Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA
Chapter 29
Www.littafanhausane.com.ng
Haisam na saukowa ya nufo inda Ramlah take zaune yasa hannu ya tasheta tsaye ya ce “Uwar gidana yi hakuri kinsan bakuwa kwanan sabon waje dole in dan tattausheta in bata hakuri. Ramlah taji wani haushi ya tokare mata wuya ta dubeshi sai taga gaba daya kalar idanuwansa sun canja muryarsa ma ta canja ta tabbatar a cikin shaukin so yake. Lallai Hannah ta caccako dankararriyar soyayyar dake zuciyarsa. Ta fusge jikinta daga hannunsa ta juya masa baya cikin fushi ta ce “Haka zaka ce mana in yi hakuri kana can kuna kashewa juna zuciya gashi nan idonka duk ya narke kana wani kashe murya to in har kwana goman dana baka bai yi maka ba ka koma sama ni inyi tafiyata. Kafin ta rufe bakinta Haisam ya jawota jikinsa ya rungumeta tsam a kirjinsa yana cewa “Haba Aunty Ramlah ya ina yabanki sallah zaki kasa alwala karfa ki bata rawarki da tsalle mana, babu wani kashewa juna zuciya da muka yi cewa nayi ta tottofa addu’a a kowacce kusurwar daki shikenan fa abin da nace mata, wannan idon nawa kuwa da kika ga ya zama haka barci ne muryata kuwa mura nake. Ta harareshi ta ce “Naga alama mura ce ta kama ka amma a yanzu daka hau sama ko? Haisam ya kyakyale da dariya ya ce “Naga alama yau Ramlah so kike ki rikice mun, yau rigima kike ji zo in goyaki mu tafi. Bata yi niyyar yin dariya ba dariya ta subuce mata ta kyalkyale da dariya ta ce “Kyaleni ni ba wani goyo. Haisam ya jawota da karfi ya ce wai dole sai ya goyata. Ramlah ta ce “To tsuguna in hau da kaina. Haisam ya tsuguna, Ramlah ta haye bayansa sannan ya fito ya lalubo mukulli a aljihunsa ya kulle ta baya. Ramlah ta ce “Ah ya zaka kulleta a ciki. Haisam ya ce “Da mukullinta ai a wajenta in zata bude saita bude ta ciki. Ya fara tafiya ya nufi bangaren Ramlah can ya tsaya cak a tsakiyar hanya ya ce “Wai wai nauyi sauko haka goyon ya isa ki karasa da kafarki. Kinsan fa ba ke kadai bace. Ramlah ta harari keyarsa ta ce “In bani kadai ba ce ni dawa nake? Yayi dariya ya ce “Ke da dan ciki mana. Ta dan ja kunnensa ta ce “Daga fada maka magana harka fara yayatu akai to saura ka dinga fada har kowa yasan ina da ciki. Kuma bazan sauka ba sai ka kaini har cikin gida kan gado furnishment ne, daman ku maza idan kuka yi sabuwar amamrya sai dai Uwar gida ta toshe kunnuwanta ta rufe idanuwanta ta daina kallonku saboda wannan zumudin sai kunyi shi. Yarinya ta ce ba tsoro take ji ba wai kai dole sai ka rakata tsoro take ji ko waya saka oho. Ramlah na baya tana yiwa Haisam tsiya shi kuma yana ta tafiya yana dariya a ciki. Har kan gado ya kai Ramlah sannan ta sauko ta shiga bandaki Haisam kuma ya mike akan gado yana nishi wai qashin bayansa ya kusa karyewa saboda nauyin Ramlah da dan cikinta, Ramlah na jiyo shi tana wanka tana dariya tana cewa ka santa. Bayan Ramlah ta fitowa sai Haisam ya tashi ya shiga shima yayi wanka ya fito daure da tawul a jikinsa ko kayansa baisa ba Ramlah ta kara danewa bayansa ta ce ya kaita kicin zata dauko ruwan sha, nan dai suka hau kokawa Haisam ya ce bazai goyata ba itama daman tsokanar sa take ba kishirwa take ji ba suka rumtuma kan luntsumeman gadon dake malale a tsakiyar dakin suka cakuda suka yamutse junansu yayin da kokawa ta koma sumbatar juna, da shafa juna da rungume juna. Haisam da Ramlah sun farantawa junansu matuka a cikin daren yau.
Kamar yadda Hannah da Haisam suke kaiwa Ramlah ziyara bayan sunyi sallar azahar yau Ramlah da Haisam sun dungumo bangaren Hannah don suci abincin rana dana dare a wajenta daman sunyi mata waya sun sanar mata, da kukunta yazo tana biye dashi tana koyon duk yadda yake yin abinci irin na *yan gayu na zamani don ta koya ta iya, ta hutar da masu aiki ta dinga yi da kanta. Haka Hannah da Ramlah da mijinsu suka kasance cikin farin ciki da kwanciyar hankali, zaman lafiya da kaunar juna.
Kwanci tashi Hannah tayi wata guda da rabi a gidan mijinta. Misalin karfe biyar na yamma Haisam da matansa suna zaune a falon Ramlah suna hira wasa da dariya. Haisam ya ce gaskiya na gaji da bin dakunanku duk mai girki tazo ta same ni a bangarena kullum ni kenan cikin rarraba kayana sai ina bangaren Ramlah na tashi zan dauko agogona sai in tuna yana bangaren Hannah idan na tashi zan dauko gilas dina sai tuna na barshi a dakin Ramlah, shekaran jiya ma sai rigar Hannah na saka ta barci saboda ashe mai wanki da guga ya wanke ya fitarmin da kayan barcin gaba daya ya hada a kayana ya kai bangarena. To na gaji kowacce ta hado min kayayyakina na bangarenta ta kawo mun nawa bangaren. Abinci ma duk mai girki tasa a dafo a zo a ajiye akan teburin cin abincina sannan kowacce tazo mu hadu muci. Ramlah da Hannah suka kece da dariya suna cewa “Kai din dai ka dinga zuwa tunda haka ka fara yi. Haisam na cewa “Naki wayon ai yanzu na fara gane wayo kuke min. Hayaniya da dariyar da suke yi ita ta hana suji ana dannan kararrawa ana ta kwankwasa kofa. Can Hannah taji ta ce “Ana danna kararrawa fa. Ta mike da sauri ta zo ta bude. Wasu mata ne guda uku hadaddu *yan gayu masu ji da kudi kallo daya zaka yiwa dukkanninsu ka gane *yan hutu ne, suna da kyau kuma dukkanninsu. Mace daya a cikinsu tana da tsohon ciki ko yau ko gobe. Hannah tayi musu murmushi gami dayi musu sannu da zuwa. Bata ishesu kallo ba balle su amsa mata kai tsaye suka wuto cikin gidan. Ta bisu da kallo zuciyarta cike da mamakin meye haka kuma lafiya daga zuwansu su hau bata rai da harare-harare. Ta sake kallon me cikin don tana yi mata kallon sani, sai can ta tuno ashe Hidaya ce matar Yaya Habib “No wonder” Hannah ta fada a ranta. Ta tura kofa ta rufe ta nufo inda suke zazzaune a sanyaye cike da fargaba tasan ko ta gaishesu baza su amsa ba. Ta bari suka gama gaisawa da Haisam sannan ta gaishe su. Kokonto ya zama gaskiya ai basu amsa mata ba sai ma wata harara da suka sakar mata dukkanninsu. Nanfa aka hau kallon-kallo tsakanin Haisam da Ramlah da Hannah da kuma wadannan baki. Hidaya ta yamutse fuska ta ce “Aisha Sulaiman, Hauwa Mamman kuzo mu koma wancan falon mu zauna mun isa muzo mu zauna tsakiyar amarya da ango. Aisha ta ce “Da kuma Uwargidansu Ramlah kin manta baki fada ba. Hauwa Mamman ta ce “Oh haka ne fa baku gani ba, amarya sai hararar mu take lallai zuwa gidanki Ramlah nan gaba sai mun shirya, to bangarenki ma *yan Uwanki da kawayenki basu isa suzo ba ashe to ta biyoki ta biyo mijinta. Suka mike suka nufi daya falon.
Ramlah ta rasa ta cewa ta bisu da kallo kawai can ta nisa ta juyo ta dubi Haisam wanda yayi shiru yana kallon talabijin amma kallo daya zaka yiwa fuskarsa kasan cikin bacin rai yake. Hannah kuwa ta sunkuyar da kai kasa hakika nan da wasu *yan dakikai zata fara zubar da hawaye.
Ramlah ta ce “Yallabai wai me su Hidaya suke nema ne dani, yaya suke so nayi. Yasa hannu ya dakatar da Ramlah ya ce “Yi shiru karma ki bata bakinki barni dasu jeki gurinsu bakinki ne. Can Ramlah ta yunkura ta mike ta nufi kicin ta shaidawa kuku da sauran masu hidimmarta su hado juices da snacks su kawowa bakinta, tazo falon da kawayenta suke suka fara cafcafkewa suna hira. Haisam ya kurawa Hannah ido yana kallonta can ta dago ta dube shi saita daure da kyar ta kirkiro wani dan busasshen murmushi. Ya ce “Yauwa ko kefa, meye abun damuwar? Ki daina damun kanki akan irin wadannan *yan matsaloli kinsan dai ba za’a sake tataburzar da akayi a Kazaure ba ko? Ba za’ayi irin yadda kikayi da su Juwairiyya ba, Sahabi, Principal, Yaya Habib da Rauda ba ko? To duk wadancan basu zamar mun matsala ba wajen wargazasu balle su Hidaya, zanyi maganinsu Insha Allah kallonsu nake yi tukunna wata rana ko kudi aka basu akace suzo gidan nan su yadar miki da magana baza suyi ba. Hannah ta nisa ta girgiza kai ta ce “Yaya da zaka ji shawarata ka taimakeni ka kyalesu dan Allah ko me zasu yimin kuma kome zasu ce kabar su ni na saba da duk irin wadannan tsangwamar tuntuni a rayuwata. Tsorona daya kada yau da da gobe suna zuga Aunty Ramlah tun bata dauka har tazo ta fara dauka zamanmu yazo yaki dadi. Haisam ya girgiza kai ya ce “Haba Hannah ai tun daga ranar da muka sake haduwa ranar da aka ce miki na rasu kika fito daga daki kika ganni na ganki kikayi murmushi hakika nasan farin cikin da kika ji a ranar bazai misaltu ba da kika ganni a raye ban mutu ba, to da yardar Allah tun daga ranar har karshen rayuwarki kin dinga farin ciki kenan, kin rabu da damuwa da tsangwama insha Allahu. Hannah tayi murmushi ta ce “Na gode maigidana, to amma ina gudun zuciyar ka da zafin fushinka irin na Kazaure. Haisam yayi dariya ya ce “Tunda na same ki yanzu komai ma a sauki zan dinga daukarsa na daina fushi da yawa my love. Suka sakarwa juna murmushi. Ya ce bude dirowar can ki mikomin Jarida zan karanta, ta mike a nutse ta dauko masa tazo ta durkusa ta mika masa tazo kusa dashi ta zauna, yana karatu ita kuma tana kallon talabijin.
Wayar dake dore akan tebur tayi ruri (land line). Ramlah tasa hannu ta dauka muryar kawarta taji Mrs. Blessing ma’aikaciyar filin jirgi a Abuja bayan sun gaisa sai ta sanar mata da cewa bizar Hannah da Haisam ta fito don haka su zama cikin shiri nan da kwana biyu jirgi zai tashi zuwa London daga Abuja. Ramalah tayi mata godiya suka yi sallama ta ajiye wayar, ta ce da kawayenta tana zuwa. Ta mike ta nufi falon da Haisam suke zaune ta fusge jaridar da take hannunsa yana karantawa tayi dariya ta ce, “Albishir nazo zanyi muku bizar ku ta tafiya kasashe ta fito nan da kwana biyu zaku tashi zuwa London daga Abuja. Haisam yayi dariya ya ce “To madallah Ramlahta ai shi yasa bana fargaba da sha’aninki yanzu ko sati biyu baki yi ba da zuwa Abuja neman mana biza har an samu. Ramlah tayi murmushi ta ce “Haba don neman biza, ai ko tashar jirgi kake nema a kwana daya zansa a nemo maka saboda kawayena wajen su uku ne acan ko banje ba in nayi musu waya zasu yimin duk abinda nake bukata, balle in tashi inje Abujar da kaina kasan dole ne ma su zage dantse su nemo min bizar da awuri sun san ba karamin sauri nake yi ba. Hannah dai sai murmushi take yi, ta ce “Auntyna godiya muke yi fa sannu da kokari. Ramlah ta kalleta tayi dariya ta ce “In banyi muku ba, wa zanyi mawa babu komai fatan alheri nake muku kuje lafiya ku dawo lafiya ku same mu lafiya. Hannah da Haisam suka hada baki suka ce “Amin. Ramlah ta juya ta nufi wajen kawayenta wadanda suka kasa kunne suna sauraren abinda suke fada. Sai suka sake jin haushin Ramlah kowacce ta rike baki don mamaki wata na salati wata na tsaki. Ramlah ta karaso da murmushinta ta zauna. Ta daga ido ta kalle su sai taga gaba dayansu harararta suke yi. Tayi mamaki matuka kafin ta ce wani abu sai taji an turo kofa an shigo gami dayin sallama, mai gadinsu ne ya zo ya durkusa a gaban Ramlah ya gaisheta ya ce “Daga gidan gwamnati aka turo wasu mata guda biyu wajen Hajiya Hannah na nuna musu bangarenta sunje sun ce a kulle yake, shine na ce bari in duba musu nan dan dai banga fitarta ba ko tana nan? Ramlah ta ce “Tana nan kace musu tana zuwa. Ya mike yana godiya ya fita. Ramlah ta kwallawa Hannah kira. Cikin ladabi Hannah ta amsa ta taso tazo wajen Ramlah. Ramlah ta ce “Baki kika yi may be Nusaiba ce ta aiko su suna waje inji mai gadi. Hannah tayi murmushi ta ce “To bari in je na gode. Ta wuce ta nufi kofar fita su duka suka bita da kallo. Wata dandatsetsiyar shadda ce a jikinta pink colour anyi mata surfani da design me kyau a zani da rigar da dankwali wato (ready made). Hannah tayi kyau matuka. Lallausan gashinta ne har tsakiyar bayanta ta sake shi bayan ta daure da pink din ribbon.
Aisha Sulaiman ta ce “Turkashi. Hauwa Mamman ta ce “Rigijigafji inji masu iya magana. Hidaya ta ce “Wani kayan sai Amale. Ramlah ta dubesu dukkansu ta ce “Ah wanne yare kuke yi ne bana jinku? Hidaya ta ce “Yaran Hausa muke yi mana. Ramlah ta ce “Ban fahimce ku ba. Aisha Sulaiman ta ce “Turkashi na ce, Hauwa ta ce rigijigafji, Hidaya kuma ta ce wani kaya sai Amale gaba daya abu daya muke nufi gaba daya muna magana ne akan babban aiki. Ramlah cikin mamaki ta ce “Wanne irin aiki kuma? Aisha Sulaiman ta ce “Hidaya ku fada mata danni idan na cika yawan magana sai jinina ya hau saboda takaici. Hidaya ta nisa ta ce “Ramlah, Ramlah sau nawa na kira kunnanki? Kin bani kunya, kina bani mamaki wai shin meke damunki ne? Ramlah me yasa kika zama makauniya alhalin kina gani da idanuwanki guda biyu, kin zama wawuya alhalin kina da wayo. Kin zama kamar baki san abunda kike yi ba alhalin kina sane. Ina miki fargabar ranar da zaki zo kina dana sani, kina zubar da hawaye da idanuwanki. Ramlah taji gabanta ya fadi ta fada cikin rudani “Wai meke faruwa ne? Me kuke nufi? Dan Allah ku fada mun abunda nayi yadda zan gane na kasa fahimtar ku.
Hauwa Mamman ta ce “Abunda muke nufi shine kinyi kuskure, kinyi sake, kin dau abin da sauki alhali ba mai sauki bane. Ramlah yanzu kece kika samarwa mijinki bizar da zai fita da amaryarsa suje su shakata a kasashen waje ke kina gida a zaune. Wai shin ke me kika dauki kishiya ne?
Karfa ki dauki Hannah karamar yarinya ce wacce bata waye ba, ki dauka baza ta bude idonta ba tayi miki rashin mutunci a gidan nan ba dubi yadda Hannah ta zama a cikin wata biyu ta goge tayi kyau tamkar wata baturiya kina zaune. Na daya tana da kyau harta fiki, na biyu ta iya kissa da kisisina da iya magana da ladabin munafurci. Da sannu zata tafi da zuciyar mijinta da Iyayensa da duk danginsa kina zaune bude da baki. Aisha ta ce “Ah to. Mudai mun zo ne mu fada miki gaskiya kin sakarwa kishiyarki da yawa duba kiga falonki shekara biyu kuna tare da Haisam baku dauki hoto ba ku biyu kin lika a falonki sai zuwan Hannah kuka hadu ku uku kuka dauki hoto kalli hoton ko kishi ba kyaji kika lika hoton kishiya a falonki. Gaba daya kin canja Ramlah kamar ba keba. Ki tsare girmanki ko ganinki tayi sai gabanta ya fadi karyarta nan gaba ta ce zata waye ta ce zata takaki. Shima dole yaji shakkar ba zai sake da ita ba. Haka rannan naji ance har gidanku kika dauketa kika kaita kuka yini, lallai kishiya ta zama kawa. “Hauwa Mamman ta ce , “Wallahi ni duk ranar da Ibrahim mijina ya tarki aure daga shi har amaryar saina babbakesu aina fada masa. Bai isa ba shi da kansa yanzu yake cemun ko bashi mace aka yi ba zai karba ba, to kin gani namiji zuma ne sai an babbaka masa wuta. Hidaya ta yamutse fuska ta ce “Ke kin fadawa mijinki ma irin hukuncin da zaki dauka idan ya qaro auren, to ni ban fada masa bama matakin da zan dauka, amma shi da kansa ya sanni ko a hanya muna tare bai isa ya daga ido ya kalli mace ba balle yayi min zancen aure a wasa ranar sai dai ya kwana a bakin get dan kulle kofata nake yi in kyaleshi, balle yayi dare. Aisha Sulaiman ta ce “Muktar mijina ai ya taba tarkar aure Ramlah kin manta da irin tashin hankalin da mu kayi ba shiri ya fasa to haka akeyi muddin kika yi sakwa-sakwa za’ayi babu ke. Tunda ta riga ta shigo yanzu ke abunda ya kamace ki Ramlah ki iya takunki, kishiya ba abar yarda bace kada ki barta ta sake ta baje ta baza kayanta tayi kane-kane ta mallake miki miji ta mallake ki. Hidaya ta ce “Wai kishiyar ma data sake mai da ita wayayyiya,
kyakkyawa irin Hannah, ai irinsu Hannah bai kamata ki sake ba saboda duk wani da namiji burinsa ya sami mace kamar Hannah balle wanda ya aureta dole ya rikice ya mace mata ke kuma kina zaune a gefe. Kiyi dai tunani Ramlah akan nasihar da muka yi miki don gaskiya mu mun hango miki abunda ke baki hango ba.
Cab Mata?? Uhm bari dai nai shiru,,,,,
Www.littafanhausane.com.ng