GIDAN AURE CHAPTER 5 ZAHRATEEY
Gidan Ahmad*
+
Lamarin rayuwa yana tafiya yadda ubangiji ya tsara da dadi da ba dadi, wasu suna hakuri wasu suna butulci ga ubangiji wasu basa duba na kasa dasu kullun sena sama dasu ta yadda ba zasu ta6a godewa Allah ba. Ina ta fama da laulayi me wuyar sha’ani ga shi uban gayyar ya koma bakin aiki, sai da nayi sati uku a Kano saboda jikina ba dadi sannan na dawo Kaduna, har yau na kasa fita aiki dan ba wani karfi bane dani, ko da na fada wa me gadi ina dauke da ciki be damu ba a cewarsa hakanne zai bashi damar mallakata ni kuma a nawa 6angaren hakan be min ba domin ba zan iya auransa ba saboda ba lailai a samu yarda a tsakanin mu ba dole zaa samu zargi.
Gidan su Ahmad sunyi matukar farin ciki da wannan cikin daya bayyana a jikina, shima Ahmad a wannan karon so da kauna ya daurawa cikin jikina a zuciyata nake cewa rashin sani yafi dare duhu domin da ya san ko cikin waye da be daura mishi so da kauna haka ba. Tabbas ya makaro lokacin da naso in samu cikin nashi ya kama ya rinka hadani da maganin hana daukan ciki a yanzu kuma da cikin ya kasance na wani shine ya daura wa kansa son cikin.
Na so in sanar dashi gaskiyar lamarin amma na kasa nafi so koma meye sai na haihu kafin ayi shi, kuma na kudurta a raina na gama zama da Ahmad tunda har ya yi sanadin dana fara muamala da wani namiji da aurena har ya kai ga samun ciki.
_________________________
*Gidan Salmanu*
Cikin amincin Allah aka yi biki lafiya aka watse lafiya amarya ta tare a 6angaren da ango ya gina mata ta gefen Mama. Burin su Mama dai be cika ba saboda amarya macece me addini, girmama na gaba da sanin yakamata, sun so ace ta shiga gidan da rashin mutunci a Faiza sai kuma adduarsu be kar6u ba, domin zaman lafiya sukeyi da uwar gida wanda hakan ya sawa zuciyar mijinsu natsuwa.
Sati biyu kenan da tarewarta a gidan kuma komai na gidan tana fahimta dai dai gwargwado hatta yadda Mama ke muzgunawa Faiza. Duk wani rashin mutuncin da Mama keyi wa Faiza ta saka wa ranta cewa ba zata ta6a bari ta gwada yi mata ba ma’ana sawa zaman aurenta ido da hanata jin dadin zama da mijinta. Kamar kullun idan Salmanu ya dawo sai dai ya jefa kullin abin da ya kawo ta window to yau ta dauki aniyar lalata wannan doka dolene a kawo abu ta daki kuma babu wanda ya isa yasa musu ido.
Fitowa tayi a dai dai lokacin Mama na alwala ta fashe da kuka, cike da tashin hankali Mama ta nufe ta har zaninta na faduwa “yar arziki irin albarka waya ta6aki a cikin gidan nan da kike da gata gaba da baya?” Sake fashewa tayi da kuka kafin tace “shikenan idan mijina zai shigo min da abu sai dai ya jefa ta taga ba zai shigo ta kofa ya ajiye ba saboda baya son matarsa ta gani ta hana mu zaman lafiya” ta fada tana kara karfin kukanta, cike da rashin gaskiya da damuwa duk Mama ta duburce “kiyi hakuri kinyi yar nan, hakan ba zai sake faruwa ba, ina kake kai Salmanu? To daga yau kar a sake irin haka idan ka shigo mata da abu ka kai mata cikin daki meye na jefawa ta taga saboda tsoron matarka, kar inji kuma kar in sake gani, ya zaka rinka abu kamar 6arawo ko mara gaskiya, ka kiyaye nan gaba” Salmanu daya fito daga daki cike da jindadin maganin Mama da akayi a yau ya amsa da “to ba za’a sake ba”.
Mama na shiga ciki suka tafa da Faiza, shima Salmanu ya sauke ajiyar zuciya cike da farin cikin sauyin da suka samu albarkacin auren Dada, tabbas ta kasance alkairi a cikin rayuwarsu hakan ya kara mishi so da kaunarta domin tana kawo haske a zaman aurensu Faiza ma ta fara samun yancin kai.
_________________________
*Gidan Faruk*
Jiya wa yau lamarin gidan bata chanza zani ba, abin dai kullun sai karuwa yakeyi gidan ya zama kamar gidan haya Faruk ya biyewa amarya Wasila sun koma kamar kishiyoyi, ya fada ta fada harda zagin iyayensa duk ta nayi, lamarin ma ya sake lalacewa domin yaran shi sun dawo hutu gida sun iske abin da yake faruwa suma sun jone yau su shiga wa Anty Wasila gobe su shigawa Faruk abin dai da Nafi tayi gudu shine yake faruwa.
“Wace yar iska ce ta sauke min ruwan dana dora zanyi wanka dashi? Idan banda rashin kirki ba, nida gidana za’a hanani jin dadin rayuwa, to wallahi an fara kaini bango zanyi rashin mutunci fiye da yadda ake tsammani” fitowa Wasila tayi tana tauna chew gum “yar iska tana can gida bi ma’ana tsohuwarka, ko kuka ince yaran daka tara marasa tarbiyya kila dayansu ta dauka, amma ka duba da kyau nafi karfin ka kirani da yar iska tunda baka kamani dumu dumu ina iskancin ba ehe, kuma da kake cewa zakayi rashin mutuncin ai dama ka saba sai dai ka kara kan wanda kakeyi din ko zai kara armashi mtss” taja tsaki ta koma daki, cike da 6acin shi kuma yabi bayanta, Nafi na zaune taji karan tsintsinka mari halamin ko kowa ya ba kowa ko kuma daya cikin su akayi wa, cikin sauri ta kwashi shinkafar da take gyarawa ta koma daki ta rufe kofa.
Yau dai abin nasu har asibiti kowa da bandeji a kai kamar goggoro, abin kunya ya yi yawa yaran har da kukan su domin wai basuyi tsammanin cewa Anty Wasila yar daba bace, sosai furucin su ya 6ata mata rai taji bakin ciki sosai ta kuma kudiri niyyar ci musu mutunci da hanasu kwanciyar hankali, Nafi dai yar “sannu Allah ya sauka ne” daga nan ta tsuke bakinta bata sake cewa komai ba har aka sallame su daga asibiti ita da take fama da cikin jikinta ina zatayi abin da zai jawo mata fitina.
nzu dan shege ya samu matsayin har yana iya watayawa a cikin gidan ubansa, sai yanzu ma ya fahimci cewa lailai Hafiz ubansa ne kuma yaran gidan suka gane cewa shi din yayansu ne kuma jininsu ne, sosai ya zama dan gatan ubansa aka chanja mishi kayan sawa kala kala aka mai dashi makarantar da yaran gidan suke zuwa, duk abin da aka yiwa yaran wanda shi bai samu ko kwatanshi ba yanzu ya samu har ma fiye da nasu, musanman ya sayowa Zaliha kaya masu kyau da tsada wanda rabonta da ganin haka tun suna saurayi da budurwa, a gidan shi bayan kayan auren ta bai ta6a sinana mata komai a harkar kula da lafiyar jiki da tsaftarsa ba, domin da ita da babu duk dayane a gurin sa.