Gangar jikinsa na aura37

Hausa novels
GANGAR JIKINSA NA AURA

Chapter37

Hannah taji dadi ta gama jarabawa a lokacin da ake tafiya aikin Hajji don haka ta shaidawa Haisam tana so taje Makka ita da Uwar biyu da Iya Salmai suje su hadu da Mahaifinta suyi Hajji gaba daya don ta taimaka masa kada yasha wuya. Haisam ya amsa mata da cewa babu komai zaiyi kokari yasa a nemo musu biza su dukka gidan ma sai su tafi, har shi da Ramlah da *yarta Hannah, da Wada da matarsa da gaba daya *yan aikin gidan mata da maza. Haka kuwa akayi, suka dunguma suka dira a kasa mai tsarki kwatsam Malam Habu ya gansu nanfa murna ta hargitse. Kamar yadda su Hannah suka yi aikin Hajji a waccan shekarar cikin sauki haka wannan shekarar ma, mota katuwa da direba aka aikowa Haisam daga gidan ambassador. Bayan an sauko daga arfa lafiya, sai suka dinga shiga kasuwanni ana ta siyayyar tsaraba. Makudan kudin da Haisam ya rarrabawa dukkanninsu kowa ya yiwa *yan Uwansa tsaraba. Kowa yaji dadin tafiyar nan sosai da sosai. Haisam da Hannah da Ramlah ne suka shigo bangaren Malam Habu dan su gaishe shi da sassafe. Suna zaune suna *yar hira saiga Uwar biyu da Iya Salmai suma daga dakinsu sun shigo don su gaishe da Alhaji Habu aka hadu ana ta hira wasa da dariya.
Hannah ta ce “Baba da kai zamu tafi fa tunda yanzu kayi umara sau da yawa ka yi aikin Hajji sai mu koma gida. Alh. Habu ya girgiza kai ya ce “*yar Baba ki barni kawai inyi zamana daman ku kadai nake da su a Nigeria kuma gaku nan akai-aikai kuna zuwa gara inyi zamana inci gaba da ibadata har lokacin mutuwa in mutu anan. Hannah ta ce “Haba Baba kaso ka mutu babu aure bayan ga masoyiyarka tana nan tana jiranka ka dawo ka aureta. Alh Habu ya ce da Hannah “Ke *yar Baba bana son shakiyanci wacce irin masoyiyata, wacece masoyiyata kuma? Gaba daya aka sa dariya. Hannah ta ce “Baba har zaka manta tsohuwar matarka *yar Uwarka, jininka Iya Salma a tuna baya mana Baba a koma ayi aure. Haisam ya ce “Baba Hannah dai nason ayi tuwona mai na ga Uwa ga Uba, Baba a duba wannan al’amarin. Malam Habu yayi murmushi ya ce “Kaima tayata kake? Kyale *yar Baba tsokanarmu take yi Salma dince ta ce mata tana so tayi aure? Iya Salma sai yanzu tasa baki da murmushi kawai take yi ta ce “Da dai na gama aure tin daga kanka amma yanzu da yake kaine ai bana ce a’a ba. Soyayya ai bata tsufa. Hannah ta rangada buda ta ce “Ai an gama daurin aure sadaki kawai zan dauko in biya, da Riyad ma zan biya kudin Makka, Uwar Biyu tayi dariya ta ce “Lallai wannan aure naku Alhazawa ne don a Makka aka kullo shi, Allah Ya sanya alheri Ya ba da zaman lafiya. Hannah ta ce “Iya Uwar biyu ko kema in tuno miki baya ne? Ta ce “Ban gane ba? Hannah ta ce “Ko kema zaki zama amaryar Iyata Salma ne ku zama ku biyu a daura dukka rana daya tunda gidanku daya tuwona maina kenan. Gaba daya aka kece da dariya. Haisam ya ce “Lallai har kin yiwa Iya Salma kishiya tun kafin ta tare. Hannah ta ce “Ai itama tsohuwar soyayya ce tun a lokacin da take kaini gida daga makaranta ta fadamun, ai shima Baban ya sani, sun so su daidaita ya ce mata masifar Iya Abu ce kawai zata hana ya aureta. Iya Salma tayi caraf ta ce “Ni da za’ayi haka ma da nayi murna saboda ni a rayuwata ina son kishiya, bana kyamar kishiya ko Abu aini nasa dole ya aurota. Hannah ta dauko turare tana ta fesa musu su dukka ukun wai amare da angonsu. Wannan abu ya yiwa kowa dadi ba kamar Hannah. Ramalah da Haisam sunsha dariya har sun godewa Allah. Yanzu Malam Habu ya yarda zai biyo su su dawo Nigeria. Haisam ya shaida masa an nadashi a matsayin Limamin Masallacin da Hannah ta gina daman sunansa aka sawa Islamiyyar ABUBAKAR IMAM ISLAMIYYA.
Su dungumo gaba daya sun dawo Nigeria su na dawowa da sati biyu bayan Uwar biyu ta je Kazaure ta shaidawa *yan Uwanta ta dawo daga Makka ta raba musu tsaraba saita shaida musu wannan abun mamaki abun murna cewar zata auri Malam Habu Baban Hanna. Don haka ranar juma’a *yan Uwan Uwar biyu waliyanta suka zo aka hadu da Haisam da *yan aikin gidan suka taru aka daura auren Iya Salma da Malam Habu bayan an shafa aka daura na Uwar biyu da Malam Habu. Wannan abu yayi kyau aka raba goro da alewa aka watse. Daya dakin na kulle aka budewa ango Habu ya shiga ga na amarensa a gefe. Ko kofar gida Malam Habu bai cika fita ba, yana gida yana shan A.C yaci kaji yasha juice da abinci kala-kala. Idan lokacin Sallah yayi yayi taku kadan zuwa Masallaci ya shiga yaja jama’a Sallah da daddare kuma ya koyawa maza magidanta karatun alkur’ani mai girma Malam Habu yayi shar da shi ya girgije duk tsufan ya ragu daman ashe wahala tafi tsufan yawa. Haka Uwar biyu da Iya Salmai sunyi shar kamar ba sune wadannan tsofaffin ba, kayansu kullum iri daya Hannah take dinko musu.
Makarantar Islamiyya a hankali a hankali ta cika makil da dalibai yara da manya. Kullum da yamma yara ne suke zuwa, a ranar asabar da lahadi kuwa manyan matan aure suke zuwa da safe goma zuwa sha biyu. Manyan Malamai masana Alkur’ani da Hadisai, kawa’idi, fikhu da dai sauransu daban-daban su suke koyarwa a makarantar. Ramlah da Hannah suma sun shiga makarantar. Iya Salmai da Uwar Biyu ma ba’a barsu a baya ba sun tashi haikan neman ilimi dan da basu iya komai ba yanzu kuwa gashi komai dalla-dalla suna koya. Matasan *yan mata ne suke ta tururuwar zuwa wajen Ramlah akan matsalolin da suka dame su akan soyayya. Ramlah na kokarin warware musu ta hanyar basu shawara, wata tambayar idan suka yi mata sai ta hada su da Hannah tana ganin Hannah zata fita sanin amsar saboda ta taba crossing irin wannan rayuwar so zata fita sanin amsar. Wani lokaci har Haisam yakan taimakawa Ramlah wajen amsa wasu tambayoyin. Aji na musamman Ramlah da Hannah suka ware a makarantar Islamiyya lokacin da babu Makaranta suna zama da matasa suna wayar musu da kai akan mecece soyayya. Duk sanda Ramlah take gudanar da shirinta Hannah ce ta farko da take fara bugo waya ta bada tata gudunmawar, Ramlah tana jin dadin haka, ita kuma alkawarine kullum a gidan radio kafin ta fara gudanar da shirinta sai ta ce fatan alheri ga Haisam da Hannah.
Wata rana Hannah ta sako kai zuwa cikin gidan Iyayenta ta iske Wada yana yiwa tsofaffi nan tsiya yana cewa “Wai ku yanzu bakwa iya cin abinci sai kuna korawa da juice, katan daya baya yi muku sati guda, ba’afi kwana biyar ba na kawo muku wancan kwalin har ya kare, musamman Iya Salma ana dauke wuta kafin a tashi inji sai kaji tana Subhanallahi bana son duhu wallahi a rayuwata, ko da a Babban-mutum ya kike yi ke da ko wuta baki ja a gidanki ba. Iya Uwar biyu kuwa ita dai a kunna mata sattilite tana kallo tana tsalle akan kujera tana dariya, su Baba Habu kuwa shi dai asha A.C a figi naman kaza.
Hannah ta talli keyar Wada, ya zabura ya juya da sauri. Sai yaga Hannah. Iya Salmai ta ce “Gara da Allah Ya kawo ki gashi nan ya zamar damu kamar kakkanninsa wai tsiya yake yi mana. Hannah ta ce “Wada bana son irin haka meye don sun shanye katan din juice a sati, daga yau katan goma zaka dinga dauko musu daga kanti yana karewa ka dauko musu katan gomar. Kake yi musu tsiya ina kai nan matarka ta ce ka kunna mata A.C har riga ka cire ka jawo kujera ka hau ka ballo murfin A.C zaka girgideta Allah Ya kawo ni gidan na nuna maka inda zaka matsa remote ka kunna. Wai kai a dole ka nunawa amaryarka kai dan birni ne zaka burgeta. To gaskiya karka kara yiwa Iyayena haka wallahi ko kayan kantin dukka suke so zansa a kwaso musu don wa nake sana’ar? Dadi ya kashe tsofaffin nan suka hau shiwa Hannah Albarka.
Allah Ya albarkaci sana’ar Hannah a shekara ta sake bude wata Super market din a Zoo road komai Hannah ta sawa hannu na kasuwanci sai kaga kamar farashi yana ta hauhawa riba tsibubu Allah Ya dubi zuciyar Hannah Yana ta buda mata ita kuwa bata gajiya da bayarwa ga Iyayenta da *yan Uwanta talakawa na Niger dana Babban-mutum da duk al’Ummar Annabi da suke neman taimako.
 Yara da dama Hannah ta dauki nauyin karatun su, da yawa ta dau nauyin yi musu aure da yawa ta biya musu Makka. Wata rana Haisam ya dawo daga wajen hidimominsa da yamma kai tsaye bangarensa ya nufa don ya watsa ruwa yaji sanyi a jikinsa kafin ya fito lambun da yake zama yayi hira da matansa kullum da yamma. Abun mamaki sai yake jiyo ana yin busa mai dadin gaske wacce ta yi masa kama da wata busa da yake matukar so a rayuwarsa. Yayi sauri ya bude labulan windon dakin sa ya leka sashan da busar ke tashi, sai ya hango Hannah zaune cikin lambun tana busa abin busarta. Cikin sauri ya fada ban daki ya watsa ruwa bayan ya shirya ya fito ya nufi cikin lambun inda Hannah take. Ya lallabo ta bayanta ba tare da ta sani ba, ya tsaya cak kusan minti goma yana sauraranta, ya kare mata kallo tsaf ya ga tayi dammara da mayafinta ya kalli kunnanta da wuyanta ya ga sanye da tsakiyoyin nan na ta. Ya zagayo ya durkusa a gabanta yana kallon dige-digen da tayi da kwallli a fuskarta, ta dube shi tayi murmushi ta sunkuyar da kai kasa. Haisam ya ce “Lallai yau kin tuna baya kuma kin soso min wani abu mai muhimmanci da yake cikin kundin tarihin rayuwata. Su duka suka yi dariya. Haisam ya mike tsaye ya jawo wata kujera ya zauna ya ce “Ci gaba da busarki kuma kiyi min wakar ina sauraranki. Hannah ta mike tsaye ta kara tsuke danmararta ta kugu sannan ta koma ta zauna, su duka suka kwashe da dariya. Ta kaikaice ta fara busa tana rero wakar kiwo kamar yadda take yi masa da. Haisam yayi shiru yana kallonta yayin da zuciyarsa ta harba can ta tuno masa baya wato ranar da aka fara kawo Hannah makaranta, da bayan rabuwarsu da ita, da halin da ya shiga bayan rabuwarsu da irin busar da yake yi idan tunaninta yayi masa yawa. Bai ankara ba sai ya ga Hannah tana hawaye itama babu abin da take tunawa sai lokacin da Malam Sule ya bata wannan abun busar da kuma lokacin da Haisam yake sa ta tayi masa busa. Hannah ta kifa kai akan cinyarsa ta saka kuka, ya mike tsaye ya jawota jikinsa ya rungumeta sai shima kwalla ta fara zubowa daga idanuwansa. Ya laluba damarar da tayi a kugunta ya ce “Hannah meye wannan nake ji a kugunki kamar miciji? Ta ce “Ba miciji bane mayafina ne. Suka kwashe da dariya, Haisam ya sa hannu a aljihunsa ya ciro wani abu a daure a bakar leda ya mikawa Hannah, ta karba cikin sauri ta kwance ta duba, sai taga wata *yar karamar rigar nono mai kyau. Ta dubi Haisam alamar bata gane ba. Ta ce “Wannan fa? Ya ce “Kara kallonta dai sosai ki tuna baya. Hannah tayi shiru tana tunani, sai Haisam ya ce “Tuno ke da Nusaiba da Rauda a wajan mai kanti a makaranta? Ta ce “Laa shine ka ke ajiye da ita har yanzu. Haisam ya ce “Ai duk wani abu da ya shafeki Hannah bana mantawa dashi saboda muhimmancinki a rayuwata. Sai ta rungume shi suka koma suka zauna, suka ci gaba da busa abin busar tare.
Kwanci tashi Hannah tayi nisa a karatun likita “Medicin” sun gama shekaru uku a BUK an turasu teachin hospital na Aminu Kano don yin cilinicals. Sai yanzu Hannah ta sami ciki, wai zo kuga tarairaya da murna wajen Baba Haisam. Duk mutuncin Nusaiba da yake gani fur ya hana Hannah taje ta raka ta hada-hadar kanfen din zabe, suna so su zarce takarar gwamnan. Ya ce shi dai sai inda karfinsa ya kare amma Hannah ba zai barta ba saboda dan cikin zai wahala da ita kanta. Zabe ya doso Haisam yayi kokarinsa wajen taya mai girma gwamna yakin neman zabe. Kasancewar Haisam shine Kano, yasan *yan Kano, yana son Kanawa, Kanawa suna sonsa shi da Hannah da Ramlah saboda rin gudunmawar da suke bawa Kanawa, Kanawa sun amsa kiran Haisam sun sake zabar mijin Nusaiba a matsayin gwamnan Kano karo na biyu. Mai girma gwamnan da kansa ya jinjinawa Haisam ya kuma kuduri niyyar sai ya linkawa Haisam tara ta arziki, fiye da yadda Haiam yayi masa. Haka kuwa akayi sai dai kwangila mai tsoka bata taso ba amma Haisam yake bawa ta daruruwan miliyoyi kuma a biyashi da zarar ya gama. Haisam Kano kenan, arziki ya dada bunkasa yanzu Haisam yaso ya fi Mahaifinsa kudi dan yafi Yayansa Habib kudi shine ma yake basu kudi.
Hannah ta haifi santalelen danta kyakkyawa mai kama da Babansa amma ya dauko farar fatar Uwarsa, Hanna ta ce a sa masa sunan Babanta Abubakar ana kiransa da Walid. Bayan haihuwar Walid da wata uku Ramlah ta haifi da namiji shima mai kama da Babansa aka saka masa sunan Mahaifinta Shitu ake kiransa Khalil.
Hannah ta tashi tukuru tana ta karatu bata da matsala wajen rainon Walid tunda ga Iya Salma nan da Iya Uwar biyu suna rike mata shi, nono ne kawai take zagayowa ta bashi ta koma karatu har ya isa yaye ta yaye shi.
Tafi tafiya Hannah ta gama karatun likita da bautar kasa. Ta sake haifar *yan biyu mace da namiji masu kama da Hannah sak, Hannah ta roki Haisam da asa musu sunan Haisam da Ramlah da gudu ya amincewa bukatarta. Hai Ram Hannah kenan. Tubar kallah alhamdulillahi. Iyali sun hadu gida yayi albarka *yan dugul dugul yara zaka iske a farfajiyar gidan suna ta guje-gujensu Haisam na tsakiyarsu yana tayasu ball. Dr. Hannah Haisam Abubakar ta cika burinta ta zama cikakkiyar likita ta sami damar ta taimakawa al’umma ta fara aiki a Aminu Kano sai taga gara ta koma karatu ta karanto bangaren mata wato (gaenea)A.B.U Zaria tayi karatun shekara hudu a inda ta zama consultant gyanea doctor. Abunda Haisam ya fara yi shine ya bude mata asibiti nasu na kansu. Dr. Hannah da wasu likitocin su suke kula da marasa lafiya a asibitin.

Hmmmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *