ganin Hajiya, Ta amsa tana washe baki,

   Feena tace ” Mama matar can kayan abinci take d’iba tana ba yan’uwan ta”, “Kayan abinci Safeena”, Anty Yelwa ta fad’a tana kama hab’a, ” Wallahi kuwa cike da leda”, “Shine me idan ta basu, ba taimako bane, bana son tsegumi”, Hajiya ta fad’a,

     ” Mama wai meyasa bakya son laifin…..”, “Yimun shiru, kar na k’ara jin bakin ki”, Ta mik’e ta fice rai a b’ace kamar zata tashi sama, Su’ad tabi bayan ta.

     K’amshin turaren sa da taji, Yasa k’irjinta bugawa, Allah yasa ba shi d’in bane, Bata farga ba, Taji tsayuwar mutum kanta, D’agowar da zata yi, Suka had’a ido, Sanye yake cike suit da suka matuk’ar yi mishi kyau, Skin d’inshi na glowing, Kallo d’aya ta mishi, ta sunkuyar da kai, Tana mamakin dawowar sa,

     ” Kinyi farin cikin gani na koh?”, Ya fad’a yana tsare ta da ido, “Bana farin cikin ganin ka, kuma bazan tab’a ba”, Hannun ta ya kama, ya d’an matsa yace ” K’arya kike, You are happy to see Suraj Sa’id”,

   Saurin janye hannun ta tayi, A ranta tace “Ya dawo ba zai k’ara barin mutum ya huta ba”,

   Kayan sa ya shiga tub’ewa, Tayi saurin ficewa d’akin, Kitchen ta nufa, Ta shiga k’ok’arin had’a girki, Cikin minti 30 gidan ya game da k’amshin girkin ta, Suraj hadda had’iyar yawu tun kafin girkin ya iso.

    Fitar da zai yi ya fasa, Sashen Hajiya kad’ai yaje, suka gaisa, Tayi farin cikin ganin sa, Dan a tunanin ta ya dawo d’aukar Fetta.

    Macaroni da tasha dry fish ta zuba a food flask, Ta had’a coconut juice ta jera kan dining table, Bai jira tace ga abinci ba, Ya nufi dining area, Ba b’ata lokaci yayi serving kansa, Spoon d’aya yayi yaji masifar dad’i, ” Delicious “, Ya furta, Sai yanzu ya fuskanci dalilin da yasa baya jin dad’in kowane abinci, Sau uku yana ci, Ya kura da lemo, Yayi gyatsa.

   Wanka ta sake, tayi k’aurin abinci, Doguwar riga ta saka, ta fesa turaruka, Yana kwance kan doguwar kujera yana kallon news, Ta fito, Ta k’asan ido yake kallon ta, Da hannun ya mata alama tazo, K’irjinta ya buga Allah yasa ba wata muguntar zai mata ba, D’an nesa dashi ta tsaya, ” Matso”, Ya fad’a a d’an tsawace, Ta k’ara matsawa, “Your duty”, Ya fad’a yana nuna mata cinyar shi,

STORY CONTINUES BELOW


   Kamar ta fasa ihu, ta tsani tausa ba dan komai ba, bata so jikinsu na had’uwa, ” Hannun na na ciwo”, Ta fad’a tana k’ok’arin matso k’walla, Kafad’a ya d’age, “Ko kariya ce a hannun sai kinyi”, Ya gyara kwanciya ya tamke fuska, Bata da wani option da ya wuce tayi, Tana farawa, Yaji wani taushi sab’anin hannun su Emmanuel, Har lumshe ido yake saboda dad’in tausar, K’amshin turaren ta na dukar hancin shi, yana haifar masa da kasala, Harara ta watsa masa, Tana murgad’a baki, Caraf a idonsa,

     ” Ni kike murgad’awa baki”, “Bakina ke ciwo fah, shine nake motsawa”, Ta fad’a cike da shagwab’a tana turo baki, Ji tayi ya kama lips na k’asa ya ciza, kafin tayi ihu, ya had’e bakinsu, Yana kissing d’inta mai cike da mugunta, Hawaye ta fara saboda azaba da takaicin had’e bakin su wurin d’aya,

    Mintuna ya d’auka, ya saki yana sauke numfashi, Da hannu ya mata alama, gobe ki k’ara, Kuka ta saki tana bubbuga k’afa, ” Mugu Allah ya isa na”, Tasowa yayi zai kamata, Ta shiga d’aki da gudu, ta saka key, Dawowa yayi ya zauna, Yana murmushi “Zanyi maganin tsiwar ki”

     Fetta kuka take sosai, tana ja mishi Allah ya isa, Bakinta sai zugi yake,     Kiran wayar sa da akayi, Yayi receiving yana fad’in “On my way”,

    Knocking k’ofar yayi, Tana ji tayi banza, ” Wallahi ko ki bud’e, ko na b’alla k’ofar na shigo na taka wurin cikin ki”, Tasan ba k’aramin aikin sa ne, jiki na rawa ta bud’e, Yana shiga ta fice da gudu, Dariya yayi yace “Matsoraciya, k’aryar tsiwa kike”,

    Kaya ya canza a gaggauce, ya fice ba tare da yabi ta kanta ba, Tabi bayan sa da harara, Ta shafa bakin ta da take ji tamkar ya cire mata wasu sassa a jiki.

    Taron taimakawa gajiyayyu ya halarta, Ya bada taimakon miliyan ashirin, Ana ta haska shi a TV, yana k’ok’arin kare fuskar sa, Sam baya son yayi taimako a nuna gidajen TV, shiyasa wani lokacin yake zuwa a b’oye ya bada taimako ba tare da sanin kowa ba.

     ” Naji labarin Ya Suraj ya dawo”, Bilkisu ta fad’a, “Lokacin aiwatar da plan d’inmu yayi”, Aunty Jummai ta fad’a tana shu’umin murmushi, Wani bak’in k’ulli ta mik’awa Bilkisu, ” Kije bayan gida ki hak’a rami ki binne, yadda kika binne shi haka za’a rufe bakin Hajiya da Suraj”, Ta karb’a jiki na rawa taje ta binne.

     Ta kammala abincin dare, Tuwon shinkafa da miyar alayyahu, Ta d’ibarwa Hajiya ta kai mata, Taji dad’i sosai tasa mata albarka, Su Feena cewa sukayi baza su ci ba anyi barbad’e.

   Suraj a gajiye ya dawo, Abinci ya fara buk’ata, Yaci yana santi shi kad’ai, Jin fitowar Fetta, ya shiga yatsina baki irin ba dad’i, bata bi ta kansa ba, Ta wuce kitchen dama ruwa ta fito sha, Ya gama ci, ya goge bakin sa da tissue.

    Ruwa ya watsa, Ya saka gajeran wando, da riga mara hannu, Wasu takardu yake nema, Ya jawo drawer, yaga kud’i, Yasan bashi ya ajiye su ba, Takardar da ya gani a saman su, ya tabbatar masa kud’in da ya bar mata ne ranar da zai yi tafiya, Ya k’irga su, ko naira bata tab’a ba, Cike da mamaki ya kwashi kud’in, Ya sameta falo “Ajiyar me kikewa kud’i, ko kina tari ne”, ” Bani da buk’atar su, kai na ajiyewa kayan ka”, Ta fad’a hankali kwance, Mamaki ne ya cika sa, “Does that mean bata buk’atar kud’in sa, basa gabanta”, ” Pretending take, tana so, ajiyar su take tana tari”, wata zuciyar ta fad’a masa,

    Komawa yayi d’aki, ya mayar wurin da ya gansu, Zuciyarsa na k’ara tabbatar masa tari take.

      Washegari tayi breakfast, Ta kammala ayyukan gida, Tayi wanka ta shirya, Ta rasa dalilin da gabanta ke yawan fad’uwa, Qur’ani ta d’auka tana karantawa.

     Yaron dake ba flowers na gidan ruwa, Yayi sallama yace “Ana sallama da ita waje”, ” Waye?”, “Wani ne wai Sahabi”, ” Sahabi” Ta maimaita, “Eh yace kiyi sauri”,

    Ciki ta koma, ta saka hijab cike da mamakin waye Sahabi.

    Matashin saurayi ne, Yana sanye da English wears, Kallo d’aya zaka mishi kasan d’an duniya ne,

     ” Hab’a babe ya zaki barni ina jira”, Harara ta watsa mishi tace “Mallam idan ma turo ka akayi dan ka lalata mun aure, kayi hak’uri bana son aurena ya mutu ta wannan hanyar”, Dariya ya fashe da ita yace ” Baby ni kike denying dan nazo gidan mijin ki, na kasa jure zuwan ki”, Mai gadi da ma’aikatan gidan tsaye suke suka kallon ikon Allah,

    Juyowa tayi zata koma ciki, Ya rik’o hijabinta, Ta juyo ta wanke shi da mari, “Ni kika mara baby, Wallahi bazan barki ba sai kin bani zumar da kika saba bani, dan mijinki ya dawo”, ” Innalillahi wa inna ilahir raji’un”, Ta shiga maimaitawa,

    Ya shiga fad’in maganganu mara sa dad’i, kan ace haka hayaniya ta kacame, Hajiya dasu Feena suka fito, Bilkisu da Aunty Jummai da shigowar su kenan, Suka tsaya kallo, Masu aiki ma duk sun fito,

   “Kai Bawan Allah meye had’in ka da ita?” Hajiya ta tambaya, “Budurwata ce, mun saba had’uwa wurare tun kafin tayi aure har tayi aure muna sharholiyar mu, kwana biyu bamu had’uwa ba, shine na biyo ta”, Aunty Jummai tace ” Shine na gansu tare ranar a supermarket “, Mutuwar tsaye Fetta tayi jin sharri da rana tsaka, Hajiya kasa magana tayi jikinta na tsuma,

     ” Allah ya tona asirin ki, da auren ki kina zina”, Feena ta fad’a, Bilkisu tace “Anyi asara”, Su’ad tace ” Allah ya kare yaya kar a jawo masa cutar zamani”, “Ko ya’yan banza”, Cewar Aunty Jummai, Haka suke ta jefan ta da mugayen kalamai, Masu aiki ma nata k’us k’us,

    Gate aka bud’e motocin Suraj suka shigo, Ganin taron mutane, Ya k’araso wurin cikin takunsa na k’asaita, Zuciyarta ta buga tamkar zata fasa k’irjin ta ta fito, Yau ko shakka babu kwanan gidansu Aliya zata yi, bata so rabuwar su tazo a haka ba, Suna zarginta akan aikata zina da igiyar aure a kanta.

    Ya tambaya meke faruwa, Su’ad ce ta masa narrating, Saurayin ya k’ara ” Nifah Wallahi Yau sai na d’and’ani zuma kamar yadda na s….”, Bai k’arasa ba sakamakon wawan naushin da Suraj ya kaiwa bakin sa, Jini ya shiga tsiyaya,

   Jikinsa kyarma yake, zuciyarsa na bugawa da k’arfi, Zancen ya daki zuciya da gangar jikinsa, “Babu wanda ya isa ya shiga gonar da Suraj ya shiga, MATATA TAWA CE NI KAD’AI, na yarda da ita, kowa ya b’ace”, Ya fad’a cikin karaji da d’aga murya, Tuni kowa ya b’ace, Saurayin ya umarci yan sandan wurin su kama shi,  Fetta dake durk’ushe a wurin tana kuka, Da mamaki ta d’ago tana kallon sa, Hannu yasa ya d’ago ta, Yaja ta zuwa cikin gida.

     Suna shiga ya jefata kan kujera, Ya saka key, D’agowa ta yayi, Ya shak’eta ya had’a da bango,

      ” Uban meye tsakanin ki da wancan?”, Ya fad’a yana d’aga murya, idonsa sun rine sun koma jajir tamkar barkono.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *