GIDAN SARAUTA CHAPTER 14 KARSHE

GIDAN SARAUTA




CHAPTER 14 KARSHE





Sulaiman bai iya ya amsa tambayar da Dad keyi mashiba sema jijjiga dan uwan nashi daya shigayi babu kakkautawa yana kiran sunanshi “Yaya Almustapha!”
“Yaya,wake up please,why is he not breathing”,yayima Dad tambayar ah rude. Kan kacemai maaikatan masarautar dake harabar gurin duk sunyo kansu suna mamakin abunda yafaru din ba ajimaba kuma sega karar ambulance da alama tanayowa gurin da suke ne,haka aka daukeshi akasaka shi cikin motar kafin suka karasa sashin shi adakin shi suka kwantar dashi yayinda likita yashiga duba shi cikin gaggawa wanda already yazo da kayan aikinshi ma,allura yayi mai tareda sakamai drip wanda ah tunaninshi shine zai taimaka mai ya farfado zuwa anjima tunda makasudun ciwon bewuce ulcer dakuma Bp bane ke damunshi dukdama Bp din he’s not sure seya farfado kafin aduba. Duban Dad yayi kafin yace insha Allah zuwa anjima ze tashi,daya farka just let me know Dad dake ta zufa cikeda damuwa yace
“toshikenan Doctor,thank you very much”…… +

Murmushi likitan yayi yana “don’t worry, it’s my job”,kafin yajuya yafita Sulaiman ne yace ko inkirasu Abba ne Dad?……..

Cikin sauri Dad yace”no you don’t have to call them,kana iya tada musu hankali by calling them insha Allah zaisamu sauki soon”…..
To Allah yasa cewar Sulaiman din,atake kuma wayar Sulaiman din tashiga ruri dubawa yayi inda yaga Dr Na’im ne,babu bata lokaci yayi recieving call din bayan sun gaisa yake fada masa rashin lafiyar Almustapha din cikeda damuwa Na’im din yace…
“I knew it,indai yayi wasa saka damuwa da rashin cin abincin nan na’iya kwantar dashi”……
“Anyways I’ll be on my way,kuna gida Ina?”….
“Eh muna gida”, Sulaiman yabashi amsa kafin sukayi sallama……

Bangaren su Mai Martaba kuwa tunda suka fita sukabar masarautar straight gidansu Asma’u sukabi suka dauketa don dama already tashirya tun safe harma Daddy yace ko akaita can masarautar se su wuce amma Mai Martaba cewa yayi abarta insunfito zasubi sudauketa. tunda tafito take ta rarraba idanu kozata ganshi amma babu halamunshi haka tawuce motar dasu Hamida ke ciki ta bude tashige wani irin ihun murna suka saki tareda rungume ta cikin jikinsu daman tunda aka doso gidansu Asma’un suketa mamakin meza ajeyi Afiya ne tace”Daman kina gida all this while?”……..

Gyadamata Kai tayi ahankali, Hamida sake rungumeta tayi tana “we missed you so very much”,yayinda Amira ta turo baki tana”itada ta ruguza mana all our wedding plans,nidai banyi kewarkiba”,dariya Asma’u tayi tareda jan karan hancin Amiran tana”kedai fadi gaskiyar Amira”…..

“To wai miyasa ma kika dawo gida Sis,su Ummi basu fada miki laifin wancan jakar zalihar bane ba?”,wannan karan Afiya ne tayi magana,tsaki Amira tayi tana”ae ba munta fada mataba anma seta dinga ganin kaman muna taya Sumayya kishine bayan ninasan duk wanda yahada harka da Magajiya karshenta he’ll turn out to be like her”……..
Murmushi Asma’u takumayi tanajin yanda Amira da Afiya keta masifa kan abunda yafaru kafin tace”yanzukam baya wuceba, she’s now exposed and everyone knows the truth daman duk wani munafiki karshen shi bazaiyi kyau ba kuma duk abubuwan datayi kanta tayimawa bamuba”……..
Gyadakai Hamida tayi tareda cewa hakane Asma’u, Allah yashiryemu bakidaya yasa mufi karfin zukatan mu se lokacin Afiya tayi realising baran baramar datayi na maganar Magajiya because ita kwata kwata ma mantawa takeyi Hamida Yar Magajiya ce,jiki ah sanyaye tace Aunty Hamida I’m very sorry……
Dariyan yake Hamida tayi kafin tace”for what Kuma?”…….

“Nidai I’m sorry please”,Afiyan tasake emphasising,gyada matakai Hamidan tayi tareda cewa….

“you did nothing so,there is nothing to be sorry for”. Haka suka cigaba da hirarrakinsu wanda duk yawancin labarin akan Zaliha ne su Amiran kebama Asma’u harsuka iso kaduna straight aiport suka wuce inda already plane dinsu is ready jiransu kawai akeyi su iso kafin yatashi. Around 1:00pm jirginsu yayi landing ah aiport na Maiduguri and already har motocin dazata daukesu tazo daga hotel din da yakama musu don acewarshi bazaiso yasauka gidan sarkin Bornon ba bayan abubuwan dasuka faru din haka suka wuce hotel din wanda already ankebe musu floor daya daga shi har mutanen shi,sunyi wanka sunci abinci kafin suka huta baki dayansu inda Mai Martaban yayi niyar zuwa gidansu Zalihan washegari daganan kuma sesuyi tunanin wucewa Chad kuma. Acan Zaria kuwa wuraren azahar Almustapha yafarka ganin su Na’im yayi azaune suna dan hirarrakinsu da alama ma basusan yafarka ba dan motsin dayayi da hannunshi ne yajanyo attention din Sulaiman cikin sauri yakaraso inda yake cikeda tausayinshi yace…
“Yaya Almustapha how are you feeling now?”…..

STORY CONTINUES BELOW


Bece mishi komaiba sema maida dubanshi kan drip din dake hannunshi dayayi,ahankali Na’im yataso yakarasa gefen gadon inda aka ajiye abincin Almustaphan kafin yadauki mug yashiga hadamai tea,seda yagama hadawa sannan yaxo yazauna yana taba temperature din jikin shi tareda cewa”katashi kasha tea kafin kaci abinci”…….
“Am not hungry”,shine abunda Almustapha din yafurta Hajiya Muniba dayanzu shigowanta dakin kuma sarai taji meyace yasa cikin sauri ta tari bakinshi tahanyar cewa”mekaci tunsafe dazakace you’re not hungry Yarima?”………

Lumshe idanunshi yayi ahankali donshi maganganunsu ma ciwon Kai yakesaka mishi wallahi,daukan mug din tea din tayi wanda Na’im ne ya ajiyeshi agurin kafin tace katashi kaci ko inyi maka dure wallahi,why will you be stabbing yourself atunaninka akoina Asma’un take zataji dadin ganinka haka kokuma hakan shizai sa tadawo, we’re all worried about her dakake ganin mun na amma bamu tada hankalinmu ba inbanda addu’a da mukeyimata na Allah ya bayyana ta sabida munsan wannan ne kadai soyayyar dazamu iya nuna mata”…..
“So,maza tashi kaci abinci inkuma duren kakeso inyi maka to abume sauki ne agurina tunda ganida garada ah kusa rikemin kai bazai bani wahalaba”,dukyanda Sulaiman yaso rike dariyarsa kasawa yayi seda yadan dara Imam kuwa babu yanda ya’iya dole yatashi yasha tea din seda yashanye tas sannan Hajiya Muniba tazuba mai abinci ah plate nanma ta tasashi gaba seyaci, jijjiga matakai yayi alamar bazai iya ci ba……
“Oh duren zamuyi kenan komi?”…….
Lumshe idanunshi yayi kafin yabude bakin tasakai abincin jiyayi kaman tasamai flagen ah baki kwata kwata babu taste haka yakejin abincin abakinshi amma sabida bayason jayayya yasa yadinga karba,ah loma na biyar dinne yashiga kwarara amai, seda ya amayar harda tea din dayasha duka. Subhanallah shine abunda Hajiya Muniban tace kafin tashiga yimashi sannu,haka akasamo towel Sulaiman yagogemai jikinshi daya baci da aman suna cikin haka Dad yashigo da likitan sannu sukayi mashi kafin Hajiya Muniba tayi bayanin abunda yafaru recently,gyadakai likitan yayi kafin yace ulcer ce tayi mugun kamashi ga kuma damuwa dayasama ransa dole seyataimaka yanabin dokokinmu kafin yasamu lafiya dukdama lafiya na Allah ne……

Gyada Kai dukansu sukayi,yayinda likitan yazauna gefen Almustapha din yana masa Questions gameda yanda yake ji shikuma yana ansa masa daga karshedai likitan yayi dan gwaje gwajenshi sannan yace my suspicion was right,Bp dinshi yahau gakuma ulcer dake damunshi. Ajiyar zuciya Dad yayi sannan yace daman yanada BP ne?……..

“Yanadashi din tunda gashi yatashi yanzu”,cewar likitan kafin yamaida dubanshi kan Almustaphan yace tunda inkaci abinci amayar wa kakeyi bari insake samaka wani drip din it might help and that does not mean kadaina cin abinci ko kana amayar wan ka dinga ci koda kadanne please and batun damuwa please karage saka makanka damuwa if you’ve any problem tell them they might help you out, you’re a Doctor so,I expect you to know all the consequences”. Gyada masa kai Almustapha yayi inda likitan yasake saka mishi drip din sannan yayi masa prescribing drugs, Na’im ne yakarba tareda cewa bari yaje yasiyo, he’s a Doctor yasan damuwar Almustapha din amna bayason yayi musu katsalanda besides doctor dasukedashi dinma is doing his job perfectly but abudayane yasani zaitaimaka ma Almustapha wurin samun lafiya that’s yasamu “peace of mind” and that will only happen in akasamo Asma’u inbahaka ba kwana nawa ana rokonshi yakwantar da hankalinshi yaki and he doesn’t blame him ita zuciya haka take indai batasamu abunda takesoba bazata taba zama stable ba…

★★★
Da dare tanajinsu Afiya daga me hello sweetheart se me I missed you love, Hamida me tayata hirarma tafice gurin Ummi wannan dalilin yasa all her loneliness yadawo sabo,toma miyasa bataga Almustapha ba bayan ance dashi za azo,juyi tayi kan gadon tareda daukar pillow tarungume ah kirji gashi wayarta ma tabarshi acan gida bare tarage kewarshi koda ta hanyar kallon hotunanshi ne,wayarma tunranar data jefa ta ah drawer batasake waiwayonta ba,hango babban wayar Amira tayi kan bedside drawer ashema da karamar take waya cikin sauri tadauka tareda unlocking dinta direct pictures tashiga inda tayi arba da hotunanshi bila adadin,kallo tadingayi tanajin hankalinta nakara kwanciya wani tayi murmushi wani kuma tayi dariyan yanda yabata rai akayi hoton,jitayi anwabce wayar daga hannunta tabaya cikin sauri tatashi tana”waye wannan?”….

STORY CONTINUES BELOW


Dariya Amira tayi tana”inmutum yana kewan mijinshi yakirashi mana bawai yatsaya yana kallon hotunan shiba,you can see him for real by making video call” ……

Turo baki Asma’u tayi tana”cemiki nayi kewarshi nikeyi”…..
Nifa shawara nabaki Sister in-law, Amiran tabata ansa playfully kafin kuma kamar wanda aka tuna matada abu tace”tukunnan ma wait!”……
Tsayawa Asma’u tayi tana kallonta kafin Amiran tace….

“if I could remember Yaya was sick and worried about your disappearance to ya akayi ba afadamishi kindawo ba?”……..
“Banganeba,besan inanan ba kikeson kice?”, Asma’u tayima Amira tambayar cikeda curiousity,yes besaniba don dayasani he’ll be the first to come and see you bakisan halin dayashiga bane da bakyanan, cikeda zumudi Asma’u tace”Are you serious?”….
“How did he react?”
Gwaliyo Amira tamata sannan tace”naqi wayon bazan fadaba,kikirashi kitambayeshi”……..

Hararanta Asma’u tayi kaman zatayi kuka tace…
“banzo da wayataba Allah”…….
Dariya Amira tayi tareda kwaikwayon muryar Asma’un tana”sekince you missed my brother and you love him kafin inkira mikishi”…….
Batarai Asma’u tayi sannan tace”kada kikiran mana shima daya damu dani zainemeni ae”,daganan takoma tayi kwanciyarta alaman tayi fushi dariya Amira tayi tana I’m sorry and Yaya Imam is also sorry for not calling but I assure you bemasan ansamekiba dayasani wallahi dashizaifara zuwa gareki let me even call Yaya Sulaiman zansa ah handsfree zakiji duk conversation dinmu”, takarashe maganar tareda fara dialing number Sulaiman din. Ummi dake bakin kofa tanajinsu tace seki kirashin ae mugani uwar iyayi,cikin sauri Asma’u da Amiran suka dubi inda Ummin take yayinda takaraso tsakiyar dakin tana disconnect the call joor…….
Cikin sauri Amiran tayi disconnecting call din daman ko ringing baifara bama kafin tace”Ummi amma Yaya Almustapha besan ansamu Asma’u bako,tell her nasan ke kilan tayarda da maganarki” ……

Asma’u batasan sanda taja bargo ta lullube kanta ba tsabar kunya haka tanaji kaman ta rufe Amira da duka,wannan kayan kunyar data jamata har ina fisabillahi,dariya Ummi tayi ganin abunda Asma’un tayi kafin tace”kyale sokon mijinkin nan waishi yadauka yamana wayaune dayaki biyomu bayan besan kina tareda muba,seyayita neman naki mugani inzai sameki ah Zarian kafin Sulaiman yadawo daga Indonesia din”……
Itadai Asma’u batace komaiba dukda maganar Ummin tadaure matakai, Amiran ne tace banganeba Ummi…..

Zama Ummi tayi tareda cewa”we wanted to surprise him seya watsa mana kasa ah ido kan bazai biyomu ba se Sulaiman yadawo daga Indonesia,Kuma it was just an excuse fa bayason biyomune kawae batareda Asma’un ba ah tunanina zecigaba da nemanta ne inyasameta sesu taho tare”……
Dariya Amira tayi sannan tace”Kuna jama Yaya raidayawa fa Ummi don Allah kubarshi hakanan”……..

Dariya Ummin ma tayi kafin tace”let him be I want him to value my Daughter much more than yanda ya wahala,next week zaisamo mu ah chad insha Allah don nasan dolenshi yataho indai Sulaiman din yakoma tunda yariga yama Babanku alkawari so karkowa yafada mishi please, it’s going to be a surprise for him”……..

Gyadakai Amira tayi kafin tace”to Ummi”,sannan tadubi inda Asma’un take tareda cewa kinji mijinki bemanta dake ba he’s there busy looking for you harma haka yasashi kin zuwa kallon long lost maternal family dinshi, you’re indeed very lucky sis Asma’u don wallahi ko ah mafarki bantaba tunanin Yaya Almustapha zai iya yima wani wannan abunba”……

Murmus uhi Asma’u tasaki acikin bargonta,it feels so great to be loved by the person you love,jitakeyi kamar kada Amiran tadaina magana yayinda wata zuciyar kuma tashiga tunanin ko awani hali yake yanzun,koma miyene she hope he’s doing alright. Dahaka har bacci yayi awun gaba da’ita batareda tasani ba…….

Washegari karfe goma su Mai Martaba sukayi gidan su Zaliha balaifi sunsamu tarba mekyau wanda Mai Martaba yaji wani iri sabida yasan xuwan dayayi bawai good news yakawo ma mahaifin nataba,mutum me kirki dakuma nagarta irin haka does not deserve the news he brought to amma yazaiyi?…..

STORY CONTINUES BELOW


Kuskure ne Zaliha tariga da ta tafkashi
seda suka nutsu dukansu kafin Mai Martaba yasaka akashigo da Zaliha din tunda tashigo mahaifinta kebinta da kallon mamaki kafin dakyar yamaida hankalinshi kan Mai Martaba yayinda Mai Martaba yafara magana ahankali”I’m sorry da maganar danazo maka dukdama da nayi niyan turo mutanena suzo sumaka bayani sedekuma nagartarka dakuma zumuncin dake tsakanin mu yasa nayi tunanin zuwa dakaina,maganar Zaliha ce takawoni yarka damuka hada zumunci na aure,nan Mai Martaba yashiga yimasa bayanin duk abubuwan dasuka faru harkawowan yau kafin yakarada, I’m really sorry naso ace zan iya yanke wani decision dabaikai wannan ba amma banida yanda zanyi,she hurt us way too much………

Tunda Mai Martaba yake magana sarkin Borno ke sauraronshi seda yagama tas sannan yayi ajiyar zuciya tareda cewa”naji duk bayananka and banyi blaming dinka ba in anyway or the other infact if I was in your place zanyi abunda yafi hakama sannan bazan manta gode makaba dakayi tattaki kazo hargida kakawomin ‘yata,this really shows how kind-hearted and generous you’re, I’m very ashame of myself as her Father dabazan ma iya duban idanunka ba donnidai nasan I tried my best wurin tarbiyantar da ita bansan ya akayi tayi wadannan abubuwan ba so,i’m very sorry”,sarkin Borno yakarashe maganar murya ah raunane haka sukayi sallama da sarki Abdulrahmanu kafin suka tafi,duban Zaliha da take zaune ah inda take tundazu yayi sannan yace,”you choose to be like your Mother right ku dai abun duniya yarufe muku idanu baku ji baku gani,tokizo kiyita zama anan din muga inzaki samu kwanciyar hankalin daya dacedin kinji,kicigaba dazama muga kozaki samu sarkin dazaki auradin don ko kin samu nidai bazan sake saka hannuna acikin maganar auren ki ba bare har kisake jamin kayan kunyan dakikajamin yau ah idon mutanen dasuke kallon darajata”,yanakai aya yatashi yatafi yabarta agurin,wani irin kuka mai sauti tafasheda don bata tabajin tayi nadamar abunda tayiba seyau,itakam tasan nata yakare and she’s now back to square one tukunnanma dawani idanu zata dubi mahaifiyar ta bayan tacemata dukyanda zatayi tasan yanda zatayi tayi achieving goals dinta na zama Queen kada tayarda tadawo mata gida as a divorcee…………
Kasama tashi tayi ah wurin se sautin kukanta da ke tashi,candai dataga abun bana karebane seta tashi tafice zuwa bangaren ta donbatamayi tunanin dosan sashin mahaifiyar tataba,she’s not ready to face her now. Bangaren su Mai Martaba kuwa tunda sukabar masarautar Borno suka raba hanya dasauran don kuwa su Mallam Hudu dawanda zasu juya Zaria airport akawuce dasu sabida karfe daya jirginsu zai tashi zuwa Kaduna inda su Mai Martaba kuwa tafiyarsu Chad se gobe dasafe in Allah ya yarda. yanma lilis su Mallam Hudu suka Isa masarautar Zaria anan ne yatararda labarin rashin lafiyar Almustapha wanda jikin gaba yakeyi ba bayaba shiyasama ko gida baiwuce ba yawuce sashin nashi hankali tashe,wannan karan su Sumayya,Mom da Hajiya Muniba yasamu ah dakin don su Sulaiman tunda suka fita sallar la’asar basu dawoba. Tambayarsu yashigayi yamai jiki inda suka amsa da dasauki,Hajiya Muniba nacewa dasauki kam as compared to dazu dayake ta suma yana farfadowa. “Subhanallah abun haryakai haka?”,Cewar Mallam Hudu din kafin yakarada Allah yakara Lafiya inadai likita yazo yaduba shi?,wannan karan Mom ne ta ansa da eh karasawa yayi jikin gadon tareda dan taba temperature din jikin Almustapha din jikinshi zafi rau kaman garwashi cikeda tausayinshi yace”inasu Sulaiman din?”……

Sunje masallaci basu dawoba tukunnan,gyada kai yayi still baidaga hannunshi daga jikin Almustapha dinba,sunjima ahaka kafin daga karshe yayi musu sallama yafita,to what could be the cause of his ilness newai tunda jiyannan sunbarshi Lafiya lau if he could remember and moreover yana ganinshi ah Fada all the time. Yanacikin tunanin nan shikadai ayayinda yake tafiya a cikin harabar masarautar jiyayi ankira sunanshi wannan dalilin yasa yadago cikin sauri Dad da Sulaiman ne ke yowa inda yake seda suka karaso kafin suka gaisa Dad din natambayarshi yasuka baro mutanen Maiduguri…
“nifa I thought se gobema zaku dawo nandin”…….
Cikeda girmamawa Mallam Hudu yace…
“aa daman yaune zamu dawo sukuma zasu wuce Chad gobe insha Allahu se gashi daga isowan mu kuma natarar da labarin rashin lafiyar Yarima shiyasa ma banwuce gida ba nazo inga yajikin nashi and it seems like it’s something serious”.eh wallahi Mallam Hudu I don’t even know yazanyi insamo Asma’u because from all indications rashinta ne yajanyo duk wannan abubuwan and likita yace dole yakwantar da hankalinshi inbahaka ba abun gaba zenayi ba baya ba gashi banason su Abdulrahman suji because hankalinsu gabadaya zaidawo gida and I don’t want them to forget about the trip dasuka jima suna tsarashi,fatnmudai Allah yabashi lafiya cikin gaggawa maganar Asma’u kuma nasaka asake cikiyarta ah radio stations da gidan Tv sannan munsaka duk wanda yasameta yakawo mana information din inshallahu zamu bashi kyautar milliyan daya”,cewar Dad din kafin ya numfasa yakarada cewa”I hope this will help wurin samota”,tunda yafara maganar Mallam Hudu yasaki baki yana kallonshi da mamaki donshidai kanshi ya daure sannan yarasa wace Asma’u ce ake magana akai tunda shidai Asma’un dayasani din tuni tana taredasu tunda har borno sun tafi tare,cikeda curiosity Mallam Hudu yace”wace Asma’u kuma ranka yadade?”…….
Cikeda rashin damuwa da tambayar Dad yace”matar Almustapha din mana bata bataba tun anagobe biki sarauta”……

STORY CONTINUES BELOW


Sakan baki Mallam Hudu yayi sannan yace”Asma’u ai tuntuni tana tareda mu infact kusan satin ta daya ah gida kafin jiya mukaje muka dauketa mukayi Maiduguri da’ita”,cikin sauri Dad yace”haba dan Allah,wai dagaske kakeyi ko wasa Hudu?”……..
“Wallahi tana Maiduguri tareda su Madam da Mai Martaba,shimai Martaban baifada maka baneba?”……

“Bai fadamin ba wallahi,I know nothing about it, infact I was very upset daya tsallake zaiyi tafiya batareda annemi Yar mutane ba kawai Allah bai motsi bakina da inyi masa maganar baneba sannan nasake yi mashi uzuri da zancen zeje ganin mahaifin wancan yarinyar ne shiyasa,yanzu dai you mean Asma’u is in Maiduguri?”….
“How did all this things happen Hudu?”,dan numfasawa Mallam Hudu yayi kafin yashiga bama Dad labarin tunsanda Ummi tanemi taimako gurinshi harzuwa yau cikeda mamaki Dad yace ikon Allah,so much yafaru amma bansani ba to why on Earth zasu tafi da’ita without her husband’s knowledge fisabilillahi. Haka Dad yadinga mita ta inda yashiga batanan yake fitaba kafin yaciro wayarshi yashiga kiran layin Mai Martaba baijima yana ringing ba yadauka ko amsa gaisuwar da Mai Martaban kema Dad din Dad baiyiba sema balbaleshi da masifa daya farayi….

“Abdulrahman who am I to you?”…..
Cikeda rikida Mai Martaba yace”wani irin tambayace wannan Yaya”……
Cikeda bacin rai Dad yasake cewa”tambayarka nayi ae,seka bani amsa I said who am I to you?”……

Ahankali Mai Martaba yace”You’re my very own Brother”,cikin huci Dad yace…
“No am not Abdul”…..
“Wai miyake faruwa ne Yaya,why are you saying all this things?”,eh mana aidole infada Abdulrahman tunda har yau kanunamin I’m nothing to you,dafe kai Mai Martaba yayi cikeda damuwa yana”For goodness sake go straight to the point Yaya, you’re putting me in the dark wallahi”………
Hmmm shine abunda Dad din yace kafin yakarada,nidai inbani da daraja ah idanunka to Kai kanadashi anawa idanun hakanan in Kai bakason jinina to ni inason naka sabida haka as soon as plane yayi landing kasakomin matar Dana ah jirgi suzo kaduna Sulaiman zaije yadaukota inko bahaka ba nidakaina zanzo har Maidugurin indauketa”, daganan Dad ya katse call din batareda yajira amsar Mai Martaba dinba because tabbas yanda yanuna ranshi yabaci yanada tabbacin kanin nashi zaiyi abunda yace din duban Sulaiman yayi sannan yace in the next 2 hours kakama hanyar kaduna kadauko Asma’u ah airport,cikeda jin dadi Sulaiman yace to Dad daganan yajuya yayi gaba abunshi donshikam yanzuma zaije yadauko matarshi sutafi kadunan inyaso swa jira ah gidan abokin shi, he’s very excited finally yau Almustapha zaiga Asma’u what news could be better than this for his Brother?”……..

Bangaren Mai Martaba kuwa tunda yacire wayar ah kunnenshi yayi shiru yarasa abuncewa,he never thought rashin fadama Yayan nashi komai zai bata masa rai har haka, Ummi dake gefenshi ne tace…
“Wai meya farune Dear?”……
Cikeda damuwa yace”Yaya ne yakira ranshi yabaci don bamu fadamai ansamu Asma’u ba and yace insakata ah jirgi takoma Zaria yau yau dinnan”, Dad yakarashe maganar murya cikeda damuwa kafin yakarada “Kuma kinsan miyasa banfada mishiba?”…….
Cikin sauri tace”sabida kasan shimai tausayin Ya’yanku ne he might not agree with your decision na ayi surprising Almustapha”….
“Exactly my Dear,wallahi wannan shine babban dalilin dayasa banyi involving dinshi ah maganar ba kwata kwata and look at how it turns out to be,yanzu miye abunyi fisabilillahi”……
“Just do as he says”,wannan shine shawarar da Ummi tabashi gyada mata kai yayi tareda dan langabar da wuya yana”dolena ae indai har hakan zaisa yasauko daga fushin da yakeyi dani but,apart from this ni aganina something is fishy out there”…….

Dan shafa bayanshi Ummi tayi in a comforting manner kafin tace…
“insha Allah everything is alright kawai kayi yanda yace din inyasauko gobe seka kirashi muji yanda ake ciki”………
“To yace Mata,kafin yace jeki sa ta ta shirya to because tundazu plane din yadawo inyaso after maghrib sesu juya ko?”…..
Murmushi tamai sannan tatashi tafice inda yajanyo wayarshi yana kiran layin Almustapha don yana mamakin miyasa baikirashiba tunda suka iso Maiduguri din bayanshi mutum ne maison sanin halin da mutum yake ciki aduk sanda yayi tafiya. Wayar akashe wannan dalilin yasa yayi tunanin ko wayar Almustapha din tasamu matsalane tunda dai yasan dawuya ace ansamu matsalar wuta ah masarautar because wutansu is very stable besides ko babu NEPA sunada Solar gakuma generator,dukdai wata facility akwaita available…..

STORY CONTINUES BELOW


Asma’u nazaune dasu Hamida Ummi tashigo tana tambayarta”kinyi wankan ne?”,don dazu tabarsu suna zancen zasuyi wanka dukansu yan matan………
“Eh nayi Ummi”,zama Ummi tayi agefenta kafin tace to tashi kishirya Abbanku yace zaki koma Zaria yau. Wara idanunta tayi cikeda mamaki inda Afiya tace”Zaria kuma Ummi?”……
Gyada mata kai Ummin tayi kafin tace”kozaki hana ne?”,turo baki Afiya tayi tana a’a Ummi kawai dai naga zamuje yawo ne yanzun kuma nayi tunanin da’ita za aje Chad din shiyasa,to anfasa Dad dinku yakira yace takoma yau……
Itadai Asma’u batace komaiba sema tashi datayi tadauki kayan dazata saka tawuce bayi don bazata iya sakawa agaban Ummin ba,koda tafito ah bandakin duk suna zaune kamar yanda tabarsu jin ankira sallah already yasa ta zari darduma ta shinfida kafin ta tada sallah abunta. Dede sanda tatashi daga kan darduman Ummi tashigo tanacewa kin idar ne, murmushi tayi sannan tace”Eh Ummi”…..
Amira ne cikeda zolaya tace”Ummi yarki sewani Smilling take wai ita adole zataje gurin miji”,duka Asmau takaima Amiran tana Ummi bahaka banefa,dariya Ummi tayi tana “kyalesu duk wacce taji haushi tafito da nata mijin mugani”……

Hanyar kofa Asma’u tayi still Amira na zolayar ta harda cewa”kizo to inyi maki kwalliya mana ko haka zakije burzu burzu da fuska”,murguda mata baki Asma’un tayi kafin tafice dariya Ummi tayi tareda bin bayanta tana cewa”kayan ki fa ko abari mwa taho dashi?”…..
“To Ummi”,shine abunda Asma’un tace don ita gabadaya kunyar matar takeji. Harjikin mota suka rakata seda motar su tabar harabar hotel din kafin suka koma ciki Amira na mitar anruguza musu plan din yawonsu, Ummi ne tace kubari insundawo daga kaitan basai kujeba….
Turo baki Afiya tayi tana nidai nafasa fitan ma don bazaimin dadi bama daman gashi babu Sumayya and now sister in-law ma tatafi”,dariya Ummi tayi musu kafin tayi wucewarta ciki tana”kukuka sanidai Chad ne sekunje ko kunki kokunso”…….

★★★

Tun 9:00pm su Sulaiman suka dauko Asma’u ah airport, Sumayya kam komawa tayi gidan baya wai ita tafison tazauna kusa da Asma’un tunda tayi kewarta dayawa”…..
Dariya Asma’u tayi inda Sulaiman yace”sister in-law offence dinki is now doubled”…..

Wara idanu Asma’u tayi tareda cewa…
“topha offence har biyu ni Nana Asma’u name dame kenan?”…..
Still Sulaiman na driving yayinda occasionally yake juyowa yana dubansu yace…
“lallai matan nan bama kisan laifin ki ba kenan”,to barakiji offence din,Firstly you make my Brother sick and now you snached my Wife……
“Kai Yaya Sulaiman this’s cheating fa,nibanyi snaching matarka ba itadakanta tazo gurina sabida irin so da kaunar datakeyimin”,dariya yayi yana”to naji nakuma yarda amma maganar Yayana fa?”….
Kinyarda ke kikasashi rashin lafiya,yanda yayi maganar seda taji zuciyarta tayi dim dim yayinda takasa cemasa komai dubansu yayi tacikin mirror sannan yace”sweetheart kindaiji ko?”…..
“Nibanji komaiba darling”……
Sa hannu yayi ah bakinshi yana dariya”zankama kine yarinya”, murmushi tayi kawai kafin tacigaba da damun Asma’u da hirarraki wanda duk akan rashin lafiyar Almustapha dinne dayanda yadinga damuwa da batanta hakanan Asma’u tadingaji kamar tayi tsuntsuwa ta’isa Zaria gurinshi,it means he’s very sick and she’s there doing nothing ah Borno. Kusan goma da kwata suka iso masarautar yayinda Sulaiman yayi parking ah parking lodge kafin suka fito dukansu hanyar sashinta Asma’u tayi inda Sumayya tabi bayanta cikin sauri Sulaiman yarikota tareda cewa inazakije kuma…..
Cikeda rashin damuwa da tambayar tashi Sumayya tace..

“gurin Yaya Almustapha mana”…..
Riko kugunta yayi romantically tareda karayin kasa da murya”kije kiyime agunshi?”…
Turo baki tayi don yanzu silly Questions dinshi sunfara isanta,ashagwabe tace”zandubashi mana darling”……

Daura fuskarshi yayi kan nata kafin yace,”you don’t need to go there,his wife is here to take care of him kema kikula da naki mijin tukun”…….
Hararanshi tayi yayinda yayi pity face tareda sake narkewa ah jikinta yana”Allah nagaji Sumyna, I’m so very tired I really need a warm shower with you”,yayi emphasing “with you” din in a whisper wanda seda tsikar jikinta yatashi kokarin kwace jikinta take yi amma takasa dole tabishi bangarenshi dukda ranta bayaso besides batason wani yagansu tunda bata tare ba haryau……..

***
Parlourn look so new and amaizing dukda acikin jikinta tanajin this’s home,her very own home and where she belongs tunda ance kowacce mace gidan mijinta shine gidanta,karema parlourn kallo tashigayi ko’ina fes fes ga sanyin AC dake ratsa ko’ina ah parlourn wanda yasata jin wani special feeling nadaban,babu kowa ah parlourn hakanan bata tunanin cikin ma gidan ma akwai mutane tunda koina yayi shiru. Ahankali tadinga taka kafarta akan lallausar kafet din dake parlourn harta iso kofar dakinshi lokaci guda Kuma taji bugun zuciyarta ta karu fiye dana dazu yayinda wata zuciyar kecewa tawuce dakinta kawai amma itakanta tasan bazata iyaba barinma inta tuno zancen su Sumayya na baida lafiya sosai……

Bude kofar dakin tayi inda duhu yaziyarci ko’ina because wutan dakin akashe yake sedan hasken bedside lamp datake hangowa daga inda take karasawa cikin dakin tayi still tanajin wannan sanyin AC har cikin jikinta gakuma kamshin turarenshi datayi bala’in missing daketa shawagi ah hancinta. Zama tayi bakin gadon dede inda fuskarshi take wanda tunda jikinta ya sadu da blanket din dayake lullube dashi taji irin zafin daya dauka cikeda damuwa takai hannunta fuskarshi aikuwa batasan sanda tafashe dawani irin kukaba sakamakon zafin dataji jikinshi yadauka…….

Cikin bacci yaji kaman kukan mutum akusa dashi,and he’s sure the crying voice sounds so familiar kasa bude idanunshi yayi sabida zafin dasukeyi mashi and moreover bayason yabude idanunshi yazamanto crying voice dinta dayakeji mafarkine….
Batabar kukan ba harna wani tsawon lokaci kafin tafara tunanin kukan datakeyi din bashi zai taimaka masaba hakanan bashine gatan dayakamata tamasa ayanzuba, dukda duhun dake dakin hakan baihanata kallon yanda yake baccinshi peacefully ba,his face looks so plane and clear sa hannunta tayi tareda taba temperature din jikinshi which is still very hot, tashi tayi tana goge kwallarta kafin tawuce bandakin shi debo ruwa tayi acikin medium bowl haka tazo ta ajiye kan bedside drawern dake kusa dashi kafin takoma kusa da wardrobe dinshi inda tashiga neman karamin towel batasha wahalar nemaba tasamu sabida daman tasan duk wani ma ajiyi na kayanshi. Dawowa tayi kanshi still tana goge kwallarta dasuka kasa daina zuba haryanzu,sa towel din tayi cikin ruwan still tana tsaye yayinda take ta faman sharar kwalla mistakenly hawayenta yazuba ah fuskarshi,arazane yabude idanunshi jin kamar anwatsa mai ruwan dalma ah jikinshi wanda hakan ya tabbatarmai da ba mafarki yakeyiba,sautin kukan ne yaji haryanzu yanamai yawo ah kwanyarsa ahankali yabi inda yake jiyo sautin kukan nata arba yayi da figure din mutum tsaye kanshi don baya iya ganin fuskarta clearly,ko ah mafarki yaga wannan figure din yasan wanene but to be sure seya daga hannun shi dake karkarwa yashiga mutsutsuka idanunshi kafin yasake daurasu kanta”she’s still standing there crying helplessly”…. +

Kenan itace komi?…
When did she come,does this mean she’s not angry with him anymore komi,lumshe idanunshi masu mai zafi yayi kafin yasake bude su akanta,if she’s really the one Standing right infront of him bemasan tayaya zaifara nunamata farin cikin shiba. Bayajin karfin jikinshi haryanzu bare har ya’iya motsawa daga inda yake,motsi yafarayi da hannunshi ahankali dukda hannun na karkarwa amma baiyi giving up ba,dakyar yasamu yadaga hannu sama daniyar tabata because he just want to be sure ba illusion bane ba,he wants to be sure that she’s the one standing right infront of him. Bata ankaraba taji hannunshi ah singalalen nata hannun wanda hakan yasata tsorata tayi baya cikin sauri kafin ta ware idanunta tana kallonshi,sake miko mata hannun yayi alamar tazo gareshi don yanzukam yasan itance cikin kuka tace….
“Yaya Im..am?”…….
Shima hawayen ne tayi slipping daga gefen idanunshi and at thesame time yana sake mika mata hannu batareda yace komaiba cikeda tausayinshi tamika mai nata hannun,damkewa yayi da karfi cikin nashi don gani yakeyi inyasake zata sake guduwa tabarshine ahankali tazauna kusa da kanshi tana kallon fuskarshi yayinda tasa dayan hannunta tana faman goge kwallarta shima zuba mata idanun yayi babu ko kyaftawa because farin ciki tayi mashi yawan dama ya rasa wani word zaifada mata taji dadi aranta hakanan yanajin kukan nata namishi kuna harcikin ranshi cikin raunanniyar muryarsa irinta marasa lafiya yace”miye na kukan kuma?”….
Sake fashewa tayi da wani kukan wanda hakan yasashi janyo ta kusa dashi sosae kafin yacire hannunshi daga cikin nata yasa thumb dinshi yana goge mata kwallarta tareda yin fuskar tausayi sannan yace…
“stop crying please,nine yakamata inyi kuka bakeba,by crying kina tayarmin da hankali ne Asma’u”,rasa abuncemai tayi kawai seta shige cikin kirginshi tana cigaba da kukanta shima rungumetan yayi kamar wanda zaimadata cikin jikinshi,bubbuga bayanta yashigayi in a comforting manner dukda bayada wani karfi sosae itakuwa dukda zafin da jikinshi yakeda hakan baisa tayi tunanin matsawa daga gareshiba besides aganinta that’s where she belongs. Dakin yayi shiru se ajiyar numfashinta da akeji dakyar ta’iya tsagaitawa tace…
“I’m sorry Yaya Imam”…….
Bece mata komaiba hakanan baidaina tapping bayanta dayakeyi dinba tun dazu wani irin special feeling yakeji dayajima baiji irinsa ba,the feeling of emptiness dayakeji alokacin da bata taredashi se yaji yanzu duk wasu pore spaces na zuciyarshi sunfara filling gradually suna komawa kamar da. sake gyaramata kwanciyarta yayi ah kirjinshi dukda ma ah zaune take kafin yakai bakinshi daidai saitin kunnenta muryarshi na cracking yace…
“I missed you”…..
Dago da fuskarta tayi tana kallonshi for some seconds kafin tace”I missed you much more Mr Taciturn”,yaji dadin sunan da ta kirashi dashi amma seyake ganin kamar kalamanta ba gaskiya baneba don haka ya kawar da kanshi gefe cikeda damuwa tasa hannunta tajuyo da fuskarshi saitin nata in a whisper tace”what’s wrong”…….
Jijjiga mata kai yayi alamar babu komai kafin yasake janyota zuwa jikinshi ya rungumeta tsam yana sauke ajiyar zuciya,shiru tayi acikin physique chest dinshi tanajin heartbeat dinshi dukda tana mamakin meyasa yajuya matakai dazun anma what matters ah yanzu shine she’s with him alokacinda he needs her the most. Sunjima ahaka har wuraren 11:30pm babu wanda runtsa ajikinsu,kowa da irin tunanin dayakeyi aransa bayan wani lokaci kuma tafara jin saukar numfashinshi alamar yafara bacci wannan dalilin yasa tayi tunanin tashi tanemi kayan bacci tasaka kafin takwanta Itama. Kokarin tashi takeyi amma takasa sabida irin rungumar dayayi mata turo baki tayi ahankali kafin tafara kokarin cire hannunshi ah bayanta amma yaki saki sema cewa dayayi”Don’t leave me alone please”…….

STORY CONTINUES BELOW


Kallon fuskarshi tayi cikeda shagwaba kafin tace….
“to kafafuna duk suna kasa fa”……
Bashida karfin tashi daga kwancen dayake don haka seya saketa,harta tashi tsaye sekuma yayi saurin sake riko hannunta tareda bude rinannun idanunshi yadaurasu akan nata. Lokaci guda taji duk wasu pulse dake aiki ajikinta sundena functioning idanun Almustapha have so much effect on her bare kuma azo ga batun yatabata,fuskar tausayi yayi kafin yace in a whisper”promise me you won’t go”…….

Dakyar ta’iya daidaita kanta kafin tasaki murmushi tareda cire hannunta cikin nashi kafin tazagaya ta daya bangaren gadon ta hauro batareda tayi second thought ba, duk inda tayi binta yakeyi da rinannun idanunshi yanzuma kallonta yakeyin tana zaune ah tsakiyar gadon turo baki tayi tana”Stop looking at me like that please”….
Dauke idanunshi yayi daga kanta yamaidasu kan beautiful long fingers dinta kafin yamika hannunshi yajanyota ahankali, fadowa tayi saman kirjinshi yayinda yadan saki kara cikin shagwaba dasauri ta zare idanunta tana shirin magana amma seya hanata yin maganar datayi niya tahanyar cewa”miyasa zandaina kallonki?”…….
Sincerely tace “You’re making me feel nervous”, murmushi yayi tareda sake janyota zuwa jikinshi wannan karan harsuna jin numfashin juna cewa yayi “Really?”….
Mutsu mutsu tafari tana niyan guduwa,amma yaki sakinta sema cemata dayayi…
“inazakije?”……
Rasa abuncewa tayi atake kuma se idanunta yasauka kan bowl din ruwa da towel data kawo dan haka cikin sauri tace”yauwa daman zanyi massaging jikinka ne with normal water kozai rage zafin dayakeyi”………

Kwantar da kanta yayi ajikinshi da kaman bazaiyi magana ba can Kuma yace”I don’t need it,I only need your warmth”…….

Itadai shiru tayi batasake cewa komaiba yayinda bugun zuciyarta ke karuwa akowani dakika tanajin sanda yajamusu blanket har kansu amma ko motsi takasayi,Jin bakinshi tayi ah saitin kunneta in a whisper yakuma cewa”I missed you”,har kusan 5 seconds kafin yakarasa sentence din da “so much,I so much missed you Asma’u”…….

Kasa cewa komai tayi don only God knows irin farin cikin datakeji awannan lokacin,she really can’t believe it wai yau Almustapha kecewa yayi kewanta sauran yace yana sonta that’s the only thing she’s waiting for tana cikintunanin nan bacci yayi awun gaba da’ita shikam tun tuni yayi baccin daman. da asuba ita tafara tashi,babu laifi zafin jikinshi yafara raguwa ah yanzun sedan gumi dataji kaman jikinshi nayi kokarin banbare jikinta takeyi daga nashi amma abun yaci tura don bakaramin riko yayimata ba cikin kakkausar murya tashiga kiran sunanshi”Yaya Imam”….
“Yaya Imam dai”….
bude idanunshi yayi ahankali tareda daurasu kanta ashagwabe tace”it’s time for subhi prayer”…….

Batareda yakula zancentaba yasa hannu yasake kwantar da kanta ah kirjinshi sannan ahankali yace….
“I missed you”……
Batasan sanda murmushi ya subuce mataba kafin tadago tana kallon fuskarshi kana tace”I missed you more Yaya Imam”……..

Sakinta yayi cikin sauri tareda kauda kanshi gefe,atake Itama yanayin fuskarta tacanza ahankali tace…
“bakason ince nayi missing dinka ne ni ko baka yarda da magata baneba?”, jijjiga mata kai yayi alamar a’a kamar yanda yayi mata jiya da dare cikin sauri tace”haka kamin jiyama please tell me what’s happening”,takarashe maganar tareda juyo da fuskarshi gareta adede lokacin kuma sukaji ana shirin shiga sallah wannan dalilin yasa tasauka daga kan gadon tana barina hada maka ruwa sekayi wanka kayi sallah harta kusa isa bandakin taji yakira sunanta”Asma’u”……
Juyowa tayi tareda cewa”na’am”…..

Alama yayimata da hannu kan taxo,gyada mishi kaitayi tareda karasowa inda yake yafi two seconds yana kallonta kafin yace”Don’t ever leave me again please”, murmushi tayi kafin tazauna gefenshi tareda saka hannunshi cikin nata”is that what you were thinking?”……
Gyada mata kai yayi ahankali kamar wani maraya,taimaka mishi tayi yazauna kafin tashiga taimaka mai wurin cire T-shirt din dake jikinshi seda tagama cire Mai T shirt da vest din ciki kafin ta taimaka mai yacire wandon ma yarage dagashi sai Boxers duk yana binta da idanunshi. komawa tayi tazauna gefenshi tareda kwantar da kanta ah kafadunshi tana shafa kirjinshi slowly sabida kyaunda wurin yamata can kasa kasa tace….
“To ka kwantar da hankalinka I’m going nowhere”……
kamar karamin yaro yace”Really?”…
Gyadamai kai tayi ahankali kafin tatashi cikin sauri tayi bandaki don tasan inta biye mishi bazasuyi sallah akan lokaci ba,seda tahadamai ruwan wankan sannan tazo tataimaka mai yaje bandakin inda tafito tana jiranshi haryayi wankan,seda ta tabbatar ya tada sallah kafin tashiga donyin wankan itama harta gama abunda takeyi yana kan sallayar seda suka gama addu’o’insu kafin tatashi tsaye tareda cire hijabin jikinta ta ajiye gefe sannan tamika mai hannu alamar yatashi,miki mata hannun nashi yayi seda ta tabbatar yakwanta sannan ta lulluba mai blanket tajuya daniyar fita jitayi yariko hannunta cikin sauri tajuyo pity face yayi”inazakije Kuma?”….
Tace”my room”….
Sake kasa da murya yayi sannan yace”must you go there?”……
Gyada mishi kai tayi ahankali don tama rasa mezata cemishi,shagwabar Almustapha tsakanin jiya dayau yafara kuremata duk wani tunaninta, ahankali yakuma cewa”promise me you’ll come back?”…..

STORY CONTINUES BELOW


Ahankali tace”I promise”,sakin hannunta yayi kafin tafice ah dakin jiki ah sanyaye seda ta’isa dakintan ma sannan tafara tunanin mema tazoyi dakin,itadai kawai tasan ta tsincin kanta dason zuwa dakinta ne bawai don tanada abunyi ba,karema dakin kallo tashigayi ahankali tasan dai bahaka tabar dakinba ahankali takarasa bakin gadon anan tayi arba da singlet’s dinshi sunkai hudu ah ajiye sekuma gajerun wanduna mamakine yakamata na me sukeyi agurin bitayi tana dauka daya bayan daya harta gama kafin tawuce bandaki donsasu ah basket din kayan wanki ananne tatarar da wasu ma,da mamaki tafito ah bathroom din kafin taje wurin wordrobe dinta nanma taga wasu daga cikin kayayyakinshi and some of her belongings ma an yamutsa su, definately someone must have stayed in her room sanda batanan,to who could it be?……..

Wata zuciyar tacemata…
“Wanda kika ga kayansa mana”…..
Kenan Almustapha tarewa yayi adakinta dabatanan komi,is she really that important dazaiyi missing dinta this much?. kasa bama kanta ansa tayi don haka seta shiga gyara dakin cikin hour daya tagama komai and now the room is back to it normal self,zama tayi tana ajiyar zuciya don dan aikin datayin nan setaji duk ta gaji duban wall clock tayi inda taga har 6:30am tayi daganan kuma tayi deciding fara tunanin mezatayi masu na breakfast. ganin tafi mintuna goma batayi concluding mezata girkaba yasata tashi tayi hanyar kitchen din may be intaga available ingredients zatasan mezata girka,gashi Bayin dasuke tayata aikin ma talura babu wanda yakwana ah sashin nasu shiyasa batasa ran zatayi aikin with a helping hand ba. Around 9:00am tagama kammala komai daman chips ta soya da egg sekuma kunun alkama datayi mashi,zuwa tayi tajera abincin kan dinning table because tafison tagyara dakinshi kafin takai musu abincin can…..

Koda tashiga dakin nashi idanunshi nakan kofa looking as if he’s waiting for someone and the moment dayaganta setaga yayi wata nannauyar ajiyar zuciya cikeda tsokana tace”kadauka na gudu ne?”…….

Becemata komaiba sema tashi dayayi daga kwancen yazauna dan yanzu yanadan jin karfin jikinshi,zama tayi gefenshi tareda sa hannu ah wuyanshi tanajin temperature na jikinshi ahankali tace”Good morning”.
Ahankali ya ansa mata da “Morning”….. 1

“How are you feeling right now,hope jikin dasauki!”,tayimasa tambayar showing how much she cares,gyada mata kai yayi ahankali dakaman bazaiyi magana ba kuma don harta fidda rai setaji yace”feeling much more better”…..
“Masha Allah,to katashi kayi wanka sekaci abinci kasha drugs ko?”…….
Jijjiga matakai yayi alamar a’a,cikeda mamaki tace”bazakayi wankan ba”…..
sake gyada mata kai yayi alamar”eh”,batareda ta damuba tace…
“to katashi kayi brush sekayi breakfast ko?”…
Shima jijjiga matakai yayi alamar a’a cewa tayi….
“Brush dinma?”
Gyada matakai yakumayi alamar “eh”,batareda nuna gajiyawaba tace…
“to inkawo maka abincin kenan?”….
Wannan karan”eh” yace mata,tashi tayi tafice yana binta da idanu batajima ba segata tadawo rikeda tray din ajiyewa tayi kafin tadibamai abincin ah plate tareda hada mai tea ah cikin mug,bashi abincin tadinga yi abaki yanaci slowly harya gama don yaci sosai ba laifi shiyasa ma bata takuramishi dazancen kariba. batasan prescription na maganinba don haka tashiga tambayarshi ya za asha drugs din,fada mata yadingayi tana balla tana bashi yanasha harsuka gama sannan ta tattara kwanukan tafita dasu annanne taji ana knocking kofar……

zuwa tayi tabude kofar inda tayi arba da Sulaiman da Sumayya looking so perfect together cikeda zolaya tace “Awnn! What a perfect match,match made in heaven” …

Dariya Sumayya tayi kafin Sulaiman yace”Dole kice haka ai donki rufe mana baki ko,tonidai senayi comment”,dariya tayi tana Sis kishigo don Allah yanzu mijinki seyasani jin kunya babu gyara babu dalili,wannan karan dukansu suka sheke da dariyar kafin suka karasa tsakiyar parlourn Sulaiman Yana tambayarta jikin Yayansa,cewa tayi “Dasauki alhamdulillah”……

Eh dake yasamu strong medicine ba,jijiga kai Asma’u tayi tana dariya kafin tace kukarasa ciki mana yana daki jijiga kai Sulaiman yayi yana nibazan shiga dakin mai mataba, Sumayya ne tace jiyada ka shiga fa Dear….
Playfully yace”jiya ae matar batanan yaukuma tadawo”…..
Murmushi Asma’u tayi kafin tace”nidai inzaku shiga kushiga kadaisan baida karfin jikin fitowa”,kafin tarufe bakinta taji kamar takun mutum abayanta wannan dalilin yasata juyawa ganinshi tayi yana dingisawa cikin sauri takarasa gareshi tareda taimaka mai tanamai masifar miyasa baikirata ba yawani fito shikadai”kasan you’re not that strong shine zaka tako kai kadai what if wani abu yasameka fa”,tayi maganar kamar zatayi kuka kallonta yayi ahankali kafin murya can kasa yace”Kuka zakiyi?”….
Harara tabuga mishi yayinda tadauke kanta daga kanshi, murmushi yasaki ahankali kafin in a whisper yace”I’m fine Asma’u, nothing happens bashikenan ba?”…..
Kin kulashi tayi harsuka karasa parlourn atare su Sumayya sukace”Oh wow, lovebirds kenan?”……

STORY CONTINUES BELOW


Hararansu Asma’u tayi kafin tayi wucewarta kan dinning ta debo abincin dake gurin tazo ta jera musu tanaji Sulaiman da Sumayya na kwaikwayon abunda sukayi dazun itada Almustapha tareda yin dariya Sumayya harda cewa sweetheart inbani da lafiya inbakayi kaman zakayi kukaba zanbaka suspension na one week….
Dariya suka sake kecewa da,hararan da Almustapha yasakar ma Sumayya ne yasatayin saurin sauka daga kan kujerar takama janyo plate ba shiri don zuba abinci dukdama bawani yunwa takejiba, dariya Asma’u tayi aranta tana”Yarinya man kaza”, kafin tayi wucewarta daki bayan tace musu tana zuwa. wanka tayi abunta tashirya cikin simple doguwar rigarta ta material,sanda takoma parlourn samun su Dad,Mom da Hajiya Muniba tayi duk sunzo duba jikin Almustapha din lokaci guda taji kunya ta lullubeta because aganinta ita yakamata tafara zuwa tagaida su ah sashin su kafin sufara haduwa anan,jitayi Dad yace”Daughter zo mana”……

Cikeda kunya takarasa inda yake”Dad Ina kwana”…..
Murmushi yayi sannan yace”lafiya Lau dear,ya hanya kunyi isowar dare ba mu haduba jiya bare inbaki hakurin bata miki budget din trip dinki danayi”……
Sa hannu tayi ta lullube fuskarta tana”laa bakomai fa”….
“To Allah yayi miki albarka,babu inda yafi ma mace irin gidan mijinta barema ah irin wannan lokacin dayake tsananin bukatar ki shiyasa nace kidawo badan komai ba”,Amin ta amsa da haka tagaida su Mom dinma tanajinsu suna ta tsokanar Almustapha da “drug dinshi ta’iso daga Maiduguri”,shidai baice musu komai ba dazasu taimake shima su kwashi kafafunsu sutafi subarshi da matarshi zefi mishi komai dadi. Likita yazo yasake duba shi and alhamdulillah yace BP dinshi yasauka babu laifin hakan bakaramin dadi yayima kowa ba sannan yasake jaddada mishi karyana wasa da drugs dinshi and he should be eating his three square meals on time,shidai kawai gyada ma likitan kai yakeyi batareda yasan meyake cewa ba bangare Asma’u kuwa everything is noted in her brain don duk bayanan likitan babu wanda tayi missing,seda yatafi sannan tazame jiki tayi dakin Almustaphan tagyara fes fes haka bandakin ma tashiga wankeshi tas kafin tadawo tasa turaren wuta ah dakin. Komawa dakinta tayi ta tattara duk innerwears dinshi dataga sunyi datti tawanke,tashanya sannan takoma dakinshi don gyaramai kayanshi don dazu taga wardrobe dinshi ah hargitse abunda bata taba gani ba tunda take dashi seyau…..

Ciro kayan tayi duka tashiga gyarawa tanasa kowanne ah right place dinsa harta gama sa hannun datayi zata rufe wardrobe dinne taji anrungumota tabaya,wani irin nannauyar ajiyar zuciya tasauke tareda sakin lallausar murmushi aranta tana fadin”he’s back at the right time,don daman tafison seta gama komai”…….

Juyowa tayi tana fuskantarsa,cewa yayi”Sannu da aiki”….
Bata amsa sannun daya mataba sema cewa datayi..
“miyasa baka kirani inzo inshigo dakai ba”……
Sa hannunshi duka biyu yayi tareda zagaya waist dinta ahankali yace..
“I’m sorry Ma’am”…..
Turo baki tayi tana”bawani nan”,zesakeyin magana tayi saurin katse shida”Su Dad suntafi ne?”….
Cewa yakumayi”Yes Ma’am”….
Wannan karan heart melting harara tasakar mai kafin tasaka hannayenta tafara cire bottles na jallabiyarsa tana”Muje kayi wanka inyaso sekayi sallah kahuta tunda ankusa kiran sallar azahar”…….

Cire hannayenshi yayi daga kugunta tareda sa hannun yaciro nata daga jikin jallabiyarsa kana yace”No”,kallonshi tayi blanky”No kuma?”
“Yanzuma bazakayi wankan baneba?”….
Gyada matakai yayi ahankali,”to se yaushe zakayi Yaya Imam bagwanda kayi yanzun ba kaikanka zakaji dadin jikinka”…..

Sake cemata yayi”No”…..
Cire hannunta tayi daga nashi hannun kafin tamaida kan botiran riganshi tacigaba da cirewa…
“Wae yaushe Mr Taciturn yakoma kazami ne?”……

Murmushi yayi sannan yace”mekikace?”…..
Cikin rada tace”eh mana Yaya Imam,yau tun safe ba brush,ba wanka and you ate like this bayankuma ni Yaya Imam din dana sani mutum ne mai tsafta da kyankyami duk wani abu dazai shafi harkar lafiyarsa baso yakeyi ba,why did you change so suddenly?”,tayi masa tambayar cikeda curiousity…..

Matso da fuskarshi yayi kusa da tata cikin rada yace”You changed me Mrs Taciturn”…….

Ware idanu tayi tareda dan yin dariyan yake dukda effect din da taji ga maganarsa tasa kafin tace”kanason kace nina maida ka kazami Yaya?”…….
Shima yar siririyar dariya yayi yanzun seta samu kanta da tsayawa tana kallonshi because bata taba ganin this side of him ba,he really looks good when he’s laughing kuma ma irin dariyar datake kaiwa har cikin zuciyarnan tafi yimashi kyau,sake matsowa yayi daf da fuskarta yana kara kasa da murya”I don’t know about that anma nidai nasan duk abunda kikaga is new from me to you’re responsible for it”,dariya tayi nervously sabida uncomfortabilty datakeji intana kusa dashidin. Dakyar ta’iya cewa tonidai inma nice namaida ka kazamin inason yau atashi daga wannan alhinin akoma mai tsafta,make mata kafada yayi alamar beyarda ba……

Cewa tayi…
“Ya ilahi that means I’m not responsible for your kazanta”……
Sake make mata kafada yayi wannan karan she couldn’t stop herself from laughing at his childishness kafin tajuya daniyar tafiya tana”nikam bazaka kasheni da dariya ba Yaya Imam”……..

feeling somehow guilty ahankali yace “kyamata kikeyi komi?”….
“Am I smelling bad?” ,Cak ta tsaya daga tafiyar da takeyi kafin tajuyo tazuba mai idanu shima kallonta ya tsaya yi waiting for his answer, ahankali kuma tadinga takawa har inda yake matsawa tayi daf dashi kafin tasa hannayenta tazagaye neck dinshi slowly tareda yin dagel kadan because yafita tsayi kan ya ankara yaji bakinta cikin nashi, kissing nashi tashigayi passionately he was very shocked,so shocked dan baiyi expecting haka daga gareta ba seda tayi mai isarta sannan tacire bakinta cikin nashi ahankali in a whisper tace”Bana kyaman ka Yaya Imam ko kadan,i love you for who you’re and I’ll never….kanma takarasa maganar taji yasake hade bakinsu guri daya sede nashi kiss din is very slow and genle wanda hakan bakaramin tafiya da imaninta yayi ba, she’s feeling nothing than the sweetness and freshness of his mouth wanda har hakan yasa tafara tunanin anya baiyi Brush dinba da batanan,she can’t deny it tayi missing dinshi so much da words bazai iya zayyanawa ba,sunfi 3 minutes ahaka kafin yasaketa suna ajiyar numfashi dukansu biyu murya can kasa yace”I’m sorry”…..
Murmushi tayi sannan tace”For what”……
Kai tsaye yabata ansa da”For judging you,infact for everything Asma’u most especially that night”,sa finger dinta tayi kan lips dinshi tana “shhhhh”……
And then right there,at that moment,he just stared at her beautiful eyes dakyar ta’iya cewa”That was our past Yaya Imam”…..
Ahankali yace “but still”,sake sa finger dinta tayi akan lips dinshi tace”banace maka past dinmu baneba,bygones are bygones Yaya Imam besides it was never your fault”……

Sake daura fuskarshi yayi kan nata yanadan goga mata hancin shi kan nata yayinda hannunsu ke sarke dana juna yace”then why did you leave me all alone that night tunda kinsan it was not my fault?”,lumshe idanunta tayi ahankali tanajin komai dayafaru alokacin yafara dawo mata filla filla dakyar ta’iya cewa”I’m sorry “,don aganinta tafito tacemasa Umminshi ne taboyeta bai daceba kwata kwata daga kanta yayi yadaura akan kirjinshi tareda cewa cikin rada…..
“seda kika tafi nasan importance dinki,seda kika kika barni nasan how much you mean to me Asma’u”…..

You’re something that…
You’re something that I’ll forever treasure!….. +

“I LOVE YOU ASMA’U”…. 4

Jitayi maganarshi ta daki dodon kunnenta hakanan setaji abun kamar amafarki wannan dalilin yasa tayi saurin dago kanta daga kirjinshi tareda tsura mishi idanu kamar wata wawiya shima itan yake kallo gyadamata Kai yayi ahankali…
“Yes Asma’u! I’m in love with you dukdama bazan iya cewa ga sanda nafara son kiba all I know is:

“You’re so special more than you know and more than I show.”

“You’re my soul mate, you’re my lover, and you’re all that I see.”

“And may be it’s your smile,it’s your eyes,it’s your beautiful heart and it’s your cries that make me fall for you,ajiyar zuciya yasauke tareda cewa ahankali…

“I’ll love you forever even long after we die”,wannan karan Asma’u hawaye takeyi kamar wanda aka bude ruwan famfo, she’s feeling as if she’s the most happiest lady on earth”,begama rikita mata lissafiba seda taga yayi kneeling agaban ta dukda kuwa ba ishashen lafiya banedashiba. miko mata hannunshi yayi tareda cewa….
“I’ve a request please”…….

Itadai batace komai sebinshida idanu da takeyi gakuma kuka datakasa tsaidawa dama Asma’u da kuka bare ansamu dalili!…. 2

I know I’ve wronged you many times,I know I’ve hurt your feelings times without number and I know that I’ve never reciprocate your love in the past. But believe me I’m a changed person now because I’m in a situation whereby I cannot live in a world were you do not belong”,wannan karan kalaman Almustapha sunfara yimata nauyi,does she really deserve this. Dasauri tabishi kasa Itama ta tsuguna ah gabanshi cikin muryar kuka tace”banace maka wannan duk past dinmu baneba tun dazu?”……..

Murmushi yadan saki ganin yanda tayi maganar ashagwabe sannan yace…
“Then be my friend Dear”….
Turo mai baki tayi…
“I’m your friend since day one Yaya Imam” ….
Karacewa yayi….
“Be my life”….
Cewa tayi
“Your life is my biggest treasure already because without you the world seems empty”,Kara kasa da murya yayi don Allah kadai yasan yanda yakeji ayanzu tareda cewa”two more request Asma’u”, kallonshi tayi ashagwabe alamar yafara gajiya sake kasa da murya yayi”Please”wannan Karan kamo hannunshi tayi tasaka cikin nata sannan tace inajinka Yaya Imam……
Yace”Be light and be my wife please!”……
Murmushi takumayi sannan tace…..
“tun randa aka bada sadakina nazama matarka Yaya Imam so,i’m yours already”……
Kissing forehead dinta yayi slowly sannan yace…
“then,you’re my shoulder and my strength,you’re the person I need and the one who is there. I have you right now and it doesn’t seem fair.Cause right now isn’t enough and forever is too soon.
without you i would die from within and not know what to do.

You’re more than a friend and more than a wife too.
You’re my forever and forever isn’t long enough for me and you.

I hope there’s a place in heaven waiting just for you.
I pray there is room right there beside you for me too.

Asma’u,You’re a beautiful soul and I could forget you never. I just pray that we are always together now and forever. bude mata hannunshi yayi inda tasakar mai murmushi tareda shigewa jikinshi yarungumeta tsam feeling as if the world only revolves around the two of them. ahankali Asma’u ta amsa addu’ar dayayi ah last statement dinshi da”Amin ya Allah”…..

Da dare bayan su Sulaiman sunzo sundubashi sun tafi tadubeshi tace”Yaya Imam yabana ganin su Rukayya ah sashin nan?”……
“Wace Rukayya?”,yayi mata tambayar cikeda curiousity ahankali tace”my helpers”……
Daga remote yayi yana canza channel kafin yace…
“ninace ace sudaina zuwa, what’s the essence tunda bakyanan amma yanzu kindawo we can get them back”……..
Murmushi tayi kafin tace”Bayanzu ba”…..
“Can you do the choes alone?”….
Gyada mishi kai tayi kafin tatashi da niyar kwashe kwanukan abincin dasuka ci she can feel the way he’s busy staring at her kafin ta ankara taji yajanyota kan cinyarsa,wara idanu tayi,ahankali ya juyo da’ita tana fuskantarshi ashagwabe tace..
“Yaya Imam dai”……
Kwaikwayon muryata yayi”Matar Yaya Imam dai”,Yar dariya tayi sannan tace”tattara kayan abincin nan zanyifa”…….

STORY CONTINUES BELOW


Dan goga karan hancinta yayi sannan yace….

“Wae bazaki sakeyimin maganar wanka bane?”…..
Dariya tayi tana”ni naisa kalan kace ina kyamarka”,shima dariyar yayi tareda dan yimata light kiss sannan yace” Nima bansan miyasa ba naji yau gabadaya banason yin wanka but you know I was kidding right?”……
Ahankali tace”Uhm Uhm”…..
Sa hannunshi yayi yazagaye kugunta sannan yace”to yanzu nace wasa nakeyi Matar Yaya Imam”…….
Hadiyar wani abutayi akasan makoshinta sannan tace”uhmmm”…..

“So,i need a warm bath now”,kallonshi tayi jin yanda yayi maganar cikin rada seda yadaidaici takalli cikin idanunshi sannan yakarasa da”With you”,zare idanu tayi wanda hakan yasashi dariya batareda yashirya ba. Babu yanda baiyiba suyi wankar tare amma taki haka ya hakura tahada mai ruwan inda yashiga wankan itakuma takoma parlour ta tattare kwanuka takai kitchen sannan tawuce nata dakin tashiga wanka. Datafito shafa haddaddun natural mayukanta tayi sannan tafesa turare masu dadi da sanyaya rai,zuwa tayi tabude wardrobe dinta tabangaren da nightwears dinta ke jere gabadaya rasa wanda zata saka ma tayi don wanda tasaba sawan setaji yaubatason sakasu,she need something new and cute that’ll she’ll impress her husband with wannan dalilin yasa tafara daddaga su daya bayan daya amma still duk babu wanda yayimata because most of them ba nighties din kirki bane ba dakyar tasamo wani baby pink cotton riga iya gwiwa tasaka shidinma bawae yayi mata bane kawae dai yadaifi sauran ne sa ruffle tayi tana gyara daurin gashinta taji andaga ta cidok kamar Baby zata saka ihu taji yace”Shhhh it’s me”……
Bedireta ko’ina ba se kan gado alokacin ne ma tayi realising ashe ruffle dinta yafadi acan gaban wardrobe tunda gashi taji gashinta ah baje ah bayanta,tashi tayi da niyar sauka akan gadon yayi saurin tareta tahanyar zama agefenta yana”Ina zakije?”……

Ribom dina ne yafadi,ganin yanda tayi maganar ah rikice yasashi cewa relax barina dauko miki Itama cikin sauri tace”You don’t have to haryanzu jikinka baigama kwariba amma baka iya zama aguri daya”, takarashe maganar tareda sauka daga kan godon inda taje tadauko ruffle din sannan tadawo inda yake tana kokarin sake kama gashin nata guri daya,karban ruffle din yayi yakama mata sannan tace”muje ka kwanta to it’s late already”…..
Make kafada yayi”I’m sleeping here”,ware idanu tayi”no way”…..
Kafeta yayi da idanu”May I know the reason?”…..
“Ba girmanka bane ka kwana ah dakina Yaya Imam”,Yar dariya yayi tareda janyota kan cinyarshi Yana shinshinar kamshin jikinta me kwantar mai da hankali cikin rada yace”sede kar akuma yarinya, I’ve been sleeping in your room tunda kika tafi besides you’re my Wife we’re now one so duk wani abu nawa nakine hakanan duk wani abu naki nawane sabida haka banason sake jin wancan zancen kinji”,gyadamishi Kai tayi ahankali kwanciya yayi still tanakan cinyartashi kafin yajanyo hannunta tafado kirjinshi cikin rada yace”I like your scent”…….
Lumshe idanunta tayi tana shakar nashi kamshin turaren kanta ankara taji bakinshi cikin nata daganan kuma aka lula duniyar maaurata……

Bamu leka mutanen chadiiiiii!🚶‍♀

*CHAD, N’DJEMANA*

Washegarin komawan su Mallam Hudu da Asma’u su Ummi suka wuce Chad dasafe. Tunda jirginsu yayi landing ah airport din N’Djemana wanda yake capital city dinsu Ummi kejin tarihin rayuwarta nada sunfara dawo mata daya bayan daya,batama ga yanda garin tacanza ba seda suka shiga mota zasu wuce masarautar N’Djemana sannan taga garin yacanza sosai sabida akwai alot of improvements gashi garin yazama more modernize wanda hakan besa taji kamar ba’a mother land dinta take ba,that feeling of being home is still running between her blood. Tunda suka shiga motar daman tanagefen Mai Martaba yanakuma lura da yanayinta wannan dalilin yasa yajanyota zuwa jikinshi tareda kwantar dakanta ah kafadunshi ahankali yace everything will be alright dear, murmushi kawai tasakarmai bawai don bugun da zuciyarta keyi ya ragu baneba ahaka harsuka isa masarautar babu laifi masarautar haddiddiya ce bana wasa ba donkuwa Ummi seda tashiga masarautar ma tagane cewa ba garin N’Djemana bane kadai yacanza hardama masarautar su. At first da suka isa questions dogarayen masarautar suka shiga yimasu Mai Martaba dakansa yayimasu bayanin daga Nigeria suke masarautar Zaria take yaga fuskarsu tacanza daga murtukewar dasukayi zuwa na murmushi kankace me akashiga yin nannan dasu itadai Ummi kasa cewa komai tayi haka aka saukesu awani katafaren parlour dayasha ado su Amira de se kalle kalle sukeyi abunsu can jimawa kuma sega wani dattijo yashigo yana sanye da kaya ta alfarma daka ganshi kaga jinin sarauta gaba da baya kallo daya nayi mishi naga matukar kamar dasukeyi da Ummi sede ita tafishi haske nesa ba kusa ba,dogarayen dasuka rakoshi tundaga waje suka tsaya wanda hakan umarni ne daga gareshi shine yafara hango Ummin cikin muryar zumudi da farinciki yace *Khairiya*!…
Itama kuka tasaki tareda tashi tsaye tana fadin *Huzaifa* karasowa yayi cikeda kewa kafin yajata yarungume cikin jikinshi yanayimata yaren shuwan dabansan me suke cewa ba😂….

STORY CONTINUES BELOW


Abba da Ya’yanshi kuwa sebinsu da idanu da sukeyi dakyar suka samu suka tsagaita kafin yadubi Mai Martaba yagaidashi don tabbas bai mantashi ba dukda ma rabonsu da juna tun lokacin haihuwar Almustapha, tambayar Khairiya yayi yana nunasu Afiya share hawayenta tayi kafin tace mishi ya’yanta ne murmushi yasakar musu tareda ware musu hannu alamar suzo gareshi,kunya ce takamasu dukda hakan baihana su shigewa jikin nashiba. Atake yakira daya daga cikin dogarayen yace suje ayi announcement cikin masarautar kan cewa akwai family meeting daza ayi dayanman nan Ummi ne tace cikin yaren shuwa”I can’t wait for long anymore Huzaifa,let me meet my family it’s been long already”, murmushi yasakar mata kafin yace”Baki kaini zumudin hakan ba Khairiya sede kudin matafiya ne kunkuma debo gajiya so yakamata ku ci abinci kuhuta tukunnan. Mai Martaba ne yatari bakinshi tahanyar cewa”you don’t have to worry zamuhuta daga baya”,cikeda jin dadi Sarki Huzaifa yace toshikenan kafin yatashi yana rikeda hannun Afiya da Amira suka fita suka bar parlourn inda Ummi, Hamida da Mai Martaba suka mara musu baya kafin dogarayen ma sukabisu sunyi tafiya mai tsawo kafin suka iso wani sashi wanda yafita daban dakowanne sashi dake cikin masarautar, Ummi tasan bangaren mahaifinsu ne shiyasa tunda suka doshi gun taji bugun zuciyarta na karuwa ahaka suka kutsa cikin sashin kafin sukasamu kansu awani katafaren parlour hango wani tsoho tayi zaune kan katuwar darduma yana karatun alkur’ani ahankali. karasawa sukayi suka zaune seta kuma fashewa da kuka ganin yanda mahaifintan ya tsufa yayi kutub dashi wanda hakan ne yasa tsohon dagowa cikin sauri nan suka hada idanu cikin muryar kuka tace”Abbeey” and right there she didn’t miss the tears that slipped from his eyes. Rufe Alkur’anin yayi inda Huzaifa yakarasa cikin sauri yadaga yaje ya ajiye aciki drawern dasuke ajiyewa,cikin muryar tsufa mahaifin nata yadaga hannu yanamata Alama datazo yanakiran sunanta”Khairiya”…
Cikin kuka tace na’am Abbeey kafin takarasa gareshi suka rungume juna yana kuka mai tsuma zuciya yana kuma fadin”kiyafemin ‘Yata”….
“Forgive me please, I’m a heartless Father”,duk wanda kezaune agurin seda yazubar da kwallar tausayi Ummi daman fear dinta baiwuce tazo acemata mahaifinta baya rayeba tunda ko alokacin datake gida he was somehow old but alhamdulillah seeing him right now takes all her worries away sauran taga Amminta matar dakesonta harcikin ranta,matar da ko alokacin da duniya ta gujeta ita tagoya mata baya takuma yarda da’ita without thinking twise dukdama batabita but at least she believe in her and that’s the only thing that matters agurinta. Kan kace Mai parlourn tsohon sarkin N’Djemana yacika da Yan uwa da abokan arziki kowa senannan yakeda Ummi da ya’yanta yayinda itakuma Ummi babu abunda tafiso awannan lokaci iya taga mahaifiyarta amma babu ita babu dalilinta dakyar aka tsagaita murnace murnacen da akeyi kafin akazauna baki daya don ah tattauna……..

Tsohon ne yafara da duban Khairiya kafin yace banida bakin baki hakuri Khairiya sabida banzamo uba nagari garekiba,naguje ki ah lokacin dakike tsananin bukatata wanda haryau abun na hunting Dina, I’ve been regretting this for years now and da ace zan iya maida hannun agogo baya da nakoma nagyara laifuffukana amma hakan bazai yuyuba shiyasa akullum banida wata burin daya wuce inganki inga kindawo gida cikin Yan uwanki inkuma ga naroke ki kinyafemin and alhamdulillah with Allah everything is possible bantaba fidda rabo ba sabida nasan addu’a ta bazata taba fadi abanza ba and finally here you’re with your lovely kids and husband wanda ma banyi tsanmanin hakan ba tunda adadin nasan kinzo da zancen cewa kun rabu. Ajiyar zuciya yakumayi sannan yace Habibty kiyafemun please,my mind will never be at rest inbanji kin yafemin laifuffukana ba hakanan se inaji kamar mahaifiyar ki tana kallona da abun tunda ko bayan tafiyarki akullum maganarta baiwuce innemeki indawo dake gidaba, akullum maganarta baiwuce banyimiki adalciba har Allah yakarbi ranta to which I’m still feeling guilty cewa nice ajalinta, Ummi wani kukan tasaki najin Allah yayima Ammi rasuwa, innalillahi wainna ilaihir rajiun ashedai wanda take tsanmanin zata gani din baita zatagani ba shiyasa akullum yakamata mudinga tunawa ita mutuwa babu ruwanta da shekaru,tsufa kokuma rashin lafiya inlokaci yayine dole se antafi takan dauki saurayi,jariri aduk sanda taga dama hakanan tana iya daukan Mai cikakken lafiya tabar wanda yajima yana fama da jinya ah raye,ya Allah kasa mucika dakyau da imani Allah kuma kasa muyi kyakyawa karshe😰…

STORY CONTINUES BELOW


Amin ya rabbi. Tunda Ummi tafara kuka kowa ah parlourn yaji mutuwar Ammin tadawo masu sabuwa dan babu wanda bai zubda kwallah ba mata tagari,ga hali nagari gata dason mutane da hakuri indeed they lost a very beautiful damsel. cikin kuka Huzaifa yace Ammi hartabar duniyar maganarta dayace”kunemo Khairiya kudawo da ita cikin ku batada gatan dayafi nan itada Danta”……..
Ahankali Ummi tace”Allah sarki Ammi na Allah ubangiji yayi miki rahama indeed you’re the best Mother I’ve ever come across sede inabakin cikin rashin sanar dani dabakuyi ba uwa uwace,she needs my prayers koba komai”….
Sake sharar kwallah sarki Huzaifa yayi don Abbeey kam tuni yadaina maganar donshima kukan yakeyi….

Sarki Huzaifa yace”tun bayan rasuwar Ammi Abbeey yafara nadaman actions dinsa towards you and that was when yaturamu muje harcan NIGERIA mudawo dake amman it was not a success don ba ama barmu munshiga masarautar ba inbanda korar wulakanci da akayimana akace bakya masarautar, kunjima da barin gurin sabida ankama ki kina yaudarar mijinki,nima dai daman banyi tunanin samunkiba tunda nasan kinzo har Chad kuma kinnuna kun rabu da naki mijin atake muka kira gida muka fada inda nabada shawarar aneme ki anan Chad din may be bakima baro kasar ba while on the other hand muzamu nemeki anan NIGERIA. Ajiyar zuciya yayi sannan yace I spent 5 months in Nigeria Ina neman ki Khairiya amma babu labarin ki akoina,we did all we can amma babu labari haka anan Chad dinma shiyasa kawai na tattara nakoma can gida inda nabama Abbeey shawarar mucigaba da addu’a and I believe you know we’re looking for you may be kin buya ne, may be you were still angry with us,may be you don’t need us anymore as a family tunda sanda kikazo neman taimako gurin mu mun juya miki baya……..

Cikin kuka Ummi tace”I can never do that,you people are my only family no matter what bazan taba yin fushi dakuba”……

Huzaifa yace”then meyafaru awannan lokacin,where were you don babu irin neman dabamuyi mikiba Khairiya wanda hakan yasa Abbeey yayi loosing so many hope,wanda rashin ganinki yasa yatashi daga active mutum yakoma inactive indae akan maganar sarauta ce,sauka yayi ah karagar mulki sabida bashida focus inda ni aka daura ni, I’m now the king of N’Djemana kullum Abbeey addu’arshi Allah kada yakarbi ranshi baki dawo garemuba,so what took you so long Ina kike all this time, we’ll all like to hear your story……..

Murmushi tayi sannan tace”abubuwa da dama sunfaru Huzaifa wanda nikaina ayanzu banason intuna baya sabida rahamar da ubangiji yayimini ayanzu amma yazama dolena intuna bayadin,you people are my family you need to know the reason why najima banzo gareku ba”…..

cikin nutsuwa Ummi tashiga basu labarinta tundaga farko har karshe batakuma boye musu komaiba and many of them shed tears for her,a very heart touching story dabasu tabajin irinshiba wanda har wasu ke mamakin daman akwai mutane irin Magajiya aduniya?……..

Huzaifa kuwa cewa yayi”I’m very sure she’s the one datamin wannan wawan maganar na kinbar masarautar and you cheated your husband ashedai she was the ashole”,yayi maganar raibace wanda hakan yadansa Ummi dariya kadan kafin tace”yau inatake bagashi Allah yatoni asirinta ba and she’s in a place dabazata iya escaping punishment din laifuffukan datayiba”. …

Gyada kai sukayi dukansu yayinda Abbeey datun bayan dayayi maganar neman yafiya baisake cewa komaiba seyanzu yace”it’s all my fault Khairiya daban korekiba da hakan duk bazata faruba”……
Murmushi Ummi tayi sannan tace”Abba balaifin ka baneba komai da kake gani aduniyar nan Allah yariga da ya tsarashi, it’s in my destiny hakan zai faru and destiny can never be denied it only be dalayed. Mudauka cewa wannan kaddarorine dasuka faru damu sabida Allah yagwada imanin mu and alhamdulillah hakan baitaba sawa mungujeshiba koda na rana daya ne kuma kaga yamangace mana komai yanzu akuma lokacin dabamuyi tsanmani ba”……..

Yanzuma gyadakai mutanen parlourn sukayi yayinda wani acikin yayun Ummin “Ahmad” yace “wai ina Imam ne”,Dan basu manta sunanshi ba tun yana yaro dariya Mai Martaba yayi sannan yace….
“he’s now a grown up recently akayi nadin sarautarsa as the crown prince”……
Cikeda mamaki mebin bayan Ummi “Juwairiya” tace I can still remember the last time dakuka zo dan karami dashi yana yawo a parlourn Abbeey playing with his toys tayi maganar tana describing kankartansa da hannunta,dariya sukayi inda Saudat wanda Itama kanwar Ummin ce tace”Akhi kinmanta damun Suhail dayakeyi yakoyamai sword fighting”……

Suhail dake can gefe yace”yea I can still remember,Imam nadason sarauta tun yana kankaninshi I’m very happy dayasamu wannan matsayin”, murmushi Ummi tayi kafin tace…
“and now he’s acting kaman bayasoba bayan nasan har kasan ranshi yanason abun”.
dariya sukayi duka inda Ahmad yakuma tambayar miyasa ba azo dashiba dariya Mai Martaba yayi kafin yace”he’s coming next week insha Allah aikine yatsaida shi”,dariya Ummi tayi tareda cewa”kadaina ma Danka rufa rufa yadai tsaya dinke zaren daya warware ko”,dariya sukayi dukansu dukda basu gane inda
Ummin ta dosa ba tunda bawani hausa suka iyaba……..

Afiya dake gefene taturo baki tareda sakin kuka lokaci guda gabadaya attention yakoma kanta inda dasauri kawunnan ta da Auntie’s din sukayi kanta suna tambayarta lafiya,kin kulasu tayi suma kuma basubar rarrashinba suna kuma faman tambayarta meya faru seda tayi mai isarta sannan tadago tadube su ganin basuda niyar barinta,turo baki tayi gaba kafin tace cikin shagwaba”Bakune kuketa maganar Yaya Imam ba kadai mu ko sanin mu bakuyi ba’, takarashe maganar tareda sake fashewa da kuka dariya tabasu ba kadan ba kafin suka shiga rarrashi suna “Kiyi hakuri,we love you equally shidin don munsan yarintarsa ne shiyasa muketa tuna biya”,Saudat ne takarada “kuma bagashi kunzo yanzuba so,we’ll make alot of memories with you now and next idan kunzo zamu tuna baya”…

Yar dariya Juwairiya tayi tareda sa hannu tana gogema Afiya hawayenta tanacewa”harma cewa zamuyi tayi kuka tana kishin Yaya Imam”,dariya sukayi dukansu inda aka cigaba da hira kafin daga karshe Abbeey  yace akaisu masauki suyi wanka,su huta,suci abinci”….

To sukace kafin akayi masu rakiya har sashin dazasu zauna bakaramin mamaki Ummi tayiba ba ganin sashinta na tun tana yanmata da mamaki ta dubi Sisternta Juwairiya tace”haryanzu bangaren nan na existing”cikin zolaya Juwairiya tace”dakin dauka anyi demolishing ne kome?”, Ummi cewa tayi”Aa kawai dai banyi tunanin samunshi agyare haka ba”, dariya 
Juwairiya tayi kafin tace” to bakiji sashin nan ba’a wata ba ayi gyaranshiba it’s an order from Abba, akullum tsumayin zuwanki yakeyi shiyasa yakecewa agyara sabida bayason kizo sashin ba agyare ba”…….
“Murmushi tayi tareda cewa Allah sarki Abbeey na”….Washegari dasafe bayan sunyi Asma’u breakfast Almustapha yasha drugs dinshi tadubeshi tace… +

“Yaya Imam baka kira su Ummi ba tunda suka tafi”,Kai tsaye yace…
“fushi nakeyi dasu”,wara idanu tayi tana kallonshi da mamaki”fushi kuma?”
“Dasukayi lafin menene?”……

Yana wasa da tafin hannunta yace”kinfini sani ae”,dariya tayi”Allah niban saniba Yaya Imam”,Kai tsaye yace”ba guduwa sukamin dake ba” dariya ta kyalkyale da tana mamakin ya akayi yasani kafin tace”waye yafada maka”,yace magana ah *GIDAN SARAUTA* tana buya ne?”.
Dariya takumayi sannan tace”gaskiya kam bata buya because akwai radio masu blood tako’ina,yanzudai nabada hakuri on their behalf ayi hakuri akirasu aji ya suka isa Chad. Make mata kafada yayi alamar beyarda ba batarai tayi sannan tace”you’re being stubborn ko Yaya?”…….
Kin kulata yayi se ma binta da kallo dayakeyi cire hannunta tayi cikin nashi tatashi tsaye daniyar tafiya tana”tunda you’re being stubborn then I’ll be stubborn too and in nafara nawa stubbornness din baza ah ji saukin sauko dani dawuri ba”, murmushi yayi sannan yatashi tsaye shima yana”really?”….

Abubuwan data gani ah idanunshi ne yasata kokari guduwa amma tuni yakamota yasaka ajikinshi murya can kasan makoshi yace”are serious you want to be stubborn?”,murkudamai baki tayi cikeda karfin hali kafin tace yes wani heartmelting kiss yasakar mata ah kumatu still baimatsa daga gurinba yasake cewa”you still want to be stubborn”,kaman zata shike tace”Yaya Imam!”,dariya yayi sannan yadan saketa seyaga tafashe da kuka kuma aitake ya rikice yana meya faru kuma?……..

Cikin kuka tace toka kira su mana tunda kasan bazan iya fushi dakai dinba already”, I’m sorry matar Yaya Imam wasa nakeyi maki and about calling them kinsan banmasan inda wayata take ba?”….

Dariya tayi tace”Nima I left it at home tunsanda nakira ka ka katsemin waya nayi fushi najefata ah wordrobe daganan bansake bitakanta ba haryau”……..
Yace”kode ke kika katsemin waya ba”…
Ashagwabe tace”bawani kaine ka katse call din”, stubbornly shima yakuma cewa”I even call you back akashe fa”……..
Batasake cewa komaiba se tura baki datake tayi kamar karamar yarinya sa hannu yayi yaja bakin playfully sannan yace”to kiyi hakuri kuma koma miyene ninadauki laifin naji nayarda nina katse call din shikenan?”…….

Murmushi tayi sannan Itama tace”bazan yarda inbarka kadauki laifin da bakai kayishiba so, dukanmu munyarda mudauki laifin kawai besides what matters is we’re together now”…..
Gyada matakai yayi yana smilling kafin yaja hannunta sukayi daki yana fadin muje innemo mana wayar musata ah chargi semu kirasu cewa tayi to. Haka suka wuce daki baisha wahalar neman wayarba yasamu aikuwa batada charging kamar yanda yayi tsanmani daman akwai wuta sesuka jona charging wayar suna yar hirarrakinsu. Dayanma suka kira Mai Martaba suka gaisa inda yayi musu fada sosai akan zamantakewar aure kafin yasaka musu albarka bayan sungama magana dashi dinne suka kira Ummi atake tana dagawa tace”Imam ka manta da Ummin ka ko”,Murmushi yayi yanadan shafa suman kanshi sannan yace”kedai kika manta da Imam dinki Ummi”,dariya tayi sannan tace bawanin nan kaida kanason kamaida laifin kaina ne shima dariyan yayi sannan yace”Ina wuni Ummi?”….
Cewa tayi “Lafiya Lau dear Ina Habibty na?”……

Dan jan karan hancin Asma’u dake kwance ajikinshi yayi sannan yace tanajinki Ummi,turo baki Asma’u tayi tanamishi alamar da miyasa yayi mata haka mika mata wayar yayi daidai saitin bakinta kan tayi magana akunyace tace”Ina wuni Ummin mu”….

Lafiya Lau Habibty,how was your trip hope you land safely nayita kiranki wayar ahkashe…

“Lafiya Lau alhamdulillah Ummi wayata namanta ta agida ne tunsanda zamuyi tafiya shiyasa baki sameniba”…….
Ana wasa da waya ne Dear?
You should always keep it with you sabida amfaninta na gaggawa zai iya tasowa at anytime kinji,gyada kai Asma’u tayi kafin tace”insha Allah Ummi”….
Kokefa daman Imam din ya aika ah karbo miki acan gida kokuma kumaje tare aiyajima beje gidanba cewa takuma yi to Ummi murmushi Ummi tayi kafin tace stay blessed my dear, cikeda son surukartata Asma’u tace thank you Ummi kigaidamin Mommyn unborn da su Afiya nan tamikawa Almustapha wayar inda Ummi ke kara jaddada masa maganar zuwa gidansu Asma’un shima cewa yayi “to Ummi”,daganan kuma tashiga bashi labarin yanda sukayi da Yan uwanta dakuma yanda suketa tambayarshi kafin daga karshe tace..
“as soon as Sulaiman din yadawo seku taho tareda Asma’un ko”…..

STORY CONTINUES BELOW


Cewa yayi”insha Allah Ummi kigaidamin su please”,cewa tayi zasuji kafin sukayi sallama. Dubanshi Asma’u tayi”yaushe zamuje gidan?”….
Wara idanu yayi sannan yace”waike dagaske xuwa zamuyi?”….
Bata rai tayi”mekake nufi Yaya Imam”,kasa yayi da murya”kunyarsu nikeji Asma’u I can’t just meet them now bayan abubuwan dasuka faru”,wara idanu tayi da mamakinshi tareda cewa”kenan bazaka sake ganinsu ba har abada komi?”…..
Yace that’s not what I mean,eh mana inbahaka ba tomiye Yaya Imam?……
Look,duk abubuwan dasuka faru you’re a victim babu laifinka ko daya aciki besides kai abun atausaya makane Yaya Imam and I assure you iyayena bazasu tabayimaka wani kalloba infact they love you more than you can imagine and moreover dole in one way or the other wataran sekaje can din tunda kana taredani. Yasan maganarta gaskiyane but he’s not just ready to meet them now don haka yacemata”you’re absolutely right anma bayanzuba Asma’u kiyimin uzuri don Allah”,gyada mishi kai tayi sannan tace nayi maka Yaya Imam dina shima murmushin yasakar Mata tareda cewa “thank you Matar Yaya Imam zantura Sulaiman yakarbo miki insha Allah”,Sekuma yasake cewa”ko mu barma Munira wayar nema then we’ll buy another one for you”,cikin sauri tace”Munira fa kace”,yace yes ita akwai magana ne?…
She’s still young Yaya Imam babu maibarinta tarike waya ah gida yace toshikenan se akarbo mikidin inyaso duksanda takai rike wayar basai asaya mataba. Gyada mishi kai tayi cikeda gamsuwa aikuwa adaren ranar ya fadama Sulaiman zancen karbo wayar cewa yayi to washegari segashi ya kawo mata murna tayi sosai tareda yimashi godiya.

Bayan kwana biyu jikin Almustapha yayi sauki sosai fiye da yanda kuke tsanmanni dan yanzu yakoma normal self dinshi harma yana shirin fita Fada yaudin. Koda Dad da sauran yan Fada suka ganshi bakaramin dadi sukaji ba nan aka shiga yimashi yajiki yayinda yake amsa gaisuwarsu fuska dauke da fara’a bakaramin mamakin sanjawarshi sukayiba ayaudin bama susha mamaki ba seda akazo ana tattauna wa game da harkokin masarautar suka ga yana participating sosae tareda bada nashi shawarwarin hakan yayi masu dadi sosai atleast they now believe sunyi zaben shuguba nagari. Daren ranar Na’im yazo Asma’u tace”wata sabon gani”,dariya Na’im din yayi sannan yace”becemiki nayi tafiya baneba?”…….

Jijiga mai kai tayi ahankali kafin takoma ciki daniyar kawo mai abun motsa baki,koda ta dawo ajiye tray din hannun ta tayi tareda cewa”Ina wuni?”…
Murmushi yasaki tareda cewa”lafiya lau Matarmu sekika guje mu abunki har kike neman haukata min aboki”,dariya tayi sosae sannan tace”bagashi nadawo ba”……
Saukowa yayi daga kan kujera yazauna ah kasa tareda janyo tray din yashiga zuba exotic din data kawo mai acikin glass cup kafin yace”to tunda andawo ayi hakuri kada asake tafiya abarmin aboki shi kadai don Allah,amananshi nabaki yanzu”……
“Insha Allah,consider it done Dr”,yaji dadin kalamanta seyace thank you suna haka sega Almustapha yashigo tambayar shi Na’im yashigayi ya karfin jiki mikamasa hannu Almustapha yayi suka gaisa kafin yace”dasauki alhamdulillah,how was your trip”, Na’im dinma cewa yayi alhamdulillah kafin suka zauna hira kuma can Na’im yadubi Asma’u yace”ya mutanen Chad hope they land safely”……..

Lafiya Lau suke, murmushi yayi kafin yadan sosa kai sannan yace”wayar Hamida bata shiga I don’t know why”……
Da mamaki Asma’u tace”dagaske?”….
Yace “eh”,tace”tonidai kafin inbarsu ah Maiduguri tana using phone dinta smoothly bansani ba ko bayan tahowata wani abun yasami wayar”…..
“Probably,gashi banda nasu Afiya bare inji daga garesu”,harararsa Almustapha yayi sannan yace”mezakace ma Hamidan wai?”…..
Mayarmasa da hararar Na’im yayi sannan yace”Ina ruwanka”…….
Murmushi Almustapha yayi sannan yace”kadai bini ahankali kasan dai nidin babban yayane ko?”…..

Kallon Asma’u Na’im yayi sannan yace”wai yaushe miskilin mijin kinnan yayi bakin magana?” …..
Itadai murmushi tayi tanajinsu sunatayi kafin daga karshe dazai tafi tabashi number Afiyan tace yagwada kira zaisamesu insha Allah godiya yayimata sannan yayimasu saida safe……….

*CHAD, N’DJEMANA*

Bakaramin jin dadin zaman garin sukeyi ba wanda har suka rasa daya daga cikin dalili biyu……

STORY CONTINUES BELOW


Shin weather din garin ne da yanayinta kokuma irin kauna da hospitality da yan uwan Ummin ke nuna musu ne,abinci kuwa babu kalar wanda basuciba ah cikin nau’ikan girkin kasar Chad din kama daga maharagwe(chadian coconut beans),Gormandize,Kachumbari, Brochette de poisson dadai sauransu barinma sweet potato dinsu yanda suke soyatama daban dan randa aka fara kawo musu babu wanda yayi zaton sweet potato ne seda suka kai baki Amira takasa yin shiru tace wannan kamar dankalin hausa dariya Auntynsu Saudat tayi kafin tace”shine mana dakin dauka menene?”, Hamida ne tace nima banyi tunanin shibane ba seda nakai baki sabida yanda kuke sarrafata daban dayanda mukeyin namu”…….
Dariya Saudat din takumayi sannan tace”hope yayi muku dadi?”……
Dasauri sukace “sosaima”……
Lol toshikenan nima zanzo inkoyi yanda kuke naku Afiya ne tace muma zaki koyamana yanda ake wannan Aunty……
Ansawa tayi da inshallahu I’ll you teach dukdama Ummin ku ma ta’iya sosai. turo baki Amira tayi to ai batayimana Aunty Saudat……
Afiya tace”eh wallahi ni abincin Chad danaga Ummi tataba yi ma gurasar sunnan me dadi ne kadai wanda akeci da pepper soup din kayan ciki shima rabon da tayi harna manta. Kwanansu biyar ah Chad sukaji anata zancen wani waishi *Amaan* first born din juwairiya  zedawo hutu daga Egypt,Alexendra inda yake karanta Marine engineering acan already ma har yana final year, yanda mutanen gidan ke dabbaka dawowar nashi zai tabbatar maka da cewa he’s one of the favorite son’s na masarautar. Randa jirginsu zaisauka ah N’djemana su Amira sunga abu don tun safe aketa gyare gyare dakuma girke girke kala kala wanda har hakan yafara bata ran Afiya because ita mutum ce dabata cika son jin andamu da mutum ba kaman wani gold, around 5:30pm ya iso masarautar tareda wanda suka tarbo shi daga airport din babu inda yafara dira inbanda sashin mahaifiyarsa bayan sun gaisa ne yaje yagaida Abbeey dasauran Uncles din sa da Aunties nanne yasamu labarin  dawowar Long lost Auntynsa duban juwairiya yayi yace”Ammi(sunan dayake Kiran juwairiya kenan) kikaini inganta please, I’ll will like to meet her and her family”,aikuwa atake aka rakashi har sashin su yana hango Ummi yakarasa da sauri ya rungumeta lovingly kafin yadago yace…

“so,I finally got the chance to meet the long lost Aunty Khairiya da kullum sai anyi maganarta acikin gidan nan dukda cewan tajima batanan hakanan jimawan datayin baisa anmanta da’ita ba ko da na rana daya ne”……
“From all indications I just know you’re special”

Ummi is just out of words tama rasa maizata cemasa se murmushi dataketayi juwairiya dake gefe ne tace”Amaan nefa”……
Bude baki Ummi tayi wangalaulau cikeda mamaki kafin tace”Masha Allah,my little Amaan ne yagirma haka”,dariya juwairiya tayi inda Ummi tasa hannu tashafa kumatunshi tanasaka mashi albarka haka kawai seyaji kunyar matar nason kamashi jin yanda take fadin yarintarshi azuciyarshi yace”so,she knows many things about me”…….

Bayan tagama zolayarshine yadubi bangaren dasu Amira suke duk shi suke kallo yace”my cousins?”…..
Murmushi Amira tayi kafin tace”good afternoon”,fuskarshi cikeda annuri yace”Afternoon darling sis I’m Amaan”,yakarashe maganar tareda mika mata hannu dariya kawai tayi batareda tabashi hannun ba kafin tace”Amira”……
Yace nice name Amira,munyi kewarku dayawa fa kungujemu for so long da harna fara tunanin zuwa Nigeria inyi cikiyarku dariya Amira da Hamida sukayi inda Afiya taji gabadaya haushin shi take ji sabida yacika surutu gashi ma ita ko kallon inda yake batayiba bare har tayi tunanin zasu gaisa aranta tace”watauma Amira kadai yagani komi?”…

Dan tsaki tayi kafin tatashi tayi daki tanaji yana gaisawa da Hamida. Binta yayi da idanu yanacewa”Bata magana ne itan?”, yakarashe maganar yana nunata dariya sukayi duka inda juwairiya tace”kishi ne dai yatashi bakayi mata magana ba kayiwa sauran”…….

Da mamaki yace”banganeba Ammi?”…
Dariya juwairiya takumayi kafin tabashi labarin abunda yafaru ranar murmushi yayi sannan yace”perfect Ammi”….
“This’s the perfect choice daman ni banason auren mata biyu kinga faduwa tazo daidai da zama”…..
Kallonshi duka sukayi yayinda yawuce dakin da Afiyan tayi juwairiya na”Amaan Ina zakaje?”….
Yace”Zance zanje Ammi”…
Dariya tayi tareda jijiga kai kafin tadubi Ummi tace”Don’t mind him he likes joking all the time”….
Dariya Ummin ma tayi sannan tace”I hope harzuciyarshi ne because najima inason hada irin wannan zumuntan”….
Amin ya rabbi cewar juwairiyan kafin suka canza wata hirar kuma. Acan bangaren Afiya kuwa tunda tashiga dakin tayi kwanciyarta tareda sa earpiece akunne tanajin wata Indian song *pehla pyaar* wannan dalilin yasa batamasan sanda yashigo ba kawai seganin mutum tayi kanta yana zaune kan bedside drawer atsorace ta tashi tana shirin sakin ihu…….

STORY CONTINUES BELOW


Ahankali yasa hannu akan lips dinshi sannan yace”Shhhh”, batasan miyasa ba seta samu kanta dabin umarnin nashi. Sa hannunshi yayi yazare earpiece din dake kunnenta sannan ya marairaice murya”seriously yanzu haka akeyi cousin sis?”……

Harara ta watsa mishi danayi mefa?……
Ahankali yadaga hannunshi yana irgawa”babu sannu da zuwa,kinganni kikayi gudowarki daki and now kika harareni aikoni aljani ne anganni for the first time dai ayimin shimfidar fuska”,seyanzu Afiya taji bata kyauta ba hakanan setakejin kaman ta bata tarbiyar da Ummi tayi mata ne na gaida nagaba dakai aduk inda kaganshi akunyace tace”Ina wuni”……
Murmushi yasakar mata wanda har saida dimple dinshi ya lotsa kafin yace”Yana iya dole na in ansa tunda shiri nikeson muyi ba fada ba?”……
Murmushin Itama tayi tareda saukar dakanta kasa sannan tace”to ai baka ansan bakuma”…

Yace”Afuwan lafiya lau”……
Takuma cewa”ka sauka lafiya”……
Dan shafa suman kanshi yayi kafin yace”lafiya Lau alhamdulillah Habibty”,batasan sanda tadago da kalleshi ba hada idanu sukayi kafin yasakarmata murmushi”bakyason sunan ne?”…….
“Gyada mai kai tayi alamar eh”….
Dariya yayi kafin yasa hannu ah side daya da kirjinishi”ohhh no you broke my heart darling”,dariya tayi tareda jijjiga kai don seyanzu tagama yarda yanada surutu tabbas she’s a talkative too amma batasan miyasa ba ita bata fiye son taga wani yafita iya surutun ba ganin tana dariya yabata rai”dagaske kinyi breaking heart dina fa”…….
Batabar dariyan ba tace”kanabani dariya”…..
Marairaicewa yakumayi”I’m serious”….
Ganin kaman dagasken yakeyi yasa takuma dagowa takalleshi yace”miyasa bakison ince miki habibty?”….
Kai tsaye tace”Kai Yayana ne ae so I expect you to call me with my name like anyone does”…..

Dariya yayi kafin Yace”to ae ni inason in aure kine sabida naga kamar zamuyi suiting junan mu” ……
Dasauri ta dubeshi yace”yes cousin kinga ni banida ra’ayin auren mace fiye da daya”……..
Hararanshi tayi tace”Toni miye hadina dawannan zancen?”…..
Murmushi yayi sannan yace”sabida kinada kishi kinga inkika aureni zamu zauna lafiya without any problem and secondly I love you,Iove at first sight cousin nasan bakisan ni ba bakuma kisan halina ba amma dukda haka inason kibani dama please!”,yyi emphasising please din tsayawa tayi galau galau tana kallonshi itakam bata taba ganin mutum irinshi ba daga haduwar fari seya wani furta yana sonta without even thinking twice,can she really believe this guy jitayi yakuma marairaice murya”bakice komai ba Kinga ko hutawa banyibafa nazo nan”……
Hararanshi tayi”to aini ban rike kafarka ba”,dariya yayi”nasani cousin amma still ataimaka abani chance din”….

Tashi Afiya tayi  tasauka daga kan gadon kafin tace”tayaya zanma dauki maganarka Yaya Amaan,you don’t even know my name daga gani na seka ce kanaso na?”……
To I’m not that type of Ladies dazaka yaudara besides I’m your cousin inkanayima matan waje irin haka nibai kamata kayiminba don ko albakarcin zumuncin dake tsakaninmu ka duba……
Dasauri yatashi daga zaunen dayake yasha gabanta sannan yace”atunanin ki wasa nakeyi aduk abubuwan dana fada”…..
Tsayawa tayi tana kallonshi seyanzu take ganin kyawunshi fari,dogo ga hanci kaman shiya kerama kanshi and moreover structure din jikinshima is something to be looking at,kallo daya zakayimashi kagane yanada dangantaka da mahaifiyar ta don kuwa seyanzu take ganin kamarshi da Ummi sosai sake kasa da murya yayi”niba mayaudari baneba and all the words dana fada were right from the bottom of my heart in baki yarda ba I’ll prove it to you insha Allah”,daganan yajuya yayi tafiyarsa yabarta tsaye gurin kamar gunki……
Tundaga ranar Amaan yashiga rayuwar Afiya koyaushe yana makale da’ita tun tana gwasaleshi harta daina donshi mutum ne that’s so jovial da duk yanda kakai ga bakin hali bazaka iya yimashiba ga halin kirki dasanin yakamata wanda azaman datayi dashi ne tagane dalilin dayasa mutanen gidan ke mutuwar sonsa. kankacemai shakuwa sosai tashiga tsakaninsu wanda har iyayen kansu suka fara zargin akwai wani abu bangaren Amira ma daman tanada saurayinta Dan sarkin Gombe wanda anadin sarautar su Almustapha yaganta yace yanaso nankuma aka dinke akullum suka zaune Ummi cewa takeyi”yarana sungirma mun kusa Shan biki”…….
Amira sede tayi dariya Afiya kuma Andinga musu kenan”aa Ummi Amira dae angirma amma banda ni”……
Dariya kawai Ummi takeyi ta kyaleta don tariga da tasan yanzukam Afiya has something for Amaan koda kadan ne…..

STORY CONTINUES BELOW


Satin Mai Martaba daya ah Chad yakoma gida Nigeria kan su Ummi zasuyi wata daya sannan sudawo and alhamdulillah yasamu komai natafiya daidai amasarautar sede yayi mamaki da Sulaiman da Sumayya basu tafi Jakarta ba according to plans wannan dalilin yasa bayan yahuta yaci abinci yasa aka kiramai Sulaiman din nan yashiga tambayarshi dalilin rashin tafiyan  nasu”dan sosa kai Sulaiman yayi kafin yace we’re planning on going for honeymoon dasu Yaya Almustapha ne tunda Sister in-law din tadawo daganan se inyi dropping Sumayya ah school indawo gida”…….
Murmushi Mai Martaba yayi ganin yanda Sulaiman din keta noke noke ahankali yace”sekuyi ku tafi dawuri sabida kudawo on time inbahaka ba hakan na iya affecting karatunta kaga dae she wasted alot of time here”,gyada kai Sulaiman din yayi cikeda gamsuwa kafin Mai Martaba yace”jeka Allah yakaiku lafiya and if you people need any of my support just let me know”….
“To Abba thank you”…
Daganan Sulaiman yatashi yafice cikeda murna already yagama masu planning komai tafiya ce kawai tarage matsalar dayace Allah yasa Almustapha kada ya gwasaleshi don haryau bai fada mishi ba…….

Da dare Sulaiman yaje yasamu Almustapha yayi masa maganar tafiyar tasu sannan yajaddada mai da already yayi planing komai kallonshi Almustapha yayi sannan yace”you did so much without asking for my opinion?”……
Fuskar tausayi  Sulaiman yayi sannan yace”I’m sorry Bro naga baka da lafiya ne shiyasa”
“Okay”,kawai Almustapha din yace mishi cikeda zumudi Sulaiman din yace”we’re leaving next tomorrow fa?”….
Gyada mishi Kai Almustapha yayi wannan karan, cikeda mamaki Sulaiman din yace”you’ve no problem with that kenan?”……
Nanma gyadamishi kai Almustapha yakumayi wata irin runguma yayima dan uwan nashi kafin yace”Thank you Yaya Almustapha I assure you you’ll like everything out there,you won’t regret going there with me”……
Dariyar yanda Sulaiman din keta farin ciki yayi sannan yace”bakada matsala yaronnan”,daman can Almustapha yana planning zuwa honeymoon da Asma’u din kawai dai bai furta baneba besides bema gama deciding ya abun zai kasance ba segashi kuma Sulaiman yazomai da zancen shiyasa babu bata lokaci ya yarda. Bayan Sulaiman yayi mishi saida safe shima ya tattara laptop da news papers din dake gabanshi yayi ciki adaki yasameta tana nade inner wears dinsu seda ya ajiye kayan hannunshi sannan yazo yazauna gefenta tareda cewa”wai ke bakya gajiya da aikine?”….

Dariya tayi kawai yayinda yamika hannu yadauki daya daga cikin kayayyakin yafara ninkewa shima cikeda kaunarshi tace”daka barshi dan wannan abunne aiki”…..
“Ke danazo nasame ki kinayi nahaki yi ne?”….
Girgiza mai kai tayi alamar aa kafin tace”Amma ai kayi korafi”,dariya yayi”tunda korafine kadai aida sauki so abarni inyi tunda nayi niya”……
“To Yaya Imamu”…
Turo baki yayi…
“to waini yaushe zaacanza min sunannan please?”……

Wara hannunta tayi alamar batasaniba mischievous smile yayi sannan yyi wurgi da kayan hannunnashi tareda matsawa kusa da ita murya can kasa yace”kosai munsamu little one ne za afara ceman Abban unborn”,jitayi kunyarshi takamata lokaci guda sekawai ta sunne kanta ah kirjinshi don duk yanda zatayi ta gudu tasan ba bari zaiyiba, ajiyar zuciya yayi tareda sa hannu ya rungumeta calmly..
“I love you Mamin Unborn”……
Wara idanu tayi kafin tace”cikine dani?”…
Kissing forehead dinta yayi sannan yace”bakyason kisamu cikin ne?”……
Setayi shiru tana blushing ah jikinshi cikin muryar rada yace”sooner or later insha Allah”…….
Cikeda kunya tace Allah yarda Amin ya amsa mata da kafin yashiga bata labarin yanda sukayi da Sulaiman dazun murmushi tasaki”Honeymoon Kuma?”…..
Dagota yayi daga kirjinshi yana kallon kyakyawar fuskarta”bakiso mujene”…….
Tace”Aa Kawai naga newly weds couple ke zuwa yawanci mukuma gashi auren haryakusa shekara ma”……..

Dariya yayi sannan yadaura fuskarshi kan nata ahankali yace”silly girl kawai,to bakiji to the world we might be married for almost a year but for me the journey has just began Asma’u,it began just recently”,yayi maganar slowly kafin yakarada and insha it’ll last for till eternity”,lumshe idanunta tayi tanajin dadin kalamanshi itakanta seyanzu tasan tayi dacen miji hakanan seyanzu tasan ribar hakuri. washegari tadameshi suje gida tayi sallama dasu Ummi amma yaki sam wai shi kunyarsu yakeji dariya tayi sannan tace”wai kunyar nan harzuwa yaushe zatayi lasting Yaya Imam?”……
Yace”I don’t know really”,kama hannunshi tayi tana wasa dashi sannan tace to kayi hakuri muje don Allah kaji takarashe maganar cikin sigar lallashi kallonta yayi cikeda rashin gamsuwa kafin yace”towaima cemusu zakiyi zamuje Honeymoon komi?”.. 
Dariya tayi “to miyene aciki?”
Wara idanu yayi”oh hakama zakice to munfasa zuwa”,cikin sauri tace”Don Allah kayi hakuri wasa nakeyi makafa i promise bazan anbaci word like honeymoon bama”……
Yace”promise?”…
Tace”i promise”….
Ahankali yace”to kishirya semuje da yanma”……..
Wani irin tsalle tayi tafada jikinshi tana”thank you,thank you,thank you so much my Mr Taciturn”,dariya yayi shima kafin yadan dagata sama yana rikeda kugunta ahankali yace”I somewhat miss this name”…….
Dasauri tadago kanta”Mr Taciturn din”……
Light kiss yayi mata sannan yace”eh mana yadaifi Yaya Imam din dakike cemin wallahi”…….
Dariya tayi”really?”….
Tace”yea, seriously”…..
Cikeda tsokana tace”but the name don’t suit you anymore?”…..
Bata rai yayi tareda cewa”why?”…..
Tace”because you’re now Mr talkative not Mr Taciturn”….

STORY CONTINUES BELOW


Sauketa yayi kasa still yana rikeda ita sannan yaja cheeks dinta dadan karfi kukan shagwaba tasaki”Yaya Imam dazafi fa”…….
Yace”wayene yakoyamin surutun?”…
Ba ita matar Yaya Imam din bane takoyamin,yayimata tambayar yana binta da idanu. Turo baki tayi”aa kam niban koyama surutu ba”….
Yace”then call me Taciturn tunda bakiyarda ke kika koyamin surutun ba”…..

Make kafada tayi”naki sede Mr talkative”,rike baki yayi yana…
“to Mrs talkative”……
Dariya tayi do you really love the name shima dariyan yayi wani suna?….
Tace”Mr Taciturn  din mana” murya can kasa yace”yea, because that’s the first name dakika fara addressing dina dashi so bazanso inmanta sunan sk easily ba”. Shiru sukayi duka zuciyar fes kafin yace kinsan menene, jijjiga mai kai tayi alamar aa kafin tace”seka fada”…….
Cewa yayi sanda naga word din acikin reply din dakikamin ranar bansan meaning dinta ba and I just don’t know why that time senaji inason insan maanarta,quite sure I know I’m a person that likes to know new things amma nakin yabani mamakin urge din insan meaning din alokacin was too heavy, kinsan hankalina fa kasa kwanciya yayi har seda naje library naduba dictionary because I don’t have phone that time barema induba in a very easiest way. Murmushi tayi tana kallonshi lovingly sannan tace”hope ka ajiye littafin nan safely?”……
Yace”it’s in a safer place ae bazan taba yarda wannan book din ba yana daya daga cikin memories dinmu”, taji dadin kalamanshi setace”thank you Mr Taciturn”…..
Shima yace”I should be the one to Thank you Mrs Taciturn”se sukayi dariya kuma dukansu. Dayanma suka shirya sukaje gidan su Asma’u,basu samu Daddy ah gidaba wai sunyi tafiya da Aliyu,Musa da Mubaraq ma duk baswa gida se iyayensu Mata kawai,Asma’u ne tashiga gida tafada musu tana tareda Almustapha din aikuwa nan sukaje suka gaisa yanata sussune kai kasa waishi kunya, bakaramin dadin ganinta da mijinta su Ummi sekayiba sewani nannan akeyi dashi Ikram kuwa tunda ta dale jikinshi takasa saukowa se aikin game dataketayi ah wayarshi bewani jimaba yadauki Ikram din suka fice inda yayi ma Asma’u text zedawo da dare yadauketa……….
Reply tayimashi da to wishing him all the best…….

Da dare bayan isha segasu sundawo Asma’u nazaune parlourn Ummi tanacin tuwo miyar kukar Ummi data jima bataciba se santi takeyi Munir da Musa suka shigo niki niki da kaya da mamaki Asma’u tace”harsu Daddyn sun dawone”,don tasan daman shine inzai dawo daga kowacce tafiya seyayi musu tsaraba”,ajiye kayan Musa da Munir sukayi kafin Musa yace”bafa Daddy bane Yaya Yarima ne yasiyo waina ikram ne”, Ummi dayanzu fitowarta daga daki tace duk wannan uban kayayyakin ina ikram din zatakaisu?……
Dariya Musa yayi sannan yace ba Uncle dinta bane yasaya mata kubarmata abunta yakarashe maganar tareda fara bude lodojin duk kayan zakine aciki  kama daga chocolates,sweets, biscuits dadai sauransu sekuma daya bude wasu ledojin nan yaga toys da kayan wasan yara Ummi tace”Allah yakara budi amma don Allah kicemai kada yakara irin wannan wahalar kayan sunyi yawa ai daga zuwa bakunta seya buge da wahala fisabilillahi”…
Itadai Asma’u taunan kashinta take tana dariya tsaki Ummi tayi tace”oh nama zama abun dariya kenan komi?”……..
Cikin sauri tace”yi hakuri Ummi”,harara Ummin tasakar mata sannan tace”seki tashi kikaimai abinci yaci ai kafin yafara maganar tafiya kuma”,turo baki tayi Ummi kibarmin tuwon nikam zantafi dashi nayi dumamen shi inyaje gida zaici wani abincin dakuwa Ummi tayimata”ungo naki,nace ungo naki aidayake cemiki nayi tuwon danke nayi”…….

Kaman zatayi kuka tace”Ummi tafiya fa zamuyi gobe kinga bazan sake samu inci tuwon nan kwana kusa ba”,rai bace Ummi tayo kanta”will you stand up joor kosaina kai miki hannu”,dagudu Asma’u tayi kitchen tana dariya wanke hannunta tayi ta kuskure baki kafin tashiga daki tadauko mayafi tayafa sannan tadawo kan dinning table tadauki tray din abincin da already Ummi tashiryasu tun dazu tafice zuwa bangaren saukan baki. Samunsu tayi shida Ikram din still tana kan cinyarshi tana playing game gakuma tayi kabe kabe da remote din TV takai cartoon duk ita kadai shikuma se kallonta yakeyi yana dariya ajiye tray din Asma’u tayi sannan tace”sannu da dawowa”…….

Murmushi yasakar mata”yauwa sannu Mrs Taciturn”…….
Dariya tayi tareda jijjiga kai sannan tadauki remote akan cinyar Ikram daniyar canza channel tace shine kabiyema yarinyar nan tanasa ka kallon cartoon ko,kanma tarufe baki har ikram tabare nata baki tafara kuka wai ita abata remote dinta dariya Almustapha yayi sannan yamika hannunshi”oya kibamu abunmu”…..
Ran Asma’u abace tace”kabarni da ita tukun inbanda iskanci duk ita kadai ga waya gakuma TV and the most annoying thing bama kallonfa takeyiba”,yace”to Ina ruwanki damu?’……
Turo baki tayi batareda tace mishi komai ba sannan tashiga canza channel din wani ihun ikram tasaki inda Asma’u takai hannu zata bigeta cikin sauri yarike hannunta yakarbi remote din yamaida shi cartoon din datake kallo sannan yabama ikram din yana goge mata kwallarta yace”wayene?”..
“Adda Asma’u ne?”…
Innocent ikram ta gyada kanta tana shesheka kamar wanda aka duka gaske  dagaske,cikin rarrashi yace”to sorry ko, Adda Asma’u bazata sakeba kinji?”….

Gyada Kai ikram din tayi kafin yace”yauwa good girl cigaba da game dinki kinji”…..

Itadai Asma’u da takaici ya isheta seta tashi zatayi tafiyarta tana”ga abinci nan kaci”,cikin sauri yariko hannunta yadawo da’ita baya murya kasa kasa yace”waye zai bani abincin to?”……
Cewa tayi”oho”……
Ajiye ikram yayi akan kujerar tana game dinta sannan yasauko kasa yazauna yajanyo Asma’un tazauna akan cinyarshi fuskarta babu annuri ahankali yajuyo da fuskarta tana kallonshi yace”Miyena bata ran kuma?”……
Tace”Babu”…..
Cikin sigar lallashi yace”sabida nabar Ikram takalli channel dinda takeso komi?”……

Shiru tayi batacemai komai ba murmushi yayi yasan kawai rigima ce ke damunta bawani abuba inbahaka ba abunda yafaru yanzu aganinshi baikai yabata rantaba yasani amma seyace”to kiyi hakuri indai don ikram ne she’s a child, she’s innocent besides nibama kallon zanyiba bare har hakan yadaga miki hankali kinji?”….
Gyada mai kai tayi yana wasa da hannunta yace”to mutafi gida kawai tunda ma fushi kikeyi”,duk seya bata tausayi itakanta ma tarasa dalilin unnecessary fushin da takeyi din”abincin naka fa?”…..
Yace”nafasa ci tunda Matar Yaya Imam is not in the mood”……..
Sauka tayi daga kan cinyarshi tashiga zubamai abincin seda tagama sannan tadawo kusa dashi tace”kaci to”…..
Yace sekinyi murmushi to, murmushin yake tayi yace”this one is fake I want real murmushi right from your heart”,yanda yayi maganar seya bata dariya ahankali yace”that’s my wife,zo kiyi feeding dina to”….

Nunamishi Ikram tayi da hannunta kallon direction din da Ikram din take yayi tanata playing game dinta da alama ma hankalinta baya kansu don haka yamaida kanshi ga Asma’un ahankali yace”she’s not looking at us inzaki bani nikam kibani kinsandai yanzu nasaba da hannun ki ko?”….
Dariya tayi sannan tamatso tashiga bashi abincin yanaci harya gama kafin tattare kwanukan tamayar tayima su Ummi sallama don yace mata yanzu zasu wuce gida, nasiha sosai Ummi da Mommy sukayi mata kafin suka musu fatan alkhairi na tafiyar da zasuyi don tace musu gobe zasubar Nigeria zasu raka Sumayya makaranta daganan zasu wuce Chad. Adaren ranar suka shirya duk wasu necessities dazasu bukata itada shi tunda goben 10:00am jirginsu zai daga zuwa Lagos inda daganan ne zasu wuce ayanda Sulaiman yafada ma Almustapha din kenan……Washegari da safe sukabi sukayima kowa sallama ah masarautar kafin daga karshe suka karasa gurin Dad da Mai Martaba dake parlour zaune abunsu fatan alkhairi sukayi musu yayinda suka fito donyi masu rakiya jikin mota anma da mamakin Mai Martaba seyaga mota  dayace kawai kallonsu yayi sannan yasake dubar motan and at that moment they felt guilty sukansu sunsan laifin su,sosa kai Sulaiman yayi yana shirin magana kafin Mai Martaba yadakatar da shi da hannunshi”where are the guards?”….
Ahankali Almustapha yace”We’re going alone Abba”….. +

Hararanshi Mai Martaba yayi sannan yace”najifa abunda kayima jiya you went out without any support wani irin bahagon tunani ne wannan Imam?”….
You life could be at risk at any time shine anfanin fadawan nan fa bawai don gayu kadai sukeyimaku rakiyarba bare yanzu da mutane suka sanka nibanason irin haka please. Gyada Kai Almustapha yayi kafin kace mai har Mai Martaba yasaka ankaro motoci tareda Fadawa Sulaiman nasonyin magana amma Almustapha ya hanashi tareda cewa”tunda yanuna hakan yafi let’s just do as he says”, Sulaiman yace”to amma ai”, Almustapha baibari yakarasa ba yace it’s okay kaidai Allah yasauke mu lafiya kawai Amin Sulaiman din ya amsa da dukda bawai haka ranshi yaso ba. Haka sukayi convoy suka kama haryar kaduna suna isa basu jimaba jirginsu yadaga zuwa lagos. wuraren 1 jirginsu yasauka acan Sulaiman already yakama musu dakunan da zasu huta wanda acikin airport din take *legend hotel Lagos airport* kafin dai time na tafiyarsu yayi tunda sai dare jirginsu zai tashi zuwa Paris Almustapha da Asma’u daki daya inda Sulaiman da Sumayya na nasu dakin daban wanka sukayi,sukaci abinci sannan suka kwanta don hutuwa haka suka kare ranar acikin daki kowa da matarsa busy enjoying each others company don gabadaya basuji sunada zeal din su zagaya Lagos dinbama bare suyi tunanin fita. da dare wuraren takwas jirginsu ya tashi zuwa Paris. Sanda suka sauka ah Paris din yammacine ah kasar already tundaga gida Sulaiman yayimusu booking hotel shiyasa jirginsu nasauka sukasamu har anturo mota daga hotel din tazo daukarsu haka suka shiga gabadaya ah gajiye suka wuce hotel din Asma’u se kallon kauyanci takeyi bama tayi kallon kauyanci ba seda suka isa hotel din tunda take bata taba ganin guri haka ba komai ya tsaru,komai is just so perfect ah hotel din jitayi kawai Almustapha yajanyota jikinshi cikin rada yace”kauyancin na menene kuma?” ……

Turo baki tayi”ni ba kauyanci nakeyiba”,dariya yayi kawai kafin yajata sukayi dakin da aka nuna mai amatsayin nasu inda nasu Sumayya yana opposite nasu rufe kofar yayi sannan yajinginata da jikin kofar tareda matsawa kusa da ita sosai cikin rada yace”I missed you”,cikin sauri tace”Yaya Imam muhuta mana don Allah”,don tabbas tasan what is to come next amma dukda haka yaki kyaleta seda ya cukwikuyata kafin suka shiga wankan tare tanata kumbura baki dariya yayi sannan yace”towai innafara miyasa ba a hanani,mutum yaji dadin abu amma saiyayita batarai”,kamar zatayi kuka yace”this’s cheating you know”……
Sa hannu yayi yanadan shafa soft lips dinta kafin ahankali yace”cheating?”…
“Like how”…..
Hararanshi tayi”you know my weaknesses ai shiyasa”,dariya yakumayi tareda janyota jikinsa seda ya tabbatar taware  sannan sukayi wankan suka fito lokacinne sukaji ana ringing bell din kofar shiyaje yabude abincine aka kawo musu,karba yayi yashigo dashi ya ajiye sannan yakoma suka shirya lovingly abunsu kafin sukazo suka ci abincin tahanyar feeding juna daga karshe suka hau gado tanaganin yayo jikinta daga idanun shi tagane something is fishy bare baki tayi zatamai kuka yayi saurin sa finger dinshi sannan cikin rada yace”shhhhh,just one kiss Matar Yaya Imam” …..
Turo baki takumayi gaba wanda batasan hakan na driving dinshi crazy baneba,sake marairaice fuska yayi tareda cewa”please!”……

STORY CONTINUES BELOW


Babu yanda ta’iya dole takyale shi dukda tasan ba’a kiss din kadai zai tsaya ba wayaune kawai yayi mata seda suka gama aikin lada kafin sukayi bacci in each other’s arms to hakafa rayuwarsu takoma ah Paris kullum suna daki daga insun tashi suyi wanka,suci abinci sekuma aiyita aikin lada kallo ma baswayi bama sudamu da kunna TVn ba daduk wani facility da aka ajiye musu dukdama dayanma sukan fita harabar hotel din wurin wani garden susha hirarsu da Sumayya da Sulaiman in dare yayi kuma akoma daki sekuma washegari da yanma din duk sunyi kyau abunsu sunyi bulbul dasu ga wani freshness da skin dinsu yayi. Bangaren Sumayya da Sulaiman ma barje soyayyarsu sukeyi hankali kwance nasn kunsan jarabar Sulaiman basai na fassaramuku ba lol😂 gashi Sumayya ma ba bayaba duk wani sirri na killaci miji tasansu arana na hudun me Asma’u tagaji don itadai tunda suka dira ah Paris tasama ranta zasuyi yawace yawace don haka ta yi tunanin yima Almustapha maganar. Dasafe suna kwance kan sofa itadashi suna Playing game ah wayarsa yayinda take kwance ah kirjinshi tace”Mr Taciturn”,yace “Uhmm”,still attention dinshi nakan playing game din dayakeyi din don bayason ya fadi ashagwabe tasake cewa”Yaya Imam dai”…….
Sake cewa yayi”Uhmmm”….
Tace”Mr talkative bazaka kulaniba”….
Dan murmushi yayi still yana game din sannan yace”I’m coming Mrs talkative one minute please”…….

Wannan karan ranta baci yayi ganin completely hankalinshi baya kanta dukdama wai game din tare sukeyi inya fadi ita zata karba tayi so she react this way too when it’s her turn. Shiru tadanyi tana kallon radiant face dinshi that looks so fresh and cute har kusan na minti biyu amma still baibar game din ba maida hankalinta tayi kan kirjinshi dayake vest ne ajikinshi so it’s somehow exposed gashi ne kwance luf luf gwanin ban sha’awa agurin ahankali tashiga shafamai romantically yanajinta yace”naki wayon bazan fadi badai”…..
Dariya tayi”are you sure”,gyada matakai yayi ahankali dukda effect din hannuntan akanshi yafara mai aiki slowly bai ankaraba kawai yaji tamanna bakinta ah gurin cikin sauri yasaki wayar tafadi yana fadin “ya ilahi”…..
Dariya tasaki yayinda yadagata yasake gyaramata kwanciya ah jikinshi”kinsan dai inkika shiga hannuna kafin kifito da wuya ko?”….
Gyadamai kai tayi ahankali kafin yakarada to”kishirya yarinya”, marairaice fuska tayi”to ai magana fa nikeson muyi tundazu amma kaki bani attention”……..
Yace”wace magana ce haka?”…..
Kai tsaye tace”wai yaushe zamu fitane?”………
Dariya yayi,dan bugun kirjinshi tayi”I’m serious nagaji dazama ah daki kullum”,yace kicedai kingaji dani turo baki tayi…
“nifa bahaka naceba”…….
Sa hannu yayi yaja dan karamin pink lips dinta sannan yace wannan bakin baya gajiya dajan attention dina. kaman zatayi kuka tadaga kafarta tanadan bubbugawa ajikinshi cikin sigar shagwaba sannan tace bakace komai ba kacanza zancen kuma,light kiss yayi mata sannan yace”zamu fita amma semunje Fiji”……..
Ware idanu tayi”you mean semun bar Paris kenan?”…..
Ya gyada matakai, ahankali tace”miye anfanin zuwan namuto?”……
Yace”to enjoy each other’s company”……

To ai da zamuyi hakanma koda ah Nigeria ne amma muzo har wata kasa bamu zagaya munga gariba nibanga anfanin zuwanba, dariya yakumayi”to tell me  Ina kikeson zuwa, I’ll take you there dukdama nima basanin gurin nayiba”…….
Tace”Sulaiman ae yasani”, shafa gashin kanta yayi sannan yace “to fadamin Ina kikeson aje?”

Wara idanunta tayi tanadan tunani kafin tace inason inje Inga Eiffel Tower because I’ve been hearing about the place,kissing cheeks dinta yayi sannan yace”consider it done Wife,se ina kuma?”…….
Tace ba intuna akwai wani garden da kawata tataba ban labari since when I was in secondary school so,i’ll like to go there too”…..

Murmushi yayi yana jijjiga kai sannan yace”kituno to I’m all ears”yayinda yake mamakin ya akayi shi baisan duk wannan guraren ba because ko fiji da Sulaiman yacema betaba jin sunan garin ba,nandinma dasuka zo kawai daurewa yayi baiyi kauyanciba sannan abun nashi yasake sajewa da sarauta shiyasa ko yayinma ba lallai ka ganeba,wata zuciyar ne tace”to tayaya ma zakasan irin wadannan abubuwan after all the hardships dakayi going through,at that time inama kake da time din tunanin abubuwa irin haka it was never part of the schedules in your small world that time”………….

STORY CONTINUES BELOW


Asma’u data tuno sunan gurin cikin sauri tace “yauwa Yaya Imam sunan gurin *palace of Versailles* amma setaga gabadaya ma baya kallonta he’s busy looking at somewhere da alama kuma yashiga duniyar tunanine lokaci guda se first day data fara ganinshi agaban shagon Mallam Hudu yadawo mata ahankali tasa hannunta tajuyo da fuskarshi gareta cikeda damuwa tace”Yaya Imam”….
Firgigit yadube ta sannan yasaki murmushi”what where you saying?”…….

Batareda ta kula zancen shiba  tace”Are you trying to hide your pains  from me?”…….
Jijjiga matakai yayi alamar a’a kafin tace”then you’re mistaken,kafadamin don Allah tunanin me kakeyi?”……

Jan kumatunta yayi sannan yace”babukomai fa ke miyasa kincika sama ranka damuwa ne?”……
Batarai tayi”au yanzu nine mesama raina damuwa bama kaiba!” ….
Cewa yayi”eh Mana”,kaman zatayi kuka tace”nidai kafadamin tunanin me kakeyi”, murmushi yayi sannan murya can kasa yace”I’m just thinking of how lucky you are harma kinada friends dinda zakuyi hira sufada miki sunayen wasu gurare dukda baki taba zuwa gurinba during my childhood I don’t know what friendship is,I don’t know what love is,I don’t know what humanity is,I don’t know how to interact with people because all of them were against me,they hate me infact they don’t want me to stay in a place where they belong,dan ajiyan zuciya yayi sannan yace to kinga ah irin wannan lokacin yaushe ma zanyi tunanin irin wadannan abubuwan sabida irin abubuwan nan mutum zaiyi tunaninsu ne only if yana cikin soyayyar jama’a dakuma kwanciyar hankali”………

Asma’u da ah yanzu Kuka takeyi takwantar da kanta ah kirjinshi tanajin yanda heart dinshi ke racing kafin tace”bagashi yanzu yawuce ba yakuma zama tarihi,komai yayi farko zaiyi karshe Yaya Imam and alhamdulillah you’re now enjoying the life you’ve never imagined,you should thank God for that it’s indeed a blessing”…..
Lumshe idanu yayi yanadan shafa gashin kanta cikin sigar lallashi sannan shima yace”a blessing indeed, alhamdulillah”……..

Aikuwa washegari suka fita yawo inda suka je duk inda Asma’u ta lissafa ma Almustapha din kafin suka sake yawatawa wurare da dama,sunsha yawo kam bakarya hakanan ko’ina sukaje sesun dau hoto atake kuma Asma’u zatama su Asiya, Afiya, Amira da Hamida sharing sukuma su daura ah social media like Instagram, Whatsapp kunsandai mutane da yada abubuwa barin ma inkukayi kyau gakuma uwa uba ace mutum yanada title andinga daurawa kenan,daga masu lovebirds,best couples of the year se masu perfect match dadai sauransu. Ranar se da dare ya ratsa sosai kafin suka dawo masaukinsu gabadaya ah gajiye. kwana biyu suka kara ah Paris sannan suka wuce Fiji abunsu ah *Savasi Island Resort* suka fara sauka wurin bakaramin tafiya da imanin Asma’u yayiba don inda ah hoto aka nuna mata cewa zatayi zane ne irin na artist bawai real ba aranta tadinga fadin ikon Allah ashedai akwai irin wuraren nan aduniya,trees na cocunut tako’ina gwanin ban sha’awa ga wasu gidaje da akayisu inform of gargajiya ruwan gurin ma kansa abun kallo ne gashi bangaren dasuka sauka so peaceful babu hayaniya daga su se su suyi harkokinsu yanda sukaga dama kwanansu uku ah Savasi Island Resort suka wuce *Bouma natural heritage Park,Tavauni island.* anan suka ga amaizing greenish flowers everywhere yayinda wani portion na gurin standing body of water na zuba cikin lake sannan asanda ruwan yake zuba you’ll see it so pure and white amma in acikin lake dinne kuma seka ganshi green gwanin ban sha’awa haka suka gama kalle kallensu ah gurin yayinda suka dauki hotu na masu kyau for tarihi,kwanansu daya suka bar gurin  daga Tavauni island kuma aka rankaya *Navua River,Veti levu* isar dare sukayi gakuma gajiyar yawon dasukayitayi shiyasa suna wanka suka kwanta kan washegari zasu fita boot ride da yanma aikuwa hakan sukayi nanma sunyi hotuna sosae gwanin ban sha’awa  se yanma suka koma masauki Asma’u se haki takeyi dariya Sulaiman yayi”Yana haba sister in-law sekace wanda kikayi gudu?” ….

Yar dariya tayi sannan tace”wannan ai yawo muka zo ba honeymoon ba”,dariya Almustapha yayi tareda dagata sama yana”wayene yayita korafin ba afita ah Paris?” ….

Turo baki tayi”nine”,kai bakinshi yayi cikin nata gabadaya ma yamanta da existence dinsu Sumayya agurin dan duk sanda ta turo bakinnan gaba gabadaya rikitamai lissafi takeyi, Sumayya sakan baki tayi tana kallon ikon Allah tareda mamakin Almustapha din jitayi ansa hannu anrufe mata idanunta cikin rada Sulaiman yace”haram”,daganan shima ya sunkuceta sukayi ciki…………

STORY CONTINUES BELOW


Washegari Asma’u nata korafin kada sufita dakyar Sulaiman ya lallabata”Sister in-law wuri daya yarage mujefa kuma agarinnan ne?”. Babu yanda ta’iya dole tashirya sukaje *Sigatako sand dunes* gurin bakaramin burgeta yayiba sannan lokacin ne tagane dalilin da Sulaiman din yayita maitar aje suna komawa masauki tataresu da”ammadai bawai harzamu koma gida bane ko?”….

Dariya Sumayya da Sulaiman sukayi yayinda Almustapha yajuyo da’ita suna kallon juna yace”you’ve been acting weird this days what’s wrong?”…..

Turo baki tayi”Yaya Imam mukara hutawa Allah nagaji bazan iya zaman jirgi ba harna awanni zuwa Nigeria”, massage yashigayi mata ganin tana nemar tada hankalinta sannan yace”it’s okay we’re going nowhere basai kin tada hankalin kiba”,gyadamai kai tayi feeling relieved don gabadaya kwanan nan batasan miyasaba intayi tafiya meyawa setadinga jin tashin zuciya ga yawan gajiya dasauri bayan ita she’s a very active person shiyasa haka kawai takejin zaman jirginma will be a problem for her……

Kwana biyu suka kara anan gabadaya Asma’u tacanza ma Almustapha doing some kinds of attitude dabata saba ba abu kadan masifa kotace zatayi fushi dashi shiyasa yakebinta ahankali kamar kwai arana na hudun ne tana kwance jikinshi da safe yana bata fresh milk tanasha ah baki taji amai yazo mata dasauri tatashi tayi bandaki aguje nan tashiga kwarara amai cikeda damuwa ya wanko mata bakinta yagyara mata jiki sannan yafito da’ita straight cikin kayansu yawuce yanemo mata kayan dazata saka don wata yar pingilar rigace ah jikinta yanzu. …

Tana ganinshi da kaya ta make kafada wai ita bazata sakaba cikin muryar lallashi yace”we’re going to the hospital ne Asma’u “……..
Ahankali tace”I’m fine basai munje ba don Allah”,baikulataba sema dagata dayayi yadaura ajikinshi sannan yashiga cire rigan jikinta bude baki tayi zata sakarmai kuka yayi saurin sanya bakinshi cikin nata seda yagama rikitata sannan ya kyaleta kafin yasa hannu ya tallabo fuskarta yana kallon cikin idanunta cikin rada yace”you’re sick wifey don Allah kibari muje asibiti zama hakan bazai yuyu ba and as you can see ni banida kayan aikin dubaki anan”, dakyar da lallashi dai tayarda suka je asibitin tunda suka shiga likitan yashiga yi mata Questions game da yanda takeji kafin yayi transferring nasu to wurin dazasuyi test atake akayi aka basu result kunsan yahudawa babu bata lokaci haka suka karbo result din suka dawo wurin likitan nan ya tabbatar musu da tana daukeda juna biyu Almustapha was very shocked and stunned harma yakasa cewa komai sede kallo daya zakayi mashi kagane tsananin farin cikin dayake ciki godiya yayima doctor din kafin suka koma gida itakuwa sewani sussune kai takeyi wai ita kunya suna shiga daki yajanyota jikinshi ya rungume se hawayen farin ciki ahankali yace”I love you Asma’u”….
“You’re indeed a blessing to my life”……
Thank you!
Thank you so much!

Murmushi tayi sannan tace”I love you too Daddyn Unborn”………
Dagoda ita yayi daga jikinshi sannan yayi kissing forehead dinta slowly”so all this stubbornness unborn ne kesaki yinshi ko?”…….
Turo baki tayi”kodai yake abunshi”,dariya yayi sannan yamatso kusa da ita yana shirin capturing lips dinta tayi saurin rugawa da gudu tana”wayau ko”…

Shima dariyan yayi sannan yace”to aike ke tsokatanata da lucious lips dinkinnan,they taste like Melody”……
Jijjiga kai tayi tana mamakin shi kafin yakarada and kiyi hakuri kidaina gudu you’re not alone you know”……!
Aranar Almustapha yasanar da Sulaiman cewa Asma’u nada ciki dukda kuwa hanashi datayi tayi wai ita kunya zokuga murna gun Sulaiman kaman wanda akace Sumayyan shine keda cikin rungume Almustapha yayi yana”we’re finally going to be Father’s Yaya”…..
Dariya Almustapha yayi cikeda murna shima nantake suka shiga ma juna congratulations Sumayyan ma tayima Asma’u yayinda babu bata lokaci Sulaiman din yakira su Ummi yafada musu suma murna agunsu kaman mi atake Ummin takira tace ahada ta Asma’un awaya ana bata tashiga tambayarta how she’s feeling nan tacemata dasauki inda Ummi tashigayi mata nasihohi tareda bata shawarwari,godiya Asma’un tayi kafin sukayi sallama. Almustapha yadubi Sulaiman yace”kozaku wuce Indonesia din inyaso muzamu biyo ku daga baya tunda tanuna batason shiga jirgi kwana kusa?”……
Atake Asma’un tace”I’m okay now mutafin kawai”….
Cikin rada Almustapha yace”Are you sure?”….
Gyada mishi kai tayi assuringly. Haka suka fara shirin tafiya inda Sulaiman yayi musu booking flight zuwa Nigeria shida Sumayya kuma Indonesia koda yakawo musu visa Asma’u duban Almustapha tayi tareda cewa”ba Chad zamuje muga  yan uwan su Ummi ba?”….
Hannunta nacikin nashi yana murzawa ahankali yace”sewani lokacin kuma you’re not fully okay shiyasa gwanda muwuce gida kawai”,tace “aa damunje din yafi they’re expecting us already fa babu dadi Yaya Imam”….
Ganin tanason tayi panic yace
“Calm down Dear, Ummi sunsanar dasu you’re Ill already infact Ummin ne tace muwuce gida da naso muje kasa mai albarka amma Allah baiyi ba ki hakura kawai inkin sauka lafiya basai mujeba”,shiru kawai tamishi  besides mezata ce tunda yariga yace Ummine suka yanke decision haka. Washegari suka koma gida NIGERIA tunda suka koma Asma’u ke ganin gata kama daga kan mijinta, surukanai har Ma’aikatan Masarautar ma baki dayanta don Ma’aikata na sashinta duk sundawo gun portion din ayyukansu kamar da,gabadaya takoma wata shalele kowa nannan yakeyi da’ita Almustapha kuwa kullum yana makale da’ita indai yana gida inya fita Fada kuwa yadinga kiranta kenan awaya yana tambayar lafiyarta da Babyn because cikin yadan so yazo mata da laulayi ba laifi. Intaga irin son da suke nuna mata wani sa’in tayi murmushi wani sa’in tayi hawayen farin ciki because she knows that she’s very very lucky to have them in her life bare samun mutane irinsu azamanin yanzu sai antona gaskiya shiyasa akullum addu’ar ta Allah yacigaba da hada kawunansu baki daya Itama kuma Allah yabata ikon kyautata musu kaman yanda suke kyautata mata…..

STORY CONTINUES BELOW


Cikinta nada watanni kadan Hamida tahaifi Baby girl dinta kyakyawa son kowa kin wanda yarasa ranar suna akasa sunan Ummi bakaramin farin ciki Ummin tayiba tareda addu’ar Allah ya raya yarinya cikin addinin islama. Bangaren Na’im tunda Hamida tahaihu yasake dinkewa da zuwa gidan kullum sai yazo dasafe da yanma kuma inba ya tareda Hamidan to dole babyn na hannunshi tun Hamida namai bakin hali harta bari akwai ranar data faki idanun su Afiya tahanashi daukar Islam(sunan da suke Kiran yarinyar dashi kenan) amma seya rankafo kusa da’ita cikin rada yace”wai kintaba ganin inda ake hana Uba Danshi ne?”…..
Batarai tayi tareda hararanshi sannan tace”as far as I know bakai kayimin ciki ba bare kayi claiming ‘Yata as naka so kama daina yimin irin shishigin nan”…
Ranshi yabaci matuka gajin kalamanta aiko bakomai tayi mishi kara dukda ma shima daman awasa yafadi maganar amma seyaga tadauki zafi don haka yace”indan nayi claiming ‘yarki amatsayin nawa ne kike batarai kiyi hakuri ba laifin ki baneba laifina ne da na kamu da sonki harma nakeson abunda kika haifa”,daganan yajuya yafice ranshi nayi mishi kuna Hamida binshi tayi da idanu setaji duk bata kyauta mai ba amma sebata wani damuba thinking that he’ll come back soon tunda talura bawai yanada wani zuciya baneba. Nanne nanne har sati guda babu labarin Na’im kwata kwata gidan ma yadaina shigowa hankalinta yatashi fiyeda yanda take zato,she don’t want to admit it but she surely miss him,sau tari seta dauki wayarta zata kirashi seta fasa sabida batason zubar da ajinta akwana na goman ne takasa hakuri takira layin nashi seda yakusa tsinkewa sannan yadaga dukansu se sukayi shiru kuma ganin bayida niyar magana seta sakinmai kuka Islam ma dake kan cinyarta jin tasaki kuka itama tafara nata series of kukan atake ya rude yana tambayarta ko lafiya cikin kuka tace”Ina kaine ka gujemu”…..

Yanda tayi maganar seda ta kusan sakashi dariya amma seya gimtse ta cikin sigar lallashi yace”I’m sorry to,kiyi hakuri ki lallashi Islam i don’t like her crying, I’ll be on my way”,gyada mishi kai tayi ahankali kafin ta ajiye wayar ba’ajima ba segashi yazoshi a parlour yasamu su Afiya bayan sun gaisa Amira da neman tsokana tace”lovers fight din yakare kenan Yaya Na’im?”…

Dariya yayi yanadan sosa kai sannan yace”tana Ina?”…..
Daki ta nuna mishi jijjiga matakai yayi alamar a’a ita tashiga takiramai ita don koda dinma inkaga yashiga dakin to da jamaa aciki kokuma ace yaje duba lafiyarta ne. To Amira tace kafin suka shige ciki sudin sannan suka fada mata zuwanshi saka hijabinta tayi tanaji kamar taruga taje inda yake tsabar kewarshi da tayi,samunshi tayi ah parlournsu yana zaune kan daya daga cikin royal chairs din duk ya rame,ya fada yayi wani iri dashi kamar wanda yatashi daga jinya karasawa tayi kusa dashi yayinda haryanzu Islam batabar kukan ba tashi yayi yamika mata hannu alamar tabashi ita babu musu tamika mai Babyn abun mamaki segashi tayi shiru murmushi yayi yana jijiga ta tareda yimata wasa yayinda Hamida kezaune gefe tana kallonsu adoringly har Islam din tayi bacci ahannunshi still be ajiyeta ba tana hannunshi yana kallon innocent face dinta. Hamida ganin bayida niyar magana yasata dubanshi ahankali tace”I’m sorry Yaya Na’im”…….
Dagowa yayi yana dubanta sannan yace”yawuce”ahankali cewa tayi”thank you” ……..
Tashi yayi tsaye sannan Itama tatashi tahowa yayi inda take tareda mika mata Babyn yana”kikwantarda  ita  ah daki tayi bacci”,gyada mishi kai tayi tareda kai hannunta daniyar karbanta amma da mamakinta setaji yajayota yahada su itada Babyn yarungume ajikinshi Hamida samun kanta tayi da kasa tureshi ahankali yace”I love you Hamida,don Allah kiyarda in aureki I want to spend the rest of my life with you and this little angel”…….

Shiru tayi tanajin wani irin feeling nadaban gamedashi don tasani tabbas ba kowanne namiji bane zaiyi tolerating dinta kaman yanda Na’im keyi ayanzu,nafarko itaba budurwaba shi saurayi nabiyu kuma gata da babynta wanda ba fleshy blood dinsa ba amma hakan baitasa yanuna mata wani negative impact ba to in sonda yake Mata ba genuine baneba na menene to?”…..
Tana cikin tunanin nan ne taji yakuma cewa”uhmm Ummu Khairiya say something please”……

Murmushi tayi kawai tareda dagowa batareda ta kalleshiba sannan takarbi Islam ah hannunshi tajuya daniyar tafiya cewa yayi”all these attitudes serves as yes kenan?’…..

STORY CONTINUES BELOW


Gyada mishi K
Kai tayi batareda ta juyo ba wani genuine murmushi yayi sannan yafurta kalmar alhamdulillah kafin yajuya yayi tafiyarsa. Haihuwan Hamida dayan wattanni Asiya ma tahaifi Baby girl dinta kyakyawa inda akasaka sunan mahaifiyar Mijinta Aslam Asma’u da Almustapha yaso hanata zuwa sabida yanayin jikinta amma sam taki tarikicemai harsaida Ummi tashiga maganar sannan yabari shima da sharadin tare zasujesu cewa tayi”to tayarda”,haka sukaje sunan suka dawo ranar don ya hanata kwana sam.

*9 Months later*……

Yau tunda tatashi cikinta keyi mata wani irin severe pain amma ahaka tadinga daurewa bata nunama kowaba Almustapha na lura da yanayinta yacanza haka yadinga tambayarta ko lafiya amma setace mishi kalau take at first kin shirin fita Fada yayi seda ta takuramai da he might be needed over there sannan yatashi yashiga wanka sanda yafito yagama shirin shi sannan yadauki hula yasaka tareda fesa turare jikinshi, zuwa yayi gabanta tareda kai mata light kiss ah cheeks dinta sannan ya tsuguna dede cikinta daya totso gaba yakai mata wani kiss din ah tumbinta adede wannan lokacin ne taji cikin yasake wani irin murdawa babu shiri tasaki kara wanda hakan bakaramin ruda shi yayi ba cikin sauri yashiga tambayarta lafiya nishi take tana nunamai cikinta ganin gabadaya tafita hayyacinta yasa yadauko mata hijab yasaka mata sannan ya sunkuceta suka fice hankalinsu Rukayya tashe sukabi bayansu haka koda yafita harabar masarautar gabadaya masu aiki da dogaraye hankalin su yatashi daga masu zuwa sufada ma uwayen dakinsu semasu Allah yasauketa Lafiya Almustapha bebi takan kowa ba yayi gurin mota seda yasata ah bayan motan sannan yama tuna ashefa bai iya driving ba duk wannan dimimin juyawa yayi rai bace atake kuma sega driver yazo kusa dashi yana mikamai hannu alamar yabashi key din mota harararshi yayi ya wurgamai key din sannan yabude bayan motar yashiga yadagata tareda kwantar da’ita ajikinshi yana aikin yimata sannu ahaka har suka isa bar masarautar suka dauki hanyar hospital daga driver har Almustapha sunmanta ma cewa akwai asibiti acikin masarautar kuma ma kosun tuna shi driver aganinshi baikamata akaita inda ake duba bayiba shiyasa yadauki wannan hukunci abunda baisaniba shine da ace Almustapha yatuna babu abunda zaisa yaki cewa akaita gurin tunda bayinma mutane ne nd doctors tawannan bangaren dasuke musu aiki ah clinic din specialists ne. Suna shiga asibitin aka karbi Asma’u akayi labour room da’ita Almustapha cire hulan kanshi yayi cikeda damuwa tareda hargitsa gashin kan yana karanto addu’o’i aranshi da fatan Allah yasauke ta Lafiya. Kan kacemai asibitin ya cika da mutanen masarautar kama daga kan fadawa zuwa manya manyan Fada, Sulaiman nazaune kusa da Almustapha yana comforting dinshi tareda bashi kwarin gwiwa su Ummi dasu Hajiya Muniba ma duk suna gurin alokacin ne kuma su Mommy da su Mubaraq sukazo daga gidansu Asma’u don Ummi dakanta takira tafada musu halin da ake ciki,duk sunyi zugum kowa da abunda yake rayawa aranshi can sukaji anbude labour room din dasauri gabadaya attention dinsu yakoma gurin dayake sunsan itakadai ake karbar haihuwar ta awannan bangaren dasauri Almustapha yayi gaban Doctor din yana tambayar ta”How’s my wife?”……
Murmushi likitan tayi sannan tace “Calm down ranka yadade your wife is safe and sound. She gave birth to a Bouncing Baby boy, congratulations”…..

Wani irin sanyi Almustapha yaji yana ratsa zuciyarshi slowly wallahi da ace doctor dinnan namijice kamarshi babu abunda zaihanashi hugging dinta murmushi yasaki sannan yazube kasa yayi sujjada yanayima Allah godiya kafin yataso yace”can I see her please?”…
Yanda yayi maganar cikin sigar roko seda yasa likitan dariya gyada mashi kai tayi tana Smilling”Yea,sure zaka iya ganinta”,ai bebari tarufe baki bama yawuceta tareda tura kofar dakin yashiga yarufo taciki tsayawa yayi yana kallon Asma’un dake sanye da maternity gown gabadaya ta galabaita tsabar wahala hakanan yana iya hango rodi rodin hawaye ajikin idanunta da alamun tasha kukanta karasawa yayi kusa da ita yazauna sannan yakamo hannunta yayi kissing kafin yakara dubanta”Thank you so much Asma’u,nagode Allah ubangiji yayimiki albarka”.
Lumshe idanunta tayi tanajin dadin kalamanshi kafin takwantar da kanta akirjinshi tace”Amin ya Allah”, kissing soft gashinta yayi sannan yace”Ina Babyn namu?”….

STORY CONTINUES BELOW


Turo baki tayi”Nima bansani ba”……
Dariya yayi jin yanda tayi maganar kamar wanda zatayi kuka ahankali yace”ba guduwa akayi dashibadai Matar Yaya Imam may be suna gyaranshi ne”,yana gama maganar kuwa segashi anbudo wata kofa dake cikin dakin Nurse ce sanye da uniform dinta tafito yayinda hannunta ke rike da Baby anyi mishi wanka ansamishi sutura maikyau karasowa kusa dasu tayi tareda mika musu Babyn fuskarta daukeda murmushi tace”Congratulations”……

Atare suka sa hannu suka karbi yaron so innocent and cute dashi gashi kuwa hargefe gefen fuskarshi ga shi fari tas dashi kaman kataba jini yafito Asma’u ne tayi kokarin cema Nurse din thank you dukda kuwa kanta nakan yaron haryanzu suna kallon little angel din da Allah yabasu. Fita Nurse din tayi tabasu guri Almustapha yadubeta yasake kallon Babyn sannan yace”badake yake kama ba hasken ki kadai yadauko”……..

Dariya tayi tana”to ai kaima badakai yake kama ba da Yaya Sulaiman yake kama?”….
Wara idanu yayi yace”to shi Sulaiman din dawa yake kama?”,shiru tayi batace komai ba don tasan Sulaiman din nadan yanayi da Almustapha dukda bacan sosai ba but sincerely speaking Babynsu ubansa yadauko kama daga hancin,idanun,bakin dama komai she just don’t want to admit it ne. Suna cikin haka Ummi tashigo fuskarta dauke da murmushi sannan tace”abun rowa ne kuma?”.
“Don dan nakune sekuwani kule daki kukadai Kuna kallonshi?”.lokaci daya Asma’u taji kunya ta mamayeta dasauri tacire hannunta ajikin dan tabarma Almustapha dariya yayi yana fadin”daga baya kenan Yarinya”……

Karban Babyn Ummi tayi tana fadin”Masha Allah, Allah yaraya Baby boy”……
Amin Almustapha yace inda Asma’u ta ansa aranta kafin yace”yauwa Ummi dawa yake kama sincerely speaking?”…..

Kallon yaron tayi tasan exact replica din Imam dinta ne amma setace”dawa zaiyi kama inba da Mamansa ba?”……

Turo baki Almustapha yayi sannan yace”mema yakaini tambayarki Ummi?”….
“Namanta kedin me goyon bayan Asma’u ne akoda yaushe”……
Dariya sukayi duka kankaceme su Mai Martaba da sauransu suka fara shigowa duba Babyn kowa na yaba irin kyawunsa aranar aka sallamesu suka koma gida kullum masarautar bata rabuwa da baki masu zuwa barka har ranar suna. Ranar suna anci,ansha ankuma taru sosai fiyeda yanda kuke zato koina farin ciki akeda murna inda akasama yaro suna *Abdulrahman* maisunan Mai Martaba kenan,da dare Almustapha yazo ganin Asma’u da ‘Danta wanda haryanzu tana sanye cikin kayanta medan karen tsada daya amshi jikinta zama yayi gefenta yana rikeda Babyn kwata kwata baya gajiya da kallon kyautar da Allah yayi mishi ahankali yadubeta yace”mezamuna kiranshi”…….
Tace”I don’t know wallahi suggestion dinka nike jira”…….

Murmushi yayi sannan yadago yaron yayi kissing forehead dinshi sannan yace”We’ll call him *SULTAN*”…..
Tace”nice name”…..
Ummi dakanta takira Ummin Asma’u tanayi mata maganar zuwa wankan Asma’u gida tanason taji raayinsu murmushi Ummi tayi sannan tace”tayi zamanta agidan mijinta duk dayane da ace babu maikula da’ita anan dinne setazo gida amma yanzu kotazo ma Babanta zaiyi fada yace shiba yason irin wannan al adun kinga Asiya ma gwaggon tane taje tayimata zaman arba’in yahanata zuwa gida kwata kwata…….
Murmushi Ummi tayi sannan tace”toshikenan daman nakira inji raayinkune amma in acikin dangin ku ma kunason wata tazo tayi mata zaman arba’in din she’s higly welcome”……
Dariya Ummi tayi tace” ‘Yafa takuce kuyi yanda kukeso duk dayane”, murmushi Ummin Almustapha tayi sannan tace toshikenan Allah yaraya manashi daganan sukayi sallama. Almustapha dayaji Asma’u bazataje wanka ba murna kaman yayi yaya dadinma dandai Ummi tace seyanda iyayenta sukace shiyasa ma baisaka bakiba.

★★★
Watan Sultan biyar yayi bulbul abunshi,gakyau da freshness dayaketa karawa dagashi har mahaifiyar shi tsabar hutu da kulawa dasuke samu ah masarautar,yaro harya fara kokarin yin rarrafe abunshi ga farin jini kowa so yake ya dauka yanzuma Asma’u nazaune tana samishi Pampers dan ita kwata kwata bata yarda da tabarma Bayinta aikin danta ba she prefer tayimasa komai da kanta inbadai dan abunda baza a rasa ba, acewarta tarbiyar yaro inba Uwa tasa idanu ba to gaskiya akwai matsala don kuwa bakowa ne yadamu da abunda ba nashi ba wanima ah nashin ya akakare bare azo ga yayi na wani shiyasa gwanda tasaba da shi tunyanzu yanda inya fara tashi zatasan all his moves. Almustapha ne yashigo sanye da kananun kaya da alama duk agajiye yake zuwa yayi yadaga Sultan din sama yanayi mashi wasa irin na Uba da Dansa daman already tagama sakamai Pampers din murmushi tasaki sannan tace”har angama practicing koyar motar ne nayau?”,don Almustapha yadage da koyon mota dukda kuwa yanada masu tukashin still he want to be independent……
Gyada mata kai yayi yana fadin I’m so tired zuwa nayi inyi wanka kona ji dadin jikina tashi tayi tsaye sannan tace”barina hada maka ruwan wanka to sekayi ka huta ko?”……
Alama yayimata da hannu kan tayi magana ahankali because Sultan din yafara Gyan gyadi da alama bacci yakesonyi dariya tayi sannan tashige bandaki tana jijjiga kai sanda tagama hada ruwan tafito already harya kwantar dashi kan gado tace”yayi baccin kenan?”….
sa hannu yayi ah lips dinshi”shhhhh,karki tasheshi”…..

STORY CONTINUES BELOW


Tace bazai tashi bafa Yaya Imam yaronnan da shegen nauyin baccin tsiya kanta ankara taji ya sunkuceta tana shirin magana ya hade bakinsu guri daya seda yayi mai isarsa sannan yakyaleta cikin rada yace”muje muyi wanka kada kitadamin yaro”……..
Kaman zatayi kuka tace”nifa banjima dayin wanka ba”…..
Dariya yayi”ehdai muje second round zakiyi”……..
Koda suka fito tare suka shirya dubanta yayi sannan yace”akwai maganar danakeson muyi Asma’u”,cewa tayi “to Yaya Imamu na inajinka”……

Kallonta yayi fully sannan yadaga kafafunshi yadaura akan gadon tareda folding dinsu guri daya Itama thesame thing tayi tana murmushi kafin ahankali yakamo hannunta yasaka cikin nashi sannan yace…
“maganar karatu zamuyi Asma’u,tunda na aureki baki taba kwatanta yimin maganar cigaba da karatun kiba bayan nasan yana daya daga cikin manyan burikan ki?”…….
Dariya tayi cikin sigar wasa tace”to incemaka miye Yaya Imam?”……
Serious face yayi sannan yace”ba maganar wasa nike mikiba Asma’u,i’m serious sannan inason kifadamin duk abunda yake ranki gameda maganar dazamuyi yanzu din”,still cikin sigar wasa ta jijiiga mai kai”Yes sir”……
Murmushi yayi shima sannan ya jijiga kan”you’re unbelievable you know”……
Dariya kawai tayi kafin tace”Allah dagaske to mezan cemaka Yaya Imam?”……
Tun ran gini tun ran zane. Allah yariga da yajima da kadartawa nibazanyi karatu ba bautar aure zanyi and to be sincere I’m very happy with my life now,yace aa Asma’u you still have chance inkinaso zaki iya cigaba da karatun ki babu mai hanaki besides you’re still young…….
  Cire hannunta tayi daga cikin nashi sannan takai fuskarshi tanadan shafawa ahankali tace”Thank you amma there is no need for that”….
Yace”why?”…
Tace”because karatun bazai yuyu ba Yaya Imam?”….
Yasake cewa”kifadamin dalilin dazaisa kice bazai yuyu ba?”…..

Komar da hannunta tayi kasa tana wasa dasu kafin ta sunkuyar dakanta kasa tace”atunanin ka Ina aure a *GIDAN SARAUTA* abu mai sauki ne ince zanyi karatu?”….
“Atunanin ka Ina aurenka amatsayin ka na crown prince zan tsallake responsibilities din dake kaina ne intafi wani karatu sabida son ra’ayin kaina,kaima kasan hakan bazai taba faruwaba”,dago da kanta yayi da hannunshi yana”ki kalleni Asma’u”.
Kallon cikin idanunshi tayi annanne taga how sorry he feels for her ahankali yace”kece Crown Prince din?”….
Tace”aa but I’m your wife”….
Yace”naji you’re my Wife to anma fadamin miye responsibilities dina?”,Dan shiru tayi  kamar bazatayi maganaba kafin tace”zaka wakilci Abba aduk sanda bayanan ko in ya bukaci hakan and you’ll be the next king after him”……
Yace”good”, yanzudai Ina kingane inda na dosa ko?…
Still tana kallonshi tace”but still”,sauri yayi yadaura yatsanshi akan lips dinta”shhhhh”,tsayawa tayi tana kallon cikin idanunshi cikin rada yace”kikoma karatun ki don Allah, I’m responsible for katsewar karatun ki indai har baki cigaba da karatun ba kinzama abunda kikeson zamaba bazan taba yafewa kaina ba”…..
Cikeda mamaki tace”you’re not responsible for it, you’re a victim too Yaya Imam so,why are you blaming yourself? “…..

Yace”nasani amma dai aida sunana akayi anfani akayi koma miyene sannan dabaki hadu daniba da babu wanda zaiyi tunanin hada mana sharri agurin iyayen mu har zuwa abunda yafaru yau”,gyada mishi kai tayi sannan tace”haduwata dakai Alheri ne Yaya Imam, it’s a blessing to my life sabida haka kadaina ma wannan tunanin please “…….

Janyota yayi kiiiiii kamar babyn roba tadawo dab dashi sannan yamikar da kafafunshi yajuyarda ita yasakata ah tsakankanin kafafunshi tareda sako kanshi ta wuyanta yayinda hannunshi ke zagaye da cikinta cikin rada yace”I know about that nidai kawai kiyarda zaki koma karatun ki”,turo baki tayi gaba ganin yanda yadage da maganar jin tayi shiru yasa yadanyi kissing wuyanta tareda cewa”uhmmm”…
“Kiyi magana mana”….
Jin yana neman rikitata tace”to kabari muyi magana dasu Ummi tukun”……
Sake matseta yayi jikinshi tareda fadin”munriga mungama magana dasu ke kadai akejiran jin response dinki”, murmushi tayi sannan tadan kalleshi tagefe”Yaya Imam kacika wayau”…..
Dariya yayi”just say yes”……
Tace”okay, okay,Allah yazaba mana abunda yafi alkhairi”,cewa yayi “kokefa,Amin ya rabbi”…….

STORY CONTINUES BELOW


Haka Almustapha da Sulaiman suka shiga yimata cuku cukun makaranta tareda su Amira and Afiya ah *Chicago* because suma WAEC and NECO dinsu yayi kyau matsalar jamb ne basuci ba dukansu shiyasa Mai Martaba yace akan subata lokaci suna Mata gwanda ah fitar dasu wajen suyi karatunsu acan tunda sunada halin yimasu din. sunnemi shawara gurin Na’im inda yafada musu wata institution agarin CHICAGO din yace”they’re one of the best indai abangaren Medicine ne infact har other courses ma yace inbacan ba kuma to kunema musu ah India”,atake Almustapha yace Chicago din yafi Allah yasa albarka aciki. cikin wata daya suka gama komai don Sulaiman dakanshi yaje har Chicago din yakarbo musu admission letter yayi musu registration da komai sannan ya nema musu gidan dazasu zauna acan din kafin yadawo gida Nigeria yafada musu sufara shirin tafiya in the next 10 days jirginsu zai tashi don haryayi musu booking flight bada private flight din Abba zasu tafiba tunda ba ranar dawowa cewa sukayi “to” nan suka shiga shiri babu kama hannun yaro, Sumayya dai gabadaya wani iri takeji don batason sutafi subarta ita kadai ah gida ga tsohon ciki haihuwa yau ko gobe amma babu yanda ta’iya besides mezata je tayi tunda ita tagama nata karatun?………

Daman Hamida ne mezaman Itama kuma aurenta da Na’im ansaka rana yanzuma sauran sati dayane yarage meaning immediately after bikin su Asma’u zasu tafi by then kuma Hamida will be at her husbands house so she’ll be alone……

Ranar dasu Asma’u zasu tafi dasafe angama saka kayansu ah mota za ayi masu rakiya zuwa airport sede cikin yan rakiyan babu Almustapha dan Mai Maitarba yaturashi yayi representing dinshi awani taro daza ayi ah *Giwa* gashi goma za afara taron dole yatafi dawuri. Yana rikeda Sultan yadubeta sannan yace”take very good care of him and yourself please”….

Kaman zatayi kuka ta gyada mai kai sannan tace”you too ka kula dakanka don Allah banda wasa da abinci”,dariya yayi sannan yace”nakoma little Boy yau Mommy Asma’u is lecturing me”,dan bugun kirjinshi tayi playfully sannan tace”kai naga kamar bakadamu da tafiyar nan bama”,sekuma ga hawaye suna zuba ah idanunta cikeda damuwa yace “Ya ilahi, Asma’u wayafada miki bandamu ba?”….
I’ll miss you more than anyone inkuma baki yarda ba to zaki gani aikuwa tafiyarsu da sati segashi yazo Chicago yanata rawar jiki nan tagane sarauta ce kawai tahanashi nuna kewarta dazaiyi asanda zata taho din kokuma kilan alokacin bayason nuna mata damuwarsane don kada nata hankalin yatashi dakyar ta lallabashi yadawo gida Nigeria daganan kuma tamaida hankalinta sosai kan karatun ta don aganinta batada damar yin wasa tunda gata iya gata surukanta da mijinta sun nuna mata and the only thing she’ll pay then with shine tamaida hankali tayi karatu tafita da result mekyau. batasha wahalar rainon Sultan ba donkuwa suntafi da Rukayya baiwarta wanda duk cikin bayi tafi aminta da ita sannan su Afiya ma ai department dinsu badaya ba so time din lecture dinsu yaban banbanta shiyasama wani sa’in take barmusu shi agida if suna free inkuma dukansu zasu tafi seta tafi da Rukayyan tayimata rainonshi. Kowani karshen wata Almustapha yake zuwa duba su yayinda in anyi hutu sukuma sesuje gida,hutun karshen shekara dasukaje ta takura mishi kan sujesu Chad aikuwa haka sukaje sukayi musu sati biyu bakaramin dadin zuwansu mutanen Chad din sukayiba kuma Ummi ma taji dadin hakan sosae kafin suka juyo gida Nigeria. Sanda suka gama year two zasu shiga three Almustapha yashiga neman admission shima waizaiyi furthering karatun shi seda yagama kammala komai sannan yasamu Mai Martaba da Dad yafada musu Mai Martaba yace”Imamu basai ka boyemin ba kafito kacemin zakabi matar kaman bazan hanaka ba”….

Cikeda kunya Almustapha ya sosa kanshi sannan yace”harda karatunma zanyi Abba”,dariya Dad damai Martaba sukayi sannan sukace”Allah yataimaka wannan abune maikyau dazai anfane ka damu bakidaya”,Dad yace “barema karatu azamanin yanzu is never a waste”…..

Haka suka tattara suka koma tare Asma’u nata tsokanarshi yace”Yarinya harda ke na taimaka fa wayasan how many sleepless nights kikayi thinking about me?”….
Dariya kawai tayi tana karajin sonshi na ratsata daman gidan dasuke part biyu ne dayana Almustapha wanda Sulaiman ne yayi wannan dabaran tunda zaina zuwa sannan daya kuma nasu Afiya din to anma dukansu anasu Afiyan suke zama harda Asma’un seyanzu dasuka dawo da Almustapha bakidaya yasa ta tattara takoma bangarensa itada danta. Dun karshen wata Almustapha seyaje Nigeria yaduba masarautar dama iyayensu baki daya and on the other hand Sulaiman nanan handling everything with his parents don yanzu yamaida hankalinshi kan masarautar bakidaya tunda iyayenshi sun nuna hakan suke so Sumayya ma nanan da Baby boy dinta mesunan Dad ana kiranshi *Asad* yayi wayau sosai abunshi,Hamida ma tasake samun wani cikin bayan Islam tananan haihuwa yau ko gobe adede wannan lokacin ne kuma *Amaaan* yadage shifa yanason ayi aurensu da Afiya kwana kusa don tuni su Mai Martaba sukasan dashi aikuwa nan yaturo iyayenshi akayi masu tarban mutunci aka bayar atake tareda saka ranar biki December me zuwa lokacin suna hutu sannan karshen shekara almost kowa yana hutu agida, Mai Martaba yace”naso hada auren Afiya da Amira amma Allah baiyi ba kowa da nashi lokacin don ita nata mijin baifito ba bazan tauye ma Yar uwarta hakkinta ba Allah yasa hakan shiyafi alkhairi”…
Su Dad da Mallam Hudu cewa sukayi”Amin”,bangaren Amira kuwa ko akwalar rigan ta don already sunyi da masoyinta seta gama karatu barema da yanzu suka zo gangara shima kuma yana Masters dinsa daman yace”insun gama duka se ayi bikin anutse sabida shi bayason ya katse mata karatun ta and tabbas indai akayi auren to ba lallai bane iyayenshi subari ta karasa tunda *GIDAN SARAUTA* ne suma while on the other hand Amaan is a stable mutum yagama karatunsa harma yana aiki. Bikin Afiya anyi shagali sosai dakuma events kala kala sannan anyi walima ma inda aka gayyato babbar Malama tayi wa’azi sosae kan zaman takewar aure wanda ya ratsa zukatan mata da dama daganan akawuce da’ita Chad gidan surkananta kan inta kwana biyu se suwuce Egypt da mijinta tunda acan yake aiki yanzu dukdama yace yanason yadawo nan gida yayi aikin sa yafi anma seta karasa karatun ta inyaso sesu dawo bakidaya…….

STORY CONTINUES BELOW


*TWO YEARS LATER*

Katon hall ne ke makare da mutane da dama yayinda daya daga bangaren hall din dalibai ne kesanye da convocation gown dinsu gwanin ban sha’awa hakanan kallo daya zakayi musu kagane irin tsantsan farin cikin dasuke ciki,kan stage din kuwa dinbin malamansu wanda duk suma fuskokin su na daukeda annuri yayinda sauran sashin gurin kuma iyayene da yan uwa da abokan arziki dasukazo taya yan uwansu murna wanda ciki kuwa harda su Mai Martaba, Ummi, Mom,Dad da Hajiya Muniba,Amira sekuma Sulaiman da Sumayya dake zaune can gefe daya inda two little princes da kansu kusan daya sunata tumurmusa akan cinyar Sulaiman din yayinda Sumayya kuma kedauke da jaririya ah hannunta da alama ba ajima da haihuwarta ba…………….

Gani nayi daya daga cikin yara biyun yadubi Sulaiman tareda cewa”Daddy kaga Yaya Sultan yana mintsinina ko?”……
Sulaiman daya gaji da rigimarsu yadubi Sultan sannan yace”Sultan?”…..
Kanma yarufe baki Sultan din tace”Allah Daddy shiyafara neman tsokana na”,kama hannunsu Sulaiman din yayi yahada guri daya sannan yace”it’s Okay Boys tsaya kuji”…
Little king ansanshi da fada ne?’…..
Dasauri Sultan yagirgiza kai, Sulaiman yace yauwa good Boy,”to shi little prince ansanshi da neman tsokanan nagaba dashi ne?”………
Nanma dasauri *Asad* yadaga kanshi alamar a’a, murmushi Sulaiman yayi sannan yadaga su duka yadaura akan cinyarshi kafin yace”Oya little Prince should apologize to the little king?”……

Asad na hararan Sultan yace”I’m Sorry Yaya Sultan”…..
Gyada mishi kai Sultan din yayi alamar ya hakura kafin Sulaiman yasake cewa “to the little king should also apologize ko?”…..
Murmushi Sultan yayi sannan yamika ma dan uwannashi hannu yana fadin”I’m sorry Asad”, Asad dinma wannan karan sakar fuskarsa yayi, murmushi Sulaiman yayi yana kallonsu so lovingly shikanshi yasan Sultan baida rigima kamar Danshi Asad, Sultan nada hakuri da saukin kai even at his young age gakuma rashin magana da miskilanshi, ahankali Sulaiman yashafa lallausan  suman kanshi kafin yace”he’s just like his Father”……

Jiyayi anfara magana tacikin microphone don haka yamaida attention dinshi bakidaya kan podium nan aka fara program din wanda shine main purpose na taron duk dumbin jama’an dake gurin,anyi welcoming guests ankumayi speech sosai gameda graduating students din yayinda wasu daga cikin daliban da basu gamaba sukayi presentation game da bangararruka da dama kafin akayi congratulating new Doctors wanda they went through alot of struggles kafin suka kawo matsayin dasuke ayau ciki kuwa harda Asma’u Muhammad inda aka bata best  graduating student sabida irin kwazo da kokarinta sanda aka kirata stage dakyar ta’iya tashi sabida irin nauyin da cikinta yayimata dakyar ma take iya takawa tana sanye da convocation gown dinta gwanin ban sha’awa don kowa yaganta seyaji ta burgeshi despite she being married hakan behana ta yin abunda yakawo ta makaranta ba sannan hakan baihanata achieving goal dintaba, Almustapha da baya yarda yayi nesa da ita yataso  daga seat dinshi dake kusa da graduating students din yazo yakama hannunta yana taimaka mata harsuka isa kan stage din yayinda yake sanye da hadaddiyar suit datayi matukar karbar shi donkuwa babu Macen dazata ganshi agun tace be burgeta ba hakanan duk wanda yaganshi tareda  Asma’un seyaji sun matukar burgeshi wasuma daukar su hoto suka dingayi because one look zakayi masu kagane irin tsantsan kaunar da sukeyima juna. Envelope vice Chancellor din yamika mata tareda yimata congratulations sannan yakarada”she’s indeed an examplary woman to all the women in the world”…..
“I Salute you Asma’u”,cewar Vice Chancellor din tareda daga mata hannu alamar girmamawa murmushi tasaki feeling as if she’s the luckiest woman on earth sabida tasan ba effort da dedication dinta bane ba kadai harda support din mijinta, family dinta dakuma Allah which is ahead of everything, without prayers and determination tabbas tasan bazata ma ganta anan ba ahankali tafurta”Alhamdulillah”….
Murmushi Almustapha yayi sannan shima yace”Alhamdulillah Ummu Sultan”…..
Se suka saki dariya dukansu biyun wanda yayi melting hearts din mutane da dama dake agurin. Sunyi hotuna sosai da yan uwa da abokan arziki kafin suka kwasa suka koma gida don suhuta sabida dukansu sungaji anyini ana didima………..

STORY CONTINUES BELOW


Kwanansu biyu ah Chicago suka tattara suka koma NIGERIA daman Almustapha yariga Asma’u kammala nashi karatun su Afiya ma tuni suka gama tunda sudin normal courses sukayi, Afiya kam harta koma Chad tareda Amaan tsohon cikinta nema yahanata zuwa convocation dinsu Asma’u din,auren Amira ma ansaka date nanda watanni biyu insha Allah se shirye shirye sukeyi don ko kafin su Ummi sukaraso Chicago seda sukabi Dubai sukayi sayayya tukunnan………

Sanda suka iso gida Sultan yaga ana sauko da kayyayakinsu masu yawa yadubi Almustapha din sannan yace”Abeey bazamu sake komawa Chicago bane?” …..
Murmushi Almustapha yayi sannan yashafa kanshi playfully ahankali yace”zamu sake komawa anma sede in hutu kawai yanzu zaka dawonan da makaranta” …
Turo baki Sultan din yayi yanada maganar fada amma miskilanci tahanashi shima kuma Baban yagane yaron nada magana ah bakinsa amma shima miskilancin bazai barshi yatambaya ba…………..

Satinsu biyu da dawowa Almustapha yahada mata walimar zama full Medical doctor wanda antaru sosai dan harsu Asiya seda sukazo daga kaduna Itama tasake haihuwa har yara biyu abunta,Aliyu ma da amaryarsa yazo duk sun manyanta kowa da family dinshi bata tashi mamakiba seda taga Zahra da tajima basu haduba don sunyi loosing contact din juna kuma akwai zuwan datayi last year tace bari tagwada zuwa gidansu anma se akacemata ai tayi aure ah Gombe cewa tayi Allah yasanya alkhairi kawae sannan tadawo gida abunta without collecting her digits don aganinta koba komai Zahra na’iya kaiwa invitation gida tunda tasan gidansu and she’s sure za akira afada mata amma batayi hakan ba setayi tunanin to maybe batason friendship da’ita ne, murmushi tasakar ma Zahra yanzu suka gaisa cikin aminci batareda ta nuna mata komaiba don ance bakon ka annabinka ananne Zahran ke fada mata auren anyishi unexpected ne don Itama bawai tanaso bane,tace auren dole akayimin shiyasa banfada mikiba..

Murmushi Asma’u tayi sannan tace”bakomai Zahra, amma zanbaki shawarar indai mijinki baida matsala kiyi zamanki kiyi hakuri may be this’s your destiny”…..
Feeling guilty Zahra tace”bawai baiyimin baneba bakuma banason shi baneba sede nidin banason inzamanto cikin kawaye masu cin amana Asma’u”,sai kawai tasaki kuka tuni Asma’u tarikide tana bata hakuri”Zahra meyayi zafi haka,sokike kitaramana jama’a aje ana gulma anacewa gantsareruwar likita dake kina kuka, it’s unlike you please kidaina”, Asma’u tayi maganar cikeda damuwa cikin sheshekar kuka Zahra tace kinsan wa aka aura min kike wannan maganar?…

Kai tsaye Asma’u tace”bansaniba wallahi sekin fada”….
Cikin kuka Zahra tace”Mukhtar,Dr. Mukhtar dinkifa Asma’u”……..

Take kan Asma’u ya kulle tace wani Mukhtar kuma,cikeda takaici Zahra tace”your first boyfriend”,se lokacin Asma’u tafara tuno rayuwarta nada waifa ashe tataba yin wani saurayi mai suna Mukhtar lallai rayuwa kenan soyayyar Mijinta yasa tamanta da duk wani namiji daya taba shigowa rayuwarta. Murmushi Asma’u tasaki sannan tace dagaske shi kika aura?….

Kallon yanda take murmushi Zahra tayi cikeda mamaki sannan tace”eh shifa ashe Babanshi abokin mahaifina ne so bamutaba sanin hakaba se bayan rabuwarku ranar Abbanshi ya aikeshi wurin Baba nan yaganni daganan kuma yadinke dazuwa gidan mu haryafara nuna interest akaina nibanta ba bashi chance ba sabida gani nake kamar yazama yaudara, I’m a true friend to you kuma bazan taba son inyaudarekiba shikuma yanace don yalura ina sonshi I’m just backing off sabida kene ahaka dai haryanuna ma iyayen mu yana sona sukuma suka hada auren dukda raina bayaso, bawanda nafada ma Asma’u,I felt guilty and I’m still feeling thesame way haryau nakasa bama mijina rights dinshi as a husband anma ahaka Mukhtar yake hakuri dani kullum maganarshi Allah yanuna mishi randa zaku hadi yakawo karata gurinki nikuma babu abunda nake tsoro irin yakawo karantawa because ni aganina I’ll loose a great friend like you shikuma gani yakeyi you’ll bring me back into my senses bayan bahaka baneba,I don’t want to loose you Asma’u shiyasa nazo dakaina don infada miki because Yarima yatura min invitation na walimarki ta email Ina and I saw it shine nafada ma Mukhtar din shikuma dagudu ya amince muzo din”……

STORY CONTINUES BELOW


Zungurinta Asma’u tayi sannan tace”Amma fa bakida hankali Zahra,tukunnan intambayeki ma?”…

Shiru Zahra tayi ganin yanda Asma’un ke reacting unlike yanda tayi zato,tace kinason “Yaya Mukhtar?”
Shiru Zahra tayi,zungurinta Asma’u takumayi playfully sannan tace”kifadamin mana don Allah”….

Saukar dakanta kasa tayi cikeda kunyarta sannan tace”inason shi,so mai tsanani”……
Janta Asma’u tayi tarungume sannan tace”then you can have your husband, he’s all yours Zahra I’ve mine too sannan bana wasa da harkokin sa sabida Ina tsananin sonsa,tunda can bason Mukhtar nakeyiba inxaki iya tunawa besides auren hadi akayi muku Allah yariga da ya kadarta ke matarshi ce,kidaina yima Yaya na hali don Allah and moreover banason kina kwasan zunibi gurin Allah sabida duk mace data guji mijinta Allah yana fushi da’ita,kikoma gareshi kinemi yafiyarshi kuzauna lafiya abunku….
Murmushi Zahra tayi sannan tace”Are you sure”,zungurinta Asma’u takumayi tana dariya”no I’m not”…….

Aikuwa harcikin gida Mukhtar din yazo suka gaisa yanata fadin *Ranki shi dade* dariya tayi sannan tace”Don Allah Yaya Mukhtar kadaina sani jin kunya”,shima murmushin yayi sannan yashiga tambayarta ya bayan rabuwa kafin daga karshe yace”nakawo karar Matata gurinki,tundaga Gombe nayi tattaki nazo”…….

Murmushi Asma’u tayi sannan tace”karkada mu matarka tagane laifinta dan dakanta takawo karan kanta so,mun warware komai insha Allah kuma bazata karaba”….
Yace”dagaske kike?”,yayi maganar with so much excitement on his face tace”gatanan ai kunfi kusa”…..

Kallonshi Zahra tayi sannan tasakar mai murmushi babu shiri yatashi tsaye”tashi mutafi masaukinmu”….

Dariya sosae Asma’u tayi sannan tace”aidai kabarta zuwa anjima ko”…
Yace”to da anyi maghrib zanzo indauki abata”…..

“Allah yakaimu Asma’un tabashi ansa”…
Yace Amin kafin yafice yabasu guri fuskarshi cikeda annuri……

Aisha ma tazota ranar Asma’u dai murna kaman tayi yaya don taga mutane da dama datajima bata gansu ba don wasu ma harta fidda ran sake ganinsu. Ashe bayan tafiyarsu anyi renovating clinic din masarautar angyarata sosai tareda expanding dinta inda akasake introducing sabbin wards sannan ankaro kwararrun likitoci wanda ayau akayi launching hospital din sannan ayau aka fito da prisoners din masarautar wanda sunjima suna serving punishment dinsu ciki kuwa harda *Talatu* takara girma takara tsufa gakuma wahala da tayi mata yawa Asma’u data ganta seda tayi hawaye sannan tajata jikinta tarungume tareda cewa”Iya Talatu kizauna taredani please,inason kizama daya daga cikin yan Amana na”……..
Kuka Talatu keyi sannan tace”ke yarnan akullum rama mugunta kikeda alkhairi, Allah dai ya albarkaci rayuwarki da Ya’yanki”…..

Cewa tayi Amin tana goge nata kwallar Itama……..

Zuwa dare kowa ya watse Asma’u tayi lilis tagaji ga cikinta medan karen bata wahala dakyar ta’iya tayi sallar isha’i kafin tashiga tayi wanka tasaka katuwar rigar bacci kasancewar cikin dake jikinta,Sultan already yayi bacci ah bangaren su Sumayya daman haka sukeda Asad kamar tip da tire inwannan nanan to zaka samu dan uwanshima agurin………..

Hijabinta tasaka sannan tawuce dakin mijinta samutayi yanata rubuce rubuce cikin wani takardu……..

Jin footsteps din mutum ne yasashi dagowa yadubeta sannan yace”Yauwa Dear zo kiga yanzu nake shirin kiranki daman”…….
Zuwa tayi tazauna kusa dashi tana”yaudinma bazaka huta ba Yaya Imam?”……
Kamo hannunta yayi yasaka pen cikin hannun nata sannan yamika mata wasu takardu yace”your signature”…..
Dasauri tace”na menene?”…..
Yace”bakiyi trusting dina bane?”,kallonshi tayi sannan tasaki murmushi”I trust you, infact more than I trust myself”……
Yace”then kiyi signing”,babu musu tasaka hannu tayi signing ah inda ake bukatar signature dinnata sannan tasake mikamai littafin yace….
“no keep it with you na asibitin ki ne”……
Wara idanu tayi”asibiti nafa kace”…..
Gyada mata kai yayi sannan yace”this’s my gift for you, congratulations Doctor Asma’u”,tsayawa tayi kawai tana kallonshi da mamaki don she’s just out of words gani takeyi words basu isa su nunamishi how much grateful she’s to have him as a husband ba”,ganin tayi shiru and she’s starring at him seyace”go through the documents”…….
Sekuma tafara budewan kamar wata wawiya aikuwa sunanta tagani barau barau akai,sunan asibitin ma sunanta ne murya na stammering tace”I don’t even know how to thank you Yaya Imam,don Allah kafada min dawani baki zanyi maka godiya”……
Dariya yayi ganin yanda tadauki abun seriously sannan yace”just one kiss is enough”……
Bugun kirjinshi tayi playfully sannan tashige jikin nashi tana fadin”kaiba”…..
Rungumeta yayi yana fadin wai yaushe twins dinnan zasu fitone nikam?…

STORY CONTINUES BELOW


Kin kulashi tayi sema cewa da tayi”thank you, Allah yakara budi, Allah kuma yabiya maka bukatunka naduniya dana lahira”…
Yace”Amin Matata,bakice Allah yabarmu tareba”……
Tace”insha Allah only death will do us apart”,yace Amin ya rabbi………

Dago da’ita yayi sannan yace”kinason asibitin yazama private ne kokuma free?”……
Tace”duk decision din da kayi daidai ne”,jan karan hancinta yayi sannan yace”asibitin kine banawa ba Asma’u”…..
“Aa namudai,nidakai duk abu dayane”,dariya yayi sannan Playfully yace”Kuma fa hakane anmadai dukda haka kifadi raayinki”……….
Sake kwanciya jikinshi tayi sannan tace”nidai anawa shawaran mubarshi ah private hospital tunda kayi free har guda biyu ga na cikin masarautar nanmma free ne to why not mugwada business dawannan din inyaso in munsamu ribar damukeso semu fara wasu business din apart from hospital work kaga yanzu duniyar nan you can’t just be seating without being independent tunda sarautar ma da da takeda guarantee yanzu batada shi,gashidai right dinka ne amma se ah tauye maka shi. Sunusi lamido is a very good example Yaya imam yataba tunanin zai wayi gari bayakan throne?…..
Betaba but in the end that’s what happened we’re in a world where kowa yanda yaga dama yakeyi shiyasa we should always be ready for what is to come dukdama bamwa fatan hakan ta faru but Incase tafarun we should prepare for it. Bafata nakeyi ba kuma bawai inaso hakan tafaru baneba anma yau in akace anyi dethroning din Abba kenanfa sarauta ta Kare ah hannun mu?….
Where will we go?
Zamu kwashi property din masarautar mutafi da itane dukda ma wasu abubuwan mu mukayi?..

Ya girgiza matakai alamar a’a,tace to kagani we’ve a very big family dole munayin abu da tunani dakuma yanda zaiyi benefiting kowannenmu…
Tunda take magana yatsura mata idanu harta kai karshe ahankali yace”what will i do without you Asma’u?”….
“Where will I be?”…….
Dariya kawai tayi tana kallonshi adoringly, ahankali yace”kina gani kaman wasa ko?”, seriously life without you will be so difficult because you’re my strength Wife, you’re my support and moreover the love of my life infact  akomai ma kinyine Asma’u!….
You’re the best in my eyes,yanda yayi maganar seda yasake sata sakin wani dariyan,dan numfasawa yayi sannan yadagota daga jikinshi suna kallon juna,matso da fuskarshi yakumayi daf danata harsuna jin numfashin juna sannan cikin rada yace…….

_”do you know that:If beauty had a name,it would be your name_?”
_If innocence had a face, it would be your face,_ 
_If love had a description,it would be your life and then If I were to fall in love again and again,it would be only and only you Asma’u!_”….

Batasan sanda hawaye suka fara zirara ba daga idanunta ahankali yasaka bakinshi yana lashe hawayen tareda cewa…
“ke miyasa kuka baya yimaki kadan ne”…..
Ashagwabe tace”you just keep surprising me dole inyi kuka”, murmushi yayi tana shirin sake magana yayi saurin hade bakinsu guri daya don yasan baiwuce tace zata gode mishi baneba and shikuma bayason haka…

ALHAMDULILLAH indeed everything that has a begining must surely have an end. Nan nakawo karshen labarin GIDAN SARAUTA duk laifin danayi ciki Allah ya yafemana baki daya sannan kada Allah yaba ku ikon daukan wannan laifin amatsayin daya daga cikin darasin daya kamata kudauka ah littafin wurin daya dace adauki darasi Kuma Allah yabada ikon dauka din sannan Allah ubangiji yabamu ladan tare……….
Amin summa Amin…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *