Gangar jikinsa na aura20

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA

 Chapter 20

Wata rana da yamma Hannah da
Indo sun je rafi
sun
debo ruwa suna tafe suna hira
sai suka ji Hassan
me
yekuwa yana sanarwa yana
cewa “Yekuwa jama’a ga
wata sanarwa, mai girma
dagacin garin nan ya ce
a sanar muku, mata wadanda
mazansu suka rasu
suka barsu da suzo fadarsa yanzun
nan. Ma’aikata daga
Nigeria sunzo musu da tallafin
taimako. Gwamnatin
jihar Kano a Nigeria ta aiko da
taimakon kudi za a
raba musu jari domin su rike
kansu da marayun *ya*yansu.
Amma kada wata ta kuskura
taje idan ba mijinta
bane ya mutu, sai wacce mijinta
ya mutu. Indo ta
zunguri Hannah ta ce “Hannah
muje wajen taron nan ko Allah
zai sa mu dace. Hannah ta rike
baki ta ce “Babu ruwanmu
yanzu idan muka je ai mun
shiga uku a
wajen Inna cewa zata yi munje
mun tona musu asiri ci
muka rasa ko sha. Indo ta ce “To
shike nan amma idan
muka je mu tambaye ta ko zata
yadda. A hanya suka
dinga haduwa da mata
wadanda mazansu suka rasu
suna ta tafiya gidan dagaci don
karbar wannan tallafi
mai tsoka. Kowacce taga su
Hannah sai ta ce “Au,
baza ku taho fada ku karbi
wannan tallafi ba daga Nigeria
fa baki suka zo. Indo ta ce
“Gaskiya Hannah in baza ki ba ni
zanje saboda idan muka
kuskura muka je gida
Inna Haule baza ta barmu ba,
amma idan mun riga
munje mun karbo babu
yadda zata yi damu fada ne dai
da zagi ya zama jiki. Hannah ta
ce “To mu shiga
gidan Adama mu ajiye ruwan
muje din daman gudun
fadan Inna nake, to ko babu
abunda muka yi ma kulllum
zagin mu take muje kawai. Suka
shiga gidan Adama suka ajiye
ruwan da ya ke kansu suka nufi
fada
wajen taron. Mata ne makil akan
layi suma su Hannah
suka je karshen suka tsaya.
Wata kyakkyawar mata ce a
zaune a kan kujera da
tebur a gabanta an dora wasu
files a kan teburin.
Kallo daya zaka yiwa matar
kasan tana cikin daula fatar
jikinta mulmul-sumul. Duk da
matar ba fara bace amma ba
baka bace kalarta mai kyau ne
kayan jikinta
kuwa ko ba’a fada maka ba
leshin zai doshi dubu hamsin
sarkar gwal da dan kunnenta da
zubbunan
gwal reras a hannunta wasu
manyan warwarayen
gwal ne a hannunta guda hudu
sai sheki suke yi. Matar mai
fara’a gata bata kyamar
talakawa sai gaggaisawa
dasu take suna yin hannu. Ta ce
kowacce tazo gabanta
ta rubuta sunanta don asan
yawansu kuma nawa ya
cancanta a basu. Kowacce tahau
zare ido saboda basu iya rubutu
ba cikar wajen da batsewarsa
aka rasa
wacce ta iya rubuta sunanta.
Matar ta ce “Yanzu duk
cikinku babu wacce ta iya
rubutu ta zo ta taimaka min
mu rubuta sunayenku? Hannah
tayi shiru kamar ta ce ta iya
amma gudun surutun *yan gari
nan kar a ce ta cika nuna iyawa
sai tayi shiru. Indo ta zungureta
ta ce
“Hannah bakin iya rubutu ba ki
rubuta mana.
Hannah ta ce “A’a Indo babu
ruwana a samu wani yazo
yayi dan kar ace nazo garinku
na zake. Matar ta sake cewa “To
tunda babu wacce ta iya rubutu
ina ganin ba zaiyu mu aiwatar
da aikin da zamu aiwatar ba a
yau sai
mun nemo wacce ta iya rubutu
sannan saboda da mata zalla
muke so mu kafa kungiyar, dole
mace ce zata zo
ta rubuta mana sunayen. Indo
da taga kiri-kiri zasu rasa kyautar
bata san sanda ta ce “A’a ranki
ya dade ga Hannah ta iya rubutu
 Saura suka hau cewa
“Hannah
taimaka mana ke kuwa ashe
daman kin iya rubutu, rubuta
mana kar mu rasa. Matar ta ce
“Wace ce Hannah?
Ta fito tazo nan. Hannah taje
gaban teburin matar ta
tsaya ta ce “Gani ranki ya dade.
Matar ta kalli Hannah
sama da kasa wata burgujejiyar
doguwar rigace wacce
aka dinkata da wani wagambari
mai kauri irin na da dinnan
itama kanwar kakarta ce ta bata,
gashinta a tufke a tsakiyar kai
tayi gammo dashi da zasu
debo ruwa, sai wani yalallen
gyale baki ta yana a kanta da
takalminta dan madina a
kafarta. Matar tayi murmushi
ta ce “Yaya sunanki? Hannah ta
ce “Suna na Hannah Abubakar
Imam. Matar ta ce “Hannah
Abubakar kin iya rubutu?
Hannah ta ce “Na iya ranki ya
dade.
Matar ta ce “Ko da yake ku anan
Franch kuke yi ba turanci
ba ko irin na *yan Nigeria?
Hannah ta ce “Ni nafi iya
turancin
Nigeria, french din kadan-kadan
na iya mijina yana koya min.
Matar ta ce “To jawo kujera kizo
nan
kusa dani ki dinga rubuta
sunayensu, ki fara rubuta
sunan ki sannan ki rubuta
sunayen sauran. Hannah ta
zauna tana rubuta sunayen
matan nan daya bayan daya
suna tahowa a layi. Ta gama
rubuta sunayen sai
magaruba tayi sai aka tsayar da
shawarar sai gobe da safe
karfe tara na safe su kara
taruwa anan don a raba musu
tallafin suka nufi gidajensu.
Matar kuma gidan dagaci
aka kaita a can zata kwana, na
mijin kuma da suka zo
shima aka kaishi wani gida aka
sauke shi tunda dare yayi dole
su kwana. Kowacce ta tafi gida
tana
murna tana dokin gobe tayi su
koma fada. Hannah da Indo
kuwa sai suka hau faduwar
gaba suna shirya kalmar da
zasu furta wajen kare kansu
daga fadan Inna Haule. Ai kuwa
daga shigarsu gida ta fara yi
musu fada don labari ya kai
mata cewar anga su Hannah a
fada sunje karbar jari. Tana
cewa “Dole Hannah ki barmin
gidana saboda so kike ki
koyawa Indo qinji da fitina
wanda da bata iya ba, ki tafi can
gidan ku acan ake yunwa
ake neman jari mu nan Allah Ya
rufa mana asiri. Kema
Indo tunda wanda ya dau
nauyinki ke da *ya*yanki ya
rasu Bello ne daman ya ce shi
zai dinga ciyar da ku gashi ya
mutu dole kema asan yadda
za’ayi idan bangaren
gadonku zaku siyarmin to, idan
ma wani zaku siyarwa dai duk
daya ki karbi kudinki keda
*ya*yanki ku koma can Tawa
local Government garinku. Ba
zaku zo
ban haifeku ba ku samun
hawan jini tunda kun hallaka
mazan naku ni dai ku kyale ni.
Washe gari da sassafe su
Hannah suka tashi suka hau
ayyukan gidan, bayan sun gama
suka leka ko ina
basu ga Inna Haule ba ta shiga
makwabta sai suka debi
bokitansu suka cewa Masa’ud
dan gidan Indo in Inna tazo ya
ce mata sun tafi rafi debo ruwa.
Atamfa
mai kyau Hannah ta daura basu
tsaya a ko ina ba sai
a fada wajen taro, sunma dan
makara don yanzu tara da
rabi tayi suka ajiye bokitansu a
lungu suka je taron.
Matar ta kalli Hannah tayi
murmushi ta ce “Hannah ke
muke jira ki fara kiran sunaye in
rarraba muku kudin.
Hannah ta gaisheta faram-faram
da fara’a sannan ta karbi
takardar ta fara kiran sunanta ce
“Hannah Abukar Imam
ce ta farko, matar ta ce “To ki
kira sunayen daya bayan
daya suzo su bi layi sai kawai in
dinga mimmika musu
kudin a layi Hannah ta fara kiran
sunayen, kowacce
tana zuwa tana shiga layi kamar
yadda sunayen
suke a jikin takardar. Bayan
Hannah ta kammala kiran
sunayen sai matar ta mike ta ce
“To madallah Assalamu Alaikum
jama’a. Su duka suka ce
Wa’alaikumussal am. Ta ce
“Ni sunana Haj. Hindatu Umar
daga Kano state Nigeria.
Nazo nan garin mai suna Dashi
karkashin karamar hukumar
Magarya a Janhuriyar Niger ne don
in kawo wa *yan uwana mata
tallafi da taimako yadda matan
da suke da maza su ke samun
taimako daga wajen
mazajensu to ku da baku da
maza sai ku samu sana’ar da
zaku taimakawa kanku da
marayun *ya*yanku.
Suka sa tafi raf-raf suna cewa
“Allah Ya saka da alheri
mun gode Hajiya Hindatu. Ta ci
gaba da cewa “Daga gwamnatin
Jihar Kano, matar maigirma
gwamnan jihar
Kano ta bude wata kungiya
wacce za’a dinga taimakawa
mata da mazansu suka rasu
suka
barsu, shine taga ya dace mu
shigo makwabciyar kasarmu
Niger suma mu hada kai da
gwiwa mu taimaka musu
saboda abunda yayi Nigeria shi
yayi Niger duk Uwa daya Uba
daya muke. Tafi suka hau yi
suna murna suna cewa “Allah Ya
kiyaye Nigera da gwamnatin
Jihar
Kano. Hajiya Hindatu Umar ta ci
gaba da cewa “Yanzu
anan garin zamu kirkiro wani
suna mu saka wa wannan
kungiya tamu don muci gaba da
turo muku da
tallafi ta ko ina daga kasarmu.
Bani zan bawa kungiyar
suna ba ku da kanku ya kamata
ku saka mata suna. Nan
dai wannan ta ce a sa mata kaza
waccan ta ce asa
mata kaza, daga karshe sai dai
aka tsayar da shawara
akan a sawa kungiyar suna
Hindatu Umar. Tayi dariya ta
ce “A’a ba suna na za’a sa ba
saboda watakila ba
zaku sake gani na ba sai dai
kuga an turo muku wata
saboda muma can *yan
kungiyar muna da yawa. Idan
aka
turo ni yau gobe wata za’a turo
muku. Amma yanzu
tunda ga wacce ta iya rubutu da
karatu Hannah ita zata
dinga wakiltarku idan ta kama
ma har can Nigeria zata
dinga zuwa tana karbo muku
tallafi ina ganin idan kun amince
asawa kungiyar sunan Hannah.
Gaba daya
suka hau cewa mun amince asa
sunan Hannah.
Daga karshe matar ta jawo wata
jaka ta fara mika musu damin
kudi kowacce kudin data samu
idan
aka kiyasta da kudin Nigeria zai
kai kimanin dubu sha biyar-
biyar. Bayan kowacce ta karba
ta ce ba’a
kare ba.
Akwai atamfofi da wasu kudade
da za’a sake basu shima daga
gwamnatin Nigeria sai dai basu
zo da kudin yanzu ba amma
idan zaiyu su nada wata daga
cikinsu da zata je ta wakilce su
don taga waje taci gaba
da zuwa tana karbar musu
lokaci-lokaci. Murna ta kama su
sai suka hada baki suna cewa
“Mun
wakilta Hannah a matsayin
wakiliyarmu. Hajiya Hindatu ta
juya ta kalli Hannah ta ce “Kin
amince Hannah za ki bini
Nigeria ki dinga karbo musu
taimako? Hannah
tayi murmushi ta ce “Hajiya me
zai hana sai in biki din, akan
haka suka yi sallama cewar
Hannah zata bi
Hajiya Hindatu Kano don karbo
musu wasu tallafi masu
yawa,
kafin Hannah tabi matar sai da
taje da sauri gidan Kawu Ahmad
ta shaida masa duk shawarar da
suka
yanke akanta ya amince ya
kuma yi mata fatan Allah Yasa su
dauketa aiki acan tayi ya ce, idan
da
sarari taje makarantarsu ta
karbo sakamakon jarabawarta
ta nemi aiki ko Allah Yasa ta
dace. Ta raba kudinta gida biyu
ta bashi rabi. Ta sake raba nata
gida biyu ta
bawa matarsa Hajir, ko gidan
Inna Haule bata je
dauko kayanta ba, kawai ta fada
motar su Hajiya Hindatu
Umar sai tafiya daman Hajiya
Hindatu tayi sallama da
dagaci da sauran hakiman garin
ta basu kaudi masu yawa
suma ta sanar musu zata tafi da
Hannah donta sake
karbo musu wasu kudaden
taimako. Sunyi murna
sosai sun shi albarka sunyi
musu fatan Allah Ya kiyaye
hanya. Mutumin da suka zo
dashi mai suna Shehu shine
yake tuka motar. Hajiya Hindatu
a baya ta zauna Hannah ce ta
zauna a gidan gaba, motar kirar
Hummer Jeef dindimemiya mota
mai dauke da rundimemiyar
rikoder an saka sauti mai tashi a
hankali sai sanyayyiyar na’aurar
sanyi ce ke dukan jikin Hannah.
Cikin motar ma abun kallo ne
lausasan kujerun
motar su suka sa Hannah ta
nutsu ko magana bata
iyayi. Ta ce a ranta “Allah Ya
baku duniya wannan mota ce
kawai ba gida ba. Allah mai
azurta wanda Ya so. Sun hau titi
dodar suna zuba gudu a titi sai
hanya.
kafin karfe uku ma a cikin garin
Kano tayi musu tafiya
suke kamar bayi suke yi ba
saboda babu wata kura ko
gajiya irin ta matafiya a tare da
su. Hannah sai kallon
Kano takeyi galala komai yaci
gaba ba kamar lokacin
data zo ba. Babu abunda ya
fado mata a rai sai ranar
da ta zo wajen Haisam zuwanta
Kano na farko kenan
kuma bata taba saka ran sake
dawowa ba ashe zata
dawo yanzu Allah Ya kawo dalili.
Ta dinga kallon hanyoyi ko
zata gane gidan su Haisam
amma ina ba tama gane
Hanyar ba balle ta gane gidan.
Haisam, Haisam take ta kira a
zuciyarta yayin da kwalla ta cika
mata idanuwanta Ta mudubi
Hajiya Hindatu take
kallonta ta ce “Hannah yaya dai
naga kamar kwalla ta cika
miki ido ko iskar A.C ce tayi miki
yawa a ido a rage? Hannah
ta ce “A’a babu komai suka ci
gaba da tafiya can Hajiya
Hindatu ta ce “Hannah ga
garinmu fa, Kano kenan TA
DABO TUNBIN GIWA kin taba
zuwa Kano ne tunda naga
kamar a Nigeria kika yi karatu?
Hannah ta ce “Nan F.G.G.C Kazaure nayi na taba
zuwa Kano amma
sau daya shekaru biyu da suka
wuce amma bazan iya tuna
ina ne unguwar dana zo ba,
Sulemanu cresent
sunan unguwar. Hajiya Hindatu
ta ce “Oh Sulaiman cresent
sunan unguwar ai bamu da nisa
sosai yanzu muna Ahamadu
Bello way zamu bi ta wajejen
dai, ni a
Sokoto road farm center nake
zan nuna miki kwanar.
Hannah ta ce “To suka ci gaba
da tafiya.
Dai dai get din wani
tsantsareren katafaren gida
motar su Hannah ta tsaya yayin
da mai gadin ya taso da
sauri ya bude musu. Hajiya
Hindatu ta kalli Hannah ta
ce “Hannah nan gidana ne ina
so muyi sallah muci abinci
mu huta wajen gobe sai in kaiki
wajen kungiyar su baki tallafi a
kaiki can garin naku ko?
Hannah ta ce “Babu komai na
gode. Hannah taga duniya
wannan gida shine
ake kira aljannar duniya saboda
kana shiga farfajiyar
gidan wasu fulawoyi ne an
zagaye wani dan tudu yana
bul bulo da ruwa sanyi garai. Ga
lilo irin na hutawar nan da ake
saka shi a gidan attajiran gaske.
Wasu
Dawisu ne da talo-talo da
tsuntsaye masu kyawu
aka watsa a farfajiyar gidan
suna ta yawo can gefe kuma
wajen wanka ne (Swimming
pool) an kewaye da wasu
kujerun hutawa can gefe kuma
wajen wasannin
yara ne na motsa jiki (games)
wajen basket ball, table tennis,
foot ball da dai sauransu. Sai
kuma ga wata tafkekiyar kofa
wacce zaya kaika cikin gidan.
Daga
can baya kuma boy’s quater ce
itama kamar wani katafaren
gida. Arziki ma anan ai ba’a
magana kai kace a turai kake ba
a Nigeria ba. Hajiya Hindatu
ta yunkura zata fita daga cikin
mota ta juya ta kalli
Hannah wacce ke zaune tayi
turus ta ce “Hannah fito
mana. Hannah taja kofar zata
bude ta kasa sai da Hajiya
Hindatu ta fito daga kujerar
baya ta bude
mata ta waje, sannan Hannah ta
fito. Gidan ya bawa Hannah
sha’awa kwarai da gaske. Ta ce
“Hajiya gidanki yayi min kyau
wallahi. Ta kalli Hannah tayi
murmushi ta ce “Na gode
Hannah.
Wani dogon saurayi ne
kyakkyawa a gefe a zaune akan
wata kujerar roba yayi tagumi
ya rike kai. Hajiya Hindatu taje ta
same shi tana zolayarsa ta ce
“Mijin me akayi maka yau? Kana
gani na ko ka dago kayimin
magana ko budurwarce ta bata
maka rai? Daga nan Hannah ta
tantance kanin mijinta ne wasan
kanin miji take yi masa. Ya dago
a sanyaye ba fara’a dakyar
ya kalleta ya ce “Auntyna muje
daga ciki muyi magana.
Hajiya Hindatu ta kyalkyale da
dariya ta ce “Kai dalla
rago nasan fada kuka yi kai da
Ummi duk yadda aka yi.
Ya ce “Wannan mai sauki ne
muje ciki dai. Ya juya ya kalli
Hannah ya ce “Aunty wace ce
wannan? Ta ce “*yar Niger ce,
ya ce “Niger? Daman Niger kika
je yau
kwana bakwai bakya nan? Ta ce
“Eh muje ciki dai,
Hannah zo mu shigo ciki. Suka
isa wani tafkeken falo wanda
zan
iya kiransa da aljannar Duniya,
nan Hajiya Hindatu ta ajiye
jakarta akan kujera ta
kishingida don gajiya. Ta ce
Hannah zo ki zauna bakuwa
kema kin gaji. Hannah
tayi murmushi dukka sassan
jikinta ya dau sanyin na’ura, a
fakaice kallon alatun da suke
jifge a falon
take, tana tambayar zuciyarta
abin da bata sani ba bata taba
gani ba. Saurayin yaje wajen
wata
telephone da take sakale a jikin
bango ya dauka yana latsa
wasu lambobi can da aka jima
ya ce “Hello Hajiya ga
Aunty ta dawo ashe wai Niger
taje. Hajiya Hindatu ta tashi
zaune ta ce “Lah Hajiya kake
gayawa ashe Niger naje,
daman haka kake kai in angaya
maka magana sai ka fada? Ya zo
a sanyaye ya zauna akan kujera
ya ce
“Aunty dole fa Hajiya tasan kin
dawo kuma ina kika je tunda
neman ki ake yi tuntuni. Hajiya
Hindatu ta ce “Hajiyar a asibiti
take ko kuma a ofis? Yaya mai
jikin ina ta tambayarka baka
bani amsa ba? Ya ce “Yana can
yaji sauqi. Ta ce bari inje inyi
Sallah in je in duboshi,
har yanzu basu sallame shi ba?
Yana premier hospital
ko Aminu Kano aka mayar
dashi? Ya ce “Yana can dai.
Ta ce “Wai meke damunka ne
duk da kyar kake magana na
lura? Hannah ta ce “Wani ne
bashi da
lafiya? Allah Ya sawake. Hajiya
Hindatu ta ce “Wallahi
mai gidana ne bashi da lafiya
yana asibiti. Hannah ta girgiza
kai ta ce “Kai kai Allah Ya sawake
masa,
ciwon ya tsananta ne haka har
da kwanciya a asibiti me
ya same shi? Ta ce “Ciwon
zuciya yake ta fama dashi wallah
Hannah. Hannah ta ce “Zuciya? Allah Ya bashi lafiya.
Hajiya Hindatu ta ce “Amin,
shigo ga
bandaki muyi sallah ko azahar
bamu yi ba gashi uku da
rabi yanzu la’asar ta kusa.
Hannah na biye da ita har wani
katafaren daki mai dauke da
wani kayataccen
gado a ciki dakin, kuma da wani
kayataccen bandaki.
Hajiya Hindatu ta ce Hannah ta
shiga bandaki tayi alwala idan ta
fito sai ta shiga. Hannah ta shiga
bandaki sai da tasha kallo ta gaji
sannan tayi alwala ta
fito. Hajiya Hindatu ma ta shiga
ta dauro alwala. Suna idar da
sallar azahar sai kawai suka yi
la’asar don lokaci yayi. Hannah
na tahiyar karshe Hajiya Hindatu
ta
idar tana jan carbi suka juyo ana
rafsa kuka kamar na mutuwa a
babban falo a guje Hajiya
Hindatu ta tafi
Hannah kuma ta hau sauri tana
so ta idar taje itama taga meke
faruwa Hannah taji ihun ya kara
karuwa da Hajiya Hindatu ta fita
kuka wiwi suke yi. Hannah
ta fita da sauri ta iske mata
makil a falo ana ta kuka.
Hannah tayi kasake tana
kallonsu bata san me ya faru ba
balle tasan me zata ce musu.
Hajiya Hindatu ce ta taso
tazo ta kama hannun Hannah ta
kawo tsakiyar matan
nan wadanda suka doshi su
ashirin. Hannah ta durkusa
akan kafet ta gaishe su wata
kamilalliyar Dattijuwa
mai kyau ta dago luhu-luhun
idanuwanta ta dubi
Hannah ta juya ta kalli Hajiya
Hindatu ta ce “Ramlah wacece
wannan? Ta ce “Wannan ita ce
Hannar Haisam. Su duka suka
bude baki suka ce “Hannah,
Hannah ce
wannan ina kika nemota? Ta
rushe da kuka ta ce “Har Niger
naje na nemota. Sai gaba daya
aka rushe da kuka. Hannah ta
kasa gane abunda ake nufi,
kanta ya daure abun ya bata
mamaki. Ta ce “Meke faruwa, a
ina nake anan? Haj. Hindatu ta
goge hawaye ta ce
“Hannah nan Kano ne, ta nuna
wannan dattijuwar matar ta ce
“Wannan ita ce Mahaifiyar
Haisam. Hannah cikin mamaki ta
ce “Mahaifiyar Haisam! Haisam!!
Haisam!!! Hajiya Hindatu ta ce
“Haisam, ta nuna wannan
saurayin ta ce “Wannan shine Izzuddin
kanin Haisam ne, ni kuma ba
sunana Haj. Hindatu ba, sunana
Ramlah ni ce matar Haisam.
Hannah ta zabura ta
mike tsaye ta ce “Ramlah, meke
faruwa, me nayi miki?
Ramlah ta jawo hannun Hannah
ta zaunar da ita ta ce “Zauna
Hannah zan baki labarin Haisam
yanzun
nan.
Hannah ta koma ta zauna a
sanyaye ta tattara hankalinta
baki daya tana sauraron Ramlah.
.
Kukan da nake yasa nakasa
karisawa sai kuma Gobe in Allah
ya kai mu……….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *