GIDAN SARAUTA CHAPTER 1

GIDAN SARAUTA





CHAPTER 1





MASARAUTAR ZAZZAU

Katuwar masarauta ce dabazan iya misalta muku girmanta ba wanda inka shiga cikinta garine guda danko tako ina kai kawo akeyi kama daga bayi dakuma kuyangu kowa da potion din aikinsa wasu na bangaren girki,wasu suna tsaye matsayin dogaraye wasu kuma na fannikan gidan suna gudanar musu da aikin daya kamata.
Masarautace babba wanda ke daukeda bangararruka daban daban hakanan takunshi kofofi kala kala,masarautace mekyau don tundaga wajenta zaka gane an zuba kudi gurin tsarata, intsaya inamuku bayanin wannan masarauta wani bata lokacin ne don nasan kunsan kyauwun masarauta barin ma ace na zaria.

Tafiya yakeyi ahankali kamar bazai taka kasa ba,kaman wanda tsoron kasan yakeji yayinda yake sanye cikin kananun kaya black T-shirt da black jeans. tunda yake tafiyar yake wuce dogaraye dake tsattsaye amma cikinsu babu wanda yabashi girmamawan daya kamata sema kuskus da wasu suka shigayi suna gulma,ko kallo basu ishe shi ba in fact kanshi na kasa har yakarasa wani madaidaicin kofa wanda ina iya cewa daganin side din yana daya daga cikin bangare marar kyau cikin masarautar baki daya, tunda yadoso gurin banga halaman kuyangu ba, gurin shiru kaman wanda anyi mutuwa. ahankali yatura kofar yashiga tareda rufowa taciki.

wata yar kofa yashiga wanda itakadaine nagani acikin compound din sauran kuma fili ne yar kankanuwa dake dauke da tarkace,daga gefe daya murhu ne da dan tukwane na girki sekuma ta dayan gefen kayan wanke wanke ne ah ahjiye masu datti da alama dai nan gurin ahalin gidan ke wanke wanke dakuma girki, kaman yanda yataho kanshi na kasa haka ma yanzu still kanshi na kasan yayinda ko sallama babu yakarasa cikin gidan. wasu yan mata biyu na hango suna zaune ah tsakiyar parlourn sun zabga uban tagumi inda parlourn kuwa ko kujeru babu cikinta se kafet din dake shinfide kasa tayi daka daka da’ita,takode tafita hayyacinta,karasawa yayi gabansu tareda cewa “Yajikin Ummi? dayar ne datake matukar kama dashi tace”to Yaya Almustapha dasauki za ace” daganan baikuma cewa komai ba sema wucesu da yayi yashiga dakin. karewa dakin kallo nashiga yi shima kafet ce irinta parlourn shimfide kasa duk tayi daka daka da’ita sewata katuwar katifa da wata dattijuwa ke kwance akai ko motsi batayi da alama katifar ma taci duniya.
zama yayi a dede setin kan dattijuwar tare da sa hannu yana taba temperature din jikinta idanunta biyu amma bata magana sede binshi da idanu datakeyi,rike hannunta yayi sosai cikin nashi yayinda ahankali cikin muryarshi me sanyi dakyar yace “Sannu Ummi” batace komai ba kuma bawai daman yayi expecting tayi maganar bane tunda yasan batayi din yajima zaune gurin yana kallonta kamin daga baya yajingina kanshi da jikin gini tareda lumshe idanunshi.

Afiya kanwarshi ce tashigo tareda zama gefenshi,yaji shigowanta don haka yabude idanunshi yadaurasu kanta tace “Yaya Almustapha bamuci abinci ba yunwa mukeji” ajiyar zuciya ya sauke sannan yace “kayan abincin sun kare ne?”
Jijjiga mishi kai tayi alamar eh,tashi yayi batareda yace mata komai ba yafita komawa gun yar uwarta Amira tayi don tana da tabbacin yafita nema musu abunda zasu sama bakin salatin su ne,yau kimanin shekaru 15 kenan,ace dai tun da suka dan yi wayau amma babu wanda suka sani amatsayin ubansu dayawuce Yayansu Almustspha,shine cinsu shine shansu,biyan kudin makarantarsu ne kawai baya musu shima sabida akwai makaranta free cikin masarautar na both islamiya da boko dukda kuwa har suka kare karatunsu na firamare da kuma secondary dasuke yanzu ss2 kullum ana cikin tsangwamarsu dayi musu gori,kaf rayuwarsu basu san miye jin dadi ba se wahala,basu da walwala,basu san miye farin cikin rayuwa ba,sunsan ance ubansu ne sarki ubansu ne ke mulkar garin zariya sede sunanshi kawai sukeji basu taba ganinshi ba dukda kuwa suna muhalli daya,basu san dadin uba ba don ko neman su betabayiba hakana bedamu da sanin ko suna existing ko baswayiba shiyasa sometimes idan common Bayi da kuyangu namusu wulakanci basu taba damuwa tunda wanda yayi sanadiyar zuwansu duniyar kuma me gidan be damu dasuba bare har yasa wasu suga mutuncinsu.
Amira ne tadubi Afiya tace Sis,nitunda nake bantaba ganin me irin rayuwarmu ba hakana bantaba ganin me rashin sa’a irinmu ba,anya kuwa dagaskene mu ‘ya’yan Sarki Abdulrahman ne,anya ba tsinto mu akayi aka kawomu gidan nan tareda mahaifiyar mu suka taimaki rayuwarmu ba…..
Afiya rasa abunda zatacema yar uwar tata tayi se hawayene daya fara ambaliya a idanunta,Amira kuwa bazama ta iya kukan ba don inda sabo tasaba,tayi kukan tagaji har hawayenta sundaina wahal dakansu tunda basu taba samun me lallashinsu ba,kara numfasawa Amiran tayi tareda kura ma ceiling ido tana
Jin sautin kukan yar uwartata har cikin ranta.
Sunfi awa suna zaune a haka sega Almustaphan yadawo rikeda yellow and black leda ah hannunshi,karba sukayi suna mishi godiya yace “kuyi anfanida wannan kafin nasamu kudi in sayo mana kayan abincin” sukace
“Toh Yaya. mungode” juyawa yayi yafita batareda yace musu komaiba. Amira ce tayi yunkurin bude ledar don ganin meya kawo musu,shinkafar gidace yasiyo kwano daya se taliya guda biyu dakuma mai a leda.

Story continues below

Duban Afiya Amira tayi tana fadin “bari mudafa garau garau tunda ga mai kuma akwai sauran yaji daman” Amira takarashe maganar tana duban Afiya don neman karin bayani. “Toh” kawai Afiyan tace mata yayinda Amiran ta dauki ledar tafita don fara gudanar da girkin.

Tunda Almustapha yafita ah masarautar yarasa ina zeje yazauna yaji ko ransa zatayi masa dadi.

★★★

Gidane madaidaici wanda bazaka ganshi kace talaka ke zama cikinsa ba haka na bazaka ce gidan masu kudi baneba sede ace ma masu gidan middle class people ma’ana irin muhallin masu rufin asiri,wanda basu rasa ci ba bare sha hakama sutura, suna dai dashi dede gwargwardo.

Shiga nayi daga cikin gidan inda naga bangare uku ah jere ne sede na tsakiyan yafi girma sena gefe biyun kuma duk girman su dayane sekuma daga can nesa nahango boysquaters dakuma dakin me gadi dayake daga bakin kofa kusa da gate,balaifi filin gidanma ya hadu don anyi interlocking dinsa yayinda andan yi shuke shuken flowers ta gefe sekuma can gefen hagu Dam ne agefe mehade da tank a sama inda akayi decking aka daura akai se parking space dake dauke da motoci guda uku masu kyau cikinta.

Daya daga cikin bangaren da su biyu girman su daya nashiga,wata tsohuwa nahango zaune kan kafet yayinda wata yar budurwa ke kwance kan cinyarta tsohuwar na tsefe mata kitson kanta tundaga nesa ka hango gashin sekaji yaburgeka tsabar kyaunshi dakuma tsayinshi,yarinyarne cikeda shagwaba tace “washhhh Hajja dazafi dai”.

Hajja tace “Yihakuri Mesuna nadaina miki dazafi toh” turo yar bakinta tayi gaba sannan tace “toh Hajja,kokefa” dariya Hajjan tayi sannan tace “kede ba a raba ki da raki wallahi” suna cikin haka ne suka jiyo sallama daga waje ansawa Hajjan tayi yayinda Asiya tacigaba da kallon Tv ana mata tsifa.

“A’a a’a Mubaraq yau kataso da wuri kenan?” Saurayin da Hajja takira da Mubaraq yasamu guri yazauna yana cire hulan kanshi sannan yace “Eh wallahi Hajja kinsan yau juma’a ai daga massallaci nataso senaji yunwa nikeji kuma yau banda niyar cin abinci a waje shiyasa nataho gida direct” yatsina fuska Hajja tayi tana “Uhmmm. aikadinga fama kenan tunda shi mutum bazai nemi mata yayi aureba,wannan wahala har yaushe?”

Yar dariya yayi don yasan ya debo abun magana kuma,yace “karki damu Hajja nima nadamu nayi aurennan lokacine dai beyi ba”

Harararshi Hajja tayi sannan tace
“Aikullum maganar kenan. rayuwar gudu take Mubaraq, shekaru sunja,koh ance maka shekaru talatin da biyu wasane?”
sosa kai Mubaraq yashigayi da car keys dinsa yana fadin “Ayi hakuri Hajja za asan nayi” Hajja tace “kaikasani dai dan nidai bazan fasa fada maka gaskiya ba” Mubaraq yace “Toh Hajja” kafin yasauke idanunshi kan Asiya dake kwance anamata tsifa. lokaci guda mood din fuskarsa ta canza,rai bace yace “Wannan din kam bah Asiya bace komi?” dagowa Asiya tayi tareda dubanshi batareda tace komai ba,wani tsawa ya dirar mata wanda har Hajja seda ta zabura yace “ke wato baki da kunya koh?” turo baki gaba Asiya tayi tana babbatarai Mubaraq yasake harzuka “koh ba magana nake miki ba?minti na nawa da shigowa amma ko kallon inda nake bakiyi ba sabida gaki figagga koh? toh tashi kibani guri banason kallonki tunda ke bakida kunya”

Tsaki Hajja tayi tana ya isheka,kana shirin cire mana dodon kunne be ishekaba harsaika korar min mesuna ko bakaga tsifa nake mata bane ba?…

Amma dai Hajja kinsan abunda take bata kyautawa ko intana mana mu na cikin gida wataran ana waje zatayimawa bekamata ana barin taba…
Kamin shiru nace,kadebo gajiya zakazo ka takurama yarinya kakira wance tasaba ma bautar tayimaka mana tunda dai kasan wannan din bayi zatayiba nifa banason anatakura ma jikokina wallahi,kuda kuke yara wayamuku haka? ….
Zuciyarshi tafarfasa yakeyi amma babu yanda yaiya da Hajja inbahaka ba seta hadashi da Daddy abun yakoma wani abu daban don haka yabuga tsaki yatashi yashige ciki Asiya kuwa tayi lukwi ajikin Hajja kamar munafuka…..

Dakin Mommy yashiga batanan seyawuce kitchen don acan yayi tsanmanin samunta itada ‘Yar lelen nata,tunkan ya Isa yakejiyo kamshin girki yakaure ko Ina murmushi yasaki yayinda yakarasa cikin kitchen din yana sanda rungume Mommyn yayi tabaya Yana Mommyna wani delicious kike girka mana haka?….
“Mubaraq you’ll never change,you always behave like a seven year old child”…
Murmushi yasaki mekarama kyaukyawar fuskarsa annuri yakarbi wukan dake hannun nata ya ajiye gefe sannan yakamo hannun duka yayi kissing”Mommy nihar zan girma ne ah idanunki?, I’m always your little boy and I’ll always be”.jijjiga Kai tayi tare da jan cheeks nashi to naughty Boy kabarni nayi aiki Daddynku yakusa dawowa…..

Story continues below

Dariya yarinyar dake gefe tasaki wanda akallo daya dana mata bazata wuce sa’ar Asiya ba,yankan fruits take abunta ahankali Kuma cikin nutsuwa Ina wuni Yaya Mubaraq,tayi maganar ahankali cikin yar siriruwar muryarta…..
Lafiya Lau Ma’ulele ya aiki?….
Alhamdulillah,yanaka yau ka dawo dawuri….
Kede bari yar kanwata yunwa ne yagudo dani naji nan duniya babu girkin wanda nakeson ci sena Mommy da Ma’ulele,dariya tayi sosai na yanda yayi maganan tun tana nuna batason sunan dayake kiranta dashi harta hakura don ta lura bayida niyar bari…….
Karasa yanka last pineapple din tayi tareda ajiye knife din….
Mezan kawo maka kaci to?….
Duk abunda ya sauwaka,to Big Brother consider it done….
Dan Bata rai Mommyn tayi tana Ina Asiyan itabazatazo takai maka ba ko baka ga aiki mukeyibane mudin….
Mommy kinsan Hajja ae…
Jijjiga Kai Mommyn tayi batasake cewa komai ba inda Asmaun tace yanzu zankai mishi indawo mukarasa…..

To Yar albarka sekindawo,haka tazauna tahada mishi abincin kan tray sannan tafice takai mishi side dinsu inda yayunsu biyu ma nanan biyun Kuma basu dawoba don haka seda takuma Karo abincin dakuma cokala kamin takoma gurin Mommyn don su karasa tanajin Hajja nata mita yarinya se shegen wayon tsiya dason nuna tafi kowa sanin yakamata,kekuma Zainab Kita biye musu wataran seta sa yayanta sun rabaki da naki Ya’yan tukunnan, murmushi Mommyn tayi tanaji sannan tace Husna karkibari maganar Hajja tamiki zafi kinsanta se ahankali….
Asmau da hawaye yacika idanunta tayi karfin halin rikesu tana Mommy karki damu inda sabo ai munsaba yanzu Kam……
Shafa kanta Mommyn tayi sannan tace Allah yamiki albarka kiyi mugama kada Ummi taneme ki acan bakyanan…..
To kawae tace mata inda suka cigaba da gudanar da aiki seda suka gama tas sannan suka kai na mahaifinsu side dinshi kamin tatafi side dinsu…..

Ah parlour tasamu mahaifiyarta nama kanwarta Munira kitso wanda suke matukar kama se Munir twin brother din Muniran dake can gaban TV yana game…..
Munir wai yau babu islamiya ne katasa TV agaba?….
Befasayin game dinba yace Adda Asmeey anbamu hutu jiya nafadamiki ae sede inkin mata….
Murmushi tayi ehto kilan mantawan nayi…..
Kinmanta Kam don inajin sanda yake fada miki cewar mahaifiyartata,Ya Hajja suke?…
Lafiyansu kalau Ummi,yanzu muka gama girkin Daddy yakusa dawowa murmushi Ummin tayi sannan tace to sannu da kokari sekishiga ki watsa ruwa ko?…..
To Ummi Ina Sadiq ne baya side dinsu….

Yayi wani gun kenan tunda baki sameshiba inkinyi wankan kidan wankemin jikin autana tana bacci ah daki banason tacigaba da baccin nan laasar takusa….
To shikenan cewar Asma’u din sannan tatashi tashige dakinta babu bata lokaci tashiga tube kaya…..

*Asalinsu*….

Alhaji Muhammad Dan asalin katsina ne daga wata kauye batagarawa wanda nanne asalin iyayensa sede as time goes on and yanayin budewar rayuwa se suka koma cikin birnin katsina da zama inda yayi karatunshi kama daga firamare har secondary daga nanne kuma yasamu gurbin karatu ah jami’ar Ahmadu Bello University Zaria inda yakaranci Business administration bayan ya kamalla karatunsa da service ne yasamu aiki cikin garin zariya inda nanne yazame masa gurin zama se in yasamu sarari ne yake zuwa duba iyayensa can cikin garin katsina….
Wani zuwa dayayi gida ne Hajja da mahaifinsa suka matsa masa maganar aure to anan ne yace musu shibaida zabi ah yanzu don besaka maganar aure ah gabanshiba tukunnan amma insun takura suna iya sama mishi mata cikin Yan uwa haka kuwa akayi ba ajima ba akasaka bikinsu da Zainabu kyaukyawar yarinya mai dattaku haka ta tare ah gidan daya saya ah zariya suna zaman lafiya abunsu har Allah ya azurtasu da yara hudu maza Uku se Mace daya Mubaraq 32yrs ne dansu nafari se Aliyu 28yrs se Musa 25yrs sekuma Halima 21yrs wanda ah yanzu haka tayi aure tana gidan mijinta ba a Jima dayin bikin ba…….

Tun auren su Alhaji Muhammad basu taba samun matsalaba tsakaninsa da matarsa ba hakanan bata rageshi da komaiba sede Alhaji Muhammad yakasance mutum matafiyi meyawan tafiya kan harkokin kasuwancinsa don shiyasa ka agaba,koda yagama karatunshi bewani dogara da gwamnati ba don anashi ganin sudin basu da tabbas…..
Ayawan tafiye tafiyenshi ne Allah ya hadashi da Maryam ah Gombe bafulatanar Gombe kyaukyawa da hankali wanda hali irin natane yajashi zuwa gareta yakai ga maganar aure tunda ya tunkari mahaifiyarsa da maganar auren yafara samun matsala don daru ta tada baza ayi ma Zainab kishiya ba me tamishi dazaice zaimata kishiya….
babu Hajja, Zainab bata rageni da komai ba kawai Allah ne yadauramin son wancan baiwar Allahn Kuma naga inada dama shiyasa nakeson auren ta,daru sosai akasha da Hajja seda Kawu ya taka Mata birki sannan Muhammad yasamu sa’ida dukda hakan bawai tasauko bane alokacin Halima nada shekaru biyar koda ya tunkari Zainab da maganar aure bata nuna bacin ranta ba fatan alkhairi tayimishi dukda kuwa taji wani iri aranta amma tasan bazata iya hanashi ba tunda Allah ya halasta masa Kuma Allah yaga zuciyarta tana kula da mijinta dede gwargwado tasan bata rageshi dakomaiba…..

Sede Asma’u tafi Asiya kyau da haske kasancewar itan mahaifiyarta tadauko ah haske dakuma tsayin gashi da yanayin jiki da komai,daga idanu,hanci,baki komai na mahaifiyarta tadauko, Asiyan ma nada kyau don ba acemata mummuna ba sannan suma tushen fillon ne tunda gaba da baya fulani ne……
Tunda suka taso kusan Kaya kala daya ake sayamusu komai ma tare akeyi masu makaranta tare suke zuwa da dai sauransu sede sun ban banta ah hali sabida Asma’u sanyin hali ne da ita batada hayaniya ga nutsuwa ga kokari dasanin meya dace,ga girmama na gaba da ita,gatada shiga ran jama’a duk wanda yazauna da ita seya so sake hada hanya da ita shiyasa tazama Yar gata acikin gidan kowa yayinta yakeyi don akwaeta dason aiki dakuma tarairayar yan uwanta sabanin Asiya da takeda rawar Kai dason jiki, batason aiki kwata kwata sannan bata damu da girmama nagaba da itaba ga rashin manners of approach dukda kuwa Itama akwae kwazo da son karatu don duk rashin jinta when it comes to studies tana maida hankalinta wannan banbancin ne yasa kowa bawai yacika shiga harkanta bane sede suyi da Asma’u,Asiya mesunan Hajja ce don haka tazamo mafi soyuwa agurin Hajja don ko tabata batason ayi wani abun da takeyin ma harda zugin Hajja don bakaramin daure mata gindi tayi ba sannan Asiya da Asma’u sunason junansu amma Asiya takan tsangwami Asma’u din ganin anfi ji da ita……….

Hajja kuwa bawai tanason Maryam bane haryanzu don gaisuwarta ma dakyar take amsawa shiyasa ko bayan rasuwar Kawu data dawo gidan ah bangaren Hajiya zainab tasauka hakan nan tasama Asma’u ido da sauran yaran bata cika shiga jikinsu ba kaman sauran jikokinta don Yayan Ummin ma biyarne Asmau 18,Sadiq,Munir Munira se ikram autar ta….

Ayanzu haka Asma’u da Asiya sungama matakin sakandire sunajiran admission yafito sunyi applying Ahmadu Bello University Zaria…..

Asma’u takasance meson girki da gyare gyaren guri hakanan Hajiya Zainab shiyasa tasu tazamo daya,kullum tana manne da ita tana koyan samfarin girki kala kala….

Mubaraq yagama karatunsa tun tuni yanzu yana PHD ne ma at the same time Yana lecturing ah makarantar Ahmadu Bellon faculty of engineering,yayinda Aliyu shima yagama nashi karatun Yana taimakawa Alhaji Muhammad wurin tafiyar da kasuwancin sa don tuni yabar aikin gwamnati kuma yana samu sosai alhamdulillah tunda Yana fulfilling all his familys needs harma yataimakama na waje….


Tunda yabar masarautar yarasa ina zaije shiba abokiba don anashi duniyar besan me ake kira da aboki bama tunda tun tasowarshi betaba experiencing wannan relationship din ba.he always mind his ways and live his life alone,to koma yanason huldar abokan takan wazai so yazama abokinshi?….
Tafiya yake ahankali kaman me tsoron kasa duk wanda ze kalli Imam yakamata yagane akwai jinin sarauta attattaredashi sabida halaye irin nashi narashin son yin magana dama yanda yake tafiyar da al amuransa seda ya tabbatar yayi nesa da katangar masarautar sannan yasamu guri yazauna tareda lumshe idanunshi sa hannu yayi ah aljihun shi yaga babu kudi sawayayi ah dayan aljihun sannan yasamu wata kodaddiyar dari biyu wanda tagama cin duniya….
Furzar da iska yayi daga bakinshi sannan yasake lumshe idanunshi masu daukan hankalin yan mata,maganin Ummin sa yakusa karewa besan yazaiyi ba besan inazai samo kudiba shine tunaninshi don duk wata dabara ta Kare mai ah yanzu…….
Duba wrist watch dinshi yayi sannan yaga time ahankali yakuma tashi yacigaba da trecking seda yaji yagaji sosai sannan yatari machine me machine dinne yatsaya yana kare masa kallo sannan yabuga tsaki yaja machine dinsa yayi gaba yana cewa Allah ya sauwake se akacemaka ko fatara ta kamani se in dauke ka,toni ba dan iska irin ka bane ba…..bin me machine din yayi da kallo batareda yace komai ba sannan ahankali yasaka hannunsa cikin aljihunsa yacigaba da tafiya sanda ya Isa kasuwan ma laaasar tayi likis,yasani duk duniya babu me kin kyamatarsa se Mallam Hudu agurinsa ne kawai yakesamun sauki donnhaka straight shagonsa yawuce seya samu guri abakin kofa yazauna batareda yace komai ba tundaga nesa Mallam Hudu yahangoshi se ya saki murmushi yasan halin abunshi amma shima yau tsiya yake shirin yi mishi don haka yacigaba da harkokinsa yayi kaman besan da zuwansa ba shiko Imam maganar ne bazai iyayi ba,yace yazo dinne bazaiyiba don nauyi bakin sa ke masa haka yacigaba da zama ah gurin har maghrib ah lokacin ne Mallam Hudun yafito don rufe shagon yakauda Kai kaman beganshi ba seda ya rufe har ya juya yafara tafiya se yaga ko yabar Imam ba maganan zeyiba tunda daman halinsa ne don haka yajuyo yana Yareema mekakeyi anan?…..
Murmushi kawai Imam din yayi sannan yamika ma Mallam Hudun hannu sukayi musabiha kafin dakyar yace Ina wuni…
Lafiya Lau ya jikin Hajiya?…
Seda suka fara tafiya sannan dakyar yabudi baki yace “dasauki”,wanda alokacin har Mallam Hudu yafidda ran samun ansa,zanje massallaci yanzu gobe sekazo za akawomin kaya ah Daf seka saukeminsu se inbaka kudi in Allah yakaimu…..
Jijjiga Kai yayi alamar to sannan yajuya yatafi, murmushi Mallam Hudun yayi sannan yace zanga ranar da bakinka ze budu Yarima don kuwa rashin maganar ka nadaya daga cikin abubuwan dasuke cutar dakai da yan uwanka sannan ahankali yakuma cewa Allah ga bayinka nan cikin wani irin hankali da bantaba ganin wani cikin sa ba,ya Allah ka duba musu ka kawo musu dauki…..
Yakarashe addu’ar da Amin sannan yawuce massallaci don kada ya rasa jam’i…….

*****

Makeken parlour ne nagaske wanda yake dauke da kayan sarauta tako Ina tundaga bakin kofar zakaji hancinka na ziyartar wani kamshi medan karen dadi sannan tundaga kofar shiga wannan bangaren zaka gane cewa me bangaren bata wasa bace dubada yanda kuyangu ke da hada hada gurin ganin sun cinma aikin su babu wanda zaka gani ah zaune kokuma ah tsaye batareda yana gudanar dawani aikiba…….

Wata dattijuwa nahango zaune kan kujera irin ta sarauta tadan kishingida jikin kujera yayinda bayi sunkai shida suna zagaye da ita suna mata fifita yayinda biyu nazaune ah gabanta daya nagyara fruits yayinda dayan na bata tana ci ahankali daka gansu kasan ah tsorace suke baswa son suyi wani mistake ayi musu hukunci don haka kowa taka tsantsan yakeyi…..

Ana cikin hakane sega wata tashigo cikin sauri tareda zubewa gaban Matar tana takawarki lafiya Magajiya, Allah yaja da tsawon kwana….
Amin duka sauran bayin suka ansa yayinda jakadiya tacigaba da magana ..
“Ranki shi dade yau me martaba beci abinci ba haka aka dawo dashi”,dasauri Magajiya tatashi tazauna,wani abinci ne aka sarrafa mishin?”…….
Shiru jakadiya tayi don tana tsoron bada ansa don tasan sauran,ba tambayar ki nikeba Jakadiya?kinyimin shiru kina zazzare idanu awani dalili?….
Cikin in ina jakadayi tace”Wainar masa ce da miyan ganye”…
Dafe Kai Magajiya tayi ranta na tafarfasa jitake kaman tarufe jakadiya da duka sede babu hali tunda dattijuwa ce duk rashin imanin ta bazata bugu wacce ta girme mata ah shekaru ba don haka tace waya girka?…..
Aliya ce sabuwar me girkin me martaba da aka canza,wani harara Magajiya ta daka mata sannan tace amma ai na fada miki kifada mata dokokin abincinsa ba koban fada Miki ba?….
Wallahi kinfada uwargijiyata akasi akasamu wai tamanta ne…..
Duba daya daga cikin bayin tayi tace Surayya je
Kikira min Sarkin gidan yari da Sarkin mazga yanzunnan,tasake duban wata daga cikinsu tace kekuma laure jeki kiramin Aliyar yanzunnan,to Magajiya nansuka fice cikin sauri don aiwatar da abunda akasakasu…..

Story continues below

Baa Jima ba segasu sundawo dukansu duban Sarkin mazga tayi tace ga Aliya tayi laifi ayi Mata hukunci da bulala ishirin sannan Sarkin gidan yari yasata ah gidan yari cikin kuka Aliya tashiga bada hakuri amma ko kallon inda take Magajiya batayiba sema duban jakadiya da tayi tace kinemi wata tamaye gurbin ta sannan aka kara irin wannan kuskuren hardake zan hukunta tunda yakamata kina duba irin ayuukan dasukeyi bawai ayitayin duk abunda akaga dama ba…..
To uwargijiyata in Sha Allahu za a kiyaye nan gaba…….
nan ta tashi tafice jiki na bari…..

****..
Tunda suka tashi suka wanke yan kwanikan dasukayi anfani dashi da dare yayinda Amira tashiga shirin tafiya makaranta Afiya Kuma tafara share sharen gidan……
Seda tagama shirin sannan tayima yar uwarta sallama tanacewa seki shirya in an fito break se indawo ke kije tunda Yaya Almustapha baya gida….
To Amira,amma nikam da kinbi tanawa ma damunyi zaman mu tunda komunje dinma kusan kullum se an koro mu ance mutafi muje muyi aiki shiyasama ni Kinga nadaina damun kaina….

Afiya nasan da hakan sede kinsan makaranta nada anfani ah garemu kiduba halin da Umma take ciki yakamata muyi kokari muzama wani abu sabida mufidda mahaifiyar mu awannan halin…..
Hakane kuma to sekin dawo din Allah yadauramu akansu karsu zo yau batakai ga rufe bakinta ba sega laure jakadiya tazo tana hararar su tareda toshe hancinta waiku don jaraba kullum sai kunsa anzo wuri medan Karen kazantar nan ankiraku?…..
Afiya nashirin yin magana Amira tayi saurin rike hannunta alamun tayi shiru..
Laure wake kiranmu?…..
Tsaki Lauren tayi sannan tace shafa kiji ai tambayar rainin wayaune ma wannan wazai kiraku inba Gimbiya ba….
To muna zuwa cewar Amiran…..
Juyawa laure tayi tana yar wakokinta sannan tace kada ma mutum yazo mana yaga abunda zaifaru dashi…..
Murmushi Amiran tayi wanda yafi kuka ciwo sannan tacire hijabin makarantar kamin tasamu kayanta tasaka sannan tace tashi mutafi…..
Babu inda zanje nikam don bazai yuyu mubar Umma itakadaiba yar kwafa Amiran tayi sannan tace sekace yau kika saba barinta kinsandai ko bakije ba se anbiyoki anci miki mutunci sannan ah tasa ki gaba gwanda muje Umma Kuma Allah zecigaba da Kare Mana ita kaman yanda yasaba haka Afiya na kunkuni ta tashi suka tafi side din Gimbiya Hamida wacce wai abaki sukejin Yar uwarsu ce ta jini,yayarsu mahaifi daya……
Koda suka karasa bangarenta samunta sukayi kwance kan gado tarungume pillow tana waya se wani murmushi takeyi tana yauki….

Sunfi minti arbain ah tsaye still tana wayan seda tagama sannan tayi wurgi da wayan tareda tashi tazauna,harara tazuba musu
“tun yaushe kuke dakin nan?”…
Tun dazu cewar Amira….
Ku bakusan mutum nawaya ku fita bane ko gulma da munafurcine yasaku tsayawa don jin abunda nike fada?….
To duk iskancina bekai na matsiyacin Yayanku ba me lalata da ‘ya’yan mutane…..
Ran Afiya ya baci tanashirin magana Amira tadamke hannunta kamin Amiran tace kiyi hakuri Gimbiya bazamu sakeba…
“Better”…
To your normal work as usual Kuma daga yau kada kuyarda insake sawa ah kiraku don na lahira seyafiku jin dadi wallahi…….

Dasauri Amira tashiga bandaki don hada mata ruwan wanka yayinda Afiya na yamutsa fuska ta isa ga wurin kayan Gimibiyan tamika mata towel seda ta daura sannan tashiga bayi lokacin har Amiran tagama hada mata ruwan wanka don haka tazo tajona yar uwarta suka kama gyaran dakin Gimbiya Hameedan saida suka gama tas kowa ranshi ba dadi sannan Afiya tafita zuwa bangaren kitchen don karbo breakfast din Gimbiya yayinda Amiran tashiga taimakawa Gimbiya wurin gyara jikinta bayan tafito haka aikin kenan kullum su suke mata komai harta tausa da bata abinci sannan suyita mata fiffita har saitace ya Isa……..
*****
*London*

Kwance yake kan makeken gadonshi yayinda ‘yan mata biyu ke kwance jikinshi kowa da irin harkar da take yimishi hankali kwance shikuma se karban sakwwnni yakeyi suna cikin badalar su ne wayarsa tashiga ringing jiki ba kwari yace

Can someone disconnect that call for goodness sake!ynda yayi maganar seda ya tsorata duka matan turawa biyun Justina dake kusa da bedside drawer da wayan ke kai tayi saurin daukan wayar yayinda dayar tacigaba da yamutsashi yana ta surutai, tunkan tayi disconnecting har ya katse call din sekawae ta mayar kafin tasake ankara wayar tasake daukar ruri ture joy yayi daga jikinshi yana huci tareda jan gashin justina”didn’t I ask you to disconnect that damn call?”….
Kokarin kwace kanta tashigayi tana”I’m sorry Prince”…
Wurgi yayi da ita Itama yana”get out of my room now!”….

Story continues below

Jikina bari suka tashi sukafice dukansu still wayar na ringing se sake Kira akeyi Kamar kayan jaraba,tsaki yasaki tareda shafa kanshi sannan yadauki wayar tareda picking call din……
Yarima inaka shigane inata kiranka baka dauka?….
Wani kululun bakin ciki yakeji because he’s busy enjoying with those girls amma Magajiya ta bata mishi budget cikeda bacin rai yace Mama darene fa kinsan by this time yakamata Ina bacci amma kika kirani ko awani dalili oho!…..
Cikin sauke murya Magajiya tace haba autana shikenan ban isa inkira Baby boy dina ba inason jin muryarsa,kasan dai nayi kewarka ko?….
Turo baki yayi kaman wanda yana gabanta, I’m sorry Mama just that kinbata min budget dina ne,sorry to Son,ya kake,yaya London da makaranta inafatan komai na tafiya smoothly….

Gyara kwanciya yayi kan makeken bed dinshi don ya lura yasamu opportunity yanzu because he’s running out of cash daman yanata tunanin taya zai tunkari Mai martaba da maganar tunda ko sati biyu baiyiba daya turomasa 2million ah account dinshi itakuma uwartasa bayason kiranta sabida kullum inyakiradin maganar yadawo gida takeyimishi……
shagwabe murya yayi inafa smoothly Mama babu cash and you know kudi is everything right, I’m nothing without money…..

Lokaci guda hankalinta yatashi tace dagaske baka da kudi shine baka Kira ka fadamini ba Sulaiman….
To ai kedinne Mama dana kiraki seki fara maganar dawowana gida shiyasa banson Kira amma wallahi banida kudi. ..
Dan kwafa tayi sannan tace zanturoma kudi amma maganar zuwa gida yazama dole Yarima rabonka da gida kusan shekaru biyar ahaka kakeson abaka sarautar kodanma Kai daman wan Babanka ka dauko bakason abun kwata kwata toka rufamin asiri Kaine hope dina Yarima babu wanda nakeson yagaji sarauta Kamar ka inkuma baka dawo kusa damu kafara gudanar da duties dinkaba bana tunanin Mai martaba zeji dadin haka……
Yamutsa fuska Yarima yayi,to ai Kinga matsalar ni Mama banason sarautarnan kema kinsani bama nina cancanta ba tunda I’m the Youngest son,no one deserves the throne other than Brother Almustapha yakarashe maganar yana magiya….

Kai! Magajiya tayi wata irin tsawa wanda saida Yarima Sulaiman ya tsorata harcikin dodon kunnensa sannan ahankali yatashi daga kwance yazauna akan gadonshi…..
Cikin bacin rai Magajiya tace idan har nasake jin irin wannan maganar ah bakin ka ranka bazai maka dadi ba wallahi ko sunan yaron nan nasake ji abakinka ranka inyayi dubu seya baci and I warn you for the last time kafin satinnan yakare ka tattaro naka ya naka kadawo Nigeria inbahaka ba nidakai ne acikin gidannan sannan takatse wayar tana hucin takaici…..
Furzar da iska yayi ah hankali sannan yayi wulli da wayar”Damn it,I told her I’m not after the throne meyasa baza abarni in huta ba miyasa baza a bar mutum ya shakata ma rayuwarsa ba,I don’t want to be caged in there.i want to be a free Man,I mean a free Man!”yakarashe maganar yana tsakin takaici yasan Magajiya she will not take her words back tunda tace yatafin as a command dole yatafin if not shikanshi bazai ji da dadinba don haka yasama ranshi dole yakoma Nigeria cikin satinnan din……

****
Yau tunsafe bayan tagama taya Ummi ayyuka tashige daki ta dale gado don karanta wani littafi da Aisha tadameta takaranta wai ya hadu sosai,aikuwa littafin bakaramin tafiya da hankalinta yayi ba waishi *ALKAWARI BAYAN RAI* na *SUMAYYA ABDULKADIR* tana ganin masu karanta Hausa novel amatsayin marasa aikin yi dakuma bata lokaci seyau ta tabbatar ba bata lokacinsu sukeba tunda gashi tunda tafara da safe bata iya ajiyewa sallah ne kadai ke tadata daga kan gadon sekuma in Ummi tai Kiranta each and every page takaranta she’ll be yearning to know what will happen next se yanzu Allah yabata ikon gamawa….
Lumshe idanunta tayi ahankali tana tunano abubuwan dasuka faru cikin littafin,towai daman haka soyayya yake?
haka mutum yakeji when he’s in love,haka yake reacting dakuma sacrificing…
dan shiru tayi nadan dakiku sannan ta lumshe idanunta,when will she fall in love and who will she fall for,ya yake? will she be lucky to get the love in return kokuma son maso wani zatayi,ya gayen ze zama dogo ne ko guntu, fari ko Baki, kyaukyawa ko mummuni duka babu wanda tasani dan ware hannun ta tayi ahankali sannan tafurta “only God knows,but I hope he’ll be dashingly handsome in everyway”……

Murmushi ne yasubuce mata sekuma taji kunyar kanta, ahankali tadan bugi kanta”Ya Allah what am I thinking?”….

Jitayi Munir namata sallama ah kofar dakinta don haka ta ansa sannan yace Mommy na kiranki….

Wurgi tayi da pillow dinta sannan tace to inazuwa, Allah sarki yau Mommy tunsafe bata ganni ba dole tanemeni.. .

******

*****
Yauma kaman jiya yaje kasuwa shagon
Mallam Hudu seyasake neman guri yazauna batareda yayi magana ba murmushi Baba Hudun yayi sannan yafito yasamo shi zaune,dan dafa shi yayi sannan yace daga makaranta ka fito ne?……
“Ina wuni”,yagaishe shi ciki sanyayyar muryarsa…
Lafiya Lau Yarima,yajikin Hajiyan?,murmushi kawai yama Baba Hudun batareda yace komai ba suna nan tsaye sega motar kawo Kaya ta zo nan Almustapha yashiga aiki najido kayan yana shigar dasu shagon inda sabo yasaba don wannan shine aikin da Baba Hudun kesashi yi har yadan samu abun rikewa ah hannunshi yakuma saima kannensa abunda zasu sa ma bakin salatinsu dukda ma wani sa’in yakan dauki kyautan kayan abinci yabasu,sede ba kullum za ayi maka ba dole watarana mutum ze gaji shiyasa shima Almustaphan yakeson yin aikin yasan yasamu da guminshi ne bawai yazama maroqi ba seda yagama kwashe uban kayayyakin sannan mallam Hudun yamasa sannu tareda cewa to ga kudin ka nan Yarima…..
Lumshe idanu Almustapha yayi bayason wannan sunan kwata kwata inda Mallam Hudun yasan yanda yakeji inya kirashi da wannan sunan dakoda wasa bazai taba koda kwatanta kiranshi da sunan ba sede duk yanda yakeji din bekai girman darajar Mallam Hudun dayake gani ba don haka bazai iya budan baki yace masa bayason sunan ba….

Dukar dakansa yayi kaman bazaice komai ba se can sannan yace ka ajiye kudin agunka kawai zanturo Amira, murmushi Mallam Hudun yayi sannan yace to amma dai katafi musu dawannan yanzun nan Mallam Hudun yajuya cikin shagon yadauko taliya da macaroni bibbiyu yasaka mishi ah leda hadeda ledan maggi da Onga roll daya se Mai kwalba daya yace to gashi ka Kai musu ko kafin Amiran tazo…..

Karba yayi batareda yace komai ba sannan yabar gurin mallam Hudun da kallon tausayi yabishi dashi sannan ya jijjiga kanshi yakoma cikin shagon nashi…..

Waishin wanene Almustapha?
Menene asalinsa,menene labarin masarautar Zazzau,meyasamu Ummi?,meye dalilin dayasa Almustapha suke cikin wannan yanayin?….
*ASALINSU*….

Sarki Sulaiman babban sarki ne acikin Nigeria da babu yankin dazakaje ba asan dashiba tsabar tashen da mulkinsa yayi dama kuma adalcinshi ga talakawanshi,asalin iyayenshi nomads ne(Wanda akafi sani da fulanin daji) tun kakanni wanda basu da takaitaccen gurin zama suna yawo ne depending on the weather tayanda zasu samu su ciyar da dabobbbinsu dama su kansu ahakan ne har Allah yasauke su acikin garin Zaria wanda tun alokacin ba abakin komai take ba don mutane tsirarru ne kawai agarin.tunda sukazo garin Zaria suka ji dadin zama agarin se suka kasa yin gaba suka kafa gida da kasuwancin su wanda ahakan ya bunkasa har suka saba da mutanen gari akazama daya. with time population na karuwa ah garin har garin Zaria yafara zama babban guri alokacin da Allah yadauki ran Sarkin garin bashi da magajin daza abama sarauta don haka akanemi wanda yacancanta aka bama wanda shine mahaifin sarki Sulaiman shima bayan shekaru tsufa taxo se mulki yadawo hannun sarki sulaimanu wanda alokacinshi bakaramin taka rawar gani yayiba don ganin yayi wani abun alfahari ah yankin Zaria haka rayuwa tacigaba, Sarki Sulaiman yazama abun soyuwa ga kowa bama a zaria kadai ba ah kasar Nigeria bakidayan ta.matar shi daya kwallin kwall wanda tunda ya aureta basu samu haihuwa ba har na tsawon shekaru takwas hakan Kuma besa yakara aureba dukdama irin takuramasa da jama’a sukeyi da irin hakurinshi dama Kuma addu’a dasukeyi gakuma subjects nayimusu Allah yabama Zuwaira ciki kaman da wasa bakaramin farin ciki sukayiba lokacin har yar kwarya kwaryar walima seda akayi sanda Zuwaira tahaihu ‘da namiji tasamu nanma murna sosai akayi ranar suna akasama yaro suna Almustapha wanda mutanen gari ke kiranshi da Yarima tun haihuwarshi Zuwaira da Mai martaba suka dauki son duniya suka daura ma yaron komai yace yanaso za ayimishi har tasowanshi, Almustapha yazamanto me kiriniya da son yawace yawace da freedom,tun yana shekara biyar akeson fara koya mishi swordfighting da hawan doki amma kwata kwata bayaso sabida baida passion for sarauta kwata kwata wannan abun baidamu su Sarki ba se suka barshi ah tunaninsu yarinta ne with time zefara dakanshi, Yarima Almustapha nada shekara bakwai Allah yasake bama Zuwaira ciki wannan karan anyi murna sosai don harta fidda rai ga haihuwa sede murnar batakai na lokacin haihuwar Almustapha ba +

haka akayi suna lafiya akasama yaro Abdulrahman tunda aka haifi Abdulrahman yazama abun so acikin masarautar sabida yaron akwai shiga rai haka Almustapha yadauki son duniya yadaurama tilon kaninshi komai yasamu na Abdulrahman haka Abdulrahman dinma yataso yanason dan uwanshi komai tare sukeyi hakanan Almustapha bayason laifin kaninshi komai yana shigan masa sede abunda ya banbantasu Abdulrahman na matukar son sarauta tun yana shekara biyar yake koyon fada dason hawan doki daduk wani activities na sarauta,gashi da kwazo da kaifin basira gakuma son manyance alokacin ne Kuma akafara matsama Almustapha yadinga koyon abubuwa sede ranshi bayaso ko anfara koya mishi seya gudu akwae ranar da sarki Sulaiman yakirashi yayi mashi fada sosai wanda hakan betaba faruwa ba yayi kuka sosai sannan yadau alwashin fara yin abunda mahaifinshi keso don bayason bacin ransu kwata kwata don haka yafara participating dukda kuwa ranshi bayaso,bakaramin dadi Mai martaba yajiba ga canzawan ‘dan nashi sekuma yawanci karfin koyon yakoma kan Almustapha aka daina bama Abdulrahman din attention sosai wanda hakan bakaramin sosa mai rai yayiba sede be nuna ba saboda shi yarone dabai cika tada hayaniya ba bekuma cika nuna damuwarshi ah fili ba sede yakebe gefe yayi kukansa me isansa yashare hawayensa, Abdulrahman yakasance yaro meson rubuce rubuce barinma akan abunda yafaru dashi dakuma abunda yakeso tunda yafara wayau yakan zauna yazana kanshi ah zaune akan kujerar sarauta kokuma yana tsaye rikeda sword jikinshi da kayan alfarma shiyasa koda yalura bazai samu sarautar ba anfison abaman Yayanshi seya rubuta cikin diary dinsa how he felt and the rest…..

Almustapha cikin yan watannin daya biyo baya yalura Abdulrahman yadaina sakewa kaman da don haka yatambayeshi amma besamu ansa daga gareshiba don haka yashiga bincike wanda ahakan ne har ya karanta diary din bakaramin kuka yayi ba ranar sabida irin son da yakema kaninshi Allah ne kadai yasani,duk wani abu dazai bata mishi rai baso yakeyiba jin yaron yake har cikin ranshi don haka ya daukar ma kanshi alkawari tun ranar babu Mai mulkar garin Zazzau bayan mahaifinsu inba Abdulrahman ba don haka sanda yagama junior secondary school dinshi yadage yanason tafiya Madina wata Islamic school karatu anyin gwagwarmaya kafin Mai martaba ya yarda aikuwa tunda Almustapha yatafi besake waiwayen gidaba seda yagama secondary school sannan ne yace yanason yakarasa karatunshi ah waje…… Mai martaba yalura Almustapha bayason karatu ah gidane kwata kwata don haka seya kyaleshi shikuma Abdulrahman duk karatunsa agida yayi kama daga primary har secondary school sannan yakanyi participating wurin taimakon mahaifinsa halarta wasu abubuwan dakuma ziyarta garuruwa dakuma solving problems na talakawansu in the absence of his Brother wannan dalilin ne yasa kowa yafi sonshi Kuma suke jida shi ahaka har yasamu gurbin karatu ah jami’ar Ahmadu Bello wanda alokacin ba’a jima da budetaba sosai yamaida hankalinshi kan karatunshi Kuma hakan behanashi cigaba da ayuukan dayasaba ba…..

STORY CONTINUES BELOW


Sanda Almustapha yagama kammala karatunshi yajona Masters Mai martaba har America yaje don dawo dashi amma fir yaki yanuna karara shifa bazai dawo ba indai har zaa matsa masa kan maganar sarauta……

Bakaramin tashin hankali da bacin rai mai martaba yashiga ba sannan yace babu shi babu Almustapha sannan duk wanda yasan yana da dangantaka dashi to yatabbatar ya yanke da Almustapha tunda shida ya haifeshima ya yafeshi hankalin Zuwaira bakaramin tashi yayiba da shikanshi Abdulrahman din, yana mamakin miyasa Yayanshi zekai wannan gandun sede dukansu babu wanda ya Isa ya karya dokan Mai martaba sabida umarni ne daga gareshi sedaga bayane jakadiya take fadama Abdulrahman din Almustapha yayi sacrificing throne dinne for him tunda yalura yanaso Itama saudaya yataba fada mata wanda hakan yasamu asaline sabida irin shakuwarsu,duk wata shawara awurinta yakenema, bakaramin kuka Abdulrahman yayiba sannan yaso fadama Mai martaba amma jakadiya takisam tace amana ne Almustapha yabata shidinma don ya cancanta yasani ne shiyasa tafada mishi haka Kuma inhar Yayanshi na iya yimishi haka mezai hana yacika burinshi tunda talakawama shi sukeso ba wansa ba dakyar yabar maganar, Mai martaba kuwa tunda yadawo daga America hope dinshi kan Abdulrahman yakoma wanda shikuma Abdulrahman din be zuba mai kasa ah idoba ahaka yakarasa karatunshi sannan akafara maganar nema mishi auren Magajiya yar gidan waziri dukda dai bawai yanaso bane sede bazai iya duban mahaifinshi yace bayason zabinshiba ahaka akayi auren sannan suna zaman lafiya da Magajiya sede akwaita da mulki da isa gata dason sarauta batada sassauci ga bayinta kwatakwata bata daukesu abakin komai ba,laifi kadan bawa zaiyi ayi masa hukunci metsauri ashekarar aurensu tasamu ciki wanda akullum bata dawani buri daya wuce taga ta haifi ‘Da namiji wanda zai gaji sarautar zazzau ahaka har cikin yacika wata tara akazo gandun haihuwa sekuma Allah da ikon shi yabata santa leluwar budurwa bakaramin bakin ciki taji ba don bahaka tasoba taso ace ita tahaifi air to the throne dukdama ita kadaice Matarsa sede tasan gidan sarauta yanzunnan se ah matsa ya kara aure haka ta rungumi yarta tanasonta dukda kuwa ba macen taso haihuwa ba amma ai ‘da ‘dane sannan wahalar haihuwar duk dayane Gimbiya HUMAIRA nada shekara uku Allah yasake bama Magajiya wani cikin wannan karan murnar tafi takowanne lokaci don kuwa kowa yana tsanmanin za ahaiho namijine sede Allah da ikon shi batasamu ‘da namijin ba seta Kuma haihuwar mace Halima,tundaga wannan lokacin Magajiya tafara shige shige don aganinta zama be ganta ba inbata samu ‘Da namiji ba. bayan shekara biyu se Allah yasake bata ciki wanda alokacin bokanta ya tabbatar mata cewa ‘Da namiji zata haifa sede Allah dayafi komai seyabata mamaki tasake samun ‘Ya mace kuka kam tayishi ranar kaman zatayi yaya sannan tacima boka mutunci don aganinta yacuceta yayi mata karya ahaka tacigaba da rainon ‘Ya’yanta mata wanda tun tasowarsu takoyamusu rashin daukar Dan Adam da daraja don kuwa bayi ba ahannun Magajiya kadai suke wahala ba harma ah hannun ‘ya’yan Magajiya alokacin ne kuma Allah yadauki ran sarki Sulaiman adalilin wata yar ciwo dayayi na kwana biyu wanda yazo da ajali tunda yafara rashin lafiya yakecewa anemo masa Almustapha,acemasa ya yafemasa duniya da lahira sede kash Allah beyi haduwarsuba….. tabbas anyi rashi bama agarin Zazzau ba kadai agabakidaya kasar Nigeria kowa ya jijjiga da rasuwar bawan Allan,haka aka yimashi sallah aka kaishi gidansa na gaskiya daganan aka rada Abdulrahmanu matsayin sarki wanda Ina iya cemuku harma yafi mahaifinsa aiki dakuma yin adalci tsakanin mutanensa wannan yasa kowa kesonshi da girmama shi cikin shekara uku yagama shiga ran kowa sannan babu inda baya shiga don halarta taro na sarakuna bama ah Nigeria kadai ba har neighbouring countries dinmu sannan tunda yahau mulki yake neman dan uwansa sede shiru babu labarinsu kwata kwata,awannan lokacin ne aka gaiyaceshi zuwa wata taro na sarakunan kasashe baki daya ah *Chad* nan yakama hanya yatafi inda anan ne Allah ya hada shi da Yar Sarkin Chad yagani yace yanaso inda yanemi aurenta babu bata lokaci akabashi ita dubada irin mutunci da girma irin nasa tunda Magajiya taji labarin auren Khairiya da Abdulrahman hankalinta bakaramin tashi yayiba, hankalinta bekara tashibama seda tayi ido hudu da Khairiya babu inda taragu daga kyau har mulki da kudi gashi kuwa Mai martaba yadauki son duniya yadaura mata don jida ita yake Kamar kwai banawasaba gashi Itama tazo tanashiga ran jama’a dubada hali irin nata compared to Magajiya me wulakanta bayi ita da take tasu ma,shekaranta daya dazuwa gidan tasamu ciki har Allah yasauketa lafiya tasamu santalelen ‘danta namiji ranar murna agurin Maimartaba Allah ne kadai yasani daga Khairiya yayi sama yana juyi da ita cikin daki gaban kuyangu tsabar farin ciki sannan yadauki ‘Dan yana karemasa kallo tareda yi masa addu’a,samun guri yayi yazauna bayan bayin sunbasu guri sannan ya janyo Khairiyan zuwa jikinsa…..
I’m very grateful for this gift Khairiya, I’ll forever be thankful to you,kinbani kyautar dabansan irin godiyan dazanyi miki ba…Dan furzar da iska yayi sannan yasake dubanta
“the owner of the throne is back Khairiya, Almustapha is back!and the throne belongs to him”…..

STORY CONTINUES BELOW


Murmushi tayi tareda Kara shigewa jikinshi don tasan irin son dayake ma Yayanshi kullum maganarsa shine Allah yabashi ‘Da namiji yasamishi suna Almustapha sannan yadaurashi akan kujerar Almustapha dayabari……
Allah ya rayamana shi Abban Almustapha….
Kissing forehead dinta yayi ahankali sannan yace …
“Amin Ummin Almustapha,kinfara koyon yarenmu sosai yanzu, you’re a great learner”….
Murmushi tasakar Mai me melting heart dinshi sannan tace….
And the credit goes to you….
Murmushi kawai yayi yana karema yaron kallo kwata kwata baya gajiya da kallon yaron hakanan bayason barin yaro seyake ganin kaman inyasakeshi ze sake guduwa kaman yanda Yayanshi yagudu yabarshi……

Kallon ta yayi sannan yakalli yaron “he look exactly like his mother, I’m jeolous Khairiya”…
Dan Jan hancinshi tayi “don’t be jeolous because he’ll be like you one day”….
Yar dariya yayi “anyi one one kenan”……
Uhmm Mana….

ahaka akayi suna akasama yaro Almustapha anyi bikin suna sosai,anyi sadaka anci ansha awannan ranar sannan ba ataba yin taro agarin zazzauba irin na ranar sunan Almustapha…….

Magajiya kuwa ko barka bataje tayima Khairiya ba kowa yaganta yasan tana bakin ciki da wannan haihuwar haka ‘ya’yanta ma tabi tasamusu tsanar ‘Dan uwansu tun yana yaronshi sannan tundaga wannan lokacin tashiga makirci yau tahada ma Khairiya wannan gobe tahada mata wancan sede babu wanda tayi succeeding aciki, Almustapha nada shekara hudu Magajiya tasamu ciki shima haihuwar Mace tasake samu inda sukasamata Hamida bayan shekara biyu sega wani cikin Kuma wannan karan se Allah yabata ‘Da namiji inda suka sa maisunan marigayi sarki Sulaiman Maimartaba yayi farin ciki da haihuwar acewarsa Almustapha yasamu abokin wasa dukdama duk haihuwar da Magajiya takeyi yakan nuna farin cikinsa don kuwa Mata ma ‘ya’ya ne Kuma yana kula dasu dede gwargwado and duk abunda sukeso anayi musu……

Tunda Magajiya tasamu Sulaiman tasaka ma ranta cewa shine zai gaji sarautar Zazzau dukyanda za ayi setayi yanda zatayi tahana Almustapha mulkan garin zazzau koda kuwa hakan na nufin ta kaudashi daga duniya ne sede she won’t go directly by doing that sede inhar the other way din yaki tafiya yanda tasone…..

Sulaiman yataso yanason dan uwanshi Almustapha, he’s just a free boy baya dason bin maganar mahaifiyarshi se abunda ranshi keso yakeyi Sulaiman nada shekara biyar Almustapha nada goma shabiyu duk wani harkansu tare sukeyi sannan Almustapha nakula dashi yanda yakamata sede Almustapha mutum ne dabaya magana miskiline gashi da shariya becika damuwa da alamuran mutaneba ga sarauta da jinkai ga kyau duk wanda yasaka ido akan yaron seyaji yaburgeshi manya da yara kowa girmama shi yakeyi acikin masarautar dama garin baki daya awannan lokacin ne Magajiya tafara shirin gudanar da aikinta don kuwa ta lura sam Almustapha baya kama da Mai Martaba ko kadan uwarsa yadauko don kuwa daka ganshi kaga ba jinin Nigeria bane ba dukda kuwa bawai wani haske ne dashi ba amma yanayin fatarshi da gashin shi kadai ze baka amsa……
ranar Almustapha yadawo daga lambu kenan dayanma yashiga dakin mahaifiyarshi yasamu guri yazauna….
Kallonshi tayi sannan tace harka dawo daga lambun ne yau?…..
Uhm kawai yace Mata, murmushi tayi sannan tace Mallam Hudu bebaka unripe mango ka kawomin ba?….
“Bebaniba Ummi”..
Kuyangun dake mata fifitane sukace kilan yamanta ne Aunty….
Nima tunanina kenan Hindatu Kuma wallahi yau inbanci mangoron nanba zan iya zazzabi,Yar dariya Hindatun tayi sannan tace ba akai ga haka ba bari zanje inkarbo miki yanzunnan inyaso Jamila tafara miki tausan kafin nadawo…..

To Hindatu Allah yamiki albarka, nan kuwa Hindatu tafice aguje don karbowa Jamila nashirin barin yin fifitar Almustaphan yadaga mata hannu alamun tabari sannan yataso ahankali cikin takunshi na kasaita yazauna kusa da kafafun Maman nashi yana yimata tausan ahankali sannan yana dan satan kallon cikin ta don yaga Kamar yadan kumbura murmushi tayi lura da kallon cikin dataga yanayi sannan tariko hannunshi ahankali tadaura akan cikinta “you’ll be a Brother soon Yarima”….
Lumshe idanunshi yayi ahankali don bakaramin dadin news din yajiba sannan yadan saki murmushi,yanason kanne yanaso ace shima yanada kannenshi uwa daya uba daya it feels good sabida yagaji da wulakancin Magajiya da Yayanta duksanda taganshi da Sulaiman seta cimishi mutunci wurin yayyunsa matakam baya samun sauki har humaira da Halima sukayi aure baya tunanin maganar kirkita taba hadasu …….

STORY CONTINUES BELOW


Cire hannunshi yayi acikin nata sannan yarungumeta batareda yace komaiba,tasan rungumar na nuna farin cikinshi ne,tasan halinshi sarai bazai taba magana ba ko shakka babu Almustapha mahaifinta yadauko wurin miskilanci da sarauta dakuma mahaifin shi dan ko sarki Abdulrahman ma ba bayaba wajen kasaita suna nan zaune ahaka har Hindatu tadawo da unripe mango ah yanke karban plate din yayi yanabama Ummin nashi ah baki tanaci suna haka ne wata baiwa tashigo wai ai tayi bako daga Chad tayi mamaki sosai don ah iya saninta babu wani dan gidansu datasani dayace zaizo mata amma seta zari mayafinta tafita anan ne tayi arba da bakon dabatasanshi bama kwata kwata gaisuwa sukayi cikin yarensu na Chad sannan yace mata daga Chad yazo aikine ah Zaria baida gurin sauka Kuma yajima dasanin cewa tayi aure anan shine yace bari yazo su gaisa….

Godiya tamishi sosai da ziyara sannan ta tambayeshi mutanen Chad duk yace mata kalau suke sannan tace akarasadashi gurin Mai martaba sugaisa ace bakontane daga Chad zedan kwana biyu anan…….

Aikuwa Maimartaba yaji dadin ganinshi sannan aka bashi masauki mekyau abunda Khairiya batasaniba he was hired by Magajiya sabida suyi conspiracy against her kwanan shi biyu ah gidan kullum inyadawo daga inda yake karyar yaje aiki seyaxo gurin Khairiya sudan gaisa sudan taba hira Kuma wannan abun yafara jan yan magance magance cikin masarautar wanda bayin Magajiya ne sukafara kintsata wai ai ba dan uwan Khairiya bane to miyasa zena zuwa gunta hira,wasu suce kode tsohon saurayinta dai hakadai magana tafara nisa har Magajiya taje gun Mai Martaba tafara mashi abunda taji anafadi gwanda yayima Khairiya magana ta sallami bakonta karya jamata matsala…..

Tsaki Mai Martaba yayi sannan yace “nifa Magajiya Kinga bana son gulmace gulmace da kananan magana,wani sa’in kuke bama bayinnan daman suna fadan wasu abubuwan dababu Kai babu gindi don haka kar inkara jin zancen banzan nan abakin ki”……

To kawai tace mishi yayinda tana fita tawuce gurin bokanta tafadamishi tanason Maimartaba ya zargi Khairiya sannan duk abunda ita tafadamishi ya yarda,aikuwa boka yace to ….
Ranar da daddare Khairiya na bacci ah dakinta se ga dan chadin yazo side dinta wai ita ke neman shi, Hindatu akafadamawa don haka tace bari ta tambayi uwargijiyanta tukunnan dakin babu haske da duhu don haka daga bakin kofa tayi sallama setaji ta ansa mata Kuma kamar muryar Khairiyan ne seta fadamata sakon nan tace ah shigo dashi ba Karamin mamaki Hindatu tayiba sede babu jaa amaganar shugabanta dole tabi abunda tace don haka seta fita don bashi ikon shiga dakin idonta yaciko da kwalla don tarasa abunyi…..
Abunda Hindatu bata saniba ba Khairiya ne tayi magana ba daya daga cikin kuyangun Magajiya ne tazo ta labe haka yashiga dakin yadale gado yakwanta gefen Khairiya can cikin masarauta kuwa anfara gulmace gulmace kan sarauniya Khairiya tashigar da kato dakinta kan kace mai magana tagama karada ko Ina duk inda ka tsuguna gulma akeyi, Almustapha na dakinsa yana duba wani littafi yaji kaman dogarayensa nadamunsa da hayaniya don haka yatashi yafita don ganin meke faruwa samun su yayi suna ta yan magance magance,tsayawa yayi yana kallonsu don kuwa ah tsarinsa daya tsaya agabansu from his reaction suke gane meyakeso amma seyaga yau basu zube kasaba don mika masa gaisuwa sannan basuyi shirun ba kaman yanda yabukata sema daya daga cikin dogarayen ne yace wayasani ma ko shima ba asalin ‘Dan Sarkin bane kawai ta yaudaremu ne…..
Wani ma yadauka”ahto nidama tunda inamamaki miyasa yaron nan bedauko ubansa ba akamanni,ashe ga dalili nan ah fili”…..
Lumshe idanu Almustaphan yayi don yaji zafin maganar amma seyakoma daki don saka kayansa yawuce side din mahaifiyarsa don jin meyake faruwane,yanajin wani na Kuma cewa matsalar auren nawajen kenan basuda tarbiya kwata kwata…..

Wannan karan waziri dakansa yaje yasamu Mai martaba yake fada masa sannan yace yazo yagani da idanunsa babu musu Mai martaba yatashi yabi bayansa sanda ya iso bangaren Khairiya acike yake da bayi da dogaraye suna ganin Mai martaba kowa yakama hanyarsa yakoma bakin aikinsa haka yashiga sashin nata yanajin kirjinshi nabugawa dukda kuwa baya tunanin ze ganta dawanin kaman yanda jama a keta fada sede kash yanashiga yayi arba da abunda idanunsa da jikinsa bazasu iya dauka ba lumshe idanunshi yayi sannan yafara furta innalillahi wainna ilaihir rajiun,kamin kace me ya yanki jiki yafadi dasauri waziri yayi kanshi yana ihun sunanshi yayinda alokacin Khairiya ta tashi sakamakon jin ihun Wazirin datayi,aikuwa ‘Dan Chad din dagudu yafice don neman tsira don yasan in aka kamashi bazai ji da dadi ba, awannan yanayin ne Almustapha yazo yasamesu ganin mahaifiyarshi na kuka yakarasa gareta tareda rungumeta yayinda zuciyarshi nayi mashi zafi alokacin ne kuma aka fita da Mai martaba…..
Almustapha bansan komai ba,wallahi banyi komaiba Almustapha, believe me son…..
Sa hannu yayi yarufe mata bakinta shima idanunshi sun ciko da kwallah”I trust you Mother,basai kinyi magana ba”…….
Haka suka kusan shide awa daya shi kuka ita kuka daga karshe ta tashi don zuwa dubo jikin Mai Martaba amma tundaga waje tagane ba lallai abarta tashiga ba dukda haka takarasa shashin nashi don trying luck dinta sede tundaga bakin kofa tahadu da Magajiya,”ke dakata!”….
Ina zakije,munafuka algungunma kodai so kike kikarasamin mijine bayan abubuwan dakikayi duk basu isheki ba?…..
So kike kikarasa shi har lahira?,to baki isa ba Khairiya don kin asirceshi yafita acikin tunaninshi awancan lokacin toyanzu baki isaba!…
Kuka Khairiya tashigayi tana nibansan komai ba,wallahi banyi komaiba Magajiya don Allah kibarni inga Mai Martaba innayi mishi bayani zai gane……
Dariya Magajiya tayi harda shewa sannan tazare mata idanu”da tsafin naki ba?”…
Jijjiga Kai Khairiya tashigayi yayinda Magajiya tace”Yo inbada tsafin kiba damai zai gane,bayan kowa yaganki kiri kiri da kwarto ah gado daya wani bayani ne kuma zakiyi wanda yafi wannan?kifada mini wani bayani zakiyi.inma zaki tashi kibarnan tun cikin ruwan sanyi gwanda kitashi inbahaka ba insa dogaraye sumiki dan banzan duka dake da ‘Ya’yan shegun dake cikin ki”……
Tsugunawa Khairiya tayi gaban Magajiya tana rokon ta tayi hakuri tana kuka kaman ranta zai fita duk wanda yaganta seyaji tausayinta amma Magajiya fir taki sema sawa datayi dogarayen suzo suyi waje da ita,haka sukazo sunajanta tana kuka tana tutturjewa hargaban shashenta Almustapha dake ciki yaji kaman kukan mahaifiyarshi don haka yayi saurin fitowa hango walakancin da dogaraye keyimata ne yasashi saurin tafiya aguje nan yashiga dukansu ai tuni suka koma kanshi kuma sede shima ba baya ba he’s well trained seda yamusu likis duka sannan yadawo kusa da Ummin shi yadagata yana hawaye suka karasa gaban shashen nata sede Magajiya da dogaraye na tsaye agurin anata wulli da kayan mahaifiyarsa lumshe idanunshi yayi ahankali yanajin wani irin zafi a ranshi yayinda Ummin tasake hannunshi takuma tafiya da gudu tana bama Magajiya hakuri harda rike kafafunta ball Magajiya tayi da’ita wannan karan seda ta gwaru dawani dutse dakarfi Almustapha yashiga Kiran Ummin nashi *Ummi!Ummi* sannan yaruga aguje zuwa gurinta Magajiya tana iyacewa tunda yaron yazo duniya yaune tafara jin muryarshi don magana betaba hadasuba…..

STORY CONTINUES BELOW


Ahankali yadaga mahaifiyartashi sannan ya yagi rigan jikinshi yashiga goge mata goshinta inda yafara jini still tana shirin kwatar jikinta ne don taga mai martaba sede wannan karon yarike hannunta ka Kam,kamata yayi suka tsaya sannan yayi hanyar barin masarautar duk inda suka wuce anakallonsu kowa na tofa albarkacin bakinsa sede daga ita harshi babu wanda yadaga ya kallesu seda suka bar masarautar sukayi nisa sosai sega Mallam Hudu yazo yana kuka shabe shabe yana kigafarce ni uwargijiyata abu irin haka yafaru dake bazan iya komai akai ba……

Murmushin dayafi kuka ciwo Khairiya tayi sannan tace Mallam Hudu kaima Ka yarda dani ko?,kayarda bazan iya aikata abunda ake zargina dashiba ko?….
Jijjiga Kai yayi cikin kuka yanacewa nayarda dake ko kowa ze juya maki baya nina yarda dake nikuma na tabbatar me martaba ya yarda dake sede in wata kulla kullar akayi…..
Fatana Allah ya kubutar dake daga wannan al amarin don magana duk ta baza gari,cikin kuka tace bana tunanin zan iya warware kaina daga zargin nan zankoma kasata wurin iyaye na inada tabbacin me martaba dakanshi zezo nemana…..
Cikin kuka Mallam Hudu daya kasance mutumin ta me kula Mata da lambu dakuma kawo mata ya’yan itatuwa yace, insha Allahu watarana komai zezama labari……inamiki fatan alkhairi…..
Jijjiga mishi Kai kawai tayi yayinda Almustapha yadubeshi yace don Allah ka kwaso mana gwala gwalan Ummina dakuma dukwasu sarkokinta tanan ne zamu samu kudin tafiya can din…
Shafa kan Almustapha yayi ahankali sannan yace to kujirani anan Allah yasa ba mutane sosai agurin…
Amin,nan suka samu gindin bishiya suka zauna yadan kwantar da kanta akan cinyar yarasa ta ina zai rarrrasheta,shibe iya rarrashiba besan ya akeyiba se sukayi shiru dukansu yayinda ita tana hawaye kadan kadan…….

Kukan nata harcikin ranshi yakeji don haka seya damke hannunshi tareda lumshe idanunshi sunkai two hours agurin kafin Mallam Hudu yadawo seda yarakasu kasuwa suka saida wasu sannan yarakasu chemist akayi mata dressing goshinta sannan suka shiga motar Maiduguri wanda daganan ne zasu wuce Chad din, alokacin da sukayi harkokinsu Allah yataimakesu labari begama baza gari ba……

Sanda suka Isa Chad mahaifin Khairiya yace bazai karbe ta ba don already yaji labarin komai taje tasayar da mutuncinta amatsayin Yar Babbar gida bakaramin kuka tasha ba sannan yace daga ranar ya yanke alaka da ita har abada sannan beyadda duk wani nashi yataimaketa ba,ahaka suka juyo Nigeria itada Almustapha don cewa tayi dole ma tasan yanda zatayi tasamu magana da Abdulrahman sede kash koda suka dawo Magajiya taki barinta kwata kwata seda tayi ta Mata magiya wanda kullum ah wajen masarautar suke kwana dukda kuwa cikin dake gareta sannan tabarta……
Bakaramin farin ciki tayiba da tasamu zataga Maimairtaba sede to her own surprise tunda tashiga gabanshi yanuna besanta ba amatsayin bakuwa yaganta tambayartama yayi damai zai taimaka mata sekawai tafara hawaye babu kakkautawa kallonta yashigayi ahankali seyaji yanason sanin miye matsalarta duk da baisanta ba seyakeji deep inside his heart yasanta kaman yanada wata alaka da ita sede besan na menene ba, Magajiya na ganin irin kallon da me martaba kema Khairiya setasa aka fitar da ita nan takaita side dinta sannan tace mata Mai Martaba yayi loosing memory dinshi due to the shock dayasamu na abunda yafaru sannan likita yace ba ason atuna mishi da abun yafaru sabida ze iya zama hadari ga rayuwarsa kuka Khairiya tashigayi tana innalillahi wainna ilaihir rajiun,wannan wace irin kaddarace ita yazatayi da rayuwarta….
Koina tashiga basauki anata hukunta ta akan laifin dabatasan dashiba……

tsaki Magajiya tayi sannan tace ke munafuka kiyi abu sannan kice ana hukuntaki akan abunda bakiyiba Mai Martaba yana cikin wannan halin ne adalilinki kinajina…..sabida haka babu ke babu zama amatsayin matarshi gwanda ma ki tattara kikoma inda kikafito zefiye miki don acikin garin babu inda zakije akarbe ki da mutunci wasuma yunkurin kasheki zasuyi…….
Sa hannu Khairiya tayi ah baki tana kuka sannan tace kitaimaka mini don Allah kada ku koreni anan banida gurin zuwa,banida inda yafi nan banason nayi nesa da Mai Martaba tsaki Magajiya tayi sannan tace bakida matsayi acikin masarautar nan sede in matsayin baiwa zaki zauna……

STORY CONTINUES BELOW


Cikin kuka tace wallahi nayarda,nayarda zan zauna amatsayin baiwa har lokacin da mai martaba zai gane ni ya fahimceni, murmushin mugunta Magajiya tayi sannan tace ko bayi sesunfiku daraja ah gidannan….. 1

Nayarda Magajiya,nayarda daduk sharrudan ki……

Hindatu najin duk abunda yafaru taje tasamu Waziri tafadamishi ga hukuncin da Magajiya ta yanke don haka yazo yasamu Magajiya yanuna mata abunda tayi bata kyauta ba Kuma indai yana ubanta baza ah mayar da Khairiya baiwa ba tunda Mai Martaba bashi ya yanke hukuncinnnan ba ana iya barinsu subar masarautar sunemi gun zuwa kokuma inzasu zauna se abasu Yar karamar gida cikin nan tunda ita ta bukata……

Dahaka aka yanke hukunci aka bama Khairiya wata Yar karamar gida acikin masarautar wanda ko talaka akabashi wannan gidan kyauta seyayi mita amma bata damuba fatanta kullum Maimairtaba yazo nemanta batada wani addu’a daya wuce wannan har Allah yasauketa lafiya tasamu yan biyu mata inda tasamusu Amira da Afiya….

Almustapha kuwa tunda haka tafaru aka haramtamishi zuwa duk wata makaranta ah garin don koyaje kullum cikin tsangwamarsa akeyi shi shegene,agida be hutaba haka ma ah school hakan kuma besa yataba fadawa mahaifiyarsa halin da akecikiba don aganinshi ze Kara mata wani damuwar ne bayan wanda take ciki ayanzu……

Haka rayuwa tacigaba harma daga karshe yadawo makarantar da aka gina ma ‘ya’yan bayin na cikin masarautar inda nan yakarasa secondary school dinshi,su Amira ma sunfara wayau alokacin sede suma gurinsu babu wata sassauci kullum cikin tsangwamarsu da zaginsu ake gakuma bayi da aka maida su na karfi da yaji……

Abinci ba abasu ah masarautar hakanan babu wani tallafi da akeyi musu, Mallam Hudu dai shine me taimakonsu da abinci sekuma dan dakon da Almustapha keyi mishi seyadan samu wani abu dahaka Almustaphan ya yanke shawarar shiga jami’ar Ahmadu Bello University koda kuwa cin namansa za anayi kullum acikin makarantar he needs to study,he need to be something better in life,he need to be independent shiyasa ya zana jamb and yafita da score mekyau inda babu bata lokaci
Suka bashi admission, MBBS daman abunda yayi applying kenan, Mallam Hudu ne yataimaka mishi gurin biyan kudin makaranta nan yafara, the first year dayayi ne smoothly with great result dukda kuwa yazama abun kyama ga kowa don rumor ake agari shi dan iskane Kamar uwarsa bashida aiki se lalata ‘ya’yan mutane da shaye shaye wanda duk wannan maganganun daga tushen Magajiya yafito, abun baya damun shi inda sabo yasaba yana living life dinshi all alone ne,gashi da kyau da aji ga Kuma ilimi uwa uba amma hakan besa mata suna xuwa kusa dashiba sabida kowa tsoronshi takeyi……
Ah second year dinne Ummin su tafara rashin lafiya har yakai ga tasamu stroke, bakaramin tashin hankali yashiga ba awannan lokacin haka suka kaita asibity anma babu kudin yi mata treatment don haka akayi dismissing dinsu wannan shine dalilin fara shaye shayen Almustapha sabida abubuwa sunmishi yawa,zafi yamishi yawa right from his childhood he experience alot and now it’s the matter of his Mother’s health he can’t bear loosing her,he want to protect her she’s all that yakedashi sede ta Ina zefara samo kudin?…
Babu,bashida abokin dazai tambaya,bashikuma da dan uwan dazai tambaya sannan be Isa yatambayi wani babban mutum agaribama sede awulakantashi don haka yashiga damuwa sosai wanda inbayasha kayan maye ba bayajin sassauci ah ranshi,anacikin hakane Sulaiman dake London bejima da tafiya ba yaji labarin rashin lafiyar Ummin don haka yasa akanemai number Mallam Hudu don Almustapha bashida waya(aganinshi inya rike wayar ma wazai Kira,wayane dashi dahar zeso jin muryar sa bayan kowa kyamatarsa yakeyi),bayan Sulaiman yayi magana da Mallam Hudu ne yaji matsalar komai sannan yace ze turo masa kudi amma kada yace ma Almustapha shiyaturo don bazai karba ba domin Sulaiman yalura Almustapha ja baya yake dashi sabida mahaifiyarshi shikuma har cikin ransa yakejin dan uwanshi Kuma yakeson shi tsakani da Allah…….

Ahaka akafara treatment din Ummi har aka rubuta mata drugs takesha, sannan yacigaba da zuwa school watanta uku ah asibity aka sallame ta haka suka dawo da ita gida sede adaga akwantar tun su Amira na shekara takwas suke wahala da mahaifiyarsu yayinda shikuma yake zuwa makaranta……

Suma Kuma sukanje nacikin masarautar ahaka rayuwa tacigaba, Almustapha nada kwazo wanda harsu kansu malaman sukanyi mamakin baiwar da Allah yayima yaron he never fails any course nor any practicals har final year dinsa wanda suna shirin gamawa,sede ranar da zasuyi final practical exams dinsu jikin Ummin shi yamatsa sosai suka koma asibity inda yayi missing exams din wanda hakan yayi leading to se yayi spill na karatunshi haka the following year din Kuma thesame exams dazaiyi ranar anbata masa rai seyasha giya yakwanta bacci beje yayi exams dinba se wannan shekarar dayasake yin registration yana fatan Allah yabashi ikon yin jarabawar yasamu yarabu da makarantar dama Kuma tsangwamar dayake sha acikinta wanda yayi almost 8years yanzun yana enduring…….yanason ya huta dana makarantar atleast amma abun yamishi yawa ga Magajiya ma bata barshi ba sharrin yau daban na gobe daban,mutanen gari ma insun debo talaucinsu suzo sumishi sharrin sata ahukuntashi sannan abiyasu…..
Sulaiman kuwa tunda yatafi yaki zuwa gida sabida wani manufa da Magajiya tasa agaba wanda shi anashi ganin bazai iya cika mata burinta ba abu daya yasani babu wanda throne dinnan ya cancanta da kaman Almustapha sabida duk wani rumor da akeyi daduk wani magan gane magan gane da akeyi betaba sama ranshi Almustapha ba dan uwanshi na jini bane Kuma har abada babu mai ciremishi wannan raayi shiyasa yadaukar ma kanshi alkawari no matter how hard it may be shibazai karbi sarautan Zazzau ba face Yayanshi Almustapha wannan kenan…..

*★*★

Yana zaune akan wani fancy chair, yanzu yafito daga practicals jikin shi sanye da labcoat yayinda idanunshi kesanye da eye glasses,lumshe idanunshi yayi ahankali yana tunanin duniyar baki dayanta dama abubuwan dake cikinta dakuma irin rayuwar dayayi tun sanda yayi wayau,yasandai 12years of his life shidan gata ne babu abunda yanema yarasa,kowa sonshi yakeyi hakanan kowa nan nan yake yi dayi he never thought for once his life will turn out to be this way tunda yake betaba sama ranshi zeyi wahala irin wanda yakeyi ayanzu ba,shiyasa akace never be too proud of who you’re because everything can change,inma kudi kake ji dashi ze iya karewa hakanan inma mulki kake ji dashi shima karshenta na iya zuwa tunda akwai mutuwa,akwai rashin lafiya akwai Kuma fin karfi,sannan duk mulkin ka ko arzikinka kada ka wulakanta nakasa dakai because you might end up being like them,ya yarda dawannan maganar tunda gashi shi akaran kanshi yafaru bama akan wani ba….from sanda yake da shekaru 12 zuwa yau dayake da shekaru 29 yana neman talatin, meaning shekaru 17 kenan rabonshi dasamun farin ciki he has been in this situation for good 17 years yana iyacewa acikin shekarun babu ranar dayayi murmushi wanda yakai har cikin zuci sedai yayi na yake ahankali yafurta “when will all this come to an end”kafin ya furzar da iska ahankali….
Sekuma dayar bangaren zuciyarshi tace”very soon Imamu Almustapha,very soon in Sha Allah”………
Bude idanunshi yayi daga lumshesun dayayi sannan yadubi wristwatch din hannunshi dasauri yatashi don tunawa dayayi lokacin shan maganin Umminsu yayi ahaka yafara tafiya don yawuce gida duk inda yawuce seyaji ana kuskus kokuma ah tsaya ana kallonsa ko wasu na nuna shi,shi abunma mamaki yakebashi dubada yanda mutane basudamu da nasu al amurarba sannan baswa duba nasu flaws din sena wani.abu dayane yasani cikin su babu mai kusantar shi da maganan duka kowani abu so far as he’s in his right senses sede suzage shi ko su fadamai maganar banza wanda shikuma ko kallo basu isheshiba,the only state dasu ke ci mishi mutunci shine when he’s drunk…… +

Ayanzu ma tafiya yakeyi yanashirin barin harabar makarantar wasu yan mata ne agabanshi suna tahowa ‘dayar se kallonshi takeyi kamar wanda zata cinye shi lura da abunda takeyinne yasa tagefen nata tayi saurin rike hannunta gam tanacewa muyi sauri Aisha mudauko kayan kada tailor dinnan yagudu……
Wabce hannunta Aisha tayi sannan tace Bebe kibarni bakiga hadadden gayen dana gani bane takarashe maganar tanashirin zuwa gurin Almustapha,damkota
Muniba tayi cikin sauri sannan taje saitin kunnenta tana”don ubanki inkinaso kigama anfani ah idon duniya sekije ki ai”….
Dasauri Aisha takalli kawartata with questionable look irin bangane me kike fadi ba,cikin rada da tsoro Muniban tace shine Yarima Almustapha Aisha,aituni jikin Aisha yafara ‘bari sema tayi gaba tabar Muniba agurin tana yau na shiga uku na lalace Muniba cewa fa akayi inmutum ya yarda yahada ido dashi toseyayi anfani dashi,nashigesu na Allah yasa bamu hada idanuba Aisha takarashe maganar kaman zatayi kuka tana tatttaba fuskarta……
Yar dariya Muniba tayi sannan tace keba uwar jaraban son maza ba sekin debo ma kanki ai…..

Wallahi nadaina Muniba dagayau kawai yamin kyau ne shiyasa,danasan shine Almustapha koma nasan zamu hada hanya aiko makarantar ku bazan zo ba,nikam wace irin kaddarace takawoni cikn SAMARU yau,dariya Muniba tayi harda rike ciki tana to ya isheki Kuma kina exaggerating abun kuma…..

Duka Aishan takaima Muniba din don ubanki ba dole ba dondai baki taba jin abunda ake fada akanshi baneba shiyasa and it happens I swear because har hukuntashi mahaifinsa yakeyi…….ammadai yayi asara,ga kudi,ga kyau,ga iya gayu amma yasa ma kanshi wannan jarabar wannan wace irin rayuwace kaman ancema yana tsafi ko Muniba?……..

Tsaki Muniban tayi sannan tace ke matsalata dake yawan surutu nima bansani ba I just know that ko hanya banason hadawa dashi sabida halayensa danake jin labari,kede kibar zancen kawai kadama muja ma kanmu,zomuje indauko kayan mukoma gurin macucin tailor dinkin nan……
To nadaina Aishan tafada cikeda fuskar tausayi daka ganta kasan ah tsorace take baki dayanta….

Sanda ya isa gida samun su Amira yayi suna cin abinci,sannu dazuwa sukayi mishi sannan Amiran tazubo mishi abinci bedamu da kanshi ba matsawa yayi kusada Ummin sannan yajingina mata pillow ya kwantar da’ita ajikinshi sannan yayima Amiran alama data miko mishi plate din abincin haka yashiga bama Ummin abinci tanaci ahankali harseda tanuna takoshi sannan yadauki drugs din yabata tasha…….
Kallon fuskarta yayi sannan yace ahankali kaman wanda bayason magana”How are you feeling Mother?”……
Lumshe idanunta tayi alamun dasauki,bekuma cewa komai ba sema cigaba da kwanciya datayi ah jikinsa yanajin su Afiya suna hira abunsu jefi jefi kallonsu yashiga yi cikeda tausayin kannen nashi…….

*****
Sadiq da Munir na playing game agaban Tv yayinda Asma’u tana ironing school uniform dinsu Aliyu yashigo yana dariya kasa kasa”wai ina Asmeey ne”…..
Turo baki tayi tanajinshi taki kula shi don tasan yaganta neman magana kawai yakeyi kara daga muryarsa yayi “Asma’u!,wai inatake ne yadubi su Sadiq dasuke game yace bakuji ina neman Ma’u bane dabazakuje ku kiramin itaba”…..
Sadiq ne yace Allah Yaya Aliyu bamujiba hankalin mu baya gunka we were busy playing game…….
Eh ai daman ku inkuka fara game ba asamun hankalin ku maza kukaje kuka kiramin ita yanzu if not nakwace kayan game din Kuma bazan bakuba kwana kusa…..
Munir ne yatashi dazuman yaje yakirata don yaman tama tana guga ah parlourn nan yayi arba da ita turo baki yayi sannan yakoma mazaunin shi ashema gatanan……
Adda kinaji anata kiranki shine kikayi shiru,harara ta dalla mai sannan tace ai yaganni ….
Dariya Aliyun yayi sannan yazauna ah kujerar dake kusa da inda take gugan yace”lallai yarinyar nan kinraina ni wallahi,innaganki zanta kwalla miki kirane?,kodan Kinga muna sonki shine kike mana yanga…..
Kai Yaya Aliyu nifa bahaka bane ba…..

STORY CONTINUES BELOW


Ware hannu yayi sannan yace to miyene,ai na miki text cewa he’ll be coming this evening amma kinayi kaman bakiga massage din ba,nakuma Kira ki several times baki dauka ba…..
recently nagani kuma Ummi tasani aiki, hararanta yayi sannan yace kiyima Ummi sharri kinji,ba laifin ki bane don Kinga abokina yanason kine…..

Yar dariya tayi sannan tace nashiga uku Yaya Aliyu kanasani inajin kunya…..
Rankwashi yakai mata,kunyar banza inzaki tashi kije kishirya gwandama kitashi don yadameni wallahi….
Kashe socket din tayi sannan tace nifa kabashi hakuri babu inda zani Allah,Inka takuramin zanfada ma Mommy wallahi……

Rike baki yayi yana kallonta sannan yace ke ai bantaba ganin bakauye irinki ba wallahi dama Asiya yace yanaso dukda rashin kunyarta bazan ji haushi ba because bazata watsamin kasa ah idanu ba….
Murmushi tayi sannan taninke sallayar datayi gugan kai tana naji bakomai yanzuma se inkirata taje be baciba, tashi yayi yana banaso nima inada baki da kafafuna kekuma kiyita zama kina koran samari naga ranar aurenki ….
Dariya kawai tayi batareda tace mishi komai ba har ya isa bakin kofa yajuyo yana Darling Sisto tsayamana….
Juyowa tayi tana kallonshi ‘dan marairaice fuska yayi yana taba cikinshi…
“Allah tunsafe cikin nan bega komaiba”…..
Dariya tayi”kaje Asiya tanema ma abinci mana”…
Sake marairaice murya yayi kaman Karamin yaro”haba Yar kanwata shalelen Daddy,Ummi da Mommy kitaimaka mana”….
Toshe kunnuwanta tayi tana dariya”Kai Yaya Aliyu Matarka tashiga uku da zakin baki”,kanne mata ido daya yayi sannan yace”ance miki nidin nawasa ne…….
to naji barina ajiye kayan nan zanzuba insa akawoma don bazan yarda inhadu ma da abokin ka ba inma wayau kakemin…..
Dafe Kai yayi don ya lura plan dinshi couldn’t work se kawai yayi gaba abunshi…..
****
Kuka take sosai wanda tundazu Laure kanta takasa lallashinta don haka tatashi don zuwa ta sanar ma Magajiya ah bangarenta,tana shiga ta zube kasa tana mika gaisuwa sannan tace Uwargijiyata akwai matsala….
Kallonta Magajiyan tayi cikeda damuwa sannan tace inajinki….
Kai tsaye Laure tace Gimbiya Hamida ke kuka tun dazun nakasa lallashinta,tashi Magajiyan tayi sannan Lauren tabi bayanta nansuka fice zuwa side din Hamidan duk inda suka wuce bayi nazubewa kasa suna mika gaisuwa koda suka isa Laure daga waje ta tsaya yayinda sauran ma suka fito don basu guri……..
Zama Magajiyan tayi gefen Hamidan yayinda tayi saurin fadawa jikinta tana kuka Mama yadaina sona,wai yafasa aurena bansan yazanyi ba bazan iya rayuwa babushiba…….
Bubbuga bayanta Magajiya tadingayi ahankali tana comforting dinta seda tayi shiru sannan tace dago ki kalleni Hamida, ahankali tadago tana duban mahaifiyar tata”yanzukam inaganin yakamata kihakura da Sa’id dinnan tunda shi bainuna dagaske yakeyiba daman tunda mun zuba miki ido ne kuma bawai daman munasonki dashi ne ba,kina Yar gidan sarauta Yar babban gida kyaunta kishiga irin wannan gidan,Hamida ‘ya’yan sarakuna nawa sukazo neman auren ki amma kika bujure…
tukunnan kinaduba shekarunki kuwa,kina neman ashirin da shida yanzu babu maganar dabamaji ah gari amma ahaka muka toshe kunnenmu mukayi kaman bamuji ba to ya Isa hakanan Hamida, you’ve to think twice yakamata kiyima kanki fada zanbaki nan da sati biyu kiyi tunani inbaki samu mafita ba nikuma zanyi ma Maimartaba magana yabama daya daga cikin masu neman auren ki izini su turo……
Kuka sosai Hamidan keyi “Mama karkimin haka shikadai nikeso bazan iya rayuwa inbabu Shiba”….
Lumshe idanu Magajiya tayi sannan tace munmiki kokari ai,Kuma bana ganin Sa’id nada niyar aurenki sabida haka kiyi hakuri kawai ‘yata haka tacigaba da rarrashinta hartayi shiru tasan inbahaka tayima Hamidan ba bazata dawo cikin hankalinta ba yanzu kusan shekara goma suna tareda Sa’id amma kullum akayi maganar aure seya kauce gashidai shiba dan kowa……

****

Koda Magajiya takoma sashinta sega talatu tazo nan tazube gabanta tana mika gaisuwa kafin Magajiya tabata izinin zama…..
Kallonta Magajiyan tayi sannan tace wani labari kika kawomin?…..
Numfasawa talatu tayi sannan tace Uwargijiyata yau sati biyu kenan rabon da Yarima Almustapha yasha kayan maye…..
wani tsawa Magajiya ta daka mata”don ubanki waye Yariman?”….
Jiki na ‘bari tace yi hakuri ranki shi dade subutar bakine……
tsaki Magajiyan tayi sannan tace “naji tashi ki tafi sannan kifada ma Hilun yacigaba dasamin idanu aduk wani al amuransa banason yabata komai”…..
In Sha Allah zan fada masa nagode!…
Tsaki Magajiya takumayi sannan tace tashi kitafi yau kin batamin rai sabida haka baki da kyauta,jiki ah sanyaye ta tashi tafice ah dakin bayan fitarta ne Magajiya tayi bangaren Mai Martaba seda akayimata iso sannan tashiga fadar nashi nacikin gida nan kowa ya watse yabarsu su biyu,gaishe shi tayi irin tasu ta sarauta sannan tanemi guri tazauna…..
Dakaga sarki Abdulrahman kaga Sulaiman sabida irin matukar kaman dasukeyi,dubanta yayi ahankali sannan yace Yayana yace miki gobe zesauka ah kaduna?…..
Sunan da mai martaba ke Kiran Sulaiman din dashi kenan…..
Aa Mai martaba befada min ba munyi kwana biyu bamuyi wayaba, toshikenan gobe in Allah ya yarda zedawo gida……
Bakaramin dadin news din tajiba amma se batawani nuna ba tace Allah yakaimu goben….
Amin ya amsa, sannan tace nabarka lafiya Mai Martaba….
Murmushi kawai yamata inda tafice kaman tayi tsalle tsabar murna, finally Sulaiman zaidawo gida, finally burinta yakusa cika………
****
Gudu take sosai tundaga side dinsu seda ta iso side din Mommyn sannan tatsaya tana haki,samunsu tayi ah parlour baje anata hira at thesame time kuma ana kallo, Mommy ne tadubeta lafiya Husna wannan uban haki dakike tayi din gudun duk na menene?…..
Cikin hakin tace Mommy ina Asiya take, Asiya dayanzu tashigo parlourn tace gani Miyene kike nemana?….
Dagudu Asma’un takarasa gareta tareda rungumeta tana tsalle Aseey kinsamu admission,anbaki Mass communication,wani ihu Asiya tasaki tareda kankame yar uwarta nan suka shiga murna can tasaketa tana waya fada miki don Allah Sis?…..
Jan hancinta Asma’un tayi sannan tace Yaya Aslam mana yanata kiran wayarki baki daukaba wai, Allah sarki banganiba nashiga bandaki ne, I’m so!so happy finally burina yakusa cika takarashe maganar tana kara kankame yar uwarta…….
Dariya yan parlour kowa keyi fuskarsu daukeda annuri, Mubaraq ne yayi gyaran murya yana”toke uwar gayyan taya wasu murna baki duba naki bane?”….

STORY CONTINUES BELOW


Sakan baki tayi don ita seda yayi magana ma sannan ta tuna itamafa neman admission din take,she was just so happy for her sister that tamanta danatama sabida tasan irin yanda Asiya keson zama news caster tun tana karama wannan shine burinta, ahankali tadan dafe kanta Allah Yaya Mubaraq nama manta….
Jijjiga Kai yayi in disbelief sannan yace Asma’u you’re unbelievable ah swear,Ina jamb slip din naki?…..
Yana gurin Asiyan duka, Asiya ina nawa?…..
Dan shiru Asiya tayi sannan tace nikika bama daman, bana tunanin yana gurina, Allah kena bama ki ajiyemana Asiya sede inkin manta ne takarashe maganar with assurance don ita tasan ita tabama…
Tonidai baki baniba kedai kinyarda awani gurin ki don ni nawa tun ranar nabama Yaya Aslam ya ajiye akan inyaji admission yafito yaduba mini……
Nan take idanun Asma’u yaciko da kwalla don tana da tabbacin tabata, Hajja ne tace ah to kinjidai ita ah mijin dazata aura tabawa wayasani kokema cikin samarin ki kikabama kin kasa tuna waye ne……
wannan karon kasa controlling tears din ta tayi Musa ne yace Asiya inbaki fita ah parlourn nan yanzu kinnemo jamb slip dinnan ba zanjimaki ciwo acikin gidan nan,wawiya marar hankali kawai,ke bakisan darajar yar uwarki ba, you’re so selfish that you only know about yourself….
Dakikiya kawai cewar Mubaraq,fita tayi tana kumbura baki yayinda Aliyu yayi inda Asma’un take yariko hannun ta sorry Ma’u kidaina kuka za agani……
Goge kwallarta tashiga yi batareda tace komai ba,ran Mubaraq yayi matukar baci jin yanda Hajja keta mitan an takurama Asiya,abun murna yasame tama bazasu tayata murnaba sun bata mata rai,tsaki yayi sannan yace ai daman ke Hajja Asiya kadai kikasani acikin gidan nan sannan yafice yabar gidan batareda yasakema kowa magana ba…….
Suna nan zaune shiru wurin minti talatin sega Mubaraq din yashigo yana waya sannan yadubi Asma’un yace MBBS kikayi applying ko?…

Jijjiga mishi Kai tayi alamar eh,dan murmushi yayi sannan yafadima wanda suke wayar full name nata da course din kuma…..
To sena jika Musbahu,sorry nasaka shiga school da daddaren nan….
Ah dayan bangaren abokin yace kada kadamu kaikam, I’m at the school already I’ll get back to you as soon as nagani….
To sena jika nan Mubaraq yasamu guri yazauna yace akwai lecturer danasani ah medical college din yanama cikin school din naroke shi yaduba admission status dinnaki inyaso gobe semu ciro sabon jamb slip din because I’m very sure wannan wawiyar ta batar dashi……
To kawai tace mishi, Mommy ne tashiga lallashinta tana tayi hakuri yayinda Musa yace kuce munkusa samun likita ah gida……

Dariya tayi, Aliyu na cabdi aiko suma nake ina farfadowa bazan yarda wannan figigiyar ta dubaniba,turo baki tayi gaba sannan tace kai Yaya Aliyu tunban samu admission dinbama…..

Dariya sukayi duka, yayinda Mommy tace we trust you Daughter in Sha Allah kinsamu ma…..
Mommy kidaina fasa mata Kai wannan karan Aliyu ne yayi magana,hararanshi tayi yayinda Mubaraq yace wai nikam tsaya Aliyu,kwana biyun nan wani irin tsama kukeyi da Ma’u ne naga kunsa juna agaba….
Dariya tayi sannan tace Yaya Mubaraq barni da Yaya Aliyun nan nine dede dashi….
Gwaliyo yamata yana”kede kice inrufa miki asiri bakyason aji me ake ciki shine kikeneman rufe mini”…
Alama tayi mishi da yayi shiru kada yafada suji… Mommy na lura se suka tuntsure da dariya Musa cikeda zolaya yace ankusa kawo mana goro kenan!….
Tashi tayi zata gudu yayinda phone din Mubaraq yayi ringing ai ah sukwane tadawo tazauna, dariya Mubaraq yayi sannan yayi picking call din daga yanayin yanda yake maganar zaka tabbatar tasamu admission din yana ajiye wayar yace”congratulations Doctor in making”,wani tsalle tayi tafada jikin Mommy tana murna,rungumeta Mommyn tayi tana I’m happy for you child,tsaki Hajja tayi ta tashi tashige ciki tana mita…..seda sukayi murnar su me isansu sannan Mommyn tace takira Asiya suje sufada ma Daddyn su…..
Haka suka tafi don fadamishi sosai yamusu murna, sannan yace yaushe za afara registration Kuma?….
Atare sukace Monday Daddy,Yar dariya yayi sannan yace duk wannan zumudin shiga jami’an ne Daughters?…..
Dariya kawai sukayi batareda sun yi magana ba, I’m happy for you both Allah yasanya albarka ranar Monday din seku fara ko?ga yayunku they’ll help you out…..
To Daddy nan sukayi mishi saida safe sannan suka koma bangaren Mommy din, Asma’u ne tamusu sallama nan Mommy tace to Daughter gobe akwae zuwa kasuwa fa zaki rakani dai ko?……
Cikeda jindadi tace zanje Mommy dama najima banje kasuwaba……
To Allah yakaimu…
Amin,nan tayi musu saida safe tafice….

STORY CONTINUES BELOW


Tunda ta tashi da safe tayi ma Ummi share share sannan tayi wanke wanke tagyare ko ina tas tasa turaren wuta, around 8:30am Ummi ta tashi daga bacci don ba ita keda girkiba yau.sanda tafito parlour ta iske koina se kamshin turaren wuta yakeyi su Munir suntafi islamiyan safe kasancewar yau asabar babu na yanma se safe kawai,ikram ce kawai ah kwance tsakiyar parlourn tana tsotsan ‘dan yatsan ta tana kallon cartoon …

Ummin ne tace Autan Mami Ina Addanku don ba kasafai Ummi tacika Kiran Asma’u dasunata ba kasancewarta ‘yar fari…
Cikin ragwabarbiyar maganarta tace”cana ‘yaki Ummi”….
Juyawa tayi tabar ikram din kwance gun ah daki tasamu Asma’un tafito daga wanka se cancanda kwalliya takeyi,ware idanu Ummin tayi sannan tace “tashi da sassafen dakuma wannan kwalliyar duk na menene wai?”….
‘yar dariya tayi cikin ko inkula tace Ummi kasuwa zamuje da Mommy….

Hararanta Ummin tayi sannan tace yaushe Mommyn tace zakuje kasuwa?…
Kai tsaye tace jiya da daddare tafada min kafin inbaro side dinsu mantawa nayi ban fada miki ba we were carried away by maganar admission dina…….
to amma dasafe zakuje kasuwan ne?…..
Nima bansani ba Ummi,tsaki Ummin tayi sannan tace kekam ba a rabaki da halin yan fari wallahi don ance za aje kasuwa kawai se kikayi concluding dasafe za aje Kuma fisabilillahi zuwa kasuwar ne duk wannan kwalliyar?….

Turo baki tayi Kai Ummi sekace yau kikasaba ganina Ina kwalliya…dariya Ummin tayi sannan tace bayau nasaba gani bakam kuma ahakan in anyi kwalliyar adauki niqab ah kwakuma ba…..
Sa hannu tayi tarufe fuskarta tana yar dariya”Allah Ummi inason kwalliyan sede bana iya fita dashi ah fuskana shiyasa duk randa nayi nakesa niqab”….
To sannu bagidajiya dakekam mummuna ce danashigesu na,don zanga ta ina saurayi zeganki ba kwalliya yace yanaso,yanzu tunda babu zuwa kasuwan baccin asarar za akomane?…..

Aa Ummi senaje gun Mommyn tukunnan inji sanda zamu fita,to ke kikasani dai aini yau naji dadin batun kasuwan nan don ko ba komai ai anyimin fefes da gida dawuri basai antashi daga asararren baccin nan ba…..
Kayanta tashiga sawa tana yar dariya tareda addu’an Allah yasa kasuwarnan dasafe za aje ba saida yanma ba aikuwa tana gama shiri tayi bangaren Mommy bayan sun gaisa ne Mommy tace Daughter badai shirin kasuwarne wannan ba…..

Eh Mommy harna shirya koba dasafennan zamujeba?….
Seda yanma ai kinsan bakowa za asamu da safen nanba kuma customer na ma nasan befito ba yanzun hakana inyamuran danasaba sayan Kayansu bazamu samesu ba kibari se bayan laasar…..
To Mommy Allah yakaimu,Amin Daughter……
Barina shiga gurin Asiya to….
Tana daki kinsanta sarkin chatting.

*****
Yanzu fitowanshi daga cikin masarautar zewuce kasuwa to his own surprise seyaji Karan motaci sunfito daga haraban gidan bejuyaba hakanan bedaina tafiyar dayakeyiba,haka motocin sukazo suka wuce tagabanshi sunkai biyar seyake mamakin Ina Mai Martaba zeje dayanman nan don yasan yawancin tafiyanshi inzeyi dasafe ne,abunda besani ba za aje tarban Sulaiman ne ah airport din kaduna…
Koda ya Isa kasuwan samun guri yayi yazauna ah gefen shagon Mallam Hudun shiko Mallam Hudun kwata kwata besan dazuwanshi ba sabida he’s busy attending to his customers don yau customers sunyi yawan da ‘ya’yan aikin shi ma duka aiki sukeyi,yana da babban shago ne acikin kasuwar wanda kuma Allah yayi mishi farin jini sabida iya kasuwancin shi dakuma rashin tsawallawa Kaya kudi…….
Mahdi ne daya daga cikin ‘ya’yan shagon yace Mai gidana Yarima yazo yana waje ko ince yashigone…..
Aa Mahdi barshi innagama zansamo shi don wannan ko kashigo min dashi sede ya koremin customers da rashin maganarsa……
Dariya Hajiya Zainab tayi “haba customer yakore ma customers kuma sabida rashin magana, shidin kurma ne?”….
Dariya Mallam Hudu yayi sannan yace Hajiya tsantsan miskilanci ne wallahi magana wahala takeyi masa…..
Ah lallai sede miskilancin kam cewar Mommy sannan tace nikam akwai semolina ne?….
Eh akwai Hajiya buhu nawa kike so,dariya tayi kaidai customer ba a rabaka da abun dariya……
Asma’u dake gefe duka tanajin conversation dinsu setaji tanason sanin wanene wannan miskilin,miyasa magana take yimasa wahala,daman akwai irin mutanen nan aduniya wanda har magana ma wahala zatayi musu,to kode dan masu kudi ne don sune takeji anacewa sunada dagun kai da girman kai…….
Tana cikin wannan tunanin ne Mommy tace nikam Daughter munada sauran Maggi ne agida?…..
Eh Mommy amma inaganin ya kusa karewa,to shikenan bari musaya kawai banason sayan gutsul gutsul dinnan nan Mommy tajuya tace ah miko mata Maggi packet goma seda suka gama sayayyarsu tas akayi lissafi suka bada kudi sannan Mommy tace afitar musu da kayan asa ah Mota, Mahdi yafara daukan kayan yana ajiyewa agaban shagon seda yagama sannan yaxo yafara dauka yanasawa ah Mota duka Almustapha na kallonshi ganin kayan bana karewa bane seya tashi cikin takunshi na kasaita ya nufi kayan dede lokacin su Asma’u suka fito tabbas taganshi daga yanda yake tafiya batayi tunanin dan dako bane setaji tanason ganin fuskarshi hanyar inda suke tanufa yayinda Mommy tace Daughter zomu duba shagon nan kozan samu irin curry dincan dayakare…..
To Mommy,babu yanda ta iya haka tabi Mommyn shiko suna gama sa kayan ah mota yakoma mazauninshi bayan sun sayi curry dinne sukadawo suka shige mota don tafiya se dube dube takeyi kozata ganshi sede unfortunately bataga ko wulgawarsa ba dan tsaki tayi tareda bugun kanta sannan tace”to inaruwanki dashi for goodness sake, he’s a stranger Asma’u”……
Mommy ne tadube ta jin tayi magana, kekuma dawa?….
Dasauri tace babu Mommy nagajine kawai……dariya Mommyn tayi sannan tace sannu Daughter aidanasan zaki wahala dabamu zo tareba…..
Kaman ance ta daga idanunta carab se cikin nashi….
jitayi gabanta yashiga dukan uku uku batareda tasan dalili ba dasauri tadauke kanta still zuciyarta baidaina dukan uku ukun dayakeyiba,dan ajiyan zuciya tayi yayinda batasan sanda zuciyarta ke maimaita mata cikin wata sauti cewa he’s handsome runtse idanunta tayi ahankali gabadaya takasa focusing setake tunanin ko har yanzu kallonta yakeyi juyawa tayi ahankali kaman barauniya setaga tasake arba da kyawawan idanunshi sake saurin dauke kanta tayi wannan karan ambaton sunan Allah tashigayi don bugun zuciyar ta karuwa yayi….bayan yan wasu sakanni seta sake tsintan kanta da sake kallon direction din dayake wannan karan ma sake hada idanu sukayi,sede ayanzu abun haushi yabata tareda bata mata rai aranta take fadin”lallai wannan bayida manners kwata kwata,nama kamashi yana kallona amma ko kunya baijiba bare yayi tunanin dauke Kansa cikeda bacin rai tasake kallon inda yaken still itan yake kallo murkudamai baki tayi tareda sakarmai wata muguwar harara sede abun mamaki ko gezau beyi ba barema yasan tanayi,mamaki ne yakamata seta dan daga hannunta tana dan waving mashi taga kozai yi responding anma shiru,jiki ah sanyaye tamaida kanta kasa yayinda alokacin Kuma motarsu ta tashi dasauri tajuya tana sake kallonshi setaga still same direction yake kallo……
Seyanzu tagane cewa he was not looking at her,yes his direction na gareta sede gabadaya hankalinshi bayakanta infact yatafi wata duniya ce da ita kanta batasani ba,duniyar dashi kadai yasan halin da yake ciki cikeda damuwa tafurta”what could he be thinking haka?”….dan furzar da iska tayi tareda lumshe idanunta ahankali sede me duk rufe idanun dazatayi fuskarshi take gani,bude idanuntayi dasauri tana innalillahi wainna ilaihir rajiun azuciyarta tana addu’ar Allah yasa ba gamo tayi da aljani ba…… +

*****
Tunda yasauka daga matakalar jirgin yakejin wata fresh air nadaban wanda bai taba jin irinshi ba tareda wani irin sabon feelings,that feelings of being home,furzar da iskan bakinshi yayi ahankali sannan yashiga karema filin jirgin kallo tabbas acikin shekarun dayayi bayanan kasarshi tacanza sosai Kuma ansamu cigaba dubada yanda yaga airport din yagyaru sannan dayanda akayi modernizing nashi bakamar daba ahankali yacigaba da takawa har ya iso gurin tarban matafiya dogaye ne suka zube agabanshi suna mika mishi gaisuwa tareda yimishi maraba dazuwa mahaifarsa,kasarmu Nigeria me tattare da dumbin albarka haka yacigaba da tafiya yayinda wasu daga cikin dogarayen suka mara mai ba sanda ya isa yaga jerin motocin seda yaji gabanshi yafadi aziciyarshi yana “meyakaishi,dama bece ze dawo ba”…
‘dan tsaki yayi yashiga motar sannan ya furzar da iska”back to prison”……
Haka suka kama hanyar Zaria yana kishingide ajikin seat din motar wayarshi ne tashiga Kara babu kakkautawa,duban wayan yayi daya daga cikin yan matanshi ne na holewa yana katsewa sega wani Kiran kuma……
Murmushi yasaki sannan yadan furta”I’ll surely miss your company girls”,sekuma yadanyi tsaki don tabbas yasan akwai matsala besan ranar komawarshi America ba hakana Kuma shiba mai hakuri bane gurin rashin mata akusa dashi……
Shiyasa yake tunanin yanda zasuyi rigima da Magajiya Kam….

Tunda suka iso masarautar yaga angyarata tsab anyi mata kwalliya yayinda dogaraye tundaga bakin kofa suke zubewa kasa suna mika gaisuwa gakuma kide kide da akeyi irin na sarauta parking motar akayi ah parking space kafin aka bude mishi motar yafito nanma gaisuwa tako ina yi mishi akeyi, Magajiya damai Martaba dasuke tsaye can gefe baki yaki rufuwa ya hango su ahankali yadinga takawa garesu, he hate being caged in here sede abu daya yasani by just looking at their faces seyaji duk wani bacin ranshi yatafi tabbas yayi kewarsu, indeed there is no place like home yanazuwa gabansu ya hadesu duka guridaya ya rungume cikeda jin dadi………
Nayi kewarku Mama da Abba na…..
Shafa kanshi Mai Martaba yashigayi ahankali yayinda Hamida tace to nima abani hug dinnan mana little kani,yar dariya yasaki tareda ‘dan goge kwallar farin cikin data dan xubo mishi sannan yasake su yakarasa gareta tareda rungumeta”I missed you big sisy,so much”……
Nima nayi kewar naughtiness dinka,dan ware idanu yayi
yana Allah?…
Aiko nadawo Kuma zancigaba daga inda natsaya…..
Murmushi kawai tayi yayinda suka dunguma sukayi cikin masarautar anata kide kide da rawe rawe duk inda sukabi bayi da dogaraye sesun mika gaisuwa………
Ahankali yadubi bangaren da gidan su Almustapha yake yanason ganinshi dama ‘yan kannenshi sede be isaba ah yanzukam inbadai yanason tashin hankali bane don haka yabisu suka cigaba da tafiya ….

STORY CONTINUES BELOW


★*★

Tunda suka dawo daga kasuwar taketa ma Ummin ta complain ita tagaji, Ummin jin tagaji da complain dintane tace “wai nikam yau kika fara zuwa kasuwa ne ?”…..
Dan turo baki tayi Ummi nayau din na daban ne, Allah munyi yawo sosai,to sannu cewar Ummi sannan takara da sekije kiyi wanka kafin akira sallar maghrib ko…..
To nan ta tashi tashige cikin gida don watsa ruwan seda tayi sallar isha sannan tafito batasamu Ummi ba don yau itake da girki probably ta tafi bangaren mahaifinsu…..
Aliyu, Musa da Sadiq ne suka shigo suna hirarsu gwanin ban shaawa,bajewa sukayi ah parlourn inda hayaniya tayi yawa batajin mema ake fada ah TV din don haka ta tashi don tafiya, Aliyu ne yace kekuma yau bakin hali kikejin yi?…..
Aa Yaya Aliyu zamufara ko?…
Dariya yayi sannan yace nayi shiru to kije ki kunshe ah daki kamar taliya…..
Dariya kawai tayi sannan tawuce abunta don tasan neman magana ce kawai koda tashiga dakin wayarta ne tashiga Kara Kuma bakuwar number,tsaki tayi don ba tun yau number kedamunta da Kira ba tareda turo mata wasu sakonni marasa Kai da gindi babu ma abunda yafi ci mata rai dayawuce da tanemi sanin wayene se aka ki fadamata yanzuma wani Kiran ne yashigo kawai setayi deciding kashe wayar tareda kwanciya don yin bacci sede abun ya faskara data rufe idanunta fuskarshi take gani, innalillahi wainna ilaihir rajiun tacigaba da nanatawa aranta tana addu’a itakam anya ba gamo tayi da jinnu ba?……

*****
Seda dare ya tsala sosai sannan yafito daga shashin shi hannunshi rikeda car keys dogarayen ne sukayi niyar binshi yayinda yace musu aa shikadai yakeson fita, side dinsu Almustaphan yanufa harzai shiga seya duba agogo karfe shabiyu na dare ne seyayi tunanin by now sunyi bacci zebari da asuba kawai yanemi Almustapha din sesuje tare,juyawa yayi ze koma bangarenshi seyaji yanason zuwa club Kuma yaje yayi harka don haka yanufi motarshi yatadata yafice daga masarautar sanda ya Isa club din se casu akeyi dan murmushi yasaki yasan bazai samu kaman can ba amma yaya zaiyi ahankali yakarasa wurin bar man din yanamishi maganar yamiko masa beer….
To Oga inazuwa,samun guri yayi yazauna wani saurayi yagani gefenshi yashawu sosai kuma secewa yakeyi akaromasa……
Tsaki Bar Man din yayi sannan yace bazan Kara ba wallahi sokake Oga na yakoreni kenan, baka biya na jiyaba nayauma baka kai ga biya ba tukun Kuma sesawa kake inakara baka wannan wace irin jaraba ce?…….
Murmushi Sulaiman yayi sannan yace nawa ne kudin nasa zan biya,kallonshi Bar Man din yayi tareda washe baki”ah to ai shikenan ka hutasheni wallahi”,sekuma yadubi Almustaphan yace daga yau kada kayarda kasake zuwa don bazan iya harkar bashiba…..
Yar dariya Almustaphan yayi tareda nuna Bar Man din da ‘dan yatsanshi cikin maye yana “Kai,ni sa’an ka ne?”……
Jin muryarshi ne yasa Sulaiman din saurin juyawa nanko yayi arba da ‘Dan uwanshi,mutsutsuke idanunshi yakuma yi don ya tabbatar da abunda idanunsa yagane masa aikuwa shidinne cikeda tashin hankali yayi kanshi yana Yaya Almustapha meyakawo ka nan?…
Subhanallah what the hell are you doing here,yayi masa tambayar cikeda tashin hankali don inkwana wani zeyi yana fada masa yaga Almustapha ah irin wannan gurin to bazai yarda ba, Almustaphan ne cikin rashin karfi yadan ture Sulaiman din dakyar ya iyacewa “waye kai”…
Cikeda tausayawa Sulaiman din yadaga shi yana zillewa har suka isa mota sakashi yayi ciki sannan yarufe motar yakoma ciki don biyan kudin, nawane kudinka yayima Bar Man din tambaya Kai tsaye……
Dubu goma, hararanshi Sulaiman din yayi sannan yaciro kudin yabashi don baida lokacin sa insa da shi, “Allah dai ya sauwake yan gida daya da jarabar shaye shaye,niko uwarku yazataji?”……
Cikeda bacin rai Sulaiman din yadawo tareda shake wuyanshi”dawa kake?”…..
Cikin jin zafi Bar Man din yace badakai nakeba wallahi,tsaki Sulaiman din yayi sannan yace”ka iya bakin ka wallahi”….
wallahi na iya baki na daga yau Bar Man din yafada yana haki sakinshi Sulaiman din yayi yafice, nankuma yarasa inazashi don kuwa bayason shiga da Almustapha gidansu cikin wannan yanayin
don haka seyaje dab da masarautar yasamu wani dan lungu yayi parking sannan ya kishingida jikinshi ah jikin kujera besan sanda bacci yayi awun gaba dashiba shima, Almustapha ne yafara tashi wuraren hudun asuba mutsutsuke idanunshi yayi yanason yagane ah Ina yake mamaki yayi sosai ganinshi acikin mota sekuma ahankali yafara tuno abunda yafaru,sa hannu yayi yashiga bude murfin motar sede kirip arufe motsinshine yatashi Sulaiman,dasauri yadube shi tareda tsallakowa bayan da Almustaphan yake”are you okay Brother?”…..
Shiru Almustaphan yayi sannan bedago yakalleshiba…..
taba jikinshi Sulaiman din yayi cikeda damuwa seyaji babu zafi kuma,komawa yayi yajingina jikinshi da jikin kujerar yace
“I’m sorry naganka in that state,but I’m so disappointed Brother,innnine nayi abu haka is okay but as for you I can’t believe it”……….
murda kofar Almustapha yakuma yi sede haryanzun ah rufe take, murmushi Sulaiman din yayi don yasan hakan da Almustaphan yayi yanason yabude mishi motar ne yafita……
Sorry na shiga abunda bai shafeniba,sede ba laifina bane namanta cewa Yayana bedauke ni abakin komai ba infact he never sees me as his very own Brother……shaaa I’ll let you go yakarashe maganar murya ah karye sannan yabude motar babu bata lokaci Almustaphan yabude yafito dasauri Sulaiman din yashiga gabanshi tareda da rungumeshi yana furta “it’s been long Bro, atleast I should get a brotherly hug mana”……
Seda yasakeshi sannan yajuya don shiga motar, Almustaphan ne batareda ya juyoba yace “wait”….
Cak Sulaiman din yatsaya yanajiran jin mezaice sekuma yaga yayi gaba abunshi batareda yace komai ba jijjiga kai Sulaiman din yayi tareda sakin murmushi”don’t worry Brother I won’t tell anyone,lumshe idanunshi yayi “secret!”….sannan shima yashige motar don komawa cikin masarautar……
*****
Tunda safe dayaje gaisheda Magajiya ta titsiyeshi”Sulaiman inakaje jiya da daddare?”…..
‘dan Sosa Kai yayi nikuma Mama,badai niba gaskiya wawan harara tasakar mai” nasan komai Sulaiman,kada ma kayarda kace zakamin karya sannan inayimaka gargadi kafita harkan yaron nan inba sokake raina ya baci ba Kuma duk wani abunda zakayi kayi shi cikin masarautar nan domin fitanda kanayi awajen yazama kaman cin mutuncin masarautar nan ne dakuma zubar da kimanta as the air to the throne…..

STORY CONTINUES BELOW


To Mama abunda ya iya cemata kenan sannan yafice yabar shashenta cikeda tunanin ya akayi tasani,indai haka ne dole tana da spy,spy dinma masu bin Almustapha fa, tambayar kanshi yashiga yi to mesukeso?……..

Bayan fitarshine Magajiya tashiga Kiran Laure,cikin sauri tazube agabanta”gani uwargijiyata”……

Kicema talatun tafada ma Hilu yau zamu fita da dadddare…..
To in Allah ya yarda zan fada mata,tashi kitafi… to uwargijiyata …..

*******
Yau Monday Kuma yaune zasufara fita registration shiyasa tunsafe tagama ma Ummin ta aikinta sannan tashirya cikin doguwar abaya tayi veiling wanda bakaramin kyau yayi mataba babu wani make up datayi inbanda lip gloss datasaka, Asiya kuwa anyi kwalliyar nan kaman wanda za aje dinner ko wani event haka suka shige mota don tafiya inda Aliyu ne zekaisu tunda bayida abunyi yaudin………
Tunda suka shiga makarantar suke processes na registration din haka ranar suka yini zubuk cikin makarantar koda suka dawo gida agajiye suke Kuma wai ahakan basuma gama ba,seda sukayi sati daya cir suna registration kafin suka samu suka gama, Allah yataimakesu ah first week sukayi sunada time din hutu the other week kafin afara lectures Kuma………
Suna dan hira da Ummin ne washegari takecewa yauwa Ummin nikam nahadu dawani Mukhtar wai yasanki….
Ummi dake gyaran wake tace ah ina Kuma kika hadu dashi?…
Wani Mukhtar? Ummi tayi mata tambayoyin ajere..
Dan Gombe ne Ummi wai su makotan ku ne acan yasansu Hajiya da Baffa duka family members fa ashe shima anan yake Medicine yanama aji biyar…….
Habadai, Allah sarki Mukhtar daman anan yake karatu bansaniba,nasanshi wallahi yaron gidan Alhaji Bala neighbors din mu. kice yaro yagirma he was at his young age sanda nayi aure fa….
Dariya Asma’un tayi Kai Ummi, yanzu kan yagirma yazama dan gaye dashi wai baisan ah garin nan kike zamaba yayi azan ah kaduna muke……
Allah sarki anan mukeda zama yanzukam yazo ai,eh yace zezo wai daga kamar mu yagane ni yace duk yanda akayi wannan Yar Adda Maryam ne…..
Ayya yaron kirki don Allah kigaidaminshi kuma kice inaganin zuwan shi…
Insha Allah zanfada mishi
Haka sukacigaba da hira duk akan Mukhtar din da mutanen gidansu tana bata labarin rayuwarda sukayi abaya can tunkafin tayi aure……
Tunranar da Sulaiman yasamu Almustapha ah club basu sake haduwa ba hakanan befada ma kowa ba dukda kuwa atunaninshi Magajiya tasani,yauma sanye yake cikin alkyabbar shi yayi kyau sosai suna shirin fita da mai Martaba zuwa kauyikan dake yankin Zaria dukda bawai yanason zuwa bane sede bazai iya yima Mai Martaba musu ba……
Yau kwanansa biyu behadu da Yayartashiba yar murmushi yayi sannan yayi bangarenta as usual tana kwance yayinda kuyangu namata fifita se Afiyya dake yimata tausa tunda Hamida tahangoshi take washare baki,seyau kasan hanyar inda nake….
Sa hannunshi duka biyu yayi ah kunnuwanshi I’m sorry Sis,tuba nike….
Afiyya data ganshi takasa boye excitement dinta “Yaya Sulaiman”…..
Kallonta yayi yanason ganeta, ahankali yace Afiya?…
Irin he’s not sure dinnan, murmushi tasakar mishi yayinda ta tashi da gudu tafada jikinshi Yaya Sulaiman yaushe kadawo?….
Hugging nata back yayi sannan yace little Sis kinanan,kece kika girma haka ina little Amira yashiga jero mata tambayoyi babu kakkautawa….

Tana gurin Ummin mu,munyi kewanka Yaya Sulaiman,dan shafa kanta yayi nima nayi kewarku sosai I missed those days danake zuwa gunku ah boye…..
Dan goge kwallarta tayi don bakaramin farin cikin dawowanshi taji ba he’s indeed a caring Brother kwata kwata tama manta ah dakin Hamida take shima Sulaiman din haka seda tayi musu magana cikin masifa, Sulaiman hankalinka daya kuwa kekuma mahaukaciyar wace garice?…
Kinamin tausa zaki tashi?….
Dasauri Afiya tajuya gareta cikeda nadama don duk tsiwarta tana tsoron Hamida don ba karamin aikinta bane ta hada ta da Magajiya don haka tashiga magiyar bada hakuri…….

Kama hannunta Sulaiman din yayi sannan yakarasa gaban gadon da Hamidan take yazauna Itama yazaunar da ita wani ihu Hamidan tayi yazaka barta tazauna min kan gado banason shashanci Sulaiman, murmushi yayi sannan yace ma sauran bayin sufita seda suka fice sannan yadubi yayarta shin yanzu Sis abunda kikeyi kin kyauta kenan?…

STORY CONTINUES BELOW


Harararshi tayi danayi mefa?…
dakika mayar da kannen ki bayinki,cikin tsawa tace niba kanne na bane wayannan yan iskan inkuma maganar dazakayimin kenan katashi kafita kabani guri,kallonta yayi cikeda disbelief sannan ya girgiza kanshi Allah yasauwake,yakawo ranar dazaki gane Adda Hamida…..

Tsaki tayi batareda tace komai ba yayinda yakama hannun Afiyan, ahankali tacire hannunta cikin nashi don seyanzu talura zata iya jazama kanta magana dama shi Sulaiman din juyowa yayi yana kallonta,gyada mishi Kai tayi alamun yatafi she’ll handle everything….
Are you sure?…
Kuma gyadamai kan tayi,duba wristwatch din hannunshi yayi ganin time nakurewa kuma yace zamu fita da Mai Martaba anjima zanzo ingaida Ummi in Allah ya yarda……
Allah ya kiyaye…
Amin little Sis….
Nan ya fice yabarta tsaye ah gurin… Hamida ko bakaramin bata mata rai yayiba sannan tadauki alwashin seta fadama Magajiya abunda idonta yagane mata…….

*****
Gabadaya yarasa nayi yaudin don kuwa maganin Umminsu yakare batasha na daren jiya ba gashi babu kudi agurinshi kwata kwata bare yasayi koda guda dayane,daya rasa abunyi kawai seya wuce direct shagon Mallam Hudu kilan yasamu abunyi koya dan samu wani abu yasayamata maganin koda nayau ne kadai kafin asan abunda Allah zeyi kuma nangaba sede to his own surprise yanazuwa shagon Mallam Hudun bayan sun gaisa se yake cemishi ai mutumin dayasaba bada kudin taimako na magani ah asibity yaji yasake zuwa gari Kuma yana bada kudi ah asibity shiyasa jiya dayatashi daga kasuwa yaje kuma ya karba musu, lumshe idanu Almustaphan yayi cikeda jin dadi koma waye wannan mutumin Allah yayi mishi albarka shine kawai abunda zai iya fada,dakyar yabudi bakin shi yace “Nagode Mallam Hudu”…

Murmushi Mallam Hudun yayi sannan yamika masa dubu hamsin din yace ga kudin nan sekuma yakara mishi dubu
goma seka cika kasayi maganin na wata daya kaman yanda akasaba,wannan karan Almustapha rungume Mallam Hudun yayi he’s just out of words, Allah yakawo mishi mafita batareda yawani wahalaba,abunda Almustaphan besaniba Sulaiman ne yabawa Mallam Hudu kudin don kuwa yaje yaduba Ummi Kuma yatambayi su Afiya maganin Ummin sesukace masa yama kusan karewa gudun kada yasiyo yabasu Almustaphan yatambayesu ina sukasamu shine yabama Mallam Hudun kaman yanda yasaba yi ada can baya…..
Tunda Almustapha yafita chemist din da suka saba sayan maganin yawuce yasaya sannan yawuce gida don Kai maganin….
******
Yau Monday Kuma yaune zasu fara fita makaranta dukansu sunada 8:00am don haka suka shirya dawuri,sannan Daddy bayan yakuma dawowa daga tafiya yakawo musu tsarabar mota wanda zasuna tafiya makaranta da ita tare bakaramin murna sukayi ba already daman duk sun iya driving don su Aliyu kan koya musu yanzuma sungama yima kowa sallama ne yayinda Asiya ce rikeda key sewani kaudi takeyi haka tayi driving nasu zuwa school seda tayi dropping Asma’un sannan tawuce nata faculty din akan tajirata inta gama nata lectures din zatazo su tafi gida……
Tunda tashiga GST din tamaida hankalinta ga abunda malamin keyi kuma babu laifi tana gane wa sosai don kuwa malamin nada method of teaching sosai koda Malamin yafita seta kasa tashi tana ganin yanda ‘yan uwanta keta fita jitayi anmata sallama ansawa tayi tareda kallon yarinyar wacce take kusan sa arta ko ace saartace ma…..

With a beautiful smile yarinya tamika mata hannu “I’m Zahra and you?”….
Murmushi Asma’un tamata tareda mika mata nata hannun “Asma’u, I’m Asma’u Muhammad”….
nice name cewar Zahra din,can we be friends nima sabuwar zuwace and it seems like thesame course mukeyi ko?….
Kallon Zahran tayi sannan tace Okay bakomai,may be we can confide with each other ma amma sede ni MBBS aka bani bansan keba….

Dariya Zahran tayi wanda har seda hushiryarta ya bayyana,nasani nima shidinne ai duk wanda kikaga munyi GST tare yau MBBS yakeyi bakiga bamu da yawa ba?..
Hakane kam Asma’un tabata ansa yayinda Zahra tace se 2:00pm mukeda lectures kuma yanzu 9:30am kinga malamin ma yafita dawuri kozamu dan bikan abunda Malamin yayi mudanyi refreshing kwakwalwarmu…..
Yar dariya Asma’un tayi,kumafa haka ne go ahead….
Nan suka shiga yima juna bayani inwannan batagane nan ba seta fada ma yar uwarta hakadai,kafin kace mai har sun saba kaman wasu kawayen dasuka jima tare…
****
Yau tun asuba talatu tazo gurin Magajiya tana haki,harararta Magajiya tayi miyene kikazomin da sassafen nan?……
Kiyi hakuri Uwargijiyata amma yazaman min dolene inzo infada miki,to miyene kifada mana kinata wani nuku nuku Magajiya tayi maganar rai bace sabida antasheta daga daddadan baccin datakeyi…..

STORY CONTINUES BELOW


Talatu na haki sabida uban gudun datasha tace Uwargijiyata naso fada miki tun ranar amma nayi shiru ina tsoro sede yau abun yakai inda bazan iya boyemiki ba Yarima Sulaiman ne yayima bayi fyade yau baiwa na hudu kenan da abun yafaru dasu kuma iyayensu sunyi maganar kaiwa Kara gurin Mai Maitaba dukda yaran basu fada musu wayene yayi musu ba shine naji inason in fada miki….

Cikeda tashin hankali Magajiya tace kije kikawo min yara hudun yanzunnan,tashi tayi jiki nabari tafice bayan kaman minti goma segasu sundawo tareda bayin zubewa kasa sukayi suna mika gaisuwa yayinda dayar da abun yafaru da’ita adaren jiya taketa sheshekar kuka cikeda bacin rai Magajiya tace ke dallah yimana shiru kina wani kukan munafurci,kebama abun alfahari bane agareki ace Yarima guda yakwanta dake shasha sha marar wayau,dakyar indo tahadiye kukan datakeyi kamin Magajiya tasamu guri tazauna gyaran murya tayi sannan tace”kubude kunnuwanku dakyau kuji mezan fada muku”…
Jijjiga Kai sukayi sunajinta yayinda tace Laure tamiko mata kullin data ce tadauko miko mata tayi sannan tajefa musu gashi kuje kuraba wannan sannan kurufe bakin ku banason inji shi ah kunnen wani inbahaka ba na lahira seyafiku jin dadi daga ku har iyayen naku….

Jiki na bari sukace to Magajiya zamu kiyaye,tashi kutafi,harsun tashi zasu tafi tace kudawo, dawowa sukayi dubansu tayi irin duban wulakancin nan sannan tace zan neme ku akan al amarin sannan iyayen nakuma aturomin su in rufe bakinsu haka ko akayi iyayenma dasukazo kudi tabasu sannan tace suyi shiru if not zatamusu hukunci me tsanani(innalillahi wainna ilaihir rajiun,lokaci yazo da kudi yazama abun so akoda yaushe wanda har ze rufe ma bawa ido daga ganin gaskiya,duniya inazaki da muya Allah kasa mufi karfin zukatan mu)….

Bayan sun tafine tadubi Talatu”kinshirya abubuwan danasaki yau?”…..
Eh na shirya Uwargijiyata da Maimartaba yashiga fada yau da safe zeje yakai karar…..

Jinjina Kai Magajiyan tayi sannan tace to shikenn Allah yakaimu, Amin cewar Talatun yayinda Magajiya tajefa mata wani kulli kudi ne aciki jikina bari Talatu tashiga godiya sannan tafice……..

Yau litinin Kuma yauce ranakun da mutanen gari dama na masarautar suke kawo kara ah fada don akarba musu hakkinsu sannan ake yanke hukunci.tun karfe takwas me martaba yashiga fadar masarautar wanda anan yake zama kowace litinin donjin matsalolin mutanensa dakuma neman hanya don magance masu ita…..

Haka duk masu Kara suka shiga kawo wa ana yanke ma masu laifi hukunci yanda yadace dasu har aka iso kan wani bawan Allah kuka yakeyi sosai kamar ranshi ze fita sannan yagaida Mai Martaba ansawa yayi sannan yace yafadi matsalarsa…..
Cikin kuka yace Allah yaja da tsawon kwana Mai Martaba ni talakane me tsoron Allah dakuma neman na kaina,bantaba cutan waniba kaman yanda banason ah cuce ni matana biyu da ‘ya’yana goma banida wani hanyar ciyar dasu seta hanyar kiwon kajin danake yi,inada kaji guda talatan Kuma dukansu arana kowannensu takan zuba kwai uku wanda muke fitarwa musayar har musayi abincin dazamusa ma bakin salatinmu kwatsam shekaranjiya semuka tashi babu kaza ko guda daya wani yabiyo dare ya kwashesu bakaramin tashin hankali muka shigaba nida matana inda muka shiga cikiyarsu cikin unguwa nanne wani saurayi yace yaga sanda wani yaro yafito da kaji da daddare yatafi dasu amma beyi tunanin sato su yayiba Kuma yace zegane fuskar yaron don kuwa shima yaje saida nashi kajin jiya se suka hadu bayan yadawo ne yaji muna cikiyar namu…..
Mai martaba yadubi tsohon sannan yace inayaron yake?…

Kiranshi tsohon yayi yayinda saurayin yazo yazube gaban Mai Martaba yana mika gaisuwa, Kallon shi Mai Martaba yayi sannan yace ya akayi kasan kajin na wannan mutumin ne?…..
Ranka ya dade ta hanyar gidan naga yafito Kuma danaje saida kajin na hadu dashi tabbas kaji guda 30 ne don har rokon mai sayarwan yayi kan yasaya amatsayin dubu sittin yanason sayama mahaifiyarsa magani ne don da Mai sayan kajin dubu hamsin da biyar yaso saya…..
kuma bayan nadawo naji labarin satar munkoma da shi Mallam Audun yaga kajin yace tabbas nashine sede sunyi rigima damai saidawan yace bazai bayarba donshi saya yayi se ankawo masa kudinsa……
Maimartaba ne yadubi dogarin dake isar mai da sakon zuwa ga mutane sannan yace wayene aka kama yayi Satan?……

STORY CONTINUES BELOW


Cikin sauri yaron yace Almustapha ne sunan yaron, Mai Martaba seda yaji gabanshi yafadi amma bece komai ba sema cewa dayayi aje akawo shi nanfa dogaraye suka fice don zuwa kawoshin,nan aka cigaba da jin matsalolin wasu ana bada hukunci kafin akawo mai laifin se acigaba da nasu sunkai minti talatin kafin suka dawo tareda Almustapha don shikam takun kasaita yashiga yi musu dukda zaginshi dasukeyi ah hanya ko kallo basu isheshiba dukda yana mamakin laifin meyayi daza a nemeshi don koda wasa bazaice alkhairi ne ke kiranshiba sanda suka isa fadan seda aka gama dawanda akeyi din sannan aka cigaba da nasu yayinda Mai Martaba ya umarci da afaro daga farko don yaron yaji laifin da ake tuhumarsa dashi har aka iso inda aka tsaya kamin Mai Martaba yace Ina Mai kajin yake, nan aka fito dashi…..
daya daga cikin dogarin ne yace wannan ne yazo yasayar da kaji agurin ka?…..
Babu kunya babu tsoron Allah saurayin yadubi idanun Almustapha yace eh jiya da safe yazo har yarokeni in Kara masa kudi zesayama mahaifiyarsa magani ne…….

Shide Almustapha tunda akafara maganar ko dagowa beyiba bare ya kallesu kanshi nakasa,yariga yasani sharri akeson yi mishi and they’ve succeeded, wanda yake claiming anyimai satar ne yace har Mai maganin Kam nadauko nan Mai Martaba yace ashigo dashi,se awannan lokacin Almustapha yadago don ganin memaganin tabbas shine wanda yake sayan magani agurinshi,tambayar shi akayi shin Almustapha yazo yasayi magani ah gurinsa….
Jijjiga Kai yayi alamar eh sannan yace yazo yasaya jiya da safe….
Duban mai chemist din Mai Martaba yayi sannan yace nawa yakawoma?….
Dubu sittin ranka shi dade…….
Nan shima aka sallameshi,kallon Almustapha Mai Martaba yayi feeling somehow sannan yace to Almustapha kaji laifin da ake tuhumarka dashi kayarda kayi?……
Almustapha zuciyarshi wani irin Kuna take mishi dabazai iya misaltawaba,mezai ce?bayan anriga anmishi kulla kulla,ta inama zece bashi bane bayan duka ga evidence anfiddo lumshe idanunshi yayi ahankali yayinda bayamason ko kallon inda Mai Martaban yake seyau yakejin wata irin tsana ta wannan mutumin tafara shigan shi har amishi sharrin sata amma bazai iya komai akaiba,tukunnan ma bai nuna yamasanshi ba bare yace akwai alaka ah tattare dasu.kowa yayi shiru ah fadan anajiran amsar Almustapha sede shiru kakeji wurin minti biyar….
Mai Martaban ne yakuma cewa shirun dakayi na nufin ka amsa laifin dakayi kenan ko?……
Nan ma shiru awannan lokacin ran Mai Martaba ya sosu amma seyace nabaka nan da sati daya kanemo ma mai kaji kudinshi kadawo mishi dashi sannan yadubi tsohon yace ka karbi kajin ka tunda besayar ba nan da rana itayau zamu karasa daga inda aka tsaya………

Batareda yace komaiba yajuya yafita ah fadan dan satan kallonshi Mai Martaban yayi yakasa yarda yaron zaiyi sata dukda bawai saninsa yayiba Kuma abunda yasa yayi mishi hakan yanason yagano gaskiyar al amarin ne……
Tunda yabar fadar zuciyarshi keyi mishi wani irin kuna,he know for sure Magajiya ce tayi wannan abun tafiya yake baisan inda zaijeba sannan tunaninshi daya ah inama zaifara neman dubu sittin kafin wani sati……

Babu inda ya tsinci kanshi se ah inda yake sayan giya donji yyi awannan lokacin idan ba giyan yasha ba bazai taba jin dadi aranshi ba aikuwa seda yasha din sannan yawuce cikin makarantar alokacin Kuma tafara yi mishi aiki ajiki…….

******
Bayan Zahra da Asma’u sungama discussion dinne suka dan taba hira duba lokaci Zahra din tayi ganin har shabiyu cikeda mamaki tadubi Asma’u tace Asmeey har 12 yayifa gaskiya lokaci na gudu muje cafeteria muci abinci kafinnan lokacin sallah yayi semuje massallaci daganan muwuce lecture ko?…
To Zahra muje daman yunwa nikeji,haka suka tashi sukabar cikin lecture hall din sede to there own surprise dasuka fito hadarine sosai yagama karade koina dakuma halama za akece da ruwa nan bada jimawaba don haka Zahran tace muyi sauri kekam kada ruwa yarike mu ah hanya.haka suka tafi cafeteria din Allah yataimakesu seda suka kusa isa sannan aka fara ruwa shima yayyyafi ne kafin daga baya ruwa yakece kamar da bakin kwarya…….
***
Samun wata dutse dake cikin makarantar Ahmadu Bello university Zarian yayi ya jingina jikinsa ruwa akeyi sosai kaman da bakin kwarya amma baidamu da irin ruwan dake jika shiba,to inama yake cikin hankalinshi bare har yasan me yakamata yayi wajen taimaka wa kanshi daga tashi daga gurin…..
Students da suna tafiya ruwa ya kamasu ah hanya duk sun samu square roots kaman tacikin faculties ko kuma gaban classes inda dai akwai roofing dukdai don kada su jike….
wasu samari dake tsaye ah gaban wani roofing tareda wasu student din suna jiran ruwa yatsaya sutafi respective places dinsu suka hango saurayin dake zaune jikin dutsen ruwa na dukan shi daya daga cikin samarin yace ah haka zaka kare wawa shashasha,dan shegiya kawai….
wani daga cikin su ne yace wai kaikuma dawa kake ne haka?….
Samari hudun ah tare sukace dawaye inba *Lucifer* dincan ba,dayan dabaiyi magana ba yace au Prince Almustapha kuke nufi wai daman shine a can kuma har wani Lucifer kuke kiranshi?…
wani tsaki sukayi tareda hararan abokin nasu,wai ma Prince,yanzu fisabilillahi wannan marar Imanin kake kira da wannan sunan?,to bari kaji ko acikin masarautar tasu bashida wannan gatan barekuma awaje….
Daya daga cikinsune yakuma cewa kai kakai nan ma Ma’aruf mutumin da bayi sunfishi daraja acikin Masarautarma to me kake tunani yaufa ubanshi dakanshi yayi musu sharia dawani dasafen nan wai yasace Mai kaji,can you imagine Dan sarki da sata,satan ma na kaji.
Dan murmurshi Salim yayi,Allah kenan abokaina,Allah ba azzalumin bawansa bane ba sewanda ya zalunci kanshi,shiba yace shaye shaye da lalata yaran mutane shine abunyiba to yacigaba yaga inxai samu mafita….
Aikam dai barima kuga indanyi raha cikin ruwan nan daman Dr Ibrahim yabata min rai dayaki karban assignment dina,mikama wata yarinya jakanshi yayi sannan yayi inda Almustaphan yake sauran ma biyoshi sukayi suna dariyar mugunta jan hannunshi Ma’aruf yayi yana kai Lucifer dan ubanka me kakeyi anan?…..
Shiko peacefully kallon shi yakeyi batareda yacemai komai ba kuma babu wata alamar yaji tsoron ganin Ma’aruf din,mari Ma’aruf din yakai mishi tareda cewa ‘Dan iska jibeshi se shegen innocent face amma Allah kadai yasan abunda ke zuciyarka dariya sauran suka shiga yi inda suka shiga mocking saurayin dasuka kira Prince Almustapha,daga karshema cire mishi rigar shi sukayi dalibai kuwa sunsamu abun kallo don kuwa wanda baswa gurinma suntaho,harma wasu suka karu daga karshe ball suka shiga yi dashi kamar kwallo acikin ruwa,duk jikinshi yabaci da cabi tundaga nesa take hango samari na dukan wani harma suna ball dashi kirjintane yashiga dukan uku uku itadai yaune first day dinta ah school dinnan meyake faruwa ne,makarantar babu tsarone komi?ah iya saninta dai ABU makaranta ce sananniya wanda sunada rules and regulations nasu kominsu na tafiya cikin tsari to amma indai haka ne mezaisa abari ana bullying wani batareda securities sun dau matakiba,mezaisa dalibai suna ganin anacin zarafin wani suyi shiru harma su tsaya ah gefe sunagani suna dariya tsabar rashin imani, harma wasu nada guts din dauka ah wayoyinsu,miyasa mutane basuda tunanine wani irin hawaye ne taji ya gangaro daga fuskarta batareda sunmata sallama ba itakam bazata iyaba bazata iya ganin anacin zalin wani ba dukda batada karfin kwace masa dagudu tafita daga roofing din tayi inda Almustaphan yake already samarin suntafi sun barshi kwance gurin kuka take sosai yayinda tacire katuwar jacket din dake jikinta wanda Yaya Mubaraq ne yabata yanzu dataje office dinshi tareda Zahra don yasanta dasanyi ya taba ta zata kama mura lullubamai tayi cikeda tausayawa yayinda Zahra nata kwala mata Kira amma kota damu don da alama bamatasan tanayiba……juyawa tayi tana kallon wa yanda ke kallonsu tana he’s not breathing,come and help him please…. Sede kaman wanda da gumaka take magana babu wanda yakulata sema cigaba da daukan video din da masuyi keyi……

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *